[Advertisements⬇️]

RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 12 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 • RIKICIN WANI GIDA


 • CHAPTER 12
 • Parlorn yayi tsit kamar ba kowa cikinta sai qarar fanka, Tsoho ya cigaba da magana, kuma za,a daura auren nan ranar jumaah me zuwa ma’ana nan da kwana 7, flrgigit suka dawo hayyacinsu kallo daya zaka masu duka zaka ga tashin hankali a fuskokinsu, Jawad ke maimaita sunan fadila a bayyane tare da kallon inda yammatan ke zaune kuka yaga rabin ransa bilkisu keyi, zuciyarsa ya hau zafi da ya hango fadila rakube tana cizgar kuka, lokaci daya ya tuna rashin kunyar tada shirga mishi, nan da nan haushin ta da tsanarta suka darsu a ransa da sauri ya girgiza kai wlh ba zaiyuwu ba da sake.
 • A bangaren Mua’amar kuwa Tunani yake yama za ayi ya auri watan da ba Hanifa ba, ai ba zai mayuwu ba da sauri ya rarafa gaban tsoho tare da ririqe mai kafa, yace tsoho, kar kayi mun haka, ka taimakeni ka bani Haneefa, haneefa ce rayuwata. Baba Mudassir yace kai Mua’amar meye haka?Tsoho ya daga ma baba mudassir hannu yace, barshi ya gama, ina jinka Amar, k0 kunya be jiba ya cigaba da cewa tsoho ka taimakeni, kaji tausayina ya qarashe fadi tare da kuka me tsuma zuciya daya kubce masa, Tsoho ya shafa: kanshi a hankali yace kayi haquri, na san menakeyi, Wata rana zakayi Alfahari da wannan hadin nawa, Girgixa kansa yayi da qarfl tare da runtse idanuwa, Samir ma ya matso yace tsoho dan Allah kar ka rabani da lslahulkhair ya xa ayi ka hadani da Amira? Damm gaban Amira ya yanke ya fadi, bata qin samir hasalima ita bata yi baqincikin wannan hadin ba, fargabanta daya Samir Islah yakeso, to idan samir ya qita to wa zai sota? Suraj zaiyi magana Baba Hassan ya wurga musu harara shi da Zayyad ba shiri sukayi gum, Shi ko Namijin duniya wato Zaid, ko a jikinsa don ya san wannan abu ba zai yuwu ba, ya ma xaayi ya auri wannan qaramar yarinya? In short ba me mun auren dole, ni banda mata da ta wuce badiyya so tsoho ma zai tashi daga wannan mafarki coz it will never happen.““
 • Tsoho ya bi su duka da ldo, Kuka sukeyi ba mazan ba ba matan ba, Idonshi ya tsaya kan Ruma ganin hawaye kwance kan fuskar Maysah yasa zuciyarsa sosuwa, ya furta a hankali Rumah zo nan, a hankali ta miqe ta nufa gunsa, yace Rumah me ya saki kuka? Rumah bakya son wanda na baki? Kuka me tsuma rai ta fashe da shi. A hankali daidai yanda zaijita taceTsoho kar ka mun haka, ya zaayi ka hadani da Yazayd? Tsoho ko ka manta rannan da-da sauri ya katseta ta hanyar sa hannu a bakinshi, ta girgiza kai, ta dan daga murya ba zan yarda ba tsoho, ba zan yarda ba, Mashayi? Mazi–tasss kakeji, Baba Abbakar ya kasheta da mari, abunda be taba yi mata ba kenan, Maysah ta dago idanuwanta da suka rine sukayi jazirta kalli babanta, a hankali tace Appa ya nuna ta da yatsa, yace ke kin isa Tsoho yayi miki zabi kice ba kyaso? Toh idan ni na haifeki baki da mijin da ya wuce Zaid, sai anyi auren nan, sai dai ki mutu Rumaysa, cikin isa da gadara Zaid yace wai wani zaid din? Ni fa ba zan auri wata yarinya a dangi ba, ina da wacce nakeso, Uncle Abbakar ya wurga mai wani mugun kallo, duk tsagerancin Zaid sai da ya ji shakkun Baban Maysah. Hajia Babba dake zaune ta gama cika pal, tace ai ba qarya yayi ba, duk cikin wannan hadi ba wanda xaiyuwu, babu yanda xaayi ni kojikokina su hada iri da dangi Aljanu da Mayu, to Alhaji tun wuri ka chanza wannan maganardon wallahi ba zaiyuwu ba, wannan maganar maganar nosense ce, maganar banza,jikana ya aurijikar Hajjo ko Aishalle? Sai dai a mafarki wollai, Parlorn yayi shlru, ta inda Hajia babba ke shiga ba ta nan ta ke fita ba, sai bambami take tayi. Kowa ya xuba mata ido, sai zagezage take tayi, Miqewa yayi sakamakkon jin kanshi da ya sara Qirjin shi ya shiga yi mai zafih ya sa hannu ya dafe, ba wanda ya lura dashi don hankalinsu na chan gun Hajla Babba da ke ta faman masifa ita ba zata hada iri da dangin mayu da Aljanu ba , Hanyar Qofa ya nufa hannunsa dafe da qirjinsa, ji yayi qaffafuwansa sun gaxa daukar sa jiri ya fara dibarsa, sai ji sukai Timmm Tsoho ya Xube qasa, nan aka shiga rigerigen nufan inda tsoho yake, Baba Hassan ne ya sa hannu wurin hancinsa beji tiririn nishinsa ba, cikin kaduwa ya ce A dauko mota, Jawad Zaid Muammar Suraj da Samir ne suka flta da gudu don dauko mota hankalin su Ya tashi ganin ba alamun Numfashi
 • tattare da tsoho, Suko matan kuka suka sa barin ma Maysah, ita ko Hajia Babba kuwa kururwa take tana cewa waiyo Mallam Kar ka mutu ka barni, kayi haquri kar baqin cikinmu ya kasheka, ka tashi Mallam. Baba Usman ne yace haba Hajia ce miki akayi ya mutu? Tayi saurin cewa Auuu be mutu ba? Be tanka ta ba anan ne Suraj Ya shigo ya ce baba ga motan nan gaban parlor, nan su jawad suka shigo ko wannensu ya dauko motarsa, nan Zaid ya cicibe tsoho shi kadai yayi wajeh dashi, bayan motan da ke pake gab da parlon ya shimfideshi a baya, kowa ya samu mota ya shiga Suraj kuwa da Tsoho ke bayna motarsa ya zagaya ya ja Motar sai Asibitin Dr Munnir na Alheri Hospital. Convoy akayi, saboda kidima Hajia babba da Hajia Ama, da Umma Hajja mota daya suka shiga, motar Zaid, Iya rudewa sun rude, hajia Ama da Umma hajja dai hawaye suke don tun rasuwar Baba Rabi’u basu qara ganin tashin hankali ba irin na yau, ita kuwa Hajia Babba bata fasa ihu ba tana Allah kar ka kashe Alhaji, Allah ka raya shi, Waiyo ni karime, Zaidu ba a iso bane? Zaid da ya qulu sosai, yana son Tsoho sosai yana fargaban rasa shi amma wannan matar ta cika mai kunne, tsawa ya daka mata yace idan ba ki min shiru ba zan zubar dake a nan, da sauri ta kama bakinta.
 • Islah a bayan mota riqe da hannun Maysah riqe da hannun Fadila a bayan motan Samir, Amira na gaba kowannen su Hawaye ke bin kuncinsu, tunda suke a rayuwansu ko ciwon kai basu taba ganin yayi ba. Amma yau shine harda yankejiki ya fadi, Suna cikin matsanancin tashin hankali wanda roqonsu Allah ya tashi kafadar Tsohonsu..
 • Ko da suka isa Asibitin Already Dr’s and Nurses najiran su a entrance don tun a hanya Baba Gambo ya kira Dr Munnir ya Sanar dashi komi. A haka aka daura tsoho a kan gado akajashi zuwa A&E wato Accident and Emergency. Da sauri Liktoci suka du’kufa gurin ceto ran tsoho, Zuriarsa na wajeh hankalin su tashe yake, kowa da kallan tunanin da yake, Hajia Babba sai kai kawo take binibini ta lewa dakihn, Hajia Ama kuwa ta kame guri guda da tsura ma dakin ido, bayan kamar rabin awa, Dr Munnirya flto yana shar’ce gumi, da sauri suka xagaye shi, ya kallesu ya girgiza kai, yace ku muje office. Har wasu saida suka riga Dr shiga ofishin shi, nan da aka zazzauna, wasu kuma na tsaiytssye don duk Girman Opishin Drya gaza dauke lyalan Zailani yayi.. Dr ya kalli Manyan Yaran Tsoho,Yace ya akayi haka? Su Baba Hassan duk suka zaro ido? Yace ya kuka bar Ciwon Zuciya yama Tsoho mummunan kamu farat daya? Duk suka dau sallalami, Ya kuka yi wannan sake? Hajia Babba tace wlh baqin cikin mu ne, Waiyo ni kaina. Zaid ya watsa mata mugun harara, ya cigaba da cewa, munsamu mun shawo kan matsalan da qyar. toh gaskia Dole ku kiyaye bacin ran sa, dole kuke mai abubuwan da yakeso, nd ku nisantarda shi daga abubuwan da baya so, Nd dolenku kumai abun da yakeso kafln ya farfado, don gudun hakan na iya sa wa zuciyarsa ta buga farat daya. Gaban kowan nensu ya fadi, Mu’ammarya girgiza kai ya fita daga dakin, Jawad ya bishi hakan nan Zaid. Duk aka bisu da ido, Dr yace idan kuma kun gaji da hidimar sa tunda ya tsufa ku barshi kawai ya mutu, Hajia babba ta zunduma uwar ashar, Dr kaci Kwal Ubanka, mu barshi ya mutu fa kace? Yace ahtoh, ai don ina ganin abunda ya ke so me girma ne, ba zaiyuwu ba, tace Dole kuwa zai yuwu, dole a aurar dasu ga maqiyansu,. Ke kima wadannanjikokin naki magana, dole suke aurensu ba don naso ba, sai don ceto ran Mallam. Ta miqe tare da fadin tashi dan Usmanu, muje mu ga yaran nan. Balki ku biyo mu duk suka bi bayantajiki a sanyaye, ya rage daga Zuriar Umma hajja sai na hajia Ama cikin ofisihn Dr. Dr ya miqe yace toh bari na barku ku zanta.
 • Ai wallahi ba zan yarda na auri wata Islahulkhair ba, Ya zaayi ma hakan? Da sauri Aunty Sadiya ta riqi danta tace Amar baka fini Tsanar wannan hadin ba banqi ayi tashin hankali ba don a fasa auren nan, but bamu da choice, i love my Father, i can’t watch him die, please son u nd bilkis will listen to me and marry dem for a short period of time, da Yaji sauqi xaka saketa ka auri Hanifar ka kaji? Kema dole muke matsa ma Suraj ya sakeki kinji? Bilkisu tana kuka tace indai wannan zaisa Tsoho ya tashi ya ji sauqi toh wlh ko waye xan aure shi. Aunty Sadiya ta rungumeta yauwa diyata. It’s just for a short period of time. Aunty Abida ta kalli nata yaran tace dat goes same for, Zaid, Jawad, Hanifa bama son wannan hadin but we love our Father. Shine Gatanmu da duk wanda muke taqama dashi. We cant let him die. I knw y’ll love Tsoho nd Ya’ll sacrifice for him ryt suka gyada kai, then do dis for him okay? Nd remember itsjust for a short period of time…
 • Aunty Zainab rungume take da dants Samir daga chan gefe Baba Gambo na kallonsu cike da takaici, kuka ko Samir kamar mace? Amirar Annoba ce? Aunty Zainab ta kalleshi ta mai Alaman ya fita, Baba Gambo yayi gaba. Ta shafa summar kansa tace ‘Samir’ yace Mami kiyi shiru, dole zan Auri Amira don ceto ran tsoho Amma dole zanyi kukan rabuwa da Islah. Mamin tace haba Samir, abunda yayi Islah shi yayi Meerah, ka duba ka gani, da sauri yace wlh shes nothing like dat-yi shiru mana. There are times da zaka so abu sai Allah ya hanaka don ba Alheri bane a gareka, sai ya Musanya maka da abun da yafi Xama Alheri, Maybe Islah ba Alheri bace a gareka, Maybe Amirar ce Alheri, kuma lta Allah Ya tsaga a rabonka da ita. Think wise son, u are d bravest i’ve ever seen, ya qirqiro murmushi yace i will marry Amira. Tayi murmushi tasan bai amince da Amira bane Aa sai dai don kawai ya faranta ran maminsa.
 • Toh ni ba sai nace muku komai ba, duk nan kun mallake hankulanku, nd kunsan whats right, so i trust u to do the right thing, Baba Hassan ne ke wannan maganar.Umma Hajja tace ai na san Yanjikoki na da ladabi da biyayya, masu son Farincikin Uwayensu, nasan ba zasu barson zuciyarsu ya shiga cikin wannan Lamarin ba, Baba Hussaini yace toh ya kuka ce? Hajia Ama tace ai nasan jikokinmu sun Amince, don suna son wannan tsohonsu sosai koh? Rumaisah tace idan akwai wanda yafl makaho makanta, kurma kurumta gurgu gurgunta, zan aureshi don ceto ran tsoho, wanda ya soni ya qaunace ni, Fadila ta kalli Suraj, tace nima na amince zan auri YaJawad duk da na san aurensa baraza ne a kaina, Amma ina son Tsoho sosai, dole nake haqura na ba Tsoho abunda zaisa shi farinciki. lslah na matsar kwallah tace Zan auri Ya Jawad. Zayyad yayi karaf yace muma mun Amince zamu auri Hanifa da Bilkis Allah ya sa hakan yafI zama Alheri Aka Amsa da Amin. Hajia Ama ta kalli Baba hussain tace na gaya muku yanjikokina Akwai ladabi Biyyaya. Yace ai nagani Allah muku Albarka Ameen…
 • Hajia Babba ta shigo da zurianta a bayanta fuskokinsu murtuk, suka zazzauna. Dr Yashigo yace toh duk kun shirya ba Tsohonku abun da yakeso? Sukace Ehhh. Yace toh MashaAllah. Allah ya tashi kafadun shi. Yace kuma a barshi ya huta, yana so kowannensu yaje gida don be son hayaniya. Haka Baba Hassan ya sa aka tattarasu akwa maida Gida. Da qyar Hajia Babba ta amince zata tafih. Daga shi’ Sai Baba Ussaini suka tsaya…

 • GASKIAN LAMARIN.

 • Kwana 2 kafin (2days Back)
 • TSOHO zaune da Family Doctor dinshi Dr Munnir, kuma amininsa wanda ya san duka Sirrin Tsoho da yanayin GIDAN nasu, , amma Tsoho ya girme mishi nesa ba kusa ba, don ko tsaran su Baba hassan ne, Tsoho yace Dr bansan yanda za’ayi yi na hada auren nan ba, don kasan dan yanzu ka haifeshi ba ka haifi halinsa ba, suna iya bijire mun suce tunda basu na haifa ba zasu mun rashin ta ido balle dukkansu soyyaya suke, toh ina tsoron su ki Amincewa. Dr ya nisa yace Akwai Shawara idan zaka iya, Tsoho yace me ke nan? Dr ya sausauta murya ya ma tsoho qusqus a hankali me kama da rada, Tsoho yayi daria yace hakan ma zaayi, ta wannan hanyan zan magance duk wata matsalata. Zanga idan Zasuyi man Hallacin nan, Zangani idan ina da mahimmanci a rayuwansu, naji dadin shawarar nan amma taya zanyi na zube qasa har na dauke numfashi na? Yace kar ka damu, akwai maganin da zan baka ka sha, beda illa. Zai taimaka maka gun aiwatar da qudurinka, kuma idan aka kawo ka asibiti, da drip din da Allurorin da zaka sha duk masu Amfani ne game da laflyayyen jiki kamar su Bcomplex d.s. so karka damu, ba abun da zai shafi Lafiarka. Tsoho yayi murmushi yace nagode likita Allah yasa mu dace yace Amin…
 • Toufa jamaaa kuna jin wannan plan din na Tsoho? Dukyabi ya tada ma Zuriarsa hankali  
 • Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]