[Advertisements⬇️]

WANI AURE CHAPTER 7 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 • WANI AURE • CHAPTER 7
 • Tare zeenat sukajero da shemah” suna kuka saboda marin da yaya DEENi yayi musu yashigi kowannesu” amman hakan bai hana zeenat aikawa shemah da zagi iri iri ba” her suka karaso parlour” inda ummi ke zaune tayi xuru …hade da zubawa sarautar Allah ido abinda ya faru Yayi maseefar girgiza zuciyarta. kirasu ummi tayi tana sake tambayar su” abinda ya hada su fada haka” alhalin da can ba haka sukeyi ba,. shemah ce tasoma magana cikin kuka Allah ummi ni bansan nayi mata wani abu ba” kawai ganinta nayi tafito daga daki” tana wasu abubuwa ,daga nan Kuma sai ta hau ni da zagi ,. zeenat zatayi magana ummi “ta katseta tace ya isa

  bansonjin komai daga bakinki . dan ta fara zargin wani abu dangane da abinda ya faru yanzu ” ummi tayi musu fada sosai da nasiha mai ratsa jiki .

 • tace karta sake ganin sunyi fada dajuna , shemah ce kawai ta iya amsawa tayi wa Ummi sallama ta wuce Amman ita zeenat kishi tattare da kunar zuci suka taru suka tsaya mata a kirjinta hakan yasa takasa cewa komai .
 • K0 byn fitar shemah ma “zeenat tsaye tayi tacigaba da kukanta tana jin haushin ummi data hanata yin magana ,alhalin gaskiya tana Gani .
 • yatsun DEENI ne kwance a gefen fuskarta wanda ya haddasa wajen dan tasawa ,dan gabadaya fuskarta ta canza kala tayi jazir
 • tun Ummi najin haushin kukanta nata har ta dawo tausaya mata dan tasan , ta daukar ma kanta wahala ne in dai akan DEENi ne .
 • Ummi na kallon yatsun DEENi kwance a fuskarta take taji wani abu ya tsarga mata ” har cikin zuciyarta taji kmr ta zubda hawayen takaici kiran sunanta tayi hade da nuna mata guri zama kusa daita.
 • cikin sanyi jiki zeenat ke daga kafafunta inda take tsaye har ta isa inda Ummi ke zaune ta zauna “kmr yadda ummi ta umarceta , Ummi ta zuba mata idanu kawai tana kallonta dan abun nata na neman fin karfinta “tsawon lokacin zeenat tana risgar kukanta ,batare da ummi tace mata komai ba , sai da ummi ta gama nazarinta tsab sannan tace duk wannan kukan na meye haka ? Kar kice min duk akan son DEENI kike neman yin fada da er’uwarki . Saboda Allah Ke k0 kunya abinda kika aikata bakiji ba . ” zeenat tayi shr takasa cewa komai dan ita kadai tasan yadda takejin zuciyarta,. Ummi tace meyasa zeenat , meyasa bakya jin maganata ne ,irin abinda zaki min kennan ko wannan shine kalar tarbiyar dana baki uhmm ?
 • kina ganin haka kawai zanki amincewa da auranki da DEENI ne” kiyi tunanin mana. koda yake baki san ciwon kanki ba shiyasa. ‘ballanantana” kisan gata neke miki .
 • mutumin da bai san da zamanki ba, bai damu dake ba” k0 kallon arziki baki isheshi ba” shine zaki zauna kina westing din hawayenki akansa takarasa fadar maganartana takaicin zeenat,. ” Ummi ta sake maida dubanta sosai gareta tana mamakin yadda zeenat din ta canza cikin lokacin kadan .Alhalin ita duk iya lokacin ta dauka tare da yarinyar bata taba ganin irin haka atattare daita ba cikin kuka zeenat tace ummi kinki amincewa da aurenmu da yaya DEENi . ai gashi nan ai …… sai kuma tayi shr” dan jin kunyarabinda take kokarin son fadl’ “dan haka tacigaba da sheshekar kukanta,.
 • ” Ummi tace uhm Ina jinki kakarasa mana , tace wlh wlh Idan kika kuskura” kika bari
 • yasan kina wannan” haukar akansa ” kin shiga uku da wulakanciinsa ” .
 • zeenat ta zube nan kasa tana kuka hade da kamo kafafun Ummi.
 • tace dan Allah Ummi ki Amince da maganar yaya kinji “wlh ni Ina sonshi a haka ” kiyi mana addu’a kawai” babu abinda zai faru inshallahu .
 • Ummi ta sake zuba mata idanun tana kallon sarautar Allah, da rashin kunya irin ta Zeenat su fa daman yayan zamanin nan ba wata kunyace ta ishe su ba . ,ummi tace” da bai ce yana sonki ba fa ?
 • Ta jeho mata tmyr ” data girgiza zuciyar Zeenat ” din” tayi kasa da kanta tana zubda kwalla ita fa ganinta bbu abinda tayi . a ranta ko cewa tayi ai shima yana sona tunda ya iya furtawa .
 • Ummi ta sake kiran sunanta tace zeenat idan bakiji kunyata” a matsayina ta mahaifiyarki ba ” , Ai kya ji kunyata ta ummin DEENI . amman tunda kin nacewa auren DEENi kuma kinji” kin Gani to wlh duk abinda kika Gani Shikenan , . dama sharadi kozan amince da auranki dashi .
 • Banda zuwa kawo kara kum duk abinda yabiyo baya babu ruwana ciki sai dai ki haye abinki tunda shi kika zaba .
 • da sauri zeenat tace to….ummi indai kin amince bbu ma abinda zai faru sai alkhari. Wani irin kallo Ummi tabita dashi wanda da Gani kasan na tausayi ne.
 • Dan yanzu ta daina mamakin duk abinda zatayi . da murna ta tashi ta koma bedroom tayi kwanciyarta tanajin dadi Ummi ta amince da aurenta da yaya DEENi . idanunta ta lumshe” tanajin Yadda soyayyar DEENi ke sake huda zuciyarta . .
 • Yinin ranar da murna zeenat tayi shi cike da tsantsar farinciki ga tarin tunanin DEENi dake sake mamaye kowane part na jikinta yau tazo mata da abubuwa masu yawa bacin rai da farinciki .
 • duk abinda takeyi Ummi na hankalce daita . kallonta kawai take tana binta da idanu . 
 • Washegari zeenat“ ta zaci ummi zata sanarwa yaya DEENi cewa ta amince” sai kurum taji ummi ta share da zance gabadaya , koda dai da wuri yake flta ,. 
 • wasa wasa ummin ta share da maganar kwata kwata harkar gabanta kawai take , . tanajin lokacin da dama idan yaya DEENi ya dauko mata maganar zata katse shi tace kar ya dameta ya rabu daita . 
 • saidai abun yana damun zeenat matuka yadda kullum yaya DEENi ke sake daure mata fuska da wulakanci iri iri. Amman takan masa uziri ganinta kila sai lokacin da ummi ta amince masa ‘ sannan zai daina nuna ko in kula dayake ,mata. 
 • shi kansa yaya DEENi baisan cewar zeenat din tasan da zance ba. kullum dai ya shigo wajen ummi sai yayi mata nacin ,shifa yana nan yana Jiranta. 
 • ita kuma tace karya dameta bayace yafi son Yarjami’a ba. 
 • “to yaje ya nema Amman ita sam bazata bashi diyarta ba ,. yana fita zeenat ta matso sosai kusa da ummi tace ummi dan Allah bakince ,kin hakura ki amince tunda na yarda ba. 
 • sai ummi ta dube tana watsa mata harara tace sakariya banza kawai”. kalli fa ko kallon arziki baki isheshi ba .Amman duk kinbi kin tsamgwami kanki .dan nuna tsiya da jaraba , . ni duk abinda nake Ina yi ne “dan Kare matuncinki , ba dan Ina kin aurenki da DEENi bane. 
 • tunda yashiga dakinsa bai sake fitowa ba” sai dai yatashi” yayi sallah kawai yakoma gado . yasawa ranshi, cewa ya hakura daita kwata kwata dan baiga dalilin da zai sa shi ya dinga batawa kansa lokaci ba . 
 • Kwance yake akan makeken royal bed dinshi ya rufe kanshi cikin alky blanket mai matukar taushi ,. bacci yake Sosai hankalinsa kwance ya rufe koina najikinsa banda fuskarsa saboda yanayin unguwar su mai’ dauke da sanyin ni’ima ,. 
 • ahankali ta bude Kofar dakin” kwance ta ganshi, yana sharar baccinsa ,sai yanzu hankalinta ya kwanta gangarjikinta yasamu natsuwa , kusan kwana biyu kennnn rabon data sashi a idanunta,. 
 • ahankali take daga kafafunta har ta isa inda yake,. kwance idanunta ta zuba masa” ido tana kare ma kwakkywan fuskasa kallo yadda tayi kyau tana fidda annuri na musamman. Ahankali ta bude idannuta suka sake sauka akan beautiful face dinshi ,. fuskarsa ta kurawa ido harwani kyalli kyallin kyauwu take fitarwa , cikin rawar hannu takai hannuta gefen fuskarsa ta dan tashafo. wani irin taushi taji wanda ya sake dulmiyar daita a duniyar kaunarsa. Take taji koina na jikinta ya mutu sai wani yammmmuu takeji. ita kanta tarasa dalilin dayasa takejin haka ajikinta. ganin bacci yake sosai yasa ta juya ahankali tabar dakin cike da shaukin soyayyar DEENi 
 • dama Ummi ce “tace ta dubashi dan har lokacin fitarsa aiki na neman wucewa . 
 • Koda ta sanar da Ummn cewar baccin yake har yanzu, yasa ummi ta nfi dakin” dakanta kusa dashi taje” kai DEENI sai data kira sunanshi” kusan sau biyu” sannan ya dan bude gengerous eyes dinshi ya kalleta dashi “tace laflyarka da haryanzu dabaka tashi ba , . tacikin blanket din ya dan yi Mika hade da salati sannna ya dan gyara kwanciyarsa yace lfy first lov ,natashi har nayi sallah ” to bazaka aiki bane yace zani. Ummi tace Ina jiranka idan kagama. ya amsa mata da to kai kawai. 
 • a hankali ya zamejikinsa daga cikin blanket din , daga shi sai dan gareni wando Mika ya sake yi yasa hannunsa ya gyara jijiyarsa dake mike . Sannan ya shiga bathroom,. duk da yamakara hakan bai sashin yin sauri ba, wanda normally haka yake da sanyijiki . wanka yayi, ya fito. ya shirya cikin kakinsa da suka dace da surarjikinsa, har ya murda handle din kofar “dazata Kai shi parlourya tuna Yayi mantuwar wasu files a dakin baccins” 
 • dan haka yakoma ciki daukowa 
 • Tsaye take a bakin kofar dakinsa tafi kusan minti biyar a wajen tana saka dawarwara yadda zata sake shiga Bedroom din sa. ummi ce tasake aikota. 
 • Ta dubashi dan taji shiru har yanzu. 
 • tana son tayi nocking Amman tsoro da fargabane suka hanata. daidai wannan lokacin DEENI ke shirin fitowa daga part dinsa . ta daura hannuta kan handle din kofar. ai agigice cikin matsanancin tsoro tasaki wani irin kara da tasa DEENI , tushe kunnuwanshi ” da duka hannushi “ai batasan sanda ta fada saman fadaden kirjinsa ba . hade da runtse idanunta gam dan tsabarjin tsoro , batasa abinda zai mata ba Jira kawai take taji saukar mari dan gabadaya tagama firgicewa. 
 • Amman abin mamaki sai taji sabanin haka.shiyasa tasaki jiki ta sake narkewa a fadadden kirjinsa tana shakar dadeden kamshin turarenn jikinsa mai birkita mata tunani “a duk sanda ta Shaka . 
 • wani irin ya dinga ji ajikinsa, yrrrrrrrrrrrrr…. yrrrrrrrrrrrrr abinda bai taba faruwa dashi ba kennan” jikinsa ya hadu da wata macce” shi tunda yake ma ko hannun macce bai ta ba rikewa ba ballanantana yakai ga hadajiki . Ya dingajin wani irin a gangarajikinsa. 
 • gabadaya tsigarjikinsa suka mike tsaye , yaji da zai iya ” rungume ta zai yi kawai . ko zai ragewa zuciyarsa radadi da ciwon dayakeji. Amman Ina… Sam bazai taba iya aikata hakan ba . ganin yadda tayi lamo ajikinsa ne yasa, cikin takaici ya bambareta daga kirjinsa cikin tsanyijiki, tsayuwa ce ta gagareta , zuciyarta ke neman tarwatsewa tsabar tsoro da rikincin data tsinci kanta ciki. ,ko ta kanta bai bi ba ya tsuke fuska yana kallonta ,itama idannuta ta zuba masa ko kiftawa batayi. ga wani irin tsoransa dake lugudar zuciyarta. ahankali muryasa a sanyaye yace malama ki daina min “irin wannan kallon na munafurci. in ba haka ba na kwakule idanun rashin kunya tsaki yaja hade da bin gefenta yazagayeta ya wuce kai tsaye part din umminsa yashiga” sai dai bai ganta ba,. dan haka ya wuce main parlour ‘dan yasan tunda bata dakinta, tana can. zaune yasameta tana yin breakfast fuskarsa a dan sake yakarasa har kusa da ita ya zauna yace gud morning my first lov, ta dubeshi fuskarta dauke da murmushi tace morning dear kata tashi lfy girarsa ya dage mata. cikin tsnayin jiki zeenat takaraso wajen, kallo daya DEENi Yayi mata yasa ta canza hanya batare da ta sake kallonsa , kan wasu kujeru dake ajiye a gefe ummi tabishi da kallo batare da tace masa komai ba ” da kanta tayi saving , din shi ,shi kuma sai wani zuba mata shawaba yake,. coffee kawai ya iya sha, ya mike tsaye cikin hanzari sakamakon wayarsa data dauki kara yana dubawa yaga ogansa ne daga wajen aiki . 
 • dan haka yayiwa umminsa sallama da hannushi ya fice wayar manne da kunnenshi . Zeenat data zuba tagumi ,Da hannu biyu tabi bayansa da kallo har yabar gurin idanunta na kansa , itama ummi data dauke idanunta daga kan DEENI “zuru tayi tana kallon Zeenat din , tana girgiza kanta . waskewa zeenat tayi hade da sakarwa ummi murmushin dole ummi tayi mata dakuwa da hannu . 
 • Byn DEENi ya gama amsa wayar oganshi ne yana zaune cikin mota wayar fk yashigo ” yasa hannu ya dauki wayar ya duba ganin fk ne yasa ya maida wayar ,mazauninta . Yakirasa yafi sau gomasha daya Amman yaki pic sai a karo na shabiyu ne ya danna wani abu “sai ga muryar fk radau yakarade koina a motar , hello…. hello DEENi kanajina Yayi shr yaki yin magana,sai ma cigaba da yayi ” da direving dinshi. 
 • fk yace haba DEENi ya kana jina zaka min shr. “duk fa” maganar bata kai haka. 
 • Ba afusace DEENi ya katse shi yace maganar ma haka harta zarce haka a waje na. km wlh wlh karka kuskura, ka tako inda nake da sunan kasan ni ai bansa cewarda kungurumin ,dan iska nake zaune ba. fk yayi murmushi yace Allah dai ya huci zuciyarka ,dan shi. bai fiyye fushi ba” kwata kwata ma bayason duk wani abinda zai kawo masa tashin hankali 
 • dan haka yayi tabawa DEENi hakuri hade da bashi baki . DEENi yaja numfashi ya sauke ajiyar zuciya . hakan yasa fk ya gane cewar ya sauko kennan fk yace to yanzu yazamuyi da maganar da big dady yace. 
 • DEENi ya tabe baki yace ya dai zakayi dan ni tuni na hakura da wannan yarinyar , karma ka km yimin wannan banzar zance. 
 • daidai da yakarasa wajen aiki ,ya katse wayar fk batare daya tsaya ji mai fk din zai kumce masa ba. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]