SOYAYYAH CHAPTER 6

SOYAYYAH
CHAPTER 6
Koda Sufyan ya fito daga masallaci motan sa ya shiga ya nufa gida, a k’ofar gida ya tsaya ya
kira abu mai aikin su ya umarce ta taje d’akin Sadiya ta kawo masa passport nata.
Ahankali take duban falour’n ganin babu kowa ta shige d’akin Sadiya dake nan kusa da na
Hajiya Ruk’ayya.
Kasancewar ita ke gyara mata d’akin yasa tasan inda take ajiye wa, nan take ta d’auko ta
fito.
Hamdala tayi ganin har ta fita daga falour’n babu wanda ya ganta, da saurin ta tanufi gate
ta fita, Sufyan ta kira dan bata ga inda yayi parking ba.
Hasken motan data gano ne ya sanya ta nufan gurin, mik’a masa tayi yayi godiya ya tafi ita
kuma ta koma gida.
Tun a hanya zazzab’in sa ya dawo dakyar ya iya ya k’arasar da kansa, yana parking ya nufi
d’akin nasu nan ya tarar da ita kwance a k’asan tails ta rik’e kanta da but hands nata, jikin
ta banda rawa babu abinda take tana kuka helplessly.
Duk halin da yake ciki haka ya daure ya nufa inda take da sauri ya zauna sannan ya d’ago
kanta ya d’aura a laps nasa, ahankula ya cire hannayen nata ya sanya nasa yana mata
kamun kai.
Ahakan wani wahalallen bacci yayi taking over nata, yana son ya mayar da ita d’aki amma
ya rasa ta ina zai soma dan yadda jikin sa ke rawa ga wani irin sanyi dake ratsa sa ta ko ina.
Kwantar da kansa yayi kan kujeran dake bayan sa ahakan shima wani wahalallen bacci ya
d’auke sa.
Duk rashin imanin ka inka gansu saika tausaya musu dan gaba d’aya jikin su banda rawa

babu abinda yake yi hakan ne zai tabbatar maka ba k’aramin jin jiki suke ba.
4:30 am
Ita ta soma farkawa addu’a tayi sannan ta mik’e zaune, kallon Sufyan dake bacci a wahale
ta tsaya yi, tausayin sa ne ya mamaye mata zuciya, bazata iya yafewa wanda ya jefa
rayuwan su cikin k’uncin haka ba.
Duk dalilin ta d’an uwan ta mai k’aunar ta ya shiga wannan hali wasu siraran hawaye ne
suka shiga zubo mata yayin da zuciyan ta ke raya mata ta gudu ta barsa at least ita kad’an
ta zata sha wahalan rayuwa babu shi.
Again kuma wani sashi na zuciyan ta ke hana ta dan yadda yayi sacrificing happiness,
family, in dad’i da komai saboda ita.
Hannun ta takai ta share masa zufan dake goshin sa nan taji wani mugun zafi da jikin sa ya
d’auka she just can’t tell how much she love her twiny, mik’ewa tayi ta nufa toilet ta d’auro
alwala sannan tazo ta tada sa.
STORY CONTINUES BELOW
Alwala ya d’auro dakyar ya fito suka yi sallah bai samu daman yin azkar nasa ba ya nufi
d’ayan bedroom d’in ya kwanta, bayan sa tafi ta shiga toilet d’in dake d’akin ta d’auko bowl
ta zubo clean water aciki sai wata blue towel data hango sak’ale jikin hanger ta fito.
Stool ta janyo ta zauna sannan a nitse ta soma sanya towel d’in cikin ruwan tana matsewa
tana danna masa, sai da temperature nasa ta sauka sannan taje ta zubar da ruwan ta
dawo, nan ta iske sa harya koma bacci dan haka itama ta nufi nata d’akin.
Kasa bacci tayi tana tunanin Mummy’n su, ko a wane hali take na rashin su Allahu a’alam
kukan da batasan ranar tsayawan sa bane ya kwace mata and duk iya tunanin ta danta
gano wanda yayi mata hakan ta kasa, abinda ta Riga tayi believing shine Lubabatu da Aisha
bara su tab’a cutar da ita ba dole someone is behind all that happened.
Kuka taci kaman ba gobe saida zazzab’in ta da ciwon kai suka dawo sannan ta tsagaita ta
koma zubar da zafafan hawaye bata san lokacin da bacci ya sure ta ba itama.
12 noon Sufyan ya farka finally zazzab’in ya sauka wanka yayi sannan ya fito falour’n ganin
bata nan ya lek’a d’akin ta inda ya iske ta tana bacci a takure, tausayi ta basa sosai ganin
yadda ta zabge kwana biyu cal, innocent face nata ya shiga k’arewa kallo yayin da hoton
suka shiga yi masa yawo akai, duk yanda yaso yarda ta aikata zuciyan sa yak’i basa had’in
kai dan haka ya yarje wa kansa bata aikata ba.
Gyara mata rufuwan ta yayi sannan ya koma falour bai damu da wani yin breakfast ba ya
d’iba passport natan ya fice.
Gurin abokin sa dake harkan visa ya nufa dan solution d’aya ya yanke ya bar k’asar da ita
bayan wasu shekaru ta dawo, without hesitation aka shiga processing musu visa nasu sai
da ya gama komai na tafiyar tasu sannan ya koma.
A falour ya sameta ta zuba uban tagumi ta lula duniyar tunani duk sallaman daya mata
bata ma san yanayi ba har saida ya k’araso ya dafa ta sannan ta d’ago a firgice tana kallon
sa.
Zama yayi a gefen ta yace ” kinci abinci?
Kada masa kanta tayi meaning no dan haka ya kira receptionist ya musu order, ba’a d’au
lokaci ba order’n nasu ya iso.
Had’e fuskan sa yayi babu alaman wasa yace ta sauko suci, ganin ransa a b’ace kuma
bata jure hakan yasa ta sauko ta tankwashe k’afan ta tad’au spoon ahankali ta soma ci,
ganin ta soma ci shima yayi joining nata.
Ringing wayan sa ya sanya su duka kai duban su, “Angelic Mom’ itace sunan da tayi
appearing a screen d’in, suna gani ya katse ba tare da Sufyan yayi attempting d’auka ba, so
take tayi mar magana amma ta kasa dan yadda annurin fuskan sa ta sauya.
Kiran ne ya cigaba da shigowa amma still yak’i d’auka, ganin kira na tara na shirin yanke wa
tayi saurin kai hannu zata d’auka, cikin zafin nama ya rigata d’aukewa yayi switching
wayan gaba d’aya.
Kallon ta ya tsaya yi ganin yanda ta shiga rera kuka wane wadda za’a cirewa rai, na sosai ta
basa haushi dan du kalan abubuwan daya ke yi saboda itane.
Ko nakan ta baiyi ba yayi wucewar sa d’aki wayan nasa ya kunna ya shige neman wani
friend nasan da suka yi karatu a Cyprus tare amma shima ba d’an k’asar bane dan Saudi
Arabia ne.
Batare da b’ata lokaci ba ya d’auka inda suka shiga gaisawa like never before, nan ya
shaida masa zai zo Saudi kuma tare da Sadiya.
Cike da k’in yarda ya sake nanata sunan he just can’t wait to meet her in person, fad’in irin
happiness daya shiga ma b’ata baki dan yadda yake matuk’ar so da k’aunar ta.
Hira sukayi sosai kafin su yi sallama suka kashe wayar, as promise tailor na gama
d’inkunan ya kawo mawa Sufyan.
Tun kuma abinda ya faru ranan suke fishi da juna, hakan kuma ba k’aramin damun su yake
ba, amma an rasa wanda zai fara sauke pride and ego nasa acikin su.
Shirye_shiryen tafiyan nasu ya ci gaba da yi harkuma lokacin bai fad’a mata what he is
capable of doing ba.
AWeek Later
Ya kama ranar da flight nasu zai tashi, tun 6 ya gama komai nasa dañ jirgin 10 zasu bi.
D’akin ta ya shiga ya ganta tsaf_tsaf da ita wane tasan da tafiya a gaban su.
Ahunkula ya k’araso kusa da ita ya zauna ita kuma ta sake had’e rai, shi dariya ma ta basa
amma ya bone ya shiga bata hak’uri ya kuma shaida mata idan akwai abinda take buk’ata
ta fad’a masa dan yau zasu bar k’asar.
Tsayawa tayi tana kallon sa totally out of word, ganin haka ya had’e hannun su guri d’aya
ya mata bayanin dalilin da ya sanya yayi deciding ya bar k’asar da ita.
She has no option does she? dan haka kawai ta amince da shawaran sa ta kuma nemi favor
daya barta ta sake sanya Mummy’n su ido kafin su tafi, dan a zuciyan ta tariga da ta yanke
inhar tabar k’asar bazata sake dawowa ba.
Ganin ya nuna k’in amincewar sa ya sanya ta hak’ura badan ranta ta so ba.
Abubuwan da zata buk’ata ta cigaba da had’a wa sannan suka dawo falour suna hiran su
na ‘yan uwa.
K’arfe 9:30 am ya kai musu kayansu kaf mota sannan ya kirata ya bada key na d’akin suka
tafi.
Basu dad’ da zuwa airport ba aka soma kiran passengers wani irin kuka ne ya kwace mata
mai ban tausayi, ganin tanajin tana gani zata bar mahaifarta, family’n ta infact everything
ma.
Rarrashin ta ya shiga yi jin anata kira sannan ya kalla abokin sa da suka zo airport d’in tare
ya basa car key d’in yaja hannun ta suka nufa jirgin.
Suna tafiya tana waiwaye tana kuka sosai har suka soma hawa steps na jirgin, koda suka zo
shiga sai da yayi dagaske ya samu ta shiga.
Shi kansa saida ya share kwalla saboda tausayin ta ga kuma yadda take kukan numfashin
ta harwani sama_sama yake yi, ahakan wani wahalallen bacci ya d’auke ta.
Hamdala yayi ga unangiji ganin tayi bacci, kuma ikon Allah har suka je bata tashi ba.
Muhammad Khaleepha dake zaune a airport yana jiran isowan su yanajin announcing na
saukan plane nasu ya sauke wata kyakkyawan ajiyan zuciya finally yau zuciyan sa zata ga
abinda take so idanuwan sa zasu ga abinda suka dad’e suna marari.
Jin an dafa sa yayi saurin d’agowa ” Sufyan Habibi ” yayi ex claiming happily.
Da sauri yakai duban sa kan Sadiya sai dai ba haka idanun sa suka so ganin ta ba dan
yadda idanun ta da fuskan ta sukayi mugun kumbura and kallo d’aya zaka mata ka hango
matsananciyar damuwa tare da ita.
Kallon tuhuma ya jefa Sufyan dashi, shikuma ya basar ganin haka ya d’ebi kayan su suka
nufa mota.
Saida suka nufa hanya sannan ta gaishe shi da dishash shiyar muryarta, cike da kulawa ya
amsa daga haka kuma ba wanda ya sake magana har suka isa gida.
Kyakkyawan tarba suka samu amma duk da haka Sadiya ta kasa sakewa.
Khaleepha uban rawar kai sai ka rantse da Allah soyayya yake da Sadiya dan yadda yake
nunawa family’n sa.
Kwanan su biyu da zuwa Sufyan ya fayyace mar duk abinda ke faruwa, sosai ya tausaya
mata ya kumayi alk’awarin kulawa da ita har k’arshen rayuwan sa.
A karo na biyu ya sake rok’on Sufyan ya basa ita amma sam ya nuna masa har abada bazai
tab’a yi mata abinda bata so ba sai dai in ta amince.
Tare da Khaleepha suka kaita school yayi niyyan ta zauna a hostel amma sam Khaleepha
yace bai san zancen ba, dan dole Sufyan ya yadda ta zauna a gidan su Khaleepha badan
yaso ba.
Kwanan su hud’u Sufyan ya shaida mata gobe zai koma Nigeria, ai fad’in tashin hankalin da
ta shiga ma b’ata baki ne dan tun alokacin ta soma rera kukan da ya zamo mata sa’a,
lallashin duniya anyi amma tak’iji.
Washe gari Sufyan yayi niyyan tafiya batare da ya mata sallama ba Khaleepha ya hana, dan
dole ya yarda ya nufa d’akin da take suyi sallama.
Tanajin k’amshin turaren sa tayi saurin juya masa baya daga kwancen da take, ba kalan
surutun da bai mata ba amma ko na kansa batayi ba, haka ya mik’e jiki a sanyaye yai
pecking forehead nata ya fice daga d’akin.
Yana fita ta rushe da wata masifaffiyar kuka she just can’t imagine life without him, how on
earth will he think of living her, does that means he don’t love and care for her anymore?
kuka take wane zata cire ranta.
Sufyan ma kaman ba namiji ba zagewa yayi shima ya shiga rusa kuka kaman ba gobe bai
tab’a tsammanin irin wannan rana zata zo ba a rayuwan sa.
Khaleepha ke aikin rarrashin sa har suka isa airport already an fara k’iran passengers dan
haka yayi saurin jan trolley nasa yayi gaba, har ya kusa isa steps na jirgin ya dawo ya
damk’e hannun Khaleepha not letting go yace ” Khaleepha na baka amanar Sadiya bata da
kowa anan sai kai dan Allah try as much as possible and protect her by any harm, stay by
her side and protect her please nasan kalan son da kake mata bare bari ka cuce ta ba “.
Damk’e hannun sa shima Khaleepha yayi yace ” I promise to you Sufyan Habibi insha Allah
I will protect her with all l’ve got, I will make sure treat her like a queen I will always bea
shoulder for her to cry “
Jin yadda aketa announcing jirgi zai tashi yasa Sufyan sake sa ya nufa jirgin yanayi yana
waiwaye.
Tunda ya tafi yake tunanin memory nasu dasu kayi sharing together tun suna k’ana na har
girman su dai_dai da “RANA D’AYA”_Miemiebee_ basu tab’a kawo wani abu makamancin
rabuwa ba a tsakanin su ba, haka har suka iso Nigeria yana cike da kewan ta.
Bayan sun sauka a airport ya kira abokin sa daya zo d’aukan sa, already dama yana airport
d’in yana jiran sa dan haka ya sanya kayan sa a mota suka nufa gida.
On there way home suka ga wani terrible accident data faru, Sufyan daya mugun tausaya
musu yayi saurin cewa da Amir yayi stopping motar.
Parking sukayi a gefe sannan suka nufo gurin, mutane sun taru wasu sai videos ake ana
yad’a news amma an rasa mai taimakon su.
Da sauri ya nufi dattijon daya d’ago hannun alaman neman taimako yace ” Baba mai kake
buk’ata”
Rik’e hannun Sufyan yayi k’amk’am sannan ya kamo na ‘yar budurwar dake rusa kuka ta
d’ayan side nasa ya had’a guri d’aya.
Cike da tsananin azaban daya ke ciki yace ” d’an samari ga amanan ‘yata Safiyya na baka ni
nawa ya k’are, bata da kowa sai Allah sai kai, jiki na na bani zaka rik’emin ita da gaskiya
Juyawa yayi yana fidda numfashi dakyar ya kalli Safiyya yace ” ‘yata inaso duk rintsi duk
wuya ki kasance tare da shi Allah ya albarkaci rayuan ku gaba d’aya”.
Kad’a kai ta shiga yi sosai wane k’adangaruwa, sam ta kasa furta ko wani kalamu.
Wani malami ne ya k’araso gurin cike da tausayawa, nan take mahaifin nata ya masa alama
da d’ayan hannun nasa meaning ya k’araso.
Ahankali ya taka ya isa inda suke, dakyar cikin alamun fitan rai yace ” Malam dan Allah na
rok’e ka da ka d’aura musu aure immediately bayan an sallaci gawana kafin a sanya ni a
k’abari “
Nan ya soma wani irin nishi yana kalman shahada har rai yayi halin sa, wata irin
masifafiyar kuka ta fashe da ita shikenan bata da kowa, ta zama marainiya ba uwa babu
uba ahankula ta sulale ak’asa sumammiya.
Sufyan daya zama mutum mutumi ganin abin yake kaman a mafarki, wannan wace irin
K’ADDARAH’ ce acikin wannan watan ya rabu da yar uwar sa abar k’aunar sa ba tare da ya
shirya ba, ga wata jarrabawar kuma ta sake samun sa batare daya shirya mata ba.
ya ya ya
shirya ba, ga wata jarrabawar kuma ta sake samun sa batare daya shirya mata ba.
Runtse idanu yayi kalamun Mahaifin ta na masa yawo aka nan take wani irin ciwon kai ya
dirar masa.
Kansa kaman zai tarwatse haka ya mik’e aka d’iba gawan iyayen nata aka nufi gidan
malamin dan sutur ta su.
Bayan an wanke su aka sallace su kafin a tafi kaisu kushewar su aka d’aura auren Sufyan da
Safiyya, sannan aka nufa mak’abarta dasu.
Bayan an binne su sun dawo Malam ya had’a crying Safiyya da Sufyan ya musu nasiha mai
ratsa jiki sannan suka shiga mota suka tafi.
Safiyya na cike da zullumin yadda zatayi rayuwa da Sufyan shi kuma yana tunanin yadda
zai rik’e ta batare da ya ci amanan da mahaifin ta ya ba saba.
Har suka isa gida ya gaza sama musu solution, he has no option than to stay with her no
matter what it takes, luckily da suka zo gate man yaje sallah without any hesitate ya wuce
da ita part nasa batare da sanin kowa ba.
Suna shiga falour’n ya nemi guri ya zauna ya dafe kansa dake tsanin sarawa da but hands
nasa, tunanin sa bai wuce yadda zai soma shaidawa Mummy da Daddy yayi aure ba batare
da sanin su ba.
Safiyya kam zamewa tayi ajikin k’ofan d’akin tana rera kuka mai ban tausayi.
Ringing ta wayar sa ta sashi mik’ewa yabar falour’n ya nufa bedroom, crying Sadiya ce ta
kira gashi duk yadda yaso rarrashin ta abin ya faskara, kukan nata ma har ya wuce na
hankali da tasan matsanancin halin daya ke ciki da bata saka sa a gaba da wannan kukan
nata ba.
Kashe wayan yayi ya shiga nanata innah lillahi wa’innah ilaihir raji’un ko yaji sauk’in
rad’ad’in da zuciyan sa keyi, sai da ya d’auka tsawon lokaci sannan jiki a sanyaye ya nufa
toilet ya sakarwa kansa shower.
Sai da ya d’au about 20 minutes sannan ya fito ya sanya kaya ya shimfid’a sallaya ya
fuskanci alk’ibla, koda ya idar kasa tashi yayi a wurin ya shiga rok’on Allah ya bashi ikon cin
jarrabawar daya jarabce shi.
Mik’ewa yayi ya haye gado abinsa dan ya sama peace of mind sai dai daya rufe ido innocent
crying face na Safiyya yake gani, nan take kalamun mahaifin ta suka soma mar yawo aka,
wane an mintsile sa ya mik’e ya nufa falour’n.
Kwance ya hango ta tana bacci a wahalance jikin ta banda rawa babu abinda take tayi
matashi da hannun ta, one more look ya sake yi mata ya tabbatar da zazzab’i ajikin ta dan
yadda ta k’ank’ame jikin nata wane mai tsoron za’a gudu da ita.
Ahankula ya mik’a hannun sa yana son tada ta amma ya kasa gashi baijin zai iya d’aukar ta,
na sosai ya shiga k’are mata kallo ” ba laifi she is cute ” ya fad’a a zuciyan sa sannan yayi
saurin mik’ewa.
K’afan sa yasa ya shiga shurin ta harya samu ta farka a firgice, addu’a tayi ta mik’e zaune ta
sunkuyar da kanta k’asa jikin ta na rawa the more.
Tsuka yaja ya kalle ta yace ” ga d’aki can kije kiyi wanka dan bansan k’azanta, sannan inhar
kina so mu shirya ki san mutuncin addinin ki “.
Sababbin hawayene suka kwarinyo mata sannan ahankali ta amsa shi, mik’ewa tayi dakyar
ta soma takawa ko taku biyu batayi ba jiri ya kwashe ta, she is about to fall yayi saurin
tallafo ta jikin sa rungumar sa tayi k’amk’am tanajin d’akin na juya mata, wata electric
spacks suka jiyo tun daga tafin k’afan su har tsakan kansu both.
K’ok’arin janye ta daga jikin sa yake amman ya kasa dan ba K’aramin rik’o tayi masa ba,
cike da takaici ya shiga takawa da ita har suka nufa d’akin.
Jin ta dawo dai_dai ya sanya ta saurin sake sa taja gefe cike da kunya ta sunkuyar dakai
tace ” sorry”
Banza yayi mata ya nufa gefen gado ya zauna ya dafe kansa ” ya Allah meke shirin faruwa
dani? ” yayi throwing ma kansa question.
Ring ta Wayana sa ya sa sa d’agowa ahankali yana bin wayan da kallo, sai da ta masa four
miss call sannan yayi picking na biyar d’in.
Hak’uri ta shiga basa sosai sannan suka yanke wayan suka koma video call, kaman a
mafarki ta hango ‘yar budurwa a bayan Sufyan fuskan ta na d’igan ruwa.
Waro idanu tayi a tsorace tana pointing mar bayan sa, juyawa yayi yaga Safiyya data fito
daga wanka takure a guri d’aya, kautar da wayan yayi yadda Sadiya bara tana gani ba ya
buga mata tsawa data mugun firgigita ta, hanyan falour ya mata pointing fuska a had’e,
saurin ficewa tayi sannan ya maidar da wayan position nata yana kallon speechless Sadiya
dake jifan sa da kallon tuhuma.
Rasa ma ta inda zai somayi mata bayani yayi hartayi zuciya ta kashe wayan, kiran ta back
ya shigayi inda ya samu tayi picking dakyar sannan ya mata bayanin komai, dan sam basa
b’oyewa juna sirrin su da damuwan su.
Hankalin ta itama ya tashi sosai amman ganin da tayi nasa yafi tashi ya sanya tayi calming
kanta ta shiga kwantar masa da hankali, sannan ta rok’e sa daya rik’e amanan Safiyya
kamar yadda shima ya bada nata, ta kuma nusar dashi du kalan abinda yayi wa Safiyya
itama za’ayi mata ko fiye da haka, jikin sane tayi mugun sanyi ganin tun a ranar farko ya
fara shouting mata, hakan na nufin kenan shima ranar daya baro Sadiya hakan aka mata, “
Ohh Allah ka yafe min “ya fad’a a mind tasa not knowing ta fitofili.
Duk yadda taso ya had’a su ya k’i daga K’arshe ma kashe wayan yayi.
Abokin sa ya k’ira ya nema alfarman yayo musu take-away dan ko bata fad’a ba yasan
tanajin yunwa.
Kiraye_kirayen sallan magarib ya sanya sa d’auro alwala ya fito falour’n dan tafiya
masallaci, hango ta yayi ta takure kanta ajikin sofa abin tausayi.
Gaba d’aya sai yaji ba dad’i dan haka ya isa inda take, ahankali ya tsuguna ya rufe gaf d’in
dake tsakanin su, jin nishin mutum kusa da ita ya sa ta d’ago a tsorace, ja baya tayi cike da
tsoron abinda zai sake biyo baya.
Ahankali wane mai koyan magana yace ” am sorry for shouting at you earlier sannan ki
tashi kiyi sallah”
With nod ta ansa sa sannan ya tashi ya fita, mik’ewa tayi cike da azaban zazzab’i da ciwon
kai ta tada sallah dan an tayar.
Acan ya had’u da Daddy dasu Nasir amma yanda kukan san bai sansu ba haka ya nemi guri
can nesa dasu, haka har aka idar da magrib suka zauna jiran isha dan k’a idar su ce hakan.
Koda time yayi aka idar ficewan sa yayi batare da ya kalla site d’in su ba, na sosai Daddy
yaji zafin hakan amma bai bari su lbrahim sun gane ba.
A gate ya had’u da abokin nasa ya kawo masa sak’on ya K’arfa ya shige ciki, tana nan inda
ya barta ta k’udun dune cikin hijab nata.
K’arasawa yayi ya mik’ar da ita ya jinginarjikin sofa sannan ya bud’e mata pack d’in abincin
da aka kawo, nan take tsohuwar yunwan ta ya tashi ahankali taja abincin tayi bisimillah ta
soma ci hannu baka hannu kwarya.
Jan nasa yayi ahankali ya soma ci yana kallon yadda take cin abincin wane bata tab’a cin
abinci ba, sosai ta mugun basa tausayi ko spoon biyar baiyi a nasa ba yaga ta cinye nata
kuma dagani kasan bata k’oshi ba dan haka ya mik’a masa nata.
A kunyace taja shima ta tashe sa a aiki sannan ta sha ruwa tayi gyatsa ta godewa
mahaliccin ta tagodewa Sufyan.
Koda lokacin bacci yayi d’akin ya tura ta shi kuma ya kwanta a falour sai dai sam ya kasa
bacci, yayin da itama ke can cikin mawuyacin hali.
Mik’ewa yayi ahankali ya nufa d’akin ya kunna wutan d’akin nan ya hango ta sai kuka take
abin tausayi, jikin ta banda rawan zazzab’i ba abinda take.
Ahankali ya k’arasa ya nemi gefen gado ya zauna, hannun sa yakai goshin ta nan yaji zafi
d’au cike da tausayawa ya mik’e ya nufa
oilet ya d’ebo ruwa mai kyau a bowl, ya d’auko
tsaftataccen towel ya fito.
Gadon ya hau ya janyo ta jikin sa gaba d’aya yana feeling yadda zafi jikin ta ke ratsa sa, a
nitse ya soma k’ok’arin zame rigan jikin ta tayi saurin rik’e hannun sa tana girgiza kai
hawaye kam kaman an bud’e lalataccen tap.
Ignoring nata yayi ya cire rigan, da sauri ta runtse idanun ta tasa hannu tana kare k’irjin ta,
towel d’in ya rik’a sanyawa cikin ruwan yana matsewa yana danna mata jikin ta, sai da
temperature nata ya sauka ya d’auka rigan nata ya mayar Mata sannan ya kwantar da ita
kan pillow ya mik’e ya d’au bowl d’in da towel ya tafi Toilet.
Zubar da ruwan yayi ya shanya towel d’in ya fito, bedside drawer ya bud’a ya d’auko
paracetamol ya tsiyayo ruwa a dispenser ya bata, dakyar ya samu ta sha ya gyara mata
rufuwan ta ya koma falour.
Nan take baccin gajiya ya d’auke sa, kiran farko na asuba ya tada sa dak’in ya nufa ya shige
toilet yayi wanka ya d’auro alwala ya fito ya tada ta ya tafi masallaci.
Koda ta tashi sosai taji dad’in jikin ta dan yayi sauk’i, toilet ta tafi tayi wanka ta d’auro
alwala ta fito d’aure da towel haka nan taji bata son miyar da kayan data cire tunowa da
tayi yace bayason k’azan ta.
Falour taje ta bud’e trolley bag nata taciro wasu kayan ta sanya sannan ta koma ta tada
sallah koda ta idar kasa tashi tayi, addu’a sosai tayi mawa iyayen ta sannan ta rok’i idan da
alkhairi a zaman su da Sufyan Allah ya barsu tare idan kuma babu Allah ya had’a kowa da
rabon sa.
Fashewa tayi da kuka tunowa da tayi idan ta rabu da Sufyan batasan halin da zata shiga ba
dan bata da kowa sai Allah sai shi.
Kaman yadda ta faru jiya a masallaci yau ma hakan ce ta faru dan sam Sufyan nunawa yayi
kaman bai san su Daddy ba, na sosai su lbrahim ma sukaji haushin abinda Sufyan ke musu
amma dan kar Daddy ya shiga damuwa ya sa suka sanya masa ido suga iya gudun ruwan sa
A falour ya dawo ya tarar da ita, gaida sa tayi ya ansa yana tambayan ta ya jiki, a kunyace ta
ansa sa ganin haka ya nufi d’akin ya soma shirin office dan ranar zai koma.
Koda ya fito zai tafi sosai ya kashe mata warning kar tayi noticeable sound da sa asan da
mutum ciki dan in tayi aka kamata shi dai babu ruwan sa ita kad’an ta zata sha wahalan ta,
sannan ya nuna mata wani leda dake shak’e da popcorn da cookies aciki dan sai shida zai
dawo.
Hakanan suka cigaba da rayuwa and babu laifi yana bata kulawa with all that he got, ta
fannin Sadiya ma sosai ta dage da karatun ta yayin da shak’uwa mai k’arfi ta shiga tsakanin
ta da Khaleepha dan yadda yake mugun bata kulawa.
Waya kam kaman ba gobe kullum cikin yinta suke, Nasir tun suna d’aukan abin na Sufyan
wasa harya zarce tunanin su dan gaba yake da duka ‘yan gidan sam bai d’agawa kowa k’afa
ba gashi yanzu almost one month dan haka yau ya yanke samun sa yaji mai yake nufi da su.
Sanin da yayi Sufyan duk ranar Friday na tashiwa a aiki da wuri ya sanya sa nufan part d’in
sa dan baije parking lot ba balle yaga babu motan Sufyan d’in a gurin.
Luckily k’ofan falour’n a bud’e take dan haka ya kunna kai d’auke da sallama a bakin sa, jin
da yayi ba’a amsa sa ba yasa ya nufi bedroom d’in Sufyan, dai_dai lokacin kuma Safiyya ta
fito daga wanka d’aure da guntun towel sanin da tayi ita kad’ai ce a part d’in.
Saida ta kusan cin tuntub’e saboda tsananin razana da tashin hankali gashi gaba d’aya
kanta ya kulle tama rasa meye ne zatayi, cikin zafin zuciya lbrahim ya soma nufar ta wane
mayunwacin zakin da ya jiyo k’amshin d’anyen nama.
A rikice ta soma ja baya yana binta har suka isa bango, wata muguwar shak’a ya mata ya
had’a da bango idanuna sa sunyi wani irin mugun ja jijiyoyin kansa duk sun mimmik’e
saboda tsananin b’acin rai da k’unan zuciya.
” Dan ubanki wacece ke? Meye had’in ki da k’anina? Mai ya kawo ki cikin d’akin sa? ” yayi
throwing mata questions d’in a tsawace.
Tsantsan azaban shak’an daya mata ya hana ta ansa sa, tuni idanun ta suka firfito ta soma
jiyo k’amshin lahira, both hands nata tayi using ta rik’e hannun sa tana son ta ceci kanta
amma ina k’arfin namiji da na mace ba d’aya ba.
Sufyan tunda aka idar sa sallan juma’a abokin sa ya janye sa yawo shaf ya manta ko abinci
bai barwa’yar mutane ba dan yace mata da wuri zai dawo, har k’arfe hud’u suna tare sai da
ya idar da sallan la’asar sannan ya tuno da yar mutane gashi jikin sa sai basa yake
something bad is going to happened dan haka ya masa sallama ya tafi..
6:53 PM O
**
Gashi dai gudu yake amma gani yake sam baya sauri, dakyar ya samu ya tsaya a wata down
town dake gefen hanya ya mata ordering pizza da shawarma.
Sannan ya tafi gidan cike da fargaban abinda zai tarar, tun a parking lot gaban sa ke tsanan
ta bugawa har ya nufa hanyan part d’in sa ba’a nitse yake ba, hankalin sa ne yayi mugun
tashi ganin k’ofan falour’n sa a bud’e sai lokacin ya tuna yau ya fita yana sauri ya manta bai
rufe d’akin ba.
Kaman an wurga sa ya fad’a falour’n ganin bata nan yayi saurin nufan d’akin inda idanun
sa sukayi masa mummunar gani, da sauri ya k’arasa ya fizge hannun lbrahim daga wuyan
ta cike da tsananin b’acin rai da Kishi.
Zubewa tayi a k’asa jikin ta na kakkarwa tana wani irin azababben tari, hannun ta takai
wuyan ta tana murzawa cike da azaba tana fidda wani irin numfashi, hawaye kam kaman
an bud’e lalataccen tap.
Wasu mahaukatan maruka lbrahim ya sakar wa Sufyan ya d’aga hannu zai rama muryan
Mummy ta daki kunnen sa..

About Ismail

Check Also

SOYAYYAH CHAPTER 13

SOYAYYAH CHAPTER 13 Lumshe idanun ta tayi hawaye masu zafi suka kwarinyo mata.  Abbah ne …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *