[Advertisements⬇️]

WANI AURE CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WANI AURE

CHAPTER 10
Wani irin kallon mamaki fk yake masa, ,gabadaya ya zamo tamkar mutun mutimi a zaune
a gurin,
Yarasa meke damun brain din DEENi, mutun Sai girman kan tsiya da nuna isa ” wai shi
DEENi wani irin bahagon mutun ne ?
Shi sam bbu ruwan shi da fadar duk magana da tazo bakinsa.
In a low voice fk yace yanzu duk wahalar danayi akan yarinyar nan yatashi a banza
kennan?
A’a bakayi a banza ba tunda gashi “zan aureta gaskiya ce dai na gaya maka,dan kasan ita
din ba ra’ayina bace.
Amman narasa dalilin da yasa zuciyata ke muradin kasancewa tare daita ” fk ya sake
dubanshi sannan yace dan rainin wayo kawai kar mai dani kmr wanda bai san komai ba
mana.
,tunda har zuciyarka ta iya amincewa daita, har kaji zaka iya aurenta definitely kana sonta”
ko yaya ne”
deeni yaja tsaki hade da furzar da iska ta bakinsa” matsala dakai kennan rashin saurin
fahimta fk yace idan son da kake mata ne ,na fahimta Amman kace wai kai baka sonta km
kake kokarin aurenta, wannan ne fa bazan taba fahimta ba, DEENI ya sake first da huci
may zafi ranshi tasoma baci muryasa a sarke” yace da alamun kana son musamu matsala
dakai fa” muddin baka daina cewa Ina son yarinyar nan ba.
ldan km kafin son haka ya daga kafadarsa alamun Shikenan, parlour ya dauki shr na wani
“dan lokaci yayinda deeni ya jingina bayansa da kujera da yake zaune, hade da runtse
idanunshi ya dan jin daci maganar fk ‘ta yaya ma ” zai nace akan yana son yarinyar byn shi
yasan aure kawai yake da bukatar yi bawata ,aba soyayya ba..
maganar fk ce ta daki dodon kunnenshi” to yanzu meyye solution tunda yarinya ta rigada
ta amince?
Ahankali ya bude rikitattun idanunshi ya sauke su ,akan fuskar fk sannan yayi

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

magana

cikin sanyi tamkar wanda aka takura masa. Yace karkadamu zan samu yaya mahamud ,Ai
kagama may wuyar “ya maida idanunshi ya sake lumshe su tamkar dai yadda yayi dazu .
girgiza kai kawai fk yayi uhmm shi wannan bazai taba canzawa zai ba.
halinsa, na nan kmr dai yadda yasan shi” haka km yataso” shi komai baya so matsawar ba
ra’ayin sa bane” duk yayi magana ne akasan ransa,”.
Ganin ya bawa banza ajiyarsa yasa shima ya mike yayi masa sallama.
Daga gurin DEENi kai tsaye fk part dinsu shemah yayi yaja ya tsaya byn ya tura ayi masa
kiranta fk tafito sanye da doguwar rigar material puppy colour mai shegen kyau hade
yane kanta da karamin mayafe baki ahankali take isowa gareshi duk step daya Sai kirjinta
ya motsa tun fitowarta ya zubawa kirjinta ido kyam yana kallon yadda kirjinta ke motsawa
lumshe idanunsa shi yayi na wani lokacin sannan ya sake budesu ahankali mutuwar tsaye
a gurin har takaraso inda yake ta gaisheshi cikin sanyi jiki bai dauke idanunshi akanta ba
yacigaba da da binta mayataccen kallo da sallamarta iso inda yake ta gaisheshi ya amsa
yana sake bin koina na jikinta da kallo cikin sanyi tace yaya faruk Gani Yace Ai naganki
,daman nazo ne na fayace miki abinda na dade Ina boyewa akanki ,nan dai yasanar mata
koma, tunda yasoma magana tayi shr kawai hade da sunkuyar da kanta badan tana jin
dadin abinda yake kokarin fahimtar dai ba ahankali ta dago ta zuba masa idanunta Sai
data tabbatar ya gama fadar abinda yakawoshi sannan tace ,dan Allah yaya kayi hakuri wlh
akwai wanda zuciyata ta dade da kamuwa da soyayyarsa , Amman kayi hakuri idan
maganata ta bata maka rai yace Ina Gaza bata min rai Ai iya gaskiyar ki kika fada Sai dai ki
sani zuciyata bazata iya hakura dake ba Amman zan baki lokaci yi tunani akai tace nifa
bawani tunanin dazanyi akai ka dai yi hakuri ka nemi wata,ta juya ta wuce tabar sa nan
tsaye,da mamaki yabi bayanta da kallo ya dauki lokacin tsaye a gurin batare yasan abinda
zaiyi ba, Ganin tsayuwa nasa bata da wani amfani yasa yasoma kokarin daga kafafunta
ahankali tafe yake yana saka da warwara da tunanin malomasarsa a gurinsa,a fusace
shemah tashiga part dinsu tana zuba tsaki da zage zage har mmnta ta tambayeta abinda
yasameta tace matabakomi
Byn kwana biyu
Da misalin karfe takwas na dare fk ya km samu shemah da zance shi fa ba zai iya wani
hakura daita ba kawai tayi hakuri ta amincewa da bukatar domin shi yana matukar son ta
km aurenta yake son yi ,tace dan Allah yaya kayi hakuri wlh da bbu wanda nake so ne ,zan
iya soka dan kaima baka rasa komai da zankika ba, kadai yi hakuri kawai
al’amarin dayayi matukar dagawa fk hankali kennan yayi shr kawai yana kallon yanayinta
tare da nazarin kalamanta masu kokarin tarwatsa masa zuciyar rasa yadda zanyi daita yayi
can dabara tazo masa.ya tsareta da idanunshi Yace ke banso iskanci da rainin hankali fa ni
zaki cewa kina da wanda zaki kike so byn Banga uban da kike saurara ba ,lafazinsa yayi
mugun bata mata rai dan haka a ranta abace tace to dole ne Sai na aurenka kaje Kanemi
wata mana ko ana soyayya dole ? ta juya a fusace zata bar guri ya fizgota hannuta,
gabadayanta ta fado jikinsa, idanun ta zaro a tsorace, ,take taji wani irin faduwar gaba, .
Hannuwansa dukka yasa rungumeta tsam ajikinsa yana sauke ajiyar zuciya daidai
kunneta ya kai bakinsa Yace maimaita abinda kikace Ina jinki cikin tsiwa tace wannan wani
irin iskanci dazaka wani rungume mutun ? Ok nine ma nake miki iskanci?
Uhmmmm fa shemah karkibari muyi haka dake zaki amince ta girma da arziki ne ko km na
jawo soyayyata ta karfin tsiya ,.batare da na wahalar da kaina ba muryarta na rawa tace
anki a amince da soyayyarka.
ko ana so dole ne ?
, dan Allah ni kasake ni ,ya zuba mata manyan idanunshi kawai yasoma yawo da hannushi
a jikinta gabadaya jikinta ya dauki kirma abinda bai taba faruwa daita ba kennan tunda
take arayuwar ta ,wai namiji ya rabi jikinta har takaita ga runguma ,dan takaici ma batasan
sanda, kwalla ta cicciko a idanunta ba, hawaye yaga yana silalowa daga idanunta ahankali
ya sauke ajiyar zuciya, ya dan sausauta rungumar da yayi mata yasa yatsansa ya dangwalo
hawayen dake bin fuskarta yana kallo Yace duk wannan kukan akan nace Ina sonki ne kike
zubda hawayen ki?
tayi shr taki cewa komai dan haushi ji tayi kmr ta daura hannuta akanta ta kurma ihu
ahankali ya sake maida ita jikinsa ya rungumeta yana shinshina wuyanta daidai nan Sai ga
big dady dake dawo daga masallaci, a tsorace yake binsu da kallo cike da mamaki da
alajabi abinda yagani, meke shirin faruwa km yau acikin zuri’ arsu ,fk yacigaba manneta da
jikinsa yana rarrashi ta amincewa aurensa, dagowar nan da zai lyi karaf idanunsa suka
sauka kan big dady dake tsaye duk da duhu ne hakan bai hana gareshi ba gabansa yaji yayi
muguwar faduwa jikinsa ya dauki kirma duk da ya tsorata Amman yaji dadi Ganin da big
dady yayi musu ,yasan hakan zai sa a aura masa shemah batare da bata lokaci ba tsabar
frigice yasa yakasa rabata da jikinsa gabadaya jikinsu rawa yake shemah da batasan wainar
da’ake tuyawa ba sake lafewa tayi ajikinsa saboda irin rungumar dayayi mata ba wacce
zata iya kwacewa bace har big dady ya wuce su a gurin shemah batasa big dady yagansu
ahankali fk yasoma rabata da jikinsa har zuwa yanzu hawaye bai daina bin fuskarta ba
hannuta yakamo yasoma tafiya ita kum tana biye dashi bbu wanda ya iya cewa
dan’uwansa komai har yakawo part dinsu yaja ya tsaya ahankali Yace shemah kiyi hakuri
dan Allah kibar kuka ba nufi na kuraki ba Ina matukar kaunarki bansan lokacin dana fara
sonki ba Amman zan baki lokacin kiyi tunani akai ,zan dawo zuwa jibi yana gama fadar
haka ya juya da kyar yake iya daga kafafunsa tsabar frigice da nauyin da suka masa
zuciyarsa tamkar zata buga, dan fargaba haduwarsu da big dady shi yasan ba makuwa
tunda har big dady yagansu aure kmr anyi an gama Amman kunya fa ,har ya iso part dinsu
wanda kusan nan samari suke zaune wayanda basuyi aure
Itama tana shiga dakisu ta wuce kai tsaye tana kuka , mamanta dake zaune a parlour tace
ke lafiyarki Amman ko juyo batayi ba fadawa tayi kan gado tana risgar kuka to meye yaya
faruk yake nufi daya sonta alhalin ita DEENi take mutuwar so .. Dan haka bata taba
aurensa ba ,tunawa datayi ba’a musu auren dole a family dinsu sai sun amince da juna
yasa taji hankalinta ya kwanta Amman gabadaya jikinta yayi bala’in sanyi haka ta wuni a
daki batare data sake fita ko parlour ba ,fk bai dawo ba kmr yadda Yace mata kusan sati
tsakani shiyasa tayi tunanin ko yayi wa kansa fada ne ya hakura daita dan haka ta sake
abinta kwasam Sai gashi a wani daren lahadi byn tagaishi a dage ,yayi murmushi yace yazo
ne akan maganar su ,a fusace tace wata magana kennan i tough mun gama da wannan
zance tunda nace ban sonka, Yace haka kika ce ,tace eh ko dole soyyaya dakai Yace uhmm
Amman dolenki ki aureni ya wuce batare da damuwa,
SOY WA Emulsifyi. Kola nut Brown Su.. Prime Vir.
DEENi yasamu yaya mahamud yayi masa bayanin shi kuma ya samu big dady da zance
tsohon yaji dadi Sosai jin sun hada kansu yace Shikenan bbu damu zai tuntubi yarinyan
tukun asan abinyi .
Nan dai aka saka ranar aure tare da yanka sadaki yaya mahamud ne yayi komai ko sisin
Kobo bata fita daga aljihun ogo deeni ba ko mahaifin zeenat yayi murna sosai da jin DEENI
ne zai aure diyarsa
Anyaka sadaki da dukiyar aure naira duba dari biyar wanda duk a aljihun yaya mahamud
suka fita .
Da kyar big dady yashawo kan Ummi dan tuburewa tayi ita sam bata yarda da wannan aure
ba big dady yace Ai tunda dai yara sun hada kansu km suna juna Ai Ina Gani magana
takare fatanmu Allah ya zaunar dasu lfy .
Lokacin da aka sanar da DEENi ansa ranar wata biyar deeni Yace wa yaya mahamud
lokacin nan bai yi yawa ba kuwa?
Dan akwai aiki da zai kaini akwaibon Ina Ganin zaifi kyau a takaita lokacin koma ba dan
haka anawa raayin nafi son ayi nan da wata uku yaya mahamud yace Shikenan kabari dai
zan samu Ummi da maganar.
Zaune take a cikin extra room dinsu wanda kusan yanzu can tafi zama tunda aka sa musu
rana da yaya DEENi ta zabga uban tagumi tana mamakin hali irin na yaya DEENi yau kusan
wata biyu Keenan dasamusu rana Amman ko sau daya bai taba kiranta da sunan zance ba
haka nan ko cikin part din Ummi yashigo bata ishe shi kallo ba takan ji tsoro da frigice sun
shigeta a duk sanda taga yaya DEENi nuna rashin damuwarsa akanta ,a kasan ranta tace,
anya kuwa banyi kuskure da wautaba wajen saurin amincewa aurensa ba domin fa zuwa
yanzu tasoma sarewa anya kuwa yaya DEENi yana sonta ?
kullum miskilancinsa sake gaba yake har zuwa yanzu dabatason cikakken matsayin ta a
gurinsa ba ,son auren yasoma fice mata arai domin ita kadai tasan fargaban da take cikin
zuciyarta ga,gorin da Ummi kebinta dashi kullun garin Allah ya waye, dan haka ta yanke
hukunci samun yaya faruk dan ta inda aka hau tanan ake sauka.ta shirya taje har part
dinsu tace daman tazo ne akan maganar mu da yaya DEENi idan fa abin nan bazai yiwu ba
gara tun yanzu abarshi
Fkya gyara tsayuwa sannan yace wani abu ne ya faru ? Tace to yaya faruk a haka ne zamu
fahimci juna in San abinda yake so shima yasan wanda banaso shi fa aure ba banza bane
kmr yadda ya dauki komai tacigaba bai taba kirana ba km ko gida yashigo ban ishe shi
kallo ba shi bashi da lokacin kowa sai na kansa fk yace kiyi hakuri bawai zangoyi bayansa
ba aikine yayimasa yawa kiyi nasa uziri Amman kina ranshi zeenat ta tabe baki dan tasan
karya ne yace wai tana ran yaya DEENi Ai abinda kake son baka sakaci dashi fk yacigaba
komai yakusan zuwa karshe da zarar kin zama a gidansa nasan dole ya baki dukkan lokacin
sa,zeenat tayi shr ne kawai ba wai dan maganar tashigeta ba , fk yace tayi hakuri zai masa
magana da sauri ,zeenat ta dago tace dan Allah yaya kar kace ni nayi maka maganar ya
sake dubanta sosai yaga duk ta wani frigice yace karki damu ni nasan abinda zanyi
Fk yakira deeni a waya Amman ba’a daga ba
Da misalin karfe goma na dare fk ya amsa kiran DEENi tare da yin sallama byn sun gaisa
yace friend dazo inata kira baka daga ba DEENi ya runtse ritattun idanunshi tamkar na may
jin bacci sannan yace wlh aiki ne yasha kaina lafiya dai ko ya fadi cikin kasala dan duk a
gajiye yake fk yace lfy dama akan maganar yarinyar nan ne yakama mushirya muje zance
gurinta, ,anhakali DEENi ya bude idanunshi jin abinda fk yace muryasa a sarke yace wacce
yarinyar km?
Fk yace sai karinka yin kmr baka san da zance ba,byn nasan tana ranka DEENi yace dan
malam karkadameni go to the point dan bangane wacce yarinyar kake nufi ba fk yace Ai
dole ka manta da ko wacce yarinya ce tunda kaga kasameta cikin kwanciyar hankali km
Ummi ta amince tsaki yaja kana yace wai zeenat kake nufi ?
Yasake jan wani tsakin mtssss wani irin hira kum kmr muna kauye byn angama magana sai
jiran lokacin fk yace kai mugun dan iska ne Ai duk da haka yakamata muje dan ita yarinyar
tasan raayinka kai ma haka ku samu fahimtar juna DEENi ya katse shi da itace Keenan ta
aiko ka fk yace ko daya ni dai naga dacewar haka DEENi yace to baza’aje ba… Kar Allah
yasa mu fahimci juna, ita tun tasowarta, bata san abinda nake so da wanda ba,fk yace
idan ita tasan abinda kake so da wanda baka so kai kasan nata?
DEENi ya sake jan tsaki hade da kamo lip’s dinshi na kasa yana dan ciccizawa sannan
ahankali yace to sarkin yakinta ni ba haka taarina da raayina yake ba Ina tunanin in har
zanje zance gurin budurwar,zanje ne dan tallar kaina in samu gindin zama to ni narigada
na samu shigar ,bbu dalilin da zai sa na takurawa kaina me kadauki ni ,nafa san irin son da
yarinyar nan take min ,kawai dai ni banda lokacin wannan shirme dakace km nasan ita ta
aiko ka fitowa ne kawai bazakayi kafada ba.
Fk yaja tsaki shima yace kai ,dan Allah wani irin bahagon mutun ne?
To wlh ka canza wannan budadden halin naka, to ko waya ce ka tsiya mata ,DEENi yace
shima din baza’a tsiya ba ,duk abinda zai faru ya faru ciki har da fasa aurena ,fk yace kai fa
kafiyye kafiya ,da maida karamar magana tazama babba, yace sake cewa yanzu dai kayi
hakuri dan girman Allah ka Sai mata ko karamar waya ce.
DEENi yace kasan Allah ko game bazan Sai mata ba, ballanantana waya, tunda har
taiya zuwa ta sameka da maganar bana kiranta fk yace kadaina cewa tasameni ni kawai
Gani nayi ya dace muje DEENi ya tabe baki tamkar fk din na ganinsa Shikenan kai ka sani ni
km kar ka sake damuna da maganar wata yarinya ya kashe wayarsa batare da ya tsaya jin
abinda fk zai ce ba .
Wasa wasa lokacin bikin ya dinga karatowa da kwanaki ya wattani har zuwa yanzu dayayi
sauran wata cif cif ayi daurin aure to Ganin kurewar lokaci yasa DEENi yasamu Ummi da
maganar shifa baya son zamansa cikin estate din taje Ummi tayi kicin kicin da ranta
sannan ta dago tana dubansa tace bangane abinda kake nufi ?
Sai da ya sake maimaita mata tukun Ummi tace sam ita bata yarda ba salon yaje yana
dinga cin amanar Yar marainiyar Allah ga babbin gurin bid dady yasa an Gina musu shida
sauran enuwansa shine kai dan iyayi zaka ce bazaka zauna ba ,to wlh kaji na rantse anan
zaku zauna Sai naga yana yin zaman naku cikin yin kasa da murya yace Shikenan first lov
na hakura duk abinda kika ce shi za’a yi tace da dai yafiye ma a yi mutun Sai girman tsiya
da iyayi yace to kiyi hakuri
Zeenat dake sauransu ta lumshe idanunta jin Ummi bata amince ba dan tana matukar jin
tsoro zaman daga ita Sai shi ahankali cikin sanyi jiki ya mike idanunshi suka sauka akan
inda zeenat ke kwance suka hada ido da sauri ta gaidashi hade da dauke idanunta ,bai
sake kallonta ba bare ya amsa gaisuwar ta.
Shirye shiryen biki ya tashi gadan gadan enmata duka a tare suke shirinsu dan yanzu
zeenat ta saki da shemah sun koma kmr da ganin da tayi wanda ma take haukar akansa bai
san da zamanta ba wata safiya suka shirya zuwa siyayar su irinta amare mutun biyu ne
abayanta mota Maryam da shemah yayinda zeenat ke gaba kai tsaye kasuwar Lagos suka
nufa sukace derive yayi parking a idimota su kum suka shiga cikin market din
Derive yaja ya tsaya suna fitowa da yaya kamil suka soma cin karo tun shigowar motar
dayaga hango zeenat zaune ya zubawa motar ido har sanda ta fito ahankali suka jiro suna
hira Amman banda zeenat dataji gabanta ya yanke ya fadi dan tun lokacin da aka mata
rana,rabonta dashi dai dai sun kusan geftashi yakira sunnanta zeenat..tacigaba da
tafiyarta dan batason abinda zai km hada ta dashi cikin sassarfa ya biyo bayanta yasha
gabanta cak taja ta tsaya suna kallon junansu,yayinda su Maryam suka cigaba da tafiyarsu
suna tsaye batare da dukkansu suyi yunkurin yin magana ba kamil ya gyara tsayuwa ya
tura hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa ya kafeta da idanunshi ta sunkuyar da
kanta kasa sannan tace lfy yaya ka tsayar dani muryasa a dashi yace Ifyr ce takowa haka
yanzu zeenat kin kyauta kennan ki zabi wani kibarni byn duk lokacin dana dauka Ina fama
da soyayyarki,a she kinsa bakya sona kibarni inata faman hauka akanki tace Allah yaya ba
haka bane Amman kayi hakuri dan Allah, ya sake gyara tsayursa, yayinda idanunshi ke
kanta har yanzu yace iya hakuri ne kawai zai wadatar da zuciyar da tayi sama shekara
biyu tana mata da miki so…. yace Shikenan bbu komai Nagode Kwarai da abinda kika saka
min tace ka dauka haka Allah yaso ni din ba matar ka bace yayi murmushin karfin hali
sannan yace haka ne fa al’amarin ubgj Amman agaskiya DEENi ya cuceni ,tace kabar cewa
tayi ta dago suna kallon juna fuskarta dauke da murmushi ta bude baki kennan Sai ga
motar DEENI ta kuno kai cikin compound din km shi suke facin Ai take maganar ta ta tsaya
sakamakon DEENi data Gani zaune a mota yana kallonsu duk kasancewar alkwai dan
duhun magariba hakan ba zai sa takasa gane bscin ransa ba , gabanta ya yanke ya fadi .
,shima kamil din shr yayi bai sake yin magana va kusan minti goma yayi yana kallonsu koda
bata ga fuskasa sosai ba tasan a daure take ,har sanda DEENi ya fito yayi matarsa key
idanunshi na kansu ,cikin tsoro da frigice zeenat tace ni zanshiga ciki kamil yace Shikenan
Allah yabaki zaman Ify ta gefensu yazo yazo ya gifta hade da jan tsaki sannan ya wuce. a
fili ta furta wayo Allahna nashi uku kamil ya sake yin murmushi dole sannan yace da’aka
me,da kika shiga uku, nifa Banga abinda ya birgeki a DEENi ba,har da kika iya zabarsa,
kalli fa yadda jikinki ke rawa saboda Allah tamkar kinga wani malaika tsaki taja hade da
zabga masa harara dan Allah kabarni naji da damuwa Ai duk kai kaja min matsala Ina
zaman zamana da yanzu Ina cikin gida
Ni dan girman Allah kabarni na wuce tun kafin laifina ya Karu.
,Murmushi karfin hali kawai yayi ,tare da nuna mata hanya da hannushi alamun ta wuce
din.
kasa tafiya tayi ” sakamakon idanushi da taji yana mata yawo a gangar ajikinta .
Gabadaya taji tamkar ya daureta ne .
takasa kwakwaran motsi” jikinta yayi bala’in yin sanyi.
taji ina ma zuciyarta na da yanci da bata kamu da soyayyayar deeni ba.
Da bbu shakka zata iya hakura da kamil tunda shima yana da nashi kyawun daidai
gwargwado.
Yayi shr kawai yana kallonta” kaunarta ce ke tasomasa tare da nukurkusan zuciyarsa.
ya dinga jin tamkar ya halaka kanshi lokacin daya tsinci idanun deeni akan su.
ya dinga kallonta “yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa ” da gske dai yana shirin yarasata
kennan ,rashima na har abada.
km ta haramta ta zama matarsa wani irin zugi zuciyarsa keyi ahankali
Yakira sunanta..Zeenat kina son deeni sosai ko ? Cikin sanyi
ta dago kanunun idanunta ta kalleshi dasu “sannan tace, wannan wace irin tmby ce ?
Yace amsa kawai nake bukata ,tace to bana son shi shikennan.
Karkimin karya mana Kina son shi kalli.kalli yadda yanayinki ya canza jikinki har rawa
yake saboda kin ganshi.
ya tabbata kennan baki sona ,rainamin hankali kawai kika dinyi.
A fusace Zeenat tace Nifa karka zageni da laifi da bansan na aikata ba. mgnr ina sonshi ko
bana sonshi ma duk bata taso ba.
kai kanka kasan bantaba amsa maka da Ina sonka ba.
ballanantana kace yaudararka nayi ka dai yi hakuri Allah ya hada kowa da rabonsa , yace
ok yanzun duk tarin son da na miki yazama tarihi kennan ?
Ta Zuba mishi ido kawai dan tasan duk abinda zata gaya masa ahalin yanzu ba fahinmta zai
yi ba shiyasa tayi shr taki cewa komai
Ahankali Ya girgiza kanshi kawai batare da sake cewa mata komai ba ya juya yasoma
tafiya.
Tayi jim jikinta ya mata tsanyi ,bata ji dadin yadda taga reaction dinsa ba .
tasan kwata kwata bata kyautawa masa ba. Amman ba yadda taiya da zuciyarta ” DEENi
shine muradin ranta.
raba zuciyarta dashi tamkar barazana ce ga rayuwarta.
Duk da taji ba dadi ba hakan bai sa taji tausayinsa yashigeta har taji zata iya hakura da
auren DEENi. Dan haka ko ajikinta ta wuce.
Jikinta a sanyaye yashigo part dinsu hankalinta a tashe
Tana shiga daki Ta daure fuskarta “ganin ya shigo dan a zatonta yana shigowa zai
zabgamata mari.
sanye yake dat shirt din su na sojoji da wando.
Tana jinshi yacewa Ummi shi ya wuce sai da safe “Ummi tace can zaka kwana ne yau ?
yace eh “akwai abinda zai maidani tace to Allah ya tsare min kai ya km bada sa’a ,ka
yawaita addu’a dan Allah yace Ina yi sai dai zan kara kulawa.
ya sake wuce zeenat zaune ko kallon inda take baiyi ba.
bayansa tabi da kallo tana jin wata irin masefaffiyar kaunarsa nabin jininta, hade da ratsa
kowani part najikinta.
, aranta tace attajirina kennan ,miskilili zaki maza.
nan ya fita yabarta da dadeden kamshinsa tare da fargaba.
sai dai, da ganin yanayinsa yana cikin tsananin fushi.
da misalin karfe tara dare tana kwance akan gado” juyi kawai take, yayinda zuciyarta ke
nazari akan irin kallon da yaya deeni yayi mata, dazu sakamakon ganin da yayi mata tare
da kamil.
taji tamkar takirashi tabashi hakuri amman tsananin tsoransa ya hanata aikata hakan,
zuciyarta ce ta bata shawara kan tura masa text ba sai takirashi ba.
dan haka ahankali ta mirgina ta janyo wayar Ummi dake kan bedside.
ta soma rubuta masa text da niyar turawa masa ” sai km taji zuciyata na gargadinta akan
kar ta sake ta tura masa text din . Tayi tana tunanin ,ta tura ne ko ta share
Tayi haka ya yafi sau goma kafin daga karshe tayi jahadi ta tura masa.
Yaya dan Allah kayi hakuri idan na bata maka rai dazu wlh bazan sake ba… daga zeenat
Byn ta tura sakon ne ta goge “sannan takoma ta kwanta lamo tana jin yadda kirjinta ke
tsarkewa,ahankali ta lumshe” idanunta ,xuciyarta ke beating tare da yi mata fadar abinda
ta aikata.
ita kanta tasan tayi babban kuskure sosai wajen tura masa text ,dan tasha jin yadda yake
yawan yi complain akan tura masa sako ko kiran wayarsa yayinda yake kan aiki,
Sai dashi duk lokacin daya gadama zai kiraka idan km baka dauka ba yazama matsala.
dan haka tayi shr kawai tana fidda numfashi sama sama.
Tsawon lokaci tana kwance “tana tunanin abinda zai biyo baya idan yaga sakonta, addu’a
take Allah yasa ba karawa kanta laifi tayi ba agurinsa.
take tsoro da fargaba suka taru suka dira mata “alokaci daya.
Idanunta a lumshe har lokacin tana saka da warwara deeni dan ra’ayi baka masa dole
ballanantana ta tursashi.
can taji alamun shigowar sako a zaburi ta mike” ta rarumi wayar jikinta har rawa yake.
idanunta ne suka ci karo da reply dinsa.
hankalinta a tashe tasoma karanta text din .
Ke…Banida lokacin karanta wannan shirmen naki na baza, aikina yana da mahimmanci
a wajena banida lokacin hada aikina da zantuttukan marasa ma’ana dan haka ki kiyaye
gaba
Tana gama karantawa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta sulale takoma ta kwanta tare da
lumshe idanunta.
Tabbas tasan ta daukarwa kanta abinda yafi karfinta
tayi shr ,tana son tayi nazari akan kalamansa tasan dai yakaranta sakonta sarai
tsabar rainin wayo ne da miskilanci irin nasa.
yasa ya nuna kmr bai da lokacinta
tayi juyi tana mai tausayawa kanta na nacewa auren DEENI.
yanzu Gabadaya son aurensa ya sire mata ya fita akanta.
, tsoro aurensa take km sai yanzu maganganun Ummi ke sake shigarta.
Inda tace zeenat,kin fahimtata ne kawai deeni dana ne dana haifa a cikina.
baki fini sonshi ba sanin halin miskilancinsa da girman kai irin nasa yasa kikaga naki
amincewa da aurenku wahala kawai zakisha a hannushi
gara yaje waje can ya nemo matarsa.
batayi aune ba taji saukar hawaye nabin kuncinta” bata hana su zubowa ba ,domin ita
kanta zata fi so ta zubar dasu ,kodan samun natsuwarta.
Km ko ba komai hakan zaisa taji sanyi da ragewa kanta radadin abinda ke nukurkusan
ruhinta.
Jikinta yayi matukar yin tsanyi ahankali tasoma sambatu..
Wayo Allahna… ni zeenat yaya zanyi da zuciyata data ta makance akan kaunarka.
Ina sonka yaya deeni har bansan yadda zan misalta tarin soyayyata gareka ba.
kaunarka ajinina da ruhina yake.
daita Allah ya hallice.bazan iya daina sonka ba muddin rai
koda baka sona ni Ina sonka km zan iya jurar komai akanka ,raba zuciyata da soyayyarka
tamkar rasa numfashina ne.
Haka tayi surutai har sanda Tajiyo motsen shigowar Ummi.
tayi shr tare da saurin juya mata baya.
tana cigaba kukanta, kasa kasa batare Ummi ta Gane halin da take ciki ba.
Zuciyarta ke mata wani irin ciwo da radadi mai zafi.
Washegari ma sukusuku ta tashi tamkar wace batada Ify ta rame sosai ” idanunta a
kumbure kallo daya Ummi tayi mata ,ta Gane kuka tayi
km daman tana lura daita jiya bawani baccin kirki tayi ba.
taji wani irin tausayinta ya tsarga mata har cikin zuciyarta “dan tasan tunda ta kwallafawa
ranta auren DEENi, ta hadu da babban aiki.
km sai ta hadu da abinda yafi haka.a addu’a dai zata cigaba dayi musu Allah ya kauda
fitana atsakaninsu.
Ahankali Ummi takira sunanta ..ta dago da kumburarun idanunta tana kallon Ummi dasu
batare da tace mata komai ba byn gaisuwar datayi mata.
,Ummi tace meke damunki ne zeenat naga duk idanunki duk sun kunbura” sai naga ma
kmr kuka kikayi.
Zeenat ta danyi murmushi dole sannan tace kai Ummi bbu komai fa, idanuna kemin ciwo
,km jiya da ciwon kai na kwana.
ta fadi hakan da hankalin Ummi ya kwanta.
Ummi tayi shr kusan minti goma tana kallonta sai da tagama nazarinta tsab sannan ta
numfasa tace shikennan Allah ya sawake kinsha magani ?
Zeenat ta girgiza kai kawai.
Ummi tace maza ki tashi kije daki ki dauko magani kisha.
a sanvave ta mike ikinta babu kwari tace to..
lumshe idanunta.
Tabbas tasan ta daukarwa kanta abinda yafi karfinta
tayi shr ,tana son tayi nazari akan kalamansa tasan dai yakaranta sakonta sarai
tsabar rainin wayo ne da miskilanci irin nasa.
yasa ya nuna kmr bai da lokacinta
tayi juyi tana mai tausayawa kanta na nacewa auren DEENI.
yanzu Gabadaya son aurensa ya sire mata ya fita akanta.
, tsoro aurensa take km sai yanzu maganganun Ummi ke sake shigarta.
Inda tace zeenat,kin fahimtata ne kawai deeni dana ne dana haifa a cikina.
baki fini sonshi ba sanin halin miskilancinsa da girman kai irin nasa yasa kikaga naki
amincewa da aurenku wahala kawai zakisha a hannushi
gara yaje waje can ya nemo matarsa.
batayi aune ba taji saukar hawaye nabin kuncinta” bata hana su zubowa ba ,domin ita
kanta zata fi so ta zubar dasu ,kodan samun natsuwarta.
Km ko ba komai hakan zaisa taji sanyi da ragewa kanta radadin abinda ke nukurkusan
ruhinta.
Jikinta yayi matukar yin tsanyi ahankali tasoma sambatu..
Wayo Allahna… ni zeenat yaya zanyi da zuciyata data ta makance akan kaunarka.
Ina sonka yaya deeni har bansan yadda zan misalta tarin soyayyata gareka ba.
kaunarka ajinina da ruhina yake.
daita Allah ya hallice.bazan iya daina sonka ba muddin rai
koda baka sona ni Ina sonka km zan iya jurar komai akanka ,raba zuciyata da soyayyarka
tamkar rasa numfashina ne.
Haka tayi surutai har sanda Tajiyo motsen shigowar Ummi.
tayi shr tare da saurin juya mata baya.
tana cigaba kukanta, kasa kasa batare Ummi ta Gane halin da take ciki ba.
Zuciyarta ke mata wani irin ciwo da radadi mai zafi.
Washegari ma sukusuku ta tashi tamkar wace batada Ify ta rame sosai ” idanunta a
kumbure kallo daya Ummi tayi mata ,ta Gane kuka tayi
km daman tana lura daita jiya bawani baccin kirki tayi ba.
taji wani irin tausayinta ya tsarga mata har cikin zuciyarta “dan tasan tunda ta kwallafawa
ranta auren DEENi, ta hadu da babban aiki.
km sai ta hadu da abinda yafi haka.a addu’a dai zata cigaba dayi musu Allah ya kauda
fitana atsakaninsu.
Ahankali Ummi takira sunanta ..ta dago da kumburarun idanunta tana kallon Ummi dasu
batare da tace mata komai ba byn gaisuwar datayi mata.
,Ummi tace meke damunki ne zeenat naga duk idanunki duk sun kunbura” sai naga ma
kmr kuka kikayi.
Zeenat ta danyi murmushi dole sannan tace kai Ummi bbu komai fa, idanuna kemin ciwo
,km jiya da ciwon kai na kwana.
ta fadi hakan da hankalin Ummi ya kwanta.
Ummi tayi shr kusan minti goma tana kallonta sai da tagama nazarinta tsab sannan ta
numfasa tace shikennan Allah ya sawake kinsha magani ?
Zeenat ta girgiza kai kawai.
Ummi tace maza ki tashi kije daki ki dauko magani kisha.
a sanvave ta mike ikinta babu kwari tace to..
kanta
da son janyowa kanta martabarta ta Diya mace .
Sai da ta dauki mintina tukun ta mike cikin sanyin jiki ta nufi dakin shi.
tsaye take akan kafafuntaa bakin kofar dakinsa zuciyarta na dokawa
tsoro taji yana shigarta sai ta daura hannuta kan handle din kofar.
sai tacire hannuta da sauri.
,da kyar tasamu tattaro duk wani kuzarin dake jikinta
karfin hali tayi wanje murda handle din kofar da iya karfinta tashiga parlour’n da
sallamarta.
shr parlour bakajin komai sai karar TV tsayawa tayi tana jirashi kusan 5 minti bata ga
alamunsa ba ko jin motsensa batayi ba .dan haka ta yanke shawarar shiga Bedroom
dinsa.
tana shiga dakin gabanta ya tsananta faduwa, cikin sanyin murya ta sake yin sallama .ya
amsa da kyar km a ciki .
Zaune taganshi yana operating system sanye cikon wando three counter da pure whit
singlet, ahankali take takowa har inda yake yayinda kanta ke sunkuye
tsugunnawa tayi a gabansa muryata na rawa tace Gani Yaya
Bai ko kall inda take ba hasali ma operating din system dinsa yacigaba dayi.
” tayi kusan minti goma tsugunne a gabansa batare daya dago idanunshi ya kalleta ba.
Shr Tayi tare da” sunkuyar da kanta kasa
Yayinda zuciyarta ke tsananta bugawa.
cikin daddaden muryarsa may cike da dadin sauraro “fiyye da komai datafi kauna
Yace tun yaushe kike tare da wance sakaran Dana ganku shekaranjiya ?
Batasan sanda ta zauna ba ,dan tsabar frigice da tsoron daya shigeta na lokaci guda .
,Zuciyarta ce tasoma rawa…rawa tare dokawa .tarasa yadda me za tace.
cikin ya’n sakanni nan hankalinta yayi matukar mugun tashi. kwakwaluwarta “tashiga
tariyo mata abinda ya faru a shekaranjiya din.
gabadaya tagama
frigita da tmbyr daya jiho mata, tunaninta ya ta’alaka ne akan ya manta da abinda yagani
din.
dan ganin ya share Bai nuna koda a fuskarsa ba.
da kyar ta iya bude bakita tare da son nuna masa, itama batasan inda zancesa ya nufa
ba.
, muryarta cike da rudani tace wa kenan ?
Sai Lokacin ne ya dago rikitattun idanunshi ya dubeta dasu .
tare da zabgamata wata uwar harara.
cikin sanyayyayiyar muryarsa, ta isa ya sake yin magana Yace wawa..ni zaki waskewa
ya nuna kirjinsa da yatsansa
bakaramin laifi zaki karawa kanki wajen nuna min bakisan abinda nake nufi ba.
Domin bana bukatar
rainin hankali ko karyata min abinda idanuna suka gane me.
Amsa tmbyta kawai nake da bukata.
take muryarta tasoma rawa alamun kuka keson kufce mata.
,ahankali ya daura yatsan hannunshi akan lip’s dinshi ” shiii… karki kuskura naga
Tear’s dinki ko rawar murya.
dan banida bukatar su .
Isaid tun yaushe kuke tare, that’s ol…
A boye ya dinga sauke ajiyar zuciya sannan ya
yacigaba ko duk dadewarku bakisan tun lokacin da kuke tare ba ?
Lokacin daya taji maganarsa na neman birkita mata Brain dinta. to up side down” wani irin
rudewa da gigicewa ta sake yi .
Ba bakinta kadai ke rawa ba ,yanzu kam har gangar jikinta rawa yake.
Ta dawo tamkar wata zautacciya Da kyar tasamu ta iya hadeye abinda taji ya tsaya mata a
makoshi.
tare da zubda hawayen da suka taru a idanunta, cikin rawar murya tace shekara biyu
kennan.
Tana gama fadar haka
, tayi saurin sunkuyar da kanta kasa dan gudun jin saukar mari.
yayinda hawayen tausayin kanta suka cigaba da bin kuncinta.
a hankali ya dinga girgiza kanshi shekara biyu kennan ya sake maimaitawa kansa.
Cikin sanyi ya maida jikinsa” ya kwanta rigingine ya Kuma cigaba da operating din
system dinsa batare da ya sake ce mata komai ba.
Take yaji zuciyarsa ya dauki beating,wanda yarasa dalilin jin haka
Kusan minti shabiyar kennan idanunshi na kan system dinshi yana cigaba da aikinsa.
,wanda mutun zai iya dauka aikin ne kawai a gabansa”
amman a zahirin gaskiya hankalinsa ya rabu gida biyu ne. kan aikinsa da nazarinta
yanayinta ” maganarta ba iya kunnenshi kadai ta tsaya ba ” har gangar jikinsa takaiwa
farmaki. ahankali ya dinga furzar da iskar mai zafi daga bakinsa . gashi dai magana yake
son yi amman taki fitowa sakamakon zuciyarsa dake bugawa.
da kyar yasamu iya bude bakinsa.
yace kina nufin shima sonki yake yi kennan
Tsoro da faduwar gaba ne suka taru suka mamaye zuciyarta.
cikin in..inna.tace wai wai haka yace “amman, dan Allah kayi hakuri .
da sauri DEENi dake rigingine ya mike zaune cikin daga murya yace mene? Nayi hakuri
ubanki”
Da sadakin nawa akanki idan da kuna kula juna ,I don’t care.
Amman yanzu iskanci ne yasa kika, cigaba sauraran wancen sakaran dan tsabar kin raina
min hankali.
Bakinta na rawa tace Ai shima yasani” shiyasa ma yace ya hakura dani.
, ok da shi m…
sai km yayi shr yakoma ya kwanta. hade da runtse idanunshi. Lips dinshi na kasa yakamo
yana cizawa a hankali ahankali ” cikin zafin rai da kunar zuciya ya nuna mata kofa da
yatsansa alamun ta bar masa dakin .
,kasa Mikewa tayi tsabar tsoro gabanta yacigaba da faduwa ,muryarta na rawa” ta sake
yunkurin bashi hakuri dan Allah yaya kayi hakuri wlh mun rabu dashi tun ba ya…
Wata irin tsawa ya daka mata take maganar ta makale “tun batakai ga karasa yin ta ba
wanda hakan yasa ta mike tsaye da sauri batare da tashirya yin hakan ba.
jikinta yacigaba da kirma.
Ahankali ya bude rikitattun idanunshi “kasa kasa yake kallonta ji yake tamkar ya tashi ya
shakota” tare da yaryarfa mata maruka” ko zai dan samu ya ragewa kansa tension din
daya addabe shi tun shekaranjiya.
amman ina baya ji zai iyayi haka.
kodan “
,sanin halin Umminsa.
yasa muddin yayi haka ranta zai baci ,hakan kadai ne yasashi kasa aiwatar da komai
akanta.
idanunshi ya watsa mata yana mai sake kafeta dasu wani irin kwarjini ya sake yi mata
wanda hakan shi ya kawo katsewar duk wani kuzarin dake tattare daita.
Muryasa a sarke yace live dis room now before I skater you Ai Bai kai ga rufe bakinshi ta
kwasa
da sauri ta soma kokarin barin dakin.
Hade da tabe baki a ranta Tace matsefafe banza kawai “anya zan iya daukar wulakancin
nan naka kuwa?
ta fice tana goge gumi duk da ba lokacin zafi bane jikinta sharkaf yake da gumi.
Tana fita ta dinga fidda numfashi sama sama tamkar mai cutar asma.
sai data goge gumin daya cigaba tsatsafo mata sannan ta shiga daki .
Zaune ta samu Ummi. Tana balle magani zata sha.
Ummi tabita da wani irin kallo tace ke km daga ina haka? Tace yaya DEENi ne yakirani”
Ummi tace yashigo ne ta girgiza mata kai” kawai ” alamun Eh ” to yana ganki duk a frigice
kmr wacce tayi gudun tsire ,ko wani abun yayi miki.
zeenat tayi narainarai da idanuwa tace A’a Ba abinda ya min.
Ummi ta sake dubanta hade da tabe baki tace ke kika sani ma idan wani abun yayi miki.
,ba kinki tsayawa waje daya ba, sai wani rawar iki kike yi akansa dan tsabar sakarci irin
naki.
Zeenat dake tsaye tana duban Ummi taji tamkar ta zubda kwalla dan jin takaicin abinda
Ummi tace mata
Tace to ni yanzu Ummi wani rawar kai nayi km ? tmbyta abu kawai yayi fa.
Tace to me Yace miki ko abinci zai ci zeenat ta sake girgizawa Ummi kai.
, baki da bakin ne da zaki dinga amsa minb da ka. cikin rawar murya zeenat tace Allah
Ummi tmbyta kawai yayi.
tmby ce kawai zai saki kiyi hujiga hujiga haka kmr an kwatoki a bakin kura.
Ki sanar dani idan wani abu yayi miki.
Tukun na ma , how many hours dana dawo parlour na iske baki nan. Km nasan tun
lokacin Kina dakinsa dubi yadda kike fidda gumi dan Allah
a sanyaye zeenat din Tace to ni Ummi me kike so nace byn .
sai km hawaye ya balle mata shar shar.
yasoma bin fuskarta. Tayi saurin tare da
sanya byn hannuta tana goge hawayen wasu na sake silalo mata.
Ummi ta zuba mata idanu kawai tana kallonta tare da nazarinta tabbas tasan duk yadda
akayi akwai abinda deeni ,yayi mata.
Amman dan sakarci da kafiya irin tata gashi tski fadar gaskiya.
sai da ummi ta numfasa sannan ,tace meyye km na kuka ke da kika ce ba abinda aka miki
,bakiyi kuka a can inda aka ritsa ki ba sai a nan ,dan kin rai nani ko..
kasa cewa komai zeenat din tayi illa sanya kai datayi cikin bathroom, tashige abunta
tana kuka kasa kasa , abubuwan sun taru sun cakude mata.
goma da ashirin ga rashin samun kulawar DEENi gareta.
ga damuwar Ummi akan ta nacewa DEENI.
cikin dare ma sam kasa bacci tayi.
Sai faman juyi kawai take akan gado tare da tunanin iri iri ta jima kwance batare da bacci
yayi nasarar dauketa ba
Wani tunanin ne yazo gara ta tashi takai kukanta gurin mai duka.
dan haka ta mike cikin sanyi jiki ” taje tayo alwala.
sallah nafila ta dingayi ba kaukautawa tare da neman zabbi Allah akan aureta da DEENi.
dan ita kanta tasan zuwa yanzu tabbas tayi kuskuren saurin amincewa da aurensa datayi .
Domin shine musababbabin abinda yasa wulakancinsa ya sake nunkuwa gareta. wanda
ita kanta tasan hukuncita abinda yafi dacewa daita kennan.
na saurin amincewa datayi da auren DEENi cikin gaggawa batare da ta neman zabin Allah
ba.
hankalinta kan tashi.
a duk sanda ta tuna da maganganu ummi. A Ranta tace anya kuwa bazan hakura da auren
nan na DEENi na hutawa rayuwata ba .
wai ace mijin da zaka aura ne” ya zame maka tamkar wani ma’alaikan daukar rai ko wani
dodo.
Kuka take sosai tana , addu’a neman Zabin Allah a game da auranta dashi.
darajar nafilar data kwana tana yi ne .
yasa washegari ta tashi sakayau daita cikin nishadi da farinciki”
ba kmr ko wace safiya ba.
duk da bata da wani kuzari da walwala. Amman hakan bai hana jin dadi ba.
kitchen ta nufa kai tsaye dan hada masa breakfast kasancewa weekend ce.
“byn wasu yan mintina ta kamla da komai na break tashirya dining. Cikin haka ummi ta
iso parlour ta zauna kan dinning table tana yi mata sannu, murmushi tayi tare da koma
kusa ummi ta zauna” ta sheida mata ta gama komai.
tana jinsa yashigo yana gaida ummi fuskasa a daure kmr kullum.
Sanye yake cikin dark blue t shirt da wando jeans .ummi ta amsa masa cike da fara’a ka
tashi Ify ya dan saki fuska kadan Yace lfy lau na tashi first lov kujera ya zauna.a tsorace
itama zeenat din ta gaishe shi ,ya amsa mata a ciki batare daya kalli inda take ba.
ummi Tace ya..ya.ayi serve din ka ne ? Ya hade rai yaki yin magana.
da kai fa nake a zubo maka abinci ne ta sake maimaita wa ?
Ya dan dubi ummi a shagwabe Yace bana ci.
ummi ta Gane tmbyrta da tayi masa ce ta hassala shi .
dan haka sake bi takansa ba da kanta ta zuba mishi komai da’ aka girka ta turo plate din
gabansa ,tare da dungure masa kai ” gashi nan miskilili sarkin zuciya Yace to ni ta yaya
za’a tmbye ni ko zanci abinci ” byn ansa zanci din”
ummi tayi murmushinsu irin na manya Tace uhmmmm DEENi kennan halinka sai kai “Allah
ya canza maka wannan budadden halin naka ” Ameen yace tare da kai spoon bakinsa.
parlour ya dauki shr baka jin motsin komai baya ga karar spoon din zeenat.
juyawa spoon din kawai take takasa kai ko loma daya bakinta sakamakon cika wajen da
DEENi yayi” duk da tasan hankalinsa da idanunshi ba’akanta suke ba.
tayi shr ta fada cikin duniyar tunanin abinda ya shafeta km yafi damunta
Wanda a halin yanzun Bai wuce aurenta da DEENi ba.
domin kuwa tana matukar jin tsoron zama dashi ba dan komai ba sai dan tsoron azabar
da zai dinga gana mata a gidansa.
hankalinta kan tashi a duk sanda ta tuna da hakan.
Ahankali Ummi ta ajiye spoon din hannuta tare da zuba mata ido kawai tana binta da
kallo tarasa meke damun Brain dinta a cikin kwanakin nan.
kusan minti goma ta dauka tana kallonta batare da ita zeenat din tasani ba .
Zeenat..ummi takira sunanta a frigice ta juyo tana kallon ummi ,ci abinci abinda ummi
ta iya cewa kennan.
DEENi dake zaune haushi kmrya kashe shi tsaki ya dan ja ,ummi ta juyo bangaren sa Tace
Ify kai km ?
Fuskarsa a dakune Yace babu , Sai da taga Ummi ta sake dubeta sannan tasoma cin
abincin, shima bawani sosai.
Byn sati biyu
Shirye shiryen bikinsu zeenat aka soma sosai ba kama hannu yaro.
anshirya komai na al’adar hausa kmr sabbabin dinkuna da gyaran jiki komai km tare
akeyi musu ita da shemah km iri daya.
musamman ummi ta dauko kwararriyar mai gyaran jikin daga india domin ta gyara mata
tilor diyarta da kyau.
duk wani gata da uwa zata yiwa diyarta “ummi tayiwa zeenat shi .
shima mahaifin zeenat din yayi iya bakin kokarin Sosai .
a nyi kamu amare idan aka feshe su da turare masu dadin kamshi na mutune India wanda
duk wacce ummi ta dauko ta gyara zeenat din ce tazo dashi.
Anyi musu murzar lalle da kitso.
amman ansha fama da zeenat gurinyin kitso dan cewa tayi ita sam na attachment ,zatayi.
sai da ummi ta bude mata wuta sosai tare da cewa ,zata sanarwa DEENi tukun ta natsu.
Sau ran kwana biyu daurin aure mutane India suka iso, kusan mutum ashirin maza da
mata sosai aka shiga hidimar da ,baki.ummi taji dadi Sosai dan kusan duk shakikanta ne
suka zo wanda km shine zuwansu na farko Nigeria idan.
gabadaya gidan nasu cike yake da baki dan haka ba kasafai zeenat din take zama a part
dinsu ba ,tana can gidansu shemah.
Zeenat Tace dan Maryam muje kirani part dinmu ina son naga ummi yau duk banganta ba.
, Maryam Tace gaskiya na gaji da yawa wlh kije kawai. zeenat ta ja saki Tace dan Allah muje
kiraki ni yanzu zamudawo.
shemah dake kwance ta mike zaune tace muje na rakaki kinsa halin Maryam da maseefar
son jikin tsiya.
, Mikewa sukayi har sun fito sai ga Maryam Tace wlh baza kubarni ni kadai ba, zeenat tace
ke km kika sani ” idan zaki muje.
Tare, suka nufo part dinsu zeenat.
tafe suke suna hira irin tasu ta amare daga nisa zeenat ta hango motar DEENI parke a kofar
part dinsu “daga gefe.
“can baya km motar fk ce sai wata motar daban wanda batasan ko ta waye ba.
Jingine yake jikin motar shi yana amsa waya sanye cikin English wear’s black jeans da
rigar ashi colour “mai gajeren hannu wanda ta fidda ainihin kyaunsa da gargasan gashin
jikinsa dake kwance kan Gabar hannushi.
idanunta fes akanshi tana binshi da wani irin kallo saboda yadda taga yakara yi mata kyau.
fuskasa har wani shekin annuri take fitarwa kmr ance ya dago idanunshi suka hada idanu.
da sauri ta dauke idanunta wani abu ta dinga ji yana tsirga mata ajikita. sai taga ya fita
daban cikinsu fk duk da bawani kallonsa tayi sosai ba.
ta sake dago idanunta da niyar sata kallonsa suka sake hada ido harara ya sakar mata
kallo daya ya sake yi mata ya kau da fuskarsa gefe yacigaba da wayarsa a kallo dayan da
Yayi mata yane yadda jikinta ya tsanyi.
kai tsaye zeenat taja hannun Maryam wacce tafi kusa daita ta juya da sauri ta karya cona
itama shemah ganin haka yasa tabiyo bayansu da sauri tana jin fk na kiranta. shemah
Tace yazaki biyo damu tana km.
zeenat Tace bbu komai mu bi nan di yafi sauki.
ta bayan part dinmsu suka shiga, da ummi tasoma cin karo ta rungume tana sakin ajiyar
,ummi tace meyye haka ?muryata kmr mai shirin yin kuka take Haba ummi yau fa duk
banganki ba ,baki ga har wata rama nayi ba ” tayi murmushi tace lallai kam kin rame dan
ga natsuwa nan suna bikin dariya mutane dake tare da ummi suka shiga yi.
Ummi tayi gaba zeenat nabiye daita tana zuba mata shagwaba.
shape shape tayi abinda zatayi suka bar gidan.
Ranar daurin auren da safe ta nufo gidansu dan dauka kayanta dazata saka.
wanda ta manta bata hadu dashi ba cikin kaya.
tafe take tana sauri. yayinda su ya faruk da abonkan DEENi ke tsaye duk cikin shirinsu na
zuwa daurin aure.
amman banda DEENi wanda dagani shi suke Jira.
Wani irin kunya ce taji takamata dan haka ta dan janyo gefen mayafinta ta rufe fuskarta
tana jin yaya faruk nacewa amaryamu ki bude idanunta kada ki fadi mana.
amman ina ko waiwayo batayi ba tacigaba da tafiyarta ta kofar baya tabi yauma.
tashigo dogon parlour’nsu ta baya kennan tasoma jiyo kamshin turarensa kafin tayi
kokarin bude fuskarta taji sunyi karo da mutun.
da sauri takarasa bude fuskarta “yaya DEENi ne wanda zai fito har wayar dake hannushi ta
fadi.
gabanta ne yayi wani irin faduwa dan har wani juya juya ta dinga ji da sauri ta tsugunna
dan miko masa shima ya tsugunna da zai dauka a tare hannunsu yakai kan wayar ,wani
irin shock ne yajata ” wanda baita kadai ba har shi DEENi yaji abinda taji.
Wani iri shima yaji ajikinsa tamkar an jona masa lantarkin.
Shine yasoma kokarin janye hannushi daga kan nata ,ahankali ta Miko masa wayar batare
da ta mike ba hade da cewa kayi hakuri dan Allah.
komai Bai iya cewa ba baya ga amsar wayar da Yayi ya barta nan tsugunne.
Bayansa tabi da kallo yayi matukar yi mata kyau har batasan yadda zata misalta ba sanye
yake cikin shadda fara kal sai kamshin yake zubawa.
gabadaya kamshin turarernsa ya gyaraye dogon parlour’n.
Ahankali zuciyarta tasoma bugawa tamkar zata basa kirjinta .
girgiza kai kawai tayi dan batasan wani irin aure take shirin yi ba haka ta juya cikin sanyi
jiki tabar gurin tana shiga ciki.m mutane akama kiranta da amarya amarya kinsha kamshi
ita dai bata iya cewa komai ba dan gabadaya jikinta a sanyaye yake.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]