[Advertisements⬇️]

SOYAYYAH CHAPTER 5 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

SOYAYYAH


CHAPTER 5

Emergency room aka nufa da ita, lokitoci kusan biyar ne suka rufa akan ta hankalin Dr
lbrahim ya kai k’ololuwa gurin tashi ganin duk iya taimakon daya dace su bata sun bata
amma abin yaci tura.
Alhaji ba kuka zaka tsayayi ba a yanzu babu abinda Baby take buk’ata sama da addu’an
mu, nice mahaifiyar ta amma tunda kaga na d’aura ya kamata kai ma ka dangana.
MieMie ce ta K’araso da gudu ta fad’a jikin Daddy crying so hard duk yadda ya so daurewa.
ya kasa dole shima yayi hugging ta back crying like never before.
Mummy kam ta rasa da wanne zataji sai safa da marwa take, kaman a k’iftawan ido taga
green light na blinking da sauri ta nufa kofan inda isan ta yayi dai_dai da fitowan Dr
Ibrahim dake ta faman share gumi at the same time kuma sai jera ajiyar zuciya yake.
“Dr how is my daughter? What’s wrong with her? Is she feeling better? ” ta shiga jera mar
tambayoyin a rikice.
” Follow me ” kawai ya iyace da ita.
Da saurin ta tarufa masa baya yayin da Alhaji da MieMie ma suka bi su.
Yana shiga lab coat nasa ya cire yayi hanging sannan ya shiga gyara neck tie nasa, guri yayi
masu pointing inda dakyar ya samu suka zauna sannan shima ya nemi guri ya zauna giving
all his damn attention to them.
K’are musu kallo ya shigayi amma har alokacin ya kasa magana, su kam iya k’aguwa sun
k’agu dan haka Alhaji yace ” Dr ka fad’a mana halin da yarinyar mu take ciki mana, idan ta
mutu ne just let me know na sani Allah daya bamu ya fimu santa shiyasa ya karb’i abar sa “
ya fad’a kalan tausayi.
Sosai Dr’n ya tausaya musu dan haka yayi gyaran murya ya fara magana ” Am sorry to
say.
” Ta mutu ko? ” Mummy tayi saurin katse sa cikin sautin kuka.
“No not at all Hajiya ki kwantar da hankalin ki Allah yayi da ragowan kwanan ta a gaba, but
to be sincere rayuwan ta tana cikin had’ari tunda ta fara samun attach at this her age…”
“Attack!! ” sukayi ex claiming not giving him room to finish his explanation.
With Nod ya basu tabbacin hakan ” Innah lillahi Wa’innah Ilaihir raji’un ” suka shiga
nanatawa.
Zubewa MieMie tayi a k’asa kaman zararriya yayin da gobaran tsanan Suwayd ke sake
linkuwa a zuciyan ta dan tasan he is the reason behind it.
Mummy ma Suwayd ne kawai ya fad’o mata dan tasan indai ba dalilin sa ba hakan baza
ta samu d’iyar ta ba, ” Bakomai Baby Allah yana tare da ke ” tayi maganan a zuciyan ta.
Magungunan da za’a buk’ata ya basu su siyo sannan yace ” zaku iya zuwa ganin ta but
you have to be very careful akan duk wani abu dazai d’aga mata hankali ko sanya ta tuna
last incident daya faru kafin ta samu attack d’in “.
A sanyaye kaf suka mik’e wata Nurse tayi escorting d’in su special room d’in da aka kaita
dan hutu, baka iya tantance yanayin kowa acikin su har suka shiga d’akin.
Kwance take lifeless an sanya mata oxygen hannun ta kuma an sanya mata drip, looking
so pale Mummy ce ta k’ok’arin k’arasawa ta zauna agefen d’ayan hannun ta tarik’e
K’amk’am cike da tsananin tausayin d’iyar tata, lafiya lau ta fita d’aga gida amma yanzu ga
yadda Allah yayi da ita gashin ta daya barbaje ta janye mata gefe.
K’arasowa MieMie tayi ta dafa kafad’an Mummy tears na forming rapidly a idon ta, girgiza
mata kai Mummy tayi tace ” Don’t dear”
Share hawayen tayi sannan itama ta zauna a gefen kafafun ta, sai sannan Daddy ya
k’araso yayi pecking forehead d’in ta cike da tausayawa sannan ya wuce stalling bills.
” Your shine fast galaxy in d sky u are d gift dat god has gives me 4 d reword of my
prayers u are d only one in my life and hereafter insha Allah I love you for ever and ever and
ever Suwayd please have mercy on me, ka tausaya wa rayuwata am nothing without you
am in so much pain.. sai surutai take dan already ta fizge oxygen din now trying to
remove the drip, da k’arfi ta fizge drip d’in tuni jini ya fara zuba mata dafe zuciyan ta tayi
dake matuk’ar suya.
“Meyasa bazai soni ba,mai nayi masa l wish dead to come and take me from this painful
word.buga kanta ta shigayi sosai ajikin bangon d’akin kafin wani lokaci tuni jini ya
wanke mata fuska.
” Innah Lillahi Wa’innah llaihir raji’un ” Mummy data dawo daga d’ebo musu abinda zasu
buk’ata tayi ex claiming cike da k’in yardar abinda idanuwan ta ke gani.
Sakin kayan hannu ta tayi ta fice tana kwalawa Dr kira da sauri ya iso dan already wata
Nurse ta shaida masa abinda ke faruwa.
D’amk’e ta yayi yana k’ok’arin hanata abinda take itakam sai fizge_fizge take wane mai
shirin tada aljannu tanaita yabarta ta kashe kanta.
Da ido yayi wata Nurse alama ta fice without hesitation ta dawo da syringe a hannun ta,
cike da dabara yayi mata alluran not long enough wani wahalallen bacci yayi taking over
nata.
Mummy kam na gefe banda kuka babu abinda take ita tsoron ta Allah yasa ba haukacewa
Zee tayi ba.
Kwantar da ita Dryayi sannan ya shiga treating mata raunin data ji, yayin da aka kira
cleaners suyi clearing garbage d’in data yi.
Blood aka nema dan yadda ta zubda jini tana buk’atan k’ari, da sauri Mummy ta k’ira
Alhaji ta k’irga masa abinda ke faruwa, Hankali a tashe yace mata ga shinan zuwa.
Yana zuwa aka gwada Blood nasa inda yayi dai_dai da nata, leda d’aya aka d’iba aka
sanya mata, duk yadda suka so sanyasa ya kwanta yak’i dan fargaban a wani hali Zee zata
tashi.
*****
Safwah na zaune lonely Safwan ya shigo tsantsan kaman da suke ya isa shaida ma twins ne
harta da blue eye nasu kala d’aya ne.
Babu abinda ya banbanta su, yana k’arasawa jikin gadon ya mik’a masa right hand nasa
tayi pecking.
Hawaye ne ya cika mata ido dan batasan taya ne zata mik’a masa nata hannun ba, gano
abinda yasa take shirin yin kuka saiya d’ago left hand nata ahankali shima yayi pecking
yana sakar mata best smile nasa da take matuk’ar k’auna.
A gefen ta ya zauna ya had’e left hands nasu guri d’aya yace ” Twiny ya jikin?”
” Da sauk’i ” ta amsa feeling cool and safe when ever he is with her.
IPhone d’in Ummy daya shigo da ita yayi unlocking password d’in yayi dialing wani
Number, dagani bana k’asar bane.
Not long enough aka d’auka, gaisawa sukayi sosai sannan ya sanya wa Safwah wayan a
kunne itama suka gaisa cike da kewan juna, hak’uri na sosai ta bata akan abinda Suwayd
yayi mata sannan ta nanata mata duk rintsi karta yarda Granny ta san they’re in contact.
“But Ammey don’t you think is yet time ki gyara tsakanin ki da Mahaifiyar ki dama ‘yan
uwan ki baki d’aya “.
” Damn it Safwah, damn it wannan ya zama first and last time da zaki sake min magana
haka idan ba haka ba ke kanki bara ki sake samu na ba, Understand? ” tayi maganan a d’an
tsawace
“But Ammey kinsan fa innallaha ma’assabirin, you have to forget the past and just move
on, there is no day goes by Granny batayi tunanin ki ba, tana matuk’ar k’aunar ki you are
her one and only daughter please Ammey ki zo ko sau d’aya ne ta ganki at least ta rage
rad’ad’in rashin ki dake damun ta”.
Tabbas babu k’arya a maganan Safwah amma taya ne zata manta da duk kalan abubuwan
da suka faru ta zo no she can’t, katse wayan kawai tayi without uttering a word.
Trying Number’n suka tayi amma tak’i picking dole suka hak’ura badan sun so ba.
A marairaice ta kalli Safwan tace ” Twiny don’t you think is yet time Ammey ta gyara
tsakanin ta da family’n ta?
“Twiny what I want you to understand is that Ammey ta kasa mance abinda ya faru, tunda
tak’i jin maganan Abuh banjin akwai wanda zata saurara mu k’ara mata time zata sauko ko
dan ta had’a mu da ‘yan uwan mu”
Gyada masa kai tayi cike da damuwa dan sosai take tausayawa Granny.
Suna cikin hiran su Mammy ta shigo duba jikin Safwah, zama tayi suka ci gaba da hiran
harda ita.
Ummy kam tanason zuwa duban d’iyar ta amma kunya da kawaici ya hanata, dan tunda
sukaje asibitin tana bacci bata sake sanya ta a ido ba gashi she is burning inside.
****
Granny zaune akan sallayar ta kallo d’aya zakayi mata kasan taci kuka ta gode Allah dan
yadda idanun ta sukayi jajur dasu.
Hannayenta ta d’aga sama tana addu’a ” Allah na rok’e ka inhar Sadiya tana raye ka kare
min ita daga sharrin abin k’i, idan ta koma gare ka kuma ka jik’an ta kasa aljannah ce
makomar ta, ya Allah ina ji ajikina tana rate na rok’e ka dan girman sunayen ka tsarkaka ka
had’a mu na nemi yafiyar ta kafin na koma gare ka”.
Wasu zafafan hawaye ne suka sake kwarinyo mata a karo na ba adadi sannan ta mik’a
hannu ahankali kan side drawer nata ta d’auko wani frame, ahankali ta shiga shafa fuskar
18 years budurwan dakejiki ta tafi tunanin wasu shekaru da suka gaba ta.
20 YEARS BACK
Alhaji Muhammad lbrahim Agadez haifaffen Niger ne, yana da arzik’i dai_dai gwargwado
ba irin na haukan nan ba, babban dan kasuwa ne da yayi fice gurin fita k’asashe
daban_daban.
A haka wata rana yaje Sudan ya had’u da Ruk’ayya inda nan take soyayya mai k’arfi ya
shiga tsakanin su, sai da aka kai uwa rana sannan iyayen ta suka yarda da auren, bayan
aure ya d’auko abarsa suka dawo Niger.
Haka nan suke rayuwar su cike da jin dad’i duk dangin sa na matuk’ar k’aunar ta
kasancewar ta mai son al_umma.
Shekarar su d’aya da aure aiki ya maida sa Nigeria sam bata so hakan ba saboda ganin ita
ta baro nata family’n gashi yanzu shima zai bar nasa, haka dai yaita convincing d’inta harta
saki ranta dangi kam kowa baiso ba amma ganin is for his own benefits suka bisa da fatan
alkhairi.
A sharad’a suka fara zama kafin ya bada contract na kalan gidan da yake so aka Gina masa
a makeken filin sa dake”Yaya Gusau Road”
Had’add’iyar mansion ce data amsa sunan mansion me d’auke da four parts, duk wani
abin more rayuwa akwai aciki kama daga, Garden, Gym Room Swimming pool da sauran
Su.
Bakomai yasa yayi four parts ba sai dan yanason idan ya haifa ‘ya’ya maza su zauna tare da
shi.
Tsawon shekara Uku da auren su amma Ruk’ayya ko b’atan wata bata tab’ayi ba na sosaita
shiga damuwa yayin da mai gidan nata ko ajikin sa dan yasani komai nufi ne na ubangiji,
duk sanda ya ganta cikin damuwa saiya taushe ta kan ta k’ara hak’uri Allah na tare da su.
In tak’aice muku saida sukayi five years da aure sannan ta samu ciki fad’in farin cikin da
suka shiga b’ata lokaci ne, in 9 months time ta haifo d’anta kyakkyawan gaske san kowa
k’in wanda ya rasa, tickets sosai ya siyawa ‘yan Niger da ‘yan Sudan dan zuwa suna.
Ranar suna naira tayi kuka dan kowa yayi k’ok’ari gurin nuna bajintar sa, yaro yaci Nasir
sunan mahaifin Ruk’ayya taji dad’i sosai da karar da yayi mata, bayan suna kowa ya koma
aka barta da wadda zata zauna da ita zuwa arba’in kasancewar haihuwan fari ce.
Nasir nada shekara d’aya ta soma laulayin wani cikin na sosai ta kad’u, yayin da sukaje
asibiti aka shaida musu babu matsala sannan aka rubuta musu madarar daza su na had’a
masa, yanada 1% years aka yaye shi dan cikin ta ya shiga six months.
Bayan 3 months ta sake haifan kyakkyawand’anta aka sanya masa lbrahim sunan mahaifin
sa this time around shima anyi shagali sosai, tunda ga nan kuma sai haihuwan ta tsaya dan
gashi auta lbrahim harya shiga shekara 10 Nasir kuma 11%.
Suna son d’iya mace amma Allah bai basu ba, gashi harsu Nasir sun kusa gama primary
school nasu dan a class d’aya aka had’e su, dan inba fad’a maka akayi ba seka d’au ‘yan
biyu ne.
Suna jss 1 Allah ya bawa Mummy’n su ciki wanda ita kanta batasan dashi ba bar saida ya
shiga five months, lokacin da suka sani kam sosai sukayi farin ciki musamman da akayi
scanning aka gano ‘yan biyu.
Bayan four months ta haifi tagwayen ta kyawawa namiji da mace, tsiran su kwana d’aya
bikin suna ya k’ayatar sosai, inda ranar suna aka sanya musu Sufyan da Sadiya.
Na sosai suke ji da yaran su both dan tasan abu ne mai wuya ta sake haihuwa dan girma
yazo.
Su Nasir na a jss 3 aka sanya su Sufyan makaranta, a lokacin da suka gama secondary nasu
lokacin k’annen su suka gama primary.
Fita dasu Uganda Daddy’n su yayi da ci gaba da karatun su, bayan 4 years suka gama suka
dawo with flying colors results, Nasir Banker lbrahim kuma business man, by the time
kuma Sufyan da Sadiya na SSS 1.
Haka rayuwar ke tafiya cike da jin dad’i da kwanciyar hankali har Allah yasa su Sufyan
sukayi candy lokacin kuma suna da 17 years, Nasir kuma yana 27% lbrahim kuma 26.
Cyprus aka fita da Sufyan dan yin karatun sa, Sadiya kam Daddy’n su ya ce ba yanzu ba sai
dai nan gaba, sam Sufyan baiji dad’in katse musu karatu taren da Daddy yayi ba haka dai
ya hak’ura ya tafi amma kullum cikin waya suke dan yarda suke matuk’ar k’aunar junan su.
Four years ya kammala karatun sa ya dawo a kwararren lauya, alokacin kuma Daddy ya
yarda da cigaban karatun Sadiya amma a Nigeria.
Without hesitation aka gama mata processing komai ta soma karatun ta, Alhamdlillah ta
gama level one nata lafiya a Bayero University, har alokacin kuma bata da lokacin k’awaye
akwai wasu dake mugun shige mata amma sam basa gaban ta dan her only friend is Sufyan
dashi take shawarar komai a rayuwar ta he is her everything.
Wani taima ko da Lubabatu da Aisha sukayi mata yasa ta fara sake musu jiki har suka zama
friend sosai, sam Sufyan baison alak’an ta da su dan haka kawai yake jin strange feeling ba
alkhairi ne su ba a rayuwar ta, duk yadda ya so ganar da ita tak’i fahaimta dole ya kyale ta
dan yana son duk abinda take so.
At Lubabatu and Aisha’s side suna zaune ne kawai da ita dan su cimma mugun nufin su
akanta, lecturers duk sun haukace akanta, samarin makaranta gata ‘yar masu kud’i ga
kwakwalwa wannan abin yasa suka d’au alwashin ruguza farin cikin ta.
Itakam baiwar Allah da zuciya d’aya take zaune da su.
“THE UNFORGETTABLE DAY”_
A gurin wannan family mai albarka, ” Sadiya yaune fa Birthday d’in Lubabatu ” Aisha ta
fad’an danjin mai zatace.
“Oh zatayi celebrating ne ” Sadiya ta tambaya.
“of course yes Babe, so me kike gani zamuyi mata tunda guy nata ya kama guri?”
“As her best friends muyi mata 5 step cake”.
“Oh Gud idea Babe, hope dai za’a barki a gidan? “
“Ai tunda da rana ne ba case”.
“See ai an dad’e da daina yayin party’n rana it’s night party “
“Ya Allah Babe banjin Dad zai barni “.
” No just chill this is the first time da zaki fara zuwa zai barki “
“Allah yasa ” ta fad’a jiki a sanyaye.
Ranar ko zama basuyi a school ba suka fice fara shirye_shirye saida komai ya zama ready
sannan ta dawo gida around 4.
Tayi murna sosai ganin Daddy’n ta yana gida dan haka d’akin sa ta fara nufa saboda
zumud’i ta fad’a masa, sai dai fafur yaki yarda babu yarda batayi ba amma yaki.
Mummy’nta ta samu ta fad’a mata dan haka taje da kanta ta lallab’a sa, ita d’in ma saida
tasha wahala kan ya amince sannan ya kirata ya gindaya mata sharud’a.
Koda ta fad’a Sufyan har fad’a sukayi dan ya nuna rashin amincewar sa and that is the first
time in life suka samu worse misunderstanding.
Duk yadda ya nuna mata b’acin ransa haka tayi biris dashi, gaba d’aya jikin sa ke basa
something bad is about to happened amma sam tak’i sauraran sa duk da itama tanajin
strange feelings.
K’arfe biyar suka tafi gurin make_up inda basu suka dawo ba sai magarib, shigan da sukayi
ya bala’in fitting su Sadiya kaman ka sace ta ka gudu dan kyau.
Sai bayan isha suka tafi gurin birthday d’in with shocked ta tsaya kallon sunan gurin
ROYAL HOTEL’ yau itace a hotel tazo party tun anan jikin ta ya fara sanyi, sai anan taji
dama taji maganan Sufyan gashi Daddy ya jaddada mata dawo wa 10 pm dai_dai..
Haka dai ta daure suka shiga da sauri birthday girl ta tawo welcoming nasu suna wani
shegen murmushi itada Aisha Wanda Sadiya ta kasa gane na mene.
Ciki suka k’arasa daga yadda taga maza da mata na chud’anya hankalin ta ya sake tashi,
dama jiran su ake dan haka nan take aka yanka cake sukayi feeding junan su with so much
adoration.
Drinks aka fara shigowa dasu kala_Kala ana mik’awa kowa, sam Sadiya tak’i karb’a dan
kawai sai taji bata yarda da lemon ba duk da sunce mata champaign ne.
Saida birthday girl ta b’ata rai sannan ta k’arba ba tare da bisimillah ba sukayi cheese kowa
ya kai nasa baki, shanta baifi da minti biyar ba ta fara fita a hayyacin ta.
Ganin haka suka shiga hamdala dan finally hak’an su zai cimma ruwa..
Luuuu ta tafi zata fad’i Lubabatu tayi saurin taro ta zuwa jikin ta yayin da Aisha ta d’auka
wayan ta a hanzarce tayi dialing wani number.
Ringing d’aya ana biyu akayi picking ” Halo Rocky kana ina ne? ” tayi saurin questioning
nasa.
“At your back “juyawa tayi with shocked tana kallon sa, tsantsan yadda ta k’agu ko ringing
nasa bataji ba.
Wata wawuyar ajiyar zuciya suka sauke a tare ita da Lubabatu sannan tayi masa muni da
Sadiya.
Idan ana fad’in first class d’an iska to rocky ya kai, kallo d’aya zaka masa ka tabbatar da ba
k’aramin dan tasha bane saboda yadda ya wani zazzago da wando kamar maijin kashi, ga
wani matsiyacin gyaran gashi kamar kafiri.
Wata shu’umar murmushi ya sake yana lashe lips kaman bak’in maye sannan ya matso ya
d’auke Sadiya chak in a bride_like style, kallon sa Lubabatu tayi tace “kasan yadda zakayi
ka had’iye kwalamar ka kafin mu fara aikin mu”.
“Wai yanzu da gaske bazaku barni in d’and’ani zumar kyakkyawan halittan nan ba? ” ya
marairaice musu fuskan kaman mace.
Aisha da ranta ya fara b’aci ne tace ” ku zauna wannan zancen banzan naku har Allah ya
kawo d’an biyun ta “.
Wucewa yayi suka rufa masa baya har zuwa second floor dake cikin building d’in, room 34
suka nufa dukan su kasancewar key d’in na hannun Aisha tayi saurin bud’e musu suka
kunna kai ciki.
Mayar da k’ofar Lubabatu tayi ta rufe suka wuce bedroom d’in dake cikin had’d’d’en
falour’n, shimfid’e ta yayi akan k’aton Italian bed d’in dake d’akin sannan shima yayi
joining nata yayin da su kuma suka tsaya daga bakin k’ofar d’akin sun saita cameras nasu.
Baiwar Allah ita kam duk wannan abu da ake bata sani ba, haka in a sexy way ya shiga cire
duk wata suttura dake jikin ta har ya za ma babu komai ajikin ta, haka shima ba kunya
babu tsoron Allah ya cire nasa.
Using nata ya shigayi as if suna making love, yarda ya hargitsa mata gashi saika rantse they
are having sex, su kuma tantiran banda hotuna babu abinda sukeyi duk kalan style d’in da
yayi da ita sai sun d’auka.
Saida suka d’au about 50 pics nasu sannan suka hak’ura shima ya mik’e ya mayar da kayan
sa, ‘yar k’aramar paper ya ciro daga aljihun sa ya sanya mata ahannun ta.
Sannan yaja comforter ya lullub’e ta, panties nata da bra Aisha suka d’auke suka tafi suka
barta.
Mummy tunda taga goma saura kwata hankalin ta yayi masifar tashi dan tare Daddy ya
had’a su ya kashe masu warning, tasan definitely idan bata dawo on time ba she is at fault
dan ita ta shawo kansa ya bar zuwa birthday d’in.
Gaba d’aya ta rasa nutsuwar ta inda ta godewa Allah ma Daddy’n nasu baya nan, safa da
marwa take tayi tana sake kiran number’n ta na ba adadi amma still yana ringing ba’a
picking tun anan jikin ta ya fara bata ba lafiya ba.
A wannan mood d’in Sufyan yazo ya same ta koda ta fad’a masa halin da ake ciki sosai
hankalin sa ya tashi dan ya d’au ko dan tana fishi dashi yasa taki picking calls nasa, ashe
ba haka abin yake ba and he knows Daddy’n su akwai hak’uri amma inka tab’o sa ba kyau
ko su maza ma ya suka cika bale ita na mace.
Ficewa kawai yayi ya hau motan sa ya shiga duba duk inda yasan zai same ta, sai dai
sam_sam bata nan har hotel d’in da akayi birthday d’in yaje, wasu suka shaida masa ta tafi
gida dan Daddy’n ta yace karta dad’e, tunda yaji haka hankalin sa ya sake tashi fiye da na
da, jiki babu kwari ya koma gida.
Tun kafin ya zauna Mummy ta taresa da tambayoyi kala_kala, girgiza mata kai ya shiga yi
yana hawaye wane d’an k’aramin yaro.
Tunda taga haka ta sake rikicewa, d’aga kanta tayi ta kalla agogo ko sauke kanta batayi ba
muryan Daddy dasu Nasirya daki kunnen ta, kallo d’aya yayi musu ya gasgata zargin da
zuciyan da take.
Dakyar ta tattaro nutsuwar ta tayi answering sallaman da sukayi, sosai gaban Sufyan ya
shiga dukan uku_uku ganin yadda Daddy ya tsare shi da ido.
“Where is she? ” ya jefawa Mummy tambayan fuska a murtuke babu wasa tattare da shi.
Kame_kame ta somayi yayi saurin katse ta ” Bata dawo ba Eh ko A’ah?”
Bata da option da ya wuce fad’a masa gaskiya, masife ta ya shiga yi kaman Allah ya aiko sa
itakam banda tears ba abinda take, ita bawai masifan dayake mata ne ya dame ta ba halin
da ‘yarta take ciki yafi komai d’aga mata hankali tunda bata sani ba tana lafiya ko kuma
mummunan yanayi.
Haka dai yayi ta fad’an sa babu mai tanka sa, gashi da zaran ya dubi writch watch nasa sai
fad’an ta dawo sabuwa, in tak’aice muku tun suna saka ran dawowar ta harsuka cire,
Mummy kam duk addu’an da tazo bakin ta yi take dan sam abin ya wuce tunanin ta, Sufyan
kam wani zazzafan zazzab’i ne ya rufesa jikin sa banda rawa babu abinda yake.
Kaf d’in su babu wanda ya rintsa Nasir da lbrahim sun riga sun gama budget ting irin dukan
da za suyi mata, kiran Sallah ya sanya su mik’ewa suka fice masallaci Mummy da batajin
dad’in jikin ta alwala kawai tayi ta tada nata a falour’n.
****
Ahankali ta shiga bud’e idanun ta da sukayi mata mugun nauyi, hasken ranan daya shigo ta
window na bugan idon ta runtse su, sai da ta d’au wajen minti biyu sannan ta iya bud’ewa.
D’akin ta shiga k’arewa kallo inda nan take ta shiga matsanan cin tashin hankali, jikinta ta
shiga k’arewa kallo ganin ta naked yasa ta rushe da wata irin masifaffiyar kuka, tuni ta fara
recaling abinda ya faru jiya wanda tunda tasha lemo bata sake sanin inda kanta yake ba.
Jin kaman abu a hannunta tayi saurin d’agowa, nan da nan ta shiga warware takardan dan
ganin me aciki.
THANK YoU VERY MUCH FOR YESTERDAY NIGHT SUNSHINE INDEED IT WAS DAMN COOL
taga ni written boldly a paper’n.
Wani kukan ta sake fashewa da shi, shikenan an b’ata mata future rayuwan ta bashi da
wani amfani kuka take kaman ta cire ranta, ta d’au about two hours tana kuka lokacin
idanun ta Sunyi wani irin kumbura fuskan ta duk ya tashi kaman mara lafiya, hawaye kam
bata san lokacin tsayawar su a idon ta ba dakyar ta samu ta shiga toilet d’in dake d’akin
tayi wanka ta d’aura alwala ta maida kayanta ta sanya ta tada sallah.
Bayan ta idar neman duniya ta yiwa pant and bra nata amma bata gansu ba dan haka tayi
saurin d’aukan side bag nata ta fice, bata sha wahalan samun napep ba amma tana shiga
kukan ta ya tsanan ta dan tuno warning na Daddy, har suka isa gidan bata sani ba saida ya
tafa hannayen sa awurin fuskan ta.
A firgice ta kalle sa sannan ta ciro 1k ta basa ta fice duk kiran da yake mata ta tsaya ta karbi
change nata bata tsaya ba dan haka yaja babur d’in sa ya tafi, gate man naganin ta ya fara
jera hamdala sai dai yanda ya ganta a firgice ya bashi tsoro sosai, yau ko gaida sa bata
tsayayi ba ta shige gida, tana k’ok’arin shiga main falour kunnen ta yayi mummunan ji.
Kaman an hankad’a ta tafad’a falour’n ta zube gaban Daddy tana wani irin kuka nishin ta
har sama_sama yakeyi, hak’uri take so ta basa amma dan yarda kuka yaci k’arfin ta ko
magana ta kasa yi.
Kallon agogo yayi yaga 8 murmushin tskaici ya sake, wato ta fita 8 ta dawo 8 ” where the
hell are you coming from? ” ya fad’a da kakkausar murya.
Shiru tayi not ready to talk sai ma volume na kukanta da ya k’aru, ” I said where the hell are
you coming from “ya fad’a a tsawace, ba ita kad’ai ba kaf mutan falour’n sai da suka
tsorata da tsawar.
Cikin tsananin tashin hankali da tsoro ta bud’e baki zatayi magana, nock d’in da suka jiyo a
k’ofa ne ya sanya ta had’iye maganan ta.
Nasir ne yaje inda ya tarar da gateman rik’e da leda a hannunsa, ” yauwa ungo wannan
Alhaji aka kawo wa ” karb’a yayi without uttering any word ya juya ciki.
A nitse ya k’araso ya mik’awa Daddy ledan d’ago da rinannun idanun ta tayi ta kalla ledan
“ROYAL HOTEL’ data gani ajiki ne ya k’ara sanyata cikin tsananin tashin hankali.
Ahankali ya karb’a sannan ya soma bud’ewa paper’n daya soma gani ya d’auko ya warware
ya fara karantawa.
Halo babe I know you are on fire yesterday night that’s why you forget your pant and bra,
gasu nanI return it back sannan akwai album namu ciki I know you will love it
Tun kafin ya ida karantawa yakeji wane ya shak’e ta ya huta, album d’in ya bud’e inda yayi
mummunan gani runtse idanun sa yayi cikin tsananin bak’in ciki da b’acin rai sannan ya
ware su akanta, ita kuwa tun lokacin da paper’n ya sub’uce a hannun sa tayi saurin kai
duban ta kai inda itama take taji kaman ta shak’e kanta ta mutu.
Saukan wasu azababbun maruka taji wanda take hab’o ya b’alle mata gefen bakin ta ma ya
soma zubar da jini.
Me nayi miki kika zab’i ki tozarta ni ki b’atan sunan? Me na rage ki dashi kika zab’i jefa
rayuwar ki mummunan rayuwa? Menayi miki? Me nayi miki? ” ya fad’a yana hawaye sosai.
Girgiza kai ta somayi amma sam ta kasa magana, ” just answer me ” ya buga mata wata
razananniyar tsawa.
“Daddy wallahi sharri akayi min, Mummy dan Allah ki fad’a masa b’atamin suna zasuyi… “
tass_tass kakeji ya sake kife ta da wasu mahaukatan marukan da saida ta kifa dan azaba,
rufe ta yayi da duka dan gani yake ta ma raina masa wayo tunda itace ajikin hotunan, tun
tana ihu harta daina ganin yana neman kashe ta Mummy tayi saurin k’arasowa dan hana
sa.
“Hajiya Ruk’ayya idan kika kuskura kika k’araso ko kikayi magana a bakin auren ki, ki barni
in kashe wannan karuwar kafin ni ta kashe ni ” tajiyo amon muryar sa.
Chak ta tsaya kalmar karuwa na amsa kuwwa a kunnen ta, hotunan ya Watson mata a
fuska inda ta durk’usa ahankali ta d’auka ” innah lillahi wa’innah ilaihir raji’un ” ta shiga
nanatawa not believing abinda idanun ta ke gani.
“Ki bud’e kunnen ki kiji ko kece ‘ya d’aya dana haifa na yafe ki, ki tashi ki fice min a gida
kafin na kashe ki, kuma wallahi kika k’ara minti goma baki fita ba zakiga abinda zan miki
yar iska kawai Allah ya tsi ” bata bari ya k’arasa ba tayi saurin katse sa ta hanyar rik’e
masa k’afa k’am_k’am
” Dan Allah Daddy karka ce haka na tuba, wallahi Daddy ko nan da gate na yarda bazan
sake zuwa ba dan Allah kamin rai idan ka kore ni bansan ya zanyi ba, bani da kowa sai ku
Mummy dan Allah ki basa hak’uri wallahi bansan komai ba, ban tab’a kusantar zina ba
balle aikatawa idan baku yarda dani ba ku iyayena waye zai yarda dani, Daddy believe me
wallahi it’s all set up anyi ne dan ayi ruining future d’ina..”
Wani wawan ball da yayi da itane ya sa ta kasak’arasa maganan da take, wani mummunan
bigewa kanta yayi da center table, glass cup d’in dake kai ya fad’o ya tarwatse mata a fuska
tsananin azaba ya sa ta kusa shid’ewa, ji tayi kaman kanta zai rabe biyu tayi saurin dafewa
tana kwance amma jiri take ji gaba d’aya falour’n juya mata yayi up side down.
Runtse ido Sufyan yayi kansa na wani irin sarawa he just can’t watch her suffering like this,
duk halin da take ciki bai hanata jan jiki ta nufi Ya Nasir da lbrahim ba.
Sukam banda kallon tsana babu abinda suke jifan ta da shi don tuni idon su ya rufe da
b’acin rai, da dashash shiyar muryan ta tace ” nasan ku yayuna ne masu sona dan Allah
kuyi wa Daddy bayani ba halina bane, ku bashi hak’uri ya saurare ni…
Saukan belt d’in da taji ne yasa ta had’iye maganar ta kallo d’aya in kayi wa fuskanta baza
ka so ka sake ba dan yadda take yoyon jini, rufeta da duka sukayi both wane zasu kashe ta
yayin da Daddy ke gefe yana ta sa musu albarka.
Mummy kam tun sautin kukan ta na fita har ya daina, Sufyan ganin idan baiyi wani abu ba
zasu iya kashe ta yasa ya mik’e yana had’a k’afa ya k’araso inda suke.
Janyo ta yayi ya rungume k’am_k’am ajikin sa ya runtse idanu dan bayajin akwai wanda ya
isa ya hanasa taimakon ta a lokacin.
“Sufyan ka kauce su halaka min yarinyar nan kafin ranka ya b’aci ” Daddy yayi maganan a
tsawace
Girgiza kai ya shigayi sai hawaye sharkaf_sharkaf danjin yadda ta k’ank’ame sa, ko
numfashi a wahalance take sauke wa, ” bazan iya ba Daddy I can’tjust watch her suffering
this much, koma me zasuyi mata su mana tare nasan k’azafi ne za’ayi mata bara ta iya
aikata abinda ake zargin ta ba, ya kamata Daddy kayi bincike kafin ka yanke mata hukuncin
da za’a zo ana dana sani.. “
Tasss tasss Nasir ya d’auke sa da mari ” rashin kunya zaka yiwa Mutane Sufyan? Duk nan
wurin wa ka riga zuwa duniya?”
Yana k’ok’arin magana Mummy tayi saurin taresa ” not a word Sufyan kar abinda tayi ya
shafe ka, rashin kunya ba halin ka ne bajust keep quite ” ganin yadda Mummy’n tasu ke
kuka ya sanya sa yin shiru.
“Kun gama? ” Daddy ya jefo musu tambayan, shiru sukayi duka ba wanda ya tanka, ” Nace
kun gama?” ya sake nanata tambayan a tsawace.
Still ba respond dan haka ya kalli Nasir da lbrahim yace ” tunda haka yace kuma ba wuce
dukan yayi ba ku ci mun ubansu duka ” nan take suka bi umarnin sa suka shiga dukan su
bak’ak’k’autawa duk yanda yaso tare ta kar dukan ta same ta abin ya faskara.
Haka nan yayun nasu sukai ta dukan su saida suka gaji dan kansu suka kyale su, gaba d’aya
Sufyan ya galabaita ko yar yatsar sa baya iya d’agawa ita kuwa tuni idanun ta suka
k’ak’k’afe numfashin ta ya d’auke.
Jin yanzu baya jin nishin ta yayi saurin d’agota abinda ya iya fahimta kawai sumammiyar
jikin ta hankali a matuk’ar tashe ya shiga tapping kumatun ta amma ina sam hakan tak’i
working, mik’ewa yayi a wahalance zai nufi dispenser ya jiyo muryan Daddy na kashe masa
warning” don’t you dare touch it Sufyan idan kuma ka tab’a Allah ya isa ban yafe maka ba
Jiki ba kwari ya dawo ya cigaba da trying lock tasa amma a banza, ” kafin na irga biyar
karuwar nan ta bar min gida idan ba haka ba zan kira polisawa su wulak’anta min ita”
Daddy yayi stating in serious note.
Dakyar Sufyan ya samu ya mik’ar da ita ya sak’ala hannun ta a kafad’an sa
sannan ya shiga takawa yana nishi da kyar dan yadda jikin sa ke kakkarwa.
Kuma dukan kun nan duk wanda ya taimaka mata ban yafe masa ba ” yayi maganan yana
jiran yaga Sufyan ya yasar da ita amma ko ajikin sa, daman ya sani koda tsinuwa yayi
Sufyan bajin sa zaiyi ba dan haka yayi shiru.
Mik’ewa Mummy tayi zata bisu ” wallahi Hajiya Ruk’ayya kin daiji na rantse ko taku d’aya
kika k’ara a bakin auren ki ” chak ta tsaya kaman an dasa ta.
Saida suka zo fita daga falour’n Sufyan ya jiyo yana kallon Mummy’n su dake tsananin
kuka, one more look ya yiwa Daddy da yayun su sannan yasa kai suka fice.
Direct motan sa ya wuce ya sanya ta agidan baya, ragowan ruwa ya hango yayi saurin
d’auko wa ya shiga yayyafa mata, ba batare da b’ata lokaci ba taja wani dogon ajiyan
zuciya, da sauri ta dafe kanta dake barazanar tarwatsewa ganin haka ya sa shi rufe Motan,
ya nufi site d’in sa bedroom nasa ya wuce ya fiddo da wata jaka sannan ya bud’e drawer
nasa ya kwashe kaf kud’in dake ciki ya zuba a jakar ya rufe, fitowa yayi ya rufe site d’in nasa
ya wuce mota ya shiga ya tada dakyar.
Wangale musu gate gateman yayi suka fice,kai tsaye “Ni’ima Hotel” ya wuce da su muna
iya cewa ikon Allah ne kawai ta kaisu.
D’aki ya kama su ya shiga da ita ya kwantar a k’aton royal bed d’in dake d’akin sanna ya
ciro wayan sa ya kira family doctor’n su ya shaida masa inda suke.
Bai wani jima ba yazo ya duba ta ya sanya mata drip yayi mata alluran bacci, Magungunan
da zata buk’ata ya rubuta masa sannan shima ya rubuta masa wanda zai buk’ata.
Kasancewar two bedroom ne da d’akin daya kama ya wuce d’ayan ya nufi toilet ya had’a
warm wata yayi warming kansa, sannan ya kwanta shima wahalallen bacci ya d’auke sa.
Sai around 3 ya tashi yana d’anjin sauk’i ajikin sa toilet ya nufa ya d’auro alwala ya fito ya
tada sallah bai tashi ba har saida ya gabatar da sallan la’ asar, na sosai yayiwa ‘yar uwar sa
addu’a kan Allah ya bayyana gaskiyan lamari.
Bayan ya gama ya nufi nata d’akin inda ya tarar ta tashi sai kuka take tsantsan yadda ta
galabaita yasa sautin kukan bata fita, da sauri ya k’araso ya cire mata drip d’in sannan ya
shiga calming nata.
Saida ya samu tayi shiru ya nufa toilet ya had’a mata warm water, ganin jiri na neman kayar
da ita yayi saurin rik’ota ya rakata k’ofar toilet ya dawo.
Receptionist ya k’ira ya musu order’n abinci, kafin ta fito aka kawo ya zauna jiran ta, ita
kam a toilet tsantsan azaba ya hanata wanke fuskanta dan ji take wane jajageggen
attaruhu take sawa.
Dakyar ta samu ta wanke crying like never before ta d’auro alwala ta fito, kayan da ta cire ta
miyar sannan ta biya sallolin ta, addu’a tayi sosai kan Allah ya bayyana gaskiyan lamari.
Had’a kai da gwiwa tayi tana cigaba da sana’ar tata ta kuka, dan kuka wane idanun zasu
zazzago ga wani irin zugi da rad’ad’i da suke mata.
Harya shigo bata sani ba saida ya k’araso ya dafa ta sannan ta d’ago tana ganin sa
dishi_dishi.
” Daddy ya kore ni daga gidan sa ko? ” tayi questioning nasa da dashash shiyar murya.
Ganin he is not willing to talk tace ” kafad’a min ya kore ni ko? Ya yarda ni karuwa ce ko?
Mummy ma ta yarda ko? Ya Nasir da lbrahim ma su yarda ko? ” ta k’arasa maganan
unstoppable tears nata na dad’uwa.
Janyota jikin sa yayi ya rungume so tight shima ya shiga taya ta kukan, ” ka tashi ka tafi ka
barni nasan kaima ka yarda ni karuwar ce”.
D’agota yayi yana kallon ta yayin da ita kuma ta sunkuyar da kanta k’asa, ” Sisi please
inason ki fad’amun gaskiyan abinda ta faru”.
Babu k’arya a tsakanin su balle b’oye_b’oye dan haka ta fayyace mar duk abinda ya faru.
“Sisi ba kya tunanin Aishan can da Lubabatu suka had’a komai
“No Bro ltrust them nasan ko wani ma bara suyi masa ba balle ni, nafi tunanin wani ne ya
min amma basu ba “.
Kallon ta kawai ya tsayayi yadda ta d’au yarda ta azawa wannan fand’ararrun k’awayen
nata, shikam yayi imanin they are behind it.
Mik’ar da ita yayi suka nufa falour, abincin da ya musu order ya d’auko take ko b’oyayyiyar
yunwarta ta taso gashi kuma batajin zata iya ci.
Dakyar ya samu taci kad’an tasha maganin ta sannan shima yaci ya sha maganin sa,
mik’ewa yayi zai fita tayi saurin rik’o hannun sa ” Bro kai ma tafiya zakayi ka barni? Kaima
ka yarda ni karuwace? Dan Allah ka tausayamin bani da kowa sai kai idan ka guje ni bansan
ya zanyi ba, bansan ya rayuwa na zata kasance ba dan Allah bro ka zauna dani at least
ciwon da zuciya na take zata ragu in ina ganin ka by my side, just stand by me and protect
me from any harm ” tayi stating crying so hard.
Juyowa yayi ya tsuguna ya rik’o hannunta ya had’a da nasa ya fara magana a nitse “I
promise no matter what ina tare dake, no matter how the dificulty it takes I will stand by
your side and protect you, just knowl will always be there for you, we are in this together
will be a shoulder for you to cry, ki daina kukan haka nan yana hurting d’ina and am not
leaving you zanje na siyo miki kaya, I will be right back ” ya k’arasa yana wiping mata
unstoppable tears nata.
With nod ta answer sa ya tashi ya tafi, country mall ya nufa ya mata siyayya kaman ba gobe,
daga nan ya wuce kwari shagon Sammanin Fatihu ya siyo mata had’ad’d’un supers da
materials ya wuce gurin tailor nata dake nan a Zoo road ya basa d’inkin da kud’in ya kuma
bak’ace sa daya d’inka ASAP.
On his way back ya tsaya a wata down town ya mata ordering pizza da shawarma da ice
cream dan favourites nata ne.
Koda ya dawo sana’an tata takeyi dan haka ya ajiye abinda ya shigo dashi ya nufe ta da
sauri, aikin rarrashin ta ya soma har ya samu ta tsagita da kukan.
Hannun su ya had’e guri d’aya yace ” inhar kina son mu shirya ki daina kukan haka nan,
idan ba haka ba nima zanyi tafiya ta na barki haba mana so nawa kike son na fad’a miki
yadda kukan nan naki ke k’ona min zuciya, ko kinason na tafi nima?”
Girgiza kanta ta shiga yi sosai tana share hawayen

nata, Murmusawa yayi yace ” tohm am

not leaving you amma sai kinyi min alk’awarin daina kukan”
Shiru tayi not ready to talk ganin haka yasa sa yunk’urin tashi ” tunda bazaki min promise
d’in ba I think gwara na tafi”
“I promise please don’t go ” ta fad’a tana shirin sanya sabon kuka.
“Okay am not going bari naje nayi sallah na dawo, kema kiyi kinji? “
With nod ta answer sa ya fice sannan ta nufa d’akin ta tayi wanka dan taji dad’in jikinta tayi
sallah..

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]