[Advertisements⬇️]

ƁATACCEN YANAYI CHAPTER 2 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ƁATACCEN YANAYI 
CHAPTER 2

Maza ne kimanin su ashirin, duk sanye da suits suna zaune shuru a boardroom. Jefi Jefi
suna dan kuskus da juna. Can kamar after minti goma saiji suka yi an buda kofar
boardroom din. Maza ne kosassu guda biyu suka fara shigowa kamun wani namiji sanye da
suit na alfarma, da gani kasan ba karamin mutum ne zai iya affording wannan kalar suit din
ba, domin limited edition designer suit ne na Giorgio Armani. Tsam duka mazan nan suka
miqe ganin ya shigo ana ta gaida sa, wani bature ne dan dattjo ya fara nufo sa cike da
fara’a.
“Welcome sir”. Ya gaida shi “Im glad to have finally met you. I’m the new managing
director of khalif constructions, the Amsterdam branch actually”. Ya fadi. Murmushi kawai
ya mai suka sha hannu kamun ya wuce ya zauna a kujerar sa ta alfarma, kujerar CEO. Sai da
aka gama setting din smart board inda ke dakin, sannan duk mutanen da suke zama aka
miqa musu wani file aka kuma umurci kowa da ya kunna computer dinsa tukun ya buda

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

baki don yayi magana.
“Where’s A-Mubaraq?”. Yayi maganar cikin wata sanyayyyar murya gami da kallon kujerar
da ke facing dinsa directly, kujerar overall director din khalif airlines and group of
companies. “Tariq? You heard me l believe”
“Ye.yes…yes si.. sir”. PA dinsa me ansa suna Tariq ya ansa cikin inina. “I sent an email to
everyone you asked me to”. Ya ansa.
“Then why is Al-Mubaraq not here?”. Ya kuma tambaya amma kowa yayi shuru “Find out
what’s wrong”. Ya umurci P.A dinsa.
“Yes sir”.
“Now!” Ya kuma fadi wannan karan cikin murya me dan karfi. “Gentlemen I greet you all”
Ya fadi, huskar sa a hade ba alamun dariya koh murmushi. “As you all know I meet with all
managing directors of this mighty group of companies every 6 months but I had to set this
meeting up 3 months to the initial time for the meeting”. Ya fadi kamun ya tsaya gyaran
murya sannan ya gama kallon faces din duk wanda suke gun.
“Embezzlement of this company’s money has been going on and the culprit or culprits i’m
sure are here amongst us. A great chunk of money has been stolen and we don’t know how,
when, where or by who”. Ya fadi. Ji kake mutanen da ke gun suna dan kananun surutu
tsakaninsu.
“How much precisely are we talking about here?”. Khalid Shuraim, managing director din
branch in Saudi Arabia ya tambaya.
“50,000 U.S Dollars. About 67,500,000,000 Saudi Riyals. That’s 18 billion naira in Nigeria’s
currency”. Be gama fadi ba kowa ya buda baki cikin mamaki. Hakika kudi da aka sace ba
kudade bane kananu. Dole a dau mataki. A nan meeting dai ya dau zafi, kowa na
presenting progress din branch inda yike, ana nuna profit and loss chart na businesses din
company din. Bayan kaman awa uku, aka gama meeting.
“We all meet in 3 months time insha Allah. I’ll have my P.A send the venue of the meeting to
you all. Gentlemen, have a nice day”. Ya miqe yayi waje, bodyguards nasa suna biye dashi a
baya. Wani tsararran office ya nufa, da isowarsu kofar daya daga cikin bodyguards nasa ya
buda mai kofa ya shiga su kuma suka tsaya a wajen kofar. A hankula ya dinga takawa har
zuwa kujerarsa ya zauna. Sai da ya sama ýan mintoci kadan ya na dan nazari kan ya buda
computer inda ke gaban sa amma duk da haka ya sama kansa da rashin concentrating
akan aikin da ke gaban sa, duk tunani ne iri iri suke ta yawo a kansa. Dago kai yayi ya qura
idanunsa a kan qaton enlargement inda ke ije a office dinsa. Wata ýar murmushi ya saki
tare ta miqewa ya nufi inda wannan enlargement yike.
Ya dauki lokaci yana kallon hoton kan ya dan shafa Jikin hoto. “T’m the man you’ve always
dreamt for your son to become right? Na mijin zaki, a man like you.. Mohammed Mumtaz
Al-Haydar”. Wanda ke hoton nan dai ba kowa bane fa ce mahaifin sa wanda ya rasu kusan
shekaru goma da suka wuce. Shekarar nan ta kasance me tsananin wuya a garesa
kasancewar koh shekara mahaifin sa be yi ba da rasuwa ya rasa Fatima, matar sa wacca ta
mutu a gun haihuwa.
Tuno wa yayi da Fatima da irin rayuwar auren da suka yi. Duk da auran su ba aure bane
wanda akayi sa akan so, sun zauna cikin haquri da juna da kuma kwanciyar hankali. A
lokacin da son Fatima ya fara shiga zuciyarsa, lokacin mutuwa ta raba shi da ita. Har yau ba
ya iya mance randa ya rasa Fatima 8 years ago..
“Mace ce”.
“Na ce maka namiji ne!”
“Mace”
“Na miji!”. Ta fadi cikin bacin rai “Cikin ba a jikina yike ba. Ni nasan na miji zan haifa”
“Haba habibty… “‘m sorry. We’re having a boy insha Allah. Daina hushi”. Ya rarrashe ta.
“Yawwa habibi na, ko kai fa”. Ta saki wata murmushi, irin wanda ke sanyaya zuciyarsa,
wanda a duk lokacin da aka basa haushi a office da ya dawo gida ya kalli wannan
murmushi a huskar ta sai yaji duk wannan bacin ran nasa ya tafi. A Kullum gode wa Allah
yike yi da kuma Abban sa da yayi arranging auran sa da Fatima.
“We’ll name our son muhammad Fadeel insha Allah” ta katse mai tunani. Murmushi yayi ya
jawo ta kusa da jikinsa.
“I thank Allah each blessed morning for making you mine”. Ya fadi tare da sumbatar goshin
ta.
“So now it’s settled, isn’t it?”.
“What?”
“We’re gonna have a boy and he’ll be Muhammad Fadeel”
“Such a party pooper, ko Kice mun you love me too”.
“Toh fa kai kace na daina karya ba kyau”. Ta fadi cikin tsokana.
“Kenan baki so na?”.
“Yo ehma..” Ba ta gama magana ba ta ga ya miqe cikin hushi ya wuce bedroom ya barta.
Yar dariya tayi kan ta miqe ta nufi bedroom din ita ma “Habibi” Ta kira shi cikin muryar ta
me sanyi amma sai yaqi kula ta. Ta matso kusa dashi ta zauna amma sai ya share ta ya juya
yayi kwanciyar sa.
“Haba habibi.. qalbi na, kaima ka san duk duniya ba irin ka a gu na. Sanyin idanu na,
tauraro me haske zuciya ta, abun alfahari na a ko da yaushe, uban ýaýa…” Bata kai ga
gama magana ba taji ya janyo ta jikinsa.
“You’re kiling me with your words” Ta ji ya fadi hawaye masu dumi suna sauko wa daga
idanunsa.
“Why are you crying?”
“Tve never felt love like this before. Never leave me please zahra”
“Shhh mutu ka raba nida kai insha Allah”. Gyara kwanciya tayi a jikinsa suka dade a haka
kan can tace mai su fita.
“Please please please let’s go do some shopping and stop by the new ice cream place”
“Amma fa doctor yace ki rage shan kayan sanyi fa. Can’t we just stay like this, I enjoy
cuddling with you”
“Pleaseeeeeeee mana, Kaga I promised Aryaman zan siya mai birthday present kuma gobe
ne. Kaima ka san I won’t breathe in ban siya mai abu ba. Kaji habibi”.
“Toh ya na iya dake. Ni kawai jikina yana mun wani iri ne, i’m having a bad feeling”
“Kayi ta azkhar, Allah na tare da mu insha Allah”.
“Toh bara na watsa ruwa na zo”. Yana shiga bandaki ita ma ta miqe ta sanja kaya zuwa wata
doguwar riga mai kyau wadda tayi matukar mata kyau dama kuma gashi ciki ya an she ta.
Cikin ta ya fito dan madaidaici dashi dan in mutum ya gani ma bazai taba zaton ya kai wata
bakwai ba.
Shima yana fitowa ya sa ýar tshirt da wando ýar three quater suka fito yana riqe da
hannunta. Sun shiga mota kenan zaya tayar da motar ta dakatar dashi.
“Me nene kuma yanzu?”. Hugging dinsa kawai yaji tayi tare da fadi mai “I love you, in all
situations. Come what may always know that I love you, with my whole being”. Ji yayi ta
kashe mai jiki da kalaman ta.
“Why is my wifey being sweet all of sudden?”, ya tsokane ta kan ya yi starting mota, Idi me
gadi ya buda musu kofa, nan ma kansu fita ta ce ya tsaya tana so ta dan zanta da Idi. Kwarai
da gaske Fatima ta daure me kai yadda take ta abubuwa a ranar.
Sai da tazo fita da nufi zuwa sightseeing tukun ta tuno da ipad dinta. Nema take ta yi cikin
kaya kan can after some minutes ta tuna ai ta mance sa ajirgi.
“Damn!” Ta fadi gami da jan ýar tsaki dun takaici. Akwai abubuwa da yawa masu
muhimmanci a gun ta da suke cikin wannan ipad din. Cigaba da shirin ta tayi ta saka wata
jacket baqa me kyau da wando wanda ya dan matse ta sannan ta sa wasu boots masu
kyau, ta dauko dan karamin veil baqi ta rufe baqin gashin ta wanda sai kyalli yike ta yi
saboda tsananin kula da kashe kudi da ake yi a kan shi.
Waya ta dauka ta kirawo Simon dun yazo ya kai ta ganin gari tunda dama shine driver dinta
wanda zai dinga tuga ta iya zaman ta a Australia wanda be wuci na 2 weeks ba. Baa yi 15
minutes ba ya kira ta cewa ya iso harabar hotel din. Ta katse wayar ta saka a cikin wata ýar
suspender tare da wallet dinta da sauran necessities dinta sannan ta jawo babban box inda
tazo dashi saboda daga ganin gari ba zata dawo hotel ba. Special guest house din Senator
zaa kai ta. Tana gamawa ta dan fesa turare sannan ta fita tana takua tsanake kamar me
tausayin qasa.
Mr Yates na hango ta ya nufo ya ansa box din ya cigaba da ja har zuwa inda yayi parking
mota.wata mota ce hadaddiya, ta taka wadda ya dauko ta daga airport dashi.
‘Lallaima, senator babban mutum ne. Na ko yi babban kamu’ ta fadi a cikin zuciyar ta gami
da sakin wata ýar murmushi a fili.
Laylah dai ýar budurwa ce me tashe, wadda bata wuci shekara 24 ba da haihuwa. Tsayawa
kwantata irin kyau da figure inda Allah ya mata bata lokaci ne, ga muryar ta wata
sanyayyya da ita, irin muryar nan me sa me gida lattin office, ga manya idanu Masha Allah.
Gashi kam har gadon baya, ga skin din ta irin wanda bature kan kira flawless, ba spot koh
daya gashi da laushin tsiya wane fur din mage, tana da dan haske iya gwargwado ga farin
jini a gun samari. Laylah dai kawai full package ce. Karya ne namiji ya mata kallo daya ya
wuce, sai ya dago ya kuma kallon ta.
Shiga motar tayi ta zauna shuru a gidan baya shi kuma Mr Yates ya zauna a seat din driver
ya fara jan mota. “should we start with the museum?”.
“No, take me to a park'”. Ta fadi.
Cikin dan qanqanin lokaci suka isa wani qayataccen park wanda yike cike tam da mutane,
ga yara suna ta wasa da guje guje. Masu sai da snacks da ice cream duk gasu nan ana ta
musu ciniki, harta masu sai da abinci ma duk gasu nan. A hankula take tafiya tana wasa da
wani dan fure da ta tsinka. Wasu tsoffi biyu ta hango, turawa ne su kuma daga ganin su
mata da miji ne. Zaune suke a wani carpet mijin na ba matar abinci a baki ita kuma tana
ansa. Jin wani abu tayi a zuciyan ta kallon wannan tsoffi guda biyu, gasu dai sun tsufa
tukub amma basu daina so da kula da junan su ba. Ta dade tana kallon su cike da shaawar
rayuwar su.
“I wish”. Ta fadi gami da dan lumshe ido kan ta cigaba da tafia tana tunanin koh zata taba
iya samun masoyi wanda zai so ta, yayi accepting dinta a yadda take har suyi aure su tsufa
tare. Tana gaba kuma kadan, wasu couples ta hango da dan su wanda bazai wuci shekara
daya da ýan watanni ba. Tafia suke riqe da hannun juna, sun sa dan yaron a tsakiyarsu. Can
sai yaron ya balle ya rugo da gudu iyayen na biye dashi suna dariya, shima yaron dariya
yike. Kawai bata ankara ba taji an auko mata, an riqe kafafun ta. Dan yaron nan ne da ke
gudu.
“What’s your name?”. Cike da murmushi ta miqa mai hannayen ta biyu ta dago sa zuwa
jikinta.
“Bubble” ya fadi yana dariya ita kuma sai wasa take da gashin sa mai laushi.
“Your name is bubble?”. Ta tambaya tana dariya.
“Bubble!” Ya kuma maimaitawa. Kan ta buda baki tayi magana taji muryan maman yaron
ta katse su.
“Owen! You naughty kid”. Yana juyo wa ya kalli mamansa ya fashe da dariya. Ita kuma
Laylah ganin mahaifiyar sa ta miqa mata danta. Cikin fara’a ta anshe sa.
“He’s a cute kid” ta fadi kan ta mai waving hannu ta wuce. Wuri ta je ta samu ta zauna
shuru bayan ta siya cold drink. Ta dade a zaune tana nazari iri iri. Kallon wasu ýan yara, ýan
mata biyu suna wasa abun su ya sa ta tuna gida, ta tuna da Auta. Bata san lokacin da
hawaye ya fara sulalowa daga idanunta ba saiji kawai tayi an kamo hannun ta an ije mata
abu a ciki. Hannun ta fara dubawa taga hankie aka ije mata kan ta dago idanu domin ganin
me karambanin da ya riqo mata hannu har ya sa abu a ciki. Sai dai me zata gani? Tana dago
kai suka yi ido hudu da wannan mara hankalin mutumin wanda ta zauna dashi a jirgi.
“You!” Ta fadi da dan qarfi
“Na tsani naga mutane suna kuka, barin ma ýar budurwa kyakyawa'”. Ya fadi yana mata
murmushi.
“Malam ina ruwanka dani”.
“Ai ga irin ta, ka taimaki mutum amma ya watsa maka qasa a ido”. Ya fadi ya tuntsure da
1
dariya.
“You always love making jokes out of people, don’t you?”. Ta fadi tana share hawayen
idanunta da hankie inda ya bata.
“Whenever distressed, remember Allah and say Alhamdulillah. You’ll feel okay”. Ya fadi ba
tare da ya Kalle ta ba ya miqe. Har ya fara tafia ya juya da nufin mata magana “Can I get
your address?” Ya tambaya.
“Why?”
“Kin mance ipad dinki a gu na”.
“Koh dai ka dauka mun ipad ba da izini na ba har na mance sa a gunka ba”. Murmushi
kawai yayi be ce mata komi ba “Jk guest house” ta fadi mai sunan guest house din Senator
inda nan ne sabon masaukin ta.
Okay, I’ll drop it by tomorrow”. Ya fada ya cigaba da tafiyar sa. Tafia kawai yike amma
hankalinsa baya jikinsa. Fuskar ta kawai yike tunawa, hakika wannan baiwar Allah sa bai
tambaya sunanta ba kyakyawa ce. Mace daya ce kawai ta taba sa shi yaji abunda yike ji a
zuciyar sa yanzu, ya kasa gane me ke faruwa dashi. Har ya isa inda ya bar Nawfal tunanin ta
kawai yike yana Fuskar ta, yadda ya izza ta tana kuka. Duk da dai kuka take, Fuskar ta ba
wata walwala sai da tsananin kyaun ta ya bayyana.
“KHALIFAH!”. Nawfal ya kira sunansa da karfi “Tunanin me kake haka?”. Khalifa ya dan sosa
kan sa yayi murmushi kan yace me ba komi.
“Kai dai fadi gaskia”.
“Nace ma ba komi, wani abu kawai na tuna”.
“Chuchu wanted to talk you in the morning amma nace baka kusa”
“Shine baka fadi mun ba tunda na dawo” ya dan bata rai.
“Kayi haquri, na mance ne sai yanzu na tuna”. Khalifa be ce komi ba ya fara laluben tablet
dinsa dun ya kira chuchu’n sa.
Ita kam Laylah zama tayi shuru, tana ta tunanin wannan mysterious man din wanda da
farko zuciyar ta ke cike da tsanarsa sabida abunda ya mata a jirgi amma kuma yanzu take
jin zuciyar nata na wani irin bugu duk sanda ta tuna abunda ta kankama tsakaninsu ýan
mintoci da suka wuce. Dago hankie inda ya bata tayi ta kai hanci, wani kan shi ne me dadi
yayi welcoming nostrils dinta. Kanshin shi ba mai karfi ba sosai sai wani dadi da sanyi sanyi
da yike dashi.
Har zuwa yamma sosai tana park din, sai da mutane aka watse sosai kan ita ma ta mige
lokacin Simon ya zo daukan ta, ta shiga mota suka wuce. A cikin motan ne yike fadi mata ai
senator na can yana jiran ta dun ya gama duk meetings inda yike dasu.
“Lay lay Laylah!”. Senator Junaidu ya dinga waqa da sunanta a lokacin da suka isa guest
house din.
“Haba baby, sai yau ka tuna ni”. Ta dan tabe baki cikin shagwaba.
“Haba Laylah na kema kinsan Kullum kina cikin raina, ban samu zama bane tunda na zo
Australia gashi wancan addababbar matar ta nace sai ta biyo ni, sai jiya na samu na sha
1
iska bayan na sa ta a jirgi zuwa dubai”. Ya mata bayani “kiyi haquri kinji sweetheart”.
Ita kam kallonsa take cike da mamakin yaudarar da namiji. Addababbar matar nan da yike
magana ba kowa bane fa ce matar sa, Uwar ýaýansa wadda ta zauna dashi tun baya da
komi har ya iso matsayin da yike a yau. ‘Lallai namiji ba dan goyo bane’ ta fadi a zuciyar ta.
“Kiyi haquri mana. Karki bari Baraka ta hada mu rigima”.
“Amma ka iya biya mata kudi zuwa Dubai bayan ni tun yaushe nike ce maka ina son zuwa
Dubai”. Ta fadi rai a bace shikuma senator ya matso kusa zai rungume ta amma ta ja da
baya.
“Haba Laylah, kar muyi haka mana. Dubai ne dai kike son zuwa Ince? Zaa samo miki visa,
Karki damu”.
“Da gaske” ta fadi tana dan murmushi.
“Na taba miki wasa?”.
“Aah baby na. Allah ja zamani”. Ta fadi gami da kissing kumatun sa.
“Yau dai special package zaa bani koh”. Ya fadi yana dariya.
“Yanzu dan visa inda zaa mun na Dubai shine kake son special package. Lallaima senator,
kaima ka san special package din Laylah Jaan kudin sa daban yike. Ai visan Dubai na ban
haqurin share ni da kayi ne”.
“Wallahi koh Baraka bata mun wannan iya shegen”.
“Toh ai Baraka kace, ni koh Laylah ce, yarinya son kowa qin wanda ya rasa”!. Ta fadi tana
neman jan jakarta “kace ma zuwa na bayi da wani amfani, sai kaje Baraka ta baka special
package din”
“Haba, yaa ki dawo. Yaushe ma zaki hada package dinki da na Baraka, mata sai qiba dukta
cika wuri kamar wata bull dozer. Koh dan kiss nace ta mun sai tace wai ita kunya, har yau ta
kasa waye wa, kayan takaici. Yi haquri ki zauna baby”, ya jawo ta ta zauna a kan cinyar sa.
1
“Karki damu, zan rubuta miki cheque na 6 million, yayi koh?”.
“Toh ya na iya, I will just manage. Baby baby kenan” ta fadi tana dan manna mai kisses a
Jikin sa. Tsam ya daga ta suka shiga daga cikin bedroom ni ko aka yi slamming door a
Fuska na wai na cika kwakwaf.
Wannan ita ce rayuwar Laylah Jaan…. rayuwar karuwanci, rayuwar bin mazan wasu, maza
masu hannu da shuni a qasa; manyan ýan kasuwa, ýan siyasa da dai sauran masu kudi.
Laylah Jaan ta kasance burin duk wani mutum wanda ya mallaki kudi da suna.
Hmmmmm ni har jikina yayi sanyi wallah. Koh ya aka yi Laylah ta tsinci kanta a cikin
wannan mummunar sana’a oho, 
Tuqi yike suna ta hira, Fatima tana ta basa labarin childhood days dinta, shikuma yana ta
sauraron ta yana dariya.
“Habibi”. Ta kira sa kamar yadda ta saba.
“Yes dear”
“Dan Allah mu shiga gun Haijo kaji”. Juyowa yayi ya Kalle ta.
“Wai ke ya kike son gara ni ne haka”. Ya fadi ransa a dan bace.
“Toh naga muna kusa da layin su ne”. Ta fadi “Amma ba komi, mu wuce kawai” ta qara fadi.
Shikuma yayi shuru bai ce mata komi ba. Can kawai yana tana fadi cikin wata iron murya
da ta sosa mai ran sa
“Uwata ma yanzu hana ni ganin ta ake, in ban ganta ba yau waya san randa zan ganta”. Har
da share dan kwallan ta duk sai yaji ba dadi, kamar bai mata adalci ba. Juyo kan motar yayi
kawai ya shiga hanyar da zata sa da su da layin gidan iyayen Fatima.
Tafe suke ba me cewa kowa komi, sai radio da ke kunne. Suna isa wani makeken gida ya yi
honking, ba tare da bata lokaci ba me gadi ya buda musu gate suka shiga. Da yayi parking
sai ya fito ya buda mata qofa suka fara tafia hannayen ta a cikin nasa kamar yadda suka
saba. Shiga suka yi cikin gida Hajjo ta tare su da fara’a. Suna zama masu aiki suka shigo
musu da refreshments.
“Ai ba ma dadewa zamuyi ba, mun zo wuce wa ne nace mu shigo”. Fatima ta fadi wa Hajjo
tana mata murmushi.
“Auu toh, Alhajin na nan ai, ku shiga ku gaisa”. Hajo ta fadi cikin fara’a. Hajjo kamar yadda
yaran ta ke kiranta ita ce mahaifiyar Fatima. Hajia Hajara ta kasance mace me kirki da
haquri matuka, bata da hayaniya gashi tana daukar kowa tamkar nata. Bata kyamatar
talakawa kamar yadda masu kudi ke yi, ita kowa nata ne. Fatima ita ce diyar ta ta uku,
akwai maza biyu gabanta, ya Fu’ad wanda soja ne, sai kuma ya Abdul, shikuma engineer
ne. A bayan ta kuma akwai maza biyu Muhammad da Mahmoud. Kasancewar ta the only
girl ya sa aka fiji da ita, fiye ma da yadda ake ji sa Auta Mahmoud.
A tsaitsaye suka gaisa da Alhaji sannan suka musu sallama suka wuce shopping mall
domin siyawa Aryaman birthday present. Aryaman nephew din Fatima ne, yaron wan ta ya
Fu’ad. Suna shiga mota ta Kalle sa ta saki wata murmushi wadda ya fito da dimples dinta.
“Thanks habibi, you always make my wishes your command”
“The things we do for love”. Ya fada shima yana mata murmushi “yanzu dai kinga Hajo
dinki koh, hankalin ki ya kwanta”. Daga kai ta mai alaman eh hankalin ta ya kwanta.
Shopping mall din gidan bene ne me dauke da about 10 storeys. A nan ma suka shiga
arguement.
“Gaskia elevator zamu shiga’
“Haba dan Allah, kai wai baka ji abunda doctor yace mun bane rannan. Na dinga exercise
sabo da cikin ya girma”.
“Toh ba muna strolling ba tare, gaskia Fatima I can’t take the stairs”
“Shikenan, je ka shiga lift, ni zan taka stairs, mu hadua 7th floor”. Ta fadi cikin bacin rai.
‘Duk na qosa ta haihu na huta da rigima’ ya fadi a zuciyar sa amma a fili sai ya jawo ta yana
rarrashin ta.
“Aah haba habibty. Allah huci zuciyar ki. Muje mu yu exercise”. Ya hakura ya bi ta suka hau
stairs ba wai dun ran sa ya so ba. A haka dai ya ta bin ta. Tun suna ma Aryaman shopping
har Fatima ta koma side din cosmetics and body care products ta fara nata siye siyan
shikuma yana gefen ta yana taya ta zabe.
“Ji mun wannan turaren, do you like the scent?” Ta tambaye sa.
“Why are you asking me if like it, ba ke zaki sa ba. It’s nice tho”. Ya ansa ta yana sunsuna
hannun sa inda ta fesa mai turaren yaji.
“T’m doing it all for you”. Ta fadi mai cikin murmushi.
Sai can yamma suka gama shopping dinsu. Har sun kama hanyar wuce wa ya hango wani
set na sleep suits na babies sun mai kyau sosai yace mata suje su siya.
“We’re taking the pink one” ya fadi wa shop attendant din.
“No habibi, we’re buying the blue one. I can’t have my little Fadeel looking like a barbie
doll” Dariya kawai ya saki sannan yace a kawo masu blue ones din. Ya biya kudi suka wuce
duk shi ke riqe da kayan da suka siya.
Kamar yadda suka zo, da zasu koma ma stairs din suka bi. Suna tafia suna hirar su, Fatima
nata dariya. Kawai isar su 4th floor sun kai tsakiyar stairs din Fatima ta turgude sai rolling
kawai yaga tana ta yi har ta kai qasa ta bugi cikin ta da wani bango. A gigice ya wurgar da
jakkunan shopping inda ya riqe ya nufi inda take, jini kawai yike gani na fito wa daga
goshin ta, ga kuma jini duk ya bata rigarta yana bi mata qafafu. Mutane an dan taru amma
ba wanda ya nufe inda suke dana niyyar kai musu agaji. Idanu cike da hawaye yike kallon
ta duk ya rasa yadda zai yi, ita kuma sai kuka take tana salati.
“Na shiga uku, zan mutu” take ta fadi cikin kuka.
“Sai ta mutu zaku taimaka min” ya juya ya fadi cikin ihu. Mutane ne a kansu sun fi a kirga
amma ba ko mutum daya da ya nufo su da niyyar taimako.
Daukar ta yayi, jini duk yana bin jikinta yayi hanzarin isa exit din mall dun zuwa inda yayi
parking motar sa. Gudu yike ta yi a mota yana mata sannu, ita kuma sai kuka take ta yi tana
fadin duk adduar da ta zo mata baki. A hanya muka suka izza hold up ya hadu. Haka nan ba
yadda zai yi dole ya jira for about 30 minutes har suka sama Wucewa. Suna isa Asibiti be
jira an kawo stretcher ba ya daga ta a jikinsa ya ruga da ita ciki. Sanin ko shi waye da
matsayin sa a qasar ya sa ba a tsaya wani formalities ba aka wuce da ita operation theatre.
Can sai ga doctor ya fito ya kira sunansa.
“Mr Abdulmalik” ya kira sa.
“Yes yes doctor, how is she?”
“In a critical situation, i’m sorry to say but gaskia operation inda zaa yi akwai chances in
rasa mutum daya koh ita koh baby din'”. A lokacin wani bugu zuciyar Abdulmalik yayi. Be
taba tunanin akwai randa zai shiga tsaka me wuya irin wanda yike ciki ba a wannan
lokacin. Dole ya zaba tsakanin matar sa da yike so kamar ran ransa ya fita koh kuma baby
dinsa da yike ta zumudin randa zai koh zata iso duniya.
“Save the mother. Do whatever you want to do but you must save my wife at all cost” ya
kalli doctor din da idanunsa wanda tuni sun koma jazur. Doctor din be ce komi ba ya koma
operation theatre. Sai da aka yi kamar awa biyu tukun Abdulmalik yaga wutar theatre din
ya sanja daga ja zuwa green, alaman an gama operation din.
Wata nurse ce ta fito bayan about 15 minutes da sanjawan wutan. Riqe take da dan
karamin baby an lullube a wani blue shawl.
“Congratulations sir, it’s a boy”. Ta fadi gami da nuna mai baby din “The baby is about 8
weeks premature so we have to incubate him”. Ta fadi sannan ta wuce da baby din zuwa
dakin da zaa sa shi a kwalba. Shi Abdulmalik koh Tsayawa be ma yi ba duba yaron dun shi
babban abun da ke gaban sa a wannan lokacin shine sanin halin da zahrar sa ke ciki.
“Khalifa Abdulmalik Al-Haydar” Doctor ya fito ya kirasa.
“Yes yes, how is she doctor, zan iya ganin ta?”
Kallonsa doctor din yayi cike da tausayi, ya matso kusa dashi ya dafa mai baya.
Kasancewar sa family doctor dun Al-Haydar family yasa shi da Abdulmalik suka shaqu.
“Khalifa, you’re a Muslim and I’m sure kasan qaddara. Kasan kuma ladan mutum wanda ya
rungumi qadr; me kyau koh mara kyau.. Be gama statement dinsa ba Khalifa ya katse sa.
“Fatima fa? Fatima na fa? I want to see her, this minute!”. Ya bangaje doctor din ya ruga
dakin da take da gudu.
“Time of death.9:21pm”. Kalaman da suka fara dukar kunnunwansa kenan da shigar
sa dakin. Dago idanunsa yayi wanda sun dade da zama jazur, ya kalli dayan doctor inda ke
dakin da wata nurse a gefen sa ta na rubutu a notepad. Ya kuma juya ya kalli zahra sa
wadda take kwance, idanunta a rufe kamar me barci. Ji yayi an riqo sa amma ya sa hannu
ya hankade wanda ya riqe sa, be ma damu da ya juya yaga ko wanene ba kawai ya nufi
gadon da zahra sa ke kwance.
“Habibty.. ki tashi barci. I’m sorry you had to pass through all these pain just to have my
baby. Na qosa na ganshi, naga da wa yayi kama amma in ba tare da ke ba bazan iya zuwa
ganinsa ba. Dan Allah tashi muje muga dan mu, kinji zahra na'”: Ya gama magana yana jiran
yaga ta buda idanunta da yike matukar son kallon su a ko da yaushe amma yaji shuru.
“Hushi kike dani har yanzu? lI’m sorry habibty, please wake up”. Wannan karan ya jawo
hannun ta ya riqe a cikin nasa yana wasa da ýan siraran ýatsun ta.
“Sir you have to take it easy on yourself”. Wata nurse ta matso kusa dashi tana fadi amma
sai tsawa kawai ya mata, ta tashi ta basa gu.
“Ki daina sa mun baki, i’m talking to my wife. Get out!”.
“Zahra dan Allah.Be gama maganan ba wasu maza biyu suka shigo suna jawo sa waje
shikuma yana kokarin fisgewa. Yana kallo wasu nurses suka kawo auduga suka sa ma
Fatima a hanci, aka hada Jikin ta yadda ake wa gawa. Subhanallah! Ina zai mance,7
months ago a idanunsa haka aka wa mahaifin sa. Wani irin kuka ya saki me shiga zuciya, ya
zuba gwiwa a qasa yana kuka yadda ka san yaro karami. Duk mutanen da ke cikin dakin
tausaya masa suke. Kowa ya kasa ce mai komi dan a wannan lokacin shi daya ya san yadda
yike ji da kuma Allah wanda ya halicce sa.
“Fatima wh… why did you leave me. I told the doctor to save you for me. Why! Ya Allah
sai da na fara son ki Fatima, sai da zuciya ta ta saba da ke, sai da idanuna suka zama
addicted to seeing your face Fatima. What will tell our son, what will tell your Fadeel?
Dan Allah Fatima ki tashi”. Yayi ta kuka har kalaman sa suka sa wasu daga cikin wanda suke
gun hawaye. Hakika yaji wannan rashin da aka mai.
Da kyar aka samu aka ja sa out of the room. Shikuma doctor already ya kira family dinsa ya
sanar dasu mummunar abunda ya auku. Can yana zaune shuru a corridor in dakin da
gawan Fatima yike sai ga ýan uwansa da na Fatima sun shigo. Hajo na hada ido dashi ta
farke da kuka.
“Fatima ashe ban kwana kika zo murn yau. Shiyasa kika ta hugging dina, kina ta kallona.
Harda mun addua Fati na. Wayyo ni”. Tai ta kukan ta ana bata haquri. Ita kanta mahaifiyar
sa kuka take, sai dai amma tana da karfin hali, ita tayi ta fama bawa dan nata da surukarsa
haquri. A nan dai close family members suka taru, masu kuka suna yi, masu suma nayi duk
dai gu ya kidime. Shi dai Abdulmalik baya cikin hayyacin sa dan duk a gigice yike. Yaya
Fu’ad ne yayi ta cika formalities din Asibiti kan aka gama suka tafi da gawar domin ayi mata
sutura a kai ta makwancinta. A lokacin da zaa tafi ne ma aka tuna da dan jinjirin data bari
wanda baza su iya tafi dashi gida ba. A nan dai aka cewa Haja Ganah ta zauna da baby din
kan a san yadda zaa yi. Ita Haja ganah kanwa ce ga mahaifiyar Fatima.
Cikin kankanin lokaci duk an sanar da ýan uwa mummunar abunda ya samu Abdulmalik.
Ana daukar gawar daga Asibiti gidanta aka kaita. Kasancewar da dare ta rasu, sai da aka
jira wayewar garin Allah tukun aka yi janaizar ta. Har a wannan lokacin Abdulmalik baya
cikin hayyacin sa, duk ya sanja, ya zama wani iri da shi, mutuwar ta taba sa ba kadan ba. Da
kyar aka iya lallaba sa yaje yaga dan sa yayi mai khutbah da Tahneek. A ranar kam ya ci
kuka, duk wanda ke gun ma sai da suka sha kuka saboda ya basu tausayi matuka.
“Da na bansan me zan ce maka ba, ban san da wani ido zan Kalle ka ba a ranar da zan tsinci
kaina da baka wannan mummunar labari, cewa mahaifiyar a ranar da ta haife ka ta rasa ran
ta. Ban sa ta ina zan fara ba, ban san ta ya zan tarbiyyantar da kai ba without your mother
by my side. I don’t know what the future holds cause right now I can’t even see the future,I
don’t know what it has in store for us. I’m sorry I could do little or nothing at all to save
your mother, I’m sorry you’ll have to grow up without a mother, i’m sorry…For everything
son. Forgive your father for he is nothing but a mere mortal. All can promise you is that l’ll
always be there by your side son, it’ll aways be us, you always nd is against the world.
Even though it would not make up for your loss, I promise to give you all the joy and
happiness in the world”. Kawai bai san sanda kuka ya kufce masa ba, tuna lokacin da yike
gardama shi da Fatima takan sex din baby dinsu kawai yike.
“You were right zahra, we now have a little boy, our son. Your Fadeel. Allah ya raya mun kai
da na muhammad Fadeel”. Ya tofa mai addua yayi hanzarin fita daga dakin idanu cike da
hawaye. Bayan ýan watanni da rasuwar Fatima, anso Abdulmalik ya auri cousin sister
dinta, Salma wadda ita da zahra tare suka tashi. Kasancewar Fatima the only girl ya sa
Hajjo ta dauko Salma tun tana ýar yarinya ta tarbiyyantar dasu tare. Aka yi akayi ya aure
Salma dun ta kula da Fadeel amma yaqi. In ba zahra sa ba, be ga ýa macen da zai taba
zama da ita ba a doran qasa.
“It’s either my zahra or no woman at all”. Ya fadi.
Bayan sallamar Fadeel daga hospital aka sama mai nanny ya fara zama da family din
Abdulmalik, wato mahaifiyar saboda Abdulmalik ya kasance shi daya tal aka haifa kuma ga
arziki da Allah ya azurta iyayen sa da shi kamar me. Duk duniya an san khalif airlines and
group of companies. Babban business empire ne wanda ya sama karbuwa da kuma
support from different countries round the globe. Kan rasuwar Mohammed Mumtaz Al-
Haydar, ya kasance mutum ne me fada a ji, yana da influence matuka a siyasar qasa da
kuma business world ma in general. Bayan mutuwar sa kuma shi ne dan sa Khalifa
Abdulmalik Al-Haydar ya gaje sa.
Bayan ýan watanni Hajjo tazo ta roqa dan Allah a ba ta jikan nata ta riqe, ko ganinsa zai
dinga debe mata kewar diyar ta.
“In ya so duk randa Khalifa ya sama mata yayi aure sai na dawo masa da dan sa”. Amincin
da ke tsakanin both families ya sa Khalifa ya yarda ba tare da bata lokaci ba.
Back to present.
“Khalifa!” Yaji an kira sunansa da qarfi “Tunanin me kake yi haka ne”. Dago ido yayi ya kalli
me magana.
“Nace ka dinga kirana Abdulmalik if we are in an office environment. At home you can call
me Khalifa all you want”
“Yes boss”. Ya fadi yana salute. “Ya kake? Done with the meeting?” Ya tambaya, Abdulmalik
be ce mai komi ba ya gyada kai alamar ehhh.
“Ka zauna kana ta tunanin ta koh?”
“Let’s go to the park”. Ya fadi ba tare da ya ansa tambayar da aka masa ba.
Toh jama’a…who is confused here, hands up in the air dun ni kai na a rude nike. Ga
Khalifatullah ga Khalifa Abdulmalik. Toh daya dai kamar me dan rufin asiri haka daya kuma
me shegen kudi. lkon Allah! And they’re both in Australia, gashi Laylah na neman daya,
shikuma daya ya hadu da Laylah. Me ke shirin faruwa ne? Wane zuciyar Laylah zata so? Me
kudi koh me rufin asiri? Wanne a cikin su zai yi accepting Laylah for the person she is. Allah
kuma zai sa da ta da Khalifa Abdulmalik Al-Haydar? Domin burinta kenan for years, ta
gansa, ta mai tallar jikinta. Hmmmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]