[Advertisements⬇️]

WANI AURE CHAPTER 9 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 • WANI AURE • CHAPTER 9
 • Shiyasa kaga bazan iya kai“ kaina gareta ba da sunan Ina sonta , bare tamin salo.
 • Nan kuma yayi ta zazzagawa Fk maseefa hade da cewa ai shi yaja masa duk wulakancin da’aka masa. Fk yace kwantar da hankalinka kabarni daita kawai ,nasan zata yarda ma ,. kawai dai itama so take ta nuna mana ,itama macece , nasanjan aji ne kawai na mata Amman ita din wacece dazatace bata sonka ,Inada tabbacin inshallahu zamuyi nasara.
 • Cikin fushi da jin haushi deeni Yace in taki yarda ka kyaleta kawai , yarinya sai kace wata gold sai wani yawo akemin da hankali akanta, yaja tsaki hade da kashe wayar batare daya sakejin abinda fk zai ce ba . Kwana deeni yayi da tunanin hade da zullumi halin da zai tsinci kansa idan yarinyar nan taki yarda dashi, duk shi Gani yake ba sonta yake ba. zai dai yi aure ne kawai saboda umarnin umminsa, bugu da Kari ma, bazai iya kaskantar da kansa wajen mace ba ballanantana harya kai shi ga furta kalmar so. Har zuwa wayewar garin ya cigaban mamakinta ganinta yake , tamkar yau aka haifeta, sannan har zuwa yanzu kallon karamar yarinya yake mata, ashe tasan abinda take yi ,uhmmmm uhmmmm ahankali ya dinga sauke ajiyarzuciya, wai zatayi tunani akai ya sake tunawa da kalmar data fadawa fk to da ko da uban wa zatayi tunani ya furta hakan a kasan rashi . kwance take akan bed din ummi Amman ba bacci takeyi ba ,hannuta rike da wani English novel mai suna ,mumy why sanye take cikin kananan kaya, pencil jeans da riga iya gwiwa a natse take karatunta dan tanajin dadi labarin yarinyar ciki litattafin ta birgeta kwaira ,ta yadda take kokarin kwatarwa kanta yanci saboda mahaiflyarta ta hanata auren saurayin da take son .. Cikin isa da kasaita yashigo dakin , tanajin motsen bude kofa Amman tashare dan batason abinda zai katse mata karatunta . Jin kamshin turarensa yasa ta dan dago idanunta suka sauka akansa , ganinsa yasa ta dan mike daga kwanciyar datayi, tasha jinin jikinta bata san meke sata jin yawan faduwar
 • gaba ba, a duk sanda taga yaya DEENi.
 • ta gaidashi batare daya kalli inda take ba ,ya amsa mata a ciki ,km cikin isa da takama sannan a takaice , tamkar dai yadda yasaba dan baya son duk abinda zai sa magana tayi tsawo atsakaninsu .
 • sai dai ita kam tsintar kanta tayi da zuba masa idanunta,tana binsa da wani irin mayyen kallo , cikakken namiji ne sosai mai ji da kansa , ko a taflyarsa zaka shida haka. gabadaya
 • bbu wata alamun ragwanta atare dashi .kana ganinsa zakaji ya birgeka ,daman aikin da shi kennan wato jami‘in tsaro.
 • Har suka gaisa da ummi dake tsaye fitowarta kennan daga bathroom ya juya da niyar barin dakin, idanun Zeenat na kansa tamkar zatace ya dawo ya zauna kada ya fita saboda tsoron masu farautarsa ,takasa dauke idanunta daga kallonsa take mji wani irin masefaffen kishinsa ya diram mata zuciyarta ta dinga rawa bata

  dauke’Idanunta a kansa ba sai data daina ganinsa . Ummi tabita da kallon tausayi tace inkin gama kallon nashi sai ki tashi ki hado masa abinsa ke kawai soyayya kika iya ba‘asan tattali ba , Zeenat ta dan turo baki tace ni dai ummi kwanannan bansa abinda na miki ba komai nayi sai kin min fada, ki dinga ganin Iaiflna , nifa bashi nake kallo ba , ummi tace eh ai nasan bashi kike kallo ba kurwarsa kike kallojairar yarinya kawai ni tashi ban guri . 

 • Washegari 
 • Zeenat tarasa dawa zatayi zancen yaya DEENi taji dadi kuma yabata shawara tamkar yadda zuciyarta ta aminta dashi ,ganinta dukwanda ta nufa da maganar baza tasamu goyon baya ba ,kmr dai yadda ummi tayi , Maryam ce ta fado mata a rai ,dan haka tashirya taje her part din su. Tana shiga part din idanunta sukaci karo da fuskar data tsana a halin yanzun arayuwarta ,kmrta juya ta koma haka taji , shemah ta hango zaune akan three site suna hira da Maryam take taji wani iri abu ya caki zuciyarta. 
 • ganinta yasa taji tamkar an soka mata kibiya ne a kahon zuciya taja ta tsaya takasa karasawa inda suke dan bazata juri zama a duk inda take ba , ganin haka yasa itama shemah ta mike ta fice Tama bar part din gabadaya . Da kallo Maryam tabi kowanne su Ahankali Zeenat takarasa tasamu waje kusa da Maryam din ta zauna zuciyarta a cunkushe , tsawon lokacin takasa cewa komai , Maryam tacewai yana ganki haka ne ? Cikin nishadi Maryam ta soma janta da hira har Zeenat ta sake Sosai Daga nan ta labarta mata duk halin da’ake ciki ,. “ Maryam ta zaro idanu waje tana mamaki tace kai da gaske kike ,to Ina girman kan nasa kuma? Zeenat tace yana nan bai je koina ba” sai ma abinda yakaru , 
 • Maryam tace in fada miki gaskiya,zeenat ta daga mata kai alamun eh “ki amince kawai” karkiyi wasa da damarki domin mata dayawa suna can suna neman miji irin yaya DEENi basu samu ba. 
 • amman idan kin yi saken da kika tsaya yauki ,wai kejan aji ,kya zo daga baya kina nadama dan irinsu tsada ne dasu ,. 
 • kin dai san halinsa da maseefar zuciyartsiya. maryam takarasa zance da 
 • Uhmmmm .. Ina ma ni Yace yana so …… 
 • jin haka yasa take Zeenat ta hade fuskarta tamau , hade da zabgawa Maryam din wata uwar harara tace kefa Yar wulakanci ce bangane dama ke yace yana so ba Maryam tace ke nifa da wasa nake dan naga kmr kin fara hassala ne Zeenat tace ,wani irin wasa wannan, nifa banson shirme . Ko kema zaki shiga layin shemah ne? Maryam tayi murmushi tace badani ba Ai tsakaninmu bbu haka yauwa naji ance ma kunyi fada da shemah Kwanaki? 
 • wai may ya hadaku fada ne , Zeenat ta tabe baki tana sauke ajiyar zuciya sannan tace shirme tamin irin naki. nan dai ta zaiyanewa Maryam komai ,suka tafa suna kyalkyale dariya Maryam tace kai tawan kina wuta , Zeenat tace Ai ni bata wasa bace ban daukar raini tuni nagama daita 
 • duk da batasan abinda tamln ba haryanzu. 
 • Maryam ta sake bata hannu suka taba, tace baki da kyau fa” sai dai idan ba’a tabo ki ba. Maryam tacigaba tawan ki Amince kawai da auren nan musha biki amman fa zakisha fama da wannan miskililin ,Zeenat ta sake yin murmushi tace indai zai cigaba da sona kmr yadda yake yi yanzu Ina ruwana da wani miskilancinsa can yakarata ,ai abinda yama fi birgeni dashi kennan. Amman nasan wuyarta dai ayi auren da sannu zai rage dukwannanjin kan nasa . Zeena ta kagu dare yayi saboda cewar da yaya faruk yayi zai dawo . ,tun tana Jiran zuwansa harta flda tsammani dan tara tayi gabadaya hankalinta a matukar tashe yake,tunaninta kar dai ya deeni ya hakura daita kmr yadda tace abashi hakuri. zuciyar tashiga rawa tamkar zata tsinke ta mike tsaye cikin sanyijiki tasoma zarya duk dai ummi na biye daita da kallo can Ganin goma tayi yasa ta nufi dakin ummi tana shiga ta fada kan gadon tana zubda kwalla,. ahankali tace Allah Allah kasa ba hakura yaya DEENi yayi ba ,. dako na cuci kaina da kaina tashiga zubda hawaye baji ba Gani tana jin zuciyarta na neman tarwatsewa tace Allah ka tausayin kajin kai na ka mallakamin abin kaunarta deeni ina sonka deeni tunda ka furta kana sona nakasa samun sukuni dan karkace ka fasa kuka take sosai hade da sambatu ,,. 
 • Shadaya daidai ummi tashigo ta dubi inda Zeenat take kwance taga alamun kmr batajin dadi karasowa tayi tace ke laflyarki kuwa da kyar Zeenat ta iya bude bakinta,tace kaina ke min ciwo ummi tace shine zaki zauna kina kuka ,tayi mata sannu taje takawo mata magani 
 • Wasa wasa sai da Zeenat tayi kwana biyar cur batare da taga zuwan yaya faruk ba.h hakan yasa hankalinta sake tashi fiyye da koda yaushe. cikin lokacin kadan ta zabge ta sake ragewa zazzabi may zafl ya rufeta, jikinta ya dauki zafi gwau , hankalin ummi yatashi , da Ganin halin da Zeenat take ciki kmr zatayi kuka. Ummi ta kira likitan dake duba su, wato family doctor dinsu , byn yazo ne yasoma aikinsa cikin sauri ganin yadda Zeenat din takeyi taki magana sai zubda hawaye kawai take ga zuciyarta na buguwa da sauri da sauri Ganin haka yasa doctor din ya dauko abin awo ,ya auna BP dinta ,cikin mintina da basu wace ashirin ba ya gano abinda yake damunta sannan ya daura mata drip hade da sanya allurar bacci ciki take ko bacci yayi awon gaba daita. Gabadaya hankalin Ummi ya sake tashi wani irin tsoro ne yashigeta lokacin daya ,da sauri tace doctor meke damunta? 
 • doctor yayi shiru yana nazarin abinda zai cewa Ummi kafin daga bisani ya numfasa ,sannan Yace akwai abinda tasa aranta wanda shine yayi dalilin haddasa mata damuwa har takai jinita ya hau sosai , Ummi ta sake maimaita abinda doctor yace ,doctor yace Amman inshallahu bbu damuwa zata samu lfy da zarar ta tashi komai zai yi dade, ummi tace to doctor na gode yayi mata sallama tare da gayamata yadda zata bata magani.duk wannan drama da akeyi deeni bai sani ba dan ko yashiga gaida Ummi baya damuwa daita ballantana yasan ko bata da lfy ne ,ita Kuma da haushi taki sanar masa Ai shi ba makaho bane 
 • Kwata kwata Fk bai samu damar zuwa ba sai acikon kwana na bakwai tukun yazo ,yasamu Zeenat din ayadda take yayi mamakin , yadda DEENi bai sanar masa ba gashi kusan kullum sai sun hadu. 
 • byn sun gaisa da ummi ne ,ya flta Yace Zeenat din ta same shi a parlour . 
 • Cikin tsanyijiki ta mike tasoma daga karta da kyar, cikin gimtsewar fuska ummi tace Ina km zaki kefa bakida lfy? 
 • Zeenat tabata fuska dan kada ummi ta hanata zuwa tace ummi sako zan karbo gurin Yaya faruk ,yanzu zan dawo , Ummi ta bita da idanu kawai Zeenat tace ummi sai nadawo cikin jin haushi da akaici Ummi tace kada ma ki dawo ki kwana a can . 
 • Da sallamarta tashigo parlour “Zaune ta same yaya faruk din suka gaisa ya sake yi mata ya jiki sannan Yace sister kiyi hakuri dan girman da rashin zuwana kmr yadda nace, wasu abubuwa ne suka sha kaina wlh, dan haka yanzun naxo naji abinda kika yanke,zeenat ta danyi shr kmr mai nazari Yace kada ki damu idan har baki son shi , kisanar dani ,danshi yace idan baki amince ba, kada atakura miki shi ya hakura, a dan firgice tace Ai yaya kaima kasan bazan iya cewa banason shi ba, ko dan ummi dan haka kace masa kawai na amince 
 • Fk ya saki murmushin murna yayi hamdala a zuciyarsa hade da godiyar cin nasara yace Shikenan ni zan wuce sai kinjimu. 
 • A ranar ummi ta nemi ciwon Zeenat ,tarasa duktana zargin ciwan nata bazai wuce akan DEENi bane ,da daddare har nafila Zeenat tayi dan Mika godiyar ga Allah. ummi tayi murmushi tace yau km ibadar ce ta motsa har da sallar dare? 
 • Zeenat tayi mata banza kmr bataji ba tacigaba da sallarta, Ummi ta sake cewa Allah yasa a dore in km nasamun NASURULDEENI ne nasan daga yau Shikenan. Abinda ke sake bawa Zeenat mamaki bai wuce Ganin yadda kullum yaya DEENi ke nuna k0 in kula akanta ba gabadaya ma Gani take kmr baisan da zamanta ba . ko magana ta fatar baki bata hadu su, idan ma yana gur’l  ita kanta batason zama in da yake yanzu ,Allah Allah take tabar wanje dan juriyarta takusan karewa. Fk bai samu ganin deeni ba, sakamakon wani aiki daya taso masa ,Amman Yace masa yabari zuwa weekend ,ya same shi a gida .sai da fk yakirasa a waya ya tabbatar masa da yana gida sannan yazo . 
 • zaune suke cikin parlour deeni byn sun gaisa fk yayi masa bayani duk yadda suka yi da Zeenat a boye DEENi ya sauke ajiyar zuciya ,sannan Yace ta taimaki kanta da kanta , kenan , fk yabishi da wani irin kallo sannan yace kai fa dan rainin wayo ne abinda yakamata kace kenan, deeni Yace nifa bawai na matsu dole sai ta amince da aurena bane. asalima ita din ba irin kalar type dina bace zan dai aureta ne kawai ,a rashi samun choice dina fk ya saki baki yana kallon deeni ,Yace Amman friend kasan itama tana da kyawunta daidaina , sai da ya dauki lokacin sannan yace ni nace maka dan kyawunta zan aureta? 
 • Ai bata da kyawun da zai rudeni ,km wlh har ga Allah da bata amince ba na hakura ,har zuwa sanda zansamu type dina. 

 • Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]