[Advertisements⬇️]

KANDALA CHAPTER 2 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

KANDALA

CHAPTER 2
Muga… lok’acin da ya karanta sai da gumi yantsitto masa, waya kawo miki takardar? +

” k’ande ka aiko aikasani…

” k’ande? K’ande?? k’ande Kina nufin ita takawo miki wannan takarda!

” tabbas ita takawo min domin har tukwici na bata!

” to wallahi ne Abbas bansan da zancen takardar nan ba sharrin k’ande ne abunda tayiwa kabiru shi taso tayimin,ina neman afuwar matata da kuma hakuri…

” karka damu mijina na kwanan nan nayarda da maganar mutane dasuke fadin k’ande ta dabance…

 ” sai anjima abbas bai tsaya ko’ina ba sai kofar gidan su mahaifin sa yatarar sannan yace barka da rana baba!

    ” aa abbas mai ke faru naganka sai huce kakeyi Allah yasa dai lafiya!

   ” ina lafiya gaskiya abunda k’ande takeyi a kauyen yanan har ya zagayo kaina kalli takardar nan!.
   
  ” bani nagani, lahhh Aishatu kenan yarinyar kirki haba Abbas wasa tayiwa dija gala, ku dinga yi mata uzuri tunda kunga yarinya ce fa!

   ” haba baba kande ce yarinya wallahi sai na hukunta ta!  Goggo fito kigane fito!

   ” me kuma yafaru abbas?

   ” kalle takardar nan!!!

” oh ne yarinyar nan abunta gaba yakeyi kabari sai tashigo kasata agaba ka zane ta kai idan yakai da karaya ma duk kayi mata ta maidaku sa’annin ta!

   ” kai abbas indai ne mahaifinka ne karka sake kayi mata komai…

     ” goggo cikin masifa tace aine uwarta ce dole nace ubanta!

    ” babane yabar gidan yana fita sadiya ta tawo tana kuka!

    ” me kuma yafaru?

” k’ande ce ta zane ni a makaranta wai dan munyi fada da kawata, baba kalle bakina yadda ya kumbura!

    ” wai sadiya bakisan hakuri bani? Ai hukunci tayi miki shige gida malama…

   ” goggo tayi salati na banu na haifi annoba da kaina shiga ki huta ne nasan me zanyi!

    ” salamu alaikum ina kwana goggo?

   ” lafiya lou lafiya ladi?

” k’ande ce tace bashin gyadar hamsin nace ta biyane tace ai babata tauye sukili takeyi dan haka bazata bani ba!

   ” goggo tace ai da saiki jata kiyi mata dukan tsiya ki daki hamsin dinki!

   ” wallahi k’ande ta dabance ki duba marin danayi mata, gashi tarama hakorina har rawa yakeyi…

   ” ya abbas yace amshi hamsin dinki!

Iya habu kinsan yau nafi kowa farin ciki, yanzu burina insamu in tafi birni wallahi..

    ” k’ande kenan wannan birni baza dai ki rabu dashi ba?

   ” ta yaya zan rabu da birni yaya haruna mahaukaci ma yatafi burni, yana can yana yimusu hauka!..

    ” k’ande dan uwanki ne fa!

    ” dan uwana ne sai akace na boye abinsa, ai wannan dan nake ko aiki baza’a dauke shi bafa! Sai dai zaman bola..

    ” haka kike gani amma haruna yahuce tunanin ki!..

   ” ta’ina? Ai degree din da yayi ta watse tunda yazama tababbe! Kinga iya habu yau zanje karatu babban kauye bari naje gida na dura musu abinci nadawo…” Allah ya shiryeki k’ande! +

    ” ameen! Harda ke iya habu!

    Tana tafiya tana yar wakarta sukayi karo da wani yaro nan ta daga hannun ta ta wanka masa mari kai uwarka bata koya maka tarbiya baniba?

   ” kiyi hakuri bansani ba…

      ” mtseew bari na kwashi maka kyadar ka, kuma ka cewa babarka ta dinga soya gyadar tana soyuwa…

    ” Aguje ya ruga Allah ya’isa muguwa..

   ” da daddare zanzo har gidanku banza mai kan jimina!

   Tana isa kan dakalin gidan su tace Alhaji baba hutawa kakeyi?

   ” eh aishatu yau banson zuwa gonar!

   ” ai gwara kadinga hutawa wai baba kai da iya habu babarku tahaifa ne?

   ” aa munada dan uwa hassan..

    ” hmm amma gaskiya baya sonku bana ganin yana zuwa…

   ” har zai sanar da’ita abirni yake sai kuma yayi shiru dab yasan kadan da aikin ta tace sai taje!

   ” to baba bari natashi na dura sanwa Allah ya gyara zumuncin ku…

   ” toh yar albarka..

” baba ya abbas yana gida..

   ” anya kuwa dazu naganshi bansan yanzu ba! Me kikaye masa…

   ” nan da nan tayi shiru sannan ta hado wata karyar uhm dama irin wasan nan nayi masa na kanwa da wa!

    ” ohooo ai yanada kyau…

      ” tana shiga soro taga sadiya ta jingina da bango, hahaha mai gyada irin wannan libe haka, kike kallona da kun nanki kamar na saniya ga baki yayi miki ganda kamar na  rubabbeyar ganda!…

   ” sadiya kallonta kawai takeyi har ta karasa ciki! Yaya abbas budurwar kace ta mutu kayi tagumi haka?

    ” nan mama farida tace naga mijin da zai kwashe asara! Allah ya taimaki haruna ba ahadashi da annoba ba!

    ” kece babbar annubar ke kin manta da yadda akayi aurenki gidanku fa masu bakin jinin jakai akece muku!

   ” ni kike gayawa haka?

   ” nafada ke wacece?

Wallahi zan sumar dake?

   ” kin dade baki sumar ba zoki sumar danAllah dama ku anyi muku tambari da yan daba…

    Lah k’ande tunda kike cacar baki da farida kice nema zakiyimin!

    ” abbas rufomin kofar nan, kinyiwa abba, kin yiwa mai aya, kin yiwa kanwarki, saura mu ai…

    ” wane mahaukacin mari abbas ya zuba mata batasan lokacin datayi kasa ba!..

    ” Ne zakiyi wa sharri? Shigeya jahila mai kama da fuskar jaki!

    ” nan goggo ta rufeta da duka ta dauke ice tana duk’anta, k’ande in banda kuka babu abunda takeyi…

   ” ki kyaleta haka goggo karki nakasa ta!

   ” ai gwara ta nakasa da nabarta haka babane ya shigo aguje ya tankada goggo menene haka yar taki?.. 
  ” da ita gwara babu, wannan yarinyar ta dabance duk yayana babu mai halinta to wallhi nakara jin kinyi wane abun gida yari zan kaiki!

    ” babane ya dauketa har dakinsa..

Kuka takeyi sosai, baba mai is goggo bata sona acikin ‘ya’yanta? ” Lokacin d’a muna cikin amarci mahaifiya ta sam bata kyale goggo ba, ta takura mata sosai hatta abinci in ta dafa sai ance tayi barbade, haka shekaru suka dinga tafiya har aka haife ki, Nan goggo tace sunan mahaifiyar su za asaka wato sadiya, Nan mahaifiya ta takada ta raya alallai sunanta za’asaKa, tunda ganan goggo ta fidda rai dake bata kullum kukanta kada kiyi halin sirrikar tata… +

   ” wata rana goggo ta gama girke sirikar tata tafito tace lallai sai ta sake wane, tana bata hakuri Amman sai ihu takeyi mata, k’ande ce ta shigo lok’acin bak’ifi shek’ara takwas ba, inna lafiya kike ihu ana jinki har awaje? Nan kik’a juya k’an goggo k’ik’ace goggo menene? 
  ” bakomai k’ande, Nan inna tace wai bazaki tashi ki chanja ba?

      ” kinje tsuhowa k’in k’usa mutuwa sai shegen fi’ilin tsiya aik’in kawai malam, wallahi bazatayi ba, kinkusa mutuwa ki bautawa Allah kin tsaya mugun hali, wallhi kika kara sakata sai Na hada miki mugunta sosai.. ” lallai k’ande tun kina kara?  ” tsohuwa kamarki ma tayi ballantana ne yarinya, ” ai yayyen ki ma basu isa ba, ” su kikace Amma ne ta dabance…

    ” tunda lokacin abubuwa suka fara sauya wa har Allah yadau ranta!!!

    ” nan goggo tace ai kin ibo halin tsiya irin nata….

        ” kayi hakuri kaje baba nadaina fitina…

     ” bazaki daina fita ba har sai kinyi karatu mai zurfi shiyasa nayi miki kwadayin haruna yaro ne mai mutunce!

    ” mahaukacin baba!

” ai ba da hauka aka haife shi ba samun haukan yayi anan duniya kuma zai warke!

    ” kazamine, kuma baya sallah gashi mugu idan kuka auramin shi ya zani ne fa shikenan sai kukaine asubuti ne da jin zafi ku da sannu!

    ” ayer ayer haruna yafi karfin k’ande wazai aure ta!

   ” baba ransa a bace yace karki kara saka mana baki in muna magana!

   ” haruna dakike gani yaje garuruwa da dama kuma yanada degree dinsa! Ke zancen sallah kuwa tun yana karami akayi masa shaida, kuma kowa yasan babu ruwansa, kuma bazai dauwama ahaka ba…

    ” kuka k’ande tasaka baba ta yaya za’ace yafe karfina bayan nafishi hankali…

   ” Akwai abubuwan da nakeso kesani cewa ita rayuwa ta muminai ce in kina kyautatawa bayin Allah, to kema Allah zai taimaki ki, kiso mai sonki ko da bai kwanta a zuciyar ki ba, domin kiyayya babu dadi…

   ” tohm ya mahaifina ina sonka babana komai daran dadewa zan zama mai taimakon al umma!

   ” inane yake yimiki ciwo yanzu?

   ” kafata ce..
  
  ” zanje gurin ta mai magani yanzu na dawo…

BIRNI

   Haruna ya samu cikakke yar lafiya, yauma kamar kullum yayi wankan sa yasaka wane yadi sai da yayi sallar walha sannan ya samu guri ya zauna!

  ” hajiya da dady suna palour suna hira Firdausi ta fito fuskar ta ciki da murmushi!

    ” har kun tashi?

” yes dad yau bamuda lecture, dady mota ta wallahi tafara lallacewa ka siyamun wane mana!

   ” in kinyi kokari a skull zan siya miki shiga kikira mun yayanku!

   ” ops gaskiya dad kadaina calling dinsa da brother namu…

    ” hmm firdausi kenan watch him full zakiga abunda bakuda shi…

   ” tsake tayi shiga dak’in nasa kai mutumin kauye mahauka ce sai kazo inji dady!

   ” itace sallamar take?

         ” mamaki ne ya cika ta tace eh ko akace maka zakazo gidan ubana ne kayimin iko?

    ” Gidan ubanki ko gidan uban mu wai ahaka kuna jami’a sai girman kai da tak’ama…

    ” mtsew dad kaji yadda ya zage ni! ” alhaji yace ai haruna baya zage banson sharri! +

   ” gyaran murya haruna yayi sannan ya durkusa yace barka da asuba!

   ” barka kadai…

” ta shigo daki nane babu Sallama naga kuma kowacce yarinya kamarta tanada hankali in batayi sallamar dan niba ai tayi dan samun lada!

   ” Alhaji yakamata asamo masu yimusu lesson domin babu mai auren su da dabi’ar nan!

   ” tabbas hakane haruna dama maganar office ne gobe kafara zuwa!

   ” aa Alhaji nan da 3mounth zatafi masters zan kuma naime aiki da kaina nagode…

   ” sis abeg mik’i kinga yadda haruna ta canja ke ingaya miki har sharri yayi mana ne da ke…

   ” what???

Ai kuwa wallahi sai munyi maganin sa…

KAUYE..

  A Ranar k’ande gida ta koma sai da aka aiko tazo inji baba sannan ta fita tun ahanya kirjen ta yake bugawa tana shiga soro taje ihun su inna sadiya ta samu tace lafiya kigayamin?

   ” baba baba sai ta fashe da kuka…

        ” Kar kice min mutuwa yayi tana kuka tana jijjiga ‘yar uwar k’ande data hango mutum akwance baba ya zaka tafi kabarni wayoo nan i tama ta suma….Baba baba sai ta fashe da k’uka… +

        ” Kar kice min mutuwa yayi tana kuka tana jijjiga ‘yar uwar k’ande data hango mutum akwance baba ya zaka tafi kabarni wayoo nan i tama ta suma….

” goggo ce ta dauk’e k’ande ta k’aita dak’i da gudu sadiya ta bita nan aka shirya baba sai gidan sa na gaske kowa a kauyen sai da yaji mutuwar alhaji yakubu, su ya abbas sai zirga zirga sukeyi har aka dawo daga kai mahaifin su, kowa agidan sai kuka yakeyi..

    ” goggo tana shigowa ta k’wara wa k’ande ruwa…

    ” wayyo Allah na shiga uku k’atana yak’are tasaka ihu wayyo Allah babana Allah yajikanka yayi maka rahama!

   ” zaki rufemana baki ko sai ranki ya baci..

     ” k’ande cikin kuka tace ai bacin rai ta fara haduwa dashi har…

   ” iya habu ta taso tace haba k’ande menene haka kuka banaki bani ba addu’a zakiyi masa…

  ” wane sabon kukan ne yazubo mata nayi shiru kikace? Kinfine sanin dacen mutuwa kuma ace masoyin kane yatafi…

   ” toh kiyi hakuri dai…

        ” babu wanda takara kulawa tunda ta kwantar da k’anta acinyar ta!

   ” mutane sai gaisuwa ake shigowa..

      ” goggo da idon ta ya kumbura ta kalle farida tace kidaina kuka domin babu abunda zaiyi miki sama da kisa kanki amatsala..

   ” farida tace bana tunanin zan samu miji kamar baba, mai tausayina mai sona ga sanin damuwa ta…

    ” haba farida Allah shi yakarbe abunsa kuma yafemu sonsa…

   ” Tohm goggo…

Yau sadakar bakwai angama addu’a su goggo sunata karbar gaisuwa!

   ” babu yadda ba’ayi da k’ande tayi wanka ba Amma tak’i in banda wari babu abunda takeyi…

” k’ande bazakiyi wankan baniba? So kikeyi kijawo mana magana!

   ” sadiya tace ai goggo bakije warin datakeyi na! Duk ta cika mana dak’i…

   ” farida tace ai nema tazo nakusa amai saboda warin hammatar ta…

       ” kuka tasaka tayi gefe tare da tausayin kanta taje sannan tace wari innayi kaina ne kuma jikina ne!

    ” iya habu da sauran yan gaisuwa sukace tsafta dai tana daga cikin imani..

    ” haba dame zanji?  ba zanyi ba ai jikina ne!

    ” hajiya asabe tace Ai k’ande ta dabance…

      ” yaya Abbas ne ya shigo ke k’ande kizo inji adam?

   ” me zanyi masa?
    
” gaisuwa zai yimiki tun daga birni yazo yimiki gaisuwa!

    ” lokacin da yatafi birni ai bai gayamin ba kuma gaisuwa bazan fito ba nayafe! Yayi masa Addu’a daga nan…” anya kinada hankali? +

   ” ai kasan haukan gadonsa akeyi…

   ” iya habu tace tashi k’ande kije mana!

    ” wallhi bani zuwa yayiwa su baba datti gaisuwar…

    ” to kai Abbas jik’ace bata fitowa…

STORY CONTINUES BELOW

  K’ande ce ta zauna kusa da goggo tana fadin tabata gurasa…

    ” anya k’ande kinji warin dakikeyi subhanallahi wannan wari haka!

   ” mikuma nayi..

” goggo ce ta k’auda k’anta wai bakinki kamar mushe, tashi kibani guri bazan shaki wari ba…

    ” haba goggo kudaina takurawa yarinyar nan cewar iya habu!

    Zo kizauna kusa dani zama tayi sannan tace Allah yajikanka baba!

   Sallama ce duk’ansu ta katsesu!

   Goggo ce tace maraba maraba sannunku aka shimfida musu dadduma…

   Alhaji mahmuda ne yazauna sannan matarsa surayya sai ‘yayan sa maza haneef da muneef sai hamza…

    ” ya hakurin alhaji yakubu Allah yayi masa rahama ya gafar tamasa..

    ” Ameen dan uwa ina sauran ‘yayan naka?

   ” suna jarabaww kuma final ce!

    ” Allah ya taimaka!

” Aka kawo musu Abinci!

   ” ina Aishatu ne?

       ” au K’ande kaganta nan!

   ” A hankali ta dago idonta dayayi jajir ta fara kallon sa taso tagane fuskar Amma takasa!

   ” Aishatu babu gaisuwa?

    ” ina yini? Alhaji mahmud kawai ta gaisar sauran ko k’allon su batayi ba!

    ” ya hakuri?

   ” Da godiya!

   ” Aisha tu zaki bini birni?

     ” kirjenta ne ya buga sannan taja numfashi tayi shiru..

    ” kow agurin yasan e zatace goggo da duk kunya ta’isheta…

    ” muazzam yace badake ake magana ba?

    ” k’allon su tayi tace bazani ba!

    “Tohm in an kwana biyu kafin nan mutuwar ta dan sakeki zan aiko a dauke ki…

    ” Ahankali farida tace lallai k’ande ta dabance!!!

Birni

  Haruna ne ya fito daga dak’insa sanyi da wani blue din yard yayi masa kyau hushiryar nan abude, ga wane irin kamshi ne ke tashi! Firdausi ce ta tawo tana kokarin shiga part din wane kamshi taje tarasa wanene yasaka wannan turare ahankali ta dago idon ta tayi tunanin uncle mu’azzam ne amma kuma mumy batace zaizo ba!

   Cikin mamaki tanuna haruna tace you…, it seems like amfara satar mana duk’iya har yaushe ka warke? Dakai nake magana mad man!!!

   ” murmushi yayi yace excuse please….” Nan firdausi tashiga wane tunanin..direct dak’in farida ta shiga sister common get up! +

   ” what wrong?

   ” wannan mahaukacin nagani ban ganesa ba fa wallhi he’s so handsome..

    ” see u mummu which handsome fari ne ya k’e driving dink’i…

   ” firdausi ce taja wane numfashi that’s cool ai, ya maganar Egypt din?

   ” farida tace we need to ask mumy again fa..

   ” am praying dad yabiya mana!

     ” Ameen dai..

  ” sis see you later inada lecture by 5 zandawo…

    ” okay bye bye..

” haruna yana isa company din yasamu mai gadi yace manager yana ciki?

    ” kunyi da shine zakuzo?

      ” baba ka taimaka kusan sati 3 ina zirga zirga ban ganshi ba kuma ina bukatar aikin!

     ” tohm muje ciki…sir kanada bak’o!

    ” how many times baba zangaya maka banida time…

    ” gudummawa zai bayar ga kamfanin nan fa!

    ” as you said it! Ya shigo..

      ” assalam
” wslm

   ” Barka da asuba!

        ” lah Nura dama kaine?

     ” Dan duniya ashe baka samu aiki ba?

    ” wallahi kam nura nadan same matsala ne but Alhmdlhi yanzu!

   ” Allah yakara sauki, inasu iya habu?

   ” duk lpya ga takarduna ko zan samu aiki anan!

    “To kaga nan kamfanin Atampha ne kuma manya ba kanana ba kuma kaima bangarin business ne so know zan nunawa manager duk yadda mukayi zakajeni!

   ” tohm nagode sosai ‘ya’yan k’a nawa?

   ” hahaha kai kazana tuzurzur har yanzu kaki aure, yayana 3!

    ” its all about time ai soonest zanyi nema!

  ” okay see you later..

Lok’acin da ya koma gida farida da firdausi ya tarar kujera yasamu ya zauna…

   ” duk’ansu sun kuro ido suna kallon sa, wayarsa ya dak’ko hello my shukra!

   ” Dafatan kana cikin s
Koshin lafiya?

   ” kema ina fatan kina cikin koshin lpya?

    ” lapia lou yaya yajikin naka?

   ” Alhamdulihi ina fata kin karasa haddarki?

   ” eh nagama bari na barka ka huta Allah yakara lpya

  ” Ameen nagode da kulawarki Allah yayi miki Albarka…

    ” firdausi ce tayi gyaran murya tace sis yaushe mu’azzam zaizo?

    ” farida tace kicemin gwarzon namiji mai hankali!

   ” eh hahaha “yana tafe..

  Yanzu abunda kayi ka kyauta haruna?

    ” Wallhi Alhaji kai nake jira kazo mutafi tare! 
To kashirya yanzu mu tafi yanzu har sati 2,…. +

    ” ku shirya kuma…

       ” dady bamason kauyen wahala muke Allah yajikan tsoho!

   ” Dan uwa nane uwa daya uba daya kuma yadda kukace tsoho kuma haka za agayawa uban ku sha sha shai…

   ” tun 4 suka dauke hanyar kauyen 5 da rabi suka i’sa su goggo suna tsakar gida suna tsintar shinkafa!

    ” Assalamu alaikum!

      ” wa’alaikussalam 
   
        ” sannunku da zuwa..

    ” A’a haruna alhamdlhi kamar bakai ba ga jar fatar takara fitowa!…

    ” ya hakurin baba Allah yayi masa rahama!..
  
   ” Ameen sun dadi azaune suna hira bayan magariba haruna yace nari naje nagaida iyah..

   ” Tohm sai kadawo…

      ” ina k’ande ne cewar baba?

   ” goggo tayi murmushi tana gurin uwar dak’inta!

    ” toh Alhmdlhi yanzu dai inason nasanar dake nan da sati 1 zanzo dakaina na dauke k’ande itakuma sadiya jibril ya dauke ta!..

   ” Alhaji tohm mungode Amma Abar mana sadiya….

   ” tohm shikenan…

   Haruna ne ya rangada sallama Assalamu alaikun iya habu!

    ” Muryar wa nakeji kamar ta haruna!…

    ” k’ande ce tasaka dariya kardai kima haukan yafara zuwa daga ne fa saike!

    ” iya habu iya habu…

     ” kande shine shine haruna kaine ko fatalwa ce?

    ” Nine goggo nasamu sauke!

    ” Nan iya habu tayi sujjada ta gode Allah!

    ” k’ande da ta kura masa ido tana ganin sarautar Allah!..

      ” to ya zancen Aure haruna!

       ” Nasamu yarinya shukrah haduwar mu tafarko taimako ne kuma tana sona tun kafin nasamu sauke mahaifin ta bakowa bani kuma tana dai karatu, atakaice dai ta cika duk Abunda nakeso ga ‘ya mace!

   ” to Alhamdulhi,k’ande dauko masa abinci zaci mana!

    ” ina ai k’ande tana wata duniyar yaya haruna ne yadawo haka dan gayu!

    ” zungurar ta tayi..

      ” afirgice ya tashi to..

” kinga yi zamanki ma inada kafafuwa!

    ” toh ne nace maka gurgune!

    ” sunata hira da iya ita dai uffan batace ba chan yace k’ande kinadai zuwa makaranta? Kinga shukrata mahaddaciya ce!

   ” to ne mainene hadina da wata yar birni?

   ” to kidai dinga zuwa..

        “Ai baka fine son karatun ba!

    ” to ne bari nagudu iya har ya fita k’ande ta rada wa iya habu akunnenta anya haruna ne kuwa?

   ” to haruna dawo k’ande tace bakai baniba…

   ” hahha to bari natuna miki wane abu kumatun ta yataba yace (k’ande tayi tsoka iya kifito ki raba) kintuna wannan tsokanar taki!

    ” tsayawa tayi tana kallon sa!

    ” oya simile mana! To haruna dawo k’ande tace bak’ai bani ba… +

   ” hahha to bari na tuna mik’i wane abu kumatun ta ya taba yace (k’ande tayi tsoka iya kifito ki raba) k’intuna wannan tsok’anar tak’i!

    ” tsayawa tayi tana k’allon sa!

    ” oya simile mana!

     ” ne wallahi bana wari….

   ” Dariya haruna yasaka ne ba haka nacemiki kina wari ba smile shine wari, har yanzu turancin ku baiyi kwari ba!

    ” wane guntun tsaki taja tunda naka yayi ai sai kayi murna, tunda mu zama mukeyi agida bamu zuwa makaranta! Aikin kawai kaje kawane ibo al’adun ya hudawa, kamafi kyau da!….

    ” haruna ya murde mata kunne yaushe zaki nutsu ne? Ke kwata kwata bakida hankali kowacce mace nutsuwa takeyi bandak’e!!!…

     ” mik’ewa tayi ta dau bota, sai data saiti kofar bayi sannan tace ohhh kajeni da mutum har yaushe aka dawoma da hankalin naka? To insu ‘yan birni basu sanka lokacin da kake hawa bola ba to suzo nabasu labarin k’a…

   ” takalmi iya habu ta cillo mata, uhm haruna kama hanya kutafi Allah ya tsareka!..

    ” iya habu mi’isa kande takeyi min haka, tun tana yarinya muke tare kuma babu abunda banayi mata amatsayin wa!…

    ” haba haruna ai k’ande ta dabance yarinya ce kadaina biye mata!..

    ” To iya abu ga dubu biyar kwayi cifane…

   ” Toh haruna nagode Allah yayi jagora!…

    ” Ameen iya habu agaida habu…

   ” k’ande tanajin tafiyar sa tafito kusa da iya habu ta zauna iya me yabaki?

   ” Dubu biyar yabamu..

      ” gaskiya iya bakya kawo wuta komai na tambaya yi kikeyi!

    ” Ai k’ande kamar ‘ya na dauke ki…

    ” shiyasa nake sonki ke da baba Allah ya jikansa!

     ” Ameen in tambayi ki mana k’ande?

    ” ince dai lafiya?

       ” Me isa baki bi k’awonki na abuja gidansa ba? Ke da kikeson zuwa birni…

     ” wai kawu mahmuda kike nufi?

   ” eh shi…

    ” Tanbijan ai wannan mutumin bana zuwa gidansa indai gidansa zanje to na hakura da birnin!

   ” saboda me keda kikace zaki jure kowanne irin aiki indai zakiyi ilimi!…

    ” kuma fa hakane, Amma gaskiya iya habu kawu mahmuda bashida kirki lokacin da goggo taje gidansa mai wake wanke aka mai da’ita kuma itace take musu girke sai da yaya abbas yaje yatawo da ita…

    ” To ai shikenan gwara muyi zaman mu ai aure ya rabamu…

    ” hmmm gadai ninan sai yadda Allah yayi dani bari naje gida na dorah Abinci nadawo…

    ” tohm ki anson goro gurin goggo…

   ” iya habu idan habu yazo kice ya kaimun gyaran cocilan….

   ” Tohm…

Salama mtseww wai ke menene haka? 

    ” me kuma nayi miki mama farida?

        ” haka ake shigowa gida sai kace yaro!

       ” Na shigo din tashi ki rufeni da duka inkin isa!

     ” Hannu mama farida ta saka ta wanka mata mari…

    ” wayoo ni kika mara?

   ” lafiya daga shigowar ki k’ande?

   ” wallahi goggo babu abunda nayi mata ta mari ne!

    ” wai haka farida!

       ” Au goyar bayanta zakiyi toh zagina tayi nagaje da rashin kunyar da takeyi min idan da na haihu ai datune inada kamarta…

    ” Allah ya kiyaye kizama uwata!Wallahi sai na rama!…

      ” Goggo ce ta hankada k’ande dak’i ke bakida hankali sa’arki ce!…

    ” farida tayi dariya sannan tace gwara ki koya mata hankali mutanen birni su sunada hankali…

    ” k’ande tace bakamar yan gidan ku ba mahauka ta ba!

    ” au ba zakiyi min shiru ba!…

    ” kuka ta saka me isa bakya sona goggo nifa yarki ce?

   ” goggo ce tafara kuka bawai bana sonki bani ba, ina sonki Aishatu…

       ” yaune rana tafarko da goggo ta taba fadar sunan k’ande….

    ” yanzu zakiyi nesa dani kuma bansan rayuwar da zaki shiga ba Dan haka nake tausaya miki!

    ” kamar yaya goggo?

      ” ke ta dabance, zamanki ga wayanda basu fahimce ki ba da matsala!…

     ” To goggo aikatau zaki kaine ne?

        “A’a k’ande komai Allah yana gani na baki tarbiya daidai gwargwado kuma tarbiyya umarni ne na Allah SWA ,rashin yin ta saba wa umarnin sa ne,kamar yadda ya zo a hadisin Ibn Umar( RA) Manzon Allah S.A.W yace:”Kowannen ku makiyayi ne  kuma kowanne ku za a tambaye shi game da abin kiwonsa”, Dan haka kiyi hakuri kiyi juriya, banda bin kawaye banda fitina banda fitsara…

    ” zan kiyaye Amma idan abubuwan sukayi min yawa wallhi sai na rama!

     ” ni dai fatana Allah ya tsareki ya kuma kare ki…

    ” Ameen goggo!

” gobe ki wanke kayanki ki shiryasu jibi zaki tafi..

    ” Tohm bari naje nasiyo karkashi…

     ” k’ande tana fita ta saka dariya hanyar lambu ta huce tana zuwa ta cinko karkashe danya ta tawo gida ruwa tasaka sannan ta dama sai taga tanata yauk’i kwarawa tayi a kasa daidai dakin mama farida!

   Ta samu guri ta zauna ta kwallara kara aguje farida ta fito zuuuu dimmm ta wadi!

    ” kande tasaka dariya sannan ta gudu…

    ” lafiya mama farida lafiya?

      ” Ta karya ne takarya ne!!!

      ” lah karkashin ke aka zubawa kenan?

  ” kunsan halin k’ande batada hakuri kudaina biye mata! Yanzu gashinan ko baki karye ba kinsha jiki…

    ” tunda ta tawo hanya take ta dariya auwalulu ne yaganta…

    ” k’ande hankalinki daya!!!

          ” kallon sa tayi cike da fitsara sannan tace hankali na uku dana babanku, dana babarka, da naka…zance ubanki… +

” kadade bakaga baban naka ba shiyasa zakace sa!!!

      ” kinsan tsaf zan iya sumar dake…

    ” ka dadi baka sumar ba shiyasa…

      ” biyota yayi ta ruga aguje…

    ” iya habu nadawo!

     ” ba sallama?

” Assalamu Alaikum

       “Wslm

       “Ina cocilan din? Au habu baka kai gyara ba?

    ” bazan iya ba!

” zakaga bazaka iya ba yau sai dai ka kwana a kasa ko bargo bazan baka ba!

   ” yi hakuri kawo na kai gyaran!

   ” Dan kan uwa kana kallona kamar wane goruba sai ka dawo…

Da safe k’ande tanata wanken kayanta..

    ” uwar dakina lafiya wanke da safe?

    ” Da banida lafiyar ai bazan wanken ba, goggo ce tace na wanke kayan!

     ” tooh Ko birni zakije?

    ” iya habu gidan wa a burni?

     ” bandai sani ba bari muzuba ido mugani…

    ” kai habu zanyi tafiya bansani ba ko zan dawo ko zan mutu ko can zan zauna kasani tsoron Allah shine gaba da komai ka dinga sallah ka dinga sallah ka guje wasa da Sallah…

    ” tohm k’ande..

Wane son k’ande ne yakara shiga zuciyar iya habu nan da nan sai kuka…

     ” iya kiyi hakuri kidaina kuka duk da bansan mekike yiwa kuka ba!

    ” wallahi k’ande banson rabuwa dake domin halin ki na daban ne…

     ” karki damu iya habu kiyimun Addu’a Allah ya shirye ne kawai…

    ” Tohm..

   Birni

Alhaji wai mike faru ne naga sai sauri kikeyi?

    ” ina sha sha shan yarannan?

       ” bacci sukeyi ai!

” yabzu ke bazakiyi wa ‘yayanki fada ba? Sunfa isa yin komai ace komai sai masu aiki ne zasu dinga yi toh wallahi aure zanyi musu in basu gyara halinsu ba!

     ” toh Alhaji yakake so nayi? Wallhi kullum inayi musu fada jine basayi…

        ”  ki cewa haruna yadau kaya a mota ya kaimun office ne na huce kauye…

      ” To Allah ya kiyaye…

     ” D’akin su farida ta shiga ku tashi malalata har karfe daya kuna barci…

    ” to mumy yaufa sunday bamu da lecture cewar farida…

       ” ai that’s good for you firdausi tashi kishiga adak’in haruna kice alhaji yace ya kai sako office!!!

     ” tohm mum mik’ewa tayi kanta ba dankwali ga wane wando duk ya matseta! 

    ” haruna yana kan gado yana waya da mukhtar kawai yaga yarinya ta tsaya a kansa oya dad yace ka dau mota akwai sako!

    ” Ko daga kai baiyi ya kalleta ba!

    ” ohh anzo birni shine za anuna mana tak’ama! Kallon sa ta tsaya yi tasa blue din Riga tayi masa kyau..” kallon ta shima yayi nan yaje wane yar ajikin sa! Ahankali yace will u get out from my room? Karki kara shigo min daki haka! Banson sha shanci… +

     ” ahankali tafita batare da tace komai ba! Tana karasawa palour taga hafsa tazo!!!

    ” feedy kina hot fa irin wannan kala haka ince anturawa mutumin!

    ” mtseww ke kyalesa nasamu wane wallahi but da problem fa dan yafeson me addini!

     ” shi yana sonki ne?

     ” nop am just playing my game fa!

     ” Dont mind dear kalamai da tarkon kwauna zaki sakar masa..

    ” anyway zan gwada but yanada kafiya fa?

       ” dallah sai kace ba mace ba!!!….

K’auye

  ” lokacin da Alhaji ya isa kauyen goggo ce tayi masa maraba sannan ya samu guri ya zauna!

  ” mama farida ce ta bude baki cikin mamaki au Alhaji da gaske birnin zaka tafi da k’ande? Taba baki tayi tace hmm bari dai nayi shiru….

   ” goggo ce tayi wane iri sannan tace uhm ai k’ande sai hakuri…

     ” Alhaji ne yace ai nima ‘ya tace dan haka  zan riketa hannu bibbiyu!!!

     ” Tohm nagode sosai Allah yabar zumunci ya kara Arzuki…

          ” babu komai ina k’anden??

       ” sallamar tace ta katse su ta dur k’usa har k’asa ta gaida shi…

    ” lpylou Aishatu muje to tinda kin karaso…

     ” Diris taje tace to ai banyiwa iya habu sallama ba!

     ” karki damu zan biya ai sai muje!

       ” to mama farida ayafemu goggo zanyi kewarki..

        ” k’ande fatana guda daya karki cuci wani karki wulankanta wane ki zauna da kowa lpya kiyi kuma hakuri!!!

    ” Tohm goggo…

    Mikomin ledar kayan nake..

     ” Aa zan dauka kabarshi!

    ” banason gaddama…

    ” Tohm gashi suna shiga ta rungume iya habu tace kiyafeni?

  ” me kikaye min kidai kiriki mutuncin ki…

     ” Tohm nasara gida nasara abokan gaba burina na farko ya cika kinsan Allah swt babu yadda bai iyayi da hukuncin sa ba!

  ” wannan haka yake..

      ” Toh kasani dai Amanace agurin ka! Addua o saiful muminun k’ande..

        ” iya habu inshaa Allahu..

Basu isa birni ba sai karfe 6 na yamma tun daga kofar gidan hankalin k’ande ya tashi ana bude musu kofa tace (tamfa tse Aljannar duniya) suna isa Alhaji ya dakko ledar ta…

    ” Dan Allah kakawo na riki..

   ” suna shiga bakowa a palour kasan tahil ta samu ta zauna…

    ” menene haka Aishatu hau kan kujerar mana!

    ” tohm tace ta zauna tana kallon dak’in…

   ” bari naje nayi sallah nadawo, ga kwana nan akwai daki na farko sai kishiga…

    ” Tohm

       ” farida ce ta sakko tana chwn gum ke ke wacce dirty girl din ce akan kujerar mu?

    ” k’ande tace nice kazamar kauye ko nasauka ne?..

     ” To yar matsiyata zaki sauka ko saina karyaki?

   ” k’ande ce ta miki ta nufi inda Alhaji ya nuna mata..

    ” ke ballagaza dauke kazaman kayanki kar kikawo mana cuta!. 

    ” wane kallo k’ande tayi mata sannan ta dauka garin sauri sai taje ta bangaje mutum…..

     ” ke wacece ke zaki bangaje ne?

    ” kayi hakuri!

   ” koba k’ande ce ke ba tasss ya wanka mata mari….

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]