[Advertisements⬇️]

QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 7 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

QADDARAR SUMAYYAH

CHAPTER 7Hannunta riqe kan qugunta tace “Dankali ne ta barmin ya huce,ni kuma ban iya ci ba,abinci rana kuma gaskiya bazan zauna qanwar qanwata tana dafa abinci tana bani ba,bayan ba cewa nayi bazan iya ba”, shiru yayi yana ci gaba da kallonta zuciyarsa na quna,da qyarya samu ya hadiye wani abu mai zafi a qirjinsa sannan ya gyada bayan wani tunani da yayi ” yayi kyau”kawai ya fada sannan ya ratsa ta tsakaninsu ya fice cikin bacin rai.Sa kai sumayya tayi itama tana shirin bin bayansa “Banza munafuka,idan ma ke kika nuna masa an gaya miki wani abun zai min” bata kulata ba tayi ficewarta ta koma dakinta,tana kammala sallar isha’i ta tura qofarta tayi kwanciyarta.
Washe gari shi ya shigo ya tada ta sallah,ta miqe tana mutstsuka idanunshi a kanta,sam bata ma ji kiran sallahr ba yau “Ki tashi haka kiyi sallar asuba” ya fada yana qare mata kallo ta cikin rigar baccinta wadda tayi mata kyau “Kinyi kyau sosai my sumy” ya fada sanda take qoqarin saukowa daga kan gadon,sai ta waiwayo ta dubeshi,dan qaramin murmushi ta sakar masa wanda yaso rudashi,ya qarasa inda take tsaye tana zura hijab dinta don fita waje tayi alwala,ya janyota da baya ya rungumeta yana rada mata “Nayi missing dinki sumy ta” sai ta zare daga jikinsa ta waiwayo tana dubanshi idanunta a waje,ta maida su kana ta langabe kai “Kai ya mukhtar,ni ban fadi haka ba sai kai dake da amarya?” Baice komai ba sai wani
guntun murmushi da ya saka ya sanya kai yana Ficewa tare da ce mata ta fito tayi salla. Yauma kamarjiya ta fito ta kammala aikinta,saidai sabaninjiyan yau a bude taga dakinsa da alama yana ciki,saidai bata san ko me yake yi ciki ba,tana fitowa daga wanka sukayi kacibus,ya zuba mata ido yana dubanta “Yanzu sumayya ko ruwan wanka ma an daina bani?” Ya fada murya a karye “Ba haka bane ya mukhtar,na dauka aikin amarya ne wannan ko,amma kayi haquri akwai wani da na dora zan zuba a flask bari najuye maka” ta fada tana shigewa zuwa kitchen din da sauri.
Tare suka karya yauma,saidai bai aikata kiran fa’iza ba da kansa ya gaya mata tazo zasu karya yajuya ya fito,saidai har suka gama karyawar bata fito din ba,harya fita daga gidan. Tana kwance kan doguwar kujerar falonta tana hutawa taji sallamar anty dije,da sauri ta sauko daga kujerar tana amsawa don ko da wasa fa’iza wadda tafi maqotaka da qofa bata yi kuskuren amsawa ba.
Rungume anty dije qanwar maman nata tayi tana mata sannu da zuwa kana suka wuce dakinta,bayan gaishe gaishe da tambayarta zaman gidan ta gaya mata komai lafiya suka shiga hira,lokaci lokaci ta dinga tashi tana duba girkinta na rana da ta dora. Kammalawarta yayi dai dai da lokacin sallah,saboda haka anty dije tace sai tayi sallah kam taci abincin,tare suka fito anty dije tayi bakin famfo ita kuma ta nufi kitchen don gama kwashe abincin. A bakin qofar kitchen sukayi kacibus da fa’iza na shirin fitowa ita kuma na qoqarin shiga,hannun fa‘izar riqe da qatuwar kula data gama shaqewa da abincin data girka wanda a zahiri ko yara gareta yafi qarfinsu su duka balle cikinta ita daya,harara ta galla mata kana cikin daga murya tace “Gafara malama na wuce,da wani idonta kamar jiqaqqiyar aya” rabe mata tayi tazo ta wuce fuuu tamkar guguwa cike da tsoro sumayya ta bita da kallo. Duk a idanun anty dijen haka ya faru,ta kada kai cike da takaici ta wuce bandakin ta daura alwalar. Tana saka hijabin sallarta sumayyan ta shigo dakin dauke da coolers din abincin,tun kafin ta saukesu anty dije ta finciki hannunta tayi bedroom dinta da ita,gefan gado ta zaunar da ita kana ta zauna kusa da ita suna fuskantar juna,cike dabacin rai ta tsareta da ido sannan ta soma magana “Kar dai kice min sumayya tsoron kishiya kike?,kada ki gayan cewa kin fara nuna mata cewa kina tsoronta?” Da idanu sumayyan ke bin anty dijen cikin sanyi jiki.
Cike da zafi tace da ita “Me innarki ta gaya miki sanda za’a kawo miki abokiyar zama” duk sai ta rude saboda tasan cewa anty dijen ba dai zafi ba,tsab ta mareka ba komai bane idan ka bata mata,cikin tsawa ta sake maimaitawa “Dake nake,nace me innarki ta gaya miki?” Cikin rawar murya da in ina wanda tuni idanunta ya fara tara qwalla tace “Tace min na zauna da kowa lafiya,kada na daga hankalin kowa,kada na zalunci kowa kada na cuci kowa idan na cuci abokiyar zama na bata yafemin ba” Kai tajinjina ta kama hannunta tana matsawa da dan qarfi,cikin kakkausar murya ta sake ce mata “Tace ki zauna a cuce ki?” Kai ta kada,idanunta ta zaro mata “Ki bude bakinki kiyi magana” “A’ah” ta fada qwalla na gangaro mata. “Tace ki zauna a zalunceki ko a rainaki?”,nan ma ta amsa “a’ah” kai ta jinjina. “Da kyau …… me yasa kika fara bawa fa’iza qofar da zata rainaki?,me yasa kika fara nuna mata kina tsoronta” shiru tayi ta kasa bata amsa don itama bata san dalili ba Ganin haka ya sanya anty dije sasaauta fushin fuskarta ta sake matsowa ga sumayya “Bamu lamunci ki zalunci kowa bama balle abokiyar zamanki,amma …… bazan lamunci ki zauna ki zama bola ba,bazan lamunci ki zama raguwa matsoraciya ba,kishiyarki ba mai son zaman laflya bace,bamu ce ki biye mata ba,bamu ce ki zama mai son tashin hankali ba,amma sam bazamu zuba ido ki zama banza ba ….. kinsam wacece kishiya…kishiya ma irin taki sumayya” kai ta girgiza,anty dije ta soma warware mata komai,dukkanin kunnayenta sumayya ta bata,sosai maganar ke ratsata,sai ta dinga dauko ta maman naana tana hadawa da anty dije,tabbas dukkaninsu gaskiya suke gaya mata. a “Kada ki yarda naga ba haka ba kinajina ko?” Anty dije ta fada tana kama kunnanta da kanta “In sha Allahu” inji sumayya tana dan murmushi,dukansu suka fito anty dije ta tada sallarta ita kuma taje ta daura tata alwalar tayi sallahr sannan suka ci abinci,suna ci anty dijen na bata labaru kala kala na kishiyoyi,wani ya bata dariya wani ya bata mamaki wani ya bata al’ajabi. Har soro ta rako anty dije sukayi sallama,tana shirin komawa ciki taj qarar machine dinsa,hakan ya sanyata dakatawa ta bude mishi qofar ya shigo tana mamakin dawowarsa yau da wuri haka bayan duka duka biyar da ‘yan mintuna ne,saidai bata ce komai ba kamar yadda anty dije ta gaya mata ta koyi yawan dauke kai da yin shiru kam wasu al’amuran da ba cutarwa ne gareta ba,ko ba hiruminta bane,ko kuma bazai cutar ko ya amfaneta ba yin magana akansa duk da cewar dama can ita din ba mai shishshigi bace.
Da murmushi saman fuskarta take masa sannu da zuwa,ya kashe mata ido daya sanda suke shiga cikin gidan “K0 ki tambayeni ma taya akai ka dawo gida da wuri k0?” Murmushi tayi tana rausayar da kai “Ai ba laifi kayi ba,kuma mai gida da gidansa ai yana da hurumin dawowa duk sanda yaga dama”mintsinarta yayi a bayanta har sai da ta sanya dariya yace ” sarkin wayo da iya magana,ko yaushe duka kika koyi wannan wayon haka?” “Ka manta rainonka ce?“ Ta fada tana kashe masa ido daya “Gaskiya ne” ya fada yana sanya hannunshi cikin alhjihunsa ya fiddo da kwado(key) yana fadin


[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]