[Advertisements⬇️]

KANDALA CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

KANDALACHAPTER 1


Ina! ina!! Haihuwa da hanji ai wallahi iya habu wannan zancen nak’e ba mai yihuwa bane! K’irasa wanda zaki zabar mun sai yaya haruna! Hehehehe ai wallahi zancen k’i k’amar asarar mi yaune dubi ne sama da k’asa duk k’auyen nan babu mai tsafta ta k’o dan k’ingan ne bak’a? Yaya habu fari!!!
” Haba uwar dakina haba sadiya haruna d’a nane kuma aikinga rufawa juna asiri zakuyi ke yar uwarsa ce?
” Tabbijan gaskiya iya habu abun nake yafara huce gona da iri Dan kinga ina kwana a gidan k’i k’o dan k’inga ina sonki?

” hahaha sautin dariyar haruna ce ta katse musu zancen so, wata dariya yasaka tare da fadin kowana biyu banyi duk’a ba. ..

Bantan uba gaskiya iya habu bakya sona wannan mahaukacin zaki hadani dashi babu arabi babu boko sai hauka da dukan yayan mutane!

” Amma dai dan uwanki ne kuma kece wadda zaki fi kowa rufa masa asiri!

” inji wa inji wa ai wannan mutumin babu abun rufa asiri atattare dashi to bari kije iya habu nefa burina dayawa kinga yanzu ina aji biyar a boko dazarar nagama zan tafi makarantar birne!

” haba k’ande sai lallaba ki nakeyi amma kina gayamin magana haruna dan uwanki ne kuma cutar nan Allah ne ya dura masa! Ahankali inkunyi aure zaije sauki kuma kinsan dai yana siyar da ice kuma fari saurayi ne kamar yadda kika bukata!

” wa kidaina lika mun danki duk yammatan dasuke garin nan kinfe kowa sanin Alhajin birne zan aura mai kudi mai mota wanda zai kaine makka, naja mota naku shiga Ac, shi kuwa ya haruna dak’in kara ne dashi.. 1

” iya habu ce ta sunkuyar da kanta ciki da kwallah..

” shikuwa haruna dayayi sakwatoto baisan akan me suke magana ba can yace iya meke farune…
” k’ande ce tayi masa wane mugun kallo sannan ta nunasa akanka ne! Kai to bari in gaya maka ko da wasa kace kana sona sai na hadaka da auwalulu ya surfaka! Yawu ta tofar mtsew kazami kawai kafara sallah da karatu…

” ke zance ubanki fa!

” dadinta ubana kace kuma kaima kanin mahaifiyar kane amatsayin ubanka yake..

” haruna kada kabiye mata kaji..

” iya habu sai anjimanki lokacin girke yayi, in kinje haushi na kiyi hakuri gaskiya ce dole nafada….

” Iya habu ce ta kalli haruna Allah yabaka lafiya kaji Allah ya yayi maka cutar nan…

” k’ande tana cikin tafiya tana yar wakar ta, tagano auwalulu yanata zukar taba, ahankali takarasa gurinsa kaikuwa Auwalulu anya kanada hankali…

” hahaha k’ande kenan ai nafiki hankali..

” dallah tafi can ko dankaga kai dan dabani to wallahi ne baka isa kayimin ba dan haka kadaina nunawa kasanni kana koremun samarina, kafi kowa sanin *ni ta dabbance*…

  ” kin daiyi kwantai babu mai sonki sai yawo a kauye..

  ” kaje botorami ai dadai na aure miji irin ka gwara ta mutu banyi aure ba banza soko kawai…

   ” zanyi maganin ki ne…

    ” da wacce itaciyar zakayi maganina?

    ” dan dai yau banason rigema ne dakinga yadda ake hukunci…

  ” kamaso mana kaga yadda nayi damaran nan babu mutunci kai bani ma da lokacin ka…

   ” ahaka tana cikin tafiya tayi tahadu da yan mata sai kwalliya sukeyi sassan nun ku fa! Sai k’ande sai k’ande!!!

  ” kunganku duk kun baje kuna kwalliya ince kun iya karatun hausa?

” ai sai da kudi ake makaranta kuma mu iyayen mu basuda karfe!

   ” ayye kuce ta gwamnatin kuka raina kuzauna jahilce yana yimuku tufka kunga tafiya…

   ” lokacin da ta isa gida Ahankali tayi sallama gudun kada goggo tayi mata fada akan zane sadiya da tayi…

   Ke menene haka sai sand’a kikeyi sai kace barauniya..

   Kugu ta rike tace inci adakin ki zanyi satar? Naga nan gidan ubana ne ko akwance naso shigowa zanyi mai ruwanki?

    ” nikuma gidan mijina ne ai!

  ” hahaha kinje ke wai ke matar baba hahaha banda abunki ai ke zai iya sak’in ki nikuwa yarsa ce kuma zama dani dole kikuwa babu dole!

   ” Wallahi kande zance ubanki ne sa’ar kice?

    ” ke ba sa’anata bave ba Amma na fiki hankali..

    ” dallah yimun shiru kina yawo atiti shekara sha takwas babu mijin aure kinyi kwantai…

   ” Maganar sai data shigarwa k’ande har tsakar kanta sannan tace ince agidanku ake raba mijin ne naji na ansa naja kannen ki su naja’atu sun girme ne Amma babu mai tsayawa dasu gwara ne kullum ana cewa ana sona!

    ” malam malam tafita kofar gida wannan mahaukaciyar yar taka kashiga tsakanina daita yanzu haka ma sai data zagine!..

     ” furaira zage kikace eh wallhi..

  ” K’ande k’ande kina ina?

    ” Naam alhaji baba malam mikuma yafaru?

    ” mahaifin nata sai da yadara wai ke yaushe zakiyi hank’ali?

  ” shiru tayi can kuma tace to ne Alhaji baba mekakeso nace maka, in nayi magana ace nayi rashin kunya?

   ” Wannan fa amatsayin goggon ki take!

   ” haba alhaji baba ina takai matsayin goggo kaifa rannan naji kana fadin babu mai matsayin goggo!

   ” uhm uhm to yanzu ki bata hakuri!

   ” ta wani kada ido tace kiyi hakuri amaryar baba!..

   ” yauwa bari naji gona nadawo..

” k’ande ta kalle ta karki zata hakuri nabaki darajar tsoho na kikace…

  ” mara tarbiya kawai…

” agurin yan gidan ku nakoya koba zuwa dandali da bin maza ba…

    ” shiru furaira tayi tare da tunani irin halin k’ande…

  Bayan ta gama girke tana zaune tana karatun spelling sai hauka takeyi spoon shine fork book shine bed amarya kinsan menene bed!

  ” mtsw…
   
   Ai dama nasan bakisan komai ba to bed shine littafi fork cokali cin abinci hahaha kikoma makaranta…

   ” Yaya isa ne ya shigo dallah malama yimana shiru bakisan ma mekike karantawa ba bed shine gado, book littafi…

  ” aa yaya karik’i sanin k’a  ni bahaka aka koyamin ba!.

” to ai shikenan..

” furaira da cikint a yak’e kartawa saboda yunwa ta mike domin zubawa..

   ” ayya ai wallahi bazata sabo ba wankan k’uturu da sabulu ne da wahala ke da shan iska yaza’ayi nadafa abinci ko sannu baki cimin ba shine zaki zuba!

   ” ai naga mijina nane yake k’awowa!

  ” Ni kuma ubana ba ina laifin k’i tsaya nazuba miki?

   ” mama furaira kyaleta tazuba miki kinsan batada kunya…

  Nan k’ande ta zubawa kowa tasaka uniform dinta sai makaranta…

   K’ande kinje maganar hadaku aure da yaya haruna?
   
  ” k’asan Allah hadin nan bazaiyihu ba ne da azaba ku da sannu…

   ” ai zancen yaje gurin baba..

   ” hahhaha awuf ai shi baban ak’wai wanda yafeshi ya nada na gaba dashi!

   ” wakenan?

     ” Allah mana tsayuwar dare zanyi akansa..

   ” k’ingama magana kanwata, yanzu kinada kudin makaranta…

  ” a’a yaya nace abinci basai anbani komai ba nidai kadaina cimun mara k’unya kaje?

    ” tohm shikenan nadaina sai kindawo..

    Ak’afar ta ta’isa makaranta tana zuwa taga malamar english ta shiga, Ajin ta shiga tace sannu malama?

   ” fitar mun a aji sai yanzu zakizo?

     ” haba malama muna da fa iyaye muna tayasu aiki kuma muma muna da uzurin mu zamu tawo ne mubar iyayen mu da wahala bayin k’okarin da sukeyi mana!

   ” Yimun shiru sha sha sha…

    ” wallahi bazanyi shiru ba tunda kafin k’i fara k’oyar dani sai dak’ika anshi k’udi aine bana fahimtar komai ba aikin ki kullum gayu da labari…

   ” id’iot zanyi maganin k’i!

   ” da wanne ganyen!

” Shiru tayi mata ajin ta shigo…

” Fita kibar mun aji… +

   ” gurin principle taje tana zuwa tace sir ak’wai matsala munada karancin malamai a makarantar nan kaf dalibai babu mai iya imaka mintina cikin harshen turanci malama nafeesa kullum sai gayu da labari Amma komai copy tak’eyi acikin littafi bugagge!

   ” yes na fahimce haka zamu sallameta zakuma mukawo k’wararron malamai mungode da k’orafin ki!

  ” karkadamu sir cigabank’u nakeso..

   ” suna break malama nafeesa tazo ta huce da jak’a ta kalle k’ande kinsa an koreni ko?

    ” ai dama nagaya miki raina mutum da wulak’anta mutum ba na mai ilimi bani ba, in koreni a ajinki nikuma nafadi gaskiya an k’oreki dan hak’a sai k’i kara gaba…

   ” malama nafeesa tasaka dariya kina k’ande shine zakice kinsa ank’oreni banza k’ucaka jahila yar k’auye!

   ” k’afin k’uce mai idon k’ande ya cik’a da hawaye, bakomai nagode…

   Tun daga lok’acin k’ande ta zama masifaffe ya ita burinta ta’ina zataje burni danyin k’aratu….

Iya habu abun duniya ya i’sheta Alhaji hassan yashigo ciki da fara’a lafiya iya habu?

   ” hassan k’ai dan uwanane inaso ka dauke dana tunda kana da k’arfe ku tafi burni aduba lafiyar sa! Inda hali ma DanAllah kadube maraici k’asa shi a makaranta…

   ” bak’omai iya naso zan tafi dashi…

   ” sai da suk’a shirya tace hassan amanace..

  ” k’arki damu iya..

Gurin k’arfe shida k’ande tayi sallama iya habu tayi mata shiru..

   ” iya habu ko k’in manta ladan sallamar ne???

   ” ke k’ande mufa kin ishemu wannan haukan nake yayi yawa..

  ” wanene k’e maganar nan? 

  ” habu ne!

” Aikuwa batasan lok’acin da tafara dukan sa ba sai data kusa yi masa raune…

   ” ke k’ande hankalin…..Aikuwa batasan lok’acin da tafara dukan sa ba sai data kusa yi masa raune… +

” ke k’ande hank’alin ki yana kanki kuwa ke kwata kwata bakya kunyar idon mahaifi ko mutuwa tana jin kunyar idon mahaifi..

” haba iya habu ko dank’in ga d’anki ne? Ita kuma mutuwa dakike zancen ta naga inkin bar gurin zata dau ran dai? Wallahi habu ka Kara yimun rashin kunya sai naci ubanka banza kawai…

” Allah yabaki hakuri ne ba rashin kunya nayi miki ba…

” mtswee kadai san ne nice dai k’ande!!!

” oh ne naga lokacin da zakiyi hankali k’ande!

” kiyimun addu’a kokuma kiyi shiru, bari naji gida nadawo…

” ki gaida goggo!

” to…

K’ande k’ande k’ande…

” jiyuwar da k’ande zatayi tace wai sumayya ince agidan ku aka radamin suna sai wane kirana kike sai kace yarinya…

” haba k’ande dan nakiraki wane abunne to bama wannan ba saurayinki aliyu ya tafi birne karatu kuma ance kano yatafi!

” birni innalillahi oh ne k’ande na shiga uku kowa yana tafiya birni banda ne! Tayaya zan tafi birne? Ahankali ta jijjiga sumayya ki gayamin ta yadda zan tafi birne DanAllah!

” k’ande birni kikace fa? Gaskiya kiyi zamanki a nan!

” k’ande ce ta cere hannu ta zabgawa sumayya mari!

” ne kika mara k’ande ni kika Mara dan nagaya miki gaskiya?

” babu abunda nakeso fiye danaji birni karatu dan haka inkinason zaman lafiya tare dani kada kikara cewa bazani birni ba bakisan a duniya babu abunda na tsana irin jahilce ba!

” rabuwa dake k’ande yazama dole domin yau kin mari ne watarana sai duka dan haka sai anjima!

” mtsew oho miki inkin rabu dani kindai san zan rayu!

” ahaka sumayya tashige har cikin gidansu…

” kande kuwa rusa ihu tafarayi har ta shiga gidan nasu da yaya abbas tayi karo yace dallah yimana shiru shagwababbe ya!

” Na kulaka ne ai ban kulaka ba!

” takalmin sa ya dauka ya kwada mata akanta!

” wayoo Allah nashiga uku mugu Azzalumi kaima sai anyiwa ‘ya’yank’a!

” nikike gayawa haka?

” aguje ta wada cikin gidan su goggo!

” menene ‘yar gidan iya habu?

” kinga yaya abbas ko?…

” kafin takarasa magana yace wallahi ne sai naci ubanki nizakiyewa rashin kunya sakara kawai!

” In baka fasa ba kai ka isa ka karyane bakaga nafika tsawo ba!

” a fusace yatawo bari kiga…

” goggo ce tace haba abbas da hankalin ka wannan yarinyar ba sa’arka bace!

” k’i barshi ya k’arya ne inya i’sa…

” haba goggo bakije abunda take cewa ba?

” haba abbas kayi hakuri kaga yarinya ce…

” ku kuke bata k’ande wallahi…nan furaira tace tayani fada abbas yarinya ta raina kowa auren ma yagagara! +

” wallhi goggo kice tadaina yimun borin aure tunda ba agidansu ake raba mijin ba!

” haba ke kinyi shi yayi ya kukeso nayi daku ne ku kyaleta mana shige mutafi daki…

” yaya Abbas yace wai ina i’sa yashiga ne? 
” suna cikin dak’insu shida kabiru okay bari naje!

” furaira tace oh ya Allah nema kabani haihuwar nan!

” goggo ce ta kalli k’ande bawai kinga natare miki ba!

” ai nasan komai bashine agurinki goggo!

” yarinyar dakika fasawa kai garin fada sai da nabada jaka 2 tukunna suka hakura, karshi ma sunce in kika kara kula musu ya zasu kaiki gurin yan kato da gora!

” kaje yan kan uwa! Bari naji nayiwa uwarta rashin mutunci nadawo!

” goggo ce tacero wata dorina nan ta shiga zubawa k’ande, wallhi baxata sabo ba na haifi ki kidinga jawomin masifa!

” wayyo allah nashiga uku ne k’ande kiyi hakuri goggo!

” Zerp zerp ai sai kinje ajikin ki wallahi dukanta takeyi ko ta’ina…

” furaira kuwa tasaka dariya gwara ace ubanki!

” yaya isa kaje kukan k’ande kardai goggo ke dukanta?

” ai gwara cewar abbas yanzu tagama yimun rashin kunya!

” kabiru yamike a’a wallhi wannan ai babu dadi kuje fa ihunta bari naje!

Haba goggo kiyi hakuri kada kije ciwo mana!

” ka kyale ne da wannan yarinyar narasa irinta wallhi!

” kabiru yace ai *ita ta ta dabance*kiyi hakuri ki kyaleta!

” banason hakurin naka cewar k’ande sai da kaga takusa nakasane shine zakazo to wallahi sai na rama!

” goggo ce ta sakar mata mari sai kirama nagani kowa yana girma banda ke!

” kabiru ne yashiga dakinsa yans dariya lallai k’ande ta shahara!

” ai wannan yarinyar ta dabance!!*ASALIN SU* +

Kauyen banjigo garine Mai dadin gaske kowanne magidance yanada gonarsa yana kuma siyar da abunda Baza a rasa ba,

Alhaji yakubu ba kowa bani ba face manomi shekarar sa hamsin aduniya mutum ne mai mutunci da cika Alkawari yanada yayye guda biyu iya habu itace babbar su sai Alhaji hassan dayake a burni sai shi, suna son juna sosai, yana da mata biyu hajiya suwaiba wacce akafi sanin ta da goggo itace matarsa ta farko kusan shekararsu arba’in tare, tana da yayanta wanda ame kira da Alhaji mahmuda sha hararren dan siyasa ne agarin Abuja yaje da zama amma babu abunda yakeyi mata sai aiki da yake mata duk shekara, goggo kowa ya santa da fada da kuma horo akan ‘ya’yanta tanada yaya guda 5 akwai isa wanda yake da shekara 27 sai abbas wanda keda shekara 24, sai kabiru yanada shekara 20, sai Aisha wacce ake kira da k’ande sai yar uwarta sadiya! sai matarsa ta biyu wato furaira shekarar su 3 da aure sanadiyar yar uwarsa ce mahaifiyar su tayi masa wasiya daya aure ta, furaira shekarar ta 24 tana zaune lafiya da goggo kuma tana son ya’yanta amma kuma jinin su baizo daya da k’ande ba…

K’ande yarinya ce dabata huce shekara sha takwas ba, bakace mai kananan ido Dai tana da hanci da kuma da kuma yar bular kumatun nan, duguwa ce kuma tanada kiba hakan yasa yaya abbas yake cimata buhu da kafa, kusan sa’anin ta sunyi aure saboda fitinar ta da shedancin ta yasa ake tsoron ta gata da fadin gaskiya, rashin kunya kuwa tun tana karama takeyi saboda iya habu tana tare mata fada haka yasanya ta zama kawarta kullum tana gidan ta! Ga farin jinin samari kusan kowa yasanta da kule kule hakan yasa ta hadu da Aliyu wanda yake tsananin kaunarta kullum yakan cemata yaushe zamuyi aure sai tace sai nayi karatu mai zurfi hakan ya sanya ya karaya da zancen ta, daya gaje yaji yasamu mahaifin ta domin ayi maganar aure bashiri K’ande ta bude masa wuta tayi nasa rashin m sannan tace dama ai kai mugune kuma baka sona tunda bakason nayi karatu to kaje na sallame ka, akwai lokacin data saka iya habu tanata kuka tace lafiya k’ande? Tace iya yaushe zakuyi mun aure nema na haihu? Dariya iya habu tasaka sannan tace wa zaiyi miki aure? Ai ke bakida hankali kuma ke karamar yarinya ce? ” k’ande ta saka dariya kice marasa hankalin sunada yawa akayiwa aure? ” iya habu tacesu wanene marasa hankalin? ” ku mana tunda baku kai shekaru na ba akayi muku aure! ” yimun shiru sha sha sha kawai..In dai bangarin karatun Allo ne k’ande tana lamba da domin tunda ta tashi bata wasa da karatun ta sai taje dan marge akafa domin a koya mata rabin fije na kur’ani hakan yana burge mutane dayawa akwai wata amarya akusa da gidansu sai taje tayi mata wanke dan ta koya mata hadisi yanzu gashinan har ta kai izu talatin, ganin hazakarta a islamiyya yasa baba yakaita banjigo secondary school a makarantar malamai sai da suka gaje da dukanta saboda tsokana, wata rana ta shigo gidan iya habu da kukanta tace iya mai isa baza ayiwa yaya haruna aure ba ayi masa magani wallahi wannan haukan nasa yana tayar min da hankali! Mata shi kyakyawa dubi hushiryar shi ” Iya habu har hawaye tayi tace wannan haukan nasa yasamo asaline daga hatsarin da yataba yi lokacin dayana zuwa birni karatu tun yana shekara 24 yanzu shekarar sa 29 amma bai rabu dashi ba nikuma na karfe ne dani ba! ” k’ande tace to kusamu mace mai hankali ku hadashi dashi mana! ” hakan yasa iya habu tayi tunani ko sonsa takeyi nan ta tayar da zancen, ” nan k’ande tayi musu wanken soso da sabulu, k’ande bata da wata kawa data huce kanwarta sadiya kullum sai sunyi fada Amma kullum sai sun shirya, mai unguwar garin Kuwa babu yarinyar da yakeso sama da k’ande…

Cigaban labari

Lokacin da goggo ta gama lik’udar k’ande ko motse batayi nan baccin wahala ya kwashe ta, goggo tunda tafara tada icce take tsake har sai da sadiya tayi sallama tace goggota sannu da aiki!

” har antaso ku?

” Yana ganki kina kunna ice ina k’ande?

” tana dak’a..

” kuma tabarki kina aza ice dan rashin tausayi Bari nacere kayana, ke k’ande kin ma kwanta adafa kice ko?

” k’ande ce tajawo ta tahau kanta tare da toshe mata baki ne sa’arki ce, daman nasace sai na rama duki cukuda cukuda!

” sadiya kuwa ko cikakken takasa ihu..

” goggo tace Kamar Ana nishi adak’i da salatin ta ta shiga kasheta zakiyi wato baki dak’u ba?

” aguje tafita waje tana ai dama nace miki sai na rama abi a tsaneka agida…

” sannu auta sannu kinje!

” goggo anya k’ande yar uwata ce?

” ai da badan a haihuwar ta nasha wuya ba da sai nace bani na haifi ta ba,

” goggo dube bayana kamar jini wallahi k’ande kazamace!!!

” tashi ki chanja kuma kema kidaina shiga harkarta!.

” to inna muje ma tuka tuwon…

” k’ande tana cikin tafiya taje kamar fitsari takeyi nan ta taba zanin ta taji jinine kai wannan jini ai kuwa bani wanke ka kakarata zubarka malam kafin ta Ankara taje wasu maza sun zagaye ta tsayawa tayi cak bayin Allah sadaka kuke nema kokuwa tambaya zakuyi?

” kallon ta sukeyi tare da huce…

” kai malamai kuyi magana mana kunsani agaba sai kace wasu zakuna kunata huce bansan rainin wayo wallhi!

” mai gari yace mu dakko ki!!!!

” hahaha to muje muji da wacce yazo yau…

” to bakin mutum mai bakar zuciya wai sau nawa zance karabu dani,???

” kinsan dai ina sonki kin kuma san saina aureki!

” sai ka auren danAllah dubi rawanin ka hahaha sai kace wuyan jimuna, kakalle ne yarinya kara kace kana sona!

” to in bazaki sone ba mai zai hana mu kwana tare!

” shiru tayi sannan ta hange wata kwalba nan ta dakko ta fasa kwalba lokaci daya ta caka a kafarsa!

” wayyo Allah wayyo azaba….

” kadaiji radadin azaba ko to haka zakaje ayayin da aka yiwa yar ka ciki kuma bala’in zina yafi wannan azabar da kaje wallhi ko karabu dani ko kuma natuna maka asiri wllhi kasan cewa *ne ta dabance*…

” Nan ya cire kwalba ciki da jijjiga kai saboda azaba…

” tana cikin tafiya tayi kicibus da auwalolo kai sarkin hankali ina abokin ka?

” k’ande kenan ai haruna yatafi birni…

” me me me birni?

” eh yatafi tun shekaran jiya…

” lallai dole nema na tafi birnin nan tabbijan wanka anata hakar rijiya ne ina maida kasa!

” auta auta..Naam goggo? +

” zo kikaiwa k’ande Abinci…

” kande kuma goggo yanzu kuka gama haurawa fa!

” ai k’ande ta dabance tana faranta min fiye da sauran ‘ya’yana fitinar ta bazata saka na gujeta ba!

” iya harkin kwanta ne?

” wai wannan warin dakikeyi fa eh k’ande?

” wallahi jini ne nikuma baxan wanke ba sai gobe gwara yabata kayan gaba daya!

” kina maccen zaki zauna jini ya bata ke dauke lagwane kije kiyi wanka kigyara kanki ai da wannan kazan tar taku aljanu ki samun damar shiga jikinku kizo kiyi sallah kuma…

” ne gaskiya…

” wallahi inbaki tashiba kabiru zankira yazani ki!

Birni

Garin kano
Nasarawa gra!

Gidan Alhaji hassan! Yanada mata daya asma’u mace ce kamila babu ruwanta ya’yan su biyu farida, zainab sai firdausi…..

Bayan sun isa Gida likita ya tabbatar masa dacewa in har suka dage Akan magani to haruna zai samu sauke!

” suna shiga cikin gida hajiya tace sannu haruna sannu!

” kallon ta Kawai yakeyi…

Farida ce ta sakko daga Sama dady sabon maigadi aka kawo???,k’allon ta K’awai yakeyi… +

   Farida ce ta sakko daga Sama dady sabon maigadi aka kawo???

   Wane mugun kallo dady ya sak’ar Mata sannan ta zauna!

    ” dady Ina yi maka magana kayimin banza nace Mai gadi NE?

     ” uwarki ce nace uwarki ce Sha Sha shai kwata kwata bakisan mikikeyi ba, to yayanki ne domin d’a nane matsayan ku daya agidan nan!

    ” haba dady yana fak’irin? Gaskiya kadaina hadamu dashi..

      ” Alhaji kadaina yimusu haka yarane fa!

    ” mtseww dama kike lallata su to bari in gayamuku inkunason farinciki na a gidan to ku farantawa haruna…

     ” hajiya tace haba alhaji wannan mahaukacin har wata kima gareshi?

Au hardake to mu zuba mugani, tashi muje nakaika dak’in ka haruna….

    ” to yace masa sannan ya bisa Har bangaren nasa dak’i ne Sai bandaki aciki…

    ” to Haruna ga dak’in da zaka dinga kwana idan kana da bukatar wane abun to kasanar dani kaje??

    ” to Ya ambata batare da Ya kara kallon sa ba!


   ” farida ce tace mumy wai me dady yake nufi ne? Kinsan bazamu lamunta rashin mutunci agurin wane bari ba!

    ” to farida haruna ai shima mutum ne in banda abunki ai duk daya kuke!

Haba momy stop it please haba mumy kinsan me kike fada?

  ” Wai what’s going on ne?  Tun dazu nakejin hayaniya! Cewar fiddausi…

  ” farida ta taba baki wannan mutum kauyen aka kawo gidan nan!

” haba dai…

    ” ke bakije wasu zantuka da dady yakeyi ba wai we are all thesame!!

    ” dad kenan ai akwai difference bama sai mun bata mouth din mu ba!

  ” oya tell her fiddausi, adinga hadamu da wane dirty man..

    ” abeg see you later inada lecture kuma kinsan baida kirki!

    ” farida tace kidaina wane sauri sauri car dinki ba awanke take ba! But ga mukullin dad ya manta ki dauka….

   “Mumy tace kunga kudaina abunda kukeyi you’re all girls be matual cuz duk kun girma..

   ” mum kenan u can’t understand wlhi bye bye…

    ” Tun daren jiya haruna yakejin sa acikin wata sabuwar rayuwa wanda hakan yasa yayi tunanin kamar gidan kawunsa wayar kusa dashi ce tafara ringing a hankali ya nutsu sannan ya fahimce inda zai dauka…

   ” assalamu alaikum

       ” haruna akwai magani agefan katifarka ka dauka kasha…
   
    ” tohm, yace sannan ya dauka yasha daga nan ya kwanta bacci..

Da safe haruna yayi wanka sannan bude wata k’waba ya dauki wata shadda ya saka bakin gadonsa ya zauna yayi shiru shi kadai…

    Hajiya da su farida suna k’an dinning sun fara breakfast…

   ” kunji ne shiru ko? Cewar dady ina dan waya ne!

    ” hajiya tayi dariya tace aikam su farida har sun fara ci ko jiran ka basuyi ba!..,a’a ina yayan naku? +

     ” wane yaya kuma dady? Cewar fiddausi..

    ” haruna mana jiki kirasa mana tun dazu ace bai karya ba!

    ” haba dady wannan har matsayin akirasa yake dashi? Gaskiya ne…

    ” will you call him ko sai na mari ki…

   ” cikin kunkine ta shiga dak’insa kai mutumin kauye gadon talauci anzo anga arzuki za’a maimayi to kazo inje dady!

   ” haruna da hankalin sa har yanzu da saura sai cewa yayi toh Amma yana ganin fuskarta yasan rashin kunya takeyi masa…

    Suna shiga gurin dinning din dady yace haba haruna how many times zan gaya maka nan gidan gidan ku ne!

   ” to Alhaji bread din ya dauka yanata kallonsa..

    ” hahaha farida tasaka dariya yaga bakon abu ba’asaba ci ba!.

    ” alhaji yace nima ubanki ta haka nasaba ci tashi kubani guri kafin ranku ya bace…

    ” haruna ya kalleta sannan yayi murmushi! 
   ” alhaji yace ya k’an naka?

    ” Ahankali yace akwai ciwo kadan Amma Alhandulilahi,

    ” yauwa sai katashi mutafi asubuti akarasa aikin!

   ” lokacin dasuka isa asubutin likita yasanar dasu cewa jikin sa yayi kyau kuma inyi nasara inshaa Allah..

   ” nagode doctor nagode…

   “Haruna bakomai wannan hakuri da kake dashi zai kaika inda baka zato!

   ” kwarai kuwa yanzu muje nasa akaika ka huta…

  ” tohm ya ambata sannan aka kawoshi yana shiga yatarar da farida na zance bai kalleta ba Amma yaji tana fadin ai wanke yakeyi mana!

  ” Amma kuma kyakyawa ne farida!

   ” ahaka salman to ai mahaukaci ne..

   ” amma yana da ilimi ko?

” eh to yana dashi yanzu masters zaiyi!

   ” kuma kikace mai wanke ne?

   ” kwarai kuwa…

K’auye

  Iya habu wallahi sai kin biyane ashirin dita ta wancan shekarar,

   ” oh ne k’ande narasa irinki wallhi ace naira shirin kin kasa barmine?

   ” iya habu iya habu wallhi zankai ki kara koto, in kuma kinfiso nayi miki Allah ya’isa sai nayi miki!

   ” k’ande ne! Har kudi zai hadamu?

   ” bazaki bayarba kenan?

   ” banda chanji dari biyar ce!

   ” kawo nakawo chanji!

      ” haba k’ande inna samu chanji zan baki!

   ” iya habu karfa na barki da Allah kikawo sai na dauka..

   ” toh gashi wannan dabi’a take Allah ya shiryeki!

   ” kowa ma shiriyar yake nema ina dalili a hanaka hakki na kinga sai na dawo daga makaranta!

   ” tohm Allah ya tsare….

   ” iya habu ina sonki fa!

    ” nema haka k’ande..Au ke harkin yarda? Ai wannan chanjin nake dare hudu da tamanin kosai zan siya nayi miki sadaka! +

   ” da sauri saurinta tace zo k’ande karki yimin…
    ” ohh to sai nayi kinga tafiyata..

   Salamu alaikum goggo ina kwana?

    ” har an shirya k’ande?

    ” gashi kuwa kinganne ina baba ne?

   ” ya akayi yar gidan baba?

    ” yauwa sannu Alhaji babana kadai ce abinci ko?

   ” eh Aishatu ya’akayi?

     ” a makaranta ance mukai kudin littafi dubu daya! Amma na dura ribata nema 1200 ne…

   ” sadiya tace mtswee sai fitinar tsiya…

   ” Ne kike gayawa haka? Yauwa baba malamar su Sadiya tace tafiye kuli kuli ga tsokana!

    ” ya kabiru Dallah yimana shiru duk wata tsokana ta huce tak’i?

   ” ga kudin makarantar sai kindawo to baba nagode…

Zakuga tsokana da fitina ganin idon ku!

    ” nikike gayawa haka?…

     ” ka huce nagaya makane har shekara nawa kabani?

     ” kabiru yace goggo gayamata shekara nawa na bata!

   ” ba sai tayi asarar fada ba shekara biyu kabani so what?

   ” hahaha yaushe kika san english din har kina wane rawar kai!

   ” ai dai da koyo akan iya komai….

     ” i can’t tolerate any nonsense so getout…

    ” hmm koma mai nene kafada nema wataran zan iya!

     ” baba yace k’ande in kindawo daga makaranta kisameni a gona!

    ” tohm Alhaji baba goggo kiyimun addu’a natafi…

    ” Allah ya shiryeki…

” sukace Amin..

Tafiya takeyi har sai da ta’isa gurin tabawa mai kosai sannan suka gaisa oh tabawa gaskiya kina ciniki…

    ” to k’ande ya san ranki?

    ” kajeki tabawa to ba mutuwa ba! Kibane na dare hudu da tamanin…

    ” kai k’ande ince basata kikayi ba?

    ” mtseww agurin mijinki na koya ince? Kinga zuba mun kokuma intafi banson hayaniya…

    ” ai dan ciniki zakiyi min da wallahi baza’ni baki ba son banzan ki yayi yawa…

   ” har na kaiki? Ke da kikeyin sana’a kintsa kina magana sai kace asararriyar aku malama zubamin…

    ” gashi amma nema ki bani sadakar!

    ” oooh mutum da abunsa Amma yana roko..

    ” hmm sai anjima..

K’ande tana cikin tafiya  taga wasu almajirai azaune sunata wasa kiransu tayi sannan ta basu kosai tare da fad’in Allah yasa naje burni karatu…

   ” Amin k’ande..
   
       ” ina kukasan suna na?

    ” ai munsan sunanki kintaba shigar mana fada komai nake na dabanne ai!

    ” Allah sarki ai dama watarana bawa shi zaiyi nasara..

   ” shiga makarantar ta babu wuya taga wasu mutane kamar turawa sunata turanci tsayawa tayi kusan minti goma can taga ana kokarin rufe gate, baba baba mai gadi ya hakane ai lokaci baiba!
   ” kina can kina k’alle kallin ki ai har tara tayi…

    ” oh ne kande na banu 9 fa kace kudu tasaka takarasa cikin makaranta uncle imran tagani da bulala…

    ” kuka wayyo uncle banda lafiya shiyasa banzo da wuri ba…

    ” na tambayi ke ne? Bani hannun ki!

    ” to to amma nagaya maka banda lafiya!

   ” zaki bani ko sai nasakake tsallen kwado?

   ” Allah y tsare mace da tsallen kwado, ai da yar kace bazaka yimata ba! zauga mata bulala yayi babu shiri ta ruga aguje tana kuka, tana shiga ajin ta samu seat kusa da badariyya ta zauna… +

    ” kande mai yafaru kike kuka?

    ” hum hum hum wai badariyya anya kinje warin bakinki kuwa?

   ” Dariyar da yan aji sukayi yasa badariyya hawaye tace ai ba laifina baniba gawaye nane ya kare!!!

   ” kande tace to kinsan da haka zaki barni na zauna ki saka cikina ya kumbura?

    ” yan class suka kara saka dariya…

    ” goggo tana tsakar gida tana gyara shinkafa sallamar kande ta katseta…

    ” ina kudin iya habu?

   ” lahh goggo itafa tace inyi mata sadaka…

    ” k’ande k’ande kikeyayi fushina to ne banda ko sisi taje tagayawa mahaifinki kuma yabiya ta.. 

   ” kaje iya habun nan…

” goggo tace rashin kunyar zakiyi mata ne..

   ” aa haka nace har tsofa yafara zuwar mata..

  ” salam aishatu inta jiranki a gona!

   ” ya Ali yace ina zatazo hankali bai isheta ba!

   ” ya abbas yace sai kace mahaukaciya…

   “Kut wallahi ne ba mahaukaciya baciba ga mahaukaci can a dangen ku!

   ” goggo ce ta gwabe bakin sa’anki ne!

   ” baba yace baruwan ku da’ita…

   ” aishatu kinason haruna? 

  ” zaro ido tayi tace baba ne kanaso na?

  ” aishatu sosai ma!

     ” to tayaya zaka auramun mahaukaci? To babu wanda na tsana irin shi ma…

   ” kafin takarasa maganar ya Abbas ya wanka mata mari ke ti bari kije haruna yana birni kuma yafi karfin ki banza haruna mai zaiyi da kucaka irinki wawiya jahila…

    ” baba yace kayi shiru abbas yarinya ce fa…

   ” mikewa tayi tana fadin wallahi sai na rama nan ra ruga aguje…

    ” abbas zance mutuncin ka wallhi kudinga kuntata mata! Cewar baba

   ” hava baba yarinyar nan bata da kunya sosai fa…

    ” yarki ce?? To zan saba muku wallhi kuka kara takura mata…

   ” ya kabiru yace wai goggo mai isa baba kison kande ne?

   ” labarin yanada tsawo gobe kutuna min zan baku…

   ” tohm su kace sannan suka fita!

   Iya habu iya habu wallhi bakya kyauta min yanzu kin zata cinye kudin nayi? nayi hakane dan Allah ya yayi wa ya haruna larurarsa!

   Hawaye ne yafara zuba a idon iya habu tace kande na karbe kudin ne domin kince min kina bukatar takalmi dama kudin dana baki na takalmin ki ne!

    ” k’ande ce ta rungume ta iya habu wataran kinfe kowa mutunci fa oh namanta inada aiki! …

    Wane aiki zakiyi k’ande?

   ” Humm ke dai kitsaya zaki gane, takarda ta dakko da bairo tafara rubuta wasika kamar haka…

    ” Assalamu alaikum

  Ne Abbas na tsaneki na kuma rabu dake daga yau zanje burni na auro mace wacce ba jahila ba! In ke ba mayya bace ba karki kara kulani!!!

       ” yauwa iya habu ina turarenki?

    ” wai me zakiye ne?

” Ke dai ki bani, dauka tayi ta faffesa ajikin takardar natafi sai na dawo…

     ” oh ne k’ande Allah yasa ba wata rigimar zaki hada ba…

    ” tunda kande tafito take murna sauri sauri takeyi har ta’isa gidan su dijangala Sallama tayi ta tarar da’ita a soro yauwa hmm gashi inje yaya Abbas…

    ” oh inason Abbas wallhi kalaman soyayyan aka rubuto?

    ” kande tace ina zan sani nidai da masifa ya aiko ne…

    ” to anshi naira 100 tukwuci..anty dijan gala ayi haka? +

    ” haba k’ande *Ai ke ta dabance*…

       ” to nagode sai anjima, tana fita ta labi abango ihun dija tajiyo uwar tana tambayar ta ba’asi!

     ” murna gurin k’ande harda tsalle…

   Ya Abbas yasiya namansa ya tafi gidan su dijan gala da murnar sa yau zaiga abar kaunar sa! Lokacin da ya isa ya aika mata yara sunfi biyar Amma taki fitowa a na shidan ne tafito idonta yayi jajir!

    ” menene ke faru eh dija?

   ” au dama bayan wanda kayimin a rubuci akwai wanda zakayi min da bakinka nagode da yaudarata dakayi wallhi Allah ya’isa mugu azzalumi…

    ” dija gala me yafaru? Me nayi???

       ” wannan fifar daka cimin mutunci acikin ta akwai abunda zaka karasa ne da bakinka?.
   
   ” muga lokacin da ya karanta sai da gumi yantsitto masa, waya kawo miki takardar?

    ” k’ande ka aiko aikasani…

    ” k’ande?  K’ande?? k’ande……

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]