[Advertisements⬇️]

GAMAYYA CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GAMAYYAH
CHAPTER 1Bayine da kuyangi bila adadin akowace kusurwa ta cikin babbar masarautar kowanne da aikin daya duqufa yanayi wasu nsu kuma a qaqqame suna gadin hanyoyin wucewa da kowace qofa ta cikin masarautar
Dukkaninsu kalar kayansu dayane mazansu da matansu kalar dark blue Wanda zaa iya kira da uniform.

Ahankali kowannansu yafara aje aikinda yakeyi yana ra6ewa gefe tareda sunkuyarda kai qasa sbd takun tahowar sarauniya Wanda sautin anklets din zinarin dake qafarta shine yake sanarda isowarta ko tahowartar tundaga nesa wanda tunda ta tashi arayuwarta ta taso agidan sarauta tasaba duk inda take sautin sarqar ke sanarda tahowarta harzuwa yanxu data manyanta sbd mulki a jininta yake.

Tana qarasowa hanyar dazata shigarda ita 6angaren mai martaba sarki ta tsaya cak batareda tace qalaba tareda juyawa ahankali tadan kalli gefenta da dama.
jakadiyarta dake gefenta tayi saurin matsowa tareda juyawa takalli kuyangin dake take musu baya kusan su shida kallo daya tayi musu suka ja baya ahankali suka tsaya tareda sunkuyarda kai.

Boyayyar ajiyar zuciya tasauke ahankali tareda shiga qofarda aka jima da wangale mata jakadiya tabita abaya aka rufo qofar. 1

Parlour ne mai wani irin girma da tsari dayaji adon royal chairs red and golden kamar zinari sai qyalli suke sai komai daya qawata palon yazamto shima red and golden dinne splits aircon kusan guda biyar sai aiki suke sanyi yakama palon takoina sbd wata irin dukiyace ta musamman aka narkar a palon.
Babu kowa a palon sbd palon farkone dazai sadaka da palon sarauta harzuwa turakar sarki
Ta sake tsayawa cak tareda sake sakin wata sahirtacciyar ajiyar zuciya akaro na uku zuciyarta na harbawa batareda tajuyo bangaren jakadiyaba murya a karye tace,

Wannan saqon na sultan(sarki) yana matuqar girgixa zuciyata sbd saqone daya zamto na baqin ciki agaresa,
Duk wani bawa ko bafade yakai wannan saqon abakacin rayuwarsane shiyasa nazabi nazo na isardashi dakaina,

Ajiyar zuciya mai nauyi jakadiya ta sauke tareda kallon sarauniya zaarah din cikin tausayawa acikin aranta afili tace,

Allah yataimaki sultana yakuma sanyaya ranki badan kinyi rashiba yabaki ikon isarda saqon sarkin sarakuna….

Katseta sultana zaraah tayi da cewa,

Haihuwa tazamar mana abar fargaba maimakon farin ciki.

Uwargijiyata Allah ya sassauci fargabarki amma dakin sake kin nunawa yarima farin cikinki da qaruwar dayasamu tunda shi yanaso ahakan kuma yana godiyar Allah da arzikin qaruwa daya basa
Allah ya raya abinda aka Haifa din yasa ayi alfahari da hakan gaba.

Ajiyar zuciya sultana tasake tareda furta amin qasan maqoshinta kafin ta tattaro jarumta da qarfin gwiwa ta gyara zaman gyalen kanta daya rufo dogon gashinta dake kwance har bayanta Wanda shima gashin harzuwa goshinta adone na wata kyakkyawar sarkar zinari ta kai sai aka rufo gyalen doguwar rigarta dark purple dataji adon duwatsu masu shegen kyau da kyalli gyalen naja har qasa kadan.

Ratsa dogon palon tayi jakadiya na bayanta ta nufi qofarda zata kaita ainihin palonsa na musamman tana zuwa wanda ke tsaron qofar ya wangale mata qofar ahankali tashiga jakadiya takoma gefe ta toge itama tana jiran fitowar uwar dakin tata.

Wani palon ne na alfarma babu kowa sai qarar ac dake tashi ahankali

Zaune yake cikin shiga ta alfarma
Dattijone sosai da Hutu da mulki na jinin sarauta daya ratsasa,
Kallo daya yayi mata da idanuwansa masu tsananin kwarjini da firgitarwa taso rudewa tayi saurin daidaita kanta ta tattaro nutsuwa da qarfin hali.

Qarasowa tayi cikin sanyin jiki da fargaba ta kallesa ta rufe idanuwanta dasuka fara canxawa murya na rawa tace,

Allah yataimakeka saqo daga GEORGIA…..

Idanuwan daya sake watso matane yasa taso daburcewa tayi saurin gyara murya cikin nutsuwa ta dauke idanuwanta daga kallonsa murya na rawa tace,

Yarima yabugo yasanarda saqon matarsa ta sauka ansamu ‘YA MACE.

Sake dauke kai tayi sbd gudun ganin yanayinsa sbd kodagajin yanda ya dauke wuta tasan ran maza ya baci babu jin dadi ko alamar farin ciki dagajin saqonta.

Tsawon mintuna ashirin shiru
Kamar daga sama taji dakakkiyar muryarsa cikin ikon mulki yace, +

Kin isarda saqon yarima Dan haka kisanardashi saqonsa ya iso
Ke kuma tukuicinki na sanarda saqonsa bazaki sakashi a idoba sai bayan shekara daya,
Karya dawo harsai matarsa tasake samun wani cikin wannan karon anan zata haihu
Zata haifi yariman da ubansa yaqi amsa.
Yana gama fadar haka ya miqe zai shige turakarsa

Dagowa tayi takallesa idanuwanta na canxawa zuwa kalar tausayin kanta dabazataga ‘dantaba ko awannan shekarar
Tsawon lokaci kenan tunda yayi aure matarsa tahaifi ya mace suka koma Georgia sarki yace karsu dawo saita sake samun wani cikin tasamu tasake haihuwar mace yasake korasu yarinyar ta rasu still yahanasu dawowa harsaita haifi namiji yanxuma gashi macen ta haifa kuma yanxunma saiwata shekara kenan kusan shekara biyar kenan rabonta da danta tana tsananin kewarsa dason ganinsa.

Cikin sanyin murya tace,

Allah ya huci zuciyar sarkin sarakuna
Na karbi hukuncina matuqar hakan zai faranta ran sarkina
Saqon yarima kuma kamar yagama isa a kunnensa ne
Nabarka lafiya.

Juyawa tayi ta nufi qofar tana isa aka bude mata ta fice
Jakadiya tayi saurin Mara mata baya kanta asunkuye sbd ganin yanayin uwar dakin nata.

Suna isa babbar qofa suka fice kuyanginta sukai saurin Mara musu baya
Bayi sai zubewa suke suna sunkuyar dakai yaukam ko kallonsu bata iyayi bare amsa gaisuwarsu dankuwa ranta amatuqar dagule yake.

Tana isa sashenta cikin tsananin sauri aka bude mata qofa tashiga
Tana shiga kai tsaye hanyar bedroom dinta tayi bayan tasake wuce palonta na musamman inda babu mashigowa duk fadin masarautar daga ita sai danta yarima sai amintacciyar kuyangarta datake kamar matsayin ‘ya agareta saikuwa jakadiya ko matar yarima bata taba shigowa nan palonba iyakacinta na farko bedroom dinta kuwa ko yarima baitaba shigaba bare jakadiya kuyangarta mai gyara mata kawai keshiga.

Tana shiga bedroom din taganta a tsaye jikin wardrobe din lafiyyan dakin tana jera mata sabbin kayanta dasuka iso.

Daidaita nutsuwarta da fuskarta tayi tareda gyaran murya batareda takalletaba.

Juyowa tayi da sauri tana ganin sultana zaarah tasaki wani irin lafiyyan murmushin daya bayyanarda dimple dinta duka guda biyu cikin tsananin taushin murya da tsantsar ladabi tace,

Ammy barka da dawowa.

Daga mata kai ammyn tayi batareda sakin fuskaba kamar yanda suka sababa murya a dake tace,

Ina buqatar hutu.

Cikin nutsuwa tayi saurin aje kayan ta nufi qofa zata fice jiki asanyaye sbd ganin yaudai ammyn bata cikin kwanciyar hankali dankuwa tunda safe take lureda ita bata cikin kwanciyar hankali.

UMMU-RUMANA….cak ta tsaya jin ammyn takirata tareda juyawa cikin ladabi tace,

Allah yataimaki ammy.

Bana buqatar damuwa takomai da kowa ko dogon motsi banaso kowa yafice daga nan shashen zuwa anjima saiku dawo ina buqatar Hutu.

Ahuta lafiya ammy”””tace cikin sanyi tareda ficewa jiki ba dadi sbd damuwar ammy na matuqar ta6ata sbd akoyaushe idan takalleta cikin annushuwa ganin take tamkar mahaifiyartace cikin annashuwar kasancewar mahaifiyarta babbar amintacciyar baiwar ammyn kuma jakadiyarda kafin tarasu.

Tana fitowa bban palon ammyn duk ta sallami sauran kuyangi da bayin sashen itama ta fita masu tsaron qofar shiga sashen kawai aka bari tareda nufar hanyarda zata sadata da bangarensu na bayi inda kowa keda daki mutum uku daki daya.
Babban sashensu na bayi da bororin masarautar ta nufa tana isa kai tsaye dakinsu ta nufa tana ganin qofar abude tasan nuratu naciki tashiga bakinta daukeda siririyar sallama.

Zaune bakin katifa taga nuratun tana qoqarin zare wandon uniform dinta zata shiga wanka ta nufi bakin tata yar katifar ta zauna tana cewa,

Yau kingamo da wuri Nima nasamu dan qaramin hutu daga ammy yanxu kiyi sauri kiyi wankan sai kiyimin koda kalbane sbd inason zanyi wankan tsarki banasan nayi da kaina a tsefe zai dameni tunda ba iska zaishaba koyaushe muna cikin uniform. 5

Kallonta nuratu tayi jin yanayin data qarasa zancen dashi kamar koyaushe tun tasowarsu sun bude ido sun tsinci Kansu a bayi kuma yayan bayi Wanda har gwara ita tanada mahaifiya rumana din batada uwa batada uba.

Fasa shiga wankan tayi ta qarasa katifar rumana din ta zauna tareda zame mata dankwali tace zonayi miki daga baya nayi wankan sbd nima aikine dani matuqa zanje karbo sabbin furannin dazaa jera a kwalbar ruwan dake girke palon sarauniya adama na farko gakuma aikin chanxa

Gyara zama tayi cikin tausayawa rayuwarsu tace,

Mamani tasha saqe saqin maganinta kuwa kafin tafita aiki?

Girgiza kai nuratu tayi cikin tausayin mahaifiyarta dakuma na rumana din datake qaunar mamani da zuciya daya duk da kyararta datakeyi.

Kamar rumana tasan me take tunani cikin sanyin murya tace,

RUMANA INA MAI HORAR DAKE KI RIQE ALLAH AKO WANE HALI KO YANAYI KIKA TSINCI KANKI DA RAYUWARKI,
IDAN KIKA RIQESA KIKA ZAMA MAI HAKURI DA DANGANA DA DAUKAR QADDARAR DAYA DORA MIKI MAI KYAWU DA MARAR KYAWU TO KODA KIKE BAIWA RAYUWA BAZATAYI MIKI TSANANIBA HAKAMA IDAN KIKA ZAMO BAIWA MAI BIN UMARNIN UWAYEN GIDANKI TO HAKAMA RAYUWA BAZATAYI MIKI TSANANIBA…

Nuratu wainnan sune kalaman ummana da ako yaushe suke shawagi cikin zuciya da kunnuwana wainda sune nake kallo amatsayin wasiyyarta gareni,
Ni baiwa ce uwata da ubana bayine harsuka rasu,
Banida wani gata ko martabarda zan kalli kaina amatsayin wata mace ko ‘ya mai qima sbd nima zanqarasa rayuwatane amatsayin baiwa kamar iyayena,
Tun lokacinda nayi wayo

cikakkiyar mai yanci ta hanyar ‘yantawa
Allah yakarbi adduata amma adaidai lokacinda yantawar batada amfani sbd tana kwance ciwon ajali Wanda yasa na yanke rai daga samun ingantacciyar rayuwa…..

Katseta nuratu tayi da cewa,

Ba’a cire rai daga rahamar uban giji rumana,
Ki zamto mai gode masa da kowace irin niima,
Ke mai saa ce sbd koda kasancewarki baiwa kinfita dabam acikin bayi sbd ke abar qaunace ga sarauniyar datafi kowace mace matsayi acikin masarautarnan sultana zaarah kasancewarki ‘ya ga amintacciyar baiwarta
Ko ahaka kika duba zaki godewa Allah da wannan ni’imar.

Ajiyar zuciya tasauke ahankali tareda zare kanta ta juyo ta kalli nuratun tana tattare dogon gashinta tace,

Kibar kitson kiyi wanka kikoma bakin aikinki da wuri sbd gudun kwana gidan kason masarauta.

Tashi nuratun tayi tana jawo kayanda tafara maidawa tana cewa,

Bazan samu yin wankaba kuma sbd lokaci yashiga kuma wlh tsananin aikine asashen sarauniya adama sbd komai na sashen zaa canza har sitirunta kaf ko tsokalinda aka siyo jiya bazai shiga sashentaba sai sabo dal sbd kwanaki uku zuwa hudune suka rage ta kammala hukuncinta na sultan daya bata na ko qofar palonta na farko karta fito sai bayan shekara guda iyakacinta palonta na qurya zuwa bedroom dinta ko ‘yayanta anhana shiga gurinta bare kuyangi iyakacinsu palonta na farko jekadiyarta kawai keda izinin shiga sbd kamata da laifin sa likita yaje gidan ‘yarta gimbiya amatullah yayi mata allurar tsarin haihuwa suda ake fatar samun ‘da namiji a zuria sbd…..
Rufe mata baki rumana tayi tana kallon qofa tace,

Ya isa idan wani yajimu kinsan rayuwarmuce zamu qarasa a kurkuku.

Saurin kallon qofa nuratu tayi ido a firgice zufa na karyo mata sbd shaf idan tafara barin baki mantawa takeda abinda zaibiyo baya sbd masarautar takasance maitsananin hukunci babu sauqi ko bata lokaci sbd tsagwaron mulki da iko ke yawo a jinin masarautar kasancewar sarkin masarautar mai tsana tsananin zafine da zallar mulki babu sauki gurin daidaitawa kowa kansa, +

Kwarjininsa ikonsa kesa ko matansa da ‘yanyansa ke matuwar shakkar hukuncinsa shiyasa kowa a kiyaye yakeda umarninsa bare ‘yan fada da sauran hakiman sarki.

Kusan atare suka fito daga dakinsu suka jawo dakin suka kowa yanufi gurin aikinsa
Kai tsaye rumana sashen sultana zaarah takoma inda ta tararda dukkanin wasu kuyangin sashen a qofar sashen sun jeru zai zufa suke sbd tsayuwa gashi babu ikon zaunawa haka itama tabi layinsu suka cigaba da tsayin jiran lokacinda uwar dakinsu zata gama hutawa sukoma ciki domin hidimarta.

Saida rana tafadi lis kafin ta matsa sbd lokacinda ake diba nabawa sarauniya Hutu yayi idan bata fitoba ana shiga aga lafiyarta
Matsu tsaron bakin qofar sashen sukayi saurin bude mata tashiga tana goge zufanta ta tsaya a palon farko saidatayi mintuna kusan shida atsaye AC ya butsarda ita kafin ta nufi palon gaba tashiga da sallama Mara qarfi sbd gudun yin hayaniyar da ammyn bataso.

Shigarta yayi daidai da fitowar sultana din daga bedroom dinta cikin doguwar riga maroon dataji adon sequence stones masu masifar kyau sai qyalli suke wannan karon babu adon sarqar zinari a gashinta da wuyanta kamar koyaushe saidai wasu awarwaron zinari masu kauri da girma sosai hakama babu kwalliya afuskarta kamar koyaushe sbd sultana zaarah takasance yar sarautar qasar Morocco koyaushe cikin tsananin ado da kwalliya take musamman gwalagwalai naban mamaki hakama bazaka gantaba kace tanada babban jarumin ‘da sbd zamanta kyakkyawar mace mai kyawun jiki.

Durqusawa tayi cikin tsananin ladabi tace,

Barkada fitowa ammy da fatar kinhuta lafiya.

Zama ammyn tayi kan ‘daya daga cikin royal chairs din palon batareda takalli rumanarba ta ‘daga kai kafin tace,

Rumana ‘yau banason dogon motsi bare hayaniya Dan haka kisanarda sauran ayi komai cikin qanqanin lokaci kowa ya fice kema ki kammala kije kihuta bana buqatar kowa.

Angama ammy.

Miqewa tayi taje tasanarda sauran kuyangin tadawo ta nufi bedroom din ammyn tafara gyara ta canza zanin gado sbd kwana daya ‘daya yakeyi acire asaka sabo tana gama gyara koina ta sassaita AC daidai yanda ammy keso sanyinsa ya kasance takunna burners qamshi yafara tashi ta shiga toilet tayi gyaran dazatayi ta fito taje takarbo abincinta a manya manyan tururuwa ta jera a makeken royal dining din dake palon ta dawo gabanta ta durqusa a ladafce tace,

Allah yasa ahuta lfy yakuma tasheki lfy.

Ficewa tayi lokacin tuni aka fara kiran magriba daidai zata fito dake jakadiya dake qoqarin daidaita nutsuwarta tashigo.

Tsayawa jakadiya tayi a palon farko tafitarda numfashi mai zafi sbd sotake ta daidaita kanta sbd da rayuwartace amatuqar tsaka mai wuya duk tabari fargabarta tasa sultana tagano hukuncin da sultan ya yanke akan alamarin dake damun masarautar shekara da shekaru.

Tunda suka baro gurin sultan dazu tasake komawa sbd kai saqon banhakuri da tubar uwargijiyarta bisaga saqo Mara dadi data kaimasa na haihuwar mace da matar yarima tayi.

Abakin qofar fadar ta wuni tsaye cikin rana Dan nuna banhakurin uwargijiyarta Wanda saida rana ta fadi lis sarki ya aikoda izinin shigowarta.

Jiki na rawa ta zube gabansa cikin tsananin girmamawa tace,

Allah ya huci zuciyar sarkin sarakuna,
Sarkinda yafi kowane sarki adalci,
Da yardar Allah sai anmaka takwara harsai andarje a jininka,
Ba ‘daya za’a samuba ba biyuba dozin ne da yardar ubangiji saika gansu saika aurensu
Allah ya sake hutar zuciyarka. 7

Gyara murya yayi cikin wani irin iko da umarni dake nuni magana daya yakeyi yace,

Jakadiya aje aciro ‘yan mata biyar dasukafi kowa kyawu acikin kuyangun masarautarnan a killacesu afara kintsasu daga yanxu harzuwa nanda shekara daya lokacinda yarima zai dawo
Za’a kaisu sassansa amatsayin sa dakokinsa duk wadda ta haifi namiji ayimata albishirda tazama uwar sarkin wata rana.

Amatuqar kidime jakadiya zufa ya keto mata murya na rawa tace,

Angama sarki mai adalci,
Cika umarninka zaifara ne daga yanxu,
Allah dai yaqara hutar zuciyarka
Nabarka lafiya. Fitowa tayi saida ta tabbatarda tayi nisa da sassasansa ta tsaya gefe tareda sharshe zufar daketa faman karyo mata tayi shiru tsawon mintuna zuciyarta na tumamin hukuncinda sarki ya yanke dakuma sanin waye yarima akan tsantseni matarsama da yaya akasamu yayi auren bare sa ‘daka har biyar…

Sake sharce zufa tayi cikin tsananin fargaba gashi abakacin ranka matuqar sarki ya yanke umarni katsaya sanarda wani batareda ka cika umarninba Dan haka batada ikon fadawa kowa saidai kawai aiwatarwa.

Nufar sassan sultana tayi cikeda fargaba da tausayinta ta yanda hankalinta zai matuqar tashi duk randa taji zata fara shirin tarbon jikokinta na sa’dakoki.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]