GAMAYYAH CHAPTER 3

Advertisements

_____

GAMAYYAH


CHAPTER 3


Sashen sultana zaarah aka nufa da Asma’u dake waiwayen qofar sashen da aka baro bulama tanaji ajikinta shikenan sungama rayuwarsa atare saidai jiran lokaci kuma.

Lokacinda aka kaita gaban sultana aka gabatarda ita amatsayin kyauta daga yarima.

‘Dagowa tayi cikin wani irin farin ciki da murmushi takalli asma’u cikin sanyin lafazi tace,

Allah yayiwa yarima albarka bisaga wannan kyauta.

Sake kallon asma’u tayi dake durqushe gabanta tasaki murmushin farin ciki murya a tausashe tacewa jakadiyarta.,

Akaita abata ‘daki sashen bayi abarta tayi kwana biyu ana koyarda ita aiki kafin tadawo nan tafara aikinta.

Angama sultana.

Daki aka bawa asma’u kuma cikin sa’a aka basu daki daya da mamani suka zauna jigum jigum kowa babu da’din zuciya kafin aka sake zuwa aka tafi dasu bayin bayi kowannensu yayi wanka aka rarraba musu uniform dinsu sukabi layi aka basu abinci kowa da ‘yar tasarsa
Anan ne asma’u suka hadu da bulama saidai iyakacinsu kallon juna sbd Layin maza dabam na mata dabam hakama ga dukkanin alamar tsaro da dokokinda suka lura dasu agurin babu bawanda ya isa ko yakeda ikon yiwa baiwa magana sbd tsaro dakuma gudun 6arna irinta zina.

Duk wanda aka bawa samun guri yake a babban filin ya zauna yafara cin abincinsa.
Daga ita harshi ba wanda ya iyacin abincin sai kallon juna suke daga nesa ba ikon magana har aka gama aka gargadasu aka rarrabasu zuwa sassan dazasu riqa aiki kullum.

Kwanansu biyu da zuwa jikinsu ya’dan murmure daga yunwa sbd issashe kuma lafiyayyan abincinda ake basu sbd Sam babu yunwa ga bayin masarautar.
Asma’u da bulama iyakacinsu da ganin junansu idan suka hadu gurin cin abinci.

Ganin basuda yunwa kuma babu azabtarwa a masarautar yasa hankalinsu yadan kwanta suka fara maida hankali ga ayyukansu damuwar bulama ‘dayace cikin jikin asma’u da mamani.

Sosai asma’u ta dangana ta rungumi rayuwar dasuka tsinci kansu ayanxu tabi uwargijiyarta sbd ganin tana sake mata ba laifi.

Aiki da bauta takeyiwa sultana tuquru babu kyuya ga tsafta da tsananin ladabi.
Tunda sultana zaarah ta lurada cikin jikin asma’u tayi mamaki sosai ziciyarta tashiga wasu wasi takasa hkr ta tsare asma’un ta tambayeta cikin ladabi kanta na qasa tabata labarinsu kaf saidai ta boye mata asalinsu da dalilin barowarsu gida.

Cikin tsananin tausayawa sultana tace,

Karki damu asma’u Allah baya bacci kuma insha Allah za’a dauki mataki akan masu kamo bayin koba yanxu ba nasan zasu dawo.

Sosai sultana tasa jakadiya sassautawa asma’u ayukanta sbd yanayin cikinta daya tsufa kuma sosai sultana keyiwa asma’u kyautar fresh fruits masu yawa sbd anason mai ciki ta yawaita cinsu.

Kasancewarsu kusan sa’anni yasa sosai sultana tasa asma’u tasaki jiki da ita tun tana noqewa harta ‘Dan sake idan tagama ayyukanta zata zauna gaban sultana suna ‘Dan ta6a fira wani zubin harda jakadiya.Cikinta na isa haihuwa cikin ikon Allah suka haihu rana ‘daya da mamani dake aiki sassan sarauniya adama.

Dukkaninsu ‘yaya mata suka Haifa sultana dakanta tasa akai mata iso ga sarki tasanar dashi matar mafi soyuwar bawansa ta haihu tasamu mace.

Shiru yayi cikin jinjina alamarin bayi kuma da haihuwa amma saiya share sbd bayason sanin komai yanxu tunda anriga anyi haihuwar yabawa bulama dama yaje yaga yarsa yayi mata huduba.

Koda bulama yaga ‘yarsa hawaye 6alle masa sukayi sbd tarigada tafado daga bayi irinsu shikenan ita rayuwarda Allah yaxabarmata kenan.

Huduba yayi mata kafin ya ‘durqusa har qasa yamiqawa sultana cikin girmamawa yace,
Kece kika cancanta daki za6a mata suna.

Yarima daya fito sashen sultan yaqaraso sashen sultana yana shigowa yaji zancensu kai tsaye yakalli yarinyar yakalli sultana yace,

Asaka mata UMMU-RUMANA..

Kallonsa sultana zaarah tayi fuskarta daukeda murmushi tace,

Mahaifiya kayiwa takwara maheer.

Mayar mata da murmushin kawai yayi tareda jinjina kai ahankali ya shafo fuskar jaririyar yace,

Allah ya raya ummu-rumanah.

Yana gama fadar haka ya wucewarsa sultana takalli bulama tace,

Allah yaraya ummu-rumanah.

Amin sukace cikin farin ciki da godiya harda jakadiya.

Yarinyar mamani ma shine yayi mata huduba mamani tasawa ‘yarta suna NURATU.

Tunda asma’u ta haihu hankalinsu yasake kwantawa itada bulama tuni suka maida hankali ga bautarsu
Idan zatazo sashen sultana adaki suke barin ‘yayansu itada mamani daga baya sultana tace tariqa zuwa da ummu-rumanah

Sosai lokaci yaja tuni ummu-rumanah ta fara girma
Daga ummanta sai sultana da jakadiya tafi sabo dasu sai nuratu dasuke wasa tare a can sashen bayi mahaifinta ta saba dashi sbd ana ‘Dan basa damar zuwa ganinta itada ummanta wasu lokutan da haka rayuwa tayi nisa sosai.

Sultan an wayi gari baida amintaccen bawa kamar bulama sbd takai ko fita za’ayi wata qasar da amintaccen bawansa bulama yake zuwa gashi da tsananin biyayya da taka tsantsan sbd sultan nada qarfin mulki da iko sosai da wasu irin dokoki.

Ummu-rumanah nada shekara goma sha hudu cif aduniya Allah yayiwa bulama rasuwa sanadiyar ciwon ciki.

Anji mutuwarsa duk da kasancewarsa bawa hakadai asma’u da rumanah suka dangana da rashinsa saidai rasuwar ta ta6a asma’u sosai,
Ta rasa lafiya da nutsuwar zuciya tun tana daurewa tuni ciwo ya kwantarda ita hakan tasa rumanah karbar ragamar aikinta a sashen sultana.

Kwanciyar hankali tuni ta qauracewa rumanah ganin babu uba ga uwarta na jinya sosai

Sultana ma tana cikin damuwar ciwon asma’un Dana matuqar tausayin rumanah sbd jin asma’u takeyi tamkar ‘yar uwarta ta jini rumanah kuwa dama amatsayin ‘ya take agareta sbd tun tana shan nono tayi sabo da yarinyar.

Anyi maganin har andanga anbarwa Allah ikonsa amma jikin yaqi sauqi ganin haka sultana ta ‘yantata nanda nan aka shelar an ‘yanta baiwa asma’u.

Rumanah ga abin farin ciki amma Sam batajinsa ita kadai tasan yanda takejin zuciyarta ganin mahaifiyarta sai qarayin nisa takeyi.

Cikin dare Allah yakarbi rayuwar asma’u tabar ‘yarta cikin wannan duniya mai ababen tsoro. 1

Rumanah kam zuciyarta bushewa tayi sosai tabawa kowa mamakin rashin kukanta har aka kai asma’un aka dawo.Sultana zaarah lokacinda ta aika kiran rumanah tana zuwa ta durqusa gabanta kallon rumanar tayi batasan lokacinda hawaye suka taru a idonta ba tayi sauri shigewa qurya sai alokacin rumanah tasaki wani kuka daya tokare qirjinta ta zube agurin tanayinsa jakadiya tayi saurin jawota jikinta tana lallashinta. +

Andauki tsayin lokaci kafin rumanah tasaba da rayuwa ba iyayenta ga 6angare guda mamani Sam bata qaunarta bare ta rage maraicin rashin uwa sbd da mamani da nuratu take kallo amatsayin jininta.

Sultana zaarah kuwa sosai take nuna qaunarta rumanah wanda itama rumanah tana qaunarta sbd ita take gani tana rage kewar ummanta.

Da haka rayuwa taja harsuka qara zama ‘yan mata ta maida hankali sosai ga bautawa ummy kamar yanda take kiran sultana zaarah.

********
ABDULSHAMS IBN ABDALLAH MUHD shine sultan na yanxu dake mulki a meneelik wani yanki na babban birnin ethopia kamar yanda kakanni da iyaye suka bar masa, 6

Mulkinsu wani irin tsauri da zafi dashi ga wani irin qabilanci dasukedashi sbd Sam basa bayi ko borori da ‘yan qasarsu saida akawo musu na wata qasar su siya shiyasa yawanci bayin masarautar daga qasashe dabam dabam suke mafi yawansu Nigeria sbd rashin tsaro na zama Dan qasa da ‘yan Nigeria sukedashi.

Tun lokacin mulkin kakanni a wannan zuriar ta ABDALLAH muhd basuda yawan ‘yaya maza saidai mata wanda hakan yayita kawo barazana ga barin sarauta da mulki daga zuriar.

Duk wani kalar arziki na duniya Allah ya hore musu shi kobana sarautataba amma banda yaya maza daqyar cikin yardar Allah suka samu namiji ‘daya cikin ‘yaya mata goma sha biyu da sarkin yakedasu daga matansa uku.

ABDULSHAMS shine yazamto namiji daya kuma ya gadi sarautar bayan rasuwar mahaifinsa ABDALLAH. 1

Tun yana yaro qanqani mahaifinsa yake cusa masa qaidoji da hukunce hukunce masu zafi sbd karsuyi sake sarauta tabar gidansu matuqar ba magaji sbd arubuce yaje a aje duk ranarda suka wayi gari sarki ya mutu ba magani to masarautar da duk wanda ke cikinta zasu zamo qarqashin ikon masarautar kilaimee tamkar bayi dundaga kan matan sarki da ‘yayansa har bayinsu sbd wata tsohuwar muguwar gabace atsakanin masarautun.

Hakan yasa duk wanda yayi mulki basa tsayawa kan matansu da qwarqwarori suke qarawa amma duk da haka sunada qarancin maza sosai sai arzikin ‘yaya mata.

Yanxu lokacin mulkin sultan abdulshams yanada matuqar zafi da tsanani amma duk da haka baiyi na iyayensa da sauran sarukan dasuka gabata.

Zafinsa yasa dukkanin fadin qasar da zagayen ake tsoron hukuncinsa shiyasa kowa a ankare yake ba’a take dokar sultan ko acikin matansa bare ‘yaya kafinma akai ga ‘yan qasa da bayi.

Matansa biyu sultana zaarah ‘yar sultan jalaludden sarkin Libya.
‘Sai sarauniya adama ‘yar tsohon wazirin mahaifinsa. 3

‘Yayansa goma cif duka mata sai yarima tak shine namiji.

Sultana zaarah keda yara hudu
Amatullah,hindu dakuma maryamah duk suna aure,
Amatullah da maryamah a Libya qasar mahaifiyarsu suke aure sai Hindu dake aure Kuwait,yarima shine qaraminsu.

‘Yayan sarauniya adama shida dukkaninsu mata kuma duka sunyi aure sai autarta najwah.

Duk qwarqwarori da sultan yake kwana dasu Allah baiba ko ‘daya daga cikinsu cikiba bare tahaifi ‘da namiji
Hakan yake tsananin ‘daga hankalinsa ga tsufa yafara kamasa yarima yafito fili yafada bayada ra’ayin mulki ko wani Abu daya danganci sarauta

Kwata kwata rayuwarsa bata yanayi damai sarauta sbd tunda yagama primary aka kawosa Greece karatu harya gama yacigaba da degree dinsa a los Angeles kafin yayi masters duk akan doctoring shiyasa rayuwarsa kwata kwata ta turawa ce,
Daga nan yadawo da rayuwarsa a Georgia inda Yayi settling yafara aikinsa anan.

Sam bai cika zuwa gidaba sbd yanayin aikinsa dakuma rashin son rayuwar masarautarsu koina mutane,koina bayi Sam shi bayason gurunda zai kasance da mutane sosai yanason free life bayason takura shiyasa yake ganin zama acan gida is a punishment.Maheer mutum ne mai ra’ayin kansa wanda wani baya saka masa ra’ayi,
Abokansa mafi yawansu turawa ne sai ‘Dan uwansa kuma abokinsa dasuka taso tare khaleefa duk da kasancewar basa guri ‘daya shi khaleefa yana turkey ne amma suna yawan kasancewa tare idan zasuzo gida kokuma idan sun tafi wata qasar Hutu,

Shiru shiru ne baida doguwar hayaniya bare son dogon zance amma ahaka so silent dashi Allah yayisa mai tsananin son rayuwar hutawa da shaqatawa batareda takurawa ba sam shi mutum ne maison life shiyasa kana ganinsa zakaga wayayyyan mutum da ilimi ya kustsa sosai tareda Hutu da naira.

SUHAILAT BOUKAR itace gidanta yake kusadana maheer ‘yar asalin Mali karatun masters dinta takeyi anan qasar
Sosai take shiri da maheer kasancewar sunfara sanin junane sanadin abokinsa bell dayake itama friend dinta.

Sunfara gaisawa ahankali harsuka saba kasancewarsu wayayyu masu ilimi yasa suke jin dadin zama da juna sbd kowa yasan abinda yakeyi kuma kowannansu is living a free life.

Itadai suhailat tana tsananin son maheer amma ganin babu wannan ataredashi yasa tayi amfani da iliminta ta danne tareda 6oyewa koda wasa babu wanda zaice yaga alamar sonsa atareda ita sbd sanin ita mace ce meye amfanin iliminta ta wannan fannin idan bazata iya danne soyyayyar wanda baimasan tanayiba.
TAKE NOTE ‘yan mata pls mu koyi boye soyayyar wanda baisanma kanayiba ki daraja kanki na zamantowarki mace. 3

Sultana ma ba laifi sundan saba da suhailat harkiranta tanayi ta gaidata.

Duk lokacinda yazo gida maganar sultan ‘dayace wato yayi aure asamu ‘da namiji sbd dukkanin hope dinsu yanxu akansa yake
Shi alamarin na matuqar basa ciwon kai da mamaki idan ana cewa yayi aure ya haifi ‘da namiji
He is man of his own now baiga dalilin dazaisa ace anason dole yayi aureba duk lokacinda yaji yafara buqatar kasancewa da mace zaiyi auren amma ba haka kawaiba yanxu yayi aure.

Ammynsa nason yayi auren amma ita lalla6asa takeyi bakamar sultan dake son nuna masa qarfin iko ba kuma tasan tunda sultan yace maheer ‘din yayi aure to kobai tashiba sai yayi masa koyasan matar kobai santaba.
Hakan yasa sultana take kaiwa maheer ‘din ziyara idan aka ‘danja lokaci tana rarrashinsa amma dai still babu alamar zai takura kansa yayi yanda sukeso ‘din shiyasa ta hakura lalla6a sultan akan abi maheer din ahankali abarsa har zuwa lokacinda zaiji ra’ayin yin auren.

Wani shu’umin murmushi sultan yasaki lokacinda tagama fadar zancen wanda yasa gaban faduwa sbd tasan itama fada kawai tayi ko za’a dace yaji shawarar tata amma tasan sultan Sam baya ‘daga qafa ga wanda ke masa garaje.

Washe gari tun agurin sallar asuba aka bada shelar saqon sarki na bayan sallar juma’ar satin nan za’a ‘daurawa yarima aure.

Koda labarin ya iso kunnen sultana ajiyar zuciya kawai tayi ahankali batareda tace komaiba Dan tasan dole haka zata faru tayi magana asata kullen shekara.

Haka dai cikin dauriya sultana ta daure tagabatarwa da sultan SUHAILAT amatsayin wadda yarima yake kulawa acan inda yake.

Tsaf tabasa bayanin komai akan suhailat babu bata lokaci akai aike ba laifi ‘yar manyan mutane ce ita da yayanta kadai iyayensu suka haifa rayuwarsu ba takura suna yin rayuwarda duk sukeso amma sbd wadatar ilimi yasa Sam basa iskanci amma rayuwa tajin dadi da Hutu babu wadda basayi musamman arziki da Allah yahorewa iyayensu.

Sanin waye maheer da mugun ra’ayi akan abinda baiyi niyaba yasa sultan cewa sultana Zaarah ta koma masarautar mahaifinta batareda bawa ko ‘dayaba harsai ranarda matar maheer zata shigo masarautar sushigo tare.

Rintse idanuwa tayi cikin ciwon rai da tausayin maheer sbd daga ita har maheer da kowa yasan abinda sarki ke nufi da hakan
Wato tayi gidansu harsai maheer ya aminta da zaiyi aure bayan yasan hakan zai ta6a tarihi da sunan masarautar mahaifinta.

Kwana biyu tayi tana hada kayanta sbd tuni akayi mata booking ticket ‘din jirgi.

Lokacinda labari ya iso gurinsa rintse idanuwa yayi cikin daci da radadin zuciya sbd yasan me sultan ke nufi da hakan,
Duk lokacinda yakeson wani Abu daga garesa da da ammynsa yake yaqarsa.

Bude jajayen idanuwansa yayi yakalli wayarsa ya dauka babu bata lokaci yakira sarkin isarda saqo yana ‘dauka da wata irin murya mai nuna 6acin rai dayake ciki kai tsaye yace,

A isarwa da sultan saqon abar ammynah ta tarbi matata ranar dayakeso.

Angama sarkin saqo yafada cikin matuqar girmamawa kafin ya garzaya da hanxarinsa ya isarda saqon.

Murmushin manya sultan yayi yace,

Kasanar masa ranar juma’a ne saiya shirya dawowa idan kuma baidawoba ranar asabar sultana zata kawo masa matarsa har inda yake.

Koda aka sake Isar masa da wannan saqon datse wayar yayi tareda rintse ido ya budesu jajir sbd baqin cikin yanda idan sultan nason quntata masa yakeyi ta hanyar ammynsa
Banda son a xafafa zuciyarsa ace idan baijeba mahaifiyarsa za’asa takawo masa mata har wata qasa sbd anraina masa ita….

Wurgi yayi da tumbler din hannunsa a qule yace,

Wat did he think of himself sultan dayake masa haka bayan yasan he can’t tolerate seeing his ammy being disrespected.

Baigama shan haushi da mamakiba saida yakoma yatararda lbarin suhailat ce amaryarsa
Duk inda ransa yake saida ya sake 6aci sbd rashin tunanin dama tun farko ita ‘din yagabar tun kafin aci zarafin ammynsa sbd yasan idan ya auri suhailat kowa zaiyi rayuwarda yakesone babu takura sbd dukkaninsu sunada ilimi da wayewar bawa junansu freedom batareda damuwar komaiba.

Hakan yasa ba laifi ya tsaya akayi duk wani biki daza’ayi aka daura aure aka kawo amarya.

Abu ‘daya daya sani shine haihuwar da’akeson yayi rututu kamar ta awaki bazai yitaba sbd atsarinsa ‘yaya uku zuwa hudu sun ishesa sbd gidansa da familynsa suxamto yanda yakeso baya sha’awar yara da yawa bare ayi zancen mata biyu Wanda shi yana ganin Sam bazai iya ya kwana da wancan yazo yakwana da wannan ba koba komai baya tunanin zaiso mata biyu dole ‘daya zaiso so babu mgnar adalci agurin Dan haka Sam babu tsari bare mafarkin auren mata biyu arayuwarsa koba komai shi mutumne mai tsananin qyanqyami haka Allah yayisa.

A ranarda aka kawo suhailat aranar yayiwa sultan yanda yakeso yayi kwanan aureda ita
Satinsu biyu suka tattara suka koma Georgia shida suhailat.

Suhailat tasan Sam babu so atsakaninta dashi saidai wayewarta da iliminta tareda zamantowarta free yasa yakejin dadin zama da ita kuma shima sbd yanada wadataccen ilimi da wayewa yasa Sam babu ma alamar datake nuna baya sonta as far as suna respecting juna dakuma respecting ra’ayoyin junansu ya ishesu zaman aure sabanin wasu mazan dake nuna qiyayyar mace qarara Wanda hakan ba halin namiji mai ilimi bane so pls marubuta mu gyara Sam duk namijin dayakeda ilimi da wayewa baikamata ariqa sashi yana nunawa mace tsana afiliba da kyararta,idan yanada ilimi to yayi amfani dashi. 2

Wata uku da komawarsu ciki ya 6ullo nan saqo ya isa masarauta farin ciki da murna suka kama koina sai sadakar maqudan kudade akeyi da kyaututtuka baga masarautar ba kawai duk ‘yan mineelik duk wani mai arziki kyauta da sadaka yakeyi na farin cikin insha Allah za’a samu magaji amasarautar dazata hanasu zamantowa qarqashin wata azzalumar masarautar.

Lokacinda cikin ya isa haihuwa suka dawo gida ranar haihuwa kaf koina ba wani hayaniya ko ‘yan kasuwanni basu firfitoba hakadai ake zaune zaman jira baga sultanba baga ‘yan fadaba baga ‘yan gariba,

Masarautun dasuke abokantaka datasu masarautarma yau duk cikin jiran haihuwar suke suna adduar samun namiji.

Bayi kuwa sunsan yau qaddara tasasu yin laifi saidai wani kan badai nakaba shiyasa kowa ya nutsu anata addua.

Sultan dai yau yasan ‘yancin masarautarsa ya dangana ne da abinda za’a haifa shiyasa yau tsit yake yana lazimi cikin ransa.

Sultana zaarah nacan sashen da ake kar6ar haihuwar sbd haihuwar tazo da gardama
Su jakadiya sai shar6e zufa akeyi ga kuyangi da bayi ajere kofar sassan haihuwar sai gumin wahala da fargaba sukeyi sbd sunsan yau duk aka haifi mace ‘daya daga cikinsu ne zaije isarda mummunan saqonda qila abakin lafiyarsa ko ransa shiyasa gabaki ‘daya a tsure suke da fargaba tareda adduar samun namiji.Yini guda cur masarautar tayi cikin zaman jiran haihuwar suhailat,
Maheer kuwa duk yanda kowa ya ‘daga hankalinsa bai ‘daga nasaba sbd yasan dukkaninsu damuwarsu ba akan lafiyar matarsa yakeba sai akan abinda za’a haifane yazamo namiji,
Shi tausayinsa akan suhailat din ne duk da yasan tanada dauriya sbd zama da ita yanxu yasa yasake sanin halayyarta tanada juriyar danne abu ta 6oyesa acikin ranta duk qwaqwarka yanada wuya ka gano abunda ke ranta shiyasa take matuqar basa tausayi sbd shikuma mutum ne da idan bayason Abu baya iya tsayawa basa kulawarda yakamata,
Tasani babu sonta aransa amma baya nuna mata wasu halayansa ke nuna mata saidai son rayuwarsa yasa dukkaninsu jin dadin rayuwar aurensu sbd sunayintane very romantic sbd maheer romantic life is one of the best abinda yafiso arayuwarsa.

Zaune yake a lafiyyan palonsa dake sashensa idanuwansa a lumshe kwata kwata bayan hot coffee dayasha dasafe har lokacin baici komaiba duk da ankawo abinci daga kicin din sashen ammynsa anjere masa dama kaidarsane bayacin abincin kowane kicin saina sashen mahaifiyarsa.

Lokacinda limamin masarautar yakammala kiran sallar magriba daidai lokacin suhailat tayi wani yunquri tareda wahalallen nishi cikin tsananin azaba baby yafado.

Su sultana da sarauniya adama tareda sauran ‘yaya mata na zuriar gidan dake kusa duk sunzo suka miqe kusan atare kowa na kallon quryar ‘dakinda suhailat din take ciki.

Bayi da kuyangi tuni suka sake gyara tsayuwa suna hadiye yawun fargabar meza a fito ace anhaifa.

‘Daga jaririyar mai karbar haihuwar tayi tareda kallonta taga mace ce aka haifa
Ta ‘dago takalli jakadiya tana ha’do sabon gumi ta miqa mata jaririyar.

Karbar jaririyar jakadiya tayi tana kallonta yanda take canyara kuka ta qura mata ido tareda sauke nannauyar ajiyar zuciya tamiqawa masu gyarata ta fita tana tattaro kuzari ta iso gabansu sultana ta tsaya tareda sunkuyardakai tace,

Allah yaqaramiki hkr da lafiya uwar ‘dakina Allah ya albarkaci yarima da samun ‘YA MACE.

Wata irin 6oyayyar ajiyar zuciya sarauniya adama tasauke zuciyarta na cika da wani irin farin ciki amma afili kallon dakinda suhailat take ciki tayi tace,

Akimtsa uwar da ‘yar amaidasu sashensu
Jaririyar akawomin ita nizan kaiwa sultan.

Sultana ganin adama tayi mgn yasa ta ‘dagawa jakadiya kai tareda cewa jakadiya akula sosai da suhailat ta juya ta fice kuyanginta na bayanta.

Lokacinda labarin haihuwar yagama isa koina sultan baice komaiba yace akaiwa maheer ‘yarsa yayi mata huduba.

Bayan maheer yayi mata huduba aka maidawa sultan ‘yar yasa mata suna AMATULLAH.

Ba laifi anyi shagalin suna duk wani gata anunuawa suhailat da ‘yarta duk da dai tana saneda ba wani farin ciki kowa keyi da haihuwar ba.

Adama kuwa sbd jin dadin ansamu mace ba namiji ba har wani soyayya take nunawa amatullah.

Watansu ‘daya maheer yakoma itakuma ta tafi Mali ganin gida kafin daga can takoma Georgia tasamu maheer.

Bayan komawarsu suka cigaba da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali kuma sosai maheer keson amah ‘dinsa sbd yarinyar babu abinda tabaro nasa na kamanni shiyasa koyaushe take sake shiga ransa.

Ta bangaren suhailat kuwa saidai tacigaba da sawa kanta dangana da hkr saidai tunda yanason ‘yarta hakan naqara saka mata nutsuwa da kwanciyar hankali.

Tunda suka koma cikin dubaru sultana ke ‘Dan lurarda suhailat akan kada tayi family planning

Tunda suka dawo yamaida hankali ga rayuwarsa yamanta da wani batun samun magaji da sultan keso.
Shekarar amah ‘daya da sati biyu aka sake tabbatarda ciki jikin suhailat nan aka sake shiga ‘doki da duqufa addua da sadakoki akan Allah yabiya buqata.

Wannan karon saida cikin ya tsufa sultan yasa suka dawo akaro na biyu ranar naquda akayi jigum jigum jiran tsammani
Allah mai yanda yaso tasake haihuwar ‘ya mace. 1

Ita kanta suhailat tayita adduar Allah yabada ‘da namijin sbd tafara hangowa kanta da ‘yayanta kyara nan gaba.

Kai tsaye sultan yace kar akawo masa jaririyar akaiwa maheer yayi mata huduba da suna gabaki daya.

Yarima yayiwa ‘yarsa huduba yasaka mata suna fammah. +

Wannan karon babu wani shagali ganin haka yasa yarima ya tattarasu suka komawarsu.

Shekarar fammah daya da wata uku suhailat tasake samun ciki wannan karon ma sultan bai cire raiba yace sudawo
Satinsu biyu da dawowa ta haifi mace amma ‘yar kwana biyu da haihuwa ta rasu ganin haka suka komawarsu sbd wannan karon Sam ita suhailat yanxu ta rage jin dadin masarautar sosai sbd sultana ce kawai ke qaunar ‘yayanta sai adama dake yimusu soyayyar dole.

Ayanxuma tana ‘daukeda ciki tsoho sultan yace suyi zamansu harsai ta haihu anji me ta haifa saigashi ankuma samun mace shine sultana taje tafada masa.

Ganin wankin hula na Neman kaisa dare yasa ya yanke hukuncin yarima zaidawo gida atara masa barori koda za’asamu qaruwar ta hanyarsu.

Basu dawo Ethiopia ba Mali suka wuce acan gidansu suhailat sukai hutunsu na kusan sati biyu cikin jin dadi sbd gidansu gidan wayayyin mutane ne masu ilimi gasu amah ma sunason nan ‘din sbd suna sakewa sosai ga qaunarsu da Granny’s dinsu suke musu.

Daga Mali komawarsu sukayi Georgia tareda yaransu sukaci gaba da rayuwarsu.

Maheer duk cikin yaransa uku babu kamar amah acikin ransa yana tsananin qaunarta Wanda suhailat ke adduar Allah yasa ko kwatankwacin rabin qaunar dayakewa amah tasamu daga garesa.

Maheer da family dinsa wata irin rayuwar turawa ta jin dadi sukeyi babu damuwa babu takura.

Yaransa sun taso cikin turawa da yanayin rayuwar turawa dasuka ga iyayansu aciki
yanayin fatarsu dakeda sirkin yellow da brown kawai zaka zaka kalla kace musu black Americans batareda kasan asalinsu ba.

Baby AMNAH Nada shekara biyu tasake samun ciki wannan karon yazo mata da laulayi da nauyin jiki sosai shiyasa ta rage fita aiki sosai dakuma kula da gidan ta 6angare ‘daya ga amnah babu lafiya yarinyar tun tana jaririya take fama da pneumonia Wanda idan ya tashi yana wahalarda yarinyar sosai hakan yasa iyayenta ke tsananin qaunarta.

Yau tun safe jikin nata yatashi sosai sbd kwana tayi yau bada sweater da socks ajikintaba.

Koda Carolina ta shirya amah da fammah shirin zuwa school sukai breakfast
Amah ta nufi hanyar palon dadynsu da gudu tana cewa,

Dady we’re running late pls come out.

Fitowarsa daga wanka kenan ‘daureda White towel yajiyo muryar amah ‘din ya lumshe ido ya bude yakalli agogo yana cewa,

Amah will kill me today for this.

Kallon suhailat yayi data fito daga dressing room ‘dinsa daukeda kayanda sabon towels guda uku zata kai toilet yace,

Ki taremin ita na shirya zata cikamin kunne ne da surutu nakasa shiryawa.

Aje towels din tayi bakin king size bed din dake cikin qaton hadadden bedroom din nasa ta nufi qofa tana cewa,

Amah nima wlh bazan iya da surutunki ba.

Tana fitowa amah na kama handle din dakin.

Kamo hannunta tayi tana cewa,

Let’s go and check on amnah before your dad comes out….

Tsayawa tayi tareda 6ata fuska zatayi kuka 
Suhailat tayi saurin janta suka nufi room ‘din yaran dake tsare dakomai na yara.

Saurin isa tayi gurin amnah dake kwance agadonta tana fusgar numfashi daqyar.

Daukarta tayi da sauri tareda dubata taga ciwontane yatashi cikin karaji ta qwalawa Carolina kira jikinta na rawa.

Da hanzari Carolina ta iso tana cewa,

Yes ma’am.

Cikin daga murya rai amatuqar 6ace tace,

Are you trying to kill my poor baby by letting her sleeps without any sweater and socks?

Arikice takalli suhailat cikin rudewa tace,

I’m sorry ma’am but I…….

Just shut up I don’t want to hear your stupid silly excuses
Hw can you be so careless and…..

Keep quite suhailat””’ sukaji daga bakin qofar dakin ta juyo takallesa cikin takaici tace,

Baby pls…..

I said keep quite suhailat”” yasake fada yana kallon yanda Carolina ke sheshekar kukan fadanda suhailat tayi mata yace,

Why do you always wants to make things worst? Yanxu kinxo kinsamu halinda amnah take ciki instead kiyi saurin bata taimakon gaggawa kintsaya hayaniya and you seriously know hw much I hate that,Ga yara basu wuce school ba kinanan kina fada kinkasa tsayawa kiji wat was trying to say. +

Hawaye ne yaciko idon suhailat takallesa lokacinda ya juya yafice yana zuwa palo su amah suka bisa mota suka shiga ya wuce yafara ajesu school ya nufi gurin aikinsa.

Bayan fitarsa share hawayenta tayi ta miqawa Carolina amnah tace,

Quickly remove her pampy and dress let me go and change we’re taking her to the hospital.

Lokacinda suka fito tuni jikinta yaqara rikicewa tun a mota takirasa.

Tsaye suke ya zuba dukkanin hannuwansa a aljihun trousers dinsa fuskarsa sai wani irin kwarjini da glowing takeyi sbd kyan fata da hutu yana sauraron bayanan wasu new doctors da aka kawo asibitin wayarsa tayi ringin yakalli nurse din dake tsaye riqe da kayansa na theatre da wayarsa tareda wasu folders din patients din dazaiyiwa aiki ya miqa mata hannu ta miqo masa wayar yana ganin suhailat ce ya rufe idanu ya bude tareda dauka yana komawa office dinsa na qurya.

Sanin bayason hayaniya da tashin hankali yasa ta daidaita nutsuwarta tareda share hawayenta tana 6oye kukanta tace,

Baby my amnah is leaving me wlh I can feel it…

Rufe ido yayi ya bude Wanda yazamo ‘dabi’arsace yin hakan duk zaiyi mgn sbd tattaro maganar kasancewar baifiyason dogowar magana.

Jikin ne?

Eh baby kwata kwata she’s not breathing she’s loosing it….

Bring her to hospital yanxunan.

Muna hanya already.

Kashe wayar yayi tareda mayar da hannuwansa aljihu ya rufe ido.

Suna isowa akayi gaggawar fara bata taimakon gaggawa ta hanyar saka mata oxygen saidai tariga tayi nisa sosai mintuna talatin da zuwansu Allah yakarbi ranta.

Cikin jinjina alamarin doctors din dake kanta suka gama rubuce rubucensu tareda kallon maheer da suhailat ke jikinsa tana kuka sukace,

Sorry doctor maheer we lost her.

Wani irin kuka suhailat tasaki tana qanqamesa 
Rintse idanuwansa yayi ya rungumeta yana bubbuga bayanta batareda yace komaiba

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

GAMAYYAH CHAPTER 11

Advertisements _____ GAMAYYAH CHAPTER 11 Kallon adama dake qoqarin saukowa gado yayi yaga yanda jikinta …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *