[Advertisements⬇️]

AMININ MAHAIFINA CHAPTER 7 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

AMININ MAHAIFINA


CHAPTER 7Juyi kawai nake yi na kasa barcin, na rasa abinda yake min dadi a cikin raina. In normal sense nasan cewa da ace wani ne ya min ihu da daga muryan da Abbu ya min yau sai naji bacin rai saboda ni fa na tsani kawai mutum ya dinga nuna he has control over me alhalin baya da, abunda nasan cewa koh a gida nake Daddy ba zai min kwatankwacin fada da tuhumar da Abbu ya min ba, yes! Daddy zai min fada amma ta cikin lumana da nasiha ba irin na Abbu ba. Amma me yasa? Me yasa ko kadan ban ji cewa Abbu bai kyauta ba a cikin raina?? Na juya daya gefen ina kallon wani frame, hoton mu ne ni da Hafsy, ni na dauke mu ya min kyau sosai shi yasa na kai aka wanke min shi. I was extremely confused a lokacin, kwata-kwata na ma rasa a wani matsayi na ajiye Abbu balle in yanke hukunci. I never, even in my dreams wai inyi mafarkin ajiye shi a cikin jerin abokan Baba na, to amma idan ba Abokin Baba na bane shi ba to waye?? Da wadannan tunanukan barci ya dauke ni cike da wadansu irin mafarkai marasa kan gado. Ranar har so nayi in makara sallar Asubahi, sai wajen karfe shida da rabi nayi sallah, ina gamawa na koma na sake kwanciya. Yatsun kafata naji ana ja, cikin barci na janye kafafuna na maida su cikin blanket tare da kara kankame pillow. Tafiyar tsutsa naji ana min a wuyana, da sauri na bude idanuna tare da hantsilawa kasan gado har ina dan buge kaina, na dago da sauri, yanayin fuskana ya canza daga harara zuwa na mamaki. Da mamaki nake kallon su, Ni’ima ne da Sa’adiya. Zaune suke a gefen gadon suna kallona, nayi tsalle a kansu muna shewa, sai da muka gama na zauna a gefen su nace “me kuke yi ne anan yammata?” ni’ima tace ziyara muka kawo, ko it’s not allowed? Nace “ni na isa in ce? Amma da safe haka?” idanuna ya sauka akan agogo, karfe goma da rabi. Sa’adiya tayi murmushi tace “Abinci fa muka kawo wa babban Yaya.” na Kalle su “Abbu?” Ni’ima tace “to da wa?? Funkasu ne da mijin taushe mai dadi wallahi, tashi kixo ki ci kafin ya huce” na sauka daga kan gadon ina cewa “yanxu kuwa” toilet na shiga nayi brush, na fito na bude wardrobe na janyo bakar BF jacket ta cotton na dora akan vest din dake jikina, na nannade kitson da aka min na daure da ribbon na saka hular beanie muka fita falon, dama nasan yara suna makaranta don haka ban yi mamaki da naga falon babu kowa ba, sai da muka shiga second falo ne na ga Any Mubeenah zaune akan kujera, muka gaida ta ni da su Ni’ima da alamun suma sai lokacin suka gaisa, ta amsa kamar ko da yaushe, babu yabo babu fallasa. Lamarin Anty Mubeenah sam ya daina bani mamaki, shi yasa bana ganin laifin dangin mijinta akan duk abinda zasu ce a kanta, tunda koma meye ai ita ta jawowa kanta. Ace kannen mijin auren ki wai kina amsa musu gaisuwa kamar wasu baki ko irin dangin nan na nesa? Kai ko dangin nesa ne ai ya cancanci ace ka dan nuna sanayya. Na saci kallon su Ni’ima da alamun su abun bai dada su da kasa bama. Muka nufi kan dinning muka zauna, har su na zuba mana funkasun muka fara ci muna er hira. Abbu ya shigo sanye da wata farar riga da farin wando, ya gyara sumar kan shi sai wani irin sheki take yi, da sauri su Ni’ima suka taryo shi suna babban bros! Da fara’ar shi ya tare su ya jingina kowaccen su da jikinshi yana kallonsu, “wato ku dai idan ba aiko ku aka yi ba ba a ganin ku sai a gida ko?” Sa’adiya tace “bros ai kasan halin Baba, baya bari muna yawo fa” yace “ba wani nan dadin baki, ai naji ance har weekend kuke zuwa gidan su Ameenah, wannan ba yawo bane ba kenan?” Ni’ima tace “kar ka damu bros, yau yini ma zamu yi anan” yace ban yarda ba, kwana zaku yi. Ni kam idanuna yana kansu, fadar irin burge ni din da suka yi bata baki da lokaci ne, ban san sun zauna ba sai dana ji muryar Ni’ima a saitin kunnena, “me kike kallo?” nayi firgigit na kalleta, “umh?? Babu komi” ta jefa min wani irin kallo alamun bata yarda dinnan ba, nayi saurin maida hankalina ga Abbu na gaida shi, fuska a cune ya amsa duk sai naji ba dadi, ba haka yake amsa min gaisuwa ta ba. Ji nayi abincin ma ya fita daga raina, na fara tsakura ina turawa a bakina ba don ina jin dadin abincin ba. Su Ni’ima kam hirar su suke yi da Abbu suna dariya. Sa’adiya ta dan tabo ni, na kalleta a sanyaye, cike da kulawa tace “you okay?” na gyada mata kai kawai, Abbu ya kalleni na dan lokaci kafin ya maida kallon shi ga Ni’ima. Anty Mubeenah tazo tayi joining dinmu itama, lokaci zuwa lokaci Abbu yana saka ta cikin hirar da suke yi da kannen shi amma bata cika maida hankali ba duk da nima suna sako ni amma sai dai kawai in danyi murmushi ko inyi nodding a haka dai muka gama cin abincin. Hirar su suka cigaba da yi, na tashi na hada kan kayan da muka 6ata na kai kicin. Kasa komawa inda suke nayi kawai sai na shige daki, Su Mommy na kira na hada mana video call, daddy ma yana gida don haka hirar mu muka sha sosai, na basu labarin bikin da muka je har hotuna da videos din da muka yi na tura musu. Ban yi kuskuren fada musu har dare nayi a wajen bikin ba wanda dalilin haka yasa Abbu ya mun fada kuma har yanxu yake fushi dani saboda nasan kuskurene hakan, kamar nayi kirari ne na dabawa kaina wuta. Su Ni’ima suka shigo dakin na wa su Daddy sallama, nan muka bude sabon shafin hira dasu. +

Kamar yadda suka ce, yini sur suka mana a gidan. Da rana Abbu yace kar mu yi abinci, oda aka mana daga Chicken Delicacy peppered chicken da spaghetti lasagna sai yoghurt mai sanyi, muka ci muka yi nak tare dasu Hafsy. Bayan mun gama cin abincin na ja su kicin muka yi baking din cupcakes, babu kayan icing don haka bamu yi icing din shi ba. Da yamma likis Abbu yace su fito ya maida su gida, na rataya gyale a kafada ta muka fita tare dasu zan musu rakiya, cikin motar Abbu picnic su Qaseem ne a ciki sun hakimce Hafsy tana gaba su kuma suna baya Abbun yana jingine da motar yana amsa waya cikin hadadden turancin shi hannunshi daya saye cikin aljihun wandon shi, su Sa’adiya suka shige mota ni kuma na tsaya daga waje muna er hira har ya gama wayar ya shiga motar ya tayar, na ja baya kadan ina daga musu hannu, ya zuro kanshi ta cikin motar yace “yah? Baki zuwa ne ke?” na kalli su Ni’ima kafin na kara kallon shi, “can I?” ya tabe baki, “that is idan kina son zuwa fa” na bude motar nima na shiga ya ja motar. Hira muke dasu Ni’ima amma jifa-jifa idanuna su kan sauka akan Abbu dake tuki hankali kwance, wata dagawa da nayi idanuna suka sauka cikin kyawawan sparkling eyes din shi masu cike da kwarjini ta cikin madubin gaban motar, kamar wadda aka zarewa kuzari haka naji jikina yayi sanyi, gashi na kasa janye idanuna daga nashi sai shine ya janye nashin. Nayi ajiyar zuciya a hankali tare da sauke kaina kasa, ina kallon su Ni’ima suna kus-kus suna en da-re-re-ku a raina nayi fatan Allah yasa ba jirgina suka harbo ba. A gidan muka yi sallar magriba da ishai’i muka ci dambun couscous sannan muka musu sallama muka tafi. Dawowar tamu shiru, su Hafsy kadai su ke shan hirar su ni kam ina kan wayata ina buga game din piano tiles saboda bana son satar kallon Abbu da idanuna suke yi har ga Allah. Muna shiga falo ban tsaya a falo ba nayi hanyar dakina, Abbu ya tsaida ni ta hanyar kiran sunana, na juya a hankali. Cewa yayi “Plss dafa mun shayi mana” nace toh. Kayan hannuna kawai na ajiye a dakin na shiga kicin na dafa shayin da kayan kamshi a ciki, na matsa dan lemun tsami na zuba a cikin butar shayi na dora akan tray tare da kofi na kinkima na kai mishi. Yana zaune ya sa system dinshi a gaba da tulin takardu a gefen shi da alamu aiki zai yi, na ajiye akan coffee table dake gefenshi na durkusa a gaban shi, ya dago a hankali ya kalleni, “lafiya Nafeesah?” na sadda kaina kasa nace “Abbu don Allah kayi hakuri da abunda ya faru jiya, in shaa Allahu ba zan kara ba. Don Allah ka daina fushi dani!” shiru yayi yana kallona kafin ya nisa, “ba fushi nayi ba Nafeesah. Kawai ban ji dadi bane yadda kika biyo namijin da baki sani ba cikin dare, what if God Forbid, something bad happens to you Nafeesah? Bayan wannan kin duba shigar dake jikin ki kuwa? Haba Nafeesah!! Ke da nake ganinki da hankalinki da komi, how could you walk in front of many people with that dressing? And you were smiling and laughing in front of that guy, me yasa??” na sake yin kasa da kaina, ina mamakin ta yadda aka yi har Abbu ya ga irin shigar da nayi da kuma hirar da muka yi da Bilyamin, sai dai yanxu is not the right time to think about that, fata na daya kawai shine Abbu ya daina fushi dani. Last 20 to 23 hours has been like a hell to me, sukuni da walwala sun kaurace min saboda fushin mutumin nan daya; Abbu. Ji nake idan na kai gobe ba tare da na ga murmushin shi a gare ni ba zuciyata zata iya bugawa. Kaina na kara yin kasa dashi nace “kayi hakuri Abbu, ba zan kara ba” yace “dadi na dake Nafeesah kina da saurin admitting mistakes naki ki kuma yi repenting immediately, Allah yasa ki dore a haka” nayi kasa da kaina zuciyata ta fara washewa, da alamun ya huce. Yace “tashi ki je ki kwanta, ki daina damun kanki kuma ba fushi nake yi dake ba kin ji?” na dago a hankali na kalle shi kamar mai son karanta gaskiyar abinda yake fada, ya sakar min murmushin shi reassuringly. Naji wani irin sanyi ya mamaye min zuciyata, nima murmushin na sakar mishi sosai cike da farin ciki nace “Abbu nagode sosai, Goodnight!” na mike cike da kuzari da kwarin jiki na tafi, ya bini da kallo yana murmushi sai dana shiga daki sannan yayi ajiyar numfashi ya dauki shayin dana hada mishi ya fara kurba a hankali yana gyada kai cike da nuna gamsuwa. Ni kam ina shiga daki har sai dana yi dan tsalle cike da murna, na shiga bayi nayi brush na fito ina en wake wakena cike da farin ciki nayi shirin kwanciya barci, tsalle nayi na fada kan gadona, na mirgina daya gefen inda wayata take na bude, sai dana yi chatting na shiga accounts dina na twitter ne, instagram, facebook duk nayi posting ina cikin muudu mai dadi kafin na kashe wayar, na kashe wuta, na balle ma6allan gaban rigata na gaba guda uku naja bargo har wuyana, nayi addu’ar kwanciya barci na shafa na rufe idanuna, ba dadewa barci mai dadi ya yi awon gaba dani.”I heard that You are leaving the lab at the end of this week koh?” cewar Mrs Smith Head of Lab dinmu. Na gyada kaina nace “yes ma’am” tace “bayan kin gama Program din me zaki yi? Zaki wuce da HND ne?” nace “I’m not very sure ma, I’m thinking of filling D E form” tace “ina fata a nan BUK ne?” na girgiza kaina da sauri, “no ma’am, ABU Zaria ne” ta kalleni tana murmushi, “why?” na sadda kaina kasa kawai, me zan ce? Nace “maa nafi son Zaria ne sabida mun fi kusa dasu, bana son yin nesa da gida” ….ina so nayi nesa da Abbu da Iyalan sa Saboda ina jin tsoron abinda zan janyowa kaina, naso in kara da gaya mata haka sai dai nayi shiru. Ta gyada kai, tayi signing din takardar dana bata ta miko min nasa hannu biyu na amsa, tace “am wishing you all the best Nafeesah” nace “thanks ma’am” na fita.
Mun gama ayyukan mu na ranar muna zaune a cikin lab din muna hira ni da Ramlah, su Khaleesat tuni suka gama nasu IT din sati biyu da suka wuce. Nayi scrolling down ta cikin facebook account dina, anan na ci karo da status din da Muneer yayi mintuna biyar da suka wuce, “Soon…..!” na dan rausayar da kaina cike da alamun tambaya, me yake nufi? Na danna button din like. Ramlah ta kalle ni tana tabe baki, “ni har na rasa abinda zan fada miki game da Muneer wallahi. Ki kyale gayen nan haka nan kin ki kiji, yanxu har ta account din shi kike bi kina stalking din shi?” na yamutsa fuska, “stalking kuma Ramlah sai kace wata mara aikin yi? Kawai ina chatting ne na ci karo da status dinshi nayi liking, shine nayi stalking saboda Allah?” tace “ni dake da marar aikin yi duk daya nake ganin ku wallahi, wani mara aikin yi din ma ya fiki Nafeesah. Kin makalewa namiji daya kamar wata wadda bata da masoya, da girman ki da class din ki da komi. Allah ban taba ganin mutum marar fahimta ba irin ki ban sani ba ko duk sangarta ce ko kuwa? Amma……” “For Heaven’s sake Ramlah!!” na katse ta a fusace har ina hadawa da buga hannuna akan bench, “this is my life kin gane? You have no right da zaki zauna kina lecturing dina akan abinda yake feeling dina ne kina ji? Baki son Muneer fine!! Ni da nake son shi sai ki bar ni inyi ta son nashi please!!” cike da mamaki ta kalleni, ta daga baki zata yi magana nayi saurin tashi na bar mata wajen. Yinin ranar haka nan muka karasa shi cikin kuncin rai su kan su en lab dinmu sun fahimci akwai abinda ke faruwa damu don basu saba ganin mu a haka ba, we are always cheerful koda yaushe muna tare muna hirar mu mai burgewa muna tsokanar juna amma ranar kowa tashi yake yi a cikin lab din, ina kallon Ramlah sosai ranta ya baci don har sai data share hawaye, jikina yayi sanyi sosai, ni kaina nasan Ramlah bata cancanci abinda na fada mata dazu ba, Raina ne ya 6aci sosai, so many annoying thoughts were running through my mind a lokacin, zan iya cewa Ramlah Sara ne tayi akan ga6a na sauke fushi da takaicin wasu a kanta. Karfe biyu tana cika na suri jakar hannuna na musu sallama na fita, a bakin kofar na tsaya, bayan kamar minti goma Ramlah ta fito. Da sauri na tari gabanta, “am sorry babe, I shouldn’t have said what I said earlier…. M sorry, really” ta kauce daga gabana, “me zan ce miki Nafeesah? Ban cancanci in miki magana bama balle inyi intruding din personal life dinki ba, m sorry!” nasan cewa magana ce ta gaya min, naji kunya ta kama ni a lokacin, A taron mu da Ramlah I must have hurt her feelings da maganganun dana fada mata, bata cancance su ba ko kadan. Da sauri na kara tarar gabanta tare da riko hannunta, “look Ramlah! Wallahi I really didn’t meant what I said da gaske nake, ni kaina abun yana damuna Ramlah. I’m trying, ina kokarin ganin cewa nayi yaki da son Muneer a cikin raina amma na kasa. No matter how hard I try, na kasa shi yasa nake jin haushin kaina nima, ina jin takaicin abun nima Ramlah har na fiki sai dai ya zan yi? Zuciya ta taki aminta da hakan ban san ya zanyi ba Ramlah….” zuciyata ta karye na kasa cigaba da maganar, idanuna suka yi jawur, lebena na ciza ina kokarin tsayar da hawayen dake kokarin xubo min. Ramlah ta dafa hannuna fuskarta cike da damuwa, “m sorry too Nafee. Bana jin dadin abinda yake yi miki ne ko kadan, it’s hurting me. I love you babe, duk abinda zai bata ranki ina kin shi har cikin raina, na ga alamun baki son kyale shi bayan nasan cewa yana bata miki rai, I didn’t know, ki yafe min” rungumeta nayi ina tapping bayanta, “I love you too Ramlah, m sorry too. I shouted at you” ta rungume ni itama, mun dan jima kafin muka saki juna, ta kalleni fuskarta da wani expression dana kasa ganewa, ta sake cewa “m sorry Nafeesah” nace “what for again? Idan maganar Muneer ce ta wuce don Allah mu daina yin ta haka nan” ta gyada kai. Muka samu waje muka zauna muna er hirar mu har Malam Bala yazo na mata sallama na tafi tana daga min hannu, taren mu da Ramlah kenan!. +

Shirye-shiryen komawa gida nake babu kama hannun yaro, ganin abun nake yi kamar a mafarki. Kamar yau ne fa nake shirin tahowa Kano gashi har watanni shida sun wuce, na fada a cikin raina ina karewa akwatuna na kallo wadanda na gama shirya kayana a ciki. Hafsy ta leko dakin, gani na a tsaye ina karewa dakin kallo ta shigo ciki tare da maida kofar ta rufe, gefen gado ta samu ta zauna ta kalleni a marairaice, “yanxu Yaya Nafee gobe zaki tafi ba zaki kara mana ko kwana daya bane?” na zaro ido ina kallonta, “Lallai ma Pretty ashe baki tausayi na, ko don ke kina gaban Mom and Dad dinki ne shi yasa? Nima ina so in je in gansu saboda nayi kewar su sosai” ta turo baki, “to ba kina zuwa kina ganin su ba duk weekend?” nace “dat’s a different magana ai, so nake in koma kusa dasu gabadaya kin gane?” tayi rau-rau da idanu sai ga hawaye shar-shar, da sauri na zauna a gefenta na fara lallashinta har tayi shiru, nace “haba mana da girman ki kike kuka? Kar ki damu zan dinga zuwa kuma ina muku weekend kinji?” da sauri ta dago kanta ta kalleni, “da gaske?” na gyada mata kai ina murmushi, sai dai daga can kasan zuciyata nasan cewa yaudarar ta kawai nake yi don ta warware, ina fata idan na saka kafa na bar gidan Abbu ya zama fita ce ta har abada, ko a mafarki bana fatan in sake komawa. Da biyu nake gaggawar in koma gaban su Daddy na, ina so inyi nisa da Abbu da gaggawa, he has started putting some effects on me wanda duk iya kokarina nason ganin na hana su affecting dina abun ya ci tura, shi yasa nake so in bar gidan as soon as possible kafin abubuwan su fi karfina. Hira na fara jan ta dashi ina tsokanar ta, nan da nan ta ware ta fara dariya, tare da ita muka cigaba da shirye shirye, na fidda kaya masu dama da wasu daga cikin kayan kwalliyata na ba Harira tayi ta godiya kuwa. Ana kiran magriba muka bar shirin muka yi sallah, Hafsy ta dauko littafan ta na taya ta muka yi bitar karatu har aka kira Ishai’i muka yi, muka fita wajen cin abinci. Muna gamawa muka koma kan kujeru muna kallo, duk da kallon daga ni sai Hafsy ne su Abdullahi wasan su suke yi abin su. Abbu da Anty Mubeenah suka yi sallama suka shigo falon, muka musu sannu da zuwa duk suka wuce dakinsu da alamun kayan jikinsu zasu canza. Anty ce ta fara fitowa, kamar yadda nayi zato ta canza kayan jikinta zuwa doguwar riga, Kai tsaye kan dinning ta wuce ta zauna. Ba a jima ba Abbu yayi joining dinta shima ya canza kaya zuwa na barci, riga da wando na M$S, muka cigaba da kallonmu har suka gama cin abincin suka dawo inda muke suka zauna. Hirar su suka fara yi su da ‘ya’yansu, Anty tace “Nafeesah gobe sai tafiya gida ko?” nayi murmushi tare da gyada kai, tace “eyyah! Zamu yi kewar ki ko don dadadan girke-girken ki” Abbu ya jefa mata wani irin kallo, Qaseem yace “Yaya Nafee amma zaki dinga kawo mana ziyara koh?” nace sosai ma. Hafsy tayi caraf tace “anan ma zata dinga mana weekend koh?” na kalli su Abdullahi da suke kallona cikin zakuwa da son jin amsa ta, murmushi nayi nace “ehh” a hankali. Suka dauki shewa suna ihun murna, kallon su kawai nayi ina murmushi. Karfe goma tana yi na tashi na musu sai da safe, Hafsy ta mike da sauri ta biyo bayana, ina ji Abbu ya tambayeta, “pretty ina zuwa?” ta juya tace “ni dai a wajen Yaya Nafee zan kwana yau” yace “a’ah zo ki wuce dakin ki, zaki takura mata” aikuwa ta bare baki zata fara kuka, nayi saurin janyota jikina, “babu komi Abbu, taho muje kinji?” ta ware hakora tana dariya, naja hannunta muka shiga daki. Brush muka yi muka fito, nace ta zauna bari inje in dauko mata kayan barci, na fita. Falon babu kowa duk sun tafi dakinsu, naje na dauko mata kayan. Na fito kenan daidai Abbu yana fitowa daga dakinshi, ya kalleni, da sauri na sadda kaina kasa nayi niyar wuce shi da sauri, cikin wata irin murya da ban taba jin ta a gun Abbu ba naji yace “Nafeesah!” na tsaya cak duk da ba haka naso in yi ba, so nayi in yi kamar ban ji ya kira ni ba in shige dakina wanda bai fi taku takwas daga inda nake tsaye ba, but damn me and my legs. Ya tako a hankali har inda nake tsaye, zuciyata bugawa take yi da sauri har naji tsoron kar ya jiyo sautin, shiru ya biyo baya na fiye da minti biyu, jikina ya bani cewa kallona yake yi don haka naki daga fuskata balle in kalle shi. Yayi ajiyar numfashi a hankali, yace muryar shi kasa-kasa, “are you sure Pretty ba zata takura miki ba?” na tabbata ko nayi magana ma da kyar muryata ta fita don haka na gyada mishi kai kawai. Yace “umh…. Da gaske zaki dinga zuwar mana weekend?” nan ma kaina kawai na iya gyadawa. Yace “good! I’m happy to hear that. Je ki kwanta sai da safe” da sauri na wuce har kafafuna suna hardewa na fada dakin kamar wadda aka jefa, Hafsy ta daga kai ta kalleni da sauri, murmushi na sakar mata na mika mata kayan barcin ta saka nima na sa nawa, wando ne iya gwiwa don nasan ba fita zan sake yi ba da rigar vest mai budadden gaba zan iya cewa Rabin kirjina a waje yake. Na mana addu’ar kwanciya barci ni da Hafsy muka shafa, na janyo bargo na rufe mu tare da kashe mana wuta. Ban sani ba tsautsayi ne ko kuwa Kaddara ya saka ni janyo wayata na shiga social media?? Well, that was the worst moment I’ve regretted the most in my life!!!.Ban san lokacin dana saki wayar hannuna akan carpet din dakin ba, na jingina bayana da allon gado ina kallon wayar kamar wadda aka turo mata da ranar mutuwar ta, hoton Muneer ne shi da wata tsaleliyar yarinya ya dora a shafin shi na instagram, a kasan hoton naga yasa *Finally Engaged Alhamdulillah…, getting married in the next 6 months!*. Ban taba sanin cewa numfashin mutum ya kan dauke, zuciyar mutum ta daina bugawa ba alhalin mutum na raye sai a lokacin, lokacin da nayi kokarin warto numfashi na sai gani a tsakiyar carpet din dakin dafe da kirjina, Zufa ta shiga keto min ta ko’ina, jikina rawa yake yi kamar mazari. Allah kadai Yasan iya adadin lokutan dana kwashe cikin wannan hali. Kamar wadda aka zungura nayi zumbur na tashi tare da daukar wayata, ban damu da cewa lokacin karfe sha daya da rabi bane, abinda na sani kawai shine ina so inji daga bakin Muneer, cewa da gaske aure zai yi, wata zai aura ba ni ba. Na kalli Hafsy da take barcinta cikin natsuwa bana so in katse mata barcinta saboda nasan a yadda nake ji na ba zan taba yin kasa da muryata ba, ji nake kamar in bude baki inyi ta kwarara ihu har sai mutanen Duniya sun ji halin da nake ciki. Falo na fita, wutar falon a kashe take duk da haka akwai haske wanda kwayayen waje suka samar. Number Muneer na danna, take ta shiga ta fara kara. Kai kawo nake a tsakiyar falon na kasa zaune na kasa tsaye har tayi karan ta gama bai dauka ba, na sake danna mishi wani kiran, sai dana jera mishi missed calls takwas ina kirgawa ban kuma yi niyar dainawa ba, nayi imani a lokacin idan zai kwana bai daga kiran ba nima haka zan kwana ina kiran shi ba tare da gajiyawa ba. Ana tara ne ya daga cikin muryar barci, “hello Nafeesah lafiya??” sai na ma rasa abinda zan ce mishi, wani irin kuka yake shirin kufce min na datse hakorana ina maida shi ta karfi, Muneer bai kai wannan matsayin ba kuma, kuka akan namiji? Har abada! Ya sake cewa “Nafeesah, are you ok??” cikin gritted teeth nace “Muneer, you evil bastard!!” shiru ya biyo baya da alamun he was in shock, I couldn’t suppressed my anger shi yasa, “what?! Excuse me??!” ya fada shockingly, cikin rawar murya mai cike da bacin rai nace “You betrayed me Muneer!! Kayi wasa da zuciyata ka maida ni sakara, abinda ka mun ka kyauta kenan? Kana ganin hakan dacewa ne?” yace “me kike fada ne haka Nafeesah? Me na miki? Ta yaya na yaudare ki??” cikin karaji nace “kasan ina son ka Muneer!! You know it all along amma what? Aure?? Baka yi tunanin halin da zan shiga ba?” yace “I never Loved you Nafeesah!! Saboda kawai kina so na sai kiyi tunanin zan tauye kaina da rayuwata saboda ke? Why would I?? I mean ban taba cewa ina sonki ba, in fact, ban taba nuna signs na so a gare ki ba ko na taba?” kai na nake girgizawa cikin tsananin bacin rai da bakin ciki, ni Namiji yake gayawa baya so na da Babbar murya!! Muryata ta fara rawa, nace “ka cuce ni Muneer! Kaki ka so ni ka hana ni inso wadanda ke so na, you are one big devilish bastard on earth!” yace “enough Nafeesah! I’ve heard enough please, bani nace ki so ni ba, ban taba rokon ki akan ki so ni ba don haka you have no right da zaki saka ni a gaba cikin daren nan kina zagina da tuhumata akan laifin da ban sani ba kin gane?” na gyada kaina a hankali kamar wadda take gaban shi, nace “you are right Muneer!! You are right!! Laifina ne, ni naki yarda inji maganar mutane da kashedin da suke min, duk a tunanina kana so na ashe yaudarar kaina kawai nake yi….. Sai da safe kawai, sai dai I’m not sorry about waking u up, ina maka fatan uncomfortable sleep through out the night!!” na kashe wayata gaba daya. Zubewa nayi a kasan falon saboda yadda kafafuna suka yi sanyi, zuciyana kuna take yi kamar wadda ake soyawa. Duk yadda naso akan in daure kukan da yake tuko ni kasawa nayi, gani nayi idan ban yi kukan ba zuciyata zata iya fasa kirjina ta fito. Kuka na fashe dashi sosai kuma da karfi, a wannan lokacin ban damu ba wai Don mutane sun san cewa ina kuka saboda Namiji yayi dumping dina. Sai da nayi kuka na mai isa ta sannan na ta tashi ina hardewa da layi na shiga dakina, a dakin ma wani sabon kukan na dasa. Bakin cikin dake raina was incomparable da ko wani irin halin bakin ciki dana taba shiga a rayuwata, wallahi ko a cikin mafarki ban taba zaton cewa ni Nafeesah za a samu wani namiji a duniyar nan da zai daga baki yace baya so na ba sai gashi wanda na kwashe shekara curr cikin son shi da mafarkin kasancewar shi uban yaya a gare ni ya daga baki ya fadi kalma mafi munin saurare a gare ni, Lallai Duniya mai cike da abubuwan mamaki. Sai gabannin Asubahi barci ya suraro ya sace ni ina xaune a kasa na jingina kaina da jikina da gado.Juyi yake yi akan gado, barci yake ji sosai amma ko kadan barcin yaki zuwa. Gadon da yake Kai ya mishi fadi, gado ne wanda a kalla zai iya kwashe mutane biyar ba tare da wani ya takura wani ba amma kullum ta Allah shi kadai yake murzar shi, yana Juyi a kanshi, yana jin shi kamar wani mara galihu. Disappointedly ya sauka daga kan gadon, kan sofa yaje ya kwanta, yafi jin dadin kwanciya anan duk da cewa kafafun shi suna kan hannun kujerar ne saboda tsawon shi. Wani modem daya shigo dashi ya tuna ya baro shi a parlour, wasu muhimman bayanai ne a ciki ba shiri ya tashi ya fita, babu kowa a Cikin falon, wutar falon ya kashe yayi amfani da wayar hannunshi ya dauko Modem din. Kan three seats ya koma ya kwanta a parlour na daya, Family picture dinsu ya kurawa ido yana kallo. Ya gaji haka nan, Ya gaji da jiran canzawar halin Mubeenah, Ya gaji da kasancewa kamar wani marar aure alhalin yana da mata kuma yana da right din karo guda uku kwarara, yana bukatar rayuwar aure irin ta kowane normal mutane, rayuwa mai cike da soyayya da girmamawa ba irin rayuwar auren gidanshi ba, rayuwar auren da ba zaka taba ganin murmushi ko kafar matar auren ka a dakin ka ba sai idan tana bukatar either kudi ko bukatar namiji ta motsa mata, kai kuma naka bukatun ko oho! Yana ganin lokaci yayi da zai maida komi inda yake, maganar gaskiya yana bukatar mace ya kuma gaji da bin kan Mubeenah tana yankwana shi kamar wani mara galihu, Allah ya gani yayi iyaka Kokari da hakurin da zai yi. Yana nan kwance Cikin zazzafan tunani zai iya cewa ma barci ya dauke shi yaji karan bude kofar daki, a hankali ya bude idanunshi yaga Nafeesah ta fito daga dakinta, da mamaki ya bita da kallo a cikin ranshi yana tambayar ko lafiya? Yanayin tsayuwar da tayi tana tapping kafafunta a kasa nervously ga waya a kunnenta ya sashi cikin tunani me ke damun Nafeesah ne haka? A hankali idanunshi suka fara yawo a jikinta, duk da babu wadataccen haske a falon amma hakan bai hana shi hango surar jikinta cikin gajeren wando da vest din data saka, wani irin tension yaji yana building a cikin jikinshi babu shiri ya rufe idanunshi da karfi yana hadiyar yawu yana gayawa kanshi it’s not right! A hankali ya sake bude idanun yana kara kare mata kallo yadda jikinta yake swaying halittun jikinta suna motsi suna kara tada mishi hankali, yana so yayi motsi yadda zata san da wanxuwar shi a cikin falon, but hell! He couldn’t. God Forgive him but he’s enjoying seeing her in that attire, making him go mad, making him want to just drag her and kiss her senseless may be yayi wani abun worst than kiss…..! Maganar da tayi cikin fushi da daga murya ne ya dawo dashi daga tunanin da yake yi, “Muneer you evil bastard!” yaji duniya ta tsaya mishi cak kamar an tsaida kowane wucewar minti da dakika, may be he was mistaken, ba Muneer tace ba, kila ba sunan Namiji ta kira ba, kila Muneerah tace kunnenshi yake gaya mishi Muneer. Ya sake lafewa akan kujerar da yake yana kara kasa kunne, “kasan ina son ka Muneer!! You know it all along amma what?! Aure??!….” da sauri ya saka hannu ya danne kofofin kunnenshi yana girgiza kai, no! No way!! Karya ne!!! Kwatakwata ya manta a ina yake balle yace ga abinda yake yi, wani irin rugugi yake ji yana mishi ihu a cikin kunnenshi, maganganu mafi muni da daci daya taba ji an furta a gare shi, maganganun da suka girgiza shi suka yi turning rayuwar shi up-side-down, Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un ya dinga nanatawa har yaji nutsuwa ta saukar mishi, maganganun Nafeesah sun matukar girgiza shi, the fact that tana son wata halitta, halittar ma jinsin Namiji, abu ne da bai taba zato ba, bai taba zaton cewa tana da wanda take so ba, bai kuma taba zaton cewa abun zai yi affecting dinsa sosai kamar yadda yayi yanzu ba. Yana jin lokacin data tsuguna tana kuka sosai a tsakiyar falon, he wanted to man up yaje ya rarrasheta sai dai a halin da ake ciki shima rarrashin yake bukata, yana ji kamar shima ya fashe da kukan ko ya samu yaji sauki daga azabar zafin da zuciyar shi ta dauka, har ta gama kukan ta tashi ta koma dakinta bai iya tabuka komi ba sai bin ta da kallo helplessly. Lokaci mai tsawo yana cikin wannan hali kafin yayi karfin hali ya tashi zuwa dakinshi, alwala ya dauro ya kalli Al-Qibla ya fara jera nafilah yana mai rokon Allah akan ya mallaka masa Abinda ya jima yana kwatanta nashi ne…..!. +

      ☆☆☆☆☆☆☆☆

        A hankali na bude idanuna da nake ji sun min wani irin nauyi marar misali, na kai hannu na dafe kaina da naji yana sarawa kadan wuyana ya rike shima na kai hannu ina dan taba shi, idanuna suka sauka akan agogo, karfe shida ta wuce, da sauri na tashi tare da daddabar Hafsy ta tashi, muka shiga bandaki muka yi alwala muka fito muka yi sallah, dakinta nace taje tayi wanka ta shirya nima na shiga na watsa ruwa, nayi iyaka Kokari na wajen mantawa da abinda ya faru Jiya da dare, bana son tunawa ko kadan. Na fito daga toilet din daure da tawul a kirjina, na tsaya a gaban mirror ina tsane lemar jikina, idanuna sun tasa sosai sunyi luhu-luhu, ni dama nasan za a rina irin kukan dana sha jiya, kayan kwalliyata na janyo na shiga shafe-shafen abubuwa amma duk kokarin da nayi idanuna basu da alamun dawowa normal dama-dama ma fuskata swollen din da tayi ya rage sosai, tsaki naja na janyo wet tissue na goge kwalliyar da nayi, nayi simple one ko janbaki ban sa ba, riga da zani na saka nayi simple daurin dankwali, na dauki jakata na jefa wayata a ciki ba tare dana damu akan in kunna ta ba. Shades na saka a fuskata wanda ya rufe idanuna da yawancim fuskata, na zura takalmi flat na fita. Yaran ne kadai a falon suna kari iyayen basa nan, naja kujera na zauna a gefen Hafsy yayin da duk suka bini da kallo, dan murmushi nayi kawai, suka gaida ni na amsa Hafsy ta jefe ni da tambayar “Yaya Nafee me ya samu fuskar ki kika sa glass?” sai da nayi gyaran murya saboda dusashewar da tayi kafin nace mata “idanuna suke ciwo, bana so in goga muku ciwon ido ne” ta gyada kai tace Allah ya sauwake Yaya Nafee, Kai kawai na gyada mata. Muka fara cin abincin a nutse, ni kam caccakar abincin kawai nake yi duk yadda naso da inci abincin abun ya gagara, xuciyata a cunkushe take sosai, takaici da bakin ciki ya cika min ciki har babu wajen da abinci zai shiga. Suna gamawa muka fita, hango bakar Matrix da nayi nasan cewa yau Abbu ne zai kaimu kenan, mamaki ya kamani ko me ya hana shi yin break ne?? Muka shiga cikin motar, as usual a baya na zauna. Muka gaida shi ya amsa cikin wata hargitsattsiyar murya wadda tasa na kalli fuskar shi sosai kamar wadda take so ta gaskata Abbu ne ko ba shi bane? Ban taba jin muryar Abbu a hargitse haka ba, wani hargitsattsen kallo daya watso min wanda ya kada min yayan hanji babu shiri na sadda kaina kasa, ina jin Hafsy fadi ba a tambaye ki ba tana gayawa Abbu wai ciwon ido nake yi ina tsoron kar in goga musu shi yasa nasa glass, harara nake jefa mata a kaikaice sai dai wannan shine ainihin abinda bahaushe ya kira da ‘harara a duhu’ saboda ba gani na take yi ba. Har muka ajiye su a school dinsu ban dago kaina daga sadda shi din da nayi ba, suna fita na tashi na koma gaba kamar yadda muke yi, Abbu ya tashi motar muka wuce su Hafsy suna dago mana hannu. A hankali yake jan motar kamar ba tafiya muke yi ba, ya juyo ya kalle ni a karo na barkatai tunda muka fara tafiyar, gudun da zuciyata yake yi ya cigaba da karuwa a duk wucewar dakika. Kamar daga sama naji ya jefo min tambayar da nake tsoron ya jefo min, “Are you ok Nafeesah???!”

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]