[Advertisements⬇️]

SOYAYYAH CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 • SOYAYYAH

 • CHAPTER 1
 • Gidan Alhaji Muhammad Ibrahim Agadez, Unguwar Yahaya gusau, KANO, KANO STATE. 
 • ‘Yar k’aramar yarinyace ta fito da gudu, sanye take da pink coloured riga iya gwiwarta, sai black coloured skin tight,jelar gashin ta yasha gyara an mata packing da pink coloured ribboms, duka_duka bazata wuce 12 years ba. 
 • Kyakkyawar yarinyace fara k’al, face nata har wani ja yake saboda fari, da gashi kwance luf_lufa goshin ta hakan ba k’aramin kyau ya k’ara mata ba, tanada cikan gashi ga tsayi kamar balarabiya, bak’i ne sid’ik ga santsi kaman na baby, tana da dogayen eyelashes da suke kallon k’asa, da manyan idanu wanda inta zare su saita baka tsoro , kwayoyin idon nata sky blue coloured ne kamar na baturiya, tanada dogon hanci wanda ya k’arawa siririyar fuskarta kyau, bakin ta d’an k’arami ne wanda inka kalla saika zata spoon bazai shiga ba, colour d’in lips nata light red ne. Safwah kenan, yarinya maiji da hutu, kyau, gata uwa uba shagwab’a. 
 • Tana d’auke da k’atuwan pink coloured teddy bear, k’araso wa tayi gurin wata farar Dattijuwa dake zaune akan sofa tana karanta daily trust. 
 • Cike da shagwab’a tace ” Granny what say’s the time please? ” D’agowa Dattijuwar tayi ta kalli diamond wrist watch d’in dake d’aure a tsintsiyar hannun ta tace ” quarter pass 2 baby “. ‘ 
 • Tana jin haka ta kwasa da gudu tayi waje, girgiza kai wannan Dattijuwar tayi tace ” yanzu haka da kuka zaki dawo “. Parking space ta nufa ta nemi guri ta zauna a kan wasu iron chairs masu matuk’ar kyau da akayi decorating gurin da su, ga wasu red and yellow flowers masu dad’in k’amshi da suka k’awata gurin. 
 • Bata dad’e da zama ba wata bak’ar Prado jeep ta shigo, da sauri ta mik’e tana tsalle tana ” oyoyo, oyoyo “, ana gama parking driver ya zagayo da sauri ya bud’e right side sannan ya zagaya ya bud’e left side. 
 • Ahankali suka fito da legs d’insu then complete body nasu. Duba na nakai kan last guy d’in daya Fito daga motar, kyakkyawan saurayi ne fari tas, yana da suma wacce ta kwanta luf_luf akansa black coloured, tana walk’iya dan ba k’arya kallo d’aya zakai mata kasan tasha gyara, sai saje kwance akan farar fatar sa kamar balarabe wanda da ace yana da gemu da sun had’e, gashin giransa a cike yake bak’ik’k’irin yayi curve kamar cinku, ga eyelashes masu santsi zara_zara, yana da idanu dara_dara masu tafiya da zuciyar ‘yan mata, idanun nasa suna nan madai daita da kwayoyin idon nasa black , yana da dogon hanci wanda ya k‘ara k’awata ‘yarfuskar sa da d’an madai daicin bakin sa pink colour, yana da dimples a both cheeks nasa dan ko smile yayi sai sun lotsa, dogo ne shi yanada faffad’an k’irji, duk da cewan shid’in siriri ne amma ba can be, yanada 
 • six packs wanda ya k’ara fito da mazan takarsa. Guy d’innan dai Kat ne dan anacewa mutum tara yake bai cika goma ba, to nidai zance wannan ya cika saidai ko a halayyarsa asamu akasi. Suwayd kenan, Mr arrogant yaro maiji da zamani, kud’i, kyau uwa uba ilimi. Kallona na mayar kan guy d‘in dake middle d’insu, kyakkyawa ne shi sai dai kallo d’aya zakai masa kasan yafi Suwayd fara’a, dogone shima yanada saje a fuskar sa kamar balarabe

 • , suman kansa yasha gyara kaman na shahid kapoor and a fizge yana kama da Suwayd. Sayyid kenan, Mr cool, kind and breathtaking. Ahankali nakai dubana kan d’ayan shima kyakkyawa ne, dan kallo d’aya nayi masa na hango kamarsa da Safwah, da alama yayan tane. Haidar kenan, yaro mai nutsuwa, tausayi da sanin ya kamata. Duka_duka bazasu wuce 18 years ba, da sauri ta k’araso ta rungume Sayyid tanai masa sannu da zuwa, tsuguna wa yayi ya dawo da tsayin sa dai_dai da nata yai pecking ta a forehead dinta, cika shi tayi ta tayi hugging Haidar cike da shagwab’a tace ” ya Haidar sannu da 
 • zuwa, ka siyo min chocolates d’in? ” Murmushi yayi yace ” na siyo miki sweetie, bari muje ciki sai na baki “Cika shi tayi sannan ta zagaya ta d’ayan side d’in ta rungume Suwayd cike da tsoro, da 
 • sauri kuwa ya finci keta daga jikin sa ya cillar a k’asa. ” chhhhh ” ta saki k’ara sakamakon bigewa da tayi a gwiwar k’afar ta. Cike da masifa yace ” baki da hankali ne? Koni sa’an wasan kine? For how many times have I been warning u to stop using this your filthy hands on my body huh? The next time kika sake attempting yimin haka sena babballaki, banza aljana kawai “.
 • Yasa kai yayi tafiyar sa not minding halin data ke ciki, ai aljanar da Suwayd ya kirawo ta yafi komai ci mata rai dan gani take duk duniya tafi kowa muni kenan, kuka ta saki mai ban tausayi ta d’au teddy’n ta, ta kwasa da gudu tayi garden, not minding kiran da Sayyid da Haidar suke mata sending. 
 • Tana shiga garden d’in ta nufi gurin wasu fararen fure masu kyau da dad’in k’amshi ta zauna ta ciga ba da kukan ta …………….. 
 • Later during the day, gaba d’aya family’n suka had’u dan having lunch, Suwayd ne k’arshen shigowa. Kallon ko ina yayi yaga bata nan, zuba ido yayi yaga daga ta ina zata bullo amma shiru gashi kowa ya faracin Abinci amma ita bata shigo ba. 
 • Mik’ewa yayi, da sauri Mammy’n shi ta kalleshi tace ” Where to? “. 
 • Sosa kai yayi yace “ Mammy dama sak’o aka bani na bawa Granny naman ta shine zanje in kai mata “. Tsab ta gane k’arya yake dan tin yana k’arami indai zaiyi k‘arya saiya sosa kai amma tace “ ohky buh you have to be fast “. 
 • Abunka da mai jiran k’iris tuni ya fice daga Babban falour’n ya nufi garden dan yasan anan kawai zai same ta. Inda ta saba zama ya hangota kwance tana bacci tana sauke ajiyar zuciya da alama taci kuka ta gode Allah, tsugunawa yayi yakai lallausan hannun sa kan gashin ta daya kwanta luf_luf a goshin ta yana wasa da shi, ganin ta d’anyi juyi yayi saurin janye hannun nasa. Sannan ahankali yasa hannu ya d’auketa ya d’au mata teddy’n ta ya nufl part d’in Granny dan anan d’akin ‘yan matan gidan yake. Da sallama ya shiga ganin babu kowa a falour‘n yasa ya wuce bedroom d’in su, ahankali yasa hannu dan karya tashe ta ya bud’e k’ofar d’akin ya shiga sannan ya mayar ya rufe. 
 • Manyan gadajene guda biyu a d‘akin, white and purple sai pink and white in each side of the bed there is Wadrop and dressing mirror. Akan pink bed d’in ya shimfid’e ta sannan yayi kissing forehead d’inta ya bud’i baki ahankali cikin husky voice d’insa yace ” Ana asif ya Habibty, am terribly sorry is not my fault, is just that am _Blinded by your love_ insha Allah you will be my everlasting, you are my everything, my love for you is a journey starting at forever and ending at never, da sanki nake kwana nake tashi, sanki yana yawo ajikina tamkar yarda jini yake yawo ajikin b’argo, without you | feel broke like i’m half of whole, without you I’ve got no hand to hold, without you | feel torm like a sail in a storm, with out you am just a sad song Hannun ta ya d’ago yana kallon diamond ring d’in daya saka mata wanda yasan haryau batasan waya saka mata ba, brightly smile d’insa ya saki bar dimples d’insa suka lotsa yace “S love S, Safwah the moon that will never escape from the star, I am the star and you are the moon Habibty “. Lallausan bargon ta yasa ya lullub’e ta sannan ya k’ara mata gudun Ac ya fice. Babban falour’n ya koma inda ya tarar su Mammy harsun gama sun tashi, baice da kowa k’ala ba yaja plate yayi sewing kansa, hankali kwance ya fara cin abincin. 
 • Ganin 3:00 pm yayi yasa yayi saurin tashi dan zaiyi bak’i Kadsah ce ta tayi saurin biyo shi tace ” ya Suwayd please maths assignment zaka koya mana ”. 
 • cikin had’e fuska ya kalli watch d’in hannun sa yace ” 5:00 pm ku same ni a d’aki na, make you guys stuck my rules into that your cockroach heads understand? ” 
 • ” Yes ” ta amsa da sanyin murya. 
 • Cikin zubda kwalla Kuwaysah tace ” fuck you sis ya zaki kaimu assignment gun ya Suwayd ko kin manta shine? ” 
 • ” Karki zo kinji kiga yadda zanyi dake a gidan nan useless , pathetlc fool kawai ” yasa kai ya fice. Part d’in Granny suka nufa suka zauna jigum Jigum, suna zaune Ya Haidar yayi sallama ya shigo. 
 • Kallon Kuwaysah yayi dake faman zubda kwalla dan tasan yau mai kwatar su sai Allah, sannan ya k’araso ya zauna yajanyo tajikin sa abinka da mai jiran k‘iris tuni ta fashe masa da kuka, saida ya rarrasheta sannan ya tambayi Maya faru. 
 • Cikin sheshshek’ar kuka tace ” ba kadsah ce tacewa Ya Suwayd wai zamu zo ya koya mana assignment ba “. Tausayin sune ya kamashi dan yasan yau za suci k’aniyan su, sannan ya dake ya shiga kwantar musu da hankali. 
 • Mik’ewa yayi ya fice ya nufi part d’in Ummy’n su, da sallamar sa ya shiga. Ganin ta zaune a falour shima ya k’araso ya zauna cikin nutsuwar sa yace ” sannu Ummy “. ” Yauwa Aliyu na, gadanga k’usar yak’i “, murmushi yayi da a rayuwa yanaso Ummy’n shi ta kirashi da sunan . hira suka shigayi suna cikin hirar Safwah ta shigo tana turo small cute mouth d’in ta ga kyawawan idon nan nata a kumbure. 
 • Kallon ta Ummy tayi tace ” ke kuma lafiya zaki shigo mana ba sallama? Da alama ma yanzu kika tashi daga barci, kinyi Asr prayer? “. ‘ Nodding kanta tayi alamar A’ah, ” karki wuce kije kiyi yanzu na kirawo Suwayd “. ai tuni jikin ta yafara rawa ta rik’e kunnen ta alamar bada hak’uri tace ” Am sorry Ummy wallahi Aljana zai cemin “, ta fashe da kuka dan sosai kalmar aljana keci mata rai. Tausayin tane ya kama Ummy ganin daga an ambaci sunan Suwayd jikin ta harya fara rawa, ” come on Baby share hawayen ki amjust kidding you kinji? ” Gyad’a kanta tayi amma har alokacin hawaye bai dena zuba a idon ta ba …………….. 


 • Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]