TAGWAYE CHAPTER 36

Advertisements

_____

TAGWAYE

CHAPTER 36
Ammi you can’t live me, you can’t betray me kada kici amanata Ammi kada ki barni banida kowa a duniya bayan ke. Da wannan maganar Zayyad yafarka a flrgice, Yana ambaton Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ ‘Daga idanuwarsa yai yaduba d’akin sama da ‘kasa amma yarasa gane inda yake.
Ganin irin tsarin d’akin yasa Zayyad yafara mamaki “kodei Ammi ce ta buge shi a mota, domin yanayin kyaun wajen yayi kamada tsarin ginin gidan ta. Ahankali yami’ke, kansa na bala’in juyawa ayayinda yake dafe dafe har saida ya‘kai bakin ta’ga yaja labule yana leke leke ko Allah zaisa yaga’ne inda yake.
“Alhamdulillah Zayyad, ka tashi? A tsorace yawaiga “waye kai? Kuma a Ina nake? Tambayar dayaiwa matashin saurayinda ke tsaye agabansa kenan.
Sunana Doctor Faisal Muhammad, ni ne mai kulada kai, Sati guda kenan muke tare anan munajiran ranarda zaka dawo cikin hayacinka Kuma mun godewa Allah …….
Dakata Dr da mamaki Zayyad yake ‘kara tambayansa” Sati guda? Malam kana nufin satina guda a kwance anan gidan? Waye ya kawoni nan?
Hatsarin mota kayi, Mahaifinka tareda d‘an uwanka Zaid sune suka kawoka, Kuma nan gidankune Doctor Manav ya mallaka muku ita har abada. Sake baki yai Yana sauraronsa,jikinsa na rawa sosai “Kana nufin Baba da Zaid sun ganni Ido da ldo Kuma su’ne suka taima’kamin? Kenan sun yafemun dukkan laifuffukanda na aikata musu? dan Allah ka ‘kirayominsu inason ganinsu, I really miss my family alot. Rasa amsarda zai bashi yai ganin tunda yazo babu wanda ya lekosa cikin y’an uwansa duka, akasarima Zaid da Mahaifinsa kam ko bangarenda yake basu tasa lekowa ba, dashi da Miemah kacal suke kula dashi tun zuwarsa har izuwa yau. Ma‘inah ma wataran tana sace kafa zuwa wajensa tareda Y‘ar uwarta Miemah duk dacewa Zaid ya hanata zuwa wajen.
Lambar Miemah yasa awayarsa yafara ‘kiran layinta Kuma yayi sa’a sosai, abugu biyu ta amsa.
Inspector gaskiya wannan ba adalci bane, How can you imagine, yanzu mako guda kenan muna zuwa nan wajenku amma kun ‘kasa zuwa gidan Hajiya Turai ku kama‘ta bayan Kuma mun tabbarar muku cewa Maisha tana chan gidan. Doguwar nunfashi inspector Bashir ya sauke “ZMZ we are really sorry kad’an bamu lokaci kad’an idan mun kammala bincike zamuje chan mu’kamata Bi’izinillahi.
Teburin dake gabansa ya da’ka har saida kowa ya razana, ransa abace ya dafa collar rigan inspector Bashir” Are you mad? bakada hankali ne wani irin bincike zakuyi bayan munada shedu ahannu, we are having enough evidence to prove that Maisha is guilty, she is a muderer ita ta kashemin aminina Asad, and she made the twins (Ma’inah and Miemah) entire life miserable, She is a criminal Amma kawai sabida tana gidan masu kudi shine
kuke tsoron zuwa ku ka’mata.
Dakyar aka janyoshi gefe “Zaid ya’kamata ka fahimci cewa gidan Hajiya Turai tanada tsaro fiyeda yedda kake tsamanni Kuma y‘an sandan dake gidan sunfimu ‘karfi nesa ba kusaba idan bakabamu lokaci munsamo kwararrun shedu ba, wallahi bazamu samun damar zuwa cikin gidan Hajiya Turai muka’ma mai laifi ba so kamar yedda Inspector Bashir yafad’a kabamu lokaci….
Bai tsaya jin karashin maganar commissioner of poiice ba, bankado kofa yai yanacewa ” To hell with Nigerian police. Da wannan bakin ciki yafito ransa abace yanufi motarsa. Anan cikin Mota yazauna Yana zubda kwalla abun tausayi, yarasa gane anfanin rayuwarsa ayanzu, Asad shine komai arayuwarsa kuma yarasa shi alokacinda yake matukar buka‘arsa kusa dashi. Amma yad’au alwashi da’kansa zaiyi anfani da dabararsa domin ya’kama Maisha yakawota gidan dayafi dacewa da ita wato Gidan yari. Ako da yaushe mamakin mahaifiyarsa yake tun ranarda ta korosu daga gidanta Zaid bashida wani abunyi bayan kuka da damuwa, Baba ne yake shawo kansa akoda yaushe duk dacewa baison zuwa wajen Mahaifin nasa, ako yaushe idan yayi ldo hud’u da Mahaifinsa babu abinda yake tunawa sai irin musgunawar da Mahaifiyana tai musu gaba d’aya, shiyasa yake matukar tausayawa Mahaifin nasu flyeda yedda yake ‘tausayawa ‘kansa.
Ya sauke ajiyarzuciya, Sannan ya share hawayensa fes! Batareda bata lokaci ba, yaja motarsa yafara tuki. Ya dad’e Yana tuki cikin tunani da bacin rai, bai tsaya ko inaba sai Turai Mafiya’s Mansion (tsohon gidansu kenan) “Maisha dubunki ya‘kusan cika da yardan ubangiji dakaina zan kaiki hannun hukuma, you must pay for all the crimes you have
committed. Sanye takeda wata Y’ar karamar armless top wanda bata kai saman cinbinta ba dawata shegiyar skirt shima baikai guiwowinta ba. Kayan sunyi dedei da kalar jambakin dake zaune abakinta tamkar da’ita aka halicci bakin nata. Ahaka taflto ko dankwali babu akanta bare hijabi, suran jikinta duk a bayyane “A’udhubillah”.
“No. no, no,l mean iPhone XX Max, meye zanyi da wannan shirmen. Tana nuna iPhone XPlus dake hannun mai super market d’in. “Hajiya ai wannan din ma ba laifi.
Tsaki taja afiskarsa, Mallam any’a kuwa kasan dawa kake jayayya? Allah ya huci zuciyarki Hajiya. Murmusawa Maisha tai inda takece wa ‘dan sandan dake tsaye abayanta yana kula da ita, “Fad‘amusu ko ni wacece? Cikin ‘katon muryarsa yafara magana “Sunanta Maisha Saminu Maidugu Y‘ar gidan her Excellency Hajiya Turai Mafiya.
Nan ta’ke mutumin ya durkusa “Hajiya agafartamana, dasauri ya zaro iPhoneXX Max sabo pil a Leda yamiko musu kamaryedda ta umarcesu. Fashewa da dariya Maisha Tai “shege yaji kud’i, Anyway Ga kud’in wayarka nan. Yana mi’kamata wayan ta cire daga cikin kwali ta wullota ‘kasa sannan ta tattaka da takalmarta har saida wayan ya parpashe sosai, kowa ya tsaya Yana binta da kallo ita koh ko ajikinta “wayan batamin ba i rather order customize phone from abroad. Da wannan magana tafara tafiya cikin ta’kun ka’saita har saida suka kai wajen motoci aka bud’e mata tashige sannan aka rufe kofa. Tareda excord abayanta take zuwa ko ina.
Saminu yana tuki cikin kwanciyar hankali a birnin Dubai tare yake dawata Y’ar baturiya tana zaune agefensa tana debemasa kewa da flra. Saminu koh farin ciki da walwala ne yake yawo a zuciyarsa. Finally ayau burina ya cika ni Sambo arziki dakuma more rayuwar duniya,Y’ata Koh tafl Ma’inah arziki,tabbas Allah ba azzalumin bawansa bane. “Sweetheart Ina maka magana kayi shiru. cikin harhen turanci tai magana, a flrgice Saminu yadawo cikin hayacinsa “Inajinki sweetie. Ina Baby Isha? yau banganta ba. Murmusawa yai’ Takoma Nigeria nima yau zankoma da yardan Allah sabida d’azu mukayi waya da Hajiya Turai Mafiya takecewa indawo gida tafara kewana achan ‘kasa Nigeria. Wow baby you are such a darling you know, everyone loves you, I mean everyone wants to be around you. Gyad’a kai Saminu yai cikin murmushi “Thanks Helien thank you so much.
Yaya Manav dan Allah ka taima’kamin na’san babu wanda zai iya taima’kamana awannan lokacin sai kai. Har ‘kasa ta zauna agabansa tana hawaye.
“Ma’inah meye Kuma na kuka? Janyota yayi da hannunsa tamike sannan yace’ I’m sorry
Ma’inah bazan iyaba kiyi hakuri. Yaya Manav na’san cewa babu wanda Maisha zata amince dashi ayanzu bayan kai sabida Kai attajiri ne kamar yedda take bu’kata, kanada sura mai kyau gakuma kyaun fuska. Dan Allah ka amince da bu’katata sabida ta wannan hanyar ne kad’ei zamu iya kamota cikin dabara har izuwa hannun hukuma. 
Zaro tissue yai yana share mata hawaye, Alright fine, ba’komai Maisha zata shiga hannun hukuma Bi‘izinillahi. Dasauri Mainah Tamike thank you so much Doctor, Na’gode Allah ya biya. 
Because you are my little princess Miemah, Mommy ta rungumeta sosai suka mannu da juna, tana murmushi “I love y so much sweetheart. Thank you Mom I love you too. Bata rufe ba’kinta ba adeden wannan lokacin wayarta tafara ‘kala “Doctor Falsal” Dasauri tad’aga “Hello Doctor. Assalamu Aleikum Miemah, Zayyad ya farka yanzu yatashi ya’kamata kizo yanzu yanzun nan ki tsamemu. Wullo wayar tai cikin jaka, Farin ciki duk ya mamayeta ayayinda tad‘au jakar aguje tafice. Momy kanta shiru Tai tanabin d’iyarta ta da kallo sabida tafi kowa sanin halaiyarta musamman idan tana cikin farin ciki. 
Babu sallama Miemah tafad’o musu cikin d’aki tamkar daga sama. A|okacin Zayyad yana chan kusada window yana leke leke baisan hawaba bare sau‘ka kawai sai yaji an rungumeshi tabayansa “Thank God you are alive. Miemah ta sauke doguwar nunfashi tanacewa’ Zayyad ka’san yedda hankalina yatashi alokacinda kake Coma kuwa, Wallahi I nearly die. Karasa maganar tai tana dariya “Funny right? cikin tsananin mamaki da rud’ani ya waiwayo ahankali, ya kure mata ido sosai Yana binta da kallo. Babu shiri Miemah ta sakoshi, gashinjikinta ne ke tashi alokacin da sukayi ldo hudu dashi “l’ iammm I am s so so sorry Zzz Zayyad aaa actually I am ….. 
Rufemata Baki yai da hannunsa “It’s okay, Bai ‘kara fad’an komai ba, tajuya zata tafl yajanyota babu fargaba shima ya rungumeta yanacewa’ “Thank you”. Miemah batasan dalinda yasa taji wannan irin farin cikinba sai dai dasauri taja da baya “No No it’s Okay ba komai. 
Kai tsaye aka bud’e Masa gate, ya gangaro cikin gida fuuuu! Adeden Gangaren Mahaifiyarsa ya pa’ka motan inda ya fito kai tseye ya nufl ciki. Yanasa kafa cikin falon Ammi text message yashiga wayarsa, ganin layin Mahaifinsa ne yasa yai saurin bud‘e message d’in. 
Video ne, inda ake nuna Ma’inah tareda Doctor Manav cikin ofishinsa; “””Yaya Manav dan Allah ka taimaka ’kamin na ‘san babu wanda zai iya taimaka mana awannan lokacin sai kai. . Doctor yace ’ I’m sorry Ma ‘inah bazan iyaba kiyi hakuri 
“Kai attajiri ne kamar yedda take bukata, kanada sura mai kyau gakuma kyaun fiska. Dan Allah ka amince da bu’katata “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ Ba shiri Zaid yazube anan wajen “me kenan wannan vidiyon take nufi? Zunzurutun gumi ne yafara saukomasa ayayinda yami’ke dakyaryai maintaining balance d’insa. ” Nooo, no, Ma’inah will never do this. Zaid kadena wannan tunanin Ma’inah bazata taba cin amanarka ba. 
Murmushi ne ya bayyana a fuskar Ammi alokacinda tasauko falon ‘kasa idanuwarta suka fa’da kan ‘Danta Zaid, atunaninta ‘Dannata yayi da’nasanin bin Mahaifinsa ne yadawo gareta, Dasauri ta‘karaso inda yake “My Son, i know you will definitely come back to me, sabida ni’ce gatanka ‘Dana… Baimasan tanayi ba, aguje yabar wajen. Biyosa tai tana ambaton sunansa har saida motarsa ya bace mata “meke damunshi, fiskarsa yananu kamar akwai matsala? Anyway suje chan su ‘karata. Da wannan tunanin takoma falo takwanta tana kallo. 
Zayyad ka koma ka kwanta kana bukatan hutu. Fiskarta duk ya bayyana I’rin farin cikinda take ciki, Ta ‘kara dacewa” Take care of yourself zanje in sanar dasu Baba suzo su dubaka. Babu jayayya yakoma gadonsa ya’kwanta “Gaskiya Miemah ta kwanta masa a rai sosai, tanada tausayi, gakuma hankali da kula, she is one in a million. 
Tana fita sukaci karo da Ma’inah “Twinee daga ina haka sai murmushi kiketayi kina dariya da dukkan alamu Ya Zaid really surprised you with something special I’m I right? Miemah tafad’a cikin tsigar zolaya. Ma’rin ta Ma’inah tai” Kema ai fiskarki ta bayyana cewa kina cikin farin ciki matuka. ‘Dayan gira ta d’aga mata alamun zolaya tace’ Heyy charming Look alike what’s happening fad’amin. 
“Nothing serious, kinsan babu sirri tsakanin mu, Zayyad yasamu lafiya, yanzuma haka yana magana, yana iya mikewa dakansa har tafiya yanayi. Hawaye ne yafara saukomata yayinda tace’ Zayyad yana matukarji da Mahaifinsa dakuma ‘Dan uwansa Zaid amma suna kyamantansa abisa laifuffukanda ya aikata a baya Teddy dan Allah ki taimaka’masa, Please ki rokanmasa Ya_Zaid ya yagafarta masa dukkannin laifuffukanda ya aikata abaya wallahi yayi d’anasani, idan kinyi Masa wannan na’san kinyi Masa komai arayuwa Kuma bazai tasa mance irin alkhairinda kikayi masa ba Har abada. 

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

TAGWAYE CHAPTER 34

Advertisements _____ TAGWAYE CHAPTER34 “Wuukaa. lhun da Maisha ta daka kenan yayinda ta sake baki, …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *