RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 13

 • RIKICIN WANI GIDA
 • CHAPTER 13 • Sai da Tsoho yayi Baccin Awa 12 kafin Maganin bacci ya sake shi, A lokacin Daga Dr sai Baba Dr munnir yazo yana duba shi, Dr Munnir ya kashe ma tsoho ido alamun komai daidai. Sai yace Masha Allah jiki ta warware, ina ma iys sallamanka. Amma zan barka ka dan huta, Tsoho yace me zai zaunar dani tunda naji sauqi kunsan da ina cikin hayyacina ai da ba a kawo ni nan ba. Dr yayi daria yace haka ne. Nan ya rubuta musu takadar Sallamah, Baba Hassan ya kira Suraj yace kazo ka maida mu Gida.
 • Kowa yayi murnan ganin tsoho ya tako da Kafarsa. Barin ma maysah da take kukan murna, don taba Tsoho mutuwa. Sashensa yayi Hajia Babba sai rawan Jikin Alhaji me kake so? Alhaji me za a maka? Yace wanka zaiyi, nan Baba Abbakarya umurce kowa da ya bar Tsoho ya huta…

 • WASHE GARI

 • Tun daga nesa ta hangoshi bataso ya cimmata sai ta qara sauri, tun jiya take avoiding dinshi, da gudu ya tankarota, yana kiran Fadila, haba Fadila ki tsaya mana, Ya qaraso, Fadila y are u avoiding me? Tace Ya Suraj yace shhh, fadila Tsoho yaji sauki, ba abunda ke damunshi ynz, lets run, lets leave dis place, muje wani wuri a daura mana Aure, i cant do without u, kukan da take boye ya kubuce, sai da tayi me isana ba tare da ya hanata ba ta girgiza mai kai, tace Yasuraj wallahi tallahi ina sonka, zan auri Ya Jawad and zaka auri Bilkis, idan muka gudu, mukaje aka daura mana aure me mu kayi kenan? Mu bijire ma iyayen mu? Bakin cikin mu ya kashe tsoho? Gaban ya cigaba da wanzuwa frm generation to generation? If we leave, they will be seperated forever, maybe ‘this is the only way to End our Family’s Malice, Ka roki Allah yasa hakan yafl Alheri, And Allah ya ba mu ikon rungumar wannan Kaddarar, tana kaiwa nan ta ruga da gudu. Tayi sashensu, A hanya taci karo da Bilkisu data fito daga Sashen Tsoho, taja ta tsaya, Bilkisu na watsa mata harara, tace listen to me Fadila kar ki ga kamar Gobe Zaki zama Mallakin yajawad kice zaki zake, ki kira kanki matarshi, to bari kiji Yajawad nawa ne, Aurenku suna ne kingane? na dan wani

  lokaci ne, idan komai ya daidaita zai sakeki ya aureni, so i want u to keep ur distance, ban yarda ayi seducing masoyina ba. Fadila tayi munnushi ta share hawayenta. Tace Bilkisu bana son Jawad bana kaunarsa toh mesa xanyi tunanin Jan hankalinsa k0 ra’ayinsa? Kuma da kike cewa nan ba da jimawa ba zai sakeni, kin ga na miki kama da wadda zata zama bazawara in future? in kinso ki ka she aurenki ki zama bazawara, ki sami wani miji amma badai Jawad ba, i dont love him but i will make sure dat he never ever gets back to u get dis into your thick skull Jawad ya miki nisa. tayi gaba ta barta bakih bude tana mamakin karfin Halin fadila ita da ba sonsa take ba.

 • lslahulkhiar kwance a green carpet din feld din Gidan idonta lumshe, tana tuna moments dinta da Samir, time din da suke kwallo, ko kwallon kwando k0 skipping rope, Maganar Hajja Ama ta tuna inda take cewa _kuyi haquri da wa’enda aka zaba muku, ku roki Allah ya sa sune Alheri, ku Maida Soyayyar masoyan ku a kansu, ku maida Soyayyar Masoyanku Soyayyar yanuwantaka don ku Yanuwan juna ne Allah muku Albarka_ islah ta matse hawaye tace Allah kasa ya Mu’ammar shine Alheri a gareni. Tsaki taji an buga tsuuu Ta na dagowa taga Amira da Hanifa. Amira tace lallai kam kin ma kanki Kiyamul laili, gwanda da kika haqura da Yasamir, don nice matar da aka zaba mai. Gwara da kika dangana Allah hada kanku da ya Mu’ammar din Islah ta girgiza kanta ta miqe ta kakkabejikinta tayi gaba don bata son hayaniya. Hanifa da qarfi tace aikin banza, ko me zakiyi Ya Mu’ammar ba zai taba sonki ba, ni yake so ni kadai,jini na ke gudana a zuciyan shi, da komi ya daidaita zai sakeki ya aureni, dan ba zai taba hada iri da dangin mayu da aljanu ba. Chak Islah ta tsaya, kamar ba zata yi magana ba kuma sai ta dawo da baya, ta tsaya Daf da Hanifa tace, Wai tada jijiyoyin wuya na meye ne? Naga dai tsoho ya san dake ya zaba mishi ni? Duk da jinin naki na gudana a jikinshi, ki bari ya sakeni mana yazo ya aureki kafin ki gaya min magana, but as far as m concerned ni zai aura Gobe, nd m d choosed person its not my fault dat In more beautiful and talented dan u, is not my fault dat i’m chosen for him, so Maybe tsoho ya ga rashin dacewar ku ne ya zaba mishi ni, if u have a problem go meet Tsoho, amma idan zaki bi shawara ta, ki koya ma kanki Son YaZayyad don Ya Muammar will never ever come back to u, tana kaiwa nan tayi gaba ta barsu baki sake, chan kuma Amira ta pashe da daria, kaii ashe lslah na da baki haka? Wai its not her fault» wato shes more talented nd more beautiful dan u, 000 lslah got attitude, Hanifa takaici goma da ashirin, ashe wannan haka take? Ai bata taba zatan zata tanka mata ba, Ga haushin mugunta da Amira ke mata. Ji tayi kamar ta sa Ihu don takaici.
 • Ayau Jummaa Wurin Huduba Liman yayi sanarwa za a Daura auren Jikokin me Masallacin nan, ana buqatar kowa ya tsaya bayan an Idar da Sallan Jummah. Haka kuwa akayi, ana Idarwa aka daura Auren ZAWAD da HANIFA, ZAID da RUMAISAH, JAWAD da FADILA SURAJ da BILKIS, SAMIR da AMIRA da kuma MU’AMMAR da ISLAHULKHAIR bisa Sadaki dubu Hamsin lakadan ba Ajalan ba, aka shafa kuma aka wadata su da Rengem na shinkafa(lol) Tsoho baki har kunne, Angwayen kuwa kadaran kadahan duk da Mu’ammar da Jawad ba su tsaya daurin auren ba. Nidai nace oho dai an riga da an daura. K0 da ku ko baku saida Tsoho ya Daura muku aure ‘
 • Daren da Aka daura Auren abin dunia ya ishi Sabbin ma,auratan, da Angwaye musamman Amaren, daga Zaid sai Amira kadai ne basu da wata damuwa sosai k0 wannensu na sashensu jikinsu duk yayi sanyi. Kuka wiwi Rumaysa keyi, Shikenan me afkuwa ta afku, YaZayyad ya mata nisa, yanxu YaZayd ne mijin ta. Allah ka ba ni ikon Cin wannan Jarabawar. Amma ce ta dafata da sauri ta share hawayenta don bataso taga kukanta hankalinta na iya tashi, Amma ta mata murmushi cikin hausarta da har yau be fita tace Maysah kuka kike yi koh? Tace Aa Amma, Amma tace liar, na ganki kina kuka, kamar jira take ta fashe da kuka, Amma ta rungumeta sai da ta yi me isarta, tace Amma Yazayd Dan iska ne, Mashayi kuma Mazinaci ta dakatar da ita ta hanyar sa mata hannu a bakih, Sai kuma ta mata murmushi tace Maybe ke xaki kubutar dashi daga sinful acts dinshi, ki nuna masa hanya madaidaiciya, Amma how? I cant, Amma tace shhh, my Baby i trust u, u can even do more, Have Faith kinji? Ta gyada mata kai. Tace Oya tashi tsoho ya aiko A kiraki nace kina wanka, tashi kijei,jikih ba qwari ta daura dankwali ta fita. Amma ta bi bayan tillon diyarta da ido, tausayinta ya mamayeta, Allah ga Baiwar ka nan, Allah ka shige mata Gaba Amin..
 • Tsoho ya kalleta yace Rumah Nah, ba tare da ta kalle shi ba tace Naam Tsohona, yayi murmushi yace yau k0 kallona ba zakiyi ba? Ko har ynz fushin akeyi dani? Ta qaqalo murmushi, haba Tsoho nah, wani irin fushi a na zaune kalau, ya girgiza kai yace Rumah kenan, my favourite among them all. Tayi murmushi, yace A tunanin ki na shiga tsakaninki da farincikin ki na hadaki da baki‘n ciki,A Ganinki na hadaki da kunama me zafin Halbi, na san xakice anya Tsoho na sona? Ya hadani da Mashayi kuma Mazinaci? Maysah na san abinda nakeyi. Allah yayi yarinya me hankali, me tunani, me hangen nesa, da sanin ya kamata uwa uba ga ki da Hakuri, kinyo gadon kakarki Aishalle, Auren Zaid Jihadi ne, ke kadai zaki iya hakuri da halayenshi, ke kadai zaki tsaya tsaye a kansa har Allah yasa ya bar halayensa, kuma nayi istihara tun kafln nayi hadin nan, naga Aurenku Alheri ne, Kece Rufin asirinsa. Rumah kin fahimce ni? Maysah ta daga kai tana kuka, tace eh Tsoho, Allah ya bani iko Allah ya sa hakan ya zama Alheri tsoho yace Amin Rumah nah, sannan Abu na gaba, munyi magana da Mudassir yace Zaid zai fara housemanship dinshi Nextweek a Abuja a nan National Hospital,Asibiti ta bashi Gida, Amma na baku daya daga cikin gidaje na na Maitama, na yanke hukuncin dake zai tafl, sai ki fara Shirin tafia, gaban Maysah ya bada tace Allah kaimu. Yace Amin, Gani yayi sai Kyarma takeyi, hakan yasa yace toh kina iya tafia, sannan Akwai Taron duka Gida Gobe da Safe Misalln Karfe 10 na safeh. Tace toh Tsoho Allah kaimu Goben. Yace Amin Ta miqe guiwa a sake ta bar Dakin tsoho.
 • Wallahi da an san yanda na tsana ganin Fadila da ba a yi gigin hada auren nan balle a daura ba, wlh na kijininta, Bilkisu tace ni wai ya ma za,a aura mun Azzalumi kamar Suraj,ji dai randa ya kamamu ya zane, wlh na tsaneshi, Mu’ammar da yake ganin kamar ya fisu tashin hankali, babban tashin hankalinsa kuwa shine ganin an daura auren Hanifa da wanninsa, Zaid kuwa ba abunda ya damesa, chatting dinsa yake da Diyyan Shagali. Amira kuwa ta maidasu TV sai kallo take wannan yace ka za wannan yace kaza. Aunty Saadiya tace hajiar mu kice wani abu mana, toh dan ubansu sun ishe mutane da surutan banza su saman ido mana suga yanda zan warware alamarin nan,jira nake na ji ta bakin Alhaji, sai na san abunyi, Amma sun tasa ni gaba sai babatu suke tayi, ba sai na sa musu ido ba, Aunty Abida tace ynz dai haquri zamuyi gabaki daya, Sai mujira muji me baban zaice gobe. Kun gane koh? Duk suka gyada kai, Amar yace hajia me zakiyi ke goben, ni burina a warware auren nan kawai, hajia tace kai dai ka bari sai Goben u shud all trust ur Grandma. Hajia Babba Ta kalli inda zaid ke zaune tace dan gidana Yaya dai banji kace komi ba? Ya kalleta ya watsar yace ban da ta cewa, tace wai ni mesa kake man haka ne? Miqewa yayi yace Jawad ka
 • kirani idan baba ya dawo ya fice daga parlon, hajia babba ta hau masifa ina sonka kana gurxa man, sai wulaqancin tsiya shege me qiran samudawa, kowanensu sai da ya dara.. 
 • Gabaki dayan su sun Hallara parlom tsoho suna zama jiranshi, da sallama ya Flto daga dakinsa suka amsa mai, kujerarsa ya zauna aka fara kwasar gaisuwa, sai da aka gama kafin yayi gyaran murya tare da gajeruwar Muqadima, yace Ahhh A jiyan ne aka daura auren Jikokina su 12, Allah sa Alheri, ‘yan dakin hajia Ama da Umma Hajja kadai sukace Amin, Hajia Babba kuwa sai hura hanci take tayi, abu na farko, ya kira Hanifa yace taso nan, ta miqe ta nufeshi ya ciro wata envelop ya miqa mata kamar bazata amsa ba ta amsa yace dubu 50 ce sadakin ki ne,jiki ba qwari ta koma mazauninta ta xauna, haka ya kira Bilkisu, Islahulkhair, Amira Fadila da Rumaysah ya danka musu sadakin su a hannu, Sannan yace Ahh gobe lahadi, nasan gobe yan mazan zasu koma bakin aikinsu, to na yanke hukuncin kowannensu zai tafi da matarsa, Jikokin Hajia Babba suka zuba mata ido alamun zasu yi magana hannu ta daga musu alamun suyi shiru, bari taga iya gudun ruwanshi, Tsoho ya cigaba na bada kudadden da zaaje Dubai ama yanmatan kayan daki da na kitchen, da kuma lefe kuma na mallaka ma mazajen Gidaje a duk garin da suke aiki, Sannan kuma na chanza ma kowa mota nd kuma. Toh ina umurni da matan su Shirya, gobe zasu bi mazajensu… Hajia Babba tayi karaf tace kagama? Haba Alhaji? Ran tsoho a. Bace yace Karime menene haka? Tace bangane kowa yabi mijin shi ba? dame? Daga daurin aurejiya, sai kace an gaji da su,,, ta cigaba da bambami, Tsoho ya fara tarin karya kamar xai shide, tarin da karfi, kuma sai Allah ya kawo mai atishawa me zafi, ai nan hankalin kowa ya tashi, Hajia karime ta rude, sannu Ahaji, Baba hassan ya ruga firij ya dauko ruwa yana fadin Baba sha ruwa, ya ture ya shaqe murya yace ba ruwan da zansha ai haka take so ta ga karshe na koh?toh bazan sha ruwan ba, ku barni na mutu kawai tunda ba za samun yadda nakeso zan ba, ai nan ta fita hayyacinta, ta fara cewa yi haquri Alhaji, dan Allah ka sha ruwa, wlh k0 ynz kace su tafi zasu wuce, daman wai naga ba a shirya bane, amma yadda kace hakan zaayi, Allah ya huci zuciyarka. dan Allah ka sha ruwa, Tsoho ya kurba Ruwan nan taro ya watse bayan an Tsaida maganan gobe kowa xai wuce da matarsa.. Mu’ammar kamar zai yi hauka, fadih yake Hajia wai menene haka? Bangane ba? Ya akayi kika amince masa? Hajia babba tace dan ubanka so kake mijina ya mutu, haquri kawai zakuyi ku tafl dasu din, bayan sati 2 ku danqara ma shegu saki 3 3, da dadin bakih da jan magana suka amince da tafiar 
 • Hajia Ama da Umma Hajja ne zaune parlon Umma Hajja su ka tasa Jikokinsu gaba suna musu nasiha me ratsa jlki da ban haquri, tare da jadadda musu haqqin zaman tare da na auratayya, Da kuma ban Haquri, duk wanda yyi haquri zai ci ribar rayuwa a karshe suka samusu Albarka. sannan sukayi umarni da yanmatan suje su hada kayan buqattunsu kafin a aiko musu da wasu, haka suka miqe suna matsar Kwallah kowa yayi sashensu don shirya kaya..

   

About Ismail

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *