[Advertisements⬇️]

AMININ MAHAIFINA CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

AMININ MAHAIFINA
CHAPTER 1


A nutse nayi sallama dakin Daddy na, dakin a shimfide yake da tattausan carpet sakar hannu kirar kasar India, ruwan hanta ne kamar yadda jeren kayan dakin suke. A hankali na zauna a kusa dashi ina kallon yadda yake sarrafa laptop dake hannunshi cikin kwarewa, ganin bashi da niyar dawo da hankalinshi gare ni, dama dai nasan halin baba in dai yana aiki baya maida hankalinshi ga kowa har ni er gaban goshin shi kuwa har sai ya gama. Remote na dauka na canza channel daga sports zuwa Zee World. Na ma manta ranar suna shirin da nake nacin kallo, Love Look Like What You Made Me Do. Dan Murmushi nayi nace woah, ni na ma manta da shirin nan. Daddy ya dan yi glancing din wajen da nake zaune ya kafin ya maida hankalinshi ga laptop dinshi. A takaice har aka gama shirin suka fara tallace-tallace Daddy bai gama abinda yake yi ba. Ba a jima ba naji na fara hamma, remote na dauka na mayar mishi da tashar da yake kallo na mike, daidai lokacin daya rufe laptop din nashi ya kalle ni cike da kulawa. “Uwata, ya aka yi ne?” sunan mahaifiyar shi gare ni shi yasa yake kirana da Uwata, su Mommy kam Ummi suke ce min. Baki na turo cikin dan jin haushi nace “ni barci nake ji….. Sai da safe!” er dariya yayi ya kamo hannuna ya rike ya janyo ni na koma kusa dashi na zauna ina kara tura baki na. Kumatu na ya dan ja, “ohhh m soooo sorry princess, na tsaida ki koh? Akwai muhimman bayanai dana tura ne yanzun shi yasa, ayi hakuri. Gobe zamu je mu sha ice cream ni da princess dina, are we good now?” kaina na kawar daga kallonshi, yasa hannu ya juyo da fuskata zuwa gare shi, “hey, m trying to pay for what I did, aren’t we good yet?” bansan lokacin dana yi er dariya ba ganin yadda yayi da fuskarshi, Ina son babana fiye da tunaninku saboda yana sona sosai, kaunar da yake min ko mahaifiyar data haife ni bata nuna min kwatankwacinta. Ban sani ba ko don hakan yana da nasaba da cewa ni Kadai ce diyar su??. Kai na girgiza ina dan murmushi, “naji na hakura, but we will also go for shopping, agree??” ya gyada kai, yes. Tashi tsaye nayi nace to sai da safe Daddy murmushi yayi, ki tashi lafiya Uwata.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


A main parlour naci karo da Mummy, da alamun turaka zata tafi ganin yadda taci kwalliya, ba wai ta fuska ba, ta jiki sai tashin kamshi take. Murmushi nayi naje na rungumeta, “Mommy sai da safe!” bayana ta dan shafa, “OK, sweet dreams baby” ta sake ni ni na wuce dakina ita kuma ta tsaya tana kashe wutar falon.
Ina shiga dakina wuta na kunna na shiga zare kayan jikina daya bayan daya, towel na zara na daura a jikina na fada toilet din dake manne a dakina. Cikin bathtub na shiga na zauna bayan na tara ruwa mai dumi, ban jima a ciki ba na fito. A cikin toilet nayi shafe shafen da zanyi, na fito. Kayan barci na saka marasa nauyi, kayan dana bari a tsakar daki na tsince na watsa cikin kwandon da nake tara kayan datti don nasan idan na bari Mommy ta gani gobe sai raina ya baci. Mommy mace ce mai tsabta da bata jurar kazanta ko ta anini. Kan katoton gadona nayi tsalle na haye kamar wata karamar yarinya, wayana na cire daga jikin socket na kunna data, social media na shiga na fara chat da friends dina. Ban samu barci ya dauke ni ba sai wajen karfe goma sha biyu na dare. Ban jima da fara barci ba naji numfashi ya fara min wahalar shaka, rigar jikina na fara adjusting daga jikina, ji nake kamar ita ta shake min wuya na kasa numfashi. Daga karshe tashi nayi gabadaya na cire rigar na jefar kasan gado na koma na kwanta. Dama don dole nake saka riga idan zan kwanta saboda fadan Mommy, ban cika kwanciya da riga a jikina ba saboda a yawancin lokuta na kan ji kamar rigar na shake ni ne, ban sani ba hakan sabo ne ko kuwa hali ne ko cuta? Ban sani ba, n I don’t give a damn akan lallai sai na sani. +

*☆☆☆☆☆*

Kiran sallar asubahi a cikin kunnena da yake masallacin unguwar mu a jikin gidanmu yake. Na saki gurnani a hankali saboda barcin daya cika min ido, da kyar na samu na iya bude idanuna suna komawa suna rufewa, na dauki kusan mintuna biyar kafin na iya tashi zaune, gashin kaina daya tattare ya barbaje min a fuska na tattara na maida shi baya, a hankali iska ya shiga kada sassan jikina hakan ya ankarar dani yanayin da nake ciki na babu riga, da sauri na dira daga kan gadon na dauki rigata na saka. Daidai lokacin Mommy ta leko, ganina a tsaye yasa ta maida kofar ta rufe ba tare da ta min magana ba. Sighing na danyi softly cike da jindadin bata kama ni ba. Bandaki na fada direct na dauro alwala, nazo nayi sallah na zauna Ina lazumi har sai da gari ya danyi haske, tashi nayi na fita daga dakina. Sai dana je na gaida Daddy sannan na shiga kicin inda na samu Mommy da Mama Sauda wadda take taya ta en aikace-aikace suna ta kokarin hada break fast, a nutse na gaida su sannan nima naje na kama musu.
Muna gamawa na koma daki nayi wanka na fito, na bata lokacina sosai wajen fente fuskata da nau’in kayan kwalliya Kala-kala kamar wadda zata je biki. Sai dana gamsu da kwalliyar fuskata sannan na tashi na bude wardrobe dina wadda take shake da kaya kamar na mutane biyar ko fi. A hankali nake kare musu kallo har idanuna ya sauka akan wata atamfa cote d’voire ruwan coffee wadda aka mata zane da peach da yellow a jiki, dinkin riga da siket ne. Siket din pencil ne sai rigar doguwa don ta kusa kai kin gwiwa, ita kuma dinkin ya kama ni cif daga kirjina, daga uku ne ya saki sosai yayi baza. Ina gama saka kayan nayi simple daurin dan kwali, na dauko gyale mai dan fadi peach color da er karamar jakar vincci na rataya na fita bayan na dauki wayar hannuna da takalmi coffee color mai dan tudu. Akan dinning na samu Mommy da daddy har sun fara karyawa, duka kallona suka yi ganin yadda naci kwalliya cike da alamun tambaya. Kujera naja na zauna a kusa da daddy ina kallonsu, “School zan shiga in amso IT letter na daddy” daddy ya gyada kai yaci gaba da cin kosan shi yana korawa da kunun gyada mai gardi, nima kunun gyadar na tsiyaya a cup na bude nadarar peak na kara a ciki na fara sha. A nutse muka gama cin abincin, na tashi na dauki jakata tare da yafa gyalena Ina kallonsu, “Mom, Dad, zan wuce sai na dawo” mom tace Allah ya kiyaye, daddy yace “ko dai in sa driver ya kaiki tunda ba jimawa zaki yi ba?” kai na girgiza, noo daddy, zan bi bus kawai. Ya gyada kai, “kudi pa?” nan ma kai na girgiza, “I’ve enough money wit me daddy” nan ma kai ya gyada, “OK, take care baby” Murmushi nayi na juya na fita cike da jindadin yadda iyayena suke kulawa dani, ta kowane fanni ni kam sai dai in godewa Allah daya bani iyaye kamar su.
Bus na hau directly har kofar gate din KadPoly inda anan nake karatun Diploma na akan Science Lab Tech. Kasancewar an tafi hutu makarantar babu mutane sai tsilli-tsillin wadanda basu tafi hutu ba kawai, a hankali nake takawa har cikin ofishin IT coordinator namu na karbi IT letter na na fita. Hostel din mata na wuce daga can dakin kawata Ramla don nasan bata tafi hutu ba, ila kuwa, Ina sallama cikin dakinsu muka ci karo da juna. Cike da doki muka rungumi juna muna juyi a tsakar dakin kafin daga karshe muka dire a Kan gadonta muna dariya. Kallona tayi tun daga sama har kasa har sama, ta gyada kai tana er dariya, “inye diyar daddynta! Wannan fresh haka kamar wadda aka wanke da inji?” duka na kai mata a cinya Ina dariya, “ke ba baki da mutunci Ramla, duk uban kashin wannan dana tara a wuya zaki ce wai nayi fresh?” sai da muka gama shakiyancinmu na abokai sannan na kalleta, “ke ni ba wannan ba, ya zancen inda zamu je muyi IT ne don ban karbi letter na da wuri ba ban sani ba cikin wajajen da suka bamu ko zan samu?” Ta girgiza kai, “duk an cika a wajen pa gaskiya babu, nima tun last week na kai nawa suka ce wae an cika” fuskata ta dan yamutse, “lallai! Ya zanyi kenan?” kafada ta daga, “oho! Bake wae dadi gida ba kinje kin zauna kina hutu ba? Gashi next week zamu fara. Ni a Kano zanyi nawa” na kalleta “Kano? A Ina??” “cikin BUK, kin san Aunty Habi tana aiki da Lab dinsu, shine tace in je can inyi kawai. Har an kai letter sunyi accepting. Abinda ya shigo dani makarantar kenan na kawo accepting letter din” shiru nayi ina jijjiga kai, “Ramla ko dai nima can zanje inyi nawa IT din kawai? Nasan mawuyaci ne in samu waje anan” ta kalleni, “wa kike dashi a Kano?” nace oho! Daddy yana da mutane da dama acan, nasan ba za a rasa ba. Idan can dinne sai in dinga zuwa weekend gida….. Zan tambayi daddy inji dai tukun. Yaushe zaki tafi Kanon?” “ranar assabar kila” ta bani amsa. Na gyada kai kawai. Kayanta na tayata hadawa, tare muka fito da ita na janyo mata trolley ita kuma tana jan karamar jaka. Muna tafe muna hira da ita har bakin gate, anan muka ci karo dashi, My Crush!. Wata irin farinciki da murna suka rufe ni, Ya Allah ji nayi kamar in daka tsalle. Ta gaban mu ya wuce without glancing at us, duk yadda naso in daure kasawa nayi, ban san lokacin dana kira shi ba. “Muneer!!” cikin wata iriyar murya mai kama da whisper, duk da haka sai daya dakata da tafiyar da yake yi ya juyo ya kalleni, Kai na sadda kasa ina jin wasu irin abubuwa na min yawo a jiki. Cikin siririyar muryar shi da zan iya cewa ita tafi daukar hankalina game dashi yace, “ohh Ummie, ya kike?” Murmushi na saki a hankali kaina a kasa, nace “lafiya qalau, ya karatu?” “Lau…” ya amsa, “….bari in wuce sai anjima….. By the way, I like ur dressing” bin shi nayi da kallo yana tafiya a nutse ina wani irin murmushi kamar kumatuna zasu hade da kunnuwana. Sai dana daina ganin kurar shi sannan na maida Kallona ga Ramlah wadda ta coge a gefe tana jifana da harara, murmushi kawai nayi tare da daga mata kafada naja trolley din nayi gaba. Tsaki taja ta biyo bayana, “wallah Tallahi Babe kina bashi haushi a rayuwa akan Muneer dinnan, kin rabe wa namiji yana yazga ki. Yanzu kaf fadin KadPoly waye bai san cewa kina crushing din wannan player din ba, abun haushi ma da alamun baya yi dake!” fuska na hade sosai. Abinda ke hada ni da ita kenan, kushe Muneer. Bata damu da yadda na hade fuska ba taci gaba, “haba babe, ki daina bayar damu mana. There r so many guys out there ciki da wajen makarantar nan dake karakaina akan ki, don Allah ki kyale wancan yaron. Ba son ki yake yi ba!” a fusace na kalleta, “yeah right! Ai dama ban ce miki yana so na ba koh? Hakan bai dame ni ba, inda rai da rabo, zan ci gaba da bibiyarshi kuma har sai ya so ni Ramlah! Idan hakan yana bata miki rai ki kauda idanun ki daga gare mu, dats all” Kallona ta tsaya tana yi kawai, ba wai yau muka saba irin wannan musun ba in dai akan Muneer ne, Kai ta girgiza a hankali tare da furta Allah ya ganar dake! Cikin gatse na amsa da Ameeen. Muka ci gaba da tafiya har bakin gate ba tare da kowa ya sake cewa komi ba, dama zuciya ce ta kowa a wuya, magana kadan sai ta tunzura mu. Muna fita bakin gate kowa yayi nashi bangaren, ita ta hau motar Abuja ni kuma na dau drop din tricycle har Unguwar Rimi. +

Lokacin dana isa gida karfe sha biyu na rana bata karasa ba, kayan jikina na cire na saka na shan iska marasa nauyi na tafi kicin. Tare da Mommy muka hada abincin rana, ta shiryawa daddy nashi a cikin wani katon Basket mai kyau har da wani kayata shi da roses. Wannan Al’adar tunda na tashi naga Mommy tana yin ta, Indai daddy yana gari to abincin shi daga gida ake kai mishi, ba zan boye ba, abin yana burge ni, ina da niyar yin wannan Al’adar idan nayi aure. Direba ta ba ya kai mishi ofishin kula da harkar shigi da ficin jirage ta jahar Kaduna inda anan ne yake aiki a matsayin
President na wajen. Ni kam sallah nayi sannan na fito dinning din, tuwon semovita ne muka yi da miyar danyen kubewa wadda ta sha busasshen kifi da tantakwashi da man shanu sai tashin kamshi take yi, sai zobo mai sanyi Shina anyi decorating dinshi da fruits. Muna hira da Mommy jefi jefi muna cin abincin na gaya mata yadda muka yi da Ramlah game da IT dina, shiru tayi tana Kallona kafin tace “zaki iya kuwa Ummi?” er dariya nayi, “haba Mom! It’s not like ban taba zaman Kanon nan bane. I will b fine, after all anan zan dinga yin weekend dina ai” kai ta gyada, “sai ki jira daddyn ki ya dawo”.

Koda na fadawa daddy abinda ake ciki ya dan nuna damuwarshi akan gida da zan bari, yace “Uwata tafiya zaki yi ki barmu mu biyu ne a cikin gidan nan kamar mayu?” ni kaina kuma sai a lokacin naji jikina ya fara sanyi, a sanyaye nace to daddy ko dai zan bari ne sai shekara mai zuwa sai inje? dariya suka saki shi da Mommy, daddy yace “oh ma silly princess! M not that wicked da zan hana ki karatun ki, bari in kira Dr. Ibrahim abokina ne, lecturing yake yi a BUK sai muji yadda za ayi” muna zaune ya kira shi suka gama magana suka yi sallama, “wai yace zaki samu sai dai a microbiology lab din su” Murmushi nayi, “daddy kasan fa dama nace maka idan na gama wannan program din zan nemi microbiology a ABU” yace faduwa tazo daidai da zama kenan? Na gyada kaina Ina Murmushi. Yace gobe zan tura mishi letter din sai a kai, Allah sarki princess dina zan yi kewar ki!.

Da dare kuwa kamar yadda daddy ya min alkawari muka fita, chicken republic muka je ya sai min gashin kaji muka tsaya a freeze center ya sai mana ice cream da tarkacen snacks muka koma gida. Tare muka zauna muka ci komi, sauran kayan mommy ta je ta adana su. Mun danyi hira dasu kadan har zuwa karfe tara da rabi, kafin na musu sallama na wuce dakina. Kayan barci nasa na kwanta a rub da ciki idanuna a rufe, daddy gaskiya ya fada. Tun yanzu nake ji kewar su tana dabaibaye ni, anya zan iya kuwa???!
Tun da muka gama hada breakfast na koma na kwanta barci, ban tashi ba sai wajen karfe goma na safe. Brush nayi na fita falo na karya, daddy ya fita wajen aiki. Dama dai Mommy full house wife ce, babu aikin da take yi. Shi yasa nace muku rayuwar auren iyayena tana matukar burge ni, Mommy tayi karatu har matakin masters akan Pharmacy amma daddy ya hanata aiki, duk wasu bukatu nata kuma ya dauke su ba kamar sauran mazajen yanzu ba da idan matarsu tayi karatu taki yin aiki sai labari yazo ya sha banban saboda ba zasu raba hidimomin gida tare ba. Wanka na shiga nayi, na fito na shirya cikin doguwar riga ta wani material grey mai dan nauyi, dinkin ya kamani tsam ya bi jikina, sai daga kasa ne ya baje sosai. Saboda yanayin kirar jikina dama ba wai kiba gare ni ba, er siririya ce ni amma fa Akwai kira, daga sama har kasa kam sai dai in gode Allah. Kalar fatar jikina baki ne, duk da ba wai can ba, zaku iya cewa chocolate color dai. Gyale na dauka na dora shi akan kafada ta na fita. Dakin mommy nayi knocking na shiga, tana zaune a gefen gado da dan littafin hisnul Muslim a hannunta. Kallona tayi na zauna a gefenta, a dan shagwabe nace “mommy dan Allah inje gidan Anty Uwani?” anty Uwani kanwar mommy ce, yaranta hudu duka maza, mun saba dasu sosai saboda zumuncin iyayenmu. Lokaci zuwa Lokaci na kan je can har in musu weekend. Mommy tace “kinga baki tambayi daddy dinki ba Ummie, babu ruwana pa!” kara shagwabe fuska nayi nayi nace “mommy da wuri pa zan dawo Allah” Kallona tayi na lokaci kafin ta gyada kai, “shikenan, but kar ki kai yamma fa!” cikin murna na gyada mata kai. Cike da doki na tashi, har na fita na sake komawa, purse dinta na bude na zari dubu biyar na fita da sauri ina dariya, kallo kawai ta bini dashi. A Unguwar Rimi suke zaune, sai dana tsaya na sai dangin fruits a bakin hanya sannan na karasa gidan. A can na wuni sur, sai gab da magrib sannan ta sa direba da danta na biyu AbdulJalal wanda yake kusan sa’ana ne suka rako ni gida. Daddy har ya dawo, Allah ya taimake ni ban sha fada ba saboda Daddy baya son yawo ko kadan. Bayan sallar isha’i ina zaune ina kallon film din Kaabil daga cikin laptop dina Ramla ta kira ni, murmushi nayi da naga sunanta a jikin wayata, wato har ta gama fushin kenan?? Da er dariya ta na daga kiran, “Lauratu ya ne?” haka nake kiranta idan naso tsokana. Ina jin dan siririn tsakin data saki, “ke pa u r a prof a ruining mood din mutum wallahi, meye wani Laure kamar wata Goggo a kauyen kayau?” dariya na sheke da ita cikin tura haushi, hakan ya kara tunzura ta kuwa. Sai da na gama tsokanarta sannan na tsaya ina sauraronta, hakuri ta bani game da abinda ya faru ranar, nima hakurin na bata tunda dukanmu we are at fault. Daga nan hira muka hau yi da ita, mun share fiye da awa daya muna hira har sai dana gaji don ni dama can ba gwanar hira bace musamman ma hirar waya, sallama muka yi kowa ya ajiye wayarsa. +

Da dare muna falon daddy mu duka muna en hirarraki, aka kira daddy a waya. En maganganu suka yi kafin ya ajiye wayar yana kallona, “Uwata kinji an karbi letter dinki pa!” ban san dalili ba,
gabana ya fadi ras! Rasa abin cewa nayi kawai na tsaya ina kallonshi, yaci gaba, “ranar Sunday zaki tafi mun gama magana da Ibrahim din. Sai ki fara shiri koh?” jikina naji yayi sanyi sosai, kafin kace me! Hawaye sun fara min yawo a kumatuna, cike da damuwa daddy yake kallona, “Uwata lafiya?” kai na gyada mishi a hankali, “I just started missing u ne daddy!” Dariya ya saki yayin da mommy tayi murmushi, hannu na ya rike a tausashe, “ohh my loving princess…. We gonna miss u!” group hug muka hada kamar zamu yi kuka.
+

Shirye-shiryen zuwa Kano na fara yi, hada tarkace, sallama da dangi da en abubuwa. Komi cikin sanyin jiki nake yin sa, wannan shine karo na farko da zanyi tafiya ta fiye da watanni uku. Daddy dinmu dan asalin garin Malumfashi ne ta Katsina, danginshi duk a Katsina suke zaune don haka mu kan je can idan mun samu hutu in musu kwanaki zuwa sati. Amma Ina jin wannan tafiyar ta banbanta, zuwa zanyi fa in zauna da mutanen da ban sani ba na tsayin watanni hudu zuwa biyar, a garin da ban sani ba duk da cewa mun yi zaman Kano na shekaru biyu, amma that was then, I think tun ina primary 5 ne??? Haka dai naci gaba da Shirye-shiryena har zuwa ranar Sunday. Sai wajen karfe biyar na yamma muka bar Kaduna, daddy ne ke jan motar, mommy na gefen shi ni kuma ina gidan baya. Tafiyar tayi min wani irin sauri, sai naga kamar muna tafiya ne akan iska ba kan kwalta ba. Cikin dan lokaci kankani mun isa Kano, unguwar Tal’udu muka wuce tunda anan gidan yake. Naji daddy yana ba Mommy labari game da abokin nashi, yace lecturing yake yi amma ba a staff quarters yake zaune ba, yace dan asalin garin Kano ne kuma yanzu haka yana neman kujerar dan Majalisa ne. Yaran shi uku da matar shi daya…, ni dai tunda naji yace yana harkokin siyasa na maida hankalina kan wayata, dan siyasa? Allah ya gani basu cika burge ni ba, ban son siyasa.
Kugi na karshe da motar tayi a cikin garejin gidan ne, tun daga cikin mota nake karewa gidan kallo. Ba wai yanke hukunci kai tsaye ba, yanayin gidan tafiy kafin ace mallakin just a lecturer (sorry lecturers, m not underestimating ur payment or something). Gida ne hawa daya, parking lots din gidan cike yake da manyan motoci ba na wasa ba, ga bikes da kekuna ina ji na yaran shine. Daga nan kana iya hango wani dan karamin garden a can gefen gidan, har wani dan karamin wajen wasanni na gani.
A hankali muka fito daga cikin motar, already wani da nafi kyautata zaton mai gadi ne ya fara kwasar kayana yana shiga cikin gidan dasu. Shi yayi mana jagora zuwa wani babban falo daya min kama da fadar uwargidan sarkin Kano, ya sha jere na wasu narka narkan leather seats kala biyu, farare da browns, ko wane jeren kaya yana da nashi dinning table, Plasma TV wadda zaka yi zaton zata cinye bangon falon saboda girmanta. Kafafunmu suka nutse cikin wani tattausan rug carpet kamar auduga, nayi iya bakin kokari na wajen ganin cewa ban hangame baki nayi kauyanci ba, maganar gaskiya ban taba shiga tsarraren falo irin wannan ba duk da cewa ba laifi nayi shige-shige a parlours da gidaje na manyan mutane, wannan kam looks extraordinary sosai. Kujera muka samu muka zaun 3 seats, ina tsakiyar su daddy, er aikin gidan ta fito daga kitchen ta gaida su daddy kafin ta shige wata kofa a cewarta zata kira madam. Ina jin lokacin da daddy yake gayawa Mommy ai Ibrahim din baya nan, yaje wani seminar. Ni dai ba baki, I was very
nervous a lokacin. Mintuna kamar goma sai gata ta fito, Ya Allahu!! Meye wannan a gabana? Naji zuciyata tana tambaya lokacin da nayi tozali da matar. Don fari fa Akwai fari kamar Baturiya, kyawu ma Akwai shi Masha Allah, wata irin kiba marar fasali ne da ita. Lokacin data zauna akan kujera suna gaisawa dasu daddy sai naga ta shirge a waje guda kamar kayan wanki. Da kyar na iya saisaita kaina na dan zame daga kan kujerar na gaisheta, da er fara’ar ta ta amsa har da ambatar sunana, “Safeenah ko?” na gyada mata kai a hankali. Ta maida kanta gasu daddy suna er hira, idanuna suka ci gaba da wandering a cikin falon bana ma jin me suke fada. Aka kira magrib daddy ya fita sallah, ni da Mommy kuma muka yi a cikin falo don bamu samu albarkacin samun gayyata zuwa dakin matar gidan ba, kuma ba a nuna min inda zan zauna ba, karewa kayana ma suna nan baje a tsakiyar falon. ‘yar aikin gidan muka tambaya ta nuna mana bayi dake nan cikin falon muka shiga muka dauro alwala, motar daddy naje na dauko prayer mat muka shimfida anan muka yi sallah abinmu. 7
Daddy yana dawowa daga sallah yace mommy ta tashi su tafi, nan fa idanuna ya raina fata da naga Mommy ta yiwa er aikin gidan magana akan taje ta gayawa matar gidan zasu tafi, idanuna suka yi raurau kafin kace me na fara hawaye shabe-shabe. Ba a dauki mintuna biyar ba sai gata ta fito tana taku da kyar, ban sani ba na takama ne ko kuwa dalilin kibar ta ne? Sallama suka yi dasu ta koma daki abunta. Hannuna mommy ta kama na musu rakiya har bakin motar su, zuwa lokacin kam kuka nake har da shessheka, suka saka ni a tsakiya suna lallashina har na samu kukan ya lafa. Ina nan tsaye suka shige mota suka ja suka tafi bayan na sha nasihohi daga gare su. Na bi bayan motar nasu da kallo har suka bar gidan aka maida gate aka rufe, na maida kallona ga dankareren gidan da zan rayu a ciki zuciyata cike da tarin damuwa iri-iri, daga can kasan zuciyata ina jin wata irin nadama na dabaibaye ni, Me ya kaini???? A hankali wasu siraran hawaye suka biyo kan Kumatu na…..!

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

2 thoughts on “AMININ MAHAIFINA CHAPTER 1”
  1. How could i extend the range on the Wireless N router? I have an Xtreme N handheld router (Dlink). I need to extend the reach from the wireless signal. I discover how to do it for a new G signal. I want to find out how to do them for an N sign. Is it possible make use of regular N routers when repeaters. If so, just how do i configure them. Thanks for the information.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]