[Advertisements⬇️]

SOYAYYAH CHAPTER 4 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

SOYAYYAH


CHAPTER 4
Haka ya k’araci surutan sa ya mik’e ya nufa toilet yana shiga ya sakarwa kansa shower.
Ya Sadeeyq da wani mugun speed yake driving ikon Allah ne kawai ya kai su lafiya, already
dama Mamy ta k’ira doctor’n su dan haka without hesitation aka nufa emergency ward da
ita.
Sosai doctor’n ya shiga treating nata inda batare da b’ata lokaci ba ya gano karaya a
hannun ta na dama, wayyo karkuso kuji yadda ihun Safwah

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ya karad’e asibitin duk wani

mai imani yaji saiya tausaya mata.
Bayan like 2 hours aka fito da ita zuwa d’akin hutu bacci take helplessly wanda zai shaida
ma d’ankaren wahalan data sha.
Ya Sadeeyq da Mamy doctor ya nemi gani inda ya shaida musu karayan, ta kad’u iya
kad’uwa dajin aika_aikan da Suwayd yayi kallo d’aya zaka mata ka hangu matsananciyar
b’acin rai, ganin yadda ranta ya b’aci yasa Sadeeyq ya fara tausan ta duk da shima daurewa
kawai yake.
Umarni doctor’n ya musu dasu je suga condition nata, batare da b’ata lokaci ba suka fice
daga office d’in nasa zuwa d’akin da aka kaita.
Ahankali Mamy ta k’arisa tajowo kujera ta zauna ta site d’in Safwah na hagu taja hannun
ahankali tana shafawa tsantsan so da tausayin ta ne suka mamaye mata zuciya.
You most pay for this Suwayd ” shine kawai kalamun data iyayi.
Girgiza mata kai Ya Sadeeyq yayi yace ” please Mamy don’t say such words, ko bakomai ai
Suwayd yayan tane mene aciki dan ta masa laifi ya hukun tata I see no reason da zakice
haka, Allah ya k’addara hakan zata faru koda bata sanadin lil bro ba so sai muce Allah kare
aukuwan na gaba… “
Ringing d’in wayan Mamy ne ya katse masa kalamun nasa, Mummy shine tayi appearinga
screen d’in.
Without hesitation ta d’auka ” Assalamu Alaikum ” aka fad’a a d’ayan side d’in.
“Wa’alaikumus Salam ” Mamy ta amsa a nitse wanting to hide her problems.
” Mammy bamu room numban da Safwah take, gamu duka Mun k’ariso”.
Kallon Sadeeyq Mammy tayi tace yaje ya shigo dasu Mummy, with nod ya amsa ta ya fice.
A reception ya iske ilahirin Alhaji Muhammad lbrahim Agadez family members ko wannen
su d’auke da d’umbin damuwa Suwayd ne kawai babu aciki directing nasu yayi zuwa
d’akin.
Da sallama suka shiga d’agowa Mammy tayi tana kallon su d’aya bayan d’aya totally out of
word dan ganin babu Suwayd.
“Lallai dole ta dage da addu’a dan tana tantama in babu shafan aljanu ajikin sa, amma ta
yane zaiwa yarinya irin wannan aika_aikar ya kasa zuwa duban ta tabbas he must pay for
all what he has been doing ta k’arashe kalamun zucin nata sannan ta shiga welcoming su
Granny.
Ana kiran sallan magrib Safwah ta farka, a time d’in harsu Granny sun tafi kasantuwar
hospital d’in basa son tara mutane.
Tunda ta farka ta gaza furta ko wani kalma dan yadda hannun ta ke tsananin zugi da ido
kawai take bin Mammy dake sallah.
Tana k’aunar Mammy har cikin ranta, yayin da kuma gobaran tsanan d’anta ke sake ruruwa
a zuciyan ta, wasu irin zafafan hawaye ne suka zubo mata sakamakon wani irin sharpP pain
da yayi hitting nata.
Tun tana daurewa har ta gaza ta fashe da wani irin masifaffen kuka, wanda hakan ya sanya
Mammy saurin idar da sallan ta ko addu’a bata samu tayi ba.
Na sosai ta tausayawa Safwah dan ganin yadda take murza kanta kan pillow’n da take,
d’ayan hannun ta kuma sai yarfa shi take hakan ne zai tabbatar maka ba k’aramin azaba
takeji ba.
K’arasawa tayi jikin gadon ta zauna sannan ta jawo kan Safwah ta d’aura akan cinyar ta
sannan ta shiga aikin rarrashi which dakyar ta samu ta shawo kanta tayi shiru.
“Where is my Ummy? I really want to see her Mammy call her for me ” ta fad’a da muryan
kuka.
” Am sorry Baby sunzo kina bacci ki bari gobe zata zo ” Mammy ta fad’a da muryan rarrashi.
” No Mammy am dying please call her right now, jikina na bani bazan kai go..”
Da sauri Mammy ta taushe mata baki tana girgiza mata kai ” No Baby cuta ai ba mutuwa
bane stop saying such word ” Mammy ta fad’a a d’an kid’ime dan seta ke gani kaman
abinda Safwah ke fad’a ne zai faru.
Sayyid daya shigo ne yasa su kallon k’ofan atare, murmushin k’arfin hali ya sakar wa
Safwah sannan ya K’araso ciki, har k’asa ya duk’a ya gaida Mamy sannan ya ajiye ledojin
daya shigo dasu a gefe.
Ringing wayan Mammy ne yasa Sayyid kai duban sa kan dadduman da ta tashi, Sweetheart
shine sunan da tayi appearing a screen d’in murmusawa yayi dan yasan Abbah ke k’ira
sannan ya d’auko ya mik’a mata.
Kwantar da Safwah tayi sannan ta fita a d’akin, Sayyid mai jiran k’iris tana fita yayi
replacing position nata.
K’in kallon sa Safwah tayi ta juyar da kanta d’ayan side d’in, juyin duniya amma tak’i
juyowa sai kuka take hakan kuma ba k’aramin tada masa hankali yake ba.
Kaman zaiyi kuka ya shiga rok’on ta inda ta sake fashe wa da wani matsanancin kula.
Ahankali ya d’ago kanta daga kan pillow’n ya aza akan cinyar sa sannan ya fara magana
ahankali.
” Love is always patient and kind. It is never jealous. Love is never boastful or conceited. It
is never rude or selfish. It does not take offence and is not resentful. Love takes no pleasure
in other people’s sins, but delights in the truth. It is always ready to excuse, to trust, to
hope, and to endure whatever comes, Safwah my heart only beats for you, about such
words you said to Mammy earlier bana so in k’araji ko kin manta promise namu sai munyi
aure mun haifi princess mai kama dake munyi rising nata sannan mutuwan zai d’auke mua
tare, ko kin manta da promise namu na living together till death, please Baby ki dena irin
maganan nan banso”.
Tunda ya fara magana take kallon sa with so much adoration duk da kasancewar bata san
mene so ba amma tasan irin matsanancin son da Ya Sayyid yake mata, itama kuma tana
sonsa don batajin zata iya rayuwa idan babu shi.
Suwayd zaune a reception ya had’a kai da gwiwa yana tunanin hanyan da zaibi yaga halin
da Safwah take ciki, dan yasan ko sama da k’asa zasu had’e Mammy bara ta barsa ya shiga
ba.
Gashi ya riga yayi promising kansa no matter how difficult it takes sai yaga Safwah.
Kaman an mintsine shi ya d’ago inda yayi kyakkyawan gani dan a lokacin ne Mammyta
fita.
Jikin sa har rawa yake saboda tsananin farin ciki, batare da b’ata lokaci ba ya nufi d’akin
sannan ya rik’e handle d’in ahankali ya tura.
Abinda kunnen sa ya jiye masa ne ya hanasa k’arasawa ciki, tuni zuciyan sa ya shiga wani
irin suya yayin da wani bala’in kishi ya tokare shi.
Tuni numfashin sa ya shiga kai komo, “I Love you so much Ya Sayyid, When I tell you “I
love you” I don’t say it out of habit or to make conversation. I say it to remind you that
you’re the best thing that has ever happened to me and insha Allah our dream will come
true dearie na”.
” lyeeee ashe haka Baby na take lover girl ” Sayyid ya fad’a cike da neman tsokana.
Rufe idanun ta tayi cike da kunya sannan ta turo masa d’an k’aramin bakin ta tace ” Allah
bana so “
Dariya suka sake cike da burgewa, ” BAMMMMMM!!! ” sukaji anyi banging k’ofa da
k’arfi…
Na sosai Sayyid yayi mamakin wannan al_amari and duk yadda yaso gano waye ya kasa
dan haka kawai ya basar ya cigaba da making precious nasa happy har bacci yayi taken
over nata.
Yana cikin kallon beautiful face nata yana admiring kyawun ta Mamy tayi sallama ta shigo.
” Damn it ” ya fad’a ahankali dan yasan finally yanzu Mamy zata kora sa and truly baya son
yayi missing ta.
Katse masa zancen zucin nasa tayi ta hanyan make sa a k’eya.
“Awchh Mamy it hurts ” ya fad’a wane mai shirin yin kuka.
“I know tunanin me kakeyi ” tayi questioning nasa tana tsare sa da firgitattun idanun ta.
Sosa k’eya ya farayi yana kame_kame, Murmusawa tayi tace ” I’ave got you tashi ka tafi
gida”
Marairaice mata yayi yace ” please Mamy let me stay with you guys “.
” No it can’t be possible tashi ka tafi dare na k’arayi and not a word again “
Wane zaiyi kuka haka ya miyar da kan Safwah kan pillow yayi pecking forehead nata yama
Mamy sallama ya tafi, koda yazo fita handle din k’ofar ya rik’e yak’i fita idon sa kyam akan
Safwah.
Gyaran Muryan da Mamy tayi ne yasa sa juyawa ya fita ya rufe musu k’ofan ahankali
Ab’angaren Suwayd lokacin da yayi banging k’ofar ya juya ko gaban sa baya gani, dan
yadda zuciyan sa ke masa k’una fuskan sa yayi wani mugun ja yayin da jijiyoyin kansa suka
mimmik’e, wani irin numfashi yake fitarwa wane mayuwan wacin zaki.
Sai yau ya tabbatar da kuka rahama ne dan yadda yake so yayi amma tears sun k’auracewa
idanun sa.
Wanne wane irin MAKAHON SO ne tabbas so baiyi musu adalci ba if not ya za’ace at the
same time shida d’an uwan sa, Aminin sa sunyi falling ma k’anwar su and kowannen su
bazai iya rayuwa babu ita ba wanne wace irin K’addara ce, yana son Safwah yana k’aunar ta
and he is ready to die for her hundred times if needed he can’t just imagine his life without
her, zai iyayin komai akanta in fact koda kisan kai ne inta kama he promise no matter what
saiya mallake ta saboda dashi ta dace not Sayyid.
IPhone 7+s nasa ya ciro yayi dialing wani number without hesitation aka d’auka.
” Halo Maza yane? ” aka fad’a daga d’ayan side d’in.
” Kana ta ina? ” Suwayd ya ansa shi in return da wata irin murya.
Tun anan ya gane ba lafiya ba and yasan k’arshen zancen bazai wuce Safwah ba dan haka
batare da b’ata lokaci ba ya sanar masa.
Kwatance inda yake ya masa dan haka in less than 15 minutes yazo kasancewar he is
nearby ya d’auke shi suka tafi, Basu zame ko ina ba sai BAR.
Suna isa suka had’e da clique nasu aka shiga shan wine kaman ba gobe, bashi ya tafi gida
ba sai 12:00 am zuwa lokacin ya dawo normal duk problems nasa have solve.
Sosai gate man nasu yayi mamaki dan tunda yake dasu iyakan su 9:00 pm a waje amma
yau Suwayd har 12:00, sannu da zuwa yayi masa sannan ya basa hanya ya wuce.
Hankalin Haidar da Sayyid ba k’aramin tashi yayi ba gani Suwayd bai dawo ba gashi bai
sanar dasu inda zasa ba, wayansa kuma na ringing amma ba’a picking.
Suna wannan halin sukaji sallaman sa a tare suka mik’e suka shiga throwing masa
questions, kona kansu baiyi ba ya shige toilet.
Haka suka zauna zamanjiran sa, koda ya Fito still ko d’aga kai baiyi ya kalle su ba yayi
shirin sa na bacci ya haura gadon nasu yayi kwanciyar sa.
The both of them where totally out of word haka nan suma suka nemi guri suka kwanta
kowane da tambayan dake masa yawo a mind.
Saida ya tabbatar a beautiful sleep take over them sannan ya tashi ahankali yadda bazai
tada su ba ya nufi wadrop nasa.
Diary nasa ya d’auko yayi rubutu aciki sannan ya mayar, komawa yayi gurinsa ahankali
without noticeable sound ya shiga k’arewa ‘yan uwan nasa kallo, right hand nasa yayi
placing ma Haidar aka ahankali sannan ya fara magana da voice nasa da bai gama dawo
wa dai dai ba.
” Forgive me for what happened earlier d’an uwa”.
Hannayen su ya had’e guri d’aya sannan shima bacci yayi gaba da shi.
The following day
Kowa ya gama hallara a dinning, tun shigowan Suwayd yayi noticing wasu pathetic looks
da Abbah ke mar sending
Ya ilahi what if Abbah knows I stay late at night? Ohhhh my geee I know am dead “
“K’araso mana babana ” maganan Abu ya tsamo sa daga zancen zucin da yake.
A sanyaye yaja jiki ya k’arasa yaja empty chair nasa ya zauna, gaishe da iyayen nasu yayi
suka amsa yayin da Abbah ko kallo bai ishe shi ba yace da ‘yan uwansa da sauran yaran”
let’s eat”
Umarnin sa suka bi kowa ya shiga cin abincin sa cikin kwanciyar hankali, illah Suwayd dake
cike da fargaba.
“Son I’ave been noticing you tunda ka zauna ka kasa cin abinci sai tunani, what’s wrong
with you?” Ummy tayi questioning nasa cike da kulawa.

Kafin ya kai ga amsa ta ya tsinkayi muryan Abbah ” Hajiya Safiyyah kici abincin ki kawai,
idan bazai ci ba ya tashi ya bamu guri “.
Abu ne ya karb’i zancen ” A’ah baza ayi haka ba mu farajin damuwar sa tukunna, babana
meya faru?”
” Babu komai Abu ” ya amsa calmly.
Itadai Granny ido kawai take binsu dashi, Daddy ne ya kalli Suwayd yace ” babana inason
ganin ka after the meal
Dum_dum k’irjin sa yabada dakyar ya nemo courage yace ” tohm Daddy”.
Saboda zullumi gaba d’aya ma ya rasa appetite nasa, tissue yaja ya goge bakin sa ya mik’e.
“Ka k’oshi ne? ” Mummy ta jeho mar tambayar.
Namma kafin ya amsata Abbah ya katse sa ” wai dan Allah ku kyale shi mana kada Allah
yasa yaci, yaro ne shi daza a lallab’a cikin shi ko namu? “
Daga haka ba wanda ya k’ara magana har suka k’are breakfast nasu.
Duk yadda ‘yan matan suka so sake zuwa duba ‘yar uwarsu Abu yak’i yace dole sai sun tafi
school dan haka suka yi sallama da iyayen su driver’n su ya wuce dasu school, Sayyid da
Haidar ba yadda basuyi da Abu ba amma yace sai sunje school
Granny, Abbah, Abu da Daddy zaune a babban falour sai innocent Suwayd zaune a k’asa da
ya sunkuyar da kansa k’asa yana wasa da kyawawan ‘yan yatsun sa kaman mutumin kirki
kana iya rantsewa bashi ne monster d’innan ba.
“Babana ina kaje jiya? ” Abu ya jefo mar tambayan a nitse.
Shiru yayi not ready to talk hakan kuma sosai ya sake k’ufular da Abbah.
” Dan uban ka bada kai ake magana ba ” Abbah yayi maganan a tsawace.
Da sauri ya d’ago dan ya fuskanci ba k’aramin b’acin rai ya sanya mahaifin nasa ba.
“Abu dan girman Allah kuyi hak’uri ” yayi apologizing nasu.
” We are not here for your sorry save it, what we want to know is ina kaje ” fad’in Daddy.
Shiru ya sakeyi a karo na biyu dan he he don’t have nothing to say, fad’a Abbah ya rufe sa
dashi na sosai the thing he hate most in life, dakyar su Abu suka shawo kansa yayi shiru but
saida ya kashe masa warning.
“Ka tashi ka b’ace mana da gani mutunin banza mutumin wofi kawai ” Abbah ya fad’a one
more, rai a b’ace ya mik’e ya fice yanaji wane ya fashe da kuka dan takaici.
Gyaran murya Granny tayi sannan ta farayi musu nasiha ta kuma yi musu umarnin da a
dawo da Safwah ayi jinyan ta a gida.
Godiya sukayi mata then Abbah yace da k’annen nasa su tafi aikin su shi zaije asibitin, da
haka suka watse inda Abbah ya karb’i abincin su Mamy ya wuce asibitin.
Isan Abbah ya tarar da Mamy nawa Safwah susan kai da murmushi kwance a fuskan sa yayi
musu sallama ya shiga.
Gaishe sa Mamy tayi ya amsa, then Safwah amsawa yayi sannan ya mata ya jiki, amsawa
tayi a kunyace ita batasan meyasa ba duk cikin iyayen nasu bataji kunyan kowa sai Abbah.
Murmusawa Abbah yayi ya k’araso ya zauna a gefen ta na hagu ji take kaman ta nitse dan
tsanin kunya, ” Mamy taya ni gani wai ni da daughter na amma ban isa na mata magana ba
sai ta haujin kunya “.
Dariya Mamy tayi tace ” ai Safwah badai shiririta ba”
Covering eyes nata tayi da d’ayan hannun nata, jan hancin ta yayi yace dasu zaije ayi
discharging nata kaman yadda Granny ta buk’ata.
Safwah wane an tsunduma ta a aljannah dan sam batason zaman nan na asibiti tafiso gata
ga Ummy’n ta.
Abbah na fita Mamy ta had’a masu kayan su, tare da Dr’n suka dawo ya sake dubata ya
mata tambayoyi ta amsa sannan ya sallame su.
Mamy sai tsokanan ta takeyi dan ganin yadda take ta murna saida suka biya Abbah ya mata
shopping sannan suka wuce gida.
Duk yadda Mamy taso Granny tabar mata jinyar Safwah tak’i dole ta hak’ura zata na zuwa
duba ta all the time Ummy kam kunya ma bai barta tayi magana ba.
Later During the.
Safwah zaune ita kad’ai a falour’n Granny, k’ishirwa take ji sosai gashi she is far away from
the fridge duk yadda taso tashi ta kasa dole ta zauna jiran ko Allah zai kawo mai taimakon
ta.
Bada dad’ewa ba Suwayd ya shigo, gaban ta ne yayi wani mummunan fad’i bashi taso Allah
ya turo mata ba dan ko zata mutu bazai tai maka mata ba amma k’ishirwan da takeji bazai
barta ba dole ta nemi favor nasa ko zai wulak’anta ta inhar zai bata.
” Ke ina Granny ” ya fad’a fuska a d’aure.
Da d’ayan hannunta tayi mar pointing, ” Are you deaf? ” ya buga mata tsawan da saida yasa
fitsari ya tawo mata.
” Tana daki ” ta fad’a in between tears.
” Toh uban me kuma nayi miki? ” yayi questioning nata.
“Nothing” ta fad’a da saurin ta,” Ya Suwayd dan Allah ka taimaka min da ruwa” ta fad’a
abin tausayi.
K’are mata kallo ya shigayi yayin da tears nata ke tab’amar zuciya, amma yayi kaman baiji
ta ba har saida ta maimaita.
Fridge ya nufa instead of ya bud’a k’asa saiya bud’a saman freezer, goran ruwa mai
kank’ara ya d’auko da gangan despite of knowing Safwah is not fan of ruwan sanyi.
Itakam binsa da kallo kawai take tasan za’a rina, glass cup ya d’auko sannan ya dawo
giving distance between them, bud’ewa yayi ya tsiyaya sannan ya mik’a mata yadda ko za’a
kashe ta hannun ta bazai kawo ba gashi duk yadda taso moving body nata ta kasa.
“Ke fa nake jira ki karb’a kinsan banda lokacin b’atawa musamman akan shashashu irin ku
“ya fada yana sending mata glares.
” Na had’a ka da girman Allah Ya Suwayd ka matso kamin nitsa ” tayi manganan now crying
so hard.
Inda tasan yadda yake burning inside in tana kuka da ta dena, matsawa yayi a fusace kafin
ta mik’o hannu ya sakar mata both na cup d’in dana goran a jikin ta, wani irin numfashi
taja kaman zata shid’e saboda tsananin sanyi runtse idanun ta tayi tana maijin tsananin
tsanar sa.
“Eyyah Aljana ya haka? bari na k’ara miki gudun Ac dan jikin ki ya bushe da wuri kar mura
ya kama ki”.
Girgiza masa kai ta shigayi amma ko nakan ta baiyi ba ya wuce, wani irin kuka ne ya kwace
mata wanda garin haka ta fama karayan ta azaba biyu ga sanyi ga tsananin zugin da
hannun ta yake.
Duk rashin imanin ka inka ganta saika tausaya mata, mugun kam ware Ac’n yayi ya fice…. *******

1:30 pm
Sayyid zaune a class duk bayan minti saiya duba wrist watch nasa, hakan zai shaida maka
how much he miss and really want to see her.
Ko kad’an bai fahimtar abinda ake koya musu har teacher’n yayi noticing, a firgice ya d’ago
lokacin da yaji saukan chalk a face nasa sam bai san how and when teacher’n yayi trowing
masa ba.
“What the hell are you thinking of? ” yayi throwing masa question sounding damn serious.
In stemming yace ” n.. Nothing sir “.
” Sure?” ya sake questioning nasa.
“Yes am very sure sir ya answer confidently.
“Okay class let’s call it a day ” teacher’n yayi stating yana ficewa daga class d’in.
Sayyid i yayi kaman an tsunduma shi a aljanna nan take ya soma tattare belongings nasa.
Yana k’ok’arin janye wani book nasa yaji an rik’e da sauri ya d’ago..
Brightly smile nata ta sake masa at the same time shima ya miyar mata da cool smile
nasa, “Where is my abib alby? ” tayi questioning nasa.
Shiru yayi na d’an lokaci sannan yace ” he dey for house “
“Hope dai lafiyan sa k’alau?”
“Bashi da lafiya ” yayi replying nata wearing sad face.
“Subhanallahi what’s wrong with him? Since when? An kaisa asibiti? Mai Doctor’n
yace?” tuni hawaye suka fara forming rapidly a idonta.
Sakin baki da hanci Haidar yayi yana kallon ta lallai Zee bata da hankali ” Mene abun kukan
kuma ” Haidar yayi mata tambayan cike da d’umbin mamaki.
Sayyid kam duk sai yaji ba dad’i hanky ya mik’a mata a nitse yace ” ungo wipe your tears
am just kidding”
” No Sayyid inason in gansa hankalina bazai kwanta ba sai na sanya sa a idona ” tayi
maganan now crying so hard.
” Lallai kin d’au wa kanki dala ba gammo, tunda kinsan ko zaki mutu Suwayd bare barki
ki gansa ba, school d’in ma da dayadda zaiyi blocking naki ki daina ganin sa da tuni yayi,
dan haka ma is better ki fara sanyawa kanki dangana dan two months kawai suka rage miki
na ganin sa ” Haidar ya fayyace mata yadda bazaiyi hurting feelings d’in ta ba.

Sabon tashin hankali ta shiga dan ta tsani taji ana maganan candy nasu tasan definitely
tana rabuwa da Suwayd rayuwar ta tazo k’arshe, ahakan ma ganin da take masa kullum ne
yasa takejin sauk’in rad’ad’in sonsa da zuciyan ta take, ita kam ta yarda duk kud’in
mahaifin ta inhar gidan su Suwayd zasu d’auke ta aiki zatayi kodan ta rik’a ganin sa.
” Dan Allah ku taimakamin nagansa, can’t tell how much am missing him, just want to see
how he is feeling and tell him how much I care and love him koda hakan yana nufin b’acin
rai na, nasani kuna min kallon maras hankali but believe me wallahi ba laifi na bane laifin
zuciya ta ne, I want you guys to just know that am “BLINDED BY HIS LOVE kuma ko da zan
mutu zanyi alfahari na mutu da sonsa, now will you guys help me? ” tayi begging nasu tana
kuka mai tsuma zuciya, dafe saitin zuciyan ta tayi cike da azaba nan take nishin ta ya soma
chanzawa.
Gaba d’aya hankalin su ya tashi ga wani mugun tausayin ta da ya mamaye musu zuciya “
Calm down Zee, calm down Okay indai Suwayd ne zaki gansa amma sai kin daina kukan
haka ya isa kinji? ” Sayyid yayi maganan cike da tsanin tausayin ta.
Gyada masa kai kawai tayi amma har alokacin bata dawo dai_dai ba nishin ta sai sama
yake yayin da ta sake damk’e saitin zuciyan ta the more.
Ranar ko Sallah basu samu damn yi a school ba, suna tafe Zee na biye dasu a baya suka fita
daga school d’in, inda driver’n su ke parking sika nufa.
Excusing kanta tayi taje tace da driver’n ta ya tafi, ba yadda baiyi da ita ba amma tak’i binsa
dole ya hak’ura yayi kaman ya tafi, Moran su Sayyid na fara tafiya ya shiga tracing nasu.
Not long enough suka isa, Zee na cike da zulumin abinda zai biyu baya, a waje nata
driver’n ya tsaya jiran ta.
Duk yadda suka so su shiga da ita cikin gidan tak’i dole suka barta a parking space suka
shiga ciki dan turo mata Suwayd.
Suwayd zaune a garden dai _dai gurin fararen furen da Safwah ke zama, yana sanye da
black shorts da faran singlet sosai yayi kyau yayi styling curly hair nasa looking so damn
much kaman d’an larabawa.
Kaman an mintsine sa ya mik’e, without hesitation ya fice daga garden d’in parking space
ya nufa dan yasan by now su Sayyid sun dawo kuma definitely yasan wurin Flower d’in sa
zai wuce and can’t take it, dole duk yadda zaiyi ya stopping sa saiya yi.
D’agowan da zaiyi sukai ido biyu da Zee he just can’t believe abinda idanun sa ke gani, Zee
a gidan su no it can’t be happening to mai tazo yi masu gida lallai in gurin sa tazo she is
going straight to the hell, dan wallahi he won’t spare her, he will make sure made her regret
knowing him in her life.
Baiwar Allah tunda idanun ta sukayi arba dashi taji kaman an sauke mata wani nauyi,
kyakkyawar murmushinta ta sake masa with full of joy and happiness.
Sam batasan how ya k’araso inda take ba sai ji tayi ya fusgo hannun ta cike da mugun ta.
“What the hell are you doing here? ” yayi maganan a tsawace.
Azaban rik’on daya mata sam ya sa taka sa komai runtse idon ta kawai tayi nan take kuma
hawaye ya fara forming rapidly a idonta.
Waina hannun nata ya shiga yi da mugun qarfin dayake ji dashi cike da mugunta, tun tana

iya daurewa har ta soma kuka. “Suwayd ka sakemin hannu please da zafi.”
“Uban me ya kawo ki gidan mu?” Ganin bata da niyyan magana ya sake murd’a hannun
nata. ” Suwayd please you are hurting me” ta fad’a a wahalance tana kuka. “You are not
ready to talk kenan nasan maganinki” janta ya shigayi izuwa gate.
“Ina ni zaki mayar mahaukaci ina miki magana?” Jefata yayi k’ofar gidan su cike da yarfi,
nan ta qara volume na kukan nata sakamakon bigewan da tati a gwiwoyin k’afar ta,
k’ok’arin mik’ewa ta shiga yi amma ta kasa dan ba k’aramin buguwa tayi ba.
“Don Allah kalle ki, ke ko kunya ma bakiji ba ace kinzo gidan su saurayi? Saurayin ma da
baya son ki baya k’aunar ki dama ana sonki ne to da sauk’i, and let me tell you wannan
haukan da kike bare tab’a bari na so ki ba sai dai ya k’ara min tsanan ki, so nawa kike so na
fad’a miki na tsane ki bana k’aunar ki eh? to ki bud’e kunnen ki kiji da kyau duk sanda kika
sake trying zuwa gidan mu saina miki wulak’ancin da baki tab’a zato ba, banza mai zuciyan
Kare ni du a jakai ma ban tab’a ganin kaman ki ba mace har mace amma babu zuciya andai
ji kunya, and right now ki tattara filthy legs naki ki bar k’ofar gidan nan before I did
something stupid”
” Nogede Suwayd, na kuma gode Allah da ya jarabce ni da “MAKAHON SONKA” wanda
sam baya bari naga laifin duk abinda ka min, if you dare think you will make me hate you
with this thing you are doing better wake up, cause the more ka wulak’ata ni the more
sonka ke ratsa duk wata sassa ta jiki na, “I LOVE YOU” and am ready to die for You hundred
times if needed, Break my heart destroy my soul and leave me crying i’d still love you like
use to and i won’t expect you to love me in return, loving you is the most sweetest thing
that had ever happened to me, Some broken heart, may never mend, Some memories may
never end, Some wet tears may never dry, But my love for you will never die”.
Wiping unstoppable tears nata tayi sannan ta d’aura ” Suwayd loving you is like
breathing how can I stop? Someday you’ll realize I was there, when no one else was. That
loved you like no other, and will never stop. I cared, when no one else cared ” ta k’arashe
tana kuka sosai sannan ta mik’e dakyar ta shiga tafiya, tana yi tana waiwayan sa tana isa
inda driver’n yayi parking komai ya rikice mata, sam ta gaza gane a duniya take ko a lahira
nan take jiri ya d’ebeta ta fad’i daganan bata sake sanin inda kanta yake ba.
A hanzarce driver’n ta ya ciccib’e ta ya sanya ta a mota sannan ya dannawa Dad nata kira ya
shaida masa abinda ke faruwa, umarni ya masa da ya wuce da ita AKTH suma suna nan
tawo wa, da saurin sa yaja motar ya tafi.
Suwayd yadda kuka san fir’auna sam baiji komai ba game da abinda ya aikata mata ba,
juyawa yayi zai shiga gida nan yayi tozali da Haidar da idanun sa suka chanza launi,
jijiyoyin kansa duk sun mik’e saboda tsananin b’acin rai, ya rasa a wani layi zai sanya d’an
uwansa bai tanka masa ba kawai ya juya a fusace ya shige gida, d’age kafad’a yayi irin I
don’t bloody care d’innan yabi bayan sa.
****
Sayyid Haidar kawai yayi assigning yaje ya nema Suwayd ya turawa Zee shi kuma ya wuce
gurin Sweetheart tasa.
Da sallamar sa ya shiga jin shiru ba’a amsa sa ba ya kunna kai, hango ta yayi helpless tana
bacci da sauri ya k’arasa inda take.
Jirwayen hawayen daya gani da kumburin idonta kawai ya isa ya shaida masa yadda taci
kuka ta gode Allah, one more look ya k’ara mata yaji shima kamar ya sanya kuka dan yadda
yaga jikin ta na rawa.
Yadda sanyin Ac ke ratsa sa saida ya firgita sa dan yasan yadda Habibty’n sa ta tsani sanyi,
bai gama wondering ba yaga skirt natan a jik’e ga kuma jarkan ruwa nan da cup yashe a
cinyan ta.
Mik’ewa yayi ahankali ya nufa d’akin su, Wadrop nata ya nufa ya d’auko mata Baby pink
colored best nata da sky blue leggings, side na scarfs nata ya bud’a ya d’auko mata shima
blue.
ky
D’iba yayi ya nufo falour’n inda ya hango ta ready to fall dan yadda wuyan ta ya k’age, da
sauri ya k’arasa ya tare ta sannan ya rungumota ahankali ya shiga changing mata kayan
ahankali yadda bare fama mata ciwon ta ba.
Kaman ‘yar Baby ya shirya ta sannan ya d’auke ta in a bride_like style ya nufi bedroom d’in
su da ita.
Shimfid’e ta yayi ahankali sannan yaja lallausan bargon ta ya rufe ta, gudun Ac ya rage
mata sannan yai pecking forehead nata ya tofe ta da Addu’a ya fita.
Giftawan mutun ya gani da sauri amma duk iya binciken sa ya gaza gane ko waye, bai wani
damu ba ya wuce nasu part d’in.
Tun lokacin da Sayyid ya tare ta tana k’ok’arin fad’i ta farka amma tak’i bud’e idon ta, dan
tasan tayi breaking mar promise na cewa ta daina masa asaran hawayen ta.
Batasan hurting sa ko kad’an ya sha fad’a mata zuciyan sa ke k’una duk sadda ya ganta
tana kuka gashi ita kuma harga Allah bata son abinda zai tab’a mata shi, tana son sa sosai
bata son b’acin ransa…

Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]