[Advertisements⬇️]

RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 10 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

RIKICIN WANI GIDA

CHAPTER 10
Maysah tace ina zaki kaimu? Ki tsaya, Fadila tayi parking tare da sauke ajiyar zuciya, first of all kar da ki qara yi man haka, Shikuma Jawad din ya qara gigin tabani yagani, zan bashi mamaki wlh, Maysah tace kiyi haquri’ sis let it pass, fadila tace ya wucei, Maysah tace let me drive, ba musu fadila ta fito ta koma sit din Maysah ita kuma ta koma ta shige tare dajansu suka nufa Gida.
Jawad ke hada kayanshi, shi zai koma Gombe, tunda uwarshi ta haifeshi ba a taba Embarassing dinshi haka ba, kamar ace yarinya kamar wannan fadilar ta gaya mai magana bema ta komai ba? Dole ya ne yabar garin, haka ya bar Gidan be ma kowa Sallama ba har bilkisu. Ba wanda ya san anyi, Mu’ammar be fada ma kowa ba, Maysah ma haka. Bilkis tayi tayi ya fada mata abin da yasa shi tafi ya qi fada, sai kuma ta sa kuka wai satin shi 3 bezo weekend ba, gashi yau friday bazaizo ba? Bayason kukanta yace kar k damu zan biyo Jirgi Insha Allah Yau din nan, just to see u, don ni zaman Maid ya Isheni, dadi kamar xai kashe Bilkisu ta shiga kichin don hada ma Yajawad Abinci. Kafin ta shiga ta tsara kwalliya. Badiyya ce ta flto daga Airport din Garin London, kasancewar ba yau ne ta fara zuwa qasar ba, ta sha zuwa da Alhazawanta, Taxi ta tsaida tare da fadawa ciki, tace ya kaita cikin gari, sai da sukayi tafla me nisa kafin ta sauka ta biyashi, sannan ta tsaida wani Taxi din, tace Ya kaita Illford shopping center, ya kaita ta sallameshi, ta shiga ciki, wurin Babban wuri ne, ba shagon da babu, wuni bangaren yara ta nufa, ta siya Toys da kaya, kafin ta matsa ta shiga lodo chocholates, tayi siyayya sosai kuma ta kashe kudi, Fitowa tayi ta tsaida Cab, tace akai ta Rand Street, Ba ajima ba suka iso Unguwar, ta lumshe ido tana tunano kwatancen gidan Zaid Ali a qwaryar boka. Ta na tunowa ta na ma me mota kwatance sai ga su har gaban Gidan, a lokacin har dare ya farayi, ta biyashi tare da kinkimar leda ta yi qofar gidan, hannu ta sa ta danne Bell din.
Wata hadadden yarinya nagani da ba ta wuce 20years ba tsaye kan stool, gaban ta wani ne da alamun dai mijinta ne hadadde ne me cikar kamala, tie ta ke ciremai, shi k0 sai kissing kumatunta yakeyi yana mata waqan My short wifey, tana mutsu mutsu tace Yazayd kaga dai ka Bari, sauri’ nake da wanne zanji da rigiman babies dinka k0 da rigiman Ka? A lokacin ta gama kwance tie din, ya sunkuceta cike da so da qauna yace Yarinyata,bazan gaji da fada miki ina sonki ba, i love u so much. Hanyar daki yayi da ita sukaji an dann Bell, Zarah tayi saukowa daga jikin mijinta, tace I will get dis, i think mummyn becky ce, kaje ka fara shower din kafin nazo, idan kagama ka fara masu Miemee da Blebie, tana fadan hakan ta na tafia don bude qofa, unlocing qofar tayi tare da bude qofar, Gabanta ya yanke ya fadi, mamaki ya cika Zarah, hasken da ta qara besa ta qi ganeta ba Baki na rawa tace Ba-diyyah, Badiyya a ranta tace shegia guntuwa sai kyau take qarawa, a fili kuwa murmushi tayi tace Hello Baby Zarah, its good to see u too, ta raba ta shige gidan tare da barin matar gidan a waje, zarah ta shigo tana qoqarin qaqaro murmushi sannu da zuwa, ta shiga kicin ta kawo mata juice da cookies, Zayd ne ya sauko yana Yarinyata ke da waye? Maman becky~ maganar ta maqale a fatar bakinshi sakamakon ganin wata yayi kamar Badiyya. Badiyya ta miqe ta tako kusa dashi, murya qasa qasa tace Hello Luv, Zarah tayi saurin shan gabanta, me ya kawoki Gidan na? Diyya tayi murmushi tace mutum yana tare da wanda yakeso, nazo qasar ne, shisa nace sai nazo na gaidaku, ban kyauta ba? Zarah tace kin kyauta mungode, now leave, Diyyah ta kalli Zaid Ali tace how rude of ur wife, is dis how she treats ur visitors? Zaid ya jefeta da wani irin mugun kallo, yace badiyya ki bar gidan nan, tace not until i have wats rytfully mine back, Zarah da qarfih tace kina hauka, wasu yara yan duguiw guduiw kyawawwa suka fito da gudu daga wani dakih, Badiyyah ta nufesu tare da
rungumesu, Hello sweethearts, look wat i bought for u, ta miqa musu ledojin tsarabar da ta musu, Miemee ta kalli uwarta tace Mummy who is she‘!? Zarah tace miemee do u remember dat monster dai was chasing u in ur dreams?? Da sauri ta gyada kai Tace is she d monster mummy? Zarah ta daga mata kai alamun Eh. da gudu miemee ta ja er uwarta biebee sukayi daki. Badiyya ta dago cikin duniyanchi tace dats very brave, kina brainwashing yaranki, mesa baki fada musu nine dia daddy’sfirst love ba? Zaid ya daka mata tsawa Enough, get out now before i call d cops, nd u knw here u dont bribe cops, so ki fita tun muna shaida juna Badiyya, Zarah tace u are asking her nicely, ta finciko badiyya ta wurgar a waje kamar wasu kayan wanki, ta koma da sauri ta dauko ledojijinta ta watsa mata su a fuska ta nuna ta da yatsa stay away frm my husband. Kika sake dawowa gidan nan zakiga abunda zai faru dake.Ta kullo qofar sa qarfih. Zaid ya sunkuceta yace karki damu, she isnt going to ever come back, nd if ta qara dawowa, she is going to tace me not u. Ta rungume shi tace i love u ya zayd lets go nd calm ur babies down yayi murmushi tare da nufar dakin yaran da ita
Kuka Badiyya keyi sosai, wai itace nan? quwa tayi tana bin hanya tana kuka, Zarah nd Zayd must pay for dis, wayarta ta ciro ta latso Bokanta, tana kuka tace Boka sun wulaqantani boka ina so kayi musu–shiru tayi ta bi wani gu da kallo, Numfashinta qiris ya rage ya dauke sakamakon wanda ta gani tsaye daga gefe sanye da 3qtr da top sai Hula Qube ta mazan hausawa, waya yakeyi kuma da harshen hausa, Boka yace hello hello diyyan shagali kina jina? Da sauri Badiyya tace zan sake kiranka, ta share hawayenta ta nufa gurinsa tun da ya dago kai ya kalleta be dauke idonsa ba, ya cigaba da wayarsa Jawad kasan dai banda manyan kaya? Ka dinko min kuma kace ma tsoho ba sai ya biyoni ba, cikin satin nan zan dawo, Bye i gotta go. Daidai nan Badiyya ta fashe da kuka da sauri ya qarisa gunta Hey Miss, are u okay? Ta girgixa mai kai, wat happened to u? Cikin kissa tace yau na xo banda ma sauki, kailonta yayi yace kina jin hausa ne dama? Ba gashi nayi kaji ba? Muje na sama maki masauki, tace bansan kowa ba, pls take me wit u, bansan hannun da zan fada ba, kaga kai musulmi ne danuwana pls ka taimakeni ya danyi guntun tsaki yace da uban wa ya kawo ki nan din? Tace wlh Grads naxo, ya tsaida musu Cab, ya shiga gaba ta fada baya da sauri, Wooow take fada a ranta, wannan gayen ya hadu,ban taba ganin hadadden gaye kamarshi ba, yo wannan ai ya fi wanda tazo qasar danshi kyau, Ai dole zatayi aiki kan wannan, dole take samun wannan a matsayin Miji, tana tunane tunanenta suka iso wani dan qaramin gida, Ya fito ta bi bayanshi ya bude suka shiga, har dakin shi ya kaita, yace ki kwana a nan kafIn gobe na sama miki gurin zama, ta yi mai far da ido, tace Nagode sosai Allah ya saka da Alheri. Ya miqe zai fita, tace Bawan Allah kai dan Nigeria ne? Ya daga kai eh, wani gari yace Maiduguri, tayi farrda ido, laaa ashe dan garin mu ne, pls ya sunanka? Cikin qosawa yace Sunana ZAID MUDASSIR ZAILANI Badiyya ta maimaita sunan Zaid sunanka? Ya ce eh sunan kenan, ya bar mata dakin, badiyya ta fada gado tana murna, Zaid ya tafi Zaid ya dawo, wannan zaid din yafi Zaid Ali kyau da wayewa, to su zarah a jiqa zaid a sha na sami wanda ya fi shi komai, daman wanin hanin ga Allah baiwa ne wannan zaid din bazan yarda ya kubuce mun ba, haka ta kwanta tana me farincikin wannan sauyi da Allah ya mata. Zaid M.Zailani jikan Alhaji M.Zailani, da Hajiya karime da ga Mudassir da Abida Fari dogo me cikar halitta, Shekarunsa 28, a yanzu ya gama karatun likitancinsa a nan Oxford University, Zaid ya cika komai saidai matsalarsa Daya shaye shayen da yakeyi da taurin zuciya, be bin mata, a ganinsa mata matsala ne, yanmatan turawa sun sha chusa kansu gunsa amma ya na basarwa, Tina kadai yake saurara itama Iyakarsa da ita romance be zarcewa da yaga ta na neman wuce gona da iri zai tsallaketa, Zayd be shakkar kowa abunda ya sa agaba shi yakeyi, ba me chanza mai raayinsa tun yana qarami, ko Jawad sai dai ya shafa mai laflya gurin Kaffiya, sun Sha fada da Zayyad, Lokacin da suke makaranta Zayyad na mai nasiha kan shayeshaye, amma sai ya fara mai masifa yana fadin its a free world, so kowa yayi harkan gabanshi, duk Zuri’ar M Zailani daga iyayen zuwa jikokin ba me shan ko da sigari ne, sai Zaid, be flye shan taba ba sai Giya, shan giyansa ma na masu aji yakeyi, sai dare yake sha. Hakan ya kasance a yanzu, fridge ya bude ya dauko kwalbar Giyyanshi ya fara kwankwada, yana lumshe idanuwa. Badiyya ce ta flto daga dakih ta na neman kicin Ganinshi tayi kwance kan 3sitter, daga shi sai singlet, nan da nan diyya ta kwadaitu da shi, haka ta haye Zaid, cikin bacci yaji ana shafanshi, ya miqe da sauri idanuwansu suka qanqance, Zaid ya hankadeta, cikin tangadi yace keee, are u trying to rape me?? Diyya ta mai far da ido, ta sa hannunta kan bakinta tace mai shhhh, ya koyi shirun, ta fada kanshi ta shiga kissing dinshi, ya biye mata, tana qoqari zuge mai belt yayi saurin watsar da ita a qasa, ya nuna ta da yatsa dont even think abt dis. Yayi cikin daki ya barta yashe a qasa, side smile Badiyya tayi tace muje zuwa. Daki ta bishi ta ganshi yashe kan gado, gyara mai kwanciya tayi ta bi ta baya ta runguneshi, suka yi bacci, assalatu ya tada Zaid, ganin Badiyya yayi rungume dashi tana sharar bacci, komi da ya faru jiya ya dawo mai, ya qare ma Badiyya kallo, kyakyauwa ce, daman akwai masu kyan nan a Naija, well haka yake son mace wayayya, ya miqe ya shiga toilet yayi wanka tare da dauro alwala, be tada ta ba k0 da yayi sallah, ya shiga kicin dan hado musu brk fst, 8am ta flto Tana wannan yauqi tana kwarkwasa ta zubejikinshi,ta bashi peck G’mrn My Zaid, be hanata abunda take mai ba, m so hungry, yace i cooked u brkfast, tayi farrr rely? Show me, Yace i will let me, ta gane me yake nufl ta daga shi da sauri, ya riqo hannunta ya kaita har kichin, suka zauna suka ci tare, harda feedingjuna, cikin kwana 3 badiyya ta siye zuciyar zaid, haka yake son Matan Naija su kasance a waye, kullum suna maqale da juna‘ Badiyya ta fahimci Zaid, iyakanshi Romance. Sai ta daina zaqewa tana biye mai yanda yakeso.
Ta kalleshi cike da qauna tace My jawad, wats kroubling u dis days? Yayi faking smile yace bakomai baby, tace me ya sa ka tafi ba tare da kamin bankwana ba 3weeks? Kuma da kazo last week bamu samu munyi magana ba, me ya faru? Yace bakomi kissu na, tace har ka fara boye mun abu k0 ya jawad? Noo baby ba haka bane toh menene? Nan ya kwashe komai ya gaya mata game da abunda ya hadasu da fadila, bilkisu ta tashi tana huci kam balaee, Shine ka qyaleta? Yace hey babe chill mana, ya wuce, tace wlh be wuce ba, ya kamo hannunta duka biyu yace nace ya wuce ko? Ta ce naji, ta miqe ta barshi zaune.Dakin Aj ta shiga ta na huci ke lpya? Tace kinji kinji, ta kwashe komai ta gaya mata ita ma tace balaee, harda Ya’amar dina aka ma rashin kunya, tashi muje sassan su.suka fita gabaki daya.
Hajia Ama zaune tana bare gyada, su Bilkisu suka shigo, sai da gaban hajia ama ya fadi don ba zata iya tuna ranar qarshen da suka shigo sassanta ba, Ba su da niyar gaisheta, tace mai gado lapya? Bilkisu ta watsa mata harara hanifa tace ina maras kunyan jikarki? Fadila nake nufl Hajia Ama tace ba sa nan suna chan gidan Yayanku haflz dukkansu 3, yayansu dai ba yayanmu ba, don mu bamu hadajini da mayu da aljanu ba, hajia Ama tace kuyi hqn’, Bilkis tace idan bamuyi hqr ba hauka zamuyi? Suraj da Zayyad da suna cikin dakin Amma, tun shigowar su sukejin su, Suraj yace yaran nan basu da kunya, ya fita Zayyad ya bi bayanshi, ke uban wa kuke ma magana haka? Hanifa ta kalleshi galala ta watsar, dan ubanki nikike ma wannan kallon? Tace an kalla din, bilkis tace ke kika tsaya kulashi, ni ai idan na raina bola ko shara ba zubawa cikinta, tass kakeji ya kamtseta da marih, ya juya ya ba hanifa nata Allah ya isa mugu azzalumi shege daniska, charr ran maxa ya baci, belt ya ciro ya fara shauda musu, Zayyad ya qwace su yace ku gudu, yaja shi yana haba, meyasa ka biye musu, hajia Ama ma fadan biye musu da yayi takeyi. Da gudu suka yi sassan Hajia Babba suna kuka, hankalinta ya tashi, da qarfl ta fito, wai waye, uban me kuke ma kuka? Nan suka shirga mata qarya da gaskia, wai Zayyad da Suraj ne suka kullesu suka musu dan banzan duka, ko dankwali bata sa ba tayi sassan Hajia Ama da sauri masifa na cinta, Aishalle yau sai kin ci buhun ubanki, kika sajikokin ki suka ma bayin Allah duka ko? Nima yau sai munyi na mu, Ama ta fito, suraj da Zayyad na bayanta, tana kar ku sake kuce komai, kuna jina? Ama ta kalleta tace kiyi hqr yaya karime, ba haqurin da zanyi, shegu mayyu wanda suka gaji maita, sai na daka ki yau cikin gidan nan, tayo kanta gadan gadan ta maqure nata wuya, Suraj ya naniko hajia babba ya watsar a qasa, wani irin Ihuuu hajia babba ta sake kamar an sa Lasfika, daidai nan Jawad ya iso, yana zuwa ya sakar ma Suraj nushi a hanci, suraj beyi watawata ba, ya rama nan dambe ya kaure, Zayyad yazo da niyyar rabasu, Jawad ya kaimai nashi nushi a baki, nan zayyad ya zuciya ya rama, sai abun ya koma 2in1,lhu su hanifa keyi hajia babba nayi, Hajia Ama tayi saurin shiga sassan Umma hajja don ta ga k0 su baba Abbakar na nan, fadan qarfi akeyi anan fadila, Maysah da Islah suka shigo gidan, ganin fadan maza yasasu sakin kuka duka, Maysah tayi sassan Tsoho da gudu, bawanda ya iya shiga fadan sbd duk mata ne, Islah tayi boys qrts don neman Yasamir. Harjawad ya far habo gajini ta baki. Shigowan shi gidan kenan, daga nesa ya hango su suna dambe, hango jawad yayi yana firda jini, dan uwanshi uwa daya uba daya aka ma wannan taron dangi? Balaeee, yarda trollynsa yayi ya cire er whyt top dinsa yayi wurgi da ita, ya ruga da gudu, wani tsalle yayi ya chafko Zayyad ya hadashi da bango, ya finciko Suraj ya dinga kaimai nushi, abunka da wanda ke gymin Jawad ya dago kai ya kalleshi ya sakar da murmushi suka tarar ma Suraj, suna duka, daidai nan Tsoho ya iso gurin Ba kasafai yake fitowa daga parlomsa ba, amma yau shine har sassa, Su hanifa sai kuka akeyi, hajia babba na ganin tsoho ta qara fashewa da kuka, Samir ya rugo da gudu tare da Mu’ammar zasu shiga hannu Tsoho ya dagabmusu alamu su tsaya, tsoho yace ku bar fadan nan, Ku bari nace, Jawad ya bar dukan Suraj, shi
ko wannan cigabawa yayi da kilar suraj kamar Allah ya aikoshi, tsoho ya qara cewa nace ka bari k0? Ai da alamu be jin tsoho, da qarfl Tsoho Yace ZAIDU

Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]