[Advertisements⬇️]

ƁATACCEN YANAYI CHAPTER 6 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ƁATACCEN YANAYICHAPTER 6Throughout ranar Laylah ta rufe kan ta a cikin bedroom dinta ba abunda take in ba kallon palms in ta ba inda Abdulmalik ya rubuta number dinsa. Ba karya tana son sa amma tana gudun abun da zai biyo baya in ya gane koh ita wacece. Bata ganin zai yi accepting dinta a yadda take, bata so kuma ya fara tsanarta. Bata so kuma ta fara soyayya dashi daga baya su rabu dun tana gudun ya kawo maganar aure. Haka ranar ya gushe tana cikin daki tana ta tunanin, ta qulla wannan ta kunce wancan. A karshe ta miqe ta wuce wanka. Har saura kadan ta fara durzan hannu ta tuna da number din a haka ta koma bedroom ta dau karamin wayarta ta rubuta number din kan ta dawo ta fara wankan ta. 2

Abdulmalik shuru shuru yana ta jiran response daga Laylah amma yaji shuru. Da ka gansa ka ga wanda ke cikin damuwa. Ya rasa ya akayi son wannan Laylah ya mamaye zuciyar sa har yike ganin dole ya mallaketa. Har ya fara tunanin bata matsayin mahaifiyar Fadeel ta hanyar auran ta indai zata amince. Gashi dan nasa tun randa ya hadu da ita a park ya kasa daina hirar ta. Kullum Laylah this, Laylah that, in yana yi wayancewa kawai Abdulmalik yike kamar be san ta ba ya ta sauraron yaron.

Zaune yike a study room dinsa da laptop dinsa a kunne a gabansa. Yana cikin aiki ne amma ya fada nazari, tsananin tunani har Nawfal ya shigo ya zauna gaban sa for about 15 minutes be sani ba har sai da Nawfal din ya dan tabo sa.

“Wai tunanin me kake ne haka?”. 2

“When did you arrive?” Ya tambaya dan uwan nasa.

“Kusan 30 minutes fa amma baka ma sani ba hankalin ka na can kana ta tunani”. Ya fadi ya qure Abdulmalik da idanu sai kallon sa yike ta yi.

“Abdulmalik you love her”.

“It’s that obvious?”. Ya tambaya yana dariya “wallah Nawfal ban taba tunanin after Fati akwai macen da zata shiga zuciya na ba. Ji nike I can do anything to have Laylah”.

“A relationship based on lies? Abunda kake so kuyi kenan? Don’t you think it’s high time ta san koh kai wanene, it’s obvious ita ma neman ka take. Infact ba ita daya ba, Abdulmalik duniya ya kamata su san who the real khalifa Al-Haydar is. For how long?”.

Dogon numfashi Abdulmalik ya ja sannan ya sauke ijiyar zuciya kan ya kalli Nawfal “ka san meyasa nike boye identity na?”. Ya tambaye sa. Kai ya juya mai alamun aah be sani ba.

“Na dade ina tambayar ka ai”.
I have my own reasons for hiding it from you all, harta Begum bata sani ba”. Sai da ya dukar da kansa qasa kan kuma sauke ijiyar zuciya ya fara ba Nawfal labarin yadda aka yi. +

Let’s take a walk down to 8 years ago…….. on the night of 1st January.

A daren 1st January everywhere was blasting with celebration na shiga sabon shekara. Mohammed Mumtaz Al-Haydar yana cikin hotel room dinsa a babban hotel inda ya sauka a united Arab Emirates. Shiri yike dan zuwa wani new year dinner da wani business partner dinsa balarabe yayi organising. Masu aiki maza guda biyu ne a kansa wanda duk sanda zai yi tafia suna tare dashi. Daya na daure lace din takalmansa while daya yana daura mai tie. A haka Abdulmalik ya shigo da fara’ar sa ya izza Babansa.

“My king”. Mohammed ya fadi yana murmushi. Dama tun randa begum Sahar ta basa labarin daukar ciki ya fadi mata indai Allah ya basa yaro zaya basa suna Abdulmalik, his king, the king of khalif airlines and group of companies. In kuma mace ce she’ll be Malikah, his queen and the princess of khalif airlines and group of companies. Ita kuma begum Sahar ta fadi mai ta dade tana son sunan “Khalifatullah” dan haka in suka haifi dan su zata dinga kiransa da Khalifatullah.

“Har ka gama shiri?”. Ya tambaya dan nasa.

“Yes father. Mamu na jiranmu a qasa”. Ya fadi mai. Cikin hanzari Mohammed ya gama shiri ya riqe hannun dan sa suka sauka qasa inda Al-Mubaraq ke jiran su. Mohammed ya dau Al-Mubaraq tamkar qani, ba kowa bane ya san ba abunda ya hada su illa mutunci. Cikin fara’a Al-Mubaraq din ya gaida uban gidan sa da kuma dan sa sannan suka wuce.

A gun dinner din ne Mohammed Mumtaz Al-Haydar yayi making announcement cewar daga yanzu zai sauka daga kujerar CEO kuma insha Allah dan sa Abdulmalik khalifa Al-Haydar ne zai gaje sa, inda dan uwansa Ishaq wanda aka yi adopting dinsa tun suna yara ya nuna be yadda da decision din wan sa ba, ya zaa yi Abdulmalik ya zama magajin Mohammed bayan shi yana da rai . Washe gari da sassafe suka koma Nigeria a inda Mohammed Mumtaz Al-Haydar ya kuma qara kiran cabinets dinsa emergency meeting dan signing dim handing over documents din khalif airlines and group of companies to his son a nan ma Ishaq yazo rai a baci koh walwala babu. Ranar kowa ya halacci meeting din with the exception of Al-Mubaraq wanda shi dama an riga da an saba da fashin sa. Ganin babban matsayin sa a kampanin ya sa yike wasa da zuwa aiki duk yadda yaga dama. +

A gun meeting din ne Mohammed ya bada umarni da a basa ruwa saboda glass inda ke gabansa ba ruwa, ya shanye. Wata ýar waitress ta taho tana tafia tana yanga ta miqa mai wani glass din ruwa. Ya karba yana mata murmushi ya shanye ruwan. Shan ruwan ke da wuya aka ga ya fara cije cije ya sa hannayen sa biyu a chest dinsa. Kan ka ce mai ya zuba a qasa jini na zuba ta baki, ta hanci. Abdulmalik da ke kusa dashi ya ruga da gudu ya riqo babansa. Shikam Ishaq yana tsaye yana kallon wan sa nata aman jini. 1

“Go after that waitress! Now!”. Ya daka tsawa kan ya dau babansa aka ruga waje da shi da gudu. Koh da bodyguards din suka fita babu ita ba labarin sa. Nan aka wuce da Mohammed hospital inda aka ije sa a wani confidential room sannan aka hana a sanar da press dun baa son labarin ya isa jama’a. For 2 days aka hana kowa ganinsa sai rana na uku ya bada umarni akan a kira mai dan sa.

Abdulmalik na shiga ya kalli Babansa kawai hawaye suka kufce masa.

“Aah kai kuma, kada ka zama rago mana. Abunda mahaifiyar ka ta hane ka dashi tun kana yaro shine ka zo zaka yi dun bata kusa koh. Maza share hawayenka”. Ya fadi a hankula, muryar sa da kaji ka san yana cikin wani hali.

“Matso kusa”. Ya fadi yana nuna ma dan nasa gefen gado, yazo ya zauna. Yana zama mahaifin sa ya riqe masa hannu. “Take care of Sahar, she’ll be distraught at the news of my death”.

“Abba….,”. Abdulmalik ya kira sa yana kuka “please stop this, i’m trying to process your trip abroad”.

“Shhhhhh the poison has spread, it’s late. Mutuwa zanyi. Pray for me, that’s all I need right now”.

“Lokacina yazo Abdul. But before I go you should
know this; kasan mutanen da zaka yi harka da, ba kowa da ke dariya da kai ne ya zama masoyin ka ba. Ba abunda dan Adam bazai yi ha dun dukiya. An kawar dani ne saboda handing over in business da nayi into your name, and I bet you’re the next target, dole ka kula. Don’t let the Al-Haydar empire fall into the wrong hands. Kaga 40 years ago, mahaifi na na a ranar da yayi handing over group of companies dinnan to my name, a ranar aka yi assassinating dinsa and yanzu gashi nima haka. Dan Allah ka kula, mahaifiyar ka ka kula da ita. Ba sai ta san abunda na fadi maka ba..,., she’ll worry unnecessarily. “. Ya tsaya tari ya riqe sa. +

“Khalifa Al-Haydar should be…..a….a…. mys…..mystery t… to the world. Kada kayi trusting mutane blindly, kaga kawun ka kiri kiri ya nuna disapproval akan handing over the position of CEO to your name, na gida ma kenan suna ma bakin ciki. I know who is responsible for this, na san wake son kashe ni, kuma na san kanka zai dawo, plea….se son ka kula”. Ya kuma tsayawa tari. Abdulmalik kam sai kuka yike yana mai sannu yana tambayar sa sunan wanda ya mai wannan muguntar amma inaaa har rai yayi halin sa. Sai doctors kawai suka shigo suna basa haquri. Shi dai a ransa yana kyautata zaton adoptive brother din babansa ne zai aika ta wannan mummunar aikin tunda dama tun asali kawu Ishaq ya kasance mutum mara imanin a tsoron Allah.

Back to present……

“Tun daga ranar na fara boye identity na, na rage yarda da mutane, and tun daga ranar 8 years ago na fara undercover research a kan wanda ya kashe Abba. I’m close to getting the culprit kuma ina kyautata zaton shi koh su ke satan funds din company”. Ya fadi wa Nawfal lokacin idanunsa sun rikida sun koma jazur.

“Bu….but aka ce uncle died of a heart attack”.

“Abunda nace wa doctors su sa a death certificate dinsa kenan amma Mohammed Mumtaz Al-Haydar was poisoned to death. His death was planned most definitely by his brother, brother inda ya dauka ya maida shi mutum”. Nawfal ya shiga tashin hankali, mutuwar uncle dinsa, wan mahaifiyar sa sai ya dawo mai tamkar sabo. Tun yana yaro ya shaqu da kawun nasa wanda shi ya tsaya masu matsayin mahaifi lokacin da nasu mahaifin ya mutu suna yara. Bayan rusuwan mahaifin su da shekara biyu mahaifiyar nasu ta kwanta barci bata kuma tashi ba. Tun lokacin iyayen khalifa suka zama musu iyaye, Begum ta riqe su tsakanin ta da Allah da zuciya daya. Shi da kannensa mata guda 3.

“Yanzu what’s the next step?”. Ya tambayi Abdulmalik.

“Very soon, the world will get to know the true khalif Al-Haydar, for now dan Allah ka cigaba da misleading mutane”. Ya roqi dan uwan nasa. Nawfal be ce komi ba ya ja khalifa jikinsa yayi hugging dinsa.

“Koh rai na kace na cire na baka wallahi khalifa i’ll gladly give it to you. Halaccin da kuka mun da kai da iyayenka bazan taba mance wa ba”. Ya fadi yana kuka.

“Ya isa kan Begum tazo ta ganmu hankalinta ya tashi”.

Murmushi yayi ya share hawayensa. “Toh Laylah fa?”.

“Ita ma very soon zata gamu da Khalifa Al-Haydar inda ta dade tana nema”. Ya fadi yana wata ýar dariya “send an invite over to her, a private invitation. Sannan ka bada umarni a gyara the most expensive suite a Khalif empire for the meeting”.


“Man! What are you planning?”. Ya tambaya.

“It’s confidential. Wannan meeting din shi zai determining future dinmu, if I have a future with her or not. It means a lot to me”.

Ita kam Laylah tsawon kwana uku ba abunda take yi in ba tunani ba har dai finally tayi making up mind dinta. Waya ta dauko ta tura mai text.

*I finally have an answer, let’s have dinner together. It’s on me*. Ta tura.

Sai da ta jira reply dinsa kan ta tashi ta fada bandaki domin fara shiri.
Abdulmalik ya riga ta isa restaurant din dun haka ya zauna shuru yana ta danne danne a wayar sa har ta iso. Kanshin turaren ta kawai ya isa ya sanar dashi da isowar ta. Dago kai yayi ya Kalle ta yana murmushi. +

“It’s safe to call you babe, isn’t it?”

“Not so fast mister”. Ta fadi tana dariya.

Zama tayi suka gaisa kan waiter yazo da menu suka yi selecting abunda zasu ci. Har suka kusa gama cin abinci bata dago zancen ba shikuma Abdulmalik duk he’s restless, ya qosa yaji response dinta.

“Sooo….”. Ya buda baki ya fara magana. Kallon shi kawai tayi ta dan yi murmushi. Abdulmalik akwai rashin haquri, tunda ta iso ta lura da cewa ya qagu yaji answer dinta.

“In tambaye ka mana”.

“Allah sa ina da ansar tambayar ki”.

“Wani irin so kake mun?”. Sai dai Abdulmalik ya dau lokacin sosai yana wasa da juice inda ke gabansa, yana ta juya juice din da straw inda ke ciki. “So na tsakani da Allah”.

“Hmmmmm Laylah how do I explain how I feel to you? Without you my heart is always anxious. A da nayi tunanin after loosing my wife bazan taba son wata ýa mace ba a duniya not until I met you, komi ya sanja. Na rasa yadda nike jin ki a zuciya na”. Sai da ya tsaya ya dan jan numfashi kan ya cigaba.

“I’m not saying all these to deceive you, koh kadan ban zo da yaudara ba. Subconsciously, my heart chose the path that leads to your heart, nayi nayi na danne zuciya na, nayi suppressing feeling din but i’m only human, I can only fight against destiny but never can I change it. Abu daya nike nema a wajen ki; amincewar ki, ni dai talaka ne, i’m not rich but I promise to treat you like a queen, sai kin zama abun kishi a cikin mata ýan uwan ki, under the sun I promise to be your shade, in the rain i’ll be your umbrella, i’ll be your best friend, your support system. I’ll be your soldier and fight all your battles, i’ll be a shoulder you can always lean on, duk madubin da ba fuskar ki ban kallo, duk abunda baki so bani so, duk wanda ya bata miki rai sai ya hadu da fushi na, ke kadai zaki zama tauraruwar da ke haskaka rayuwata and i promise the next lady i’ll love this way will be our daughter insha Allah……”. Be yi niyyar tsayawa amma hawayen da yaga tana zubdawa ya sa dole ya tsaya. Rarrashin ta ya fara tare da miqa mata hankie. 1

“Did I say something wrong?” Ya tambaya “I’m sorry…..”.

“Shhhh”. Ta sa hannu a baki “You talk alot”. Ta saki ýar murmushi idanunta cike da kwalla. 1

“It feels so good….. The feeling of being loved. Na mance when last nayi feeling that way”. Ta fadi mai tana goge hawayen da ke zuba a kan kumatunta. “I love you Abdulmalik, right from day one. Ban damu da class dinka ba, ban damu da rashin dukiyar ka ba, duk ba wannan bane a gabana amma sai dai I don’t see a future for us. Bana tunanin zaka iya zama dani, bana taba tunanin zan taba samun acceptance from you after knowing my true colours. And it’s a shame i’ll lose the love and companionship of someone like you amma wallahi ka san cewa ba dun baka da kudi bane nake qin ka. Har ga Allah ina son ka amma…..”. Bata kai da
gamawa ba ta kuma fashewa da kuka. Be ce mata komi ba yayi shuru yana kallon ta kawai. Sai bayan kamar 10 minutes ya buda baki ya mata magana. +

“What if I’m ready to accept you the way you are? Zaki yarda dani? Nifa Allah ban zo da wasa ba, so na gaske nike miki. Kinga dai ni ba yaro bane, bazan yaudare ki ba”.

Murmushin takaici ta saki kan ta basa ansa “Abdulmalik kenan, I doubt you’ll accept me after hearing everything”.

“How about you try me. Wallahi I won’t judge”. Sai da tayi dogon nazari kan ta basa reply.

STORY CONTINUES BELOW

“Shikenan, how about we meet this weekend. I promise zan fada maka komi, koh karya daya bazan sako a ciki ba. In kaji komi then you decide if you still love and will accept me me for who I am”. A haka suka rabu. Sai da ya tabbata ta daina kuka kan ya rakata inda tayi parking mota ta shiga. Tayi tayi ta rage mai hanya amma ya qi.

“Shikenan sai da safe”. Ta fadi da dan murmushin ta sannan ta shiga mota.

“Laylah”. Ya kira sunanta kan ta rufa qofa.

“Yes?”.

“Take care”. Murmushi kawai tayi tace mai “you too”. Zuciyar ta na saqe saqe iri iri ta tuqa mota har gida.

Tana shiga taji gidan da dan hayaniya tana ta mamakin baqin daren da suka yi kawai sai taji an fado jikinta.

“Auntie! Auntie”.

“Hey young lad! You’re all grown up”. Ta fadi tana wa dan yaron wasa da gashin kansa. Reyhaan ne jikan Yasmeenah. “When did you arrive? Where’s your mommy and Amaan?”. Ta fadi tana riqe da dan yaron dan shekara takwas a kafadar ta.

Da hanzari ta qarasa ciki tana kwala ihu “leeeeeeeeek”. Tayi ta kira da karfi. Tana hango ta ta fada jikinta tana kukan murna. Ta dade bata gan ýar uwan ta ta ba wadda ta zama tamkar babbar yaya gare ta. “Shine baki fadi mun zaku zo ba, where’s my new niece?”. Ta tambaya referring to baby inda leek ta haifa wata uku da suka gushe.

“I wanted to surprise you. Sorry”. Leek ta fadi tana riqe da kunnuwanta.

“Yara na sun girma”. Ta fadi tana kissing din Amaan kanin Reyhaan, wanda daga shi sai baby inda aka haifa. Murna ranar a gun Laylah da Yasmeenah baya misaltuwa. A cikin wannan murnar ne kuma sai ga me gadi ya shigo wai wani yazo neman Laylah.

“Ka shigo da shi waiting room”. Ta fadi wa me gadin kan ta wuce dakin ta ta samo dan veil ta rufe kanta ta fito waje. Koh da ta isa waiting room din sai ta sama wannan mutumin ne da yazo ya dauki Fadeel the other day a park. Nan da nan ta ganesa, suka gaisa fuskar ta a sake kan tayi wa masu aiki umarni da a kawo mai refreshments.

“Lafia kuwa da dare haka. Ya aka yi ma ka gane gidan”.

“I must say the Al-Haydar’s are well connected”. Ya fadi yana murmushi. Ita ma murmushin tayi bata ce komi ba tana mamakin ziyarar sa. Sai da ya dan zauna kan ya miqe ya bata wani dan invite.

“This is a personal invite from khalifa Al-Haydar”. Ya fadi “He wants to show his appreciation on behalf of our young master”. Ya fadi mata. Ita dai ji kawai tayi kamar a mafarki wai abun da ta dade tana nema yazo har gida cikin sauki ya same ta. Kwalban wine ya miqa mata sannan yayi mata sallama ya wuce. Yana Wucewa ta buda dan envelope inda invite in ke ciki. Card din farko ta fara dubawa…..

*Trade at Al-Haydar empire. Friday night, 8:00Pm sharp💋*
Second card din kuma kamar pass ne wanda a jikinsa akwai secret code da ba kowa ya sani ba. Fadawa tayi cikin lush leather seat inda ke waiting room din. Mutuwar zaune tayi dan jin kanta take kamar a dream. Har tsawon 20 minutes ta kasa komi sai da Yasmeenah taji shuru ta biyo ta. Koh da Yasmeenah ta shigo ta izza ta ansan envelope din kawai tayi ta duba abunda ke ciki ta sa ihu.

“Yarinya me goshi”. Ta fadi tana guda “In my 35 years of being in this business ban taba ganin yarinya me farin jini irin naki ba”. Ta fadi tana ta murna.

“Ai sai mu shiga ciki in fara shirya diyata, Khalifa Al-Haydar ya wuci wasan yara”.

“It’s such a pity mother”. Suka jiyo muryar leek “Tunda nayi hankali ba randa bana addua Allah ya kubutar daku daga wannan hanyar da kuka zabawar kanku amma a ina. Jibi yadda kike murna dan anyi mata tayin sayan jikinta”. Ta fadi cikin hawaye. 1

“And you little sister….. is this the path you’ll tread on forever? Yaushe zaki gane wannan rayuwar bata kamace ki ba”. Ta fadi sautin kukan ta na qaruwa. “Bazan iya zama da ýaýana a nan ba. My mistake for coming home, ina tunanin koh in kika ga jikokin ki zaki yi hankali amma inaa old habits never die…”.

“Kullum mamakin ki nike Yasmeenah, ni meyasa baki sa ni a wannan sana’ar ba? Amma kike sa yaran wasu?”. 1

“Big sister….”. Laylah ta buda baki tayi magana amma ta kasa.

“Zan bar gidan nan, this night itself and wallahi bani kuma dawowa sai randa kika shirya barin sana’ar nan kuma kika kaini gidan ubana. Kin ce ba ta hanyar banza kika haife ni ba amma ubana fa? Meyasa ba zaa nuna mun shi ba? Meyasa koh sunansa ba zaa fadi mun ba?”. Suna ji suna gani leek ta ja ýaýanta wanda har sun fara barci suka wuce. Yasmeenah kam jiki a sanyaye ta wuce dakin ta, ita ma Laylah ta wuce nata dakin. Daren ranar kasa barci tayi. 1

Shikam Abdulmalik tunda ya koma gida yike ta tunani, duk ya ji ya kasa barci dun haka ya dauko waya yayi dialling number din Laylah. Lokacin ita kuma har barci ya dan fara gaba da ita.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]


“Hello” ta ansa wayar in a groggy voice.

“Na tashe ki koh?”. Murmushi kawai tayi wanda ya yasa zuciyar sa jin wani sanyi. “I just wanted to hear your voice, now I can rest in peace”. Ya fadi.

“Sleep well”. Ta ce mai.

“You too…. I love you”. Ya fadi ya kuma ji ta saki wani murmushi. Shima murmushin yayi kan ya ije wayar.

Ita kam Yasmeenah tun daren ran lahadi da diyarta ta fadi mata maganganu ta bar gida bata kuma fita daga dakin ta ba. Ba karya maganar ya sosa mata zuciya, ya kuma fama mata tsohon miki wanda ta dade da tunanin koh ya warke. In banda kuka da tunani ba abunda take yi. Da kyar Laylah ta iya samu ta rarrashe ta after 3 days.

“She hates me koh?”. Yasmeenah ta tambaya Laylah tana kuka a jikinta.

“No! I’ve never witnessed a mother-daughter bond like that of you guys. It’s natural for her to act that way”. Laylah tayi ta rarrashin ta. “Amma Yasmeenah I also think it’s high time ki ansa mata tambayoyin ta. Allah na tuba baa san gawar fari ba…..”. Bata gama magana ba ta miqe zata fita daga dakin. Har ta kai kofa ta juyo ta kira sunan Yasmeenah.

“Yasmeenah”.

“Yes love”.

“Al-Haydar will be my last operation. I think it’s high time for change”. Ta fadi a hankula sannan ta juya ta wuce.

Laylah na fita ta kira leek tace mata dan Allah su hadu a wani park kusa da hotel inda tayi lodging. Suna haduwa Laylah ta fada jikinta tana kuka tana bata haquri da cewar dan Allah su sasanta da Yasmeenah dan tana cikin wani hali. Ta kuma fadi mata duk abunda ke tsakaninta da Abdulmalik da kuma decision dinta na barin prostitution. Leek tayi murna kwarai sannan ta ba Laylah karfin guiwar fadi wa Abdulmalik labarin ta, tsakaninta da Allah banda karya.

A haka har ranar friday ya iso, ba randa Abdulmalik baya kira dun yaji muryar ta kawai, ranar da Laylah zata hadu da Khalifa Al-Haydar sannan kuma ranar ta na karshe a karuwanci. Tunda ta tashi da safe ta shige wani dan daki inda ta dau wani Ghana must go ta buda. Riga ce da zani duk sun kode har sun fara hujewa dun tsanani
ijiya, da wani dan dankwali irin na fulani. Kallon kayan tayi ta dauka ta sa a jikinta sannan ta zo ta qura wa mirror kallo. Rayurwata a da kawai ta fara tunowa tana kuka sosai. Yanzu koh duniya zata nade bazata iya komawa yadda take da ba, the innocent and naive ýar Baba.
A haka barci ya kwashe Laylah. Jin shuru ya sa Yasmeenah bin sahun ta, ta san a duk lokacin da Laylah ke da meeting da client tana zuwa gun ta shiri amma kuma sai wannan karan taga sabanin haka so sai kawai ta bi. Tana isa ta izza Laylah ta ci kuka har barci ya kwashe ta a qasa.
+

“Hey baby, wake up. It’s past 3 already”. Ta fadi tana shafa mata lallausar gashin ta. A hankula Laylah ta buda ido ta dan wa Yasmeenah murmushi. Ce mata taje tayi sallah Yasmeenah tayi sannan in ta gama ta same ta a dakin ta. Hakan aka yi. Tana idda sallah ta wuce daki ta sama Yasmeenah na ta hada ruwan wanka. Dago kai tayi ta ga Laylah ta zauna shuru ta qura wa hotunan da ke bangon dakin kallo, hotunan Yasmeenah ne da leek, tun tana karama har zuwa girman ta. Wani hoton kuma na leek ne da yaran ta. Murmushi Yasmeenah tayi kan tayi magana

“Special gyara zan miki yau, irin namu na ýan Borno”. (Shout out all my Borno folks🙌🙌). 3

Dariya kawai Laylah tayi bata ce komi ba, hankalinta na kan hotunan. “Yasmeenah”. Ta kirata a hankula.

“Yes love”.

“I’ve known you for about 10 years now, amma koh so daya ban taba jin kin ambaci gida ba. You hardly talk about your relatives, all I know is ke shuwa ce from Borno nothing more, nothing…….”.

Bata gama magana ba Yasmeenah ta katse ta “Time for your bath, the water’s ready”. Ta fadi tana jan hanci alaman tana riqe hawaye. Laylah bata kuma pressing issue dinba ta tube shuru ta shiga qaton bathroom din ta zauna cikin bathtub wanda cike yike da ruwan turaren which was made out of sandalwood da jasmine flower. A haka ta zauna shuru ba mai cewa kowa komi, Yasmeenah ta dauko wani scented shampoo din ta wanke mata kai kan ta fito after spending about 30 minutes a bathtub din. Towel ta daura sannan ta daura wani karami a ka sannan ta fito ta zauna shuru a bakin gado. Yasmeenah ta fito ta kawo mata turaruka wanda zata bi jikinta dasu, dakin duk ya dau kanshi. Sai da ta gama shafa jiki kan ta koma vanity table, Yasmeenah ta zo da hair dryer zata busar da gashin ta.
+

“I’ve never come across a lady as pretty and graceful as you are”. Yasmeenah ta fadi a hankula.

“Come on, duk da tsufar ki kin fa fi ni kyau. Kinga yadda maza ke kallon ki in muka fita kuwa”. Laylah ta ansa ta.

Sai da tayi dariya sosai kan ta buda baki tayi magana “I’m made for just one man”. Ta fadi kan ta tsaya ta goge hawaye. “Dazu you were asking about relatives, ina da ýan uwa amma almost 40 years kenan rabona dasu, rabona da gida since I was 15”. Ta fadi wa Laylah wadda ta zare ido cike da mamaki.

“Baki taba missing dinsu ba?”.

“I have, always. Da su nike kwana ba tashi a raina”. Shuru Laylah tayi cike da mamaki, Tabbas Yasmeenah ta dade tana kunshe da bakin ciki a ran ta wanda ta qi fitowa ta fadi wa kowa. Duk kusancin ta da Laylah ba sa ta taba opening up to her ba.

“As for Leek….. I swear Laylah she has a father. Me rufin asiri, dan gidan kirki”. Ta fadi mata.

“Toh ki fadi mata shi mana”.

“Ban san Inda zan nemo shi ba Laylah, be taba damuwa da mu ba. Ban tunanin zai iya tunawa da ni bare wata diyar sa”. Ta fadi hawaye suka kufce mata.
Ba so na yike ba bare ita, gudan jinin sa. For 35 years I’ve been preserving myself for him, koh so daya ban taba siyar da jikina ba, I know that doesn’t make me a saint amma you can bear me witness Laylah, bana abunda ya wuce hada ýan mata da maza masu kudi. Leek kam iya gwargwado na bata tarbiyya, ban bari ta baci ba. Na mata aure…..”. Ta fadi tana ta kuka. Laylah ta juyo tana ta bata haquri. Sai da hawayen suka tsaya sannan ta cigaba da drying ma Laylah hair dinta. +

“And I’m happy for you, zaki bar wannan rayuwar. You’ll start a new life. I’m very proud of you Laylah, ba kowa ce mace zata iya sacrificing abunda kika yi sacrificing ba, you’re a lady like no other. May you be happy always.”. Laylah ita ma kuka mara sound ta fara.

“So what are your plans?”.

“In na dawo gobe, zan fadi wa Abdulmalik gaba daya tarihi na. If he accepts me for who I am, zamuyi aure. I’ll be the best mother to his son. Zan tuba, i’ll finally go for pilgrimage, dama na dau alwashin bazan taba ziyartar gari me tsarki dabaibaye da Jirwaye ba, i’ll go for cleansing. Sannan zan raba dukiya na into 2, half zan ba Abdulmalik to start up something, to secure our future…… If there’s ever one. Dayan kason kuma zan cigaba da juyawa”. Yasmeenah ta ji dadin plans din Laylah sannan ta mata fatan alkhairi.

Ana gama busar da kan aka yi styling dinsa da kyau, lokacin ana neman karfe 7 kuma dama already P.A din khalifa Al-Haydar ya fadi mata cewa 7:30 on the dot driver zai zo ya dauke ta saboda boss ba mutum bane me son a bata mai lokaci. Sai da tayi isha ta sa kaya. Wani killer lingerie ne da Yasmeenah ta siyo mata, sabbi pul, red colour ta sanya. Sun mata kyau sun fito da curves dinta. A saman su ta sa wani black dress, dogon straight
dress ne haka wanda ya dan kama jikinta yayi mata kyau sosai. Takalmin kafar ta shima black, gashi kafar ya sha anklet. Idanu kam sun sha kohl, lips dinta kuma ta zuba wani uban killer blood red lipstick. Ba kwalliya fuskar tam daga kohl sai lipstick inda ta sa amma ta fito tayi matukar kyau sosai. Jacket inda ta daura a sama shima black ne sai red clutch inda ta riqe a hannu. Sai 7:40 pm ta sauko, tana taku a hankula ga Kanshin turaren ta na tashi a ta ko wani angle.
+

Tana fitowa, driver ya sauko daga wata Shegiyar Mercedes Benz wanda ke da customised plate din Al-Haydar a jiki ya buda mata kofa yana gaidata. A hankula ta ansa sannan ta shiga gidan baya ya mayar da kofa ya rufe shima ya shiga nasa bangaren ya rufe ya fara jan motar. Saboda boredom ta ciro wayarta tana ta daukar selfie daga baya ta koma buga game sai dai gaba daya hankalinta ba akan game in yike ba. Ji tayi gaban ta na wani mugun faduwa, sai kace yau ta fara haduwa da manyan maza masu kudi, duk ji tayi she’s nervous. Bata san meyasa a duk sanda the name khalifa Al-Haydar is mentioned take jin wani faduwar gaba, without even meeting him, he’s already intimidating her, ina ga in an hadu. Cike da wannan nazarin suka isa Al-Haydar empire. Bata ma ankara an isa ba sai da driver ya buda mata kofa.

Sai da ta ja numfashi tayi wani dan guntun addua a zuci kan ta sauko motar tana murmushi ta shiga cikin makeken hotel din, wanda daya ne daga cikin businesses din Al-Haydar. Kuma yana hotels irin haka, masu girma kusan guda 5 a Nigeria banda wanda suke kasashen waje. Tana shiga lobby din ta isa counter da fara’ar ta.

“Yes ma’am, how may I help you”. Receptionist din ta tambaye ta cike da fara’a.

“A meeting with khalifa Al-Haydar”. Ta ansa.

“Any invitation?”. Ta tambaye ta. Ba tare da tace komi ba ta buda dan clutch dinta ta ciro wannan invite din da aka kawo mata ta miqa. Da receptionist din ta karba ta duba sai ta tambaye ta password.

Matsowa dan kusa da ita Laylah tayi ta rada mata ‘The heart of lucifer’. Murmushi matar tayi sannan ta miqa mata wani dan card a ciki wanda instruction ne a ciki sannan ta yi kira a waya sanar da Khalifa Al-Haydar da isowar baquwar sa. Bayan ta gama wayar kuma ta kirawo wani wanda kamar shima aiki yike a hotel din. Bata ce mai komi ba, kawai password inda Laylah ta fadi mata ita ma ta fadi mai yayi coding saqonta. Sai cewa yayi Laylah ta biyo sa.Tafiya suke har suka isa staircase amma sai taga basu dau stairs dinba neither did they take the elevator. Ita dai shuru tana binsa har aka isa wani qofa wanda biometric thumbprint dinsa yayi using ya buda qofar. Qofar na budewa suka shiga suka cigaba da tafia, har suka isa wani underground staircase. +

Ita dai Laylah tana ta ganin ikon Allah, irin wanan security din duk for one man, saboda tsananin kudi, aji da matsayi. Bata ce komi ba har sai da suka sauka stairs din suka iso wani hall, daga nan yace ta yi tafi in ta kai end din hall din tayi taking left turn. Murmushi yayi sannan ya mata sallama ya juya. A hankula ta cigaba da tafia har ta isa left turn din, tana koh yin left turn din ta iso saitin wani qofa wanda aka rubuta “Confidential suite….. Khalifa Al-Haydar” a jiki. Tana cikin nazarinta ta ji muryan robot Jikin wani machine na magana.

“Welcome to the Confidential suite Laylah Jaan…..”. Baki ta bude cike da nazarin yadda aka yi machine din ya san sunanta. A zuciyar ta tana tsoron kada ta shiga ciki ta yi kauyanci. Bata gama yi nazarin ba ta kuma jin machine dun na magana.

“Once upon a time a poor woodcutter wandered deep into the forest in search of wood to cut but came across a den of 40 thieves which he entered using the password……..?”

“Open sesame”. Ta fadi password din. Tana fadi kofar kofar ya buda.

“Welcome to khalifa Al-Haydar’s world”. Machine din ya kuma fadi. Wani sanyi sosai suite din ke yi ga Kanshin da ke tashi da wani dan soft music na the weekend na tashi a aha kula, ga ko ina duhu ba wani haske, candles ne aka kunna ba masu yawa ba.

“Hello… Laylah…. I am honey”. Ta ji an fadi. Wani irin ijiyar zuci ta ije tsananin tsoron da ya kamata. Tana juyawa taga wani robot ne a gefen ta tana magana. “Come this way, khalifa awaits you”. Ta fadi, tana tafe Laylah na biye da ita har suka isa wani balcony shima ba wani haske sosai amma da dan wutan da ke illuminating a balcony din she could figure a man standing, sanye yike da suit ya juya musu baya, yana kallon dan glass window inda wajen window din man made garden ne, har da wani dan moon na karya a sama tunda ginin underground structure ne.


“You can leave now honey”. Ta ji ya fadi ba tare ya juyo ba. That voice, she knows the voice somewhere, amma a ina.

“Do have a great night boss”.

“I sure will honey”. Ya kuma fadi kan ya juyo.

“Hello Laylah…… Jaan”.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]