[Advertisements⬇️]

WANI AURE CHAPTER 8 - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 • WANI AURE

 • CHAPTER 8
 • Wata daya kenan fk yaji “shiru DEENi bai kuma yimasa zancen maganarsa da Zeenat ba musamman” yazo gurinsa dan zancen daman Kuma sun dade basu ga juna ba” sai dai sukan yi waya lokaci zuwa , lokaci dama ya kirashi a waya cewa yana nan zuwa . Byn sun gaisa fk yace friend haryanzu ban sakejin batunka da yarinyar nan ba . deeni ya gyara zama ,hade da yaja tsaki sannan ya lumshe idanunsa dan takaici da Haushin maganar . ya zubawa fk ido yana kallonsa kawai domin rasa me zaice masa Yayi ,tsawon lokacin suna zaune a haka sannan fk yace friend hakuri zakayi dan Allah ba wai Ina son dawo
 • maka da hannun agogo baya bane . Amman idan maganar danayi akan Zeenat ya bata maka rai, kayi hakuri.
 • ahankali deeni ya furzar da iska mai dumi ya miko hannushi ya dafa gwiwar fk , Friend ban tasamun abinda ya bani matsala kmr maganar yarinyar nan ba” abin haushi duk lokacin da nayi kudirin hakura daita sai nakasa. Kullum addu’a ta Allah yaye min ita daga raina Amman abin ya faskara ko son yarinyar ne yakamani “oho ” fk yayi murmushi yace lailai sonta kakeyi Allah yasa itama ta soka haka . DEENi ya gintse fuska yace Ina ruwana daita first lov ce kawai damuwata ,data amince da yanzu an wuce gurin Amman tsohuwar nan sai cewa take zan cuci Yar mutane ita bazata bani Yarinya karama ba inzo Ina bata wahala fk yace sanin halin ka tayi dan kai din bana wasa bane kana raina yarinyar ne dayawa shiyasa ummi batason aura maka ita wani lokacin sai inga kmr da gaskiyar ummi DEENI yayi masa wani kallo dan ni bason iskanci idan abinda yakawo ka kennan kana iya tafiya. Fk yace zanje in sameta da kaina karka damu. deeni yace dama kabarta kawai dan ko kaje ba amincewa zatayi ba. nasan halin first lov , da zata yarda da tunin ta amince.
 • na dai fada mata cewar ni na hakura dayin auren gabadaya” idan tagaji da zamana haka tasan abinyi . Fk yayi ta dariya tare da zolayar DEENI” friend ka dai shiga da yawa da ka’ajiye duk wani girman kai ,ka dinga kiran yarinyar kanajanta ajiki ,idan ummi taga haka zatafi yarda da gaske kakeyi “Amman kai kullum fuskarka a hade kmr hadari. DEENi ya tabe baki, kasan Allah bazan taba iya kiran ko wace irin yarinyar bace, da sunnan zance koba Zeenat ba. kai ma abinda kariga kasani ne “bansan ta Ina zan soma ba ,nifa bana kawo Zeenat a raina ,in dai first lov ta yarda ” to tayi hakuri ta aureni kawai dan ni banda wani lokacin ya mace . dan ma taji dadi ta samu miji irina ,yakarasa fadar maganar yana jan tsaki fk yayi dariya yace friend banda yabon kai fa , DEENI ya dan yi murmushi gefen baki har dimple dinsa ya lotsa kai ma kasan gaskiya fada ne dai kawai

  bazakayi bacikin “nida ita wazai taimaka wani? Bbu abinda zata nuna min ” fari ne kawaiya ceceta ” wanda kai kasan ko man bleaching takara bazata taba kamo nawa ba “fk yace ai shiyasa ka daurawa kanka girman kai al’amarin mata” km duk da kafita kyau ita zuciyarka ta zaba ,ta zama abokiyar rayuwarka ”

 • zanyi maka iya bakin kokarina ,. DEENi yabishi da kallo yace sannan ya maida bayansa ya jingina da kujera , dama kabar, damun kanka akan zance yarinyar nan , wai dole ne sai na aureta ,fk yace tunda nace
 • zanyi kabarni mana ,na gwada sa‘a ta k0 ummi zata yarda . DEENi ya daga kafadarsa alamun shi yasani .sannan yace tunda ka nace kaje din Amman idan labarin ba may dadi bane ,karka zomin dashi
 • Kmr yadda fk yayi alkawari haka ce takasance yasamu ummi da zance byn sun gaisa ne yace daman akan zance deeni ne da Zeenat” ummi najin haka ta canza fuska ” har tasa karfin gwiwar da fk yazo dashi ” yayi kasa.
 • Ahankali yacigaba” dan girman Allah ummi kiyi hakuri ki amince da auren nan “saboda dukkansu naki ne a ganina wannan abin farin ciki ne . Ummi ta sake tamke fuskarta Sosai tace faruk Ina matukar ganin kimarka da mutuncinka zaifi kyau kabar zance nan” banajin cewar zan iya amincewa. fk yayi shr yana tunanin yadda zai bullo mata can dabara tazo masa yace m Shikenan Amman naso ki Amince domin deeni yana cikin wani hali nason yarinyar nan. daidai lokacin da Zeenat ta dawo daga gidansu Maryam tana kokarin shigowa parlour ummi . ,karaf zance ya fada cikin kunneta cak taja ta tsaya jikinta ya dauki kerma . Fk yace ummi kin san halinshi baya daga cikin mutane masu magana biyu ,ya min ransuwa ba zai tabayin aure ba ,inba Zeenat ba ,km duk duniya ita ya Gani yake so. zamanshi haka nasan yana damunki ummi tace in duk duniya Zeenat yagani yake so ita Zeenat din ya sameta yaji ko tana son shi ? Ko haka kawai dan shi yana sonta” zan dauke diyata nabashi batare da ya nemi amincewarta ba. Nifa bazanyiwa diyata auren dole ba dan kawai Ina son na faranta masa rai Daga inda Zeenat ke tsaye tana jin komai” take jikinta ya dauki rawa yacigaba har wani zazzabi zazzabi taji yana neman rufeta , kafafunta suka Gaza daukarta sakamakon kermar da suke , nan ta sulale kasa tana jin yadda gabanta yashiga faduwa da sauri da sauri, tarasa dalilin ummin nakin aurenta da yaya DEENi . alhalin tasan yana sonta har haka. ,to hakan na nufln ummi tafison yaya yaje waje ya aure wata , sabanin ita kennan . kawai batayi aune ba taji saukar hawaye nabin kuncinta . Da sauri tasa Hannuta ta dangwalo hawayen dake bin fuskarta, tana kallo ta girgiza kai kawai tanajin tamkar an diga mata dalma ne a zuciya ,. Ta runtse idanunta ahankali muryarta cike da rauni tace meyasa Meyasa ummi kike son ki ruguzamin rayuwa please ummi ki amince na auri yaya DEENi , Ina sonshi har bansan iya kar kaunarsa a zuciyata ba ” bazan iya rayuwa in bashi ba Fk ya fahimci abinda ummi take nufl shiyasa yace ma DEENi ya dinga kiran yarinyar suna hira. ko kuna yajata ajikinsa . Ta hakan ne komai zaizo da sauki , fuskarsa dauke da murmushi
 • yace ummi idan dan wannan ne ,karki damu , duk wannan me sauki ne zamu tuntubi yarinyar muji , idan bata amince ba Shikenan. Ummi tace da dai yafiye muku” ba ku tsaya girman kai ba, fk ya sake yin dariya yana girgiza kai yayi mata godiya ya mike . Jin da Zeenat tayi fk yayiwa ummi sallama ne yasa tayi hanzari mikewa da sauri tashige bathroom din parlour din dake manne da falon nan ta fashe da wani irin kuka ita kam zuwa yanzu tafarajin haushin ummi . Fk na flta yakira deeni bugu biyu ya dauki wayar , fk yace friend kafara da bani goron albishir ,cikin yanayi na ko in kula deeni yace kada kace min first lov ta saurareka? Fk yace ta saurareni kuma inshallahu zamuyi nasara da alamun ummi ta amince ,. duk yayi masa bayanin yadda suka yi da ummi , yakarasa zancen da ummi ta nuna tanason asamu yarinyara nemi amincewarta ….. DEENi yayi shr sannan yace to ai wannan shine mai wahalar dan bazan taba iyawa ba , fk
 • yace wai kai tsoronta kakejine ko yaya ? 
 • ,ai take deeni ya hassala a fusace ya aiko masa da wata irin uwar ashariya ” wanda yasa fk yayi sauri cire wayar daga kunnenshi ,ya dan duba sai daya tabbatar daya yana kan layi. sannan ya mayar yacigaba magana” haba friend meyasa kake saurin daukar zafi akan abinda bai kai yakawo ba . bance dole sai kasameta da kankaba ,ni dakaina zanyi komai. 
 • sai Kuma ya sausauta yana jan numfashi yace ai kai ne da wani zancen baza. naji tsorota akan me ,raini ne kawai banaso , yanzun dai kai kaje kasameta kuyi magana da in ni nakirata bafa ra’ayinta zanjira ba. umarni kawai zan bata fk yace Shikenan sai na nemeka . Zeenat zaune gaban TV dake manne a parloursu ta hada uban tagumi ,hade da zubawa TV idanun . Kallo daya zaka mata , kasan kwata kwata hankalinta bai kan shirin da’ake gabatarwa . gabadaya tunaninta ya kashi gida biyu . 
 • ga tashin hankali ummi taki amince wa da aurenta da yaya DEENi. ga kamil da yasako, gaba da zance yanason akai maganarsu gurin big dady,. hankalinta a matukar tashe yake . har ummi takaraso inda take zaune bata sani ba”. 
 • ummi ta zuba mata idanu kawai tana nazarinta sannan ta numfasa sai data kira sunanta tukun , Zeenat tayi saurin juyowa frigice tayi firgigib tana duban ummi . 
 • idanunta ta zubawa ummi kmr wata mara gaskiya ” ummi tace wai ke wace irin sakarriyar yarinyarce” da kwata kwata baki san ciwon kanki ba “kalli ummi ta nuna jikin Zeenat da dan yatsanta , dube yadda kika dawo ,duk kinbi kin sakama kanki tunanin banzaji yadda kika koma duk kin tsotse kin rame danjarabartsiya ,anason a karemiki mutuncinki ,kinki natsuwa, kisan haka . sai kiyi tayi ai. 
 • cikin haka fk yayi sallama yashigo ya zauna akan kujerar one site yana gaida ummi Ta amsa masa fuskarta a gimtse dan tasan kwanan zance ” Zeenat ma ta gaisheshi tsam ta mike taje takawo masa abin sha . ,ummi ta tabe baki tana hararata dan takaici sannan ta sake kai dubanta ga fk din’tace DEENI fa yana dakinsa. Fk yayi murmushi yace ai ba gurinsa nazo ba ,jin haka yasa ummi tashare , ta cigaba da kallonta , gabadaya parlour ya dauki shru tamkar babu mutane a cikinsa bakajin motsen komai sai karar TV. Zeenat kam kamewa tayi tashiga hankalita dan motsi kadan , ummi zatace tafiye rawar kai . ganin shru yayi yawa yasa ummi ta mike tabar gurin ta nufi dakinta . Parlour ya saura daga  Zeenat sai fk.yana Ganin ummi tashiga dakinta yasa ya juyo yana fuskantar Zeenat yace sister wajenki nazo fa . tace to Allah yasa dai lfy yace lafiya nasan zakiyi mamakin zuwa na ? Tace bawani mamaki kila akwai abinda kake son nayi maka ne . yace ba wannan bane nazo ne dan nasanar miki da wani abun alkhari koda yake bansan yadda zaki dauki abun ba. tsab Zeenat tagane abinda yakawo shi gabanta taji ya tsananta faduwa ,. fk yace deeni ya duba duk cikin yan’mata dake cikin family din nan. yaga babu wacce tayi masa km tadace dashi sai ke. Zeenat ta zaro idanu waje kmr da gaske ta nuna kanta tace ni fa kace yana so… Fk yace bawani abin mamaki bane , Dami kika tsinta a kala ,a ranta tace maganar ka gaskiya. fk yace yanzu me kika gani idan kin amince , magana zata wuce gurin big dady kai tsaye batare da bata lokacin ba . ta tabe bakinta kmr batayi murna dajin zance ba , sannan tace gaskiya kagaya masa kawai yayi hakuri danni narigada na tsaida wanda zan aura ,. 
 • fk yace waye shi kuma a ina yake km kin kai maganar wajen big dady ne? Duk alokaci yajero mata tambayar ,tace Ko daya muna dai shirin yin haka fk yace  shi din wanene tace wani ne acikin family dinmu yake humm yace inbaki shawara ta daga masa kanta” zan so ki dakatar da koma waye. dan kowa zaki aura ina tabbatar miki ba zai taba kai kmr DEENI ba. ke kanki kinsa samun irin su DEENi sai an tona. zakiyi alfahari samun mijin kmr sa “mata dayawa suna ,sonshi ban sani ba kodan sun fahimci qualities dinsa ne . 
 • sai km yace amman bazan takura miki ba in kinga bakison shi Shikenan . 
 • ta kalleshi a shashance hade da wani irin salo sannan tace nifa bance maka bana son shi ba na daice kawai kace masa na tsaida wanda zan aura ne
 • Kaga yanzu idan na canza ra,ayina da sauri haka shi saurayin nawa bazaiji dadi ba. 
 • ka dai bashi hakuri Allah ya hada kowa da rabonsa na alkhari. fk yayi shiru yana cizan yatsa hankalinsa yasoma tashi “karfa yarinyar nan ta kwafsa masa yazaci yana mata zancen zata amsa da murna ya fadi haka a kasan ranshi. can km yace to ni yanzu mekike son nace masa ? Ta sake tabe baki tace Kafada masa gaskiya kawai ,yace ba za kiyi tunani akai ba kafin ki yanke hukunci ,ko km kuje kisamu wanda kika san kin amince mata tasan deeni din 
 • sosai tabaki shawara akai, Zeenat tace naji zanyi tunanin . Fk Yace Shikenan zan sake nemeki zuwa gobe naji abinda kika yanke akai , tace badamuwa . 
 • Byn ya tafi ne tashiga dakin ummi tana murna cike da farincikin burinta yakusan cika ,fitowar ummi kennan daga bathroom aiko tana ganin yanayinta da alamun tace musu ta amince ,take ta sake daure fuskarta , ta rufeta ta fada, ai gashi nan saboda baisan darajarki ,da kimarki ba sannan bai dauke ki da mahimmanci ba ,yakasa zuwa da kansa sai abokinsa ya turo miki nasan jikinki na rawa kika amincewa ko ?. Zeenat ta bata fuska tamkar zata saki kuka tace nifa ba wani rawarjikin danayi . ummi tace wlh kiyiwa kanki fada, akan sakarcin da kikeyi ke kmr ba macce ba. 
 • sam bawani jan aji irin na sauran mata. 
 • Zeenat ta sake bata rai sosai . ummi tace gaki nan ga deeni ,inda shine nabarki dashi ya isheki wando da riga. 
 • A waya DEENi yaji duk yadda sukayi ya dinga mamaki wai wannan yar yarinyar ce zata ce sai tayi shawara to dawa zatayi ? Kuma itace wa ? Fk yace itace mace deeni yace dan Allah malam yimin shiru shiya sa fa kaga bazan iya kai kaina gareta da sunan Ina sonta ba bare tamin salo . Nan km yau zazzagawa fk maseefa yana Ai shi yaja masa duk wulakancin da’aka masa fk yace kwantar da hankalinka kabarni daita kawai nasan zata yarda ma kawai dai itama so take ta nuna mana itama macce. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]