[Advertisements⬇️]

WANI AURE CHAPTER 5 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 • WANI AURE


 • CHAPTER 5


 • Zeenat kwance a bedroom din ummi hannuta rike da wani English novel face to face tayi zurfl cikin karatun novel din saboda yadda take enjoy din novel din ya .
 • Yaya DEENI ne yashigo gaishe da ummi kafIn yaflta aiki ,byn sun gaisa ne ummi tace har ka shirya fita kennan ? Yace mata eh sannan yaja ya tsaya ya zubawa ummi idanunshi .
 • ummi ta dubeshi tace da magana ne ? Tunda tarigada tasan muddin yayi shr irin haka to da magana a bakinsa.
 • koda yake tasan dai zance nasa bai wuce maganar zeenat bane ” Kuma daman tana son zeenat din tajida kunneta idan ta amince ruwanta ” dan haka ummi kalleshi da kyau tana nazarinsa ta numfasa sannan tace masa kayi shr alhalin nasan da magana abakinka .
 • muryasa a shagwabe yace first lov kan dai maganar zeenat ne ,dan Allah first lov, ba yabon kai ba “inada qualities din da za’a bani auren kowace irin mata nake so” Kuma k0 Yar gidan waye ,. Yar taki ma daba wani kyau ne da,ita ba” dan ma zan taimaka mata “ya fadi haka fuskarsa a hade ,. ummi tace duk da haka day bazan bada diyata ba kaje waje ka gwada sa’ar ka” wai ma in tambayeka DEENi yamaida hankalinsa sosai ga umminsa” tace kai da kake ta damun kanka da zance nan kullum. kasamu ita yarinya da maganar ,kun daidaita kanku ne? DEENI yace uhmm kece dai zaki sanar mata, ummi ta nuna kanta da dan yatsanta, nice ma zan tayaka yakin nemar maka soyayyarta” lallai ma bason auren nata kakeyi ba” kashare zance kawai tunda baka shiriya neman aure ba. yace to ni first lov in na fada sai naga tamkar Raina ni zatayi, ummi tace kunji girman kan ba a hassale ummi tace dan Allah kayi hakuri kabar zance nan. haba duk kabi katadda hankalinka da nawa. yarda ne dai bazanyi. dan haka kayi hakuri kabar zancen nan kwata kwata dan ba yarda zanyi ba .

 • DEENI daya gaji dayiwa ummi magiya ya hakura yai ficewarsa ,yana jin takaici kansa, tunda daga lokacin da zeenat taji DEENi ya ambaci sunanta ta mike zunburzaune daga kwanciyar datayi, hankalinta a tashe jikinta har rawa yake tsabar rudewa” ita zeenat din yaya DEENi yake nufi ko wata daban.
 • ahankali ta furta inko ita yake nufi dakuwa ta more a rayuwarta, dan gaskiya yaya DEENi ba irin namijin da mace zatace bataso bane , ahankali ta sake furta A’a dan Allah ummi kada kimin bakinciki mana. tana jin fitarsa ta fito da sauri daga dakin tana kallon ummi dake zaune tana jan carbi, zatonta ko ummi zata mata maganar ne. Amman sai taga sabanin haka. dan kuwa ummi ko kallon inda zeena take tsaye batayi ba. dan tarigada tasan taji komai” to Kuma bayanin me zata tsaya yi mata. Ta dai yi shiru ne taga yadda zata dauki lamarin . Can kuma, ummi ta dago tana duban zeenat din tana nazarinta“ yayinda zeenat din itama ummi take kallo” har zuwa lokacin ummi batace komai ba. sai ma kau da kanta gefe datayi ,ganin ummi batada niyyar ce mata komai ,yasa zeenat kira sunan ummi” tajuyo tana duban zeenat din da kyau”. ahankali cikin sanyi murya tace ummi wai wata zeenat din yaya DEENi keso? Ummi ta dan tabe baki sannan tace dan Allah rabu dashi wai ke yake so “da aure zeenat tasa hannuwanta duka ta dafe kirjinta dasu tana zaro idanu waje “tace da gaske ni yakesoummi tace zan miki karya ne” zeenat ta marairaice murya tace shine Kuma ummi zakice masa baki yarda ba
 • ummi tace to may kike nufi kina son kice min kina son DEENi kenan ? Zeenat Tayi shiru dan bata da amsar bawa ummi dan gabadaya ilahirin jikinta bbu inda bai dauki rawa ba. ummi ta sake yin magana daman kina son DEENi ne naga duk kin tada hankalinki haka ? zeenat tace nifa bance ina son shi ba Amman ke meyasa zakice A’a Kuma ma mayye dalilin dayasa kika ki amincewa ,ummi tace ok tutseni zakiyi” kan naki yarda ko yaya , zeenat tace ba haka bane” ummi tace tsaya ma kiji abinda yasa naki yarda, DEENi “da” nane’ ni haife shi da cikina sannan ke ma kinsa halinsa sarai da shege miskilanci da saurinjin haushi mutun ,abu kankani ke hassalashi ga tarin girman kan tsiya, zeenat ta tsugunna nan gaban ummi hade da kamo hannuwan ummi duka cikin nata muryarta sanyaye tace haba ummi dan dai kawai saboda wannan halin nasa ne “zai sa kike amincewa , in dai dan haka ne’ ni na amince da aurensa kinji. ummi tace duk kinbi kin koma kalar tausayi wai ma meyya birgeki da DEENi ne naga duk jikinki ya dauki rawa haka ?. Zeenat tace ai gaskiya yaya ba irin mutunmin da za’a tsaya cewa ba,aso bane ni dai na amince ,ummi tace ko kin amince, ni nace A’a ban yarda ba ,. Zeenat ta mike cikin fushi tayi bedroom din ummi. da kallo ummi tabi bayanta dashi ummi taji matukar mamakin ganin reaction dinta musamman da tasan zeenat din ,bata fiyye nuna fushinta akan abu ba . Koda tashiga dakin ma waje tasamu ta zauna abunta tayi tagumi batayi aune ba, kawai taji hawaye na silalowa mata. ita kanta tasha mamakin ganin hawayen na zuba a idanunta “ta tambayi kanta to daman
 • can tana son DEENI ko yaya? domin abun itama yayi maseefar daure mata kai “. 
 • kuka takeyi ” iya karfinta hade da ganin laifln ummi din ,to meyyesa ummi zatace batason aurenta da ya’ya DEENi byn ita tasha kisma haka a ranta. taci kukanta sosai har sai da taji alamun kanta ya fara mata ciwo ta runtse idanunta sannan ta kwanta “nan a gefen bed din ummi tacigaba rera kukanta kasa kasa. 
 • Yinin ranartayi shi ne cikin daki hade da tunanin DEENi da kitsima kalar rayuwarda zatayi a gidan DEENi. Da zarar taga ummi kuwa take hade fuskarta sabodajin haushin abinda tayi “. kusan zuwan Maryam uku gidan “Amman zeenat taki saukowa kasa” dan gabadaya takasa samun sukuni gabadaya haushin kowa takeji. 
 • ,ita kuwa ummi sai binta take da idanu dan ma kasa magana tayi , gashi ranar Sam DEENi ma kin dawowa yayi da wuri sai wajen shabiyu , . haka ma washegari tun asubar fari yabar gida ya dai shigo ya gaida umminsa a tsaitsaye. 
 • ,byn ummi ta idar da sallah ne kafin ta soma lazimi , yayinda zeenat ke kwance akan bed , idanunta a runtse tamkar may bacci Amman Kuma ba baccin take ba. 
 • ummi takira sunanta kusan sau uku Amman tayi mata shiru alhalin tana jinta. 
 • ummi ta sake kiran sunanta tace zeenat nasan kinajina Kuma idanunki biyu Amman kika min banza , hade da ganin laifina . 
 • bakomai yasa kika ga naki yarda da maganarki da DEENi ba” nasan halin DEENi ciki da bai bashida dadin sha‘ani kwata kwata gashi da bakar zuciyar tsiya azo ayi auren nan yazo yana 
 • gana Miki azaba,. ni.. nasan abinda nake gudar miki Amman indaii kinkiji ke kika sani , kije Allah yabada sa’a. Amman ki sani idan akwai wanda zaiji dadin aurenki da DEENi a bayana yake, Amman duk da hakan bazai hanani fadar gaskiya ba idan tazo. 
 • Kuma shawarata gareki ki rage rawar kai dan idanya fahimci haka zaki sha wulakancin, daga karshe kuma mutuncinki ya zube a gurinsa. ga zaton ummi zataji zeenat din tace ta hakura da auren DEENi din ne Amman sai ganinta tayi ta duro daga kan gado ta zube gabanta durkushe. 
 • ,taji tace idan dai har kin amince ummi inshallahu bbu abinda zai faru. 
 • Ummi tayi shiru ta tsura mata idanu tana kallonta ummi tace kina nufln kin amince zaki auri DEENi kennan ? Zeenat tayi shiru takasa cewa komai  sai karyar da wuya datayi , ummi ta sake duban tace ke..bafa zan yarda da auren nan ba .take zeenat ta fashe da wani irin kuka tana bawa ummi hakuri ta amince dan Allah abin ma ya daina bawa ummi mamaki , yadawo bata tsoro ,. Cikin kuka zeenat ,tace ai shi yace yana sona ” to ta yaya ke zakice A’a ummi tabita da wani irin kallo tausayi , aranta kuma tace ya‘yan yanzu sam basu da kunya .wani irin son zeenat din ne taji yana ratsa ko wani part najikinta. ga tarin tausayin yarinyar dake matukar damunta .Amman hakan ba zai sa taji zata iya amincewa da muradinsu ba . ta kau da tausayin yarinyar a ranta ta hade fuskarta tamau ,sannan tace ke dan ubanki akan na hana aurenki da DEENi ne zaki ,ta sani gaba da kuka “dan bakisan ciwon kakin ba ,danma ke shashace ko shi dayace yana son naki” bawai damuwa yayi dake ba. tunda har zuwa yanzu bai kawo kansa gareki ba. sai kece zaki wani damu mutane da kuka akanshi ,cikin wani irin sabon kukan zeenat tace bagashi ke yayi miki maganar ba. Ummi tace OK dan yayi min maganar shine may . ni zai aura ko ke ,da kyar ta iya sausauta kukanta sannan tace ummi dan Allah ki amince mana tunda day har shi ya furta da kanshi”. ummi taja tsaki ta mike tsaye tace ni matsa, ban waje tun banyi ball dake ba shashar bazan kawai.ta wuce parlour tabar zeenat din nan durkushe. aiko zeenat naganin haka ta fashe da wani kukan har da shesheka. 
 • Da daddare misalin karfe tara ,DEENi zaune a parlour shida ummi suna kallo Amman jifa jifa take sako masa hirar duniya ” shi dai jinta kawai yake , yayi tamkar bbu abinda ke damunsa Amman shi kadai yasan abinda yakeji aransa’ zeenat ta hado masa coffee tazo har inda yake zaune ta ajiye masa nan kusa dashi tajuya zata bargurin ko kallo bata ishe shi ba ballanantana yasan ko ita wacece, hakan da yayi ne yasa ummi taji ba’adadi aranta. muryarsa a kwausashe yace ke ….. tajuyo ahankali hade da zuba masa idanunta shima ita yake kallo da ritattun idanunsa ,yace dawo ki dauki abinki konace miki ina bukatane” da sauri zeenat ta girgiza kai, ya kau da fuskarsa kamar bashi yayi maganar ba . 
 • bai sake cewa komai ba ,kuma bai kalli inda ummi ke zaune ba,ya mike kan three site yayi kwanciyarsa ” aransa yace akanki zan dinga huce takaicin abinda ummi tamin” tunda tace bazata auramin ke ba. 
 • nima na hakura da auren naki” sai tajikaki tay tasha. 
 • kunya ne hade da tsoro suka taru sukama zeenat rubdugu , taji gabadaya kakafunta sun Gaza daukarta ” ana cikin haka shemah tashigo da sallamarta “kai tsaye wajen ummi ta nufa ta zauna tana gaishe da ummi “ta amsata cikin sakin fuska ,. 
 • ,sai sannan tajuyo tana kallon inda zeenat ke tsaye kikam tamkar an dasata’ kuma sai a lokacin idanun shemah yaKai ga DEENi,dake kwance idanunshi a lumshe. itama idanu ta zuba masa tana kallonsa , tana jin wani iri ajikinta yayinda gefe daya zuciyarta ke wani irin dokawa da sauri da sauri ” shi kuma kwata kwata bai ma san Allah yayi ruwan mutun a gurinba ” ahankali ya mike tsaye yana wa ummi sai da safe “a ciki ta amsa masa dan takaicin abinda yayiwa zeenat ” suna hada ido da ummi yasakar mata murmushin gefen baki hade da kashe mata idanunsa daya wanda ita kadai tagani ” da sauri ya haye step ,. 
 • yana barin wajen atare suka sauke ajiyar zuciya daga zeenat din har shemah ” . 
 • dan har gara shemah ma akan zeenat din dan ita gabadaya a frigice take “idanunta ta dan juya da niyar satar kallon inda ummi take , ai ko take suka hada ido daita ummi ta kalli zeenat din tana watsa mata harara dan gabadaya tagama bata haushi. 
 • yana shiga dakinsa ya fada kan bed dinsa yajawo system dinsa kenan idanunsa yaKai ga phone dinshi dayaga almost 12 miss call da sauri yasa hannu ya dauki wayar yayi dealing number daya Gani bugu daya biyu “fk ya dauka yace ka kyauta angon zeenat” bukatarka ,ta biya ai dole kashare mutane. DEENi yaja tsaki mtssss sannan yace dan Allah ni rabani da wannan zancen naka na banza” haka kurum kasa mutun a one chance,. gashi kaja wa mutun wulakancin kawai ,fk yace wulakancin Kuma a gurinwa DEENi ya tabe baki tamkar fk din na ganinsa sannan yace a gurin ummi mana. to meyya faru inji cewar fk. sai da DEENi yajima bai yi magana ba kam daga baya ,yaja wani irin numfashi yace ummi fa taki amincewa da shawarka ,sai ma wani yawo ake min da hankali kamar za’a bani gold. fk ya kwashe da dariya yace mutumina kodai ka zurma ne, irin wannanjin haushi haka. DEENi yace kai nifa na hakura da yarinyar nan wlh ,dan gaskiya bazanjura wannan wulakancin ba . ga mata nan dayawa a waje suna bina kamar su lashe ni ” fk yace tsaya ranka ya dade ba haka za’a yi ba, bari zamu samu big dady da zance nasan komai zaizo da sauki. ko Kuma kai me zai hana kasamu zeenat din da kanka. DEENi ya sakejan tsaki yace maganar banza kennan ai inda takaicin yake kenan haba ai kauyancine a wajena na tsaya ina gayawa wannan yar karamar yarinyar kalmar so . fk yace kaji irin ta ko kana son yarinya Amman girman kanka na neman cutar dakai “DEENi ya katseshi ” hade da cewa kai fa dan matsala ne , nasha gaya maka ka daina cewa ina son yarinyar nan, zan dai aureta ne kawai fk yace Shikenan ajiye wannan zance. bari gobe inshaallahu zanzo muje gurin big dady DEENi baice komai ba ya katse wayarsa. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]