[Advertisements⬇️]

AMININ MAHAIFINA CHAPTER 5 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

AMININ MAHAIFINA


CHAPTER 5
Ya Allah! Cheerful Abbu din dana sani ya tafi, wannan Abbu din ban taba ganin shi ba, a fusace yake sosai kamar wanda zai tashi daga zaunen da yake ya hau ni da bugu, gabadaya jikina ya dauki rawa hawaye suka ciko idanuna, bana son fada ko kadan a rayuwata. Cikin rawar murya irin ta wanda yake so ya fashe da kuka nace, “Naje saloon ne shine na biya gidan su kawata Ramlah” ya galla min harara, “da ixinin wa??” nace “umh, ai na fadawa su Malam Bala da suka zo dauka na dazu”, yayi shiru kawai yana kallona. Malam Bala ya fada mishi tun dazun, that means he have no right to be angry at her, but still, he’s just pissed up. Dan siririn tsaki yaja ganin har na fara shesshekar kuka, ya shafa tattausar sumar kanshi da a koda yaushe a gyare take tana sheki, “it’s okay…. Bani ruwa a fridge” da sauri naje na dauko na kawo mishi, yasa hannu ya amsa fuskar shi har lokacin a murtuke, ganin nayi tsaye naki in tafi yasa ya juyo yana kallona, “what?” he sounds so pissed up at me, da sauri na hau share kwallar data fara xubo min again nace “Abbu don Allah kayi hakuri, wallahi ba zan kara ba don Allah” ya lumshe idanunshi a hankali, “it’s okay Nafeesah, banji dadin abinda kika yi ba, a gidanku kina kai har Magriba a waje?” nayi saurin girgiza kai, “to me yasa a gida na? Saboda kin raina ni ne ko kuma don kin baro gidanku kina tunanin zaki yi duk abinda kike so anan ba tare da an miki fada ba?” nan ma kai na girgiza a hankali nace “tun dazu muka taho, gidan Akwai dan nisa ne daga yau” yace “bana tolerating abubuwan nan Nafeesah kin gane? Daga yau kada ki sake wuce bayan Magriba a waje…… No! Duk inda zaki fita you must tell me first indai kina cikin garin Kano, understand?” nayi saurin jijjiga kaina, yace “you can go now!” kamar wadda take akan kaya, da sauri na wuce dakina. Sallah na fara yi kafin na kira mommy muka gaisa, labarin abinda ya faru na shiga bata, budar bakinta cewa tayi “ai yayi min daidai wallahi, wato har kin fara yawo barkatai ko?” sai lokacin naga wautata dana fada mata, na batan fuska kamar ina gabanta tare da turo baki, “mommy! Saloon fa naje saboda Allah daga can na wuce gidan su Ramlah, Ramlah ce fa kawata ke kanki kin shaida sau nawa take zuwa gidan mu ta kwana?” tace “but still baby, ba kamata ki tafi ba tare da kin fada mishi ba, kin san dole ranshi ya baci dama” na shiga diddira kafata a kasa ina gunaguni, “ni dana sani dama ban fada miki ba tunda ba zaki goyi bayana ba” ta sassauta muryar ta, “Ohh Nafeesah baki fahimta koh? Ba goyon bayan shi nayi ba, it’s just the fact. Ke yanzu amanar muce a hannunsu, kina ganin ya dace ya barki ki dinga fita kina dawowa duk lokacin da kika ga dama a garin da yake bakon ki iye? Ko kina ganin girmamawa ce ki kama hanya ki fita ba tare da kin sanar dashi ba? Wani Malam Bala is not an excuse tunda ba a karkashin kulawar shi kike ba kin gane?” na gyada kaina a hankali she’s right. Muryar daddy na jiyo ta cikin wayar, “Habibty ke da waye kuke waya kika kyale ni ni kadai a falo?” da sauri na shiga mata magiya akan Kar ta fada mishi hirar da muke don nasan kadan daga cikin aikin Mommy ne, ta ba daddy din muka gaisa. Hira muka shiga yi yawanci ta wajen aikin shi ce, mun jima sosai kafin muka yi sallama dasu. Kayan barci na na zura na bi lafiyar gado ko abinci ban nema ba. +

Ina kan sallaya ina lazumi bayan nayi sallar asubahi, ban cika komawa barci ba a irin wadannan lokutan, kofar dakin naji ana kwankwasawa, na tashi naje na bude, Harira ce. Muka gaisa da ita a mutunce tace “dan Allah Nafeesah ko zaki taimake ni da girkin yau? Bana jin dadi ne” nayi fuskar tausayi nace “Eyyah sorry pa! Meye za a dafa?” tace “ki dafa duk abinda kika ga ya dace nace “to shikenan” tace nagode ta wuce dakinta. Daki na koma na dauko karamar hijabi data tsaya a kuguna na saka na fita zuwa kicin, yam delight nayi, kafin dahu sai na dauko fresh kifi a cikin fridge na fara shirin yin farfesun kifi.
Hankalina gabadaya ya tafi ga tsame doyar da nake yi daga cikin frying pan naji motsi a bayana, da sauri na juya har mai na fallatsan min a hannu na danyi kara kadan. Abbu ne sanye da wandon Jersey me layi layi irin na sport navy blue da top grey, gaban rigar zuwa tsakiyar kirjinshi ya jike da sweating alamun daga exercise yake. Yadda kayan nan suka mishi kyau suka mayar dashi kamar wani matashi at his Twenteth, you might even mistook him da wani modeler a babban kamfanin nan dake saka kayan sports, ko kuwa….. Ban san cewa na dulmiya cikin tunani ba sai dana ji saukar tattausan hannunshi a dantsen hannuna, tingling feeling din dana ji bashi da maraba da irin wanda naji ranar nan da nayi mistaking taba hannunshi. Na zabura nayi tsalle gefe guda tare da sakin matsamin dake hannuna ya fadi a tsakiyar kicin din, Abbu ya dube ni cike da mamakina, “hey! Are you ok??” cikin zaro idanu da rawar murya nace “ehh?” yace mai ya fallatsan miki a hannu, are you ok? Baki kone ba?” sai lokacin na tuno, sai kuma a lokacin naji zafi a wajen. Na dago hannun na kalli Inda man ya taba, thankfully bai yi komi ba sai dan ja da wajen yayi, nace “lafiya lau babu abinda ya same ni…. Ina kwana Abbu?” na fada ina dan dukawa, ya amsa, tare da dorawa da, “ya aka yi kike girki tun da safe?” na duka na dauki matsamin dana yar a kasa ina cewa., “Harirar ce bata jin dadi, shine tace in kama mata” ya gyada kai. Nace Akwai abinda kake bukata ne? Ya zuba min ido kamar mai tunani, “abinda yake bukata?” me yake bukata exactly? Shi dai yasan yana cikin yin exercise dinshi yaji kamshin girki mai dadi yana bi ta cikin hancinshi, kamar maganadisu haka yaji ana jan shi har cikin kicin din…, ganin bai amsa ba yasa na juya na fara kwashe doyar dake cikin kaskon na fara tsoma mata. Yayi gyaran murya tare da fitar da dan sautin tari, “ehhhem, ruwa nake so” na bude fridge na dauko mishi mara sanyi na mika mishi da hannuna biyu ya amsa idanunshi na kaina. Na sadda kaina kasa saboda wasu particles da naga suna fita daga cikin idanunshi nashi suna shiga ta nawa kamar mashi, dan murmushi yayi ban san me yake nufi da hakan ba. Sai daya shanye ruwan tas ya miko min goran, na amsa na jefa ta cikin dustbin. “What can I help you with?” na jiyo muryar kamar daga sama, da sauri na dago ina kallonshi cike da mamaki, ta wani bangaren kuma ina tantamar Anya shine ya furta maganar? To amma waye zai furta idan bashi ba? Mu biyu ne kadai a kicin din. Kai na girgiza mishi a kunyace, ya daga kafada, “k! Let me go and take a shower then” ya juya ya bar kicin din, ni kuwa me zanyi ba kallonshi ba? Har ya fita daga kitchen din. Na maida bayana na jinginar da canter, idanuna a lumshe ina kokarin tantance abinda ke faruwa da jijiyoyina, kwalwa da zuciyata.Bakwai saura na gama shirya komi akan dinning table, a gurguje na watsa ruwa na fito. Yau kam ban tsaya yin kwalliya ba balle bata lokaci wajen ciro kaya, simple kwalliya nayi daga hoda sai janbaki, na janyo wata atamfa English maroon color, dinkin rigar fitted ne sai zani 6-pieces, na kashe saurin dankwali kaman inji ne yayi ba hannu ba, na fesa turare tare da daukar jakata na zura flat din takalmi baki naja gyale na fita falon. Gabadaya kowa ya hallara akan dinning, nima sahun su nabi. Naja kujera kusa da Hafsy kamar yanda nake yi na zauna, Anty Mubeenah na gaida wadda yau er kwalliyar safen ma da take yi ba tayi ba da alamun ba zata leka wajen aikinta ba yau kenan. Shima Abbu sai dana sake gaida shi, shi kam a shiryen shi yake cikin Kaftan riga da wando ruwan madara bai san hula ba amma fa yayi kyau kamar ka sace shi, su Qaseem suka gaida ni kafin muka fara cin abinci a nutse. Abbu ya kaimu makaranta yau, sai da muka ajiye su Hafsy kafin muka wuce. Ina zaune a gaban motar kaina a kasa, a darare nake kamar ace kyat! In zura da gudu, kira’ar Sheik Sudeis ce take tashi a cikin motar cikin suratul-Anfal, munyi nisa sosai babu mai yin magana a cikin mu. Ya kalle ni yayi dan murmushi, “me yasa ba kya sakewa ne idan ina kusa dake Nafeesah?” ya tambaya idanunshi akan titi kamar ma bashi ne yayi maganar ba, na kara sadda kaina kasa, Ya Allah! M I making it too obvious?? “umh?!” ya kara tambaya jin nayi shiru ban amsa ba, “ko kina jin tsoro na ne Nafeesah?” da sauri na girgiza kaina, yace to meye? Da kyar na iya cewa “babu komi Abbu?” ya kalleni sosai da idanuwanshi masu kama da wanda yake jin barci, da sauri na janye idanuna daga cikin nashi, yace “anya kuwa Nafeesah?” na gyada kaina da sauri, “da gaske nake Abbu, ba tsoronka nake ji ba” ya tabe baki yace “koma dai menene Nafeesah kiyi kokari ki rage shi, bana son hakan ko kadan kin gane?” na gyada kaina, yace good! Daga haka muka yi shiru har cikin makaranta, na bude murfin motar zan fita ya miko min kudi yan dubu dubu sabbi kar da ban san adadin su ba, kallonshi nayi cike da alamun tambaya, yace karbi mana! Na dan girgiza kaina, “amma Abbu me zanyi dasu?” yace ki badda mana. Na girgiza kaina da sauri, “no Abbu. Akwai kudi a hannuna wallahi, nagode sosai” ya dan hade fuskar shi, “to dama nace dake babu kudi a hannunki ne? Karbi nan tun kafin raina ya baci mana!!” a kunyace nasa hannu na karba, nace nagode Allah ya saka da alkhairi Abbu. Yayi murmushi kawai, sai dana ga bacewar motar shi daga idona sannan na shiga cikin lab. Ranar kam muka shiga shopping complex a cikin makarantar, sai da muka ga karshen 10k din daya bani tas ni da Ramlah, tarkacen kayan kwalam dana shafawa kamar zamu bude tireda.
2

    *********
Na maida littafin na rufe bayan nayi striking din date din ranar, calender ta ce wadda nake lissafin iyaka ranakun daya rage min in koma ga daddy na, in bar gidan Abbu. Gabana yayi wani mummunan bugawa dana tuno ranar da xan bar gidan? Me zai faru?? Nasan zan yi kewar su Hafsy sosai, I will miss them very VERY much! Zan yi kewar girkin da nake musu, yana saka ni jin cewa yes! M the controller, sai abinda na girka zasu ci…. Oops! Tunanin abinci da nayi yasa na kalli agogo da sauri, karfe hudu da mintuna ashirin, Abbu yaje Lagos, naji Ramlah tana cewa wai kamar wani event ne, Dr. Zai dinga zuwa makarantar da ba anan yake ba yana lecturing dalibai, yau dai kwanan shi hudu da tafiya tun ranar assabar, nasan dai duk yadda aka yi sun taso don tun dazu naji yana gaya mata bayan La’asar zasu taho. Na mike na fara kokarin cire riga da wando na kamfala din dake jikina, girki nake so inyi mai dadi wanda zai sanyaya mishi rai ya warware mishi duk gajiyar daya kwaso. Na saka wani blouse baki da riga turtle neck purple, na sakaye kaina cikin hula na fita daga dakin. Karan shigowar text a waya na yasa na dakata daga bude kofar da zan yi, na dawo da baya na daga wayar. Wow! Abbu ne!! Wani irin tsallen murna zuciyata ta dinga yi tun kafin inga abinda ke ciki., “on my way to the airport, me kike so in sayo miki a hanya?” nayi murmushi a hankali kamar wata wawuya, kwana biyun nan dai sai da Abbu yayi kokari yaga na saki jiki dashi, haka kawai zai saka ni a gaba da hira, wancan satin daya wuce ban samu naje gida ba, ranar Saturday ya dauke mu muka je Gidan Zoo muka yini a can, Washegari ya kaimu gidan Makama daga can muka shiga jifatu, siyayya iri-iri ya mana har sai da muka rasa abinda zamu dauka, daga nan muka wuce Golden Stars restaurant muka ci abincin lunch kafin muka koma gida, wannan satin naje gida ya kira daddy suka gaisa daddy ya bani wayar nima muka gaisa mun kwashe kyawawan mintuna talatin muna hira, ni kaina nasan cewa yanzu na sake dashi sosai, yana yawan yi mun text kwanan nan, idan ya min juma’a text ya kan hada da tambayar “hope kina lafiya? Babu matsalan komi koh?” idan kuwa yana gida watarana zai min text yace yana son abu kaza, zan dafa in dora mishi akan dinning, ko kuma in an yi girki bai mishi ba zai ce in dafa mishi wani abu, tun ina dar-dar har na daina tunda naga daga matar tashi har mai aikin da take girka abincin abun bai dame su ba.Sai dana yi cracking din kwalwa na kafin na lalubo abin fada, “Chocolate cookies, sweets and chocolate” cikin kamar kiftawar idanu ya maido reply, “noted and done! A tanadar mun delicious dinner pa!” nayi murmushi kamar yana kusa dani, “yes In shaa Allah. A dawo lafiya Allah ya kiyaye hanya”. Shiru shiru bai dawo da reply ba, na ajiye wayar na fita zuwa kicin. Harira nata kokarin hada wuta, na shiga kicin din. Da murmushinta ta juyo tana kallona, wani lokaci dama idan bana komi nakan kama mata da wasu ayyukan. Nace me za a girka mana ne yau kam? Tayi murmushi, tuwon semo ne zanyi da miyar egusi. Shit! Ba abinda nayi niyar girkawa ba kenan, I had to change her mind. Nace “amma tuwo? Baki ganin dare yayi, zamu iya gamawa da wuri kuwa? Don dai ni I need something simple to cook saboda yunwa nake ji” ta dakata da ciro nama da take yi daga fridge “kuma fa haka ne, me zamu dafa to?” nayi er dariya, “just watch me!” na fada store. Na fito da duk kayan da nake bukata na ajiye, ta kalle ni tare da dan dafe kai, “Ohh! Nafee ina zuwa don Allah! Na manta zan goge kayan su Qaseem na makarantar gobe” ta fita da sauri ko amsa mata ban samu nayi ba, Kai kawai na girgiza ina murmushi. Ba yau ta saba ba, duk ranar da nake taya ta girki ni nake karasa shi, bata taba rasa excuse din tafiya ta bar ni da aiki kaji pa dan Adam! Na kara gyada kai kawai na fara yanka green beans, albasa, carrots, cabbage, na watsa su cikin frying pan nayi frying sama sama. Na bude freezer da suke ajiyar dangin nama da kifi na ciro kayan ciki, na wanke su tass na dora a wuta tare da er citta, tafarnuwa da albasa. Kafin kace me gida ya kaure da kamshin daddadan girki mai dadi.
  
Dambun cous-cous nayi wanda na yanka hanta kanana a ciki, na zuba veggies dinnan dana soya, na soya cous-cous din sama-sama under low heat, kafin na kara ruwa kadan na barshi akan wuta ya turara. Nayi farfesun kayan ciki na hada lemun cocktail, ana kiran sallar Magriba na gama hada komi a kan dinning table, na ajiye numfashi cike da jin dadi. Daki na koma nayi sallah, ina gamawa na fito falo ina jiran dawowar Abbu. Nayi shiru na tsunduma cikin duniyar tunani, meye haka nake yi? Girki? Zaman jira? For what?? I sound like a married woman waiting for her husband, meye haka nake yi saboda Allah? Anya bana yaudarar kaina kuwa?? A hankali na mike jiki a sanyaye zan wuce daki na, karar bude kofa naji, da sauri na juya. Tuni nayi gefe guda da tunanikan da suke neman tarwatsa min kwalwa, na bude baki ina murmushi sosai “Abbu welcome!!”….. A hankali murmushin ya fara dusashewa ganin yana dingisa kafar shi…..
Da gudu na karasa wajen shi na riko hannunshi dake rike da brief case, tambayoyi nake watsa mishi ba kakkautawa, “Abbu lafiya? Abbu mai ya samu kafar ka? Abbu accident kayi a kan hanya?!…..” ya zauna akan kujera yana maida numfashi, “it’s just a minor targade, an gyara min. Kar ki damu” jin hanyaniya su Hafsy duk suka fito daga dakunan su, ganin halin da yake ciki tuni Hafsy ta fara kuka, sai da Abbu ya jata jikinshi ya rarrashe ta sannan tayi shiru. Ya kallemu duk munyi carko-carko a gabanshi muna muzurai, bai san sanda ya saki dan murmushi ba. “nace muku lafiya ta lau guys, oya Nafeesah dauko min abinci anan zan ci” jiki ba kuzari na koma na zubo mishi iya wanda zai iya ci na dora akan karamin coffee table na kai mishi, na koma kicin na dauko ruwa shima na ajiye mishi. Mu kuma muka koma kan dinning table muna cin abincin amma fa hankulan mu suna kanshi, muna cikin ci Anty Mubeenah ta fito daga dakinta, hankalina yana kanta har ta tsaya kusa da Abbu kamar suna yin magana ne, ta kalli kafar shi da yake nuna mata ta yi magana kafin ta nufo kan dinning din. Duk muka gaishe ta kafin muka koma wa cin abincin mu. Muna gamawa na tattara komi na kai kicin na wanke kayan tas na dawo falo, Abbu baya falon, na zauna ni dasu Abdullahi muka danyi kallo kafin na musu sallama na tafi dakina. Shirin kwanciya barci nayi na janyo wayana na shiga chats da friends dina ta whatsapp, dp din Muneer naga ya dora hoton wata kyakkyawar yarinya matashiya da alamun ta dan girme ni, naji wani abu ya soke ni a makogaro, kasa daurewa nayi na tura mishi tambayar “who is she?” mintuna biyu kyawawa kafin reply ya shigo, “a sister” nayi ajiyar numfashi lokacin dana ji wani sukuni yana ratsa ni, “Ohh! Ashe sistern ka ce…. Ya kake?” muka danyi chatting sama sama kafin ya min sai da safe wai barci yake ji, ni kuwa har da tura mishi hearts da clouds. Yana sauka nima na kashe wayana don dama saboda shi na tsaya. 
+

       Washegari ta kama daya ga watan mayu, public holiday ne don haka muna gida. Sai wajen karfe goma na fito daga dakina, nayi break fast na koma daki nayi wanka na sake fitowa falon. Su Qaseem suna zaune yanzu suna game, na zauna a tsakiyar su muka fara bugawa. Muna nan zaune muka ci karan intercom, Abdullahi yaje ya bude, sai gasu sun shigo shi da Aunty Ameenah. Da sauri na mike tsaye ina mata sannu da zuwa har ta zauna akan kujera, na shiga kicin na dauko mata lemu da ruwa na kawo mata, gaishe ta nayi ta amsa da fara’ar ta na koma gefe ina kallonta, wannan shine karo na farko da naga wani dan uwan Abbu a gidan tunda nazo. Qaseem ta tura yaje ya gayawa Abbu tazo, tare suke fito dashi, har yanzu yana dingisa kafar shi. Na bishi da kallo cike da tausayi har ya zauna, na gaida shi tare da mishi ya jiki ya amsa. Aunty Ameenah tace “tare muka zo da Abban Ikhlas, zai shigo ya duba maka kafar” na kai dubana ga kafar tashi, sai da cikina ya kada ganin yadda kafar ta kumbura suntum! Ya yamutsa fuska “kema na fada miki ba wani abu bane ba, targade ne an gyara min shi kuma, kumburin saboda targaden ya dade a jikina ne shi yasa” ta Harare shi, “ai ba cewa nayi kayi lecturing dina ba koh?” ta daga wayarta ta kira wata lamba, ba a jima ba wani kamilallen mutum da zai yi sa’an daddy na ya shigo falon, ya ba Abbu hannu suka gaisa. Kafar tashi ya kalla yana girgiza kai, “Anya haka zamu yi da kai kuwa Farfesa?” Abbu ya rausayar da kai kamar wani karamin yaro, “Abban  Ikhlas kawai neman rigima ne irin na matar nan taka, sai dana fada mata targade ne amma taki yarda” ya kara kallon wajen, “anya targade anan wajen kuwa? Bari dai mu duba mu gani” ya fiddo kayan aiki, wata er karamar naura ya fiddo ya jona da wani abu, ya kara abun a kafar Abbu sai ga komi na kafar dake kasan fatar shi ya fito a jikin na’urar, amma babu abinda muka fahimta tunda ba profession dinmu bane, ya gama dube-dubenshi ya daga ido ya kalli matar shi, “tsagewar kashi ce!!” ta zaro idanu yayin dana dafe kirji, yace yanzu bari in kira mai gyara yazo tukun. Muna nan zaune jugum-jugum har mai gyara yazo, har kuma zuwa lokacin bamu ga ko giccin Anty Mubeenah a cikin falon ba. Wani dan tsamurmurin farin dattijo ya shigo falon, maigadi wanda ya rako shi ya duba jikin uban gidan shi kafin ya juya ya fita. Mai gyaran ya fiddo kayan aiki ya fara, yana taba kafar Abbu na saki kara saidsai da duk suka juyo suka kalleni, jikina rawa yake, tsigar jikina tana tashi, Ji nake kamar nice naji ciwon. Abbu yace mu tashi mu koma daki amma fir naki, ganin mun ki tashi yasa ya kyale mu. Tunda aka fara gyaran kuka nake har da jan shessheka, ganin ina kuka sai Hafsy itama ta fara, nan da nan falon ya karade da kukan mu ni da ita, Anty Ameenah dariya ma ta hana ta lallashe mu. Mai gyaran ya gama gyaran da zai yi yawanci fara maida tarkacen kayan gyaran cikin jaka yana dan murmushi, “da alamun amaryar ce koh?” ya tambaya yana kallon Abbu, kusan a lokaci guda shi da Aunty Ameenah suka ce “ehhh?? Aah!!” ya bisu da kallon mamaki kafin ya murmusa yace to Allah ya kara sauki. Ya dauki jakarshi ya saba a kafada ya mike, mijin Anty Ameenah ta rufa mishi baya. Abbu ya kalleni a sanyaye, “bani ruwa Nafeesah!” da sauri na mike har ina hardewa, na dauko ruwan na kawo mishi na koma kusa da Hafsy na zauna. +

Mijin Anty Ameenah yana dawowa falon ya mana sallama ya tafi, Anty Ameenah ta dan taka mishi kafin ta dawo suka hau hira da Abbu. Mu kam muna zaune muna kallon news don in Abbu yana falo bamu cika kallon tashoshi barkatai ba, motsi kadai zai yi in Allah ya yarda da sannu na yake motsawa, bana ji a rayuwata na taba jin irin wannan feeling na ‘protecting’ da ‘caring’ ga kowane Bil’adama irin Abbu ba. Aka kira sallar Azuhur, Anty Ameenah ta umarce mu da mu tashi muje mu yi sallah, duk muka mike, mazan har Abbu suka fita zuwa masallaci ni kuma na tashi zan wuce dakina, Hafsy tana kan kujera tana barci, har na kai tsakiyar falon sai na juya na kalleta, “Anty ko zaki shigo kiyi sallah a daki na?” ta kalleni tana dan murmushi, “Eyyah, hutu nake yi Nafeesah, je ki abinki” a dan kunyace da jin kalamanta na juya. Ina gama sallah na koma falon, ina zama suma su Abbu suka shigo, muka bi Abbu da sannu ni da Anty Ameenah har ya zauna akan kujerar daya tashi. ‘yar aikin gidan ta fito da niyar dora abincin rana, bata san abinda yake faruwa a gidan ba, ita dai taga bakuwa ta gaishe ta sannan ta wuce kicin abinta. Muna nan zaune sai ga Anty Rahina ta shigo goye da danta a baya, na tashi da sauri ina mata sannu da zuwa, hannu na mika a bayanta ta sauko min da babyn, na rungume shi tsam a jikina, Ya Allahu!! Ina son yara kamar me! 
Anty Rahina ta zauna a gefen Abbu, sannu take jera mishi kamar bakinta zai tsinke na kula suna matukar ji da kanin nan nasu, fuska cike da damuwa take kallonshi, “me ya faru Ibrahim? Garin Yaya??” yayi shiru kawai yana kallonta, to me zai ce??
*_Flashback_*
       Yana tsaye a bakin titi a kokarinshi nason yayi crossing ya shiga wani babban shopping mall a garin Lagos kafin su taho ya tuno da ita, haka kawai ya tsinci kanshi da son yi mata tsaraba ko don shima ya faranta ranta yadda itama take faranta mishi ta hanyar yi mishi dadadan girke-girke masu kara lafiya. Don haka ne ya ciro wayar shi ya tura mata da text. 
         “……yes, In shaa Allah. A dawo lafiya Allah ya kiyaye hanya….”. Reply din data dawo mishi dashi kenan, yayi murmushi sosai, har kullum kulawar yarinyar zuwa gare shi tana matukar burge shi ba kadan, tunanin amsar da zai tura mata yake yi lokacin da aka ba wadanda suke kasa hannu su wuce, taku daya biyu yayi, bai tantance mai ke faruwa ba sai jin shi yayi kwance a kasa rike da kafar shi ta dama, ashe yabi ta wrong way ne, daidai lokacin an ba ababen hawa dake wajen hannu, ba tare da su duka sun kula ba wani mai mashin yabi ta kan kafar shi ya wuce…..! 1

              *********
Yaja numfashi a hankali bayan ya gama tunano abinda ya faru, kallonta yayi yana dan murmushi, “kawai ikon Allah da tsautsayi” ta girgiza kai, “to Allah ya kara kiyayewa” duk muka amsa da Ameeeen. Maigadi yayi sallama ya shigo dauke da manyan kuloli, Malam Bala ya biyo bayan shi rike da wasu, Anty Rahina ta umarce su dasu kai kan dinning su ajiye, suka ajiye suka juya. Ta kalli Abbu, “na dafo maka abinci daga gida, kana jin yunwa ne?” ya gyada kai, ta mike “bari in zubo maka toh” da sauri na mike ina kara rungume Baby Jameel a hannuna, “Anty bari in zubo mishi” tayi murmushi tace to shikenan. Ta koma ta zauna ni kuma na wuce kicin. Harira nata kokarin hada miya, nace “kiyi abincin kadan fa, Anty Rahina ta kawo abinci” tace to shikenan. Na kwashe plates da spoon da zasu isa na koma falo, na zubawa Abbu abincin na kai mishi kafin na koma na zubowa su Anty Ameenah, ni da yara kuma muka hau dinning. Anty Mubeenah ta fito daga dakinta, na kalli agogo. No wonder! Lokacin cin abinci yayi ai! Ganin su Anty Ameenah a falon sai data danyi turus! Kafin ta karasa, ta zauna akan kujerar dake kusa data Anty Ameenah tana dan murmushin yake, wai “su Yaya Ameenah ne? Ai ban san kuna gidan ba, ina daki ina ta barci” Anty Ameenah ta danyi murmushi, “Allah sarki! Muma mun zo duba mai jiki ne ai” tayi shiru kanta a kasa, Anty Rahina kam bata tanka ba Hankalinta na ga shayar da dan jariri. Ta gama kame-kame dai ta tashi tazo ta zuba abinci ta fara ci, Kai kawai nake girgizawa, rayuwar Auren bayin Allahn nan tana da matukar daure kai.  Ita ta fara tashi daga kan dinning din, sai dai wannan karon maimakon ta koma dakinta, kan daya daga cikin kujerun falon ta koma ta zauna. Muma muna gama cin abincin na kwashi kayan da muka bata na kai kicin na sake dawowa falon, Baby Jameel kamar yadda nake kiranshi tunda suka shigo na amsa daga hannun maman shi, yaron ya bude idanunshi farare tas Mashaa Allah dasu yana ta walainiya dasu a tsakiyar falon, Ji nake kamar in lashe shi saboda yadda yake burge ni. Na fara jujjuya shi ina jan kumatun shi ina mishi en wasanni kafin na fara manna mishi kisses a kumatu, Abbu ya maida kanshi jikin kujera ya kwantar idanunshi a lumshe; “What he’ll pay to become that baby!!”.Sai gab da Magriba su Anty Ameenah suka mana sallama zasu tafi, na leka dakin Anty Mubeenah wadda tunda aka kira sallar la’asar ta tashi da niyar zuwa tayi sallah bata dawo ba, na gaya mata zasu tafi ta leko suka yi sallama ta koma dakinta. Ni dasu Hafsy har Abbu mai kafa sai da muka taka musu har gaban motar da Anty Rahina tazo da ita. Anty Ameenah ta kalleni na goya baby Jameel a bayana yana ta shakar barci abin shi, tayi murmushi cike da tsokana tace “to Hajiya Nafee a bamu baby din koh?” na fara kokarin sauke yaron daga bayana, “Allah Anty ji nake kamar ku bar min shi!” su duka suka kwashe da dariya, Anty Raliya tace “kina son yara ne har haka?” nayi dan murmushi, “sosai ma! Amma mommy taki ta haifo mana wasu” na karasa ina pouting kamar inyi kuka dana tuno diramar da muke sha da ita idan ina mata maganar me yasa bata kara haihuwa daga kaina ba? Sai tace ai Allah ne bai kawo ba, ranar nan ma dana takura mata da tambaya zagi ta dankara min tace in cewa daddy na ya karo aure mana sai a Haifa min yaran, na tuna lokacin kuka na fashe dashi saboda zagin data min, shi kuwa daddy dariya ya dinga mana. Daga ranar ban kara mata korafi ba, sai dai in yiwa daddy. Su Anty Ameenah kam dariya suke min, sun fahimci tsantsan yarinta da sokancin da aka san Yaya irinmu nayi a tare dani. Anty Ameenah tace “Kar ki damu, in shaa Allah kema zaki haifi naki, kinga kin huta kenan koh?” na gyada kaina ina murmushi, “daddy ma haka yace ranar nan!” suka kara sakin dariya kafin suka shiga motar, na mikawa Anty Ameenah babyn tare da maida murfin motar na rufe mata tare da daga musu hannu, suka ja motar suka tafi. Na dan saci kallon Abbu kallona yake sosai with astonishment in his eyes, murmushi yake yi kamar kunnen shi zai zage, na samu kaina da tambayar dalilin sudden change dinshi curiously. Na kama hannun Hafsy muka koma cikin gida ya biyomu a baya. Muna gama dinner na musu sai da safe na koma dakina, sosai nake jina a gajiye ga wani barci daya rufe min idanu. 
+

Kwana uku muna jinyar Abbu ni da yaran shi, ba laifi ya warke duk da cewa bai fara fita ba, kuma har zuwa lokacin Tafiyar shi bata koma irin ta normal people ba. Cikin wannan lokacin mun ga jama’ah ba kadan ba, ko wace rana sai mun ga bakin fuska cikin masu zuwa duba shi gaskiya Abbu yana da jama’ah sosai. Saurayin Ni’ima zai kawo mata ziyara ranar alhamis, ranar a lab muka wuni tare dasu suna jira mu tashi su wuce gidan su dani, na gaya musu Abbu ya hana ni yawo amma ina! Suka ce they wouldn’t take no for an answer, dole suka saka ni kiran shi. Na fita daga cikin lab din bayan na danna mishi kira, bugawa daya biyu ya dauka ana uku, a sanyaye na gaida shi tare da tambayar jikinshi ya amsa da lafiya, nayi shiru ina kamo bakin zaren daga inda zan mishi maganar har sai daya tambaye ni ya? Sannan na gaya mishi kamar wadda take tsoron tayi maganar, shiru ya biyo baya kafin ajiyar numfashi mai nauyi, “amma kada ki wuce karfe bakwai baki dawo ba” da sauri nace “in shaa Allahu Abbu” daga nan muka yi sallama. Ranar tun kafin lokacin tashin mu yayi muka tafi. Unguwar Galadanchi muka nufa, ashe mahaifin su shi yake rike da sarautar Galadanchi ta garin Kano, babban gida ne wanda ginin shi na asalin gidajen sarauta ne, sashen Hajiya Fati muka fara shiga ita ce mace ta biyu a gidan, mace mai karimci ta tarbe mu da faraarta, na kula su Ni’ima kamar babbar Yaya suka dauketa don a sashenta ma suka ce zasu saukar da Bashir din. Cike da girmamawa na gaidata ta amsa da fara’ar ta tare da sawa aka kawo mana ruwa, mun dan jima a sashen nata kafin muka mata sallama muka wuce sashen Hajiya Siyama mahaifiyar su Abbu. Sashen nata in ka shiga baka taba cewa dakin er dattijuwa ka shiga duk da cewa shima sashen Hajiya Fati babu laifi. Babban falo ne wanda yasha saitin royal kujeru ruwan zuma, muka zube a kan wani tattausan carpet muna gaishe ta tana zaune akan sallaya tana lazumi, kana ganin kamilalliyar fuskarta zaka san cewa ka kalli fuskar ma’abociyar addini, babu abinda Abbu ya baro nata sai dogon siririn hancinshi, ita nata yana da dan fadi, sai data gama lazuminta kafin ta amsa mana cike da kulawa. Daga nan su Ni’ima suka jani muka je dakin su muka yi sallah, kayan jikina na canza muka shiga kicin muka fara shirya kayan abinci kala kala. Na bata shawarar mu yi snacks wanda zamu basu a matsayin tsaraba idan zasu tafi gobe, don haka muka yi doughnuts wanda muka yi icing dinshi muka watsa shredded cheese da chocolate akai. Karfe biyar suka karaso shi da abokin shi, mun riga mun kai komi sashen Hajiya Fati, mun shirya koina sai kamshi kawai dake tashi a wajen. Ita uwar gida ta musu rakiya zuwa inda aka tanadar musu mu kuma muka tsaya karasa gyara kicin din, sai da muka gama gyaran jikinmu sannan muka je muka gaisa dasu. Bashir din nata kamar yanda take fada dan kyakkyawa dashi ga barkwanci, abokin nashi ne ma bai mun ba ko kadan, sai wani shisshige min yake yi yana jana da hira duk ya takura min don haka na mike nace musu zan wuce gida, duk suka kalleni da mamaki ni kuwa Na Kauda kaina gefe don ma kar suga fuskar hana ni tafiya. Sa’adiya ta taso ta kama hannuna muka fita, abokin Bashir da naji yana kira da Fahad ya taso ya biyo mu, ganin babu fuska yasa ya juya. Na saki tsaki kasa kasa, Sa’adiya tayi dariya tace da alamun gayen bai miki ba, kai kawai na girgiza mata muka wuce sashen Hajiya Siyama. Tana kan daya daga cikin kujerun falon tana kallon tashar Saudi, ta kalle mu cike da mamaki, “lafiya dai ko?” Sa’adiya tace “wai gida tace zata wuce!” tace Haba ai kin tsaya kici abinci koh?” nace “Hajiya Abbu….” tayi saurin katse ni, “kyale shi kawai, ba zaki tafi ba sai kinci abinci fa” bani da zabi dole na wuce dakin su Ni’ima don bazan iya komawa wajen su nataccen abokin Bashir ba kuma bazan iya zama kusa da Hajiyar ba. +

Sai wajen karfe bakwai da rabi sannan muka fito ni da direban da xai maida ni gida, bayan naci tuwon tsakin masara da miyar kalkashi wadda taji yajin daddawa, tantakwashi da man shanu ga kunun aya mai sanyi da Gardi a gefe. Tare dasu Ni’ima muka ci abincin bayan Tafiyar su Bashir, ta bude tarkacen kayan tsarabar daya kawo mata ta ciro min kayan shafa, turare ne da kayan makulashe naki amsa, sai da suka yi kamar zasu yi fushi sannan na saka hannu na dauko turaren ‘splendid’ tsohon turarena ne tun a secondary school, daga baya ya bata na gaji da nema na komawa kamfanin lily cool, Sa’adiya ta kara min da tarkacen sweets muka fita falo. Kicin na shiga na dauko doughnuts din dana debar wa su Hafsy, Hajiya na falon a zaune na durkusa a kusa da ita na mata sallama, ta min godiya sosai har sai dana ji kamar in nutse a kasa. Ta mikawa Ni’ima wata karamar silver grey din jaka tace ta bani, na mata godiya sosai kafin muka tashi, sai da muka je ta sashen Hajiya Fati na mata sallama kafin muka fita waje inda direba yake jira na, na shiga motar muka kara yin sallama dasu kafin muka tafi. Nayi shiru a bayan mota ina tunanin abinda zan fadawa Abbu, a raina addua nake ina karawa akan kada Allah yasa yayi fushi dani, naki jinin fushin Abbu kamar yadda na tsani bacin ranshi. Har cikin gida direba ya shiga dani, na fito daga motar ina mishi godiya tare da sai da safe, iska ake yi sosai kamar ta dauki mutum tayi yawo dashi, idanuna a rufe saboda kasar da iskar guguwa ta watsa min na shiga falon bakina dauke da addu’ar da ake yi idan guguwa ta tashi, kamar hadin baki ina shiga aka dauke wuta. Na bude idanuna da kyar ina murza su, kafin inyi adjusting da dan guntun hasken falon wanda ya ratso ta cikin shara-sharan labulayen dakin daga farfajiyar gidan wanda lantarkin solar ta samo dashi, naji kafana tayi stepping akan wani abu mai tsananin sul6i, kafin in tantance meye naji ni na fara tafiya sululuuuu…..!! A tsakiyar dakin, na kwala ihu sosai ina salati tare da laluben abinda zan kama in rike tunanin farko daya fado min a cikin raina shine hango ni da nayi na kai da bakina, kyawawan kananun hakora na guda biyu na gaba malale a cikin jinin dake fita daga bakina……. Karo na kaiwa wasu hard muscled chest wadanda ko a cikin duniyar mafarkina ban taba hangoni a kansu ba, sai ga gangar jikina a jikinsu yau kamar a mafarki, dogayen tausasan hannuwa suka zagaye bayana, daya a kuguna daya a gadon bayana, jikina yake dauki rawa kamar wadda ta rungumi kankara cikin hunturun sanyi yayin da naji wasu dogayen zara-zaran yatsu suna suna tapping din gadon bayana a hankali., ban san lokacin dana saki ledojin hannuna, purse dina da wayata akan tiles din dake cikin falon ba…..!!.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]