[Advertisements⬇️]

WANI AURE CHAPTER 3 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

  • WANI AURE  • CHAPTER 3


  • Zeenat na da kyau sai dai ba can ba” fara ce Sol Amman batada dagon hanci wannan bai sa fuskarta muni ba” haka idanunta matsakaita ne ita mutun ce mai tsananin son kwalliya wanda ko alwala Tayi sai ta sake yin wata sabuwar kwalliya, haka nan ummi bata gajiya da siya mata kayan kwalliya iri iri sannan bata ganin aibunta a duk lokacin da zata bata a gurin yin kwalliyar. abinda kawai bata so kuma bata yarda dashi ba, shine a yimata dinkin da zai bayyana surar jikinta ,nan nefa tace bazata bada goyon baya gurin bata kamasho yada zina ba , dan a cewarta shigar da yawancin ena’mata keyi a wannan zamani itace ke sake haifar da fashadi a doron kasa. zeenat akwaita da saurin sabo da mutane sannan km tana da son kawaye ita da Maryam dan ko yanzu suka san mutun ko km kuka hadu dasu sanadin wata kawar, Shikenan sun zama kawaye , shiyasa suka fi dukkan sauran en’uwansu jama’a dan daga waje ma zuwa ake gurinsu sabanin sauran” kullum kaga ana rikinci a bakin get da sune , gurin shigo da baki most especially ma na school dinsu. abinda ummi tSana kennan daga gareta yawan tara kawaye gata da matukar son gayu ,da son kallace kallacen film muddin tana gida kuwa bata da aikin yi sai na kallo ,daga wannan Chennal zuwa wata ,sai dai duk da wannan halin nata Allah yabata illimi sosai both arabic & school. Daidai misali Allah yayi mata farin jinin samari masu sonta daga waje ma biyota akeyi, sai dai bata fita dan ma ummi taki yarda tafara zance da wuri sai data kai 22 kuma duk masu zuwa gurinta da aure suke sonta “amman matsalar dai daya ce family dinsu basa yarda da macce Tayi auren wajen Amman sukan bar namiji.

  • kana duk masu son nata batajin son su har cikin ranta ‘har wani lokacin ummi kesata gaba da fada “tace maza ki tsaya ruwan ido daga karshe kirasa kowa kizo kina nema yawan yi mata fadan da ummi keyi ne yasa ta tsaida kamil dan gwaggonta” yayar mahaifinta da suke uwa guda uba guda. shima bakowa yasan suna tare dashi ba , dan bata gama tantancewa aurensa ba” kuma shi bai Fiyye zama a garin ba yana aiki ne a abuja “. haka kawai taji idan bata samu wanda yafi ba , zata iya aurensa dan shima ba laifi. Jiki dajini wata safiya ummi ta tashi da ciwon ciki , wasa wasa tun tana daurewa har abin yafi karflnta gabadaya tafita haiyacinta’ hankalin zeenat yayi mugun tashi dan bazata manta yawan labarin da ummi ke yawan bata na mahaifiyarta da irin wahalar da batasha kam mutuwarta ba ,ciki har da ce mata Tayi ta bude ido ta zabi miji wanda zai san mutuncinta kar taje gurin ruwan idonta ta kwashi gaibu ,shiyasa take masifarjin tsoron haihuwa da mutuwa dan ta kudircewa ranta, ta amince da mutuwa tunda tasan muddin kwanakinta suka Kare Shikenan “amman ita kam bazata yarda da haihuwa ba ganinta gara taita shan wahala.

  • wunin ranar da ciwo ummi ta wuni can kuma tasamu sauki dare nayi ciwo ya sake dawowa zeenat taso zuwa ta sanar da DEENi Amman ummi taki. washegari DEENi yashigo da shirin fita aiki dan bai san bata da laflya ba koda yashigo dakin yayi matukar girgiza da ganinta kwance cikin bargo da kyar take iya magana a rude yakaraso inda take ya tambayar ba lafiya ne ? Ummi tace eh tun jiya yace meyasa baki sa an tashe ni ba ,ya kalli inda zeenat ke rukube kusa da ummi duktazama wata kalartausayi. ke….Wace irin” sakariyace da baza ki iya zuwa kisanar min ba da kyar ummi ta iya bude baki ,tace ni na hanata ya furzar da huci ta bakinsa hade da cire hular kansa yayi wurgi dashi gefe ,take ya Ciro waya cikin aljihun bayan wandonsa yakira family doctor dinsu wanda side dinsu kawai yake dubawa.
  • mintina kadan sai gashi likinta dayake bai da Nisa dasu cikin sauri yashiga duba ummi sosai har drip aka sawa ummi a ranar DEENi kasa flta yayi koina byn likinta ya wuce ne, ya kirasu ya Mahmoud ya sanar masu da ummi fa ba lfy , idanunta ta zuba mashi tana kallon bakinsa yadda yake maganar ne tamkar wata mace shi yafl daukar hankalinta, bata taba jin DEENi ya birgeta ba irin na yau. duk wunin ranar kusan shi yayiwa ummi komai hatta magani da abinci a baki yabata sai gurin la‘asar su Yaya Mahmood sukazo tare da matansu sai zuwansu ne ma yasa mutane cikin estate din suka sani dan DEENi bai sanar da kowa ba, shi dai ta mahaifiyarsa kawai yake. Ai kam kace me tuni side din ummi yacika dajama’a, haka suka dinga shigowa duba ummi har dare DEENi na tare da ummi yana bata kulawa. duk yayi wani iri cikin lokaci kadan yaflta haiyacinsa zeenat na zaune a gefe guda tana jiyo hirarsu rokonsa ummi take akan yayi aure ahankali takira sunansa NASURULDEEN ….abinda yasake tada ma DEENi hankali kennan yaushe rabon dayaji ummi takira complete name dinsa ,tacigaba ban rasa komai na rayuwar duniya ba inada tarin dukiya da kadaroro wanda ni kaina basan iyakarsu ba ,burina da muradina ahalin yanzu bai wuce inga aurenka ba, Amman na fuskanci kafi son sai na mutu sannan zakayi aure . Jikin DEENi ya dauki rawa hankalinsa ya sake tashi matuka ta sake kiransa cikin tattausar muryar hade da rarrashi DEENi banida kowa daga kai sai zeenat sai kuma dan uwana wanda yake wata uwa duniya ,idan bakayi aure ka taramin jikoki masu albarka ba mezakayi min naji dadi , inaji ajikina sai na mutu zakayi aure a rude yace first lov ki daina cewa haka zanyi inshallahu kina raye Tayi murmushin karfin hali tace kullun haka kake cewa, ni tuni na fidda raina ka tashi katafi Allah ya maka albarka Amman yarinyar nan zeenat na rokeka dan Allah ko ban tashi ba kada kabari ta koma hannun mahaifinta, na damka amanarta a hannunka ,bata da kowa duk duniyar nan daga ni sai kai ,karikemin ita a hannunka har zuwa lokacin da zata samu miji . DEENi yakamo tafin hannun ummi cikin nasa ahankali yasoma magana muryasa cike da rauni da fargaba, yace haba first lov ki daina maganar mutuwa nan kece zaki aurar daita da hannuki kuma kina raye inshallahu ta girgiza kai ita kadai tasan abinda takeji cikin muryarta irinta marasa lfy tace Shikenan tashi kaje ka kwanta , hankalinsa a tashe ya fice daga dakin..
  • zeenat ta mike daga inda take idanunta na zubda hawaye ta taimaka mata suka kwanta tana kuka kasa kasa ummi tace lfy zeenat ummi . ummi ….. cikin sheshekar kuka tace banason naji kina cewa zaki mutu kibarni dan Allah ,ummi tace mutuwa ta zamemin dole sai dai idan ajalina bai Zo ba .zeenat ta saki kuka hade da kamkameta ummi ajikinta ,tacigaba da kuka mai cin rai hade da cewa ummi bazaki mutu ba inshallahu da kanki zaki aurardani ni ga duk wanda kike so da kyar bacci ya dauketa yayinda ummi Tayi nisa a bacci .

  • Shi kuwa DEENi tunda ya koma dakinsa ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zariya yake daga farkon dakin zuwa karshe kafin daga baya ya nemi gurin ya zauna. yayi tagumi da duka hannuwansa yayi zurfi cikin tunanin yadda zai yi lallai ya zama dole ya nemo mata domin cikawa umminsa burinta. sai dai shi matsalar sa bai san ta ina zai fara ba ? Bai taba yin buduwar ba ballanantana wata aba soyayya, shi duk a tunaninsa raini hakan zaijawo masa idan yaje yace yana son budurwar. ya kamo gefen lips dinsa ya dan cizawa a hankali har daga karshe ya yanke shawara zai nemi fk da zance anan ya sulale ya kwanta rigingine idanunsa na kallon celling dakin. yayinda ya rungume hannushi a saman kirjinsa yana aiyana irin type din maccen dayake son ta mallakesa,kuma wacce ya dace ya aura cikin sanyi ya runtse idanunsa gam take yasoma zaiyano irin type dinsa kyakkyawa dogowa mai dirin jiki , chocolate colour, mai dara daran idanu sannan educated mai wushiryar haka dai ya rinka yi har dare ya sula bai samu wani ishashen bacci ba. koda asuba kafin ya tafi masallaci sai da ya fara shiga Bedroom din ummi ya sameta tana sallah ya sauke ajiyar zuciya sannan ya wuce ganinta tsaye tana sallah yasan Allah yakawo mata sauki . A masallaci DEENi suka hadu da fk byn an idar da sallah “yajashi gefe guda da idanu fk yake binsa da kallo “abinda bai taba faruwa ba saboda DEENi daya idarda sallah yayi yan addu’oinsa yake wuce wa gida . fk ya dube sada kyau yana nazarinsa kafin daga baya yace lfy kuwa naganka haka ? Gabadaya fk yagama tsurewa da ganin yanayinsa sai da ya sake maimaita tambayarsa sannan DEENi yace ina fa lfy jiya ummi kwana Tayi ba lfy har tana barmin wasiya burinta da muradinta yanzu bai wuce nayi aure ba. fk yayi shr yana jin DEENi har sanda yagama bayaninsa sannan yace ba ita kadai ba har big dady ma burinsa kennan dan kojiya sai daya min maganar nida kai Amman tunda kai ummi ta damu ta tsananta gara kayi kawai kurabu lfy . DEENi yace ai bakasan inda zan nemi matar ba nifa gabadaya en,mata family din nan basu min ba sannan kuma sun min kankanta da aure ,fk yace A’a bawani kankanta” mace na kankanta da aure ne? kaine dai kawai kake ganin haka ,ni yanzu na yanke shawarar zan tsaida shemah kawai tunda na dade ina sonta nida zakaji shawarata ma da zeenat ka aura DEENi ya mishi wani irin kallon bakada hankali sannan yaja tsaki yace haba dai zeenat , fk yacigaba yarinyar akwai hankali ba kamar wancan banzar ubannata ba, dayake duk sun tsani halinsa.
  • kaga kawai sai a hada bikinka da nawa kawai kaga zeenat batada matsalar, km ko bakomai ummi zataji dadin Sosai da wannan hadin. DEENi yace Amma ban tabajin koda alamar digon sonta ba, kuma ni gaskiya ina ganin tamin yarinta dayawa duk fa shekarunta sha tara zuwa ashirin ne fa. nafison mutual girl wace ta mallaki hankalin kanta tasan yadda zata kula dani akan bed ,amman wannan Yar bbyn maimakon ta kula dani ,nine zan koma renonta. fk ya dubesa a kaikaice yace lallai yaran zamanin da kasani Amman banda na yanzu, sai su maka abinda manyan matan baza su iya ba, kana rai nata ne kawai , sai kaga mararta ta daukeka tsab, DEENi yaja tsarki kai ban son iskanci shawara nake so ba wani shirmen ka can na bazan ba. fk ya kada kafada yace well tunda kaga bata maka ba kana iya duba wasu acikin gari . DEENi ya kalleshi yana watsamasa harara “kaifa dan iskane dan kaga nazo maka da maganata shine zaka rainawa kanka hankali ” sai kuma yayi kasa kasa da murya yace kasan Allah ni fa k0 a waje ba wai ina kallon mata bane, fk yace to katsaya akan zeenat din kawai, duk inda ake neman macce mai natsuwa yarinyar nan takai ,DEENi ya sakejan tsaki yace ai inda takaicin yake kennan sai kuma nakirata ince ina sonta …ya fada yana tabe baki “hade jin takaici da haushin shawarar da fk yakawo masa ” fk yace inda bazaka iya ba kabi ta sama , ma’ana kasamu big dady da maganar kawai, kasanardashi kana sonta nasan zai ji dadi Sosai. DEENi ya sake watsamasa wata harara yace dan Allah malam ka dameni , ina ganin fa kmr kafara samun tabin hankali , wa yace dakai ina sonta “zan dai yi aure badan ina soba ,ya juya yabar fk nan tsaye yana binsa da kallon mamaki sannan kuma yace ai kaine babban mahaukacin dan iskan kawai , sai iskanci fall ciki ,shi bai ga laifinsa da yace bazata iya daukarsa a bed sai nawa sai kuma ya kwashe da dariya.
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]