[Advertisements⬇️]

WANI AURE CHAPTER 2 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WANI AURE

CHAPTER 2
Sai data gama kallonta tsab Sannan ta canza Chennal hade da tashige kitchen dan daura abinci abincin dare bakin kofar kitchen din ta dawo Tayi tsaye abunta tana cigaba da kallonta Chennal data canza, ajima ajima tana zuwa tana duba abinda ta daura. Karar bell taji ba kaukautawa shiyasa da sauri taje ta bude gudun maseefar DEENi dan tasan muddin yana gida baya son yawan hayaniya , yanzu ne zai gama daita, Maryam tagani tsaye da wasu en school dinsu su biyu tuni murna yakama zeenat ,ta rungume su daya bayan daya tana musu sannu da zuwa hade da basu hanya “suka shigo har cikin main parlour din hade da Sallamar su . waje ta nuna musu da hunnu kuzauna mana suka zauna ita kuma takoma kitchen ta duba abinda ta daura taga yayi ta kashe gas din sannan ta dawo inda tabarsu hade da kawo musu drinks mai tsanyi da snacks ta ajiye agabasun . gabadaya hayaniyya ce ta barke a atsakaninsu da murna ganinjuna ,zeenat ta kalli su Sumy hade dayin kasa kasa da muryata tace kuyi magana ahankali fa sannan tace kun kyauta sai yau kuka ga damar zuwar mana , Sumy tace ba gara mu ba muna zuwa time to time. kufa sai aikin sa rana kullum, hira suka shiga. a inda Maryam ta dube zeenat tace wai nan fa IV suka kawo mana na birth din rukky, zeenat ta zaro idanu waje I ….me Maryam tace IV. zeenat Tayi dariya hade da cewa uhmm badani ba” kema kinsa sarai baza’a taba barinmu zuwa wani birthday party ba” Sumy Tayi murmushi sannan tace ai sai da nagaya rukky Amman tace ga zance ga magana ” gashi nan, ni ai nasan bazakuyi attending birthday party dinta ba ,da day itace sarkin shishigi da neman suna , zeenat tace kmr kinsani ,duk abinda ya wuce cikin gidan nan namu “ta girgiza kanta baza’a taba barinmu ba ,ki bata hakuri kawai Amman wlh har ga Allah naso zuwa ko dan rukky Sumy tace to why not ku sace hanya kuje a boye batare da kowa yasani ba zeenat ta kalli Sumy fuskarta a hade tace kefa kin cika matsala fa wlh. kmr bada hausa nake miki magana ba. ta bude bakinta kennan da niyar sake balbale summy. sai ga DEENi ya sake fltowa parlour jikinsa sanye dajallabiya marun colour may maseefar kyau sai kyalli take zuwa ga kamshin turarensa mai mugun sanyi dadi wanda tun tasowar zeenat ta sanshi da auren Hamilton haryanzu fuskarsa a daure take tam .. kmr koda yaushe ” take ta hadiye maganarta batare da tasan Tayi hakan ba ,ta zuba masa idanu tana kallon kwayar idanunshi, sai data ya harareta, sannan ta dauke idanunta ,ta malda kallonta da hankalinta kacukam a kansu Sumy dake zaune surusuru. Yayinda gabadaya Maryam duk ta flsu tsurewa ko dan ita Yar gidan ce oho.. cikin wata irin murya mai sanyi dadi tamkar ba soja ba yace ke …… tajuyo ahankali ta sake zuba masa idanunta dan tasan da daita yake dan haka tabada duk attention dinta garesa.
bakisan kibawa mutun abinci bane? Dan iskanci sai an roka ,zatayi magana ya katseta a fusace , ai ba tun yanzu nasan ke muguwar rowa ce dake ba Tayi surusuru da idanu ,da sauritace kayi hakuri dan Allah nayi zaton ko kana azumi ne “naga kullum kana yi ” yace “oh “dama kinsa min ido ne har kinsa cewa azumi nake kullum ? Jikin Maryam har rawa yake ,a hankali tace wayoo Allah ashe ya dawo ,bari in gudu tun bai gama da ita ya dawo kanmu ba , zeenat tayi shr har sanda ya sake maimaita tambayarsa hade da cewa dan ubanki bada ke nake ba kike bina da idanu kmr zaki cinyeni” ta sake girgiza masa kai,. Tana bashi hakuri marowaciyar banza kawai mai mugun gado. shiru yayi na dan wani lokaci hade da sauke numfashi. Sannan can kuma yace ai idan bakiyi rowa ba sai Allah ya tambayeki” kuma baza’asan ke…Yar uncle Habib bace . kin taba ganin barewa Tayi gudu danta yakasa rarrafe” zeenat ta sake girgiza kai da sauri ,yace 0K ashe dai kema kinsa gaskiya dole kiyi gadon rowa. Ganin haka yasa su sumy suka nemi sulalewa duk yana kallonsu sai daya ga Maryam na shirin gudu itama dan har summy ta daura hannuta kan handle din kofar ,ya dakatar dasu da hannusa , sannan yacigaba duban zeenat yace barikiji da kyau yana mai nuna da yatsansa” nan ba gidan marowata bane gidan masu bayarwa ne aci . yace menace ? Da sauri tace gidan masu bayarwa ne.
yace gud daga yau bama ni ba ,ko wani ki kaga yazo gidan nan ki bashi ruwa da abinci yaci dan ba naki bane. ya sakejiho mata wata tambayar yace ko abincin naki ne?, da sauri ta girgiza masa kai
dan gabadaya ta sure ta kasa kwakwaran motsi sai ajiye zuciya kawai take yi ,yace” baki da baki ne kike kadawa mutane kai , tace naji kayi hakuri dan Allah. Sannan yajuya kan Maryam da kadan ya rage ta fashe da kuka , ya zuba musu rikitattun idanunsa da suka fl kama da mage masu saurin raunana mutun kai tsaye , yace ku kuma en iskanci banza kun wani cikawa mutane kunne da hayaniya tamkar kuna club ,kallo daya yayi musu kowace tabawa kafanta iska yaja tsaki yajuya ya nufi dakinsa.
ahankali zeenat take sauka ajiyar zuciya hade da dafe kirjinta , batasan meyasa ba ,idan harYaya DEENI yana guri Sam bata samun cikakkiyar natsuwa “sai tarinka ganin duk yacika guri ga tsananin tsoransa da take jI‘ yana mamaye zuciyarta .Maryam har da kuka tayi byn sun fita dan daman can ita haka take ,shegen tsoro gareta aiko, su sumy suka ce mezasu ba dariya ba dariya suka dinga yi har da rike ciki suna nuna ta aiko tace yau sai dai suyi ta zama a estate din dan bazata rakasu gun securities ba sai da sukayi ta bata hakuri sannan sukajera suna hirar abunda ya faru.
Ko lokacin da ummi tadawo tuni murna da farinciki Ganin tilon “dan ” nata yamamayeta zuciyarta nan suka zauna a parlour suna hira cikin hirar ne ummi take masa maganar aure in da tace masa yakamata yanemi mata yayi aure kasan shekararka nawa kuwa yanzu? yayi murmushi ai dole nasan shekaruna ,muke nan kullum cikin rubuta date of birth ,talatin da biyu ne kawai fa ummi Tayi dariya 32 din ne kawai kusan duk sa’annin haihuwar ka duk sunyi aure acikin estate din nan gasu yasir nan ma duk ansa musu rana dan haka kaima ka fldda mata kafln azumi DEENI yazaro idannu yana bin ummi da kallo a shagwabe yace haba first love dan sunan da yake kiranta dashi kennan tun tasowarsa ni din guda nawa nake da zakice inyi wani aure yanzu. Dan Allah kiyi hakuri my first lov zuwa wani lokaci ,duk hirar da suke zeenat na zaune tana jinsu haka kawai taji gabanta na faduwa lokacin da taji abinda ummi tace ,Amma jin amsar da yaya DEENI yabata yasa taji wani irin sanyi na ratsa zuciyarta. kamar ance ya dago idanunsa suka sauka cikin nata harararta yayi yace kallon fa kin wani tsare mutun da idanu, ummi tace uhrnm kafa dawo kennan karka takuramin yarinya ,
ya langwabar da kansa yana maida idanunsa kan ummi cikin sanyi murya yace haba first lov baki ga irin kallon da take bin mutune dashi bane, kmr bata san mutun ba , ummi tace kai da wani idanu ka kalleta har kasan tana kallonka. kuma ma ni banga komai ba kai dai ta kurace kawai dakai indai kana gida baka barin yarinya nanta huta ta sarara , ya dubi ummi ya tabe baki , Sannan yace ke….kawo min coffee ,ta mike taje ta hado coffee din takawo masa gabanta na wani irin faduwa ta durkusa har kasa ta ajiye masa .
Adaidai wannan lokacin ne zeenat ta kammala karatunta na secondary school , ta flto da sakamakon mai kyau domin tasamu almost 7 credit masu kyau .
shi kansa DEENI yaji dadi Sosai sanda ummi ta nuna masa Amman dayake miskili ne, sai cewa yayi Sam shi bai ga wani kokari da Tayi ba tunda bata cinye duka ba. ummi Tayi murmushin tace kai ne dai bakaga kokarin ta ba. Amman ni nagani km nasan Tayi kokarin Sosai. Ina laifi duk cikin wayanda suka rubuta jarabawa tare bbu wanda yakaita marks ,. yace ok inda ta cinye duka ne zan iya cewa Tayi kokarin ai wayanda suke cinye 9 credit ba finta brain sukayi ba. Ita dai wasa da kallace kallacen banza tasa a gaba. ummi ta hade fuska tana harararsa yacigaba da zagin zeenat ganin yadda ummi Ta canza fuska ne ,yasa yabar maganar , ummi ta sake duba result din tana shafawa hade da kwallawa zeenat data tashi tun sanda taji DEENi yasoma zaginta kira ,takaraso tazo ta tsaya kusa da ummi DEENi ya dauki wayarsa yana daddannawa bai ko kalli inda take ba ummi ta mika mata slip din tana murmushin tace kinyi kokari sosai , zeenat ta karba ta juya ta bar gurin dan bazata iya zama a duk inda yake ba . ummi ta dubi DEENI tace yanzu kuma sai aure zanwa yarinyata.
DEENI yajuyo a sukwane yace wani irin aure kuma first lov da rana tsaka , kudai Bari yarinya tacigaba da karatu kawai” dan yanzu kai yawaye , an daina irin wannan auren, ballanantana mata marasa illimi “ummi ta dubesa da kyau ta numfasa Sannan tace ni tawa iya secondary zan aurar daita dan ma taki sauraran masu sonta ne . itama shegen iyayi ne daita kuma dai kasan matan wannan family din basa wuce secondary ake musu aure . kuma kasan baza’a fara karatun jami’a daga kanta ba, uhm nima nafI son na aurarda abita. DEENI ya tabe baki Sannan yace Allah ya kyauta ni ko zanyi aure bazan auren yar secondary ba wlh sai wacce tagamajami’a mai tarin illimi ,kuma ba auren family zanyi ba dan baya birgeni. yakarasa maganaryana dan murmushi ,ummi tace to Allah yabaka sa’a. amman ni tawa aure zan mata da wuri . kai kasan halin big dady bazai taba barinka kayi aure a waje ba . Wlh nasoma a hada aurenka dana su yasiryace uhmmmm su dai yi nasu ni sai nan gaba .
A wata yammacin DEENI zaune akan dadduma awajen shakatawa shi da abokansa wayanda duk kusan , family ne zagaye dashi gefe guda kuma flasks ne cike da ruwan zafi da kananan cups , hira suke sosai atsakaninsu Amman banda DEENI dan gabadaya daukar hirar tasu yake shirme dan duk zance nasu akan maganar aurene wanda shi kuma Sam baya kaunarji ,dan haka ya sharesu yacigaba da lasalasar wayarsa ya yinda ya kai hannunsa daya ya dauki cup din coffee wanda orready fk ya tsiyaya masa ya kai bakinsa yasha hade da rufe rikitattun idanunshi wanda yazame masajiki ya kalli yasir da faysal dake tawowa inda suke, ya kwashe da dariya har suka karaso bai bar musu dariya ba fk yace sannuku da karasowa Mayan angwane kunsha kamshin ,faysal yace kai dai anyi dan iskan yaro , kai baka tsaya ruwan ido ba kana biyewa wannan ya nuna DEENI da yatsa fk yayi murmushi yace yayi an gwayen bana wannan karon gabadaya suka dara hannu suka bawajuna suka gaigaisa har DEENI. yasir ya dube fk yace ai gara muyi aurenmu tunda muna sonjuna kai ka zauna kar kayi har mahdi ya bayyana ,fk yace A’a nifa bance saboda me zakuyi aurenku ba . Amman gaskiya zaku takura kanku ne kawai yanzu da wani aure wayannan kananan bbys din.
DEENI ya tabe baki Sannan ya dube fk yace shiyasa rawar kan yaran ke kara yawa ba. dukkansu suka sa dariya suna cikin dariyar ne fk har da rike ciki sai gasu zeenat da suka taso daga islamiyya su biyar sukajero kowace sanye da hijab dinta raudat da shemah da samiha da Maryam sai zeenat dake tsakiyar su dukkansu kyawawane. da hannu fk yake nuna musu inda suke Sannan ya dakata dariyarsa ya kalli inda DEENi ke zaune tamkar bai san abinda ake ciki ba , k0 kallon inda suke bai yi ba, yacigaba daddannawa da sarrafa wayarsa . fk yace kai gaskiya bbys din nan fa su hadu dayawa fa , nima ko zan dan shiga daga ciki ne. yasir yace dako ka huta , kabar wannan ya nuna DEENi fk ya cigaba A’a ina ai bazan barsa ba tare zamuyi namu auren , k0 yakace mutumina kaga Shikenan mun huta da surutun jama’a DEENi ya kallesa a kaikaice yace A’a ku dai da kukaji zaku iya kuje kuyi Tayi . Amman ni ya nuna kansa da yatsansa hade da tabe baki, ba yanzu ba” har sanda su zeenat suka zo suka wuce. Suna hirarsu suna dariya Maryam ce ke basu labarin abinda ya faru jiya bbu wanda bai dara ba har ita zeenat din raudat tacewa zeenat ai ke kika daukar masa wlh kuma yarinka yi miki kennan ina ma nice daya gane kuresa suka sake yin dariya
Tun lokacin daya dawo zancensa da ummi bai wuce DEENI kayi aure ka fito da mata cikin yan,uwanka kayi aure hirar kennan sai dai idan basu zauna ba . Yau takama walimarsu zeenat ta saukar alqur’ani mai girma wanda aka shirya musu anan islamiyyarsu dake cikin estate din ,su kusan goma anyi taro walima lfy yayinda zeenat ta karbi kyaututtuka da dama saboda kokarinta har kuka ummi Tayi sakamakon tunowa datayi da er’uwarta taro ya watse lfy kowa yakama gabansa ,byn sun gama hirarsu da ya zame musu jiki suka fara hada kujerun da akayi walimar dasu . sun fito kennan suka ga Yaya DEENI da wani abokinsa zaune akan kujera biyu suna hira ,take sukaja birki samiha tacewa zeenat jeki amso wadan can kujerun, cikin zolaya tayi mata maganar dan tasan yadda takejin tsoronsa zeenat tace uhmmmm ku dai kuje “suka sa mata dariya ke wlh muguwar matsoraciyace wlh ki rage tsoransa shiyasa yabi duk ya renaki ,Tayi sororo tana kallonsu , Sannan tace to bari naje amsowa Tayi tafiya kmr zata isa gurinsa sai kuna ta juyo da sauri” aiko suka sake kwashe mata da dariya. 
muryanshi ce ta katse musu dariyar tasu lokacin daya suke kallonsa a frigice” yayinda gaban zeenat yasoma faduwa yace ke….da hannu ya nuna musu alamun suzo suka nufo inda Yake cike da tsoro ya zuba musu rikitattun idanunsa yana kallonsu daya byn daya yana nazarinsu Sannan yace da ganinku akwai alamun rashin gaskiya atare daku ?ya nuna su da dan yatsansa zeenat Tayi saurin cewa A’a cikin inda inda uhm bbu komai fa Tayi gudun Kar wata cikinsu tafada masa shiyasa Tayi saurin yin magana ,to menene na inda inda wama ya tambayeki ?Tayi shiru tamkar ruwa yacinyeta. Sannan ya juya ya kalli abokin nasa da ya zubawa zeenat idanu yana kallonta kafarsa yasa ya take kafar manir dashi
,sannan ya dawo natsuwarsa ya mai da hankalinsa kan DEENi , DEENi ya nuna su zeenat da samiha hade da shemah da Maryam yace gasu nan bansa inda sauran suka nufa ba, manir yace ina tayaku murna walima saukar alqur‘ani mai girma, Allah yasa na tsoron Allah ne ,suka hada baki wajen cewa Ameen , kallonsu kawai DEENi yayi jikinsu har rawa yake suka bar wajen.
mannir yabi bayansu da kallo yace kai sisters din nan naka fa akwai kyau DEENi ya kallesa yana watsa masa harara ok iskancin naka kuma yau agidanmu zai Kare. manir yayi murmushi yace Allah barin ma wacce take tsakiyarsu gaskiya duk tafiso haduwa DEENi ya kalli inda ya nuna sai yaga zeenat yake nufi take yaja tsaki manir yace dama ita ka zaba wlh dan nasan karshe ma auren zumunci za’a maka DEENi ya sakejan tsaki dan Allah malam karka dameni da wannan shirmen bazan ,manir bai daddara ba ya sake cewa Allah dama tsayawa kayi akayi Yar gida tunda duk tarin matan dake sonka baka kallonsu , a fusace DEENi yayi magana dan me zan kallesu alhalin banda abinyi dasu. manir yayi murmushi ina ma ni ne kai wlh tsayawa zanyi na kwashi gara son raina har sai nagaji in more kuriciyata , DEENi yace ai kai dan iskanci ne lamba daya , wlh ka guji abinda kakewa ya’yan mutane “ko dan gaba . ka dauki neman mata tamkar wani abinci, manir ya dan daki kafadar DEENi yace ai sun fi abinci dadi ,. Amman Allah koni ina son na daina bin matan bazan ,wlh abun ne da kmr wuya Amma kacigaba da yimin addu’a . DEENi ya nuna sa kai zanwa addu‘a saboda banda abinda zan roka maka, manirya dage masa gira daya yes meye dan kamin addu‘a kaga idan Allah ya shiryani sai kabani waccan Yar dimadimar sister din taka na aura , bai kulasa ba sai canza zance da yayi nan dai suka cigaba da hirarsu har zuwa sanda sukayi sallama dajuna .
Abinda zai daure maka kai bai wuce yadda ummi ke sake bawa zeenat kulawa ta musamman ba ,ta kowani part tana iya kokarin ganin ta fito da diyarta ta tsab, zeenat bata rasa komai ba tun daga dangin sutura da mayuka shafa masu tsada zuwa kayan kwalliya ana cikin haka tafiya takama ummi zuwa India dan haka ta tasa diyarta gaba suka tafl zeenat taji dadin zuwansu India tamkar karta dawo ,watan su daya suka tattaro suka diro Nigeria saboda bikin family dinsu yakusa koda ta dawo ma su Maryam sun dinka mata duk anko din da aka fidda tunda damar suna da telarsu da yake zuwa har gida ya karba dinki,. biki akayi sosai bakama hannu yaro an kashe kudi tamkar ba’asan ciwonsu ba bidia iri kuma a duk anan cikin estate din akayi komai, daga karshe akayi walima washegari ranar Sunday aka daura auren en mata biyar haka ma samarin haka aka kai kowacce gidan mijinta, ya saura mutun uku ne cal suka rage da basuyi aure ba, Maryam da shemah sai zeena amaza kuma fk da DEENi sai kamil .
L

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]