[Advertisements⬇️]

WANI AURE CHAPTER 4 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 • WANI AURE








 • CHAPTER 4




 • Har DEENi yazo gida tunanin yake akan shawarar da fk ya bashi” anya kuwa zai iya amince da auren zeenat?

 • Lokacin da yashigo yayi daidai da zeenat tana bare magani tana mikawa ummi ,ta amsa ta sha zeenatta Mika mata ruwa ,yayinda shi kuma yake tsaye jingine da jikin kofa rungume da hannuwansa duka a kirjinsa yana kallonsu, take zuciyarsa ta dinga ingizashi akan lallai bbu wace ta dace ya aura sama da zeenat bisa ga hujjarsa tacewa ,bazai taba samun matsala daita gurin kula da mahaifiyansa ba saboda irin soyayyar dake tsakaninsu

 • yasan ko yana nan ko baya nan zata kula daita, umminsa zata zamo a karkashin kulawarta tunda zeenat bata da wata uwar data wuce ummi tunaninsa ya katse lokacin da ummi takira sunansa’ tace son karaso mana yayi frigigit ya dawo natsuwarsa ahankali yashiga takowa har inda ummi take ,ya zauna zeenat ta gaidashi ta mike zata fice daga dakin bai amsa mata gaisuwar data masa sai dai yabi bayanta da kallo” ummi ta kalleshi ta kauda kanta, yace first lov yajikin naki ummi ta danyi murmushi hade da daura hannuta kan sumar kansa tace naji sauki sosai , ahankali sauke ajiyar zuciya ko baice komai ba ummi ta fahimci yaji dadin yadda yaganta ,yana nan zaune , Sam yakasa yiwa ummi zance yana san auren zeenat din ,daga karshe ma tunani yayi kawai gara yasamu ya mahamud da zance
 • dan gaskiya kunya yakeji yayiwa ummi maganar da kansa. Da yammacin ranar byn ya dawo daga office yaje har gida yasamu ya mahamud da maganar yaji dadi kwarai da gaske, har yarasa inda zai sa DEENi dan farinciki dan shima da kansa ya matsu yaga DEENi ya ajiye iyali kmr kowani magidanci ,yace Shikenan sai kasamu yarinyar da zance, ku daidaita kanku DEENi yace A’a ina ganin basai na sameta ba in dai first lov ta amince ai Shikenan.
 • yaya mahamud yace ummi bazataki ba Amman dai kasan kaidar auren gidanmu kennan bbu dole a ciki “muddin kuka daidaita kanku na iyayenmu mai sauki ne idan Kuma ita ummi ta amince ita yarinyar tace bata sonka fa? DEENi yaji haushi da takaici alokaci guda yace ai nima ba wai ina

  sonta bane kawai dai zan aureta ne.

 • Yaya mahamud yace shirme baza kennan kai yanzu idan anzo meeting cewa zakayi basonta kake yi ba ,zadai ka aureta ne ?DEENi yayi murmushin gefen baki har dimple dinsa ya lotsa sannan yace cewa kurum zanyi ina son zan aure zeenat ne ‘ Yaya mahamud yace to Allah ya mana zabi na alkhari kabari zanje gurin ummi tukun duk yadda mukayi daita zakaji DEENi yace Shikenan ya mike ya fice ,a office ma koda yaje aikinsa kawai yasa gaba . dan shi gabadaya ya manta da wani zance aure can . Mahamud yasamu ummi cike da karfin gwiwa” ganinsa ba wanda zai kai ummi murna tunda daman burinta kennan naganin auren DEENi, Amman ga mamakinsa yana gama labarta mata abinda yakawo shi, sai yaga ummi tayi kicin kicin da ranta tamkar bata taba sanin wani abu farinciki ba “sai da gaban Yaya mahamud ya fadi dan ganin yadda ummi tayi da fuska tamkar yazo mata da zance mugun abu ” tace kai ne kaga sun dace kaba shi shawara ya nemi aurenta ko Kuma shi da kansa ya sameka da zance?
 • Da sauri yaya mahamud yace A’a shine dai yazo min da zance ummi ta sake daure fuska, sannan tace ka koma ka fada masa ban amince ba ,kace masa akwai sauran mata a gidan nan yana da damar zabar duk wacce tayi masa, idan ma ya canza ra,ayinsa nakin auren family’ to yaje waje ya nemi matarsa can itama Allah zai bata nata mijin, Amman Sam ni ban yarda da wannan hadin ba ” tayi shiru na wani lokacin kana ta zubawa Mahmud idanunta tana kallon yanayin daya shiga ,ahankali ta numfasa sannan tace kana iya wucewa idan kana da abinyi ka manta da wannan shirme na DEENi .
 • Yaya mahamud yayi kasa da kansa Sosai cikin muryasa can kasa kasa da alamun km rarrashi yace dan Allah ummi ki amince da auren nan bazan iya tunkarar DEENi da maganar ba. duk da bansa dalilinki nakin amincewa ba” ummi ta dan saki fuskanta ba kmr dazu ba tana mugun son mahamud tamkar dan da ta haifa acikinta tanajinsa har cikin zuciyarta.
 • tace bawai ina kin hadin bane duk duniya idan akwai wanda zai so auren DEENi da zeenat a bayana yake ,na farko dai kaima kasan halin DEENi da dan bazar zuciya , ga saurin fushi ga maseefar miskilanci tsiya ga jin kai sannan da bakinsa yasha gayamin cewar shi bazai taba yin auren family ba sannan shi mai digiri yake so ya aura ,shine km yanzu zai zowa mutane da wani salo. ni da tawa iya secondary kadai ta tsaya” ai kai dajin zancensa ma kasan akwai wani makirci daya shirya “dan nace yayi aure ai bance lallai sai ya aure tawa yarinyar ba , Muhamud yace ummi ki duba lamarin abun tunda shi da kansa ya furta cewa ita ta masa ba za’a samu wata matsala ba ,. ummi tace Sam bata yarda da wannan tsarin ba ” ita dai yaje gaba ya nema hakurin duniya nan bbu wanda yaya Muhamud bai bawa ummi ba amman taki amincewa ,duk ta inda ya bullo mata sai itama tabiyo masa ta wata hanyar, har ran yaya mahamud yasoma baci ,yaji haushin abinda ummi tayi dan haka ya hakura ya fice ransa abace.

 • DEENi zaune a offlce dinsa ya dukufa wajen tura sakwanni a yanar gizo ,hankalinsa kwance yake bin komai daki daki , yaji daya daga cikin wayoyinsa ,daya ta dauki karar sauti mai dadi ,ya dauke idanunsa daga kallon system din yasa hannu ya dauki wayaryana dubawa ganin sunan dake yawo akan screen din ne” yasa yayi sauri dagawa yakara a kunnenshi hade da yin sallama” kana ina muryar Yaya mahamud yaji ta daki dodon kunnenshi cikin sanyi murya DEENi yace ina offlce yace ok idan katashi kabiyo inason ganinka sannan ya kashe wayar .
 • DEENi zaune a gaban Yaya mahamud kansa sunkuye a kasa yayinda idanunshi ke kallon zarazaran yatsun kafafunsa yana sauraron sakonshi da ummi tabayar a sanar dashi.
 • a gurin Yaya mahamud sam bai tsammaci jin haka daga umminsa ba ,ga mamakin Yaya mahamud sai yaji deeni yace Shikenan babu komai Allah yasa haka shine mafi alkhari. ya mahamud yace ka hakura kennan? Nashi ganin bazai damu dan ummi ta hanashi auren zeenat , dan haka Yace eh “tunda daman ba wai yana sonta bane” nan dai suka bar zance aure suka shiga wata hirar daban a inda Yaya mahamud ya tashi yaje ya kwaso wasu takardu da file files ya zubesu nan a gaban DEENi yace yasa masa hannu ciki ” kai tsaye DEENi ya zaro wani hadadden Biro daga gaban aljihun rigarsa yasoma cike gurraren da akeso yayi sign, dan gabadaya dukiyar DEENi ,sulaiman da Muhamud ne akai su suke kula daita kuma komai na tafiya daidai ” domin dukkannisu abu guda ne a gurin ummi dan ma idan ba’agaya maka ba… zaka dauka duk ummi ce ta haife su .
 • Sai da DEENi yagama sign din ,sannan yaya mahamud ya hada da mishi bayanin companies
 • din da suke son budewa a kasar American, sun turo musu da sako akan suna da bukatar mutun daya daga cikin masu company din ” yazo interview dan haka shi ya wakilta sulaiman yaje , DEENi yayi murmushin yace Shikenan bbu komai duk yadda kukayi ,daidai ne Allah ya taimaka. 
 • To byn DEENi yakoma gida ya dingawa ummi wani irin kallon, wanda shi kansa yakasa gane dalilin yin haka, yana son yi mata magana Amman yayi shr ,yayinda zuciyarsa ke kwabarsa akan ya share kawai ai baita kadai bace mace a duniya” daman ai dan ita yake son ya aure zeenat din ,da yaje waje ya aure wata wacce da bai san halinta na boye ba ai gara zeenat din Amman tunda bata so shima ya hakura. 
 • Da misalin karfe goma na dare DEENi sanye da rigar wanka dan fitawarsa kennan daga bathroom ,ya tsaya gaban dress mirrow yana karewa jikinsa kallo hade da zare rigar wanka dake jikinsa” yai saura daga shi sai boxer , yabi koina ajikinsa da turaren Hamilton 27, sai daya kammala da komai na al’adarsa da yasaba yi kafin ya kwanta sannan ya hau kan royal bed din ya Iumshe rikitattun idanunshi, alamun yana son yayi bacci’ sai dai baccin yaki zuwa kawai ya tsinci kansa da tunanin zeenat.ya rinka jinta ajikinsa , yadda yakejinta a halin yanzu bai tsammaci abin har ya zai haka ba ,, 
 • Sosai ya tsinci kansa cikin damuwa ko baya son yarinyar hakika ya tsananta da son aurenta yayi shr yana tambayar kansa abinda ummi take nufi da kin amincewa datayi,shi ya guji big dady da maganar a tunaninsa sai umminsa tafi kowa murna da jin dadi ‘ya dauki tsawon lokacin kwance kamn bacci barawo yayi gaba dashi . “ 
 • Byn kwanaki , DEENi yakasa hakuri da maganar zeenat din kmr yadda yaso shima ta sharewa da zance kawai ya manta dasu 
 • Amman yakasa, ya samu ummi da kansa a wata safiya dayazo gaisheta byn yayi shirinsa na zuwa aiki cikin kakinsa dake kara masa kyau tamkar dan shi kadai akayi“ sai kamshin yake zubawa ta koina “gashin kan nan nasa kwance luf luf luf dasu , duk da bacika yawa sukayi ba ,saboda yanayin aiki “Amman dayake Allah yayi mishi suma takoina ajikinsa ko yayi askin ma baya wani dadewa” gashin zai sake fitowa” sosai yayi kyau matuka ,ita kanta ummi satar kallonsa take harya isota ya sakar mata murmushi tace son kayi kyau sosai fa, uniform din nan nakara maka kyau ,ya dage mata girarsa daya yace Allah first lov yace ai daman can ni din may kyau ne sannan duk maccen datayi dacen samuna , ta gama samun duniyarta sai dai ta nemi lahirarta kawai ” ummi tayi dariya sosai ya kamo hannun umminsa cikin nasa muryasa a shagwabe hade da dan karyar da wuyansa, yace first lov da kanki ma kin yaba dani tace uhmm yabon gwani yazama dole “yace to meyasa bazaki bani auren zeenat ba ? Ta lissafomasa dalilinta kmr yadda ta sanarwa Muhammad ta Kuma sake jaddada masa yaje gaba ya nemi wata Amman banda diyarta ranshi ya baci Amman ya share take Yar fara’a dake fuskarsa ta dauke ” sai dai bai nuna ba , cikin sanyi murya yace to Shikenan ummi na hakura” Amman bazan taba zuwa koina neman aure ba” saboda banida nagartar daza’a soni Kuma bani aure” ummi tace ba fa haka nake nufi ba yace haka ne mana first lov” ina da munanan halayen da ban cancanci abani mata aure ba. ummi tayi murmushi tace nifa bance haka ba yace haba first lov kince mana gashin nan kema da kanki kin hanani taki yar , to waye zai amince yabani yana kaiwa nan ya cire hannun umminsa cikin nasa ya mike cikin sanyi jiki tamkar bai damu ba ,. gabadaya jikin ummi yayi sanyi ita bawai auren ne bata so ba halinsa take gudu ta yaya zata yarda ta aura masa marainiyar Allah yazo yana cutar mata da yarinya. Abin mamaki duk a tunanin DEENi na bazai shiga damuwa ba akan kin amincewar ummi , sai gashi dumu dumu cikin tashin hankali kullun sai yayiwa umminsa naci da magiya akan

 • tabashi auren zeenat ,ita kuwa ummi duk lokacin dataga ya dauko mata zance saita share hade da bata fuska . 



[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]