[Advertisements⬇️]

WANI AURE CHAPTER 11 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WANI AURE


CHAPTER 11
Part din cike yake da abonkan arzikin da en’uwa ,Ummi
Jikinta a sanyaye ta dinga ratsa mutane dake ,zaune a parlour’ har ta iso dakin ummi, da
idanun take bin en dakin da kallo.
kozata ga ummi ganin bata alamunta bane , yasa tmbye matar uncle din Inda ummi
take.
tace yanzu tashiga bathroom .
Ahankali ta fidda numfashi tare sauke ajiyar zuciya
cikin haka ummi ta fito tana ganin zeenat din.
ta bata fuskarta “ta zauna tana dubanta”
gefen ummi zeenat tasamu ta zauna fuskarta dauke da murmushi wanda da Gani na karfin
hali ne.
Cikin kasa da murya ummi tace yana ganki haka ina kayanki ?
Cikin sanyi jiki zeenat tace shi nazo dauka.
,ummi tace ke dai kin cika shiririta wlh”
komai baza kiyi shi cikin sauri da kazar kazar ba kin dinga jan jiki kennan ,kmr wata mage
Alhalin kin san halin wanda zaki aura ” dan oya oya ne .
jin haka yasa jikin zeenat din sake yin sanye, tare jin wata irin faduwar gaba “zuciyar ta
dinga dokawa da sauri tamkar baso kirjinta.
ahankali tasa hannuta ta kamo na ummi
cikin nata jikinta har rawa yake hade da rage murya tamkar mai shirin zubda kwalla tace
dan Allah ummi kiyi hakuri kinji karkiyi fushi dani ,zan canza inshallahu Amman ” kimin
addu’a.
wlh tun sanda aka samo shirin bikin nan nake jin faduwar gaba wanda narasa dalili.
ummi ta tayi shr tare da zuba mata idanu kawai tana kallonta
tausayinta ne ya sake kamata , ,duk sai taga takara ramewa ba kmr kwanaki ba hakan
yasa taji ba dadi aranta.
, ahankali ummi ta mike tare da riko hannuta tayi cikin , bedroom daita. En dakin suka
bisu da kallon sha’awa duk da basu ji maganarsu ba Amman sun birgesu.
,Har suka shigo bedroom din Ummi na rike da hannuta Ta zauna daita tana rarrashita kan
ta kwantar da hankalinta fargaban aurene kawai ke sata jin faduwar gaba Amman bbu
abinda zai faru inshallahu”
Ummi da kanta ta shirya diyatata cikin wata arniyarta geziner ligth blue sai daukar ido
take da kamshi tare da fesheta da turaruka kala kala masu sanyi kamshin take zeenat ta
fito amarya sak tayi kyau sosai
Ummi ta dauki waya tayi mata hotuna sannan takira Maryam tace tazo ta tafi daita din.
Kwanciyar tayi flat a kan gadon su shemah tana kallo da sauraran duk abinda ke faruwa.
a cikin dakin dake cike da en mata da kawaye
abinka ga mai yawan kawaye ” da mutane kala daban daban ” yasa dayawa wayan dake
cikin dakin kawayen zeenat din ne
gyara kwanciyarta tayi idanunta na kallon celling dakin hannuwanta duk rungume da
kirjinta yayainda zuciyarta ke cigaba tsalle tamkar zata fasa kirjinta ta fito waje.
ahankali ta runtse idanunta sanyi taji yana ratsa koina ajikinta duk da tarin fargaban dake
tattare daita hakan bai hanata jin jikinta yayi mata nauyi ba.
Tanaji ajikinta burinta da dokin son auren DEENi
F .ll.l
8:13 PM A HO .
duk babu shi ahalin yanzu sakamakon fargaba da tsoron kasancewa tare dashi a muhalli
daya.
Ta dauki lokacin mai tsawo kwance yayinda ta dinga jin wani iri ajikinta.
Bugun zuciyata na sake karuwa.
ta dinga kokarin ganinta ta cire damuwar dake damunta wanda a zahirance ita ta daurawa
kanta
har yanzu da take kwance jikinta a sanyaye yake takasa tabuka komai.
idanunta ta runtse tana cigaba da sauraron hirar dasuke sama sama .
Karfe goma da rabi daidai na ranar lahadi Allah ya cika alkawarinsa domin dimbin,
jama’a sun shaida daurin auren NASURULDEENI ALIYU BELLO da MUZEENAT HABIB BELLO”
daurin auren daya tara manya attajirai da kusoshin gwanati hade da maikata
bakaramin farinciki family din muhd bello suka yi ba ganin sun kara karfafa zumunci a
atsakaninsu,
dan haka farincikisu ya sake karuwa takoina ka juya, family din murna ne cunkushe a
fuskokinsu
Zeenat dake kwance har lokacin tana saka da warwara still ikinta a sanyaye yake takasa
kwakwaran motse .
zuciyarta fall da fargaba musamman lokacin da taji hayaniyar mutane ta cika gidan
alamun an daura aure, en’uwa nata shigowa ana gaisawa, ajiyar zuciya dumin hawaye taji
yana bin kuncinta shikennan ta faru takare tana matukar son deeni Amman tana jin
tsoron zama dashi hayaniyar mutane take sake jiyowa hakan yasa jikinta ya dauki
kirma,kirrrr.. sam ko kadan bbu wanda ya lura da yanayinta.
Sai ma tashi sukayi suka fita waje km har sanda suka fito tsakar gidan suna ta daukar
hotuna bbu wanda ya lura da yanayin da suka barta .
” Maryam ce data karaso wajensu taga suna ta hotuna bbu ita yasa tashiga dakin dan
dubota dan kusan tana lura daita tun jiya tamkar mara lfy .
kwance ta tadda ita tana fidda numfashi sama sama.
Da sauri ta karasa inda take bbu abinda jikinta keyi sai fidda hucin zafi, a rude ta dinga
takiran sunanta zeenat .. .eenat daman bakida lfy ne?
Kai kawai ta iya girgiza mata alamun eh da sauri Maryam ta mike ta nufi part din ummi
tasanar mata .
tare suka dawo gurinta da wasu en’uwa ummi guda biyu .
zuwa yanzu jikinta ya tsananta zafi tare da karkarwa
ban da salati bbu abinda ummi keyi da sauri takarasa kusa da zeenat din ta zauna tare da
riko hannuta” may zan Gani , haka ni fadeela?
, zeenat kina son ki kashe min kanki ne ?
Ko yaya,
Alhalin kinsa ke kadai gareni duk duniyan nan km ke kadai debimin kewar er’uwarta dana
rasa, bazan iya jurar rashinki ba dan Allah ki tausayi min mamana.
sai km hawaye shar shar daga idanun ummi sosai Ummi ke zubda kwallar tausayi diyarta
ganin yadda ta fita haiyacinta cikin lokaci daya
Ummi tace zahra kamama min ita dan Allah.
su aunty suka mata zeenat sukayi part din Ummi daita.
kai tsaye dakin DEENi ummi tabada umarnin a wuce daita.batare da bata lokaci ba ummi
takira family doctor dinsu .
sannan takira DEENi tace yasameta a dakinshi yanzu yanzu .
Doctor bai dauki wani lokacin ba” sai gashi yana zuwa yasoma duddubata tare dabata
taimakon gaggawa
ummi ta dubi doctor hankalinta a tashe tace doctor meke damunta?
doctor yace bawani abu bane damuwace kawai tayi mata yawa “amman inshallahu zata.
dawo daidai.
A gaugauce DEENi yashigo byn amsa kiran Ummi.
yana shigowa dakin mutane suka dan ragu.
ahankali yakaraso kusa da Ummi ya tsaya yana tmbyrta abinda ke faru sai data ja
numfashi sannan ta nuna masa inda zeenat din ke kwance tace zeenat ce ba lfy sai lokacin
idanunshi suka kai gareta kwance take akan bed dinshi an lullubeta da bangon rufarsa.
shr yayi tare da zuba mata rikitattun idanunshi.
Daddaden kamshin turarensa tasoma juyowa may matukar sanyi ahankal ta dan lumshe
idanunta.
Taku daya zuwa biyu yayi yaja ya sake ya tsaya” sannan ya dubi inda ummi ke tsaye yace
me doctor din yace yana damunta?
, doctor din still ya sake mashi bayani kmr dai yadda yayiwa ummi .ahankali ya sake mai
idanushin kanta yana cigaba da kallonta wannan shine karo na farko daya tsaya ya Kare
mata,
, sosai kamshin turarensa ke sake kaiwa hancinta farmaki tare da susuta mata duk wata
gaba dake jikinta.
jikinta da zuciyata suka dauki rawa wani zazzabi mai zafi yayi nasarar sake rufeta
sakamakon idanushi dake yawo a gangar jikinta.
Da sauri doctor ya nufo inda take” deeni yasa hannu ya dakatar dashi alamun kada
yakarasa gareta” dan wani abu yaji yana taso masa sanda doctor ke masa bayanin abinda
ke damunta, tamkar ya auna doctor waje dan takaicin abinda ke cin zuciyarsa.
ganin haka yasa doctor din yace a samo ruwa da towel a goge mata jiki dashi dan tazo
daya dubata yaji yadda jikinta ya dau zafi yace zai je ya dauko magani ya dawo cikin sauri
ya fice dakin.
A ranta tace doctor dama kayi zamanka dan maganinka kadai ba zai taba min
maganin damuwarta ba.
dan ita kadai tasan abinda ke cin ranta.
Wanda tun daga cikin zuciyarta take jin yake taso mata.
tare da haddasa mata tsoro da faduwar gaba.
Tsaye yake har yanzu sai suke hanuwanshi duka da Yayi cikin aljihun wandonsa.
ahankali yasoma takowa zuwa bakin gadon km idanushi akanta.
cikin sanyi ya yaye bargon da aka lullube mata jiki dashi. idanunshi fes akan fuskarta dake
lumshe tayi fayu sannan km takara rame sosai ahankali ya daura hannushi saman
goshinta.
jin yadda goshinta ya dau zafi da yadda take fidda numfashi sama sama yasanyashi kai
hannushi da sauri jikinta.
take yaji abinda ya sake frigitashi.
zafin dake jikinta ya ratsa tafin hannushi” wanda bai san sanda tausayinta ya lullubet shi
ba ya dinga jin wani abu na tsigar wa ajikinsa, ya juyo tsaitin Maryam yana harararta yace
tsayuwar me kike anan da sauri ta fice daga dakin bata fi minti uku ba Sai gata ta dawo da
ruwan ahanunta jikinta na rawa.
azaton zeenat ummi ce ko auntyta zasu goge mata jiki ,amman sai taga DEENi yakarbi
robar ruwan a hannu maryam
Gabadaya suka fita daga dakin har ummi “tare da kulle masu dakin.
Cikin sanyi jiki ya tashi ya dawo gabanta har yanzu sanye yake cikin shadda fara tas sai
kamshin turarensa ke tashi a dakin.
ahankali ya cire farar hular shi ya ajiye gefe sannan yasa hannushi duka ya tattarota jikinsa
yaja zip din rigar kasa ya zare rigarjikinta ya ajiye gefe take jikinta ya sake daukar kirma
gabanta yacigaba da faduwa.
tsoro da mamaki suka taru cika zuciyarta. aranta tace wayyo nashiga uku me yaya ke nufi
da cire min riga ? yana nufin shi ,zai goge min jiki.
tana ji tana Gani ya cire mata kayan jikinta tsab har bra dinta .
ta rage daga ita sai zani iya cibiya ,sannan ya zauna tare daurata a saman cinyarsa” ya
juyo daita suna facing juna taso tasa hannu ta Kare kirjinta amman kasancewar jikinta
bbu kwari yasa takasa aiwatar da komai “dan haka ta runtse idanunta gam.
tana jiran taji ruwa ajikinta Amman sai taji shr ahankali ta dan bude idanunta,DEENi
zaune idanunshi kyam akan kirjinta.
da sauri ta maida idanunta ta rufe dan frigice da tsoro ya dauko towel din ya matse
sannan yasoma goge mata saman jikinta zuwa kirjinta da fuskarta, ya dimauce da ganin
,hakan yasa yafi goge mata gurin a tare suka dinga sauke ajiyar zuciya.
halitatta kirjinta
can yaji ana nouking din dakin yayi sauri ya mayar mata da rigarta sannan yabada izinin
shigowa.
doctor ne yashigo da ledar magunguna ahannushi Yace abata abinci taci tukun sannan
tasha maganin.
byn tafiyar doctor DEENI yakira ummi Yace akawo tea, en’uwa dayawa suka shigo dakin
“ummi da matar uncle din zeenat ,Maryam har ma da shemah .suka dinga jero mata
sannu.
byn sun fita ne taji tamkar kar su fita dan bata son abarta daga ita Sai shi.
hakan na sake frigita zuciyarta
kadan tasha tea din tace takoshi bai wani takurata ba ,ya ballo magani ya Mike mata ba
musu tasa hannu ta karba tasha ,dan tasan halinsa ciwonta bazai hana ya jibgeta ba.
Shiya gabadaya a tsorace take dashi.
Byn tasha magani. komawa tayi ta kwanta lomo ajikinsa’ tana sakin numfashi sama sama
wani iri taji ajikinta lokacin data tsinci kanta kwance kan tattausan jikinsa.
ga kamshin turaren jikinsa gyaraye dana dakin sun buwayi hancinta.
ji take tamkar sukasance haka har abada.
, ahankali tasoma lumshe idanunta har ta rufe su ruff.
bacci ne may nauyi Yayi nasarar daukarta acikin mintina da basu wuce goma ba.
Kyawawan idanushi masu matukar haske da daukar hankali ya zuba mata.
Tare da Kare mata kallo wani zirrrr ya dinga ji ajikinsa” lokacin daya jita lefe a saman
kirjinsa
da kyar yake jawo numfashin yana fesarwa.
hannushi ya sake kaiwa wuyanta har lokacin jikinta da sauran hucin zafi.
janyota jikinsa ya sake yi .
Tare da yasanya hannuwansa duka ya rungume tsam tsam ajikinsa “yana fidda numfashi
tare da fatan samun saukin zugin da zuciyarsa ke masa wanda shi kansa yarasa dalilin
haka.
“Har lokacin bacci take rungume ajikinsa suna musayar numfashin juna mutuwar da
jikinsa yayi ne yasashi sake zuba mata ikitattun idanunshi tsawon lokaci yana kallonta
Da kyar yasamu yayo control din kansa cikin sanyi jiki ya zareta daga jikinsa ya kwantar
daita ya sake lullube ta da blanket,sannan ya Mike tsaye yana karkabe jikinsa.
rigar jikinsa yasoma cirewa ya saura daga shi Sai farar single da wanda shadda.
Wordrob dinsa ya bude ya dauke wasu kayan da zai canza ” tare da yashigewa bathroom.
Dakin ya sake dawo byn yagama shirya kansa , cikin farin yadin voyal may matukar taushi
da daukar hankali.
Agabanta ya tsaya yana makale links din gaban rigarsa yayinda idanushi ke kanta yana
cigaba da kallon fuskarta.
Ahankali ya dinga jin reaction din jikinsa na sauyawa yayinda zuciyarsa ke beating tana
tsalle tamkar zata bafa masa kirji. wanda shi kansa yarasa dalilin dayasa shi jin haka.
Ahankali ya dauke idanushi a kanta sakamakon
ji yayi “ana nouking din dakin “yabada umarnin ashigo batare daya tmbyi kovwaye ba.
Maryam ce tashigo da sallmarta.
ta gaidashi ya amsa mata a dake.
Cikin sanyi nan nasa
Yakarasa gaban mirrow ya dauki agogon ya daura a tsintsiyar hannushi tare daukar
kwalbar turaren ya feshe ilahirin jikinsa ta cikin mirrow din yake wa Maryam magana cikin
dakakiyyar ” muryasa ki kula daita idan ta farka idan kika ji zazzabi bai sauka ba ki sanar
da frst lov,a tsorace tace ta amsa masa da to…
yana fita ta bi bayansa da kallo cikin ranta tace wayyo zeenat na tausaya miki auren
wannan maseefaffe.
,Sai kinyi hakuri da wannan budadden halin na shi.
gefen gadon takoma ta zauna tana sake jin tausayin zeenat din a ranta.
Sosai zeenat tayi bacci baita ta tashi ba.
Sai gaf da magariba.
ji da Maryam tayi jikin zeenat din bbu zafi ko daya.
yasa ta sanarwa da aunty zahra
Su Aunty zahra suka sata tayi wanka da sallah.
tana zaune akan prayer mat “duk jikinta a mace taji sunce tunda jinkinta da sauki tashiyar
akaita tayi sallama da Ummi.
fuskarta cike da tsoro ta dubi aunty zahra tace dan Allah aunty karku kai ni wani guri wlh
bani da Ify
aunty zahra tace A’a kiyi hakuri yanzu za’a kai ki gidanki kya ji sauki a can.
tana kuka tana komai aka shiryata cikin wata geziner mai ruwan kasa ,Sai kamshi ke tashi
ajikinta kai tsaye gurin ummi aka kaita ta mata nasiha mai ratsa jiki ,sannan takara da ce
mata takasance may tsananin tsafta da girki domin sune manyan makamai dake kara
karfin aure.
Sai km hakuri ,kiyi hakuri kiyi hakuri mamana da duk abinda zaki Gani.gidan aure bbu
komai acikknsa Sai hakuri
Km hakuri shine jigon zaman aure
duk wata mata da kika ganta zaune gidan mijinta ,hakuri take yi
dan haka ki kula da kyau kinji mamana.
Zuciyar ummi ta tsinke tayi rauni Sai km hawaye shar shar.Suka soma zuba, en’uwa
ummi da suka zo daga india sukai taba hakuri suma sunyi mata tasu nasiha Sosai .
, ita dai zeenat bbu abinda ummi ta fada wanda bai shiga kunneta ba.
tare da kukan tausayin kanta.
duk sanda ta tuna yau , za’a kaita gidan deeni hankalinta ne ke sake tashi.kuka sosai take
har da majina.
ganin irin kukan da zeenat din ke yi yasa ummi kiran deeni a waya.
Byn yan wasu yan mintina Sai gashi yashigo da sallama ,mutane dake zaune a dakin.
suka fita gabadayansu dan basu waje.
Ahankali yakaraso cikin dakin sosai, ya durkusawa gaban ummi yayi zaman dirshan har da
tankwashe kafafunsa. ganin haka yasa itama zeenat tazamo ” tayi irin zaman da yayi a
gaban ummi” Sai dai ita zuciyarta da gangar jikinta cike suke da rauni.
badan namijin kokarin datakeyi ba da tune zuciyarta ta buga tsabar frigici.
Ummi tayi shr tare da zuba musu idanunta da suka gama canza kala saboda kukan datayi.
Tsawon lokaci tana zaune ta tasa su gaba tana kallonsu kafin daga baya tasoma magana
cikin sanyi muryata ta Kira ” sunansa NASURUDEEN.. ahankali ya dago idanunshi yana
duban umminsa dasu batare daya amsa ba.
Sai dai yadda takira sunanshi din ya girgiza zuciyarsa domin ya manta when last da yaji
takira complete name dinshi haka
Dan haka ya tattara dukkan hankalinsa da natsuwarsa gareta.
Cikin sanyi murya data sha kuka tace DEENi ga zeenat nan ta sake dawo gareka” a karo na
biyu. Sai dai wannan karon yasha bamban da sauran lokuta.
‘wanna karon ta dawo gareka ne da matsayi guda biyu ,kawarka km matarka .
zan ji matukar farinciki da kwanciyar hankali idan kuka hada kanku ,kuka zauna Ify. zeenat yarinya karama kayi hakuri daita” duk wani abinda ta maka wanda bai yi maka
ba, ka sanar min.
Ni Zan fahimtar daita ta hanyar da zata gane.
Ban yarda da duka ko zagi da cin fuska ba.
Kuka zeenat din keyi har lokacin shi kansa ya tsausaya mata matuka
Ga mamakin DEENI Sai ya ga ummi itama ta sauko gabansu hawaye ne ke bin fuskarta
wani nabin wani ,a rude deeni yasa hannushi yana share mata hawayen.
Cikin tsananin tashin hankali Yace dan Allah first lov ki daina zubda hawayenki haka, kiyi
hakuri “zubda hawayenki bakaramin maseefa bane atattare dani ” idan har yanzu bakya
son aurena da zeenat ne wlh ashirye nake dana bar miki ita har abada.
Cikin kuka ummi ta girgiza masa kanta ba kukan komai nake ba DEENI facce na tsantsar
farinciki.
Farinciki ne yamin yawa har yasani zubda su.
ta janye garesu byn ta dauke hawayen idanunta.
kama hannun deeni dana zeenat tayi “ta hade su waje guda tare da daura nata hannu
saman nasu.
Nagodewa Allah daya nuna min wannan rana may cike tarin farinciki mara misaltuwa,
zeenat ga deeni nan nabaki shi amana har abada banida kowa Sai shi.
ki zauna Ify dashi cikin amana “deeni kaima ga amanar zeenat nan naba matukar ka
cuceta “ban bazaka ji dadina ba. Dan Allah Ku kula dajunanku.
Ku rike min amanarjunanku ” ku kadai gareni byn Allah banida kowa Sai ku.
abinda tata fada kennan tana sake hade” hannuwansu waje daya.
Duk yadda yaso daurewa zuciyar kasawa yayi sakamakon ,kaunar zeenat din da yake
hangowa karara a cikin idanun umminsa.
bai so zeenat din taga kasawarsa ” dan haka ya kife kansa kan hannun umminsa ya
sumbata cikin dabara ya goge kwallar idanunshi. zuciyarsa ke kwabarsa akan alkawarin da
umminsa ke so ya daukar mata ” shi kadai yasan abinda ke damun zuciyarsa, aranshi ya
dinga ayyana abubuwa masu tarin yawa”anya kuwa zai iya daukar alkawarin nan
jikinsa yayi masa nauyi tausayin ummin ya sake mamaye zuciyarsa. muryasa a sanyaye
yace ummi ki kwantar da hankalinki inshallahu bbu abinda zai faru zan riketa amana
yayinda a cikin zuciyarsa yake sauya kudirin ,ma,anar na karba dan kada Allah ya
tuhumeshi gobe kiyama.
Yayinda ta kasa km hannuta dake cikin nashi yake ta murzawa ahankali cikin wani irin salo
da yake sa tsagar jikinta tashi.
saboda nata hannu na kife ne cikin nashi tafin hannun.
gabadaya jikinta yayi tsanyi yasoma rawa rawa “dan samun saukin hanyar tsira da son cire
hannuta cikin nashi” yasa tayi saurin cewa na karba alkwarin ummi inshallahu ni dai
addu’arki kawai nafi bukata”
cikin sanyi ya sakar mata hannu.
Allah sarki ummi wani irin farinciki ne gyaraye da tsantsar kaunar ya mamaye zuciyarta.
murmushin jin dadi ta dinga yi .sannan ta mikar da zeenat din tsaye ta rungume ajikinta .
Tace Mamana ina miki addu’ar km bazan gushe wajen yi muku addu’a ba Allah ya muku
albarka ya azurtaku da ya’ya masu albarka.
Da kyar su aunty zahra suka rikota sakamakon rukunkume ummi da zeenat din tayi .
sun fito tsakar gidan dake cike da mutane.
Wanda Yawancin duk en’uwa ummi ne da kawayenta.
Kai tsaye gidan mahaifinta aka kaita shima nasiha may tsara jiki yayi mata sosai da nuna
mata tayi hakuri ta kula da mijinta, tamkar yadda mahaifiyarta tayi. yace naji dadi kwarai
da deeni yakasance miji agareki, ina muku fatan alkhari.
Ina da yakini deeni zai rike min ke da amana
da baki duk wata kulawar da ta dace.
Ahankali take cigaba da kukanta.. aranta kuwa cewa tayi uhmmmm.
abba bakasan asalin halin deeni bane
shiya ka fadi haka.
,halinshi na zahiri kawai kasani bakasan na baniba.
yace ta daina kuka duk abinda take da bukata karta zamo may rokon miji ta tmbye shi zai
mata
,har gidan big dady Sai da aka kaita agurguje suka dawo gidan kafin motar daukar amarya
tazo.
may gyaran amarya ce ta sake mata sabon gyara na musamman zeenat din ta sake fitowa
fes abinta.
Sai sheki take zubawa ga wani irin kamshi na musamman dake tashi ajikinta.
Duk da cikin estate din zata zauna hakan bai hana motocin abokan deeni dana fk cika
kofar gidan ummi ba .
Dan daukar amare.
Shemah aka soma saukewa, sannan zeenat aunty zahra ,ke rike da hannuta fuskarta rufe
cikin mayafi” har cikin gidan ta umarceta da tashiga da kafar” dama tare da yin Bismillah”
tayi kmr yadda aunty’n tace.
sannu ahankali har suka iso dakinta ta zaunar daita akan gado.
nan da nan mutane suka cika gidan dan ganin dakin amarya.
ahankali zeenat ta dan bude idanunta da suke rufe ” tana kallon irin dukiyar da Ummi ta
narka mata a daki wanda take jin ko mahaifiyarta ce a raye.
bazata iya mata kwatankwacin haka ba, dan ma tsayawa bada labarin irin kayan da Ummi
ta zuba mata a dakin ma bata lokaci ne .
Zaune dake a gefen laulausar zanin gadonta ta cure waje daya sakamakon tsaron daya
cika. Ahankali ta kai idanunta kan agogon dake manne da bangon dakin” Karfe goma
shada ta buga daidai”atsorace ta saki ajiyar zuciya saboda wani sabon tsoro dataji yana
kawo mata ziyara.
A ranta tace kar dai deeni barinni zaiyi in kwana ni kadai.
aiko idan haka ta kasance da nashiga uku dan a gaskiya bazan iya kwanta ni daya acikin
gidan ba.
Yan kawota basu minti goma da tafiya ba.
taji saukar yayyafi sama sama wanda ya hadasawa yanayin garin yin tsanyi hade da
kamshin kasa.
“ruwa bai yi yawa ba haka nan yayyenfin bai tsaya ba.
Kusan tun lokacin da suka tafi suka barta anan take zaune bata ko motsa ba Sai yanzu
datayi tunanin deeni na iya barinta ta kwana ita kada. Hakan yasa ta Mike cikin tsoro ta
kulle kofarta ta dawo ta zauna ,zamanta ke da wuya.
Tasoma jiyo Hayaniyar muryoyin maza daban daban” a cika gidan hakan yasa taji
tsinkewar zuciya Tare da faduwar gaba da.
hankali ta runtse idanunta tana jin yadda zuciyarta ke dukan uku uku kmr zatayi tsalle ta
fito waje.
Deeni tsaye a parlour’n yayi babbake tare da dakatar da abonkansa.
yace to to..Nagode sosai da kulawarku.
rakiyar ta tsaya iya nan..
yace to to… Nagode sosai da Kulawarku.
rakiyar ta tsaya iya nan.
ba Sai kunshiga ba.
fahad ne yayi murmushi sannan Yace ko baka fada ba ma anan zamu tsaya.
muma bashiga zamuyi ba.
,dan an dade da daina wannan.
Shr tayi tare da kamkame jikinta waje daya tsoro ne ke sake kawo mata ziyara.
tun tana jiyo hayaniryasu sama sama har tadaina taji dif.alamun basa cikin gidan sun fice
Juyawa suka sake yi tare ya raka su, fahad na ta mishi tsiya iri iri
Cikin sauri sauri “gudu gudu yashigo parlour sbd ruwan daya sake yin karfi duk ya jike
masa farin yadin dake jikinsa.
Ya tsaya kulle koina.
Ahankali ya murda handle din kofar dakinta yajita a kulle .
Ganin alaum murda kofa yasa ta sake mikewa tayi taje ta bude masa.
Tana may sunkuyar da kanta kasa.
cikin sanyi jiki ya shigo dakin tare da rungumeta tsam tsam ajikinsa da hannushi daya
“sannan ya ajiye tarin ledodin dake hannushi kamshin dake dakin kawai ya isa yasa kagane
rana ce ta musamman…

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]