[Advertisements⬇️]

QADDARAR SUMAYYAH CHAPTER 16 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 • QADDARAR SUMAYYAH


 • CHAPTER 16

 • Mamaki fal zuciyar sumayya,kanta ya daure tamau,ta kasa furta ma komai sai kallon
 • mukhtar da takeyi,ta tabbata ba qarya ya yiwa fa’iza ba domin ba halinsa bane,amma
 • halayyar fa’iza har ta kai haka?.
 • “lna naki abincin?” Mukhtar ya tambayeta,ta katse tunaninta ta dago ta dubeshi
 • “Ya d’aki”
 • “Ki dauko,ban amince kema. a yau kici ba,ki zuba a |eda ki saka a share a zubar,shiga
 • kitchen ki samar mana abinda zamu ci koda indomie ce sai ki hada mana da qwai” ya fada
 • yana kashingida gami da lumshe idanunsa,tsam ta miqe ta flce don aiwatar da abinda ya
 • umarceta.
 • nhntn-tltihni-i-nnn-t-nn
 • Cikin kwanakin ta dage sosaida addu’ar neman tsari,ta santabbas sham nmutum
 • girma gareshi,zuwa yanzu ta kuma sallama kaidin fa’iza,ta fahimci irinsu matan da suka
 • dauki kishi ko a mutu ko ayi rai,irinsu wadanda zashiya aikata komai saboda kishi,sosai
 • take takatsantsan kan duk wani motsi da kai kawo nata a gidan,ba ruwanta da sabgar
 • fa’izan bare wani abu ya shiga tsakaninsu,koda fa’izan zata shekara tana takalar tashin
 • hankali bata bi ta kan(a,don ta riga ta tabbatar cewa akwai banbancin gida da kowaccensu
 • ta fito,bai kyautu ta biye mata su zamana kamar wadanda suka fito daga gurbi guda ba.
 • tittitQICO-nnnn-i-nn
 • Tun da asubahin ranar suka dinga jiyo kakarin amai a tsakar gidan nasu,sumayya ta
 • dubi mukhtar dake gefanta wanda basu jima da kammala sallar asubahin ba kasancewar
 • sun makara basu tashi da wuri ba
 • “Ya mukhtar,kamar kakarin amai nakeji fa a tsakar gida” shi din ma taji amma sam bai da
 • muradin f’Ita,tamkar bazai tanka ba sai ya daure yace
 • “Eh nima naji” yaci gaba da jan carbinsa,ganin yayi shiru ya sanya ta sake cewa
 • “Ya mukhtar ka duba mana,inajin kamar fa’iza ce fa” shiru ya sake mata ganin hakan ya
 • sanya itama ta tsuke bakinta tayi shiru tana ci gaba da saurarankakarin wanda yakefita
 • tamkar da kayan cikinta,ya kammala azkar dinsa ya haye gado abinsaya kashingida.
 • Zuciyarmusulunciya sanyata ta kasadaurewa,saita miqe ta fidda hijabinjikinga ta
 • nufl qofa,sanya baki yayi ya kirata tare da tambayarta ina zata
 • “Zanje na duba ne,bai kyautu da mutane cikin gidan ba kuma aqi Ma 3 dubata ba,bamu
 • san meke damunta ba” kai ya girgiza
 • “Dawo tausa nake so kimin”
 • “Kayi haquri naje na dubata din minti biyu kawai zan dawo sai na maka tausar”
 • “Idan ban isa da ke ba shikenan kina iya hakan” ya fada yana maida kansa ya kwantar kan
 • pillow,saijikinta yayi sanyi bata son saba masa ko kadan,saboda haka tajuyo a sanyaye
 • tahayegadon. 
 • A tausashe take masa tausar tana leqen fuskarsa ganin yaqi kulata,har ta soma tara
 • qwalla bata iya jure fushinsa,sai taji kawai ya birkitota ya danneta da rabin jikinsa yana
 • dariya qasa qasa
 • “Raguwa kawai sarkin kuka” ya fada yana lakucemata hanci,dariyata sakiya shigamata
 • cakulkuli daga haka suja shige duniyar ma’aurata wanda hakan shi ya hanasu Htowa da
 • wuri.
 • Qarfe goma ya gama shirinsa zaya fita,a tsakar gida daga can bakin qofar dakin
 • fa’izan suka ganta zaune dirshan a qasa,ta wani wargaje can qafa can qafa tana numfashi
 • da qyar,da sauri sumayya ta qarasa inda take tana fadin
 • “Hasbunallahu Iafiya fa’iza?”
 • “Banida lama” ta fada qasa qasada qyar,ta daga kaita kalli mukhtar da bai qarasogun
 • ba,yanatsayeabunsa bakinqofar dakin sumayyanyana daura agogo
 • “Yayamukhtar,koasibiti zamu?”Baicekomai ba sai hannunsa da ya sanyacikin aljihun
 • wandonsaya zaro naira dubu biyuya miqa mata
 • “Gashi sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya” ya sanya kansa soro ya tada machine dinsa ya
 • fice.
 • Tanajin rufe qofar gidan nashi ta miqe tamkar ba itace hajaran majaran ba,duk da
 • yanayin jikinta ya nuna bata da qwari sosai,ta sakarwa sumayya harara sannan ta wafce
 • kudin dake hannunta
 • “Babu inda zaki rakani munafuka” ta fada tana shigewa dakinta,kada kai sumayya tayi
 • cikin zuciyarta tana fadin
 • “Allah ka shirya,wato hali zanan dutse”.
 • Tana daki tana shafa mai bayan ta kammala wanka ta jiyo fitar fa’izan.
 • Suna zaune zasu ci abincin dare bayan ya kammala komai,tana gabansa tayi kyau
 • cikin kwalliyar laceja mai adon baqi tana zuba masa abincin data shirya musamman
 • saboda shi fa’iza tayi sallama ta shigo dakin fuskarta qunshe da murmushi hannubta riqe
 • da farartakarda,daya daga cikin kujerun dakin sumayyan ta samu ta zaunajuskarsa a hade
 • ya dubeta
 • daga ina kike takwas na dare?”sai ta rausayar da ido
 • “Haba mana muntari,ka tsaya kaji ji da nazo maka da daddadan labari”
 • “Ba wannan ba ki fara amsa min tambayar da na miki tukunna
 • “Kash,labarin da zan baka yanzun duka yafi wannan muhimmanci,amma tunda ka nace sai
 • kaji to daga asibitijikina ya rikice sai na wuce gida na kwanta acan,sai da magariba na
 • danji dama dama” shiru yayi ya soma cin abincinsa,ganin haka ya sanya tace
 • “Ka godewa Allah muntari,Allah ya kusa cika maka burinka da ka dade kana fata,ka kusa
 • zama baba,an auna niinadajuna biyuharnawatabiyu”. I
 • Qwarewa yayi da lomar abincin da ya kai bakinsa,sai ya soma tari babu
 • qaqqautawa,cikin hanzari sumayya ta miqa masa ruwan tana jujjuya maganar cikin
 • ranta,indai hakan gaskiyanetoyatabbata ITACE BATA HAIHUWA?. I
 • Sai da ya sha ruwan sosai sannan ya ajjiye cup din,hannu kawai ya miqawa fa’iza
 • wadda keta doka murmushi tana tunanin farinciki ya sanya mukhtar qwarewa,tabbas
 • burinta ya kusa cika,zaman sumayya cikin gidan ya kusa zuwa qarshe,ta kusa raba mukhtar
 • da kowa sai ita.
 • Takardar ta miqa masa don ta fahimci ita yaje son gani,ya bude ta sosai ya shiga
 • nazarinta daga farko har qarshe,gashinan rubuce a jiki,cikine dan sati takwas,amma sati
 • takwas fa suka rubuta,harya bude bakinsa zaiyi magana sai kuma ya fasa,a yanzun ba
 • muhallin yin maganar bane akwai muhallin yinta,saboda haka ya nannade takardar ya
 • cusa cikin aljihunsa ya janyo abincinsa yaci gaba da ci.
 • Dukkaninsu sumayyan da fa’iza sai suka zuba masa ido cikin mamakin ganin bai ce
 • komai ba,fa’izan ce cikin zaquwa da sonjin abinda zaya fadi din tace
 • ya baka ce komai ba muntari,Allah ya yi maka kyautar da ka dade kana jira amma banga
 • ka nuna komai ko kace min komai ba”kansa ya daga ya dubeta
 • “Naji ai kuma na gani,zankuma magantun amma lokacinyin maganar ne baiyi ba,jeki sai
 • da safe Allah ya inganta k0?” Jiki a sanyaye ta miqe ranta cike fal da mamaki,tayi zaton zai
 • dauketa ne suyirawa suyijuyin murna,ta yadawa sumayya habaici yadda taga dama,amma
 • duk da hakan ai lokaci na zuwa.
 • A sanyaye sumayya ta dubeshi bayan fitar fa’izan
 • “Amma yaya mukhtar kamar bai dace ba abinda kayin,sai nake ganin murna ya kamata ka
 • nuna irin wadda baka taba nunawa ba,d’a fa da kuje muradi shi Allah zai baka?” Kansa ya
 • daga yana dubanta fuskarsa qunshe da murmushi,sai kuma taga ya qyalqyale da dariya
 • “Yanzu my sumy koda haka ne ya cancanci nayi murnar hada iri da waccar matar?,fa iza fa?
 • Wadda ni da ke duka munsan halinta,bani da muradin samun zuriyya da kowacce mace a
 • duniya sai ke,kecenakesoki zamo ta farkoda kika samamin zuria,ki bar maganar nan don
 • Allah bana so in sakejin bakinki game da ita indai na isa da ke”
 • “Insha Allahu” ta fada zuciyarta na karyewa,ina rna inama,ina ma tana da qarfin yaqi da
 • QADDARARTA?,ina ma tana da ikon baiwa kanta haihuwa?,ina ma ace zata iya samarwa da
 • mukhtar cikon farincikinsa,duk da bata da wannan ikon amma bata jin dai dai da daqiqa
 • daya bakinta zai rufu koya gajiya wajen roqon mai badawar da ya albarkaceta ya azurta ta
 • ya kuma bata haihuwa saboda karamci tausayi da kumajin qansa,sai tayi qas da kai
 • hawaye na diga,da sauri ya daga kanta suka hada idani,da murmushi yake dubanta gami
 • da kada kai
 • “Bana so sumayya kin sani,ko ya kike sumayya haka nake sonki,sonki so ne na fisabilillahi
 • cikin zuciyata ba don wani abu da kike da shi ko kika rasa ba” bata buqatar itama bata
 • ransa saboda haka ta saki murmushi tasanya hannunta da kanta ta goge hawayen.
 • Sosai fa iza ta soma tsiro da tsurfa kala kala,gobe ace wannan jibi tace wancan,da
 • fari sumayya na qoqarim yo mata mukhtar na fuskantar haka yace bai yarda ta sake
 • hidimta mata kan komai ba,idan tana so ta tashi ta girka da kanta,nan ma ya fuskanci an
 • shiga babin barna da almubazzaranci shima ya soke yace taci duk abinda ka dafa ko ta
 • haqura,sosai abun ya qona ranta,duk yadda taso samu yaqi samuwa.
 • Sai aka tsiro tsirfar zuwa dubiya kuma,daga bangare mukhtar zuwa na fa izan,saidai
 • ko da wasa bata ga qafar yaya yahansu ko yarama ba,saidai fadima da (a zo,ita din ma
 • sama sama fa’izan ta mata sannan ta tattarata ta watsar,sai data gaji da zama ta ja
 • qafafunta ta tafi,gidan sai ya zama kamar wani gidan biki,wuni sumayya take tana karbar
 • habaice habaice daga bakunan maziyartan gidan kala daban daban,bata tabajin tsananin
 • so da buqatuwar haihuwa ba irin na wannan karon,sai a zama wata mai raguwar
 • zuciya,mikin datajima tana dannewa cikin zuciyarta na rashin magaji ya zame ma a sabo
 • fil,duk sanda suka goranta mata sai ta kasa daurewa har sai ta zub da qwalla ta rage
 • radadin da takeji cikin zuciyarta.
 • Cikin hakan mukhtarya fuskanci ta fara rama,juyin duniya yayi tambaya tace masa
 • lafiya babu abinda ke damunta,tilashinsa ya haqura saidai ya zuba ido sosai bisa yadda
 • lamuran gidan ke gudana.
 • A irin haka katsaham ya dawo gida ranar qarfe uku da minti talatin da takwas ana
 • shirye shiryen kiran sallar la’asar,wasu masallatan ma harsun fara kiran,a lokacin tana
 • qofar kitchen zaune tana hada girkin dare,yayin da dakin fa iza ke qunshe da baqin da
 • qafarsu bata daukewa zuwa gidan da sunan dubiya,suci na rana wani lokaci idan an
 • kammala na dare ma suci sannan su tafi,musamman ranar girkin fa’izan wanda taso
 • qwarai a dauke mata girki mukhtaryace bata isa ba.
 • Yazo kuwa a gaba dai dai sanda sukejeranto gorin nasu,bai kula kowa ba sai da
 • suka kammala duk abinda suka 20 da shi suka karkade qafafunsu,kowacce tazo fita sai tayi
 • turus ganin mai gidan zaune tsakar gida kusa da sumayyan yana tayata aikin kitchen duk
 • da babu wanda yacewa kowa komai cikinsu,sai su kama borin kunya kana su fice sumi
 • sumi.
 • Sai da suka gama ficewa tsaf sannan yayi kirab fa’izan ya kafa mata sharudai,duk
 • randa ya sake ganin qafar wani ya shigo har cikin gidansa ya ciwa matarsa mutunci to
 • sawunta a likkafa ta hada kayanta ta bisu tum gabanin ya dawo gidan,wannan hargagi shi
 • ya sakejanyo tsana da jin zafln sumayya mai yawa a zukatan mutane da yawa masu qinta
 • musamman uwar tafiyar fa’izan,ta kuma sake cin alwashi mai yawa akan sumayya,wannan
 • kuma shi ya kawo taqaitar zirga zirgar ‘yan bani na iya din
 • RANA DUBU TA BARAWO’
 • Tunda ta tashi yau kanta ke ciwo,don haka a daki ta kusa yini,koda yaranta suka zo
 • ma gida ta korasu don bata son hayaniya,naana ce kawai ta zauna kasancewar duka ta fisu
 • nutsuwa. a
 • Har tayi baccin qailula ta farka yarinyar na gefa nta zaune,ta miqe tana salati duk da
 • cewarkan nata ya rage ciwo amma bai sauka ba duka,ta cire hijabin data kwanta da shi
 • sabida zazzabin da ta fara ji ya flta tsakar gida ta dauro alwala,cikin takaici taje duban
 • tsakar gidan yadfa yayi kaca kaca,girkin fa’iza ne amma bata damu ta gyara ba haka
 • al’adarta take,matuqar sumayyan bata gyara ba to saidai gidan yayi ta zama haka,to ita din
 • ma bata da qyashi son jiki k0 ganin ido batq damuwa wai don bata gyara ba yin abinta
 • take,hatta da wankin toilet zata iya rantsewa bata taba ganin fa’l’zantayi ba tunda ta shigo
 • gidan.
 • Tana shiga d’aki ta sanya naana taje ta share mata tsakar gidan ita kuma ta tayar da
 • sallah.
 • Kafln ta kammala sallar nanan ta gama kasancewarta yarinya mai kazar kazar da son
 • aiki shi yasa sumayyan ke sonta,ta dawo gefanta ta zauna tana kallon sumayyan harta idar.
 • Tana shafa addu a ga mamakinta fa’iza ta shigo d’akin dauke da coolerdinta ta dire
 • tayi ficewarta,tana nannade abun sallar sai ta lura naana nata kallonta tana kuma satar
 • kallon kwanon abincin,tasan akwai magana a bakinta ne ta kasa fadi,kuma hakan yana da
 • nasaba da hanasu dauko magana daga wani guri su gaya mata.
 • Harta koma saman kujera ta kwanta don bata da sha’awar cin komai taga yari yar
 • naci gaba da kallonta idan ta lura da kyau ma kamarqwalla ce a idonta,a hankali ta miqe ta
 • zauna tayi kiranta,yarinyar ta iso gabanta ta zauna
 • “Me ya faru?me ya sameki naga kamar zakiyi kuka,ko yunwa kikeji?” Sai ta girgiza kai
 • “To mene ne gaya min” cikin raunin murya kamar kukan zai qwace mata tace
 • “Antysumayya don Allah kada kici abincin nan” sai sumayyan ta hade rai tana dubanta
 • “Me yasa?”
 • “Anty,naga amarya ta bude leda sanda kika sakami yin shara tana ta leqe sannan ta koma
 • kitchen ta bude flaskdin ta debo wani yalon abu ta barbada a ciki tajuya ta rufe ta wanke
 • hannunta” sosaitaji gabanta ya fadi,saidai bata son ta bawa yaran damar da zasudinga
 • labe ko qoqarin dauko gulmar fa’izan suna kawo mata,saboda haka ta sake hade rai
 • “Ke me yasa kika labe kina kallonta?” Da saurita girgiza kai
 • “Allah ba labewa nayi ba,tsintsiyar ce ta kunce a bakin kitchen din sai na tsaya daureta
 • shine fa na gani” shiru tayi tana jinjina zancan cikin zuciyarta,sam bata son ta baiwa kanta
 • qofar da zata zargi fa’iza kan abinda idanunta basu gane mata ba,saboda k0 ubangiji ya
 • fadi cewa HAQIQA WANI SASHI NA ZATO ZUNUBI NE,kai kawai ta kada bayan ta koma ta
 • kwanta
 • “Shikenan,bazan ci ba,amma kada ki gayawa kowa abinda kika gani kinji nana?”
 • “To anty” ta fada tana kada kai
 • “Zan tafi anty lokacin islamiyya yayi” ta amsa kana ta laluba gefanta ta dauko alawa guda
 • uku yan naura biyar biyar da takan ajjiye saboda su ta miqa mata,bata fiya son basu kudi
 • ba don kada su saba da su ta bata ma iyayensu tarbiyyar yaransu,don ba kowa keson ka
 • yiwa yaronsa kyautar kudi ba sabida gudun kada su saba da su,randa kuma basu samu ba
 • su nema kota halin qaqa,Allah ya kiyaye.
 • Sosai ta zurfafa cikin tunanin maganar da naanan ta gaya mata,sai ta kauda tunanin
 • daga ranta ta shiga addu’a cikin zuciyartaALLAHUMMAK FINIHIM BIMA SHI’ITA ta dinga
 • maimaitawa cikin zuciyarta,tana fata koma mene Allah ya mata maganinsa ya sanya
 • tsarinsa a gareta har wani baccin ya sake daukarta.
 • Kodaya dawo yau bai samu yin wanka ba saibayanyayi sallar magariba,yasan cewa
 • ba samun ruwan wankan nasa zaiyi ba saidai ya debawa kansa,hakan ne ya sanya yana
 • shigowa ya tara ya shiga bandakin,har ya shiga ya manta da towel dinsa hakan ya sanyashi
 • futowa.
 • Da hanzarinsa ya dawo zai shige,saidai wani abu da ya fisgi zuciyarsa ya sanya shi
 • dawowa da baya,abinda ya faru watannin baya yake ji 3 jikinsa tamkar zai sake maimaita
 • kansa ne a yau,a hankali ya zarw sllppers dinsa ya taka zuwa qofar kitchen din,idanunsa
 • suka sauka kan cooler din sumayya dake bude gaban fa’iza wadda ke dauke da dafa dukan
 • shinkafa qarshen qurewar girkin fa’iza kenan.
 • Cike da hanzari fata da buri take barbada garin cikin abincin,don ta fuskanci cewa
 • sam sumayya ko bude kwanon abinci bata yi ba,amma wannan karo taci alwashi kota halin
 • qaqa sai ta sanya ta taci ko loma daya ce kai tama yankewa kanta ko dura ce sai tayi mata.
 • Tana karkade hannunta cikin nishadi taji carafan riqe hannunta,tun kafin ta fahimci
 • wake da alhakin riqe mata hannu gabanta yayi wata mummunar faduwa,a hankali tamkar
 • wadda ta warke daga cutar laka ta daga kai suka hada idanu da mukhtanwani matsanancin
 • tsoro ya shigeta wanda kadan ya rage ta saki fitsari cikin wandonta sakamakon yadda taga
 • idanunsa sun sauya kala cikin sakannin da basu wuce biyar ba.
 • Wani laflyayyen mari ya yarfa mata wanda kafin ta ankare da a wanne hali taje ciki ya
 • sake bin fuskarta da wani,hakan ne ya tilasta mata sakin wata gigitacciyar qara sabodaji
 • taje tamkar fuskarta na shirin tsagewa ne,wannan shi yayi silar

  zaburarsumayya ta miqe ta

 • fito a razanetana tsammanin ko gobara ce ta kama gidan nasutunda ta bar fa’iza ne cikin
 • kitchen.
 • Fitowarta yayi dai dai da wurgo fa’iza da mukhtar yayi zuwa filin tsakar gidan
 • “Subhanallahi”sumayyata fada da qam tana nufar inda fa’iza take don ta d agata
 • “Kika tabata sai mun samu mummunan sabanin da bamu taba samun makamancinsa ba ni
 • da ke,sai nayi matuqar saba miki” taji mukhtar na ambata cikin wata kakkausar murya da
 • bata taba zata yana da ita ba.
 • Yadda ya sake nufo fa’iza gadan gadan ya tsoratasu baki daya,sumayya ta janye gefe
 • jikinta na rawa,bakinta na ambatar duk wata addu’a da tazo bakinta tare da neman agajin
 • Allah ya kawo sauqin kowacce iriyar masifa da zata faru yau a gidan,yayin da tsoron da
 • fa’iza taji ya sanyata sakinihun neman agaji domin tsantsar bala’in da zata fuskanta ya flto
 • muraran cikin idanun mukhtar tun kafln ya kai ga aiwatar da shi a kanta.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]