[Advertisements⬇️]

GAMAYYAH CHAPTER 2 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GAMAYYAH


CHAPTER 2
Asma’u bilalu bulama shine asalin sunan mahaifiyarta asalinta ‘yar qasar Nigeria ce ubanta bilalu dan Maiduguri sai mamarta ummu-rumana shuwah ce. +

Bilalu bulama Nada tarin dukiya mai yawa hakama matarsa ummu-rumana kasancewarta tanada gadon iyayenta dasuka barmata.,
‘Yarsu qwaya ‘daya tak aduniya Nana asma’u wadda duk wata soyayyarsu da burinsu sun ‘dorasa akanta.

Bilalu bulama Nada qanne biyu jabir bulama da salmanu bulama
Kowannensu matarsa ‘daya da ‘yaya uku uku banda bilalun dakeda ‘ya daya,

Jabir babban dansa shine ishaq sai qannensa mata biyu hassana da husasaina,

Salmanu kuwa sunan babban dansa bulama sbd sunan mahaifinsu yaci sai qaninsa babaye da yakurah.

Kowannensu nada arziki daidai gwargwado amma ba kamarna bilalu ba sbd shi ba qaramin arziki Allah ya hore masa Wanda hakan yasa shedan yashiga kwadaitawa qannensa dukiyarsa nan kowannensu yafara qoqarin ganin ya cusa dansa gurin Neman ‘yarsa Nana asma’u,

Tun kowanne natura babban ‘dansa a 6oye gurin neman soyayyar asmaun hardai kowa yafito fili yanuna buqatarsa tason nemawa ‘dansa auren,

Alhaji bilalu baiyi tunanin komaiba saima farin ciki dayayi saidai abun daga baya lalace sbd fada da tashin hankali daya shigo ciki sbd tuni kawuna suka rarrabe sbd alamarin ganin haka sai alhaji bilalu yace abari asma’u tazaba Wanda takeso acikin yaran dakanta sbd ya fahimci bulama shine Wanda tafiso kuma maganar gaskia yafi ishaq nutsuwa da tarbiya ga hankali amma shi bazai fadaba saidai ita asma’u tafada Wanda takeso dakanta.

Tashin farko da’a tambayeta gaban kowa ba 6oyo ta za6i bulama

Hakan datayi shiya qulla wata irin qiyayya da sabani tsakanin jabir da yayyunsa bilalu da salmanu.

Bayan auren da wata biyar aka wayi gari gidan alhaji bilalu ya qone qurmus dagashi har matarsa ummu rumana babu Wanda yafita kuma a iya binciken da akayi aka gano wutar dai kunnata akayi da man petrol.

Haka akayi zaman makoki aka watse dakyar aka samu asma’u ta dangana Wanda saida aka hada da adduoi da sauke al-qur’ani kafin tadawo daidai.

Duk inda hankalin alhaji jabir da ishaq yake yasake hargitsewa sbd sai yanxu kukaga wautarsu ta kashe su alhaji bilalu sbd yanxu duk tarin maqudan dukiyarsa yarsa zata gada tokuma ai mijinta da uban mijinta suzasu juya dukiyar kenandai alhaji salmanu yayi arzikinda ba ranar qarewarsa shikenan shi yatashi abanza.

Cikin watanni hudu shida ishaq sunkasa sukuni suna qulla yanda zasu qwato dukiyar su raba su salmanu da ita.

Ranarda suka gama qulla suka aika 6arayi gidan alhaji salmanu tsakiyar dare,

Gurin karbar takardun bulama da mahaifinsa sukai gardamar bayarwa Wanda yaja nan take aka harbe alhaji salmanu da matarsa bulama naganin haka ya buge babbansu da flower verse ya fizgo matarsa asma’u suka gudo tareda takardun dukiyar
Yakurah da babaye dama suna schools hostels suke zama.

Gudu suke sosai atsakiyar ko gani sosai basayi sbd duhun dare amma haka suke gudu hannunsa damqe Dana asma’u suna keta duk hanyarda suka samu sbd sunajinsu abayansu biye dasu.

Basu ankaraba suka gansu har sun fara barin anguwanni suna qoqarin ketawa daji amma haka suka cigaba da gudu agalabaice cikin tsananin wahala da gajiya
Can wajen gari sukaga wani kangon gida daya qone suka shige tareda boyewa.

Wani irin kuka asma’u tasaki jikinta na karkarwa
Bulama yayi saurin saka hannuwansa ya toshe mata baki sbd takun su ishaq da barayin daya jiyo yana kusantonsu.

Dudduba koina sukayi suna haskawa Allah yasa basu gansuba
Iska ishaq ya daka cikin zafi da tsananin 6acin rai yana huci yakira abbansa yafada masa 5

Cikin takaici da baqin ciki abban yace,

Kutafi tashoshin motar duk garinnan kudubasu banason kowannensu da rai takardun kawai nakeso Ku karbo saiku harbesu
Hakama atura su tiger duk wata station su zauna daga nesa da anhangosu sunzo station kafin sushiga aharbesu.

Aje wayar yay yakallesu yace kumuje tashoshin mota amma wasu su tsaya anan sbd nasan idanma sunanan kusa idan gari ya waye zasu fito idan sun fito Ku harbesu kawai.

Barin gurin sukayi sukuma su bulama najin haka koda gari ya waye sake lafewa sukayi sukaqi fitowa saida duhu yasakeyi suka fito cikin sanda suka fice tareda qarasa kutsawa cikin dajin suka fara gudu +

Jini sosai qafafuwansu ke fitarwa sbd ko takalmi babu maishi acikinsu ga yunwa ga wahala da kishirwa amma hakanan suka cigaba da tafiya sbd komawarsu nada matuqar ha’dari yanxu.

Basu hadu da qauye ko dayaba har asuba tayi musu atsakiyar daji gashi tuni asma’u tafara riqe ciki tana murqususu cikin tsananin azaba ta durqushe agurin awahalce tace,

Bulama marata zan mutu.

Da sauri ya aje takardun ya durqusa ya tallafota jikinsa shima daqyar yake hade yawu sbd bakinsa daya bushe qyam ko yawu daqyar yake samun na hadiyewa a maqoshinsa ga wata irin rana mai tsananin azaba,

Ko tsuntsaye babu adajin sbd a bushe yake babu damshin ruwa ko kadan itatuwan dajinma duk abushe suke babu mai inuwa.

Jinin dayaga yanabiyo qafafuwantane yasa yayi saurin kallonta murya na rawar wahala yace,

Asma’u cikine dake dama bansaniba?
Innalillahi-wainnalaihirrajiun.

Ganin tana Neman fita hayyacinta yasa ya goyata tareda daukar takardun yacigava da tafiya daqyar shima sbd shima yafara daina gani daidai.

Ahaka rana takuma faduwa wani Daren yayi musu a tsakiyar jeji wannan karon kam ya tabbatarda wata duniyar suka fado sbd kalar yanayin dajin ya sauya sosai
Tun yana gani har duhu yasake yi dare Yakuma tsalawa sosai cak ya tsaya tareda yanke jiki ya fadi asma’u dake bayansa ta fado da qarfi kafin ya bude idanu daqyar Dan taimakonta sai ganin yayi kamar tana gangarawa
Bude idanuwansa yayi awahalce da sauri saiyaga Ashe bakin cliff suke mai tsananin zurfi da ruwa masu tsananin yawa yana miqewa daqyar kafin yakamota idanuwansa suka rufe yasake yanke jiki yafadi tareda fadawa shima.

********
Ahankali ya bude idanuwansa dake gani dishi dishi harsuka bude daqyar suna kallon sama,
Lumshe idanuwan yasakeyi yabudesu yaga tabbas rufin sama bukkar karace yake ciki,

Qoqarin motsawa yakeyi Dan ya yunqura yatashi aka shigo bukkar yayi saurin dagowa.

Tashin namijine kamarsa dago fari tas sanyeda kayan saqi na fulani.

Qarasowa yayi da sauri tareda dafasa yana cewa,

Yi ahankali kana kariya aqafa.

Kallon qafar bulama yayi sai alokacin yaji azaba ya lura da ‘dauri amma bai damuba cikin dasashiyar murya da fargabar amsarda za’abasa yace,

Ina matata?
Inane nan?
Ina takardun dake daure ajikina?
Kwana na nawa anan?

Cikeda mamaki da rashin isashiyar hausar fahimtar me bulaman ke fada yake kallonsa kafin ya gyara masa zaman qafar mai ‘dori yace,

Kayi hkr sbd bansan mezan fada makaba amsa daya zan iya baka shine kwananka takwas anan sauran tambayar anjima idan mahaifina yadawo ya amsa maka.

Yana fadar haka ya fice
Saigashi yadawo da qwaryar magani da akushin wani irin abinci kamar tuwa kamar kunu ya zauna tareda miqawa bulama yace,

Gashi kaci saikasha magani.

Kallon abincin bulama yayi yaga shi kama ma abincin yayi masa da aman tuwon semo amma sbd yunwa da matsuwar jin inda matarsa take ya karba ya dauke numfashi ya shanye. 2

Ruwan magani ya miqa masa suma ya karba ba musu ya shanye.Jingina jikinsa yayi jikin darnin ginin qasar dakin da kusan rabin ginin karane ya dafe goshinsa ahankali tareda rufe ido yana zuciyarsa na tsananta fargabar kar asanardashi ba’aga matarsaba kokuma ta rasu. +

Qurawa qofar shigowa ido yayi yana sake tabbatarwa da kansa tabbas wata qasar suka fado sbd yanayin shigar Wanda yafita dazu da yanayin abincinsu da maganarsa tareda yanayin muhallin.

Ya jima yana tanane tunanen fargaba da rashin sukuni kafin wani dattijo sosai daya manyanta ya shigo dakin da gwararriyar sallamarsa.

Saurin ‘dogowa daga jinginar yayi yatashi zaune daidai duk da rashin qarfin jikin dake tattareda dashi tareda zubawa mutumin ido Dan amatse yake dason jin ina matarsa take.

Kallon bulama dattijon yayi kafin yajuyo yakalli ‘dansa dake bayansa cikin wani yare yayi masa magana kafin cikin hausarsu da bata fita yace,

Dama yatashi baka fadaminba kutti ?

Bai dadeba da tashi baabah magani natsaya bashi kafin naje kiranka saigashi kadawo.

Kallon bulama baaban yayi yace,

Sannu da kaji,yanzudai babu inda yakema ciwo ko?

Cikin qarfin hali yace,

Banajin komai yanxu qafardaice idan na motsata da ‘Dan zafi,
Nagode sosai baabah amma Dan Allah ina asma’u mata…..

Kwnatarda hankalinka matarka nanan tareda kai saidai itama tayi jinya ta rasa cikin jikinta amma ta warke sosai.

Ajiyar zuciya yasake a6oye sbd ba qaramin dauke numfashi yayiba Dan gudun jin muguwar amsa.

Kutti ne yasake shigowa dakin wannan karon Asma’u na bayansa bakinta daukeda siririyar sallama.

Qura mata ido yayi sanye takeda kayan saqi irin nasu da wani juyayyen ‘dankwali dako kanta bai rufe dukaba tayi wani irin mummunan baqi ta rame gabaki ‘daya kamanninta sun fara sauyawa
Wani irin tausayinta Dana kansa ya rufeshi amma dai tunda sun tsira kuma suna cikin qoshin lafiya daidai gwargwado to alhmdllh.

Cikin sanyin jiki ta durqusa qasa tace,

Ina wuni baabah.

Lafiya lafiya mai sunan innejo mijinki ya farka daga yanxu kar asake kuka Dan ba’a kuka agidan baabah namiki uzirine kema.

Duqar dakai tayi cikin sanyi ta ‘daga kai sbd akwanakin datayi agidan taga dokoki da sabbin alamuran rayuwa a gidan da mutanen garin wanda cikin qanqanin lokaci ta fahimci tsantsar jahilci da rashin wadataccen ilimin addini suke ciki Dan acikin duhu suke sosai.

Fita baabah yayi kutti yabi bayansa ta ‘dago kai ahankali takallesa sai kawai tasaki qaramin kuka ahankali tareda toshe bakinta.

Hannu yamiqa yajawota kusadashi ya rungumeta shima daurewa kawai yayi amma yasan gararin rayuwa yasamesu.

Rarrashinta yayi daqyar yana cewa,

Asma’u kiyi hkr insha Allah komai zai daidaita Dana sake warwarewa zamu koma gida mu fuskanci su……

Kallonsa tayi amatuqar razane tana girgiza kai tace,

Yaya Dan Allah mubar maganar komawa yanxu kwata kwata nan inda muke wani yankine dabashida suna acikin wani lungun daji mai nisa daya ruwa masu yawa ya raba tsakaninsu da Nigeria dakuma wasu qasashen,

Sunada kwanciyar hankali duk da suna cikin tsananin duhun ilimi da rayuwa,
Jin dadi ba komai bane idan ga kwanciyar hankali da Wanda kakeso,Bamuda uwaye ko ‘daya duk ankashesu su yakurah komawarmu yanxu zamu saka rayuwarsu acikin hadarine suma,
Mu gwada bawa rayuwa wani chance anan sbd kwanciyar hankali da nutsuwa,
Mubari gaba idan komai ya Dade da shidewa saimuje da zuriar da Allah zaibamu anan cikin kwanciyar hankali.

Shiru yayi yana kallonta sbd tagama kashe masa jiki tunowa da mutuwar iyayensu kuma tabbas komawarsu saka rayuwarsu yakurah ne ahadari.

Ganin yana tambabar yarda da zancenta yasa hawayenta tsananta cikin kuka tace,

Yaya kadaina tuno dukiya da rayuwarmu tabaya sbd rayuwa dakai anan yafimin komawa cikin daular dazata saka mu rasa juna.

Tsananin tsoro da figicin datake cikine yasa yayi saurin rungumeta yace,

Asma’u zamanki cikin kwanciyar hankali yafimin wata dukiya da daular rayuwa.

Satinsa biyu da farfadowa yafara miqewa kutti ne keta faman dawainiyar kula dashi
Ahankali yake koyan tafiya da sanda har waje suke fita suna zago qauyen Wanda tsaf yagama gano tabbas cikin duhun rayuwa suke sbd dajine zallah saidai akwai niima kasancewar zagaye sukeda ruwa.

Asma’u tuni tasaki jiki da matan gidan zuriar baabah Dan tuni aka ware musu fili acikin gidan da nufin bulama na warkewa yaje ya sassaqo icce ya Gina musu dakinsu acikin gidan.

Cikin ikon Allah ya warke sosai bai tsaya wata wataba yafara binsu kutti daji baji ba gani ya zage yazama nimiji sbd dolene yasaba da baqar wahala sbd itace rayuwar garin gashi garin koina hakine mai shegen tsawo Wanda wani gurinma idan kana tahowa baka ganin mai tahowa.

Cikin sati uku ya kammala musu dakinsu ita kuma asma’u matansu suka koya mata kara taringa binsu suna yowa tare harta hada musu gadansu na kara da tabarmar saqi.

Ahankali suka saje suka zama ‘yangari suma baabah yabasu sunan zuriarsa kasancewarsa shine shugaba agarin nan kowa agari suka sakasu cikin zuriar gidan baabah.

Duk wata wahala ta rayuwa sun iya sunsaba yanxu sbd sun tasarwa shekara biyu agarin
Kwata kwata kamanninsu sun tashi daga nada sunkoma wasu kamannin daban duk wani kyau da tsari suncireshi sunkoma munana kamar sauran ‘yan garin
Iliminsu na addini dasukazo dashi ya haskaka qauyen sbd sosai suka qararda ‘yan qauyen yanxu ba laifi ilimin addini yadan yadu Dan yanxu wasunsu na wankan janaba idan sun sadu da iyalansu.

Suna cikin kwanciyar hankali sosai sbd ana qaunarsu har mantawa akeda su ‘din ba asalin nan bane tuni aka zama daya,

Asma’u ma tuni tashiga jerin surukan gidan baabah babu bambamci
Matar kutti MAMANI ce kawai ma suke samun matsala wasu lokutan sbd kishin matan sauri.

Shekaru sunja sosai manyanci yafara kamasu amma har lokacin babu haihuwa sai 6ari takeyi data samu ciki kusan 6arinta biyar gashi girma yazo musu.

Lokacinda baabah yabuqaci bulama ya qara aure bai musaba sbd bin umarnin baabah din
Haka aka hadasa da wata ‘yar maqocinsu sbd shi baabah ‘yayansa mata takwas duk sunyi aure.

Tuni bulama ya duqufa aikin sassaqo itace ba dare ba rana sbd yiwa kantali ‘dakinda zaisata idan anyi auren danma wata uku aka dibarwa bikin sbd yasamu yin dakin cikin nutsuwa.

Cikin ikon Allah asma’u Ashe tanada shigar ciki har wata biyu amma tayi shiru sbd kar ayi tunanin fasa auren Dan ko yanxu tana tunanin bazai tsayaba.

Sauran sati biyu bikin cikin na wata biyar tuni yafito kowa yafahimci cikine da ita nan murna ta kaure sbd cikinta baita6a wuce wata biyu zuwa ukuba.

Duk da haka tace kar bulama yafasa auren ayi kawai ta yanda zai samu ‘yaya da yawa tunda yafara manyanta ba haihuwa,

Hakan datayi yaqara kawo fahimta da shaquwa tareda qaunarta ga matanen qauyen tuni aka fara shagulgulan biki irin nasu na al’adarsu.

Ana saura kwana biyu ‘daurin aure da tsakar dare asma’u ta fito fitsari ta nufi bayinsu na kara dake baya na kowa da kowa na gidansu
Tayi tagama harta juya saitaga kamar tana hango hutattaki na tahowa cikin qauyen ta bude idanu da kyau saitaga tabbas kamar mutane ne da yawa ke shigowa qauyen.

Sakin butar qasar hannunta tayi ta nufi bukkarsu da sauri tashige jikinta na rawa ta tayarda bulama,Cikin sauri da magagi yatashi Dan yadauka cikinne yasamu matsala yana kallon cikinta da sauri yace,

Innaje lafiyanki kuwa?sbd shine sunan datun zuwansu ake kiranta dashi sbd sunan mahaifiyar baabah ce tuni aka manta sunan asma’u.

Murya na matuqar rawa tana kallon qofa qasa qasa tace,

Mutane ne da hutattaki suka shigo qauyen nan na hangosu kuma……

Ihu da hayaniyarda qauyen ya ‘dauka ne ya katse maganarta suka kalli qofa afirgice tayi saurin cakumosa tana cewa,

Kajiko wlh mutane suke kashewa…

Zabura yayi ya miqe tareda damqo hannunta suka fito tsakar gidanda kowa yafito cikin tashin hankali da firgici.

Baabah cikin tsananin firgici da tashin hankali yace,

Dukkaninku kubi ta bayan gari ku gudu karku tsaya saikun kai iyakar ruwa Ku shiga Ku lafe qasan ruwa masu kamen mutane ne su sayar wata qasar amatsayin bayi.

Gaban bulama da innaje ya buga da mugun qarfi ya qara damqe hannunta tareda kallon fuskarta yace,

Duk tsanani asma’u kadaki rabu da hannuna.

‘Daga masa kai tayi hawaye na gangarowa idonta.

Dukkanin zuriar gidan sukabi ta qofar baya suka fara gudu suna waiwaye cikin tsoro da tashin hankali suna tsallake gawarwakin wainda aka kashe kwance cikin jini sai gudana yake
Ihun yara da mata tareda na maza saitashi yake ga huta da aka cinnawa wasu bukkokin.

Sun kusan isa bakin ruwa innaje tayi tuntu6e da wata gawa ta fadi tareda sakin wani razanannen ihu tana rawar jiki
Mamani dake bayansu da cikinta itama tayi saurin ra6esu da gudu zata wuce qafar innaje dake qoqarin tashi ta kifarda ita

Bulama cikin tsananin hanzari ya riqosu duka su biyun ya tayar suka wuce da gudu amma sai wani tashin hankalin sukayi arba dashi domin kuwa su kutti da sauran yan gidan sun 6ace musu

Kallon mamani yayi cikin tsananin tashin hankali yace,

Inane hanyarda baabah yace wadda mu bamu saniba?

Tsabar musiba da tashin hankali ya rudata takasa ganewa sai rarraba idanu take tana tsima cikin kuka.

Fizgarsu yayi suka nufi wata hanya da gudu Dan tsira
Qaddara ta Riga fata sai gashi tsaye turus agaban shugaban qungiyar.

Saurin kallon qasa yayi gaban shirgegen mutumin idanuwansa suka sauka kan gawar baabah kwance cikin jini ga rigarsa harta faraci da wuta.

Bai ankaraba yaji saukar dukan gora atsakiyar kansa ya dafe kai idanuwansa suka rufe ya yanke jiki yafadi agurin.

Suna ganin yanada sauran rai suka jasa aka jefa cikin qaton jirginsu na ruwa hakama innaje da mamani.

Sun samu nasarar kamo mutane sama da sittin maza da mata banda yara suka gargada jirginsu na ruwa suka lula.Saida gari yayi haske sosai yayi tsit su kutti sukaji tsit suka fito daga ma6oyarsu cikeda tsoro da tashin hankalin rashin ganin mamani dasu bulama.
Dakatarda sauran yayi ya ringa bin cikin hakukuwa batareda yana dogon motsiba yaje ya leqo qauyen.
Tsit sai koke koken dake tashi gawarwaki kuwa gasunan kwance
Jini kuwa tuni yake gudana a qauyen dabbobinsuma ba’a bariba shiyasa gawarwakin bana mutumba bana dabba ba. +

Saki jikinsa yayi sosai zuciyarsa tayi nauyi yasan tunda su bulama basa taredasu to kuwa sun mutu ko antafi dasu tafiyarda bar abada ba dawowa,
Tafiyarda gwara mutuwa da ita sbd a qasqantaccen bawa zaka qare wasuma kafin akai wahala da azaba tareda yunwa takashesu.

Komawa yayi yana daga qafa da qyar jiri na dibarsa yakirawo sauran suka shigo qauyen babu Mai nutsuwa nansuka fara tsallake gawarwaki suna birkito wainda ke kife suna duba sauran iyalan gidan dabaa ganiba.

Tuni suma wasu daga cikinsu suka fara ihun kuka sbd ganin mazansu wasu kuwa sauran matansu Dan duka iyalan gidan baabah din mazansu da matansu tareda ‘yayansu su talatin da takwas ne amma su ashirin da ‘daya suka tsira ankashe sha hudu antafi da uku.

Lokacinda suka arba da gawar baabah nan suka qara saddaqarwa nandai akayi kukan daza’ayi aka dangana 
Mazan dasuka saura haka aka hada gawarwakin sukaje nesa da qauyen suka rufesu suka dawo kowa yacigaba da rayuwarsa amma kullum cikin fargaba duk da sunsan mutanen bazasu dawo yanxuba sai zuwa nanda shekaru masu Dan tsawo sun kwatanci qauyen yasake cika sosai an hayayyafa yara sungirma sunxama samari da yanmata saisu sake dawowa su kwashe.

Tunda dai suna tsoro haka suka sake sakewa suka cigaba da rayuwa aka nada kutti amatsayin sabon shigaba Wanda wannan karon shi akan hada mugayen makamai na itace da dafin macizai da kunamu yamaida hankali sbd yadauki alqawarin angama satarsu ana siyardasu amatsayin bayi yaqi zasu shirya daga yanxu har ranarda mutanen zasu dawo.

*
Abincin dake cikin jirgin nasu ne iya sukadai suci su qoshi su kama wainda suka kamo suyita duka ba ruwansu da namiji ba ruwansu da mace ga yunwa sunbarsu da ita ga qishirwa tuni wasu daga cikinsu suka fara macewa sbd muguwar tafiyace mai nisa dazata kaisu nahiyar da
MENEELIK PALACE take
Duk Wanda ya mutu ruwa kawai suke jefasa ahaka mutanen suka rage da damansu.

Kwanansu goma sha bakwai ajirgin ruwar kafin suka isa da sassafe.
Cikin mutane sittin da ‘yan kai dasuka kamo mutane arba’in kawai suka iso dasu daga qauyensu bulama sauran duk sun mutu ahanya.
Bayan ‘yan qauyensu bulama dama sunsato wasu daga gurare da dama.

Kamar kayan wanki haka aka gargadosu dukkaninsu hannuwansu a ‘daure kusan da igiya ‘daya sbd ajere suke.

Babu Wanda zaka kalla kaga kamar baikusa mutuwaba sbd babu Wanda yake iya tsayuwa daidai sbd wahala da yunwa ga dau’da data canza musu kamanni mamani tuni kuka ya qare zuciya ta qafe banda tsanarsu asma’u ba abinda takeji sbd ganin sune sanadin zuwanta nan ga cikin jikinta haryafi na asma’u fitowa.

Bulama duk wuya da azaba asma’u yakeji itada mamani sbd ganin dukkaninsu juna biyune dasu gasu mata.
Kukansa da fargabarsa karsu mutu kafin a iso 
Basu mutuba amma dai suna kusa sbd babu mai iya jan qwaqwaran numfashi acikinsu.

A inda suke baza hajar siyarda bayinsu suka xubesu nansuka rarrabu cikin mutanen dake cikeda kasuwar Dan kar agansu da yawa dakuma kalar marasa imani agane satosu sukayi ba bayi bane babbansu  tareda manyan yaransa uku suka isa gurin wani mai siyarda ‘yayan itatuwa suka zauna sunacin abinci cikin farin ciki da nutsuwa.

Asma’u ce ta yanke jiki ta fadi da ‘dayansu ya lura yamiqe da sauri tareda yiwa ogan nuni da sauri shima ya miqe suka isa gurinta

Bulama tuni yafashe da wani irin kuka sbd yasan mutuwa tayi.Ta6ata sukayi arikice ‘dayan cikin wani yare mara dadin ji yace,

Tanada rai yunwa da wahalace muyi saurin bata abinci karta mutu kasan dokace anan duk mai siyarwa da masarauta bayi yazo dasu suka mutu aka gano wahalace kashesa shima akeyi musamman mu da satosu mukayi idan sultan dinsu yaji yankamu za’ayi abawa zakunansa namanmu.

Yawun tsoro ogan ya hadiye sbd yasan atarihin sarkin fiyedama hakan zai iyayi musu ba abin suqarasa kashetaba basuda gurin 6oye gawarta ko yarwa batareda angansuba sbd tsantsar tsaro da qa’idojin da sultan din nahiyar yake bayarwa.

Da ido yayiwa yaran alama suka kwanceta tareda fakar idanun mutane suka koma can baya da ita suka siyo mata abinci da ruwa kafin suka kelaya mata ruwa ta bude ido daqyar tanajan numfashin wahala.

Miqa mata abincin sukayi hannu na rawa ta kar6a daqyar take saita hannunta yashiga bakinta
Nan take ta cinye abincin tanashan ruwa sai amai.

Amai tayi sosai wainda yasata matuqar galabaita nantake zazzabi mai qarfi yafarasa jikinta karkarwa.

Damqo gashinta ogan yayi 6acin rai da takaicin sbd ita rayuwarsu na cikin ha’dari ya bude jajayen idanuwansa sosai yace,

Idan baki saki jiki kin nuna lafiyarki kalauba zan yanka mijinki agabanki na qona namansa nazuba tokarsa a takarda Nayi sigari dashi.

Marinta yayi da qarfi saidata kifa cikin qasa qasa da murya yace,

Kingane?

Bakinta dake jini ta goge hannu na rawa ta ‘daga kai idanuwanta na qara rinewa da Jan axaba.

Ingiza qeyarta yayi ta fadi ta lalaba ta miqe da qyar suka koma gurin sauran bayin.

Bulama na hangota gabansa yayi mummunan faduwa ya sunkuyar dakai tareda sakin sabbin hawayen baqin ciki sbd hango jini abakinta duk da tana gogewa 
Tafiyarma sai ha’da hanya takeyi a wahalce amma haka take daurewa sbd bin umarninsu karsu kashe bulama.

Sai da rana ta fadi suna aje cikin rana baci hargwara ruwa yau anbasu ganin mutane akasuwar gashi suna tsoron akwai ‘yan rahoton sultan
yamma tayi sosai suntabbatarda lokacin sultan ke shaqatawa tareda ‘dansa namiji qwaya ‘daya tal a gurin shan iskansa dake cikin masarautarsa kuma alokacin ake bada damar kai bayi sbd kullum masarautar bata gajiya da siyan bayi sbd girma da ikonta.

Isarsu masarautar yayi daidai da fitowar yarima MAHEER IBN ABDULSHAMS tareda abokinsa KHALEEFA ABDALLAH ‘Dan wazirin sultan ‘yan kimanin shekaru goma sha biyu biyu sun fito daga sassan hutawar sultan fadawan hudu na bayansu zasu gurin baturen malaminsu dayazo  koyardasu karatu.

Kallo ‘daya yarima yayiwa sashen daduke ana gargadasu zuwa sashen koyarda bayi aiki ya ‘dauke kai 
Khaleefa kuwa tsayawa yayi yana kallonsu yace,

Idan nagirma zansiyawa ummyna bayinda harsu mutu suna kularmin da ita.

Tsayawa yarima yayi cak tareda juyowa jin abinda khaleefa yace yasa yatuno da alqawarin dayayiwa ammynsa yauda safe cewar zai mata kyautarda mutuwace kawai zata rabata da ita sai kawai yace atsayar masa sa bayin.

Cikin hanxari aka tsayar dasu batareda ya kalli gefensuba yace abashi namijin qarshe da macen qarshe ya siya amafi tsadar farashi.

Jiki na rawa aka janyo bulama da asma’u dake baya aka kawosu gabansa amma daga nesa sbd warin dau’da.

Still basu yake kalloba sbd iko da mulki na jinin mahaifinsa dake yawo jikinsa yace,

Akaisu ke6antaccen guri a tsaftacesu abasu abinci da suturu kyautace zanyiwa mahaifina da ammynah akaro na farko.

Yana fada ta wuce khaleefa yabisa yana tunanin siyawa nasa iyayen amma zaibari sai ansake kawo wasu bayin.

Sukuwa dasuka kawo bayin maqudan kudaden qasar akabasu cikeda jaka suka karbe abinsu suka juya suna isa kasuwa suka siya guzurin abinci mai yawanda zai ishesu suyi wata qasar safaro wasu sudawo su sake siyarwa.

Lokacinda aka ke6esu bulama aka tsaftacesu tsaf aka basu watadaccen abinci mai kyau sukaci nantake suka ‘Dan murmure sukai fasali aka fito dasu aka nufi Sashen da sultan da iyalensa kowa keda part.

Kallonta bulama yayi idanuwansa taf da halayen tausayin gararinda rayuwarsu da abinda zasu haifa sbd tasake shiga,
Tasu qaddarar ahaka take daga ‘yaya masu gata da dukiya sun sunkoma wasu mutane masu wani yaren dabam agarinsu baabah yanxu kuwa zasu zamo wasu bayi masu bauta kuma iyayenda zasu haihu su haifarwa iyayen gidansu wani  bawan ko wata baiwar. +

Itama kallonsa take da ido jajir sbd sanin daganan rayuwarsu amatsayin ma’aurata ta tsaya takuma wargaje sbd ikon ganin junaba basudashi yanxu bare kebewa kosunga juna iyakarsu satar kallo ko ikon magana basudashi.

Ahankali aka jasa aka shige dashi babban palon sultan cikin tsananin biyayya ‘Dan Aiken yarima ya zube yace,

Allah yaqarawa sultan yawan rai da lafiya tareda qarfin mulki,
Ga babbar kyauta ta musamman daga yarima.

Kallon bawan yayi tareda sakin wani kyakkyawan qasaitaccen murmushi kafin yakalli ‘dan aiken yakalli saikin gida yace,

Sarkin gida gobe tundaga 6ullowar rana aje abudewa wanda yakawo saqonnan na yarima ma’ajiyar abincin masarautar meenelik yaringa dibar duk abinda yakeso yana kaiwa gidansa harsai rana ta fadi sanann yanxu yacire rigarsa ya shimfida acika masa itada sutura mai tsananin tsada kalolo ba iyaka wanda saiya ‘dauka daqyar sbd wannan ce kyautar yarima ta farko agareni Dan haka wannan itace kyauta mafi soyuwa araina kyautarda mutuwace zata rabani da ita 
Aje asanarda yarima kyautarsa ta faranta ran mahaifinsa ayimasa albishirda zuwa qasarda yakeson bin baturen malaminsa karatu.

Jin haka Dan aike ya zube jikinsa ba inda baya rawa sbd farin ciki yadinga rero kirari da godia kafin yafice daukeda kayanda sarki yace yana nishi daqyar sbd yawansu da nauyinsu.

Kallon bulama sarki yayi kafin yakalli su waziri cikin farin cikinsa dabai 6oyuba yace,

Wannan kyautace daga yarima bazaiyi bautaba bawan dazai riqa kula da hutawatane daga yau anadasa.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]