[Advertisements⬇️]

WANI AURE CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WANI AURE 

CHAPTER 1
Lekki Unguwace mai dauke da karancin mutane da suke rayuwa acikinta ,a silent place, saboda bata cika hayaniya mutane ba , dauke da tarin sanyin ni’ima mai dadi sakamakon kusancinsu da ruwan teku” unguwace da tattara kan manya ma’aikata da kusoshin gwamnati, hade da manyan masu kudi ,ga tarin yan yahoo boy’z domin mafi yawancisu sunfi sha’awar zama acikinta. rayuwar mutane unguwar abin sha’awa bbu ruwan wani da wani domin suna rayuwasu ne tamkar a kasarwaje . 

PLASNUW ROWS FAMILY ESTATE 

Estate ne mai dauke da tarin dangi acikinta , hadin kai tattare da zaman lfy, Sam bbu hayaniya acikin wannan family kowa kagani cikin nishadi da farinciki zaka gansa ,ga tsantsar fahimtarjuna dake tsakanin wannan family. kwakkywan family ne masu matukar kaunar junansu . 
Let alh Muhammed bello khaliyal ,haifafen garin Lagos ne ,Amman asalinsa fulanin khaliyal ne dakejahar kebbi. sananne mai kudi ne yayi tashe tun alokacin da duniya ke kwance. sannan kuma take zaman lfy, marigayi Muhammed bello soldier ne daya taka rawar Gani a kasar nan . ya rike mukamai da dama a wancan lokacin. ya rasu yabartarin dukiya da da ya’ya da jikoki bila adadin
gabadaya family Muhammed bello bbu talaka aciki domin sun gaji dukiya mai tarin yawa daga mahaifinsu . Kafin rasuwarsa dake shine babba a dakinsu kuma Allah yabashi tarin dukiya da yan’uwan , dan ganin ya inganta rayuwar kannensa kafiln daga baya ya Gina wannan katanfarin estate din mai zaman kanta. 
ya tattara kan yan’uwasa suna zaune a ciki ,yana da mata hudu hjy shema’u wacce aka musu aure tun saurayi da budurwa tana da ya’ya goma Sha biyu, mata takwas maza hudu sai hjy hauwa mai dauke da ya’ya goma maza biyar mata biyar ,sai hajiya rabi mai ya’ya takwas maza biyar mata uku sai hajiya Fatima wacce suke kira da hjy shuwa itama tana da yaya takwas mata bakwai namiji daya . bbu abinda bbu acikin wannan estate din kama daga makarantar islamiyya wajen wasa buga kwallo wajajen exercise wajen swimming pool library Sannan ga wani katanfarin Hall dake gefe wanda aka shiryashi da kayan kyale kyale zagaye da kujerun zama . an ginashine saboda taron sada zumunci , wanda zasu dinga yi a duk karshen wata . ‘ 
haka suka taso har zuwa girmansu cike da sonjunansu . anan cikin dangi mazan suka zabi matan suma matan suka zaba akayi bikinsu anan cikin estate din suka zauna tare da iyalinsu har zuwa sanda tsufa yacima marigayi Muhammed bello yayi retire. yayinda ya’yansa da ya’yan en uwa suka cigaba da kula da estate din. 
a lokacin aliyu da habib ne kadai suka rage da basuyi aure ba saboda karatu . 
Byn rasuwar marigayi bello ne aka raba gado aliyu ya dukufa gurinjuya dukiyarsa ,ba abinda yasaka a gaba sai neman kudi wanda acikin kankani lokaci ya gawurta yayi fice yayi suna a duniya, yayiwa sauran yan’uwansa zarra aliyu ya mallaki tarin dukiya da shi kansa bai san iyakarta ba. hade da tarin compenis a Lagos da kudancin Nigeria yana da gidajen saida man petir Bila adadi shine mallakin aliyu airlines yana da hannu jari da dama a compenis na kasashen duniya yana da gidaje a abuja da sauran garuruwa. 
tsananin neman kudinsa ne yasa bai ajiye iyali da wuri ba ,burinsa bai wuce ya auri mace mai matukar kyau da tarin illimi ba. 
Garin neman kudinsa ne ya hadu da fadila a india tun daga lokacin da aliyu ya daura idanunshi akanta “ya dauki son duniya ya daura mata kasancewarta kyakkywa gaske ga tarin illimi . fadila itace Diya ta biyu a gurin iyayenta su uku ne , ahmed ne babba sai ita sai farida , kin amincewa iyayenta sukayi da auren shi a cewarsu bako ne sannan kuma bakin fata. sai da aka kai ruwa rana dasu sannan suka amince da auren . 
koda yazo da ita Nigeria ma bata wani sha wuyan zama cikin family dinsa ba . kasancewarta mace mai tsananin son jama‘a da son yara cikin lokaci kadan tashaku da sulaiman da mahamud ya’ya ne ga yayyen aliyu sun shaku matuka da yaran ta daukesu tamkar ya’yan data haifa acikinta. 
suma kuma suna maseefar kaunarta dan haka suke kiranta da ummi ,duk abinda suke so itace take musu bata ragesu da komai ba saboda bata da rowa hakan ne yasa ta sakejanyo mata soyayya ta daban a gurin iyayensu. 
shekarata biyar da aure mutuwar mahaiflyarta risketa ,zuwan datayi indiya ne dazata dawo tazo da kanwarta fadila ta hada dasu Mahmoud tacigaba da rikonsu . sai da fadila ta dauki sama da shekara takwas da aure sannan tasamu cikin murna a wajen wannan family bai faduwa . cikinta na da wata tara cifta haifi NASURUDEEN daga ita har aliyu suna matukar son DEENI tamkar numfashinsu DEENI yataso cikin gata da kulawar iyayensa, da dangi gabadaya suna nuna masa tsansar gata da soyayya fiyye da tunanin mai karatu. shiyasa yataso a shagwabe a sangartacce saboda kaf estate din kowa yasan da zaman DEENI babbar matsalar da suka fara fuskanta da deeni ,shine rashin magana da bai yi ,da farko fadila ta dauka ko kurma ne sai daga baya tagane tsabar miskilanci ne kawai yayi masa yawa. duk tarin ya’yan dake cikin wannan estate din DEENI yaflta dabam acikinsu, bashida aboki ,. gabadaya baya yarda da kowa koda yaushe yana tare da umminsa ko farida ko su Mahmoud tun tasowarsa yake da burin son zama soldier yayinda ummi take bashi goyon baya wajen kiransa soja . Domin wani lokacin zai je yatasa hotonta marigayi kakansa dake manne a falonsu gaba yayi ta kallo yana shafa fuskar tsohon yana murmushin ,Sam shi bashi da fara’a ballanantana sakin fuska koda yaushe fuska nan tashi a hade take tamkar hadari , .DEENI Nada shekara takwas byn yakare primary school aka sai mishi form din shiga makarantar sojoji ba‘awani samu wata matsala ba yasamu sakamakon matsayin mahaifinsa da kakansa. sabanin wayanda basu da gata. domin a wanan lokacin idan dai kai bawani bane ko dan wani ba k0 bakada hanya a military school ,sunanka sorry. Domin kuwa kana ji kana Gani military school zai gareka shiga . 
byn wani lokacin farida ta samu miji anan cikin estate din wanda shima yakasance “Da”ne ga marigayi Muhammad bello wato habibu ubansu daya da aliyu mahaifln ga DEENI . duk da fadila ta nuna rashin amincewarta matuka , da nuna wa er’uwartata illar aurenta da Habib Amman sai taga yarinyar ta nuna tana so abunta ,dan haka ta kyaleta kuma da kunya dai ta futo fili tace batason jinin aliyu ,wanda itama kanta tasan hakan ba mai yiwuwa bane . itama ba wai shi din ne bataso ba ,halinsa ta tsana , Amman shi babban ma’aikace gwanati ne, director of land and housing&same na Lagos state gabadaya. yana da mata biyu da yaya bakwai farida ce ta uku . Ko alokaci daya auri farida takasance mace ce mai tsananin hakuri. duk da mijin nata bai kasance mutun mai adalci ga iyalansa ba. Amman bata taba kawo kararshi ga ummi ba domin tasan halin ummi Sam bata son raini. Shekarar da aka yiwa sulaiman da mahamud aure shekarace Allah yayiwa mijin ummi rasuwa wato alh aliyu Muhammad bello sunji matuwarfarar daya , mutuwar tayi matukar gigita ummi dan byn ya dawo daga sallah asuba ne yayi irin kishingide nan yana lazimi koda ummi taji shiru shiru bai sake fitowa ba Sannan bai nemeta ba kmr yadda ya saba, wanda aldarsa ce da zarar gari yayi sha …yake fitowa ko yakirata a waya Amman taji shr. tashiga dakin nasa ta tarar dashi kishingide da carbi a hannunsa. da fari ta dauka ko bacci yakeyi sai tayi nufin ta tasheshi yakoma kan gado. 
Amma sai taga alamun rashin motsi atare dashi takai hannuta wajen hancinsa da karjinsa a lokacin daya taji baya numfashi. 
take ta zube anan ta sume. har a kashare zaman makoki ummi batasan a wani hali take ba ,dan bata cikin haiyacinta’ koda ta farfado ma sai da akayi ta hadawa da addu’a Sannan aka samu kanta ta dawo daidai , dan mutuwar ta girgiza har ta kusan zarar daita . ‘ 
Byn wani lokacin su sulaiman suka cigaba da tallafawa ummi da DEENI a lokacin farida na dauke da tsohon ciki duk da itama ta danjima bata haihuwa ba, kuma har lokacin ummi bata san er’uwarta tana cikin matsala ba ,sai byn data haihu’l lokacin ne ummi taga komai bbu alhalin ga tarin dukiya kmr zai kashe habibu ,gashi yasake kara wani sabon auren matansa sun cike hudu cif. ummi tayi kuka kmr may gashi tana cikin danginsu da suke tamkar tsintsiya madauri daya. ba daman tace zata dauki wani mataki akan haka . dan tasan yadda kansu yake a hade. 
dan haka taci kukanta takoshi ita da er uwarta ahankali take furta kalmar shiyasa tun farko naki amincewa da auren nan naki da habibu ,ba dan komai ba sai dan irin haka Amman kika nace ,ga irin abinda nake gudar miki kennan Amman kika kiji , sai kuma ta tsagaita da kukanta ahankali tace ba yadda zamuyi da ikon Allah ,sannan ga rabo a tsakani. Amman duk da haka sai da ummi tayi masa tatas saboda daman ita bawani sakar masa fuska take ba kuma yana shakkarta. kullum ummi acan take wuni har ranar suna yarinya tace sunan mahaifiyarsu ummi wato muzeenat , shima habibu yayi hakan ne saboda ya wanke kansa a wajen ummi,kuma yayi nasara domin hakan da yayi yasa ummi taji dadi Sosai aranta har ta dan ragejin zaflnsa. sannan bakaramin kudi ummi takashewa bby ba. haka ma ranar suna ummi Tayi rawar Gani sosai . byn anyi suna ne ummi tasamu habibu akan dan Allah ya dinga kula da farida dan ita kadai gareta bata da kowa duk fadin Nigeria sai ita, idan ma bazai damu ba, zata bashi 
Rabin dukiyarta yakara akan nashi da duk wani abinda yake so, ita dai burinta kawai ya kular mata da er,uwa ,yayi murmushi kawai hade da ce mata yaji . Byn wani lokacin farida ta kuma samun wani ciki wanda tun yana karami take fama da laulayi tun lokacin ummi tadawo da zeenat wajenta , a kwana a tashi bbu wuya a gurin Allah harcikin farida ya isa haihuwa gurin haihuwar ne tajijiki sosai. koda ta haifi yaron ma bbu rai sannan itama tace ga garinku . mutuwar ta shigi habibu matuka yayi kuka tamkar ransa zai fita ,dan shi kansa yasan yayi babbar rashin da ba zai taba maida irinsa ba. 
yayi rashin mata mai tsananin kirki da hakuri da sanin darajar miji . Allah sarki ummi kusan har tafi habibu jin mutuwar tilon er’uwarta ta ,. a wannan Lokacin ne rikon zeenat ya dawo dindindin gurin ummi ta dauki soyayyar duniya ta daurawa zeenat tana mugun ji da Yarinyar tamkar ranta kwata kwata bata son abinda zai rabata da zeenat Sannan kuma tana debe mata kewar er’uwarta . lokacin shi DEENI na 551 a NMS, Nigeria military school dake zariya. yayinda DEENI Sam ba halinsu daya da ummi ba koda yaushe kagansa fuskar nan tasa a daure a cunkushi bbu wani fara’a ga shegen miskilanci tsiya sai dai mugun kyakkyawa ne na karshe . ajin farko, wato first class ,gashi da maseefar iya sa kaya kallo daya zaka masa ya gigitaka kaji yashiga ranka farat daya saboda tsabar kyawunsa sai shegen shiga ran mutane domin kusan yan’mata cikin estate din suna maseefarson sa yayinda yake girma kyawunsa na sake bayyana hade da miskilancinsa 
Tunda zeenat ta dawo gidan magana bata taba hadasu ba ko gaisheshi Tayi baya amsawa in dai bayaga idanun ummi ba yana da matsanancin tsafta wanda kusan a wajen ummi yagada . Cikin haka ya kammala karatunsa na secondary school ya wuce NDA burinsa kennan nason zama cikakken soja itama ummi kuwa nasake karfafamasa gwiwa da bashi goyon baya yana karantar science ne ,wato likitan soja. bansan yadda zan kwatanta muka halinsa ba Amman yakasance mutun ne shi mai bambanci ra,ayi. byn yakare karatunsa ya fito da mukami second lieutenant star biyu kennan . Zaune zeenat take a falo tana kallon wani seris film a zeeword my let home Tayi zurfi cikin kallon film din gabadaya attention dinta naga kallon ita kadai ce ummi tashiga cikin estate din yin barka taji karar Bell wanda shine kusan karo na hudu da taji ana dannawa. Cikin jin haushi ta mike dan bata son abinda zai dagata daga kallon datakeyi , tana bude door din bata tsaya ganin kowaye ba tajuya abinta takoma mazauninta sallama taji hade da shigowa ta dago kanta kennan da niyar amsa sallama sai taga mutun tsaye kikam sanye da sabon kayansu na sojoji gabadaya zeenat ta gigice hade da rikicewa tsabar tsoro dan ita Allah yayita da maseefarjin tsoron soja take cikinta ya dauki kugi Amman still idanunta na kansa ta tsaresa da kallo . 
in ina tasoma yi wa..wa.. waalai….ya dakatarvdaita da hannushi, yana zabga mata wata uwar harara muryasa a kwausashe yace yau ne kika fara ganina da har zaki wani tsareni da idanu Kona canza miki ne ?da sauri tasoma girgiza masa kai. Kai tsaye dakin ummi ya nufa tunda bai ganta a parlour ba yasan tana dakinta tana kallonsa ta kasa dauke idanunta daga garesa har sanda ya dawo fuskar nan tasa a hade yace ke ….. dan iskanci kina kallon mutune bazaki iya cewa ummi bata nan ba kin wani tsare mutun da idanuwa tamkar na maciji ,dayake bawani manyan idanu gareta , da sauri bakinta na rawa tace dan Allah kayi hakuri mantawa nayi ko kallonta bai sake yi ba yaja tsarki yayi hanyar dakinsa ta tabe 
baki hade dacewa jarababbe kawai ai yadawo kennan, itama taja tsaki ta juya tacigaba da kallonta .. [Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]