[Advertisements⬇️]

RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 8 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RIKICIN WANI GIDA

CHAPTER 8

Ko da Amira ta koma sassan hajia babba bata ce komai ba, zama tayi kusa da ita tace hajia babba fita zakiyi? Tace eh Amira, muje na kaiki a Mota na, Waaaa? Allah ya sawwaqa na shiga tuqin ki, kinga ma tafla ta, Sai kin dawo, Hajia karime ta lullube fuskarta ynda ba zaa shaedeta ba tayi waje, taci saar fita daga babban gate ba tare da an ganeta ba, Adaidaita ta tsaida tashiga tare da cewa marrabar konduga zaka kaini, yace dari 500 tace yi sauri zan baka dari 8. Da sauri me napep ya ja er qurqurarsa. Suka bar layin. Sameer da Amira ne suka flto daga gidan, suka bi bayansu Hajia Babba, tafla me nisa sukayi kafln suka iso malilo, unguwa ce me kama da qauye,jan qasa ce sai bukkoki, bukar gun basu wuce 10 ba, da alamun mutane basu flye yawa ba. Daga nesa samir yayi parking, hajia babba ta flto daga keke napep ta biyashi ta nufa wani bukar da yafi sauran kyau. Daga nesa tace bigbrosamir muje yace A’a ba musan me ke ciki ba, kamar daga sama suka ga wani mutum daga shi sai kamfan ganye, Samir yace baba ina wuni? Yace lhfy yaro? Eh baba daman wanchan bukar nake tambaya, ya nunu bukar da hajia karime ta shiga, tsohom yace eh nan ne, k0 ba bukkar er madiyo qashi ba tsoka ba? Ai yaro kar kaji komi, tun da kazo nan buqatarka ta biya(Waiyazubillah.) tsoho yayi gaba, Samir yace Wato wurin Bokanya Hajia Babba tazo? Bari kaga naje, yace kee so kike ta ganki? Dabara zanyi, yace lil sis meerah be careful pls, ta flta ta nufa bukkar. daga nesa ta farajin muryar Hajia babba samasama inda take cewa, ina so ki musu yankan qauna ya zamana ba kowa gabansa ba hajjon ba, ba Aishallen ba, daga ni sai ‘yayana, sai jikoki,na da sauri Amirah ta qarasa jikin bukkar ta kasa kunne, ‘yar madiyo tayi daria tace wannan shi yafl komi sauqi, abu daya kawai zakiyi, tayi dan buga buganta ta dauko wani garin maganin da tayi mai sidabbaru. tace amsa wannan, yaushe kike da miji? Ina nufln yaushe ne kwananki ranar girkin ki, tace gobe ne, kuma ai girkin ba.mu keyi ba akwai masu yi, Er madiyo tace toh gobe ki tafasa wannan maganin, kiyi tsarki dashi, ki kwanta dashi maigidan naki, toh daga wannan rannan ba macen da zai qara gani da gashin ido sai ke, Hajia Babba tace Er madiyo banan gizo ke saqar ba. Dan Zallani ya kusa shekara 100, ta ya zan kwana dashi? Ai an kwan biyu er madiyo a dai chanxa wata hanyar, Er madiyo tace Keeee hakan na zaba miki, idan be miki ba bani garin maganin da na baki. Da sauri karime ta fara zuba haquri, Ameerah da daria ta ci qarfinta ta zura a guje tayi hanyar mota, samir na ganinta yayi saurin bude mata qofa. Ya fincika motar yayi reverse, ita ko Ameera sai daria take tayi Samir ya dinga tambayarta ta kasa magana sai dariar mugunta da take tayi, sai da tayi me isarta kafin tayi shiru, yace Lil sis kinji yanda sukayi?ko sunganki kina leqensu? Sai ta kuma fashewa da daria Samir yace ke Nifa bansan daria me ya faru? Nan ta kwashe komai ta gaya mai, shi Samir kunyar maganar yaji ita kuwa ko ajikinta. Haka suka kama hanyar Gari… 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Ya Samir yanzu ya zamu hana wannan abun ya kasance kasan yau Girkin sassanta ne ko? cewar lslah Ameerah tace me zamu hana? Tsarki da maganin ko kwana da tsohon? Waiyo Allah da Islah da Samir kamar su rufeta da duka da kunya, Samir yayi dauriyan cewa muyi dozing dinta, maganin baccin da ba zata tashi ba for d whole nyt. Kinga ba za ta samu damar shiga dakin nasa ba, Islah tace hakane yasamir. Ya fita da sauri ya nufa chemist, magungunan bacci ya hado kafin ya dawo don samun dabarar da za a samu hajia babba ta sha magungunnan nan.. 
Ameerah amsa wannan maganin ki hada mata dan juice ki watsa mata guda 14 a ciki, yo ni na san juice din da zan hada mata, Islah tayi saurin cewa bari ni zan hada sobo ynz shine ba zai chanza kala ba, sai ki mata dabara ta sha. Duk suka amince da hakan, Islah ta shiga kicin dinsu ta hado sobo, Harda sa qanqara, ta iske yasamir da Amira ana labari, ta miqa mata tace gashi tym to do ur part. Suka balle magungunan nan suka watsa cikin sobo, Samir yace Lilsis i trust u on dis, ds our only hope make sure it works, are u doubting me or wat, da sauri yace nooo ta miqe ta nufa sassan su, Qarfe 8:30 Hajia babba tayi wanka, su karime harda wanke baki zaa je gurin darling Tsoho (lol) Ameerah ta shigo da Sallama da Jug a hannu da kofi Karime ta tabe baki Sanabe. daga ina haka, meye a hannunki? Tace sobo na hado maki, tace waa zai sha qazantarki? Ameerah tayi rau rau da fiska, Anya ke kika haifi uba na? Kina nuna min tsana qiriqiri. k0 kasheki xanyi? Ko na samaki guba ne a ciki?toh kalla Amira ta tsiyaya sobo a cup ta shanye, to kinga ban mutu ba( nikam nace Anya kuwa Amira?), Karime tace toh uban wa yace kasheni zakiyi? Baki ga nayi shiri ba? Tsoho na jirana, ko so kike naje gun Tsoho da warin baki? Amira tace Uban wa yace maki sobo na sa warin baki? Toh qamshi zai qara miki Allah ko Amirah? Eh wlh, to tsiyayo man, ta bata cupi daya karime ta kafa sai da ta shanye cup daya tass, Amirah ‘tace kakus bari kiga na gyaraki kiyi kyau don tsoho ya rude da ya ganki, bazai dlnga kula da Hajia Ama ba k0 Umma hajja, cikin maye Hajia babba tace Allah Amira? Yi man Me guduma irin na zamani-rigijib ta zube kan gado, Amira ta fashe daria, wooo hajia babba ta bugu, heheh tana darian mugunta itama ta zuve kan gadon. ni dai nace smdrms Hajia Babba nd d Amazing Ameerah
takwas na safe, Hajia Babba ta farka tayi zumbur zata miqe,ji tayijikinta ya mata nauyi. ganin Amira tayi kwance kanta da qarfi ta tureta, Amira ta farka tana soshe soshen idanuwa. ke wani irin bacci mukayi haka? Amira ta kalli agogo ta pashe da daria Baccin awa 12 mukayi kakus. karime ta dafe qirji shkn gari ya waye, ban samu ganin tsoho ba, Amira ta tashi ta kwashejugdin sobonta gami da cewa ke dai kakus wani tsoho ko asuba ba muyi ba?. 
Tun daga ranar duk inda Hajia Babba ta sa Qafarta Amira na bayanta, tayi fadan tayi masifan tayi lallashin amma taqi rabuwa da ita, daga baya ma tare suka dawo kwana a daki, wai ke meye kike bibiyata haka? Ynx duk inda nasa qafa kina biye dani kamar raqumi da aqala, amira tace ynx kakus har na isheki? To wlh duk inda zaki sai na biki ehe, Da wannan kwafsin da Amira kema hajia babba yasa bata koma gurin bokarta ba… 
Duk shirin da Hajia Babba keyi Amira ke rugujewa, don haka yasa ta yanke hukuncin sararawa na dan lokaci kafin ta san abinyi.

lyear later

Haka Rayuwa ta kasance cikin gidan M.Zailani, da dadi ba dadi, Har ynx Gaban yan sassan hajia Babba na nan, yan dakin Hajia Ama da na Umma Hajja kadai ke xumunci, yan dakin Hajia Babba daga harara sai hantara sai kuma zagege da gori suke bin yan dakin sassan dasu. A wannan lokacin samarin nan sun gama Service ko wannen su ya fara aiki Garuruwa daban daban, yanmatan kuwa ko wacce na da certificate din Computer skul. Soyyayar su kuwa qara habaka yake da girmama, Har tsoho ya san da soyayyar da suke wa junan su, kuma ya yanke hukuncin aurar dasu ga waenda suke sonsu tunda sun sassanta junan su lokaci kadai yakejira a shafa fatiha. 

M.Zailani ya kalli Baba Mudassir Yace kai Mudassiru kira min Zaidu kar ya maidani tsohon banza. Jiki na rawa baba mudassir ya kwada wa Zaid waya, sai da wayar ta kusa tsinkewa kam ya ansa da Sallama. Handsfree yasa Assalam Alaikum Baba barka da marece, tsoho yace Kai Zaidu ka natsu ka san abun da kakeyi, ka dawo gida ga yan uwanka nan shekara daya da yan watanni da dawowansu har sun gama Bautar qasa sun kama aiki kai ka tsaya shashanci, Zaid ya yi daria na yan duniya Tsoho me ran karfe, kaine da kanka?Lallai kunyi kewata, toh su ba suce maka yanayin karatu na da nasu ba daya bane? Toh karatun likitanci nayi kuma ni course dina shekara 6 ne, Kar ka damu komi yazo qarshe, nagama komai, expect me any time frm now ka fara baza idon ganina, ka gaida mun tsofin Matanka kafln nazo, kam tsoho yace komai Zaid ya kashe waya tsoho yayi daria yace Shaqiyyi. Zaune take gaban bokanta, cikin damuwa tace Boka. nagaji nagaji nagaji. Aure nake sonyi cikin shekarar nan, ace duk samarina ba na aure? Boka yayi daria, yace diyyan shagali, aike kika watsar da Daman ki, lokacin da ya dace kiyi auren ki kayi shahadar rabuwa da saurayi me nagarta me hankali, kuma wanda ya yi niyyar aurenki, tayi tagumi tace ai ni kaina, nayi nadamar rabuwa dashi, nayi nadama sosai, haba a ce shekara 2 da rabi na kasa mance shi, sonsa na nan daram a raina. wai ganina saka mai da Alheri shine abun da ya kamata nayi a wannan lokacin, amma yanzu bandamu ba, duk yanda zanyi sai na sameshi ko ta halin qaqa, Boka yace Anya kuwa zaki sameshi iyayenshi tsaye suke kanshi, tace kaii rabani, duba min shi, yana ina? Ina zan sameshi? Boka ya duqufa yana binciken shi, yace yana nan a qasashen waje, kuma shirin dawowa qasa Nigeria,yake yana tare da Iyalensa Matar shi Yaransa biyu kuma da Alamu yan biyu ne. Sai ki jira idan sun dawo qasar, sai ki nemeshi ki ga ko zaki samu saa, tace wa? Ai a bari ya huce shi ke kawo rabon wani, ynx bani adireshin Su na chan, boka ya zaro ido yace na Ingilar? Tace ko na sin ne, yayi yan bincike binciken shi kana yace leqa qwaryar nan, tana leqawa taga Garin da yake da street din da yake har kwanar gidan da cikin gidan ta gani, yauwa boka garqanjo sai kajini, yace toh shkn sai kin dace, tayi daria tace dole ne sai na dace, Badiyyan shagali dagaske kike sai kin sameshi? Ta miqe tare da sabar jakkarta tace da na qyaleshi, amma ynz ba zan qyaleshi ba, k0 yaya ne sai na samu ZAID ALI MODIBBO.

Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]