[Advertisements⬇️]

AMININ MAHAIFINA CHAPTER 6 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

AMININ MAHAIFINA


CHAPTER 6
Hankalina gabadaya ya dauke daga jikina, babu abinda nake fahimta sai tattausan kamshin dake fita daga jikin Abbu, bugawar da zuciyar shi take yi da dan sauri-sauri, dumin dake fita daga jikinshi……. Ya dago fuskata daga jikinshi yana kallona kamar hadin baki, aka dawo da wuta lokacin. Na samu kaina starring at his brown oily eyes da suke wani irin sheki kamar zaiba, “Nafee, are you ok??” cikin daukewar tunani na daga baki nace “umh???” ba tare dana yi kokarin dauke idanuna daga kanshi ba, ya dan jijjiga kafadata, “hey!” kamar wadda aka daddaba daga barci, nayi firgigit ina kallon cikin falon, Ya Allahu! What the heck just happened?? Da sauri na durkusa na tattara kayana da suka zube nayi hanyar dakina a sukwane, da sauri ya riko tsintsiyar hannuna, nayi cik ina sauraren abinda zai ce ba tare dana juya na kalleshi ba, “lafiyar ki kuwa Nafeesah?” da sauri na gyada kaina, “lafiya lau, kayi hakuri dan Allah” ina jin sautin murmushin daya saki, ya sakar min hannu dama abinda nake jira kenan don haka na bazama dakina a sukwane. Kofar dakin na maida na rufe tare da murza key, nayi wuri-wuri a tsakiyar dakin kamar wadda take neman wajen buya kafin na zube a kasan dakin akan gwiwa na, zuciyana wani irin gudu take yi, na rasa abinda yake min dadi a lokacin. Ban san iya lokacin dana dauka a wajen ina zaune ba, tare da taimakon Innalillahi…. Dana dinga ja na dan samu sukuni a cikin raina, tashi nayi na fara bandaki na watsa ruwa mai sanyi a jikina duk da sanyin da ake yi sakamakon iskan da aka gama yi. Na fito daure da tawul a jikina na tsaya a gaban mirror, lotion na shafa na saka rigar barci wadda ta tsaya min a gwiwa, duk abinnan da nake yi idanun Abbu suna cikin memory na, na rasa abinda zan yi da zai dauke min tunaninshi daga cikin raina, chatting! Zuciyata ta tuna min, da sauri na tafi inda nayi jifa da kayan hannuna tare da wayar na dauko ta, ina daga ta na dan saki kara ganin yadda screen dinta ya tsattsage, na ciza tattausan lebena na kasa ina ji kamar in dora hannu aka in saki ihu saboda yadda nake son wayata dinnan, bana so ko datti ya hau kanta. Ganin chatting din ma bai mun abinda nake so ba yasa na janyo system dina na kunna na fara kallon Baywatch, ajiyar zuciya na dan saki ganin hankalina ya dauke zuwa ga film din.
+

Sai Washegari na ba su Hafsy doughnut din dana kawo musu, tare dasu ma muka cinye shi a cikin mota. Yau Daddy da kanshi yazo daukata, yazo duba jikin Abbu ne. Sai da aka yi sallar la’asar muka wuce Kaduna, bakin daddy bai yi shiru ba a hanya yana ta bani labarin kirki da mutunci irin na Abbu, bai san cewa yanzu bana cikin mood din sauraren labarin Abbu bane, ko sunan Abbu aka ambata sai naji faduwar gaba, shi yasa yau nayi duk kokarin da zanyi wajen ganin na kaucewa haduwa dashi, nayi, sai dai dole sai da na ganshi lokacin da muke mishi sallama ni da daddy. Kaina na jinginar da jikin seats din da nake kai na lumshe idanuna kamar mai barci, hakan yasa daddy ya kama bakinshi ya bame har muka isa Kaduna.

Da dare Ni’ima ta kira ni, bayan mun gaisa take fada min wai Fahad dinnan ne abokin Bashir ya dame ta akan ta bashi number na, na tabe baki nace “kada kiyi kuskure bashi Ni’ima” tace me yasa? Nace ban gane ba? Waye a cikin ku bai san cewa Akwai wanda nake dating ba? Taja tsaki, dallah dating ko crushing?? Waye bai san cewa crushing din Muneer kike yi shi baya son ki ba?? Na dan dakata kadan kafin inyi magana, “Ramlah mai bakin Aku!! Ita ta fada muku koh?” daga can tace that doesn’t matter ko kadan ai, ni ai zan bashi number! Nace cikin gatse, “ki bashi din toh, zaki gani ne” na katse wayar tare da jifa da ita akan gado. Muneer!! Na maimaita sunan, it’s kinda strange. Rana bata taba fita ta koma ga ubangijinta ba ba tare dana tunana bawan Allahn nan a cikin raina ba, amma har ga Allah yau dai, yau gabadaya na manta da existing dinshi a duniya, Anya lafiya ta lau kuwa??! Tashi nayi na koma falo wajen su daddy muka sha hirar mu, sai dana fara hamma sannan na musu sallama na wuce dakina.Da safe na ba daddy waya na nace a canza min screen din, Koda ya tambaye ni dalilin tsagewar ta cewa nayi faduwa tayi, to me zan ce mishi? Kafin azuhur sai gashi da sabuwar Samsung edge plus, nayi tsalle, nayi ihu na rungume shi, wayar da nake masifar so kenan sai dai bana so in takurawa iyayena da zancen wayar da nasan kudin abincin wani na shekara daya ne, shi yasa nayi shiru, sai gashi yau Allah ya bani ba tare dana roka ba. Daddy kam yasha addu’a ranar kamar bakina zai tsinke, haka nake ni kam, idan aka min kyauta sai in wuni ina wa mutum godiya. Mommy na cewa ta bada ayi fura don na kula Abbu yana so sosai, duk ranar dana kai fura ranar ita ce abincin shi har ta kare. Washegari na doshi hanyar Kano cike da tsaraba don sai da muka shiga shago na saiwa Hafsy dasu Qaseem sannan muka wuce, cike kuma da wani longing, longing to see someone wanda na ma rasa a wane matsayi zan ajiye shi cikin raina., abokin Babana ko kuwa Abokin Rayuwata??!
5

Aunty Mubeenah da wata kanwarta Shakirah kadai na taras a gidan, ina ga Abbu ya fita zagaya unguwa kamar yadda yake yi lokaci zuwa lokaci da er sandar taimaka tafiya, na durkusa na gaida su, Anty Shakirah ta mun sannu da zuwa har tana tsokanata da ina tsarabar ta tunda Allah yasa tana nan nazo. Matar tana da kirki, duk tafi sauran en uwan Anty Mubeenah da suke zuwa gidan, wasu idan suka zo ko kallon mutane basa yi balle su amsa gaisuwar su, wasu kuwa kallon mutane suke yi kamar kiyashi shi yasa nima bana kula da kurar data debe su. Dariya na dinga yi tana tsokanata, na ciro chocolate din kit-kat babba na bata nace ta kaiwa yara, na ciro wani hadadden turaren wuta na asalin en maiduguri na ba Anty Mubeenah inji Mommy na, ta amsa babu yabo babu fallasa, babu godiya ba komi kamar wadda ta bani ajiya, naji haushin abun ba kadan ba, na mike daga zaunen da nake na dauki jakar hannuna na wuce dakina. Kayayyakina na ciro na shirya komi a inda ya dace, na ciro fura da nonon da aka wa Abbu na Kai fridge na ajiye, daga kicin ina jiyo hirar dasu Anty Shakirah suke yi saboda a falo na biyu suke wanda yafi kusa da kicin din, Anty Shakirah ce take tambayar Anty Mubeenah mai yasa bata son turaren? Tace to mai zanyi dashi? Idan baki so ki bani ai ban rasa wanda zan ba bane, da sauri naji tace ina so wallahi, turaren ne yana da tsada naga gashi yana da wahalar samu shi yasa! Nayi kwafa ina girgiza kaina, wato kyauta ma tayi da turaren wutar da babu yadda ban yi da mommy akan ta bani in kaiwa Anty Haleemah ba mommyn taki ita ala dole sai ita, to ga abinda ya faru nan ai!. Dakina na koma cike da takaici ban jima da shiga ba naji hayaniyar su Hafsy a falo, da sauri na fita. Suna gani na suka kwashi ihun murna duk suka rugo, kowannen su so yake ya rungume ni, ni kam dariya kawai nake ina ihun su sake ni daga cakumar da suka kin kar su kayar dani amma ina! Sai da suka gaji dan kansu sannan suka sake ni, Abbu yana bayansu ya jingina bayan shi da kujera yana kallonmu cikin murmushi, da sauri na zube a kasa ina gaida shi, can kasan zuciya ta wani irin farin ciki yake mintsini na. Yaran naja muka tafi dakina tun kafin inyi abinda zan zo ina dana sani don wani sashen na zuciyata wai rada min inje in rungume shi yake yi. A daki na baza musu tsarabar dana kai musu, nan muka baje muka ci wasu a gun wasu kuma suka diba suka tafi daki lokacin da aka kira Magriba, ni da Hafsy kuma muka yi tamu a daki. 1

Muna gama dinner na mike da niyar inje in kwanta, Abbu ya kalleni yace “Nafeesah Akwai fura ne?” na gyada kaina a hankali, wata irin kasala ta rufar min saboda yadda ya kira sunana, yace dama min pls. Na wuce kicin na dama mishi furar, nasa ayaba lokacin da nake damawa dana gama kuma na watsa kankara a ciki na dauki bowl din dana juye furar a cikin na koma falo, yana sec parlour a kishingide akan kujera da alamu waya yake amsawa, cikin harshen turanci yake wayar. Na ajiye a gabanshi na fara kokarin zubawa a cikin cup ina satar kallonshi, wayar yake amsawa cike da wata irin yanga yana yi yana wani lumshe ido, accent din turancin shi ko kadan bai yi kama dana bahaushe ba, idan kana ji sai kayi zaton ko rainon kasar Ingila ne, to waya sani? Naji ance a LA ya kammala digiri dinshi na farko. Na danyi murmushi ina girgiza kai, sau tari ina mamakin yadda Abbu yake da yanga kamar wata mace, zaka iya mistaking kace yanga ce kam idan baka zauna dashi ba don a zahirin gaskiya haka yake naturally. Ya ajiye wayar hannunshi akan kujerar yana zama sosai, “what’s funny?” da sauri na girgiza kaina “ba komi?” na mika mishi cup din, ya kura min idanu kamar yana so ya karanci abinda ya saka ni murmushin da kanshi, nayi kasa da kaina, ina jin sighing din daya saki kafin ya amshi cup din, da sauri nayi niyar tashi ya tsayar dani ta hanyar tambayana ya Daddy na? Nan fa na zauna na fara zuba mishi labari har na wayar da daddy na ya canza min, ya daga girarshi yana dan murmushi, “inye! Her daddy’s girl!!” na sadda kaina kasa ina murmushi in ma zan iya cewa kila har da blushing, ya jefo min tambayar data kada min ciki, “garin yaya har screen din wayarki ya fashe?” na yi wuki-wuki da idanu kamar wadda aka kama tayi karya, ya sake tambayana, kafin in lalubo abinda zan ce wayar shi tayi kara, yana dauka na lallaba na mike da sauri sai dakina. Ina shiga na ajiye numfashi da karfi, Allah ya cece ni yau. Kayan barci na saka, na dauko log book dina na bude na dan dudduba kafin na janyo system dina na cigaba da kallon Pinocchio dana fara yi. Wajen karfe tara da rabi naji wayana tayi kara, na daga ganin bakuwar number yasa na daga da sallamata, daga can wata familiar murya ta amsa sallamar tare da karawa da “gorgeous!” cike da mamaki nace “waye?” sai dana kusa dakin zagi lokacin da naji yace “Fahad ne, abokin Bashir Saurayin Ni’ima” na hade fuska kamar yana gani na, jin nayi shiru yasa yace “gorgeous, baki gane ni bane?” a raina nayi exclamin kalmar ‘wai gorgeous!’ cike da jin haushi nace na gane ka mana, and please suna na Nafeesah ne ba wani abu wai gorgeous ba ka gane!” ya saki wata dariya data kara kular dani, “Haba gorgeous! To me kin cancanci abinda yafi wannan sunan ma. Kawai ki bani dama in nuna miki how precious you are to me, wallahi tun ranar dana saka ki a idanuna naji cewa na samu macen dana dade ina nema a rayuwata, tun daga ranar na baki wani matsayi mai girma a cikin raina, Gorgeous, wallahi u’ve become a very special part of my being, you are my happiness, you’ve got everything I need from my wife you are classy, beautiful, hafiza…..!!” blah-blah-blah ya shiga jero labarai har na gaji da saurare, ganin yaki dasa aya yasa na tsaida shi, “please Malam! Ita wadda ta baka number dina bata yi maka bayanin ina da Mijin aure bane?” ya kara sakin dariya, “ta dai fada min cewa kina da wanda kike so and unfortunately though to my relief baya sonki in return, baby just leave him, bai san ciwonki ba. I promise you zan so ki fiye da yadda yake sonki, na miki alkawarin mantar dake cewa kin so gayen can baby, just give me a chance kinji?” ni kam ina baki? Zuciyata cike da takaicin tonon sililin da Ni’ima ta min. Da kyar na saisaita kaina daga ihun da nake ji a cikin kaina na son in sossoka mishi zagi na dai yi kokari nayi calming din kaina, after all ai ba laifin shi bane, zamu gauraya da mai laifin. Duk da haka ban iya tsaida tsakin daya fito min ba, nace “Malam I don’t need your love or whatever trash you are talking about ka gane? Don Allah Kar ka sake kira na!” na kashe wayar da sauri. Ni’ima na kira, cikin sa’a ta dauka a ringing din farko, ko sallama ban bari tayi ba na fara zazzaga mata ruwan masifa, daga farko hakuri ta fara bani, daga kuma sai ta fara tsokanata wai akan ta ma taimake ni? Nace taimakon ki din banza? Nace miki ina so ne? Tace baki fada ba, zuciyar ki ta fada min. Ganin ta maida abun wasa na kashe wayar ina kara maimaita mata ta kira Fahad ne koma uban waye sunan shi ta gaya mishi kada ya sake kiran wayata don duk ranar daya kuma sai naci Mutuncin shi, ita kuma ta jirayi haduwar mu gobe!! Tace “Allah ya kaimu” cike da izgilanci, na kashe na kashe wayar ina kwafa. Ajiyar zuciya nake saukewa cike da takaici kamar zan hadiyi zuciyata in mutu. Karan wayata naji, da sauri na wawuri wayar ina tunanin kalar zagin da zan narka, ganin sunan Mommy ne yasa na dan saki fuskata kafin na dauka, gaisawa muka yi ta tambaye ni na sauka lafiya? Na amsa mata da lafiya lau. Mun danyi hira da ita kafin muka yi sallama, na dora wayar akan bedside drawer ni kuma na kwanta bayan nayi dimming din wutar dakin.Washegari kam su Ramlah sun ga tsiya a lab, Tunda muka zo na samu gefe daya na zauna fuskana a cune, ban mata magana ba balle sauran en lab din, su Ni’ima ma Suka zo naki kallon inda suke, ina ji suna tambayar Ramlah meke damuna ne tace itama tunda taxo a haka ta same ni. Har muka tashi a ranar ban kalli inda suke ba, sunyi maganar sunyi tsokanar duk a banza. Muna fita na fara kokarin wuce su, Ramlah tayi saurin tare ni tana harara ta, “wai ke dallah malama meye kike wani yazga mutane tun dazu?” nima na harareta, nace “ban sani ba dallah bani hanya!” Ni’ima ta matso tace “in dai akan zancen Fahad ne don Allah kiyi hakuri, wallahi dana san Abun zai bata miki rai da ban bashi number din ba, kiyi hakuri sis kinji?” na ajiye numfashi tare da kallonta, “ni fa ba bashi number din da kika yi bane ya bani haushi sai zuwa da kika yi kina yada sirrina a wajen stranger. Saboda Allah meye na zuwa kina gaya mishi wai ina crushing din wani?” tayi fuskar tausayi “Nima nasan ban kyauta ba, da gaske ban san lokacin dana gaya mishi ba wallahi, hira ce tayi hira ni kuma na saki baki ina bashi labari, amma don Allah kiyi hakuri” nace shikenan ya wuce, ta rungume ni tana er dariya, thanks sissy. Na harari Ramlah nace “ke kuma ba zaki bani hakurin bane?” ta zaro ido waje, “ni kuma me nayi?” nace waye ya gayawa su Ni’ima cewa ina crushing Muneer idan ba ke ba?” ta ta6e baki, “dadin ta ma ba karya nayi ba” nayi murmushin yake, zan ga ranar da Ramlah zata yi abu like a good girl in dai akan zancen Muneer ne, she’s always playing bad, making it obvious that bata son gayen ko kadan, to amma ya zan yi? A gani na Allah ne ya dora min son Muneer bani na dorawa kaina ba. Da haka dai muka shirya muka hau hira har Malam Bala yaxo muka tafi har su Ni’ima din zasu je su ga jikin Abbu. A can muka Tarar dasu Anty Rahina suma sun zo, nan muka wuni dasu muna ta hira har Yamma tayi kafin Suka tafi. Tun daga ranar kuwa ban sake ganin kiran wayar Fahad a waya na ba.
+

Satin Abbu uku yana jinyar kafar shi kafin ya warke ya fara fita harkokin shi. Naje gida weekend muka je Malumfashi, Malam Inuwa kanin baban su Daddy ya rasu, kakanni na na ainihi sun jima da rasuwa ban yi wayo na ganni dasu ba, shi yasa su Hafsy suke burge ni ba kadan ba, suna da kakanni ta kowanne fanni abin su. Wato naji dadin zuwa Malumfashi wannan karon ba kadan ba, cousins dina duk sun dawo daga makaranta wasu hutu suka zo wasu kuwa sun zo wajen gaisuwa ne, nan muka hadu muka yi ta yawace-yawace da ziyara har ban so lahadi tayi ba, haka dai muka yi sallama da dangina muka wuce gida. Muna isowa na wuce Kano Saboda yamma tayi don haka a gajiye likis na isa gida, babu abinda na iya tsinanawa, ina gama sallah na bi lafiyar gado sai da gari ya waye.

Mun je lab Ramlah take bani labarin wata er ajinmu a Kasu zata yi aure wannan week din, er Kano ce, ta tambaye ni zan je nace ai dole ne, Sahiba mutuniyar mu ce ta sosai. Tun a ranar na kira daddy na fada mishi ba zan samu zuwa weekend wannan satin ba saboda bikin abokiyar karatun mu yace shi kenan Allah ya kaimu wani satin. Nayi shiru ban kashe wayar ba, tuni ya fahimci abinda nake nufi, “kudin anko koh?” naji ya tambaye ni, na saki murmushi mai sauti, wato Daddy ya karance ni kamar bayan hannunshi, yace “I will wire you the money in the next few minutes” nace “to Daddy nagode, Allah ya bar min kai!” yayi dariya tare da cewa “uwata kenan”. A ranar muka shiga kasuwa muka sayo ashoben bikin, muka biya ta wajen telan Ramlah muka ajiye dinkin. Ranar juma’ah muka je saloon aka mana wankin kai da kitso, ni har kunshin hannu aka min, dama gani da son lalle kamar me. Ya kuwa yi min kyau sosai, sai da Ramlah taga na hannuna wai take cewa data sani da an mata itama, na kuwa dinga mata dariya. Daga nan muka yi shatar taxi muka wuce gida, sai da muka ajiye ta kafin muka wuce. Ina shiga falon naci karo da buhunan Irish, plantain ne, kayan marmari dasu doya, tunda na gani nasan cewa Abbu ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa Ibadan taron Doctors nana fadin Nigeria, Allah ya taimaki rayuwata na mishi text na gaya mishi zamu biya ta saloon daga lab, yau da na shiga uku na ai. Na taimakawa Harira muka kai kayan kicin muka ajiye su a inda ya dace kafin na wuce dakina nayi sallah. Ina xaune Hafsy ta leko dakin tace in fita mu ci abinci, bana ma jin yunwa amma haka nan dai na fita don nasan bani da wani excuse din badawa. Na dauki gyale mai fadi na dora akan doguwar rigar jikina. Bana yarda in fita daga dakina ba tare da mayafi ba matukar nasan Abbu yana gari sai dai by mistake. Suna kan dinning table a zaune, Abbu na fara hangowa. Sanye yake da shirt din KC brown da bakin Jeans, ya kara wani irin kyau na musamman a kwanaki shida din da nayi ban gan shi ba. Na tafi da dokina na durkusa na gaida shi, shima cike da fara’ah ya amsa min, na gaida Anty Mubeenah kafin naja kujera na zauna muka fara cin abinci. Da muka gama Abbu ya fita, Anty ta wuce daki mu kuwa muka zauna a falo muna kallo har wajen karfe goma da rabi, har lokacin Abbu bai dawo ba. Na kashe kayan kallon kowannen mu ya nufi dakin shi ya kwanta. +

                        Wajen karfe uku na dare na farka, kishi ya dame ni sosai ji nake kamar numfashina zai dauke dole na farka daga daddadan barcin da nake yi, gidan dama duniyar gabadaya tayi shiru kamar babu mai numfashi babu ko karar fan saboda an dauke wuta. Fitilar wayana na kunna na lalubi goran ruwa dana saba shiga daki da ita a kullum Saboda na sanni da bukatar shan ruwa sometimes sai dai babu, da alamun na manta ban shiga da ita ba ranar. A hankali na bude kofar dakina na fito, na fara tip toeing zuwa kicin kamar wadda zata je yin sata. Daidai kafar dakin Anty Mubeenah na jiyo kamar alamun sautin tashin maganganu, ban san dalilin daya saka ni kara kasa kunne ba, muryar Abbu ce take tashi kamar cikin fushi, “For goodness sake Mubeenah! How long has it been?? Kin san yaushe rabona dake? Kina ma kirga yawan kwanakin kuwa? Me yasa ne?! Me yasa ne ba zaki yi treating dina kamar yadda kowanne namiji yake samun kulawa daga matar auren shi ba? Na tambaye ki time without numbered Mubeenah, idan ma wani laifi na miki don’t you think it’s high time da zamu manta da komi mu rungumi rayuwar yayanmu hakanan ba?” tsaki naji taja, “kace duk abinda zaka ce Ibrahim! Ba damuwata bace, yaya da kake magana a kansu inaga ai bai kamata ka sako su ba, kai kace I just need to have birth to them, you will take care of them, meye hadina dasu then??” shiru na tsawon mintuna biyu ya wuce yayin dana kara kasa kunne, a sanyaye naji muryar Abbu wannan lokacin, “hakkina fa kuma Mubeenah?” “ni fa kaga ka dame ni ka hana ni barci na haba! Saboda tsabar fitina da jaraba a kyale mutum yayi barci ma cikin kwanciyar hankali ma ba za ayi ba?” amsar Anty kenan. Cikin daga murya yace “am fed up with ur cruel habits Mubeenah, dole ki gyara halinki idan kuma ba haka ba….!” katse shi tayi ta hanyar sakin dariya, “…. Idan ba haka ba zaka kara aure? Go ahead then, ko a da can ma hakan bai dame ni ba Ibrahim balle yanzun ka gane? Allah yasa matan duniyar nan zaka auro, I wouldn’t give a damn! Now can u get out please? Ina so inyi barci!!” ina jiyo hucin daya dinga fitarwa a fusace kamar zuciyar shi zata fito waje, cikin wani irin threatening murya yace “zan shayar dake ruwan mamaki kuwa Mubeenah” cikin muryar ko-in-kula, I bet she was shrugging her shoulder up ma lokacin kila tace “m looking forward to it” daga nan naji ana kokarin fitowa daga dakin nata, a sukwane na fada bayan labule tare da saka yatsa na danne saitin wajen dake samar da hasken flashlight a wayata. Yana fitowa ya maida kafar 
dakin da karfi ya rufe ji kake 6ammmmm!!! Ina jin lokacin daya bude kofar dakinshi ya shiga, sai dana bashi kyawawan mintuna goma kafin na fito daga maboyata na fada daki ruwan da ban sha ba kenan na koma kan gado na kwanta xuciyata fal cike da tausayin ma’auratan. Me ke damun Rayuwar Auren su ne haka??Da kyar na samu na sauka daga kan gadona ganin na gaji da juye-juye barci yaki zuwa misalin karfe tara kenan na washegarin ranar Assabar. Na fito daga dakina sanye da wandon Sports da rigar shi cotton ruwan madara, na dora hular beanie akaina wadda na nannade gashin kaina na saka a ciki. Wandering na fara yi a cikin falon hannuwana saye cikin aljihun wandon. Na tsaya a kasan staircase din dake falon, tunda nake a gidan ban taba Hawa saman ba, jifa-jifa dai na kan ga ko dai Abbu ya hau ko kuma yara sun sauko kuma ban taba tambayar me suke yi a wajen ba. Out of curiosity na fara takawa ina hawa saman, Tun kafin in karasa na saki baki galala ina kallo. Gym zan kira shi ko kuwa amusement park?? Kayan wasan yara kala-kala da different types of exercising machines ne birjik a wajen, wasu na san su saboda nima ina zuwa gym duk weekends lokacin da ina gida. Na fara zagaye wajen cike da mamaki, as in Abbu will never cease to amaze beings. Kan Dip station na hau na fara kokarin dagawa amma ko motsi, da alamun yafi karfina ne don haka na sauka. Daga bayana naji ance “hey! What are you doing here??” da sauri na juya, yana tsaye a jikin wata kofa sanye da sportys ya rataya dan karamin tawul a wuyanshi, na sadda kaina kasa cikin rashin abin cewa. Ya fara takowa a nutse har yazo gab dani, ya jingina da station machine din, jin yayi shiru nasan sauraren amsar da zan bashi ne yake yi, nace “umh! Dama kawai ina zagaye ne sai kuma naga na shigo nan” yace “this is your first time here I believe?” na gyada kaina. Yace I see. Are you interested in exercising?? Da sauri na dago ina kallon shi, “sosai ma Abbu! A gida ma ina zuwa gym duk sat….” wani irin kallo yake wata min babu shiri na kama bakina na bame, na sadda kaina kasa ina jin kafafuna suna dan shaking. Kokarin fita ya fara yi yana cewa “sai ki dan motsa jikinki ko? Ni zan sauka kasa….. By the way, I like your lalle!” nayi murmushi ina kara kallon hannuna, ni kaina nasan lallen yayi kyau sosai. Yana fita na fara wasa da karafa, sai wajen karfe goma da rabi na sauko falo, break nayi na koma dakina, sai lokacin naji gajiya da barci sun tarar min na kwanta. Kiran wayar Ramlah ne ya tashe ni daga barcin da nake yi, tace gata nan ta shigo layin mu daga amsar dinki in fito waje, na tashi da sauri na dora hijabi akan kayana na fita. Abbu da maigadi da wani makocin Abbu din suna kofar gida akan dan benci suna hira, na gaidasu. Ina tsayawa sai gata cikin napep, ta fito ta biya mai napep din, ta gaida su Abbu kafin muka shige cikin gida. Muna shiga ta fara jefo mun tambaya a rikice, “ke waccan giant gaye din waye? Anan gidan yake zaune?” cikin alamun tambaya nace wa kenan? Tace “wani farin gaye haka da jallabiya baka a jikin shi??” dariya na kwashe da ita nace “wai dama baki san Abbu ba duk abinnan da ake yi?” tayi turus! Da gaske wancan ne Abbu? Na gyada mata kai, “Ya Allah! He’s cool babe, dan dai yana da mata wallahi….!” duka na kai mata ina dariya, “da bashi da mata fa sai kiyi me maras M? Kina da mijin aure a hannu dai shegiya” ta turo baki. A dakina muka zube, ta fiddo kayan sun yi kyau sosai, “sai dai rigar tayi show me da yawa” na fada cikin korafi ina kara juya rigar, ta harare ni, “to sheikha. Ina cewa gyale zaki saka?” na turo baki kafin na daga kafada sama.
+

                       Wajen karfe hudu muka isa wajen shagalin bikin. Tuni an fara shagalin, yawancin en makarantar mu sun je abin an jima ba a hadu ba nan muka hadu aka yi ta hirar yaushe gamo ana hotuna. Ana gama sallar ishai’i aka fara daukar mu zuwa wajen dinner. Mun sake wata kwalliyar cikin doguwar rigar gown ta ankon zuwa dinner, purple ce sai rose head maroon color da heel shima maroon sai er karamar jaka maroon. Mun sha kyau abinmu kamar ka sace. Mun fito muna kokarin shiga mota zuwa wajen dinner nace karo da Bilyamin abokin Muneer, da mamaki ya min magana na juyo ina kallon shi, nima mamakin ne ya kama ni kafin muka gaisa dashi yake gaya min angon abokin shine. Ya Kalle ni tun daga sama har kasa yace “amma kinyi kyau sosai Nafee” nayi murmushi sosai har da fari, I’m a sucker for compliments. Yace “naga kina yawo ke kadai, Zan iya rokon alfarmar ki zama date dina for today?” nace “y not?” na kira Ramlah tazo muka shige mota abin mu muka wuce. Muna tafe muna ta hira har wajen dinner, wajen ya tsaru sai sautin kida ke tashi muka samu waje muka zauna, amarya da ango ana kan high table. An fara shagali kawayen couple din suka fita fili muka dan taka rawa da liki muka koma wajenmu muka zauna, ana ta shagali har ban san lokaci ya tafi ba sai dana ji karan shigowar message a wayana ta hanyar vibrating, na daga karfe goma da rabi gabana yayi mummunan bugawa, na duba message din daga Abbu ne, *”Where are you now?”* na mike da sauri jikina yana rawa, su duka suka juyo suka kalleni, Ramlah tace meye? Cikin rikicewa nace “Abbu….. Gida. Gida zan tafi yanxu” tace haba! Ki jira a tashi mana dan Allah kinda fa sauran mutane suna nan” nace “noo Ramlah. Abbu just texted me, nasan ma sai na sha fada yau wallahi” ta kalle ni sosai, “to sai me? Ina ce ba Daddy bane? Nasan ko daddy ne ba zai miki fadan kinyi dare a wajen dinar biki ba” na girgiza kai, “baki san Abbu bane Ramlah….. Bilyamin don Allah ko zaka taimaka ka mika ni gida? Babu nisa daga nan” na maida maganar ga Bilyamin don nasan idan nace zan tsaya fahimtar da Ramlah zamu iya kwana a wajen bata fahimta ba, ya mike yana lalubar makulli a cikin aljihun wandon shi, ya ciro key din ya Kalle ni, “muje koh?” na wa Ramlah da wasu daga cikin mates dinmu dake kusa da inda muke muka tafi. A cikin mota Bilyamin yana ta ja na da hira amma sam hankalina baya wajen ko kadan, da kwatance yayi parking a kofar gate. Na bude murfin motor na fita shima ya fita, na zagaya ta gefen shi nace “to Bilyamin ka gaida gida, thanks for the ride” yace “Kar ki damu…. Me za a cewa mutumin ne?” na danyi murmushi nace “kyale mutumin nan naka, kwana biyu shiru amma bai neme ni ba” yayi dariya yace to sai da safe. Sai dana shiga cikin gidan kafin ya tashi motar shi ya tafi. Bakina dauke da addu’ah da komi na shiga falon, babu kowa a ciki, da sauri na shige dakina na rufe, na tuge dankwalin kaina na zauna a gefen gado ina ajiyar xuciya cikin samun relief. Wayata ta dauki kara, ganin Sunan Abbu a jiki sai dana yi kamar Kar in dauka, na dai daure na daga na kara a kunnena tun kafin inyi magana muryar shi ta doki dodon kunnena, a fusace yake maganar, “wato Nafeesah kin raina ni koh? Karfe nawa na kafa miki dokar dawowa gida idan kin fita?” jikina yayi sanyi, naji dama ban je wajen dina din ba da ran Abbu bai baci Saboda ni ba, nace “Abbu don Allah kayi hakuri, wallahi dinner din ne ba a fara da wuri ba” yace “sai kuma aka ce dole ne sai kin je wajen dinner din koda zaki kai karfe sha biyu ne a waje koh?” na girgiza kai kamar yana gabana, yayi shiru. Har ina murna ya gama fadan shi sai kuma naji yace “waye ya kawo ki yanzun?” nace “Bilyaminu ne, dan makarantar mu ne” yace “dan makarantar ku? Kawai Saboda yana dan makarantar ku zaki kwashi kafa ki shiga motar shi babu tsoron komi a matsayin ki na diya mace?” nayi saurin cewa “ai abokin…..” sai kuma nayi shiru, harshe na yayi min nauyi sosai na kasa fadar kalmar. Shiru ya biyo baya, bai yi magana ba ni kuma na kasa karasa abinda nayi niyar fada, “it’s okay!” naji yace daga can a hankali kamar ba shine wanda yake daga murya yanxu ba, “goodnight!” ya kashe wayar. Na bi wayar da kallo cikin sanyin jiki, da kyar na iya sauka daga kan gadon na cire kayan jikina nasa na bacci na kwanta.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]