[Advertisements⬇️]

QADDARAR SUMAYYA CHAPTER 20 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

QADDARAR SUMAYYA

CHAPTER 20

Kwananta biyu kwance cikin dakin babu abinda take iya hasalawa,daga kwanciya sai

bacci ga wani shegen zazzabi da yaqi sauka daga jikinta, duk lokacin da ta yunqura ta yiwa
kanta duren shayi tofa qarshensa ya dawo baki daya,abinci kuwa ko kadan bata da
sha’awar cin komai,hakan ya sanya ta haqura ta zubawa sarautar Allah ido,banda ruwa

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

babu abinda take kurba,roqon Allah take ya sassauta mata ko ya jefo mata wanda zaya
taimaketa,hatta da wayarta bata san inda ta cillata ba,a haka ta shafe kwana hudu cur bata
ga kowa ba rana gurzar ciwnta ita daya,duk da cewa taci ranar girkinta har ta fita amma
bata ga idon mukhtar ba,to idan da sabo dama ta riga data saba da hakan,data ga irin
hakan tasan an karbi kwananta ne an qarawa zainab.
Cikon kwana na biyar din cikin ikon Allah ta ji saugi sauqin jikinta,tana jin qwari qwari a
jikinta,har ta iya shiga da yammaci gab da magariba bandaki tayi wanka,tana fitowa ta
soma laluben wayarta, can cikin jakar da ta dawo daga gidan anty dije ta ganta,a nan taci
karo da dubu ukun da abdur rahman ya bata,sai taji dadin kudin don bata da ko siai a
hannunta,to ina ma taga mai batan tunda ita ba sana’a take ba,caji ta sanyaa socket din
dake daura da madubinta,ta dawo bakin gadonta ta zauna ta soma shafa mai,daga inda
take zaunen tana iya hango kanta sosai cikin madubi,ta rame sosai tayi wani fayau da
ita,sai uban fari da ta qara kamar wadda ta hadiyi qwayar qara hasken fata.
Tura qofar dakin nata da akayi shi ya maidota cikin hayyacinta,ta dubi bakin qofar,mukhtar
ke shigowa,sanye da yadi tissue na maza orange wanda ya ciza,yayi kyau sosai amma sai
taga kamarya rame,duj da bata sani ba ko idanunta ne,don idan ba makuwa tayi ba
rabonta da shi yau kwanaki shida cif. Kanta ta dauke don bata ga dalilin ci gaba da kallonsa
ba,ta soma lalubar mayafinta ta lullube jikinta saboda guntun towel ne kawai daure a
qirjinta.
Shikam kallonta yake ci gaba da yi yana son lalubar sonta cikim zuciyarsa amma ya rasa
duk da dumbin qaunar da yake jin tana zanga zanga cikin zuciyarsa wadda ya azata a
bigiren tausayi, uban haushinta da yake ji yau babu shi kamar yadda baijin soyayyarta cikin
zuciyar tasa. Bata sake bi ta kansa ba har ta gama shafa manta,ta bude drower dinta ta
fidda kayan da zata sanyasai a lokacin ta kuma dubansa
“Ka fita don Allah zan sanya kaya” ta fada idanunta tsakar nashi
“Me ya sameki haka sumayya naga kin rame?,ko duk shegen kishin da kika sanyawa ranki
ne kamar yadda zainab ta fada?”ya fadi ba tare da yayi duba ga qorafinta na farko ba
“Kan bala’i” ta fada cikin zuciyarta,wani baqinciki na takore mata qirji,wannan rainin
hankalin da me yayi kama?,ita yake tambaya ma meke damunta?
“Ba wannan ne a gabana ba,ka ficen a daki” ta fada ranta na suya,sai ya fara takowa inda
take,wani shauqinta na fusgarsa,son kasancewa kawai yake da ita,yayi kewarta kwanakin
bakwai din nan da bai ziyarceta ba
“Bari na qaraso ki gayamin nawa muka hada muka gina gidan da har dakin ya zama naki”.
Qarasowarsa ke da wuya qamshin turarensa ya daki hancinta,wani tashin hankali ya
ziyarceta,take ta saki kayan hannunta ta buqaci bandaki, nan ta fara kelaya aman da yayi
sanadiyyar ficewar ruwan tea din data samu yau ya zauna mata.
‘lafiya sumayya?,meke damunki?,me ya sameki?”haka ya dinga fadi yana riqe da
ita,dukkan alamun tashin hankali sun bayyana a fuskarsa wanda hakan yayi matuqar
daurewa sumayya kai,mukhtar din tamkar wani bugun jinnu haka ya koma,idan yaso ya
dinga gasa mata aya a hannu shi da matarsa,amma wani lokaci sai ya dinga yunqurin
juyewa ya koma mata yaya mukhtar dinta sak wanda ta sani a can baya.
Ganin qamshin turaren ke sake dugunzuma tunaninta ya sanya ta buqaceshi da ya matsa
ya barta bata so,haka ya koma baya ya zuba mata ido har ta kammala ta gyara wajen ta
dawo bakin gadon ta zauna tana maida numfashi
“Kishirya na kaiki asibiti,ni bansan baki da lafiya ba” duk da yadda take fidda numfashi dai
dai amma hakan bai hanata maida masa magana ba
“Bani buqata, me magani zaya yimin?, hin wai damuwa kayi ma da wata sumayya?,na
tabbata bakaqi na mutu ba,tunda har zaka iya hanawa a bani abincin gidanka ina a
matsayin matar ka” ta qarashe maganar tana sakin kuka don sosai batun ke ci mata qoqon
zuciya,ba wai don ta damu da abincin ba,a’ ah,ta dauka tafi qarfin komai a gidan mukhtar
din,ta dauka ita din mai iya dauka ce ta bayar ma kyauta,sai gashi ita ake hanawa abinci
“Wallahi ni bansan lokacin da akayi hakan ba,waye ya gaya miki ni na hana?”maganarsa ta
ratsa kunnenta,sai ta daga ido tana dubansa tana daga kwancen,gani take kawai raina
mata wayau zai yi,aljanu gareshi ko farfadiya ce ta kamashi lokacin da ya bawa zainab din
umarni?,baqinciki ne ya hanata magana, ganin tayi shiru ba tare da tace komai ba sai kukan
ta data ci gaba da yi yasa yace
duka mubar wannan maganar muje asibitin a dubaki tukun,zanje nayi sallah ma dawo”‘ya
fada yana ficewa.
Da fari taso taqi yarda,amma jin tsaiwa na niyyar gagararta sanda zata bada faralin sallar
magariba yasa ra taushi zuciyarta ta amince,ita kanta zata so taji meke damunta bawai
tayita zama da ciwo ba,tunda tunda take bata taba jin irin hakan ba.
Bajimawa da idar da sallar sai gashi ya dawo,zuwa lokacin da qyar ta samu ta gama tata
sallar aman ya sake tsinke mata,jikinta yayi laushi tubus sai numfashi da take
maidawa,yaso taimaka mata wajen fita amma tace bata buqata,haka ta dinga bin bango
har suka isa cikin motar.
Wani private hospital dake cikin unguwar tasu ya kaita, bayan taga likita ya bata takardar
gwaji taje lab,minti goma ta karbi sakamakon ta koma dakin ganin likitan ta kai masa
“Alhamdulillah,sai ka godewa Allah,madam na dauke da juna biyu'”‘baki dayansu wuta ce
ta dauke musu kada ma sumayya taji labari,sai ta fara girgiza kai hawaye na sauko
mata,magana take son yi amma bakinta ya gaza furta komai
likita don Allah ka daina mana irin wannan wasan sai ka dauki haqqinmu”ta fusgi
kalaman da qyar,sau ya dago kai ya dubeta
“Bama yiwa patient wasa cikin abinda ya shafi lalurar da ta kawo su,ki baki yarda bane
hajiya,ai muna da na’urar daukan hoto bismillah ga gado can hau in nuna miki” kasa tashi
tayi baki daya,ga rashin qwarin jiki ga luguden da maganar tayi mata,mukhtar dake son
tabbatar da gaskiyar labarin shi ya taimaka mata har suka isa bakin gadon.
Cikin qwarewa ya shiga nuna masu dan qaramin tayin dake cikinta wanda duka baifi wata
biyu da rabi ba,basu iya ganewa amma sun lura da wani dan digo wanda shike alamta
yaronsu kenan,wata doguwar ajiyar zuciya ya saki tare da lumshe ido yana jinsa cikin wata
sabuwar duniyaryayin da sumayyan ta fashe da kuka,jikinta baki daya rawa yake,ashe tana
daga cikin mata masu haihuwa?,ashe akwai rabon zata ga yaron kanta?,ashe ita ma din
watan watarana zata zama uwa?,zata yi raino ta kuma bada tarbiyya?,lallai ubangiji babu
wanda ya kaishi iyawa cikin mulki da kyauta, babu ko shakka ubangiji baya bacci,baya
mantawa da duk wanda ya ambaceshi ya kuma nemi agajinsa.
Barinsu likitan yayi suka gama murnarsu,don ya fahimci dukkansu ba’a cikin hayyacinsu
suke ba sannan ya sanarwa mukhtar din jikin sumayyan ba qwari,zasu riqeta su sanya
mata drip(ruwa)har zuwa safiya ko zata ji karsashi,sannan ya rubuta magungunan da zatayi
amfani da su wadanda zasu taimaka mata ita da abinda ke cikinta,sannan ya jadda masa
alfanun cina abinci mai kyau da gina jiki da qara kuzari a gareta,karba yayi saida ya
tabbatar an gama komai an sanya mata drip din sannan ya fita siyo magungunan.
Ya jima zaune cikin mota ya kasa tayar da ita,ina zaikai wannan kayan farincikin?,da wa ya
kamata ya raba wannan farincikin kada ya masa yawa ya masa illa?,da sauri ya zaro
wayarsa daga aljihu ya soma daddanna wasu lambobi kyakkyawan murmushi kwance a
kan fuskarsa.jinsa yake cikin wata duniya mai dauke dimbin farincikin da ya jima bai jishi
ba,jinsa yau yake wani na daban.
Ji take idan ga zauna gu d’aya tamkar wani mummunan abu zai faru ne tare da ita,tana jin
qwaqwalwarta ko zuciyarta daya daga ciki zai iya tarwatsewa,tunda take bata taba cin karo
da mummunan labari da ya firgita duniyarta ba irin wannan labarin,idanunta basu taba
mummunan gani ba irin na wadan nan kwanakin, su mayya kishiyarta da ciki?,ita kuwa tana
me?,wanne shirme take?,wanne baccin asarar tayi har mukhtar ya yiwa sumayya ciki duk
da uban takatsantsan din da take?,duk da raba tsakaninsu da tayi ya daina
sha’awarta?,tabbas idan har ta bari sumayyan ta rigata haihuwa cikin gidan ta dibga
babbar asara, hakazalika bata ci sunanta,gidan da take da buri a cikinsa,gidan da take so
shi da mamallakin gidan duka su zama qarqashin ikonta shine wata zata riga ta fara ajiye
iri?,tun yanzu ta fara ganin manya manyan sauye sauye ina ga ta haihu?,tun yanzun
mukhtar ya ruguza dukkan wani plan data yi cikin gidan,wani kukawa yake bawa
sumayyan wanda hakan ke nuni da qiris ya rage sun koma su dinke kamar daa koma sufi
daa dinkewa,abinda idan har ya faru ba zata taba gafartawa kanta ba,lallai ko zatayi yawo
tsirara sai ta tabbatar ta kawar da duk wata barazana dake shirin tunkaro ta.
Kamar mahaukaciya haka ta suri wayarta ta soma laluben lambar wayar aminiyarta
qawarta,wadda bata aiwatar da komai sai da shawarat,zama tayi dabas gefan gadonta jin
wayar ta shiga,cikin qananun sakanni mamallakiyar lambar ta daga,ko ta kan gaisuwar da
take jefo mata bata bi ba ta soma zayyano mata abinda ke gudana cikin gidan.
Tsawon minti talatin ta dauka kan layin wayar suna qulla saqa a mugun zare, so sai taji dadi
da shawarar data baga,shi yasa bata da kamarta,shawara ce mai saugi wadda babu zuwa
gun boka ko malami,hakanan babu barnar kudi,amma fa buqata zata biya,don dama
babbar matsalarta yanzun duka jarinta ya karye warwas,saboda ribar da uwar kudin duka
sun tafi gun ‘yan tsubbu,bata kwana arba’in bata je an mata service ba,tun tana tsoron
hadisin data taba tsintar wasu yaran ‘yan makarantar islamiya na karantawa na cewa duk
wanda yaje gun boka ko dan duba,to sallarsa ta kwana arba’in Allah bazai karbeta har tazo
ta dake tama manta da hadisin baki daya bare ta tunoshi ya zame mata birki. (daya daga
cikin abinda Allah ke jarabtar masu biye biyen malamai kenan,basu taba tara abun
hannunsu,kullum suna kan hanyar rabawa matsubbata da yan duba,ko kishiya gareki mai
irin wannan biye biyen ki lura da kyau,duk abinda miji zai baku sai ki nemi nata ki
rasa,kullum cikin babu da bani bani take,ba zaki taba ganin burbushin abun ba ko a
dakinta ko a jikinta ko a jikin yaranta,Allah ka kiyashemu ka tsare mana imaninmu).
Tana kammala wayar ta saki murmushi ita daya take magana da kanta
“Kissa ai tafi magani,ba shakka quruciyarki ta yimin rana,zan amfana da ita sosai” ta fada
tana ficewa a dakin inda kai tsaye ta nufi dakin sumayya.
Tana kwance saman carfet din dakin nata tayi matashin kai da pillow.duk da ba yadda
mukhtar baiyi ta dora kan nata saman cinyansa ba amma ta qiya.yana zaune dirshan
gabanta da faranti a tsakiyarsu wanda ke dauke da kankana da tuffa da gwanda,ayaba
yake bare mata yana miqa mata tana daga kashingide take amsa tana ci,dubansa take
kawai cike da mamaki,.yana son dawo mata mukhtar dinta,”Allah yasa ba yaudara bace,.ya
Allah kasa kada ya juyan baya”haka ta dinga fada cikin ranta tana binsa da kallo wanda shi
sam bai ma kula ba,hannu ta sanya ta shafi cikinta wansa daga can qasa ta fara jin dan
tudu kadan,lumshe idonta tayi tana jin qauna cakude da farinciki na ratsata,duk kwanan
duniya takan shafa cikin sau babu adadi,wani lokaci takan tsaya gaban madubi ta dage
rigarta tayita kallon fatar cikinta tana mamaki yau ita ke dauke da juna biyu,idanu ya zuba
mata shima yana kallonta farinciki na bibiyar duk wara gaba ta jikinsa,a haka ta bude
idanunta karaf cikin nashi,sai kunya taso kamata,murmushi yayi sannan yace
“Bakiyi laifi ba sumayya ki qaunaceshi yadda ya kamata,wallahi Allah a duniya ban taba jin
son wani abu a rayuwata ba kamar yadda nakejin son cikin dake jikinki ba,zan iya rasa
komai sabida shi,zan iya rabuwa da komai saboda shi,don Allah ki kularmin da kanki da
abinda ke cikinki komai runtsi” ko bai fadi ba tasan zancan daga zuciyarsa kai tsaye yake
fitowa,ita kanta bata san irin son da talkewa cikin ba, kai ta sunkuyar tana murmushi tare da
furta
“In sha Allah ya mukhtar
Dukkan wannan maganganun cikin kunnen zainab suka yisu wadda ta sawo kai don
shigowa dakin
“ka nunawa kucciya baka”ta fada sannan ta shigo dakin da sallama tana sake sai saita
nutsuwarta,gaban sumayya ya fadi har sai data runtse ido cikin zuciyarta tana fadin
“Allahummakh finihim bima shi’ita(Allah ka isar min da su da abinda kaso)(addu’a ce mai
kyau ga wanda yaji tsoron zaluncin wasu mutane)” murmushi taje jifarsu da shi wanda shi
kansa mukhtar din sai da yayi mamaki
“Ashe kana gun uwar gidanmu my mukhtar” ta fada tana zama kusa da shi,amsa mata yayi
sannan ta dora
“Gwara ai ka kular mana da ita sosai musamman da take dauke da cikar muradinmu,Allah
mun gode maka daka nuna mana wannan lokaci” ta fada tana maida hankalinta ga
sumayya,hannunta tasa ta riqe nata hannun.ji take kamar ta kama garwashin wuta amma
sai ta dake
“Sannu sumayya ya jikin naki?” Da qyar ta bude labbanta tace
“Da sauqi”
“Allah ya inganta ya qara miki lafiya kinji,na godewa Allah da zaki samarwa mukhtar sanyin
idaniya,naji dadi qwarai dama ke ya cancanta ki fara samun wannan matsayin,don Allah
duk abinda kike da buqata ki sanarmin kada kice zaki yiwa kanki wani abu,kada ki duba
duka wasu abubuwa da suka faru a baya,sharrin shaidan ne da kuma zuciya wadda bata da
qashi,in sha Allah ba zasu sake faruwa ba,sai yanzu na fahimci kyakkyawar zuciya da kuma
haqurin da kike da shi,don Allah mu hada kai mu zauna lafiya kinji?” Duk da bata gama
gamsuwa ba amma taji dadin maganganun zainab din,ko babu komai wake son tashin
hankali?,ai babu abinda yafi zaman lafiya dadi
“Ba komai maman nafi’u,Allah ya sake hada kanmu”
“Ba amin ba,don wallahi da kai na ya hadu da na kishiya gwara na qare rayuwata kan nawa
na ciwo” ta fada a zuciyarta,amma afili sai ta saki murmushi tana fadin amin.
Sake matsowa tayi ta karbi bare ayabar daga hannun mukhtar din,ita ta dinga barewa
sumayyan tana miqa mata,tanayi can qasan zuciyarta na mata suya,amma fuskarta kuwa
murmushi da kulawa ne kwance a cikinsu.
Kulawa ta qwarai zainab ke bawa sumayya wadda zata kwantar da hankalin dukkan
wani mai zargi,ta hanata komai,babu abinda sumayyan keyi cikin gidan banda wanke
goma ta tsoma biyar,hatta da ruwan wanka ita ke dafa mata ta ajiye mata a bandaki.girki
kowa saidai kawai taci kuma mukhtar ya kwana dakinta,sau tari zainab din kan yafewa
sumayya kwananta a zuwan yaje su kwana tare tafi samun kulawa,ta dauke dukka ayyukan
gidan bisa wuyanta,ita kadai tasan me take ji cikin zuciyarta,wani lokaci zuciya kan raya
mata ta shaqe sumayyan kawai ta mutu ta huta da ganinta da ganin abinda ke
cikinta,saidai mardiyya qawarta kan yawaita ja mata kunne da cewa, matuqar ba zatayi
haquri ba to kuwa ba zata cimma nasara ba,hakan shike yawaita taka mata burki tana jira
har zuwa lokacin da zata kammala qudirinta.
Qwarai mukhtar na jin dadin yadda take kula da sumayyan.yana yaba mata
sosai,hankalinsa ya kwanta,duk da cewa har ya zuwa yanzu akwai tasirin ragowar sihirinta
a jikinsa,a duniya yanzu babu abinda yake so irin cikin jikin sumayyan,shi yasa hakan da
takeyi yake sake saka farinta a idonsa,shi din ma ba’a barshi a baya, hidima da tattali yake
mata kan jiki kan qarfi,duk da sai data masa tutsun abinda ya dinga mata a baya,saidai
abun mamaki yaje bashiya sanar mata sam baisan sadda hakan ta dinga faruwa ba,kallon
ya raina mata hankali ta dinga masa, hakan da ya lura da shi ya sanya ya karbi lefin kawai ya
kuma bata haquri.
Ita din ma sumayyan ba’a barta a baya ba wajen tattalin kanta da abinda ke cikinta,duk
wani abu da tasan zaya kawo tarnaqi ga lafiyar cikinta tana kauce masa,har yau bata bar
mamaki ba wai itace yau da ciki bayan shekaru kusan takwas cikin na tara da
aurenta,bayan da ta riga ta debe haso?,allai rabon kwado baya taba hawa saka ko ya hau
din ma rabi zaya sauko da shi,babu ranar da zata fito ta fadi bata godewa ubangiji ba.
Mama mahaufiyarta kuwa kullum cikin kiranta a waya take da turowa a duba mata
ita,duk sanda zata aiko da abinda zata kawo mata na kayan qwalama na masu ciki,jita
kanta yaya yahanasu da taji labarin laqwas jikinta yayi,sai ta rasa me take ciki farinciki ko
baqinciki,amma jikinta yayi sanyi ta kuma taya mukhtar din murna,saidai har yau bata je ta
ganta ba,tanq gudun wulaqancin da zata taras a gun zainab,don ta yanka musu gargadi kan
zuwa gidan duk sadda suka ga dama.
..KAYAN KWALABA”
MAFARL
Zaune yake gefan gadon dakinsa yana sanya maballan rigarsa a shirin sa na fita
kasuwa. Ahankali zainab ra bude qofar dakin ta turo ta a hankali kamar wadda qwai ya
fashewa a ciki,kujerar madubu ta janyo ta zauna tana fuskantar mukhtar idanunta a
kansa,shi ya soma magana
“Lafiya dai ko?,na lura tun jiya jikinki a sanyaye yake,mu da muke cikin farinciki a kwanakin
nan”
“Kake cikin farinciki dai,kuma na kusa datse igiyar farincikin'”. A zahiri sai ta soma goge
qwalla da ta fara sakkowa a idanunta tana kallon mukhtar din
” mukhtar,wannan farincikin da muka samu idan bamuyi wasa ba yana gab da qwacewa
daga cikin gidan nan,bansan me yasa take ta qoqarin aikata haka ba,bansan me yake
damunta ba'”barin sanya takalman da yake qoqarin yi yayi.ya dago ya dubeta idanunsa
cike fal da tambaya, har ya gaza boye hakan sai da ya furta
“Kamar yaya fa?,me yake faruwa ne?” Kai ta shiga girgizawa cike kirsa
“A’ah mukhtar,barin maganar nan shi yafi alkhairi,don bansan ya zaka dauketa ba”
“Idan kina tunanin wani abu ne da zai cutar da ni qauna ce ki boyemin kiqi gayan,gaya min
zainab” dan shiru tayi a zahiri fuskarta dauke da tashin hankali.yayin da zuciyarta ke cike
fal da murna da farinciki tare da fata da addu’ar samu nasara tamkar wata wadda zata
aikata abun arziqi,bata kuma magana ba har sai da mukhtar din ya jaddada sake
tambayarta,taba goge qwalla tace
“Mukhtar,sumayya ce…Sumayya ce naji tana magana da wata baquwa da tayi,bansanta
ba,ina tunani ko qawarta ce ko qanwarta ko yar uwarsu,wai wallahi sam batayi farinciki da
samuwar wannan ciki ba,ina ita ina haihuwa bayan ko shekara ashirim baga gama rufawa
ba,dama ita can kawai nunawa take tana son haihuwa amma wlh sam bata qaunarta, bare
wai ta lura ba wani kulawa take samu yanzu daga gareka ba,tunda kwanakin baya ka juya
mata baya yanzu haka data haihu qila ka sake komawa halayyarkayanzu haka maganar da
nake maka har ta bata shawarar ta sha maganin da zai barar da cikin kawai ta huta”
Tamkar guduma zainab ta sanya ta daki qahon zuciyarsa haka yaji,take maganar da
yaya yahansu ta ta sha gaya masa shekarun baya suka bijiro mada suka cakudu da wannan
sabon batun
kai idan zaka farka gwara ka farka,matarka fa ba son haihuwa take ba,bata ma
sha’awarta,tunda kuke ka taba gani ta sha wani magani don ta haihu ko ta taba maka
maganar kuje asibiti a dubaku?,ina kyautata zatan ma ita tasha maganin da zata hana
kanta haihuwa,banda haka yarinyar dake da quruciya mai zai hanata haihuwa a irin
wannan lokacin?”. Wani fushi da bacin rai mai tsanani ya sauko masa,sai kawai ya
miqe,burinsa kawai yaje ya samu sumayya yanzun nan,da sauri ta riqeshi don ba yanzu
take da muradin nakiyar ta fashe ba
“a’ah mukhtar ina kuma zaka?”
“Sakeni zainab,sakeni naje na sameta” wani mugun marairaicewa tayi sannan tace
“Shi yasa fa naqi gaya maka tun jiyan.yanzu me zakaje ka yiwa yarinyar mutane kana cikin
fushi haka?,idan baka iya kama barawo ba sai shi barawo ya kamaka,zauna muyi magana
akwai mafita” babu musu ya koma ya zauna yana maida numfashi
“Mukhtar,kada ka damu,ni mai qaunarka,ina son abinda kake so,idan baka manta ba nike
kulawa da sumayya.to kada ka damu,zan sanya ido sosai a kanta,sannan zan hana duk
wani abu faruwa har Allah yasa ta haihu lafiya na maka alqawari” hakanan yaji kalamanta
sun kwanta masa a rai,sai ya sauke ajiyar zuciya
“Na gode zainab,don Allah na roqeki ki kula da ita,a duniya yanzu babu abinda nakeso
sama da cikin nan don Allah” wani shegen kishi ya takore mata,cabdi,a haka zata bari
sumayya ta fara haihuwa,ai ba zaya yiwu ba,a fili tace masa
“Na maka alqawari tare ma zamu dinga wuni insha Allahu kada ka damu”jikinsa a sanyaye
ya gama shirin zuciyarsa na bugawa,mamaki da haushin sumayya ne fal cikin zuciyarsa,da
kamar ya wuce abinsa ba tare da ya mata sallama ba zainab din ce ta tursasashi kan sai ya
shiga din,koda ya shiga sumayyan sai taga yanayinsa ya sauya sosai,ba kamar yadda ya
saba mata ba, gabanta ne ya dinga faduwa tana fatan ba halayensa na baya bane zasu
dawo,don ko kusa bata da buqatar wannan yanayin.
Har ya juya zai fita sai ya sake waiwayowa ya dubeta
“Ki kularmin da cikina,din bazan iya jurewa ko yafiya gareki ba ga duk wani abun qi da zaya
samu cikin nan ba” dai ya juya ya fita,kanta ne ya daure sosai,me yake nufi kenan,ta jima
tana qoqarin lalubo amsar,daga qarshe abinda qwaqwalwarta ta bata shine tsabar son
cikin da mukhtar din keyi ne haka ta barwa ranta taci gaba da sabgoginta.
******** ****
Bata gushe ba tana ci gaba da cusawa mukhtar tunani kala kala kan zub da ciki sumayya
ke qoqarin yi,amma ta nuna masa tana bala’in takatsantsan akan faruwar hakan, sosai ya
shiga damuwa da tashin hankali,mamakin sumayyan yake yi,da ya matsanta kan sai ya
mata magana yana son daukar mataki,bazai iya jura ba idan wani abun ya samu cikin sai ta
masa alqawarin zata nuna masa da idanunsa zai gani saboda hukunci da huja yafi.
KUNDIN QADDARA”
BAQAR RANA
Tun da safe ta hada mata shayi kamar yadda ta sabarwa kanta,duka yana cikin
qudurinta da tsarinta. Ranar kusan da wuri mukhtar ya fita,tana kwancan har ya fita din ko
abin kari ma bata masa ba saboda mugun qudirinta data qulla aiwatarwa a yau din nan ko
farkawa bata nuna tayi ba, hakan ya sanya data shiga da shayin ta zauna tana jan sumayyan
da hira,bata bar dakin ba sai data tabbata ta kammala shan shayin,sannu a hankali ta
soma hamma,zainab din ta dubeta fuskarta qunshe da murmushi wanda ke dauke da
manufofi uku,manufar cimma nasara da manufar mugunta,sai kuma dadi daya kamata
saboda tafuskanci magungunanta zasu soma aiki lokaci guda yadda take so
“Kwanta ki huta qanwata na fuskanci kamar bacci kike ji”
“Wallahi kuwa,duk jikina ya mutu” ta fada tana jan pillow ya yada kai saboda nauyi da taji
kanta ya soma yi sakamakon bacci mai nuyi daya lullube idanunta. Leqa fuskarta tayi ta
tabbata ta soma baccin sannan ta sake sakin murmushi,a nutse ta nufi drower din gefan
gadon sumayyan ta fiddo magungunan da suke soke cikin rigar mamanta,magunguna ne
har saches uku dukka na zub da ciki ne,saches daya aka balla guda gudu wanda ita tayi
amfani da shi ta zubawa sumayyan cikin ruwan shayin data kammala sha yanzu,sai wata
‘yar qalamar kwalba da wani saches din wanda duka maganin dake bugarwa ne da saka
bacci wanda yawanci yan shaye shaye aka sani suna ta’ammali da shi. Dorasu duka tayi
kan drower din sannan ta fice.
Kitchen ta shiga ta samo kofi cikin kayan sumayyan ta zuba ruwa ta dawo kusa da
magungunan ta ajuye,ta bude kwabar kayanta ta ciro hijabi ta ajiye saman kanta sannam
ta nufi ma’ajiyar takalmanta ta ciro ta sanya mata daya daga ciki a qafafunta,sai data qare
mata kallo ta tabbatar komai ya kammala sannan ta saki dariya ta fice zuwa dakinta.
Tazarar mintina goma ta bada kamar yadda aka ce mata magungunan zasu fara aiki
amma maganin baccin zai sa ba zasu tashi aikinsu gadan gadan ba sai bayan minti
ashirin,dakin ta sake nufa ta leqata sai ta tarar har yanzu baccin take amma tana motsawa
akai a kai,jinjina kai tayi ta sake komawa dakinta.
Kai tsaye ta dauki wayarta ta laluba lambar mukhtar,bugu uku ya daga tare da yin
sallama,bata bi ta kan amsawa ba ta soma magana cikin yanayi na matuqar rudewa qwarai
da gaske
“Wayyo Allah mukhtar mun shiga uku,mukhtar na kasa riqe amanar da ka bani” cikin wani
mugun tashin hankali ya miqe tsaye daga inda yake zaune sannan ya fara tambayarta
“Lafiya zainab yi magana mene ne?”
“Kasan ka barni a daki ina kwance ina bacci.to ina tashi naga lokaci ya ja,sai na tuna
sumayya na barta bata ci komai ba,da sauri na shiga kitchen na hada mata abun kari na
nufi dakinta,ina shiga naga babu kowa na duba gidan baki daya ban ganta ba,ina falo ina
taraddi ina ma shirin kiran wayarka ko kasam zata fita?,kawai sai gata ta dawo dauke da
wata baqar leda ita da wannan ‘yar uwar tata,da nayi mata magana ma kallon banza ta
yimin tayi tsaki ta wuce daki,sai ma qyaleta sabida nasan masu ciki da fushi,sai daga baya
na sake leqata sai na tarar tana shan wani magani, na mata zancan abinci tace ta qoshi bata
buqata taci a waje, na qyaleta na dawo ina hidimar gida,bayan wajen minti talatin sai na
fara jiyo ihunta tana wayyo cikina wayyo bayana inzo in taimaketa” sai ta fashe da kuka
kamar gaske,.ya gaji da dogon jawabi kawai jira yake azo gurin
“Ki gayan me ya faru?”
“Jini ma gani daga jikinta mukhtar yana fita wanda ke nuna kamar bari tayi”
“Me!”Ya fada da madaukakin sauti, kafin ta kai ga amsawar ta soma jiyo kumar sumayyan
na kiran sunata,dadi ya kamata komai yazo a daidai kenan?,sai ta sake dububurcewa
“Tana kirana mukhtar don Allah kayi sauri kazo mu kaita asibiti kada mu rasa cikin nan” sai
ta katse kiran kawai cikin gaggawa ta nufi dakin sumayya.
Murququsu ta cimmata tana yi da malelekuwa daga saman gadon har qasan carfet din
dakin,tun daga kan gadon jini ne har qasan dakin,wata azaba ke ratsata ilahirin jikinta,duk
da azabar da takeji bai hana hankalinta tashi ba,tasha jin ana cewa zubar jini hadari ne gun
mace mai ciki tun daga shigar ciki zuwa haihuwarsa,tsoro fal da fargaba ke zaga
zuciyarta,tsoron rasa cikin jikinta,tsorom rasa gudan jininta
“Ki taimaka kin don Allah amarya kada na rasa baby na” ta fada hawaye da gumi na hade
mata saboda tsabar azabar radadin da mararta ke mata,ga tarin mamakinta sai taga zainab
din ta sheqe da dariya
“Kadan kika gani,ci gaba da karbar gashin ciwon rasa d’a kafin ki rasa mijinki ma baki
daya,nice sila ba zan iya taimaka miki da komai ba,burina nake so ya cika” sai ta sake
takowa zuwa gabanta ta ranqwafo
“An fada miki akwai ranar da kishiya zata so kishiyarta ne?,an gaya miki ni sauna ce da zan
dinga miki bauta?ko an fada miki wawiya ce ni bansan me nake ba?,lallai dukkan wanda ya
riga ka kwana tilas ya rigaka tashi,wannan ya isheki ishara game da kaidin kishiya,ke
yarinyace,bakisan komai ba sumayya,daga yau zaki shaidi kaidin kishiya” ta fada tana
2
juyawa ta fice ta barta a dakin tare da komawa falo tayi zamanta.
Runtse idanunta tayi wani abu na dawafi kan qwaqwalwarta,babu shakka ayanzun
maganganun da zainab ta furta mata sunfi mata ciwo fiye da ciwon dake
nuqurqusarta,tana nufin ita ta mata silar abinda ke faruwa yanzun da ita?,me ta aikatama
zainab din haka mai muni da zata zama silar rabata da abinda ta jima tana dakon isowarta
gareta?,don kawai sun hada miji?,saboda kawai suna qarqashin inuwa daya?WANNAN
ITACE KAWAI HUJJAR?dafe mararta tayi tana ci gaba da kallon yadda jini ke kwaranya
yanabin qafafunta tare da bin lafiyar carfet dinta.
Tana jin qarar tsaiwar motarsa ta miqe da hanzari ta shige dakin sumayyan,kanta
tsaye ta nufi kan drower din ta kwaso magungunan dake ajiye a kai ta riqe a hannunta
tana kallon sumayyan taba murmushi sannan tace
“Yanzu zaki ga babban kaidina don na tabbatar bakisan da zaman wadan nan magungunan
ba,baki ta saki tana kallonta tare da jijuya kai cike da azaba,ko magana ma ta kasa yi,sai da
taji takun shigowarsa yana qwala musu kira ta saki kuka tana jujuyasu tare da matso
hawaye tana fadin
“Me yasa kika aikata haka sumayya?,me yasa zaki raba shi da farincikinsa?,abinda ya jima
yana nema sumayya shine yau zaki zama silar rabashi da shi, ina ma ni Allah ya bawa
sumayya kin cika butulu ta gaske,wayyo Allah yau mun rasa yaronmu'”sai ta rushe da
kuka,wani duka zantukanta suka yiwa dodon kunneta,sai ta daga kai tana duban baki qofa
saboda ganin inuwar mutum,take idanunta suka sauka cikin na mukhtar wanda ke dauke
da tsantsar bala’in da bata taba katarin ganinsa cikin idanun nashi ba,tsaf mukhtar yaji
duka abinda zainab din ke fada.yi tayi kamar bata ganshi ba taci gaba da cewa
“yanzu har da maganin ‘yan shaye shaye sumayya da tarbiyyarki da komai..
“Kasa ci gaba da daukar batun kunnuwanta sukayi, dummmm taji sunyi mata,a hankali ta
soma jin jiri na kwasarta tana daga zaune,cikin ‘yan sakanni wani duhu ya mamaye
idanunta ta daina gani ta daina ji.
*********
****
Sannu a hankali ta soma yunqurin bude idanunta har taci nasara ta kammala budesu
baki daya,idanunta suja sauka kan ruwan dake rataye yana shiga jikinta sannu a
hankali,take abinda ya faru da ita ya dawo mata tartayi hanzarin fadin
“la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin “bakinta ya furta
“Hmmmm,kamar gaske” muryarsa ta daki dodon kunnuwanta,da sauri ta waiga ta dubi
bangaren da sautin ke fitowa,mukhtar ne tsaye hannayensa nannade a qirjinsa,duba daya
zaka yi masa ka fuskanci a yamutse yake,har yanzu idanunsa jajur suke tamkar an badesu
da barkono,kafin tace wani abu ya tako zuwa gaban gadon da take. Babu shakka da zata
iya da tashi zata yi ta arta ana kare saboda yadda kamanninsa suka sauya baki daya kamar
wani mayunwacin zaki
“Sumayya,ban taba zaton soyayya zata juye ta koma qiyayya ba sai yau,babu shakka kin
Cuce ni kin zalunceni, kuma Allah ya isa tsakanina dake, don bazan taba iya yafe miki ba,na
zauna da ke tsawon shekaru ina kare martaba da mutuncinki, ina tattalin farincikinki ashe
ni nawa kike rusawa,meye aibuna da bakison ki haihu da ni?,me yasa baki gaya min ba tun
wuri nayi nesa da rayuwarki?,a yau na tsaneki tsanar da ban taba yiwa wata halitta
makamanciyar irinta ba, na gani da idona ba gaya min akayi ba”zuciyarta na mata wata
iriyar muguwar suya ta bude baki don kare kanta duk da rashin qwarin gwiwar da take da
ita,sai ya watsa mata magungunan da kuma sakamakon gwajin da ka yi mata na dalilin
barinta wanda ya nuna maganin zub da ciki ta sha
“Allah ya saka min sumayya na dora buri kanki amma kin zalunceni” abun mamaki kawai
saiga hawaye na fita a idonsa,abinda bata taba tsammanin ganin ba agreshi
“Zan bar rayuwarki kije kiyi duk yadda kika ga dama da ita,KIJE NA SAKEKI SAKI UKU don
bazan tab iya ci gaba da rayuwa da ke ba” wani tashin hankali ya rikito mata,sai ta ware
baki daya idanunta tana son tabbatar da gaskiyar lamarin,ko dai barin da tayi ya shafi
awaqwalwarta da jinta?.
“Haba my dear wannan danyan hukunci haka?,ai yayi tsauri” ta fada tana isowa gareshi
cike da kisisina
Dakata da Allah!”‘ya katseta cikin kakkausar murya,gabanta yayi mugun bugawa saboda
ta tuno da sharadin da malam ya gindaya mata nacewa kada ta kuskura tace komai har a
qare lamarin,saboda ba qaramin so yakewa cikin ba hakanan har yau duk da daurin da aka
yiwa zuciyarsa da sanya masa ganin baqin sumayya har yau sonta na da sauran tasiri cikin
Zuciyarsa,itadai kawai ta sanya layarta cikin bakinta tayita taunawa,jajayen idanunsa da
suka firgitata ya zuba mata
“Tunda sumayya ta iya yimin haka a rayuwa,to babu macen da zan aura ta kasa aikata min
haka,saboda haka kema kije na sakeki saki uku!”
“lyee!” Ta fada cikin madaukakiyar murya fitsari na kubcr mata take ya fara bin qafarta
saboda azabar rudewa,kai ya sanya ya fice daga dakin,wanda kammala fita su
mama(babar sumayya) suka sanyo kai da alama dama suna cikin asibitin.
Zainab qanwarta ce akan gaba,sai mama da yaya abubakar halima na biye da shi,umma
sadiya qanwar babansu na biye da su
“Yaya sannu yanzu muka ga ya mukhtar din ma ai ya fita” ta fada ba tare da sun ankara baki
daya da yanayinda take ciki ba,haka ma basu lura da zainab dake tsaye gefe ba tana tsuma
tare da kallon fitsarin da ya gama wanke mata qafafu. Kallo daya mamanta ta yi mata ta
fuskanci ba dai dai taje ba duk da cewa akwai ciwo tattare da ita.
Da idanu kawai take binsu tana fata ta farka daga mummunan mafarkin da takeyi, sai
da maman ta qarasa gefan gadon ta zauna ta soma yi mata sannu sannan sumayya ta
tabbatarwa kanta idanuntq biyu,a zahiri komai ke faruwa,wata cukuikuya ta yiwa maman
nata tana sauke wata ajiyar zuciya tare da fadin
“Ya sakeni mama,ya rabu da ni bayan bani da wani laifi”,cikin rudani suke kallonta duk
suna zaton zafin ciwo ne
“Sumayya zafin ciwo ne duka hakan?” Sai ta fashe da wani kuka mai azabar cin rai tana
maimaita fadin
“Walllahi mama ya sakeni.yanzun nan da kuka ganshi ya fita sakina yayi mama” salati suka
saka baki daya wanda ya dawo da zainab hayyacinta
“Allah ya isa ‘yarku ta jawo min masifa,ta jawo min zawarci kashi na biyu garin qoqarin
zubar da cikinta” ta fada tana wucewa fuuuu ta bar dakin.
Shiru ya ratsa dakin, babu wani abu dake tashi sai shashsheqar kukan sumayya wanda
zainab da halima ke tayata saboda tsantsar tausayin ‘yar uwarsy.yayin da zuciyoyin sauran
ke quna,zancan zainab kuma ke musu kai kawo
“Mama har saki uku yaya mukhtar ya yimin, mama wallahi ban aikata ba,na fishi son naga
na haihu mama ki..” Sai ta fara jan numfashi da qyar wanda hakan ya sanya su sake
rudewa,da sauri yaya abubakar ya nufi reception don kiran nurse ko likita,cin qanqanin
lokaci sai gashi tare da likita wanda yake gab da tashi Allah yasa bai fita ba,waje ya fid dasu
baki daya sannan ya rufe dakin,take suka rude da koke koke cike da tashin hankali.
Kusan mintina talatin sannan likitan ya fito bayan ya gama dubata ya mata allurar bacci
tare da sanya mata wani ruwan.ya sanar musu bata buqatar hayaniya,sannan don Allah su
guji tada mata hankali idan baso suke ta hadu da hawan jini ba,don ko a yanzun jini nata ya
fara sama,bugu da qari kuma ta zubda jini mai yawa,godiya suka yi masa sannan suka
koma dakin kowa ya samu gu ya zauna zugum,dukkansu da abinda suke saqawa
zukatansu,daga bisani yaya abubakar ya fice dan yi musu siyesiyen abubuwan da zasu
bugata kafin suga yadda hali zaiyi.
Tun a hanya take sumbatu,ko da wasa bata taba zaton ramin da ta haqa zai rufta da ita
ba,bata taba ganin masifa irin wannan ba,taga samu taga rashi,gidan da takewa kanta
hasashen samun abun duniya yau dare daya an rabata da shi
“Ina!!,wih sam bazai yiwu ba,mukhtar ko baka qaunar Allah sai ka ci gaba da zama da
ni,babu wanda zan sanarwa ma ka yimin saki uku,wallahi yanzu na fara aurenka” maganar
da tayi kenan wadda ta sanya mai adaidaitam juyowa ya dubeta, banda kayan jikinta da
basu nuna alamun akwai hauka tattare da ita ba da babu abinda zai hana yace
2
mahaukaciya ce,a qofar gidansu ya sauketa ya juya ya kama gabansa.
Tunda ya bar asibitin gida ya wuce kansa tsaye tamkar wani mahaukacu,kuka yake
wiwi da haka ya kashe motarsa qofar gidan ba tare da ya samu qwarin gwiwar tura dan
matsakaicin get din ba bare ya iya shiga da ita,dakinsa ya wuce ya fada saman gado yana
dafe da kansa, me yasa sumayya zata yi masa haka?,wanne abu ya mata da zata saka masa
da wannan?,zata rabashi da gudan jininsa,sata rabashi da burin rayuwarsa,shin ta manta
cewa samun d’a shine CUKAR BURINSU shi da ita?,wani kukan ya sake saki kamar qaramin
yaro,sai a lokacin ya fara ambaton sunayen Allah daya bayan daya,sannu a hanakali
nutsuwa ta fara saukar masa,yabar tumurmusa gadon da yake yayi luf saman gadom cikin
yanayin na kwanciyar rub da ciki idanunsa na ci gaba da fidsa qwalla masu zafi.
Kwana daya rak amma sunti kwanaki dubu ciwo da wahala a rayuwarta,baki daya ta
sauya kamar ba sumayya ba,tayi wani mugun dashewa wanda ya sanya nurses suka soma
tunanin tana buqatar qarin jini ko babu jini jikinta,da likita ya duba sai yaga magungunan
qarin jini ma kadai sun isheta sai maida kai gun cin abin mai lafiya.
Ko kallon abincin bata yi bare ta kai ga ci,ko ruwa bata iya kurba a bakinta, ki da yaushe
tana kwance idanunta rufe kamar mutum mutumi,sai da malam yazo shi daya ya shiga
dakin sukayi magana ta tsawon mintina kusan ashirin shi da ita sannan aka fara samun
salama,takan karbi duk abinda aka bata taci koda zata yi amansa, hakan ba um ba um um
sai zubda hawaye tamkar qwayar idonta zai tsiyaye, kusan kowa tausaya mata yake tare da
girgiza da al’amarin,duk da cewa har yau malam kawai ta iya yiwa bayanin abinda ya faru
shi kuma ya sanar da abubakar da umma sadiya,sosai umma sadiyan ta fusata qwarai tace
sam ba zasu yarda ba tilas su maka mukhtar a kotu shi da zainab din baki daya, baisan halin
sumayyan bane?,yarinyar da kusan shi ya qarasa yi mata tarbiyya,malam ne ya hana yace
sam hakan baida amfani,tunda koda sun aikata hakan ba zasu iya maida hannun agogo
baya ba,ba zasu iya gyara lamarin ba tunda abinda zai faru ya riga da ya farun,da wannan
zancan suka rufe batun suka maida hankali wajen kula da lafiyar sumayyan.
Da wani yammaci sumayyan na zaune jingine da bango,bata jima da yin wanka ba tana
sanye da atamfa,mamanta ne da zaina da halima sai khadija da hajara cousing dinta
zauneba dakin suna dan taba hirarsu,sallama akayi suka kalli bakin qofar baki daya suna
amsawa,haj salamatu ce wato umma mahaifiyar abdur rahman ita da qanwarsa
bahija,duk da quncin da zuciyarta ke ciki saida sumayyan ta washe haqora ta sake gyara
zama tana mata sannu da zuwa.
Cikin mutuntawa suka gaisa su halima suka gaidata tare da miqewa suka fice don zuwa
karbo canjin ruwan da suka siya cikin shagon asibitin a dazu
“Sannu sumayya ya jiki?.ya kuma mukaji da wannan abu” umma ta fadi fuskarta dauke da
alhini da tsantsar tausayi,qasa tayi da kanta hawaye na zirarar mata
“Alhamdulillahi umm” ta fada muryarta a karye
“Ki yi haquri kan haquri sumayya,duk da na sanki dama ke gwanar haqurin ce,haqiqa Allah
ba azzalumin sarki bane, ni sam bansan meke faruwa ba,abdur rahman da bahija dai sunje
zasu miki sallama da yake zai sake koma wa jami’atu ummul quraa zai hado masters
dinsa,to da suka dawo sai suka ce sun tadda gidan naku a kulle,babu wanda ya kawo
komai don har mukhtar din ya kira ya masa sallama baice da shi komai ba,sai jiya da safe
saiga mukhtar din yazo gaida kawun nasa,a nan yake gaya masa duk abinda ya faru,wallahi
mama ina jin batun na tabbatar sharrin kishiya ne da asiri ke dawainiya da yaron,cikin
kwana uku tal da faruwar lamarin kada kiso kiga yadda ya fige ya lalace,babban abun
haushin ma duk yadda muka so tunatar da shi wace sumayyan wallahi yaqi fuskanta yaqi
gane wacece ita, har yau da haushi da zargin abun a ransa,amma babu komai mai gaskiya
yana tare da Allah, kuma in sha Allahu Allah zai miki KYAKKYAWAN SAKAMAKO”
” babu komai ai umma,kowanne bawa da irin tasa QADDARAR,kuma shi aure rai ne da
shi,da zarar zaman ya qare sai kiga ko babu sanadi an rabu”.hawaye ne kawai ke ci gaba da
tsiyaya idanun sumayya,tamkar ta zura a guje haka take ji,bata qaunar jin duk wani zance
da ya danganci mukhtar din,tunda mukhtar ya yi mata haka a duniya yaqi bata dukkan
yarda da amincinsa bayan yasan wace ita to babu wanda bazai iya cin zarafinta ya ha’inceta
ya wulaqanta ta ba.
Maganganu masu sanyi umma ta dinga fada mata masu kwantar da rai wadanda suka
sauke kaso mai yawa na bacin rai baqinciki da firgicin da take ciki, sosai taji sukuni cikin
zuciyarta,sai wajejan la’asar sannan umma ta musu sallama ta tafi bayan ta ajiyewa
sumayyan dubu uku tace tasha lemo.
Cikin kwana biyar jikinta yayi sauqi sosai,hakan ya sanya likita ya bata sallama tare da
gargadarta ta rage damuwa ta kuma kula da lafiyarta.
Sosai take samun kulawa daga dukkan wani da yake cikin gidan nasu,kowa haba haba
yake da ita,dakinta daban wannan karon malam yasa aka ware mata don kada su takura
mata,amma duk da hakan wani lokaci cikinsu haliman take kwana,ganin yadda kowa ke
son farincikinta ya sanyata warewa,tayi qoqari qwarai wajen fidda damuwa daga ranta duk
don saboda su,duk da abadini hakan ba mai yiwuwa bane gareta.
Watanta guda da komawa yayanta abubakar ya siya kata foam na wata makarantar
koyon sana’o’in hannu na mata don rage mata kewa da dauke kaso mafi tsoka a cikin
lokacinta wanda hakan zai taka rawa matuqa da gaske wajen hanata tunani ko
damuwa,kama daga dinkin labulaye, zannuwan gado,suturu kayan sawa,carfet zuwa
saqa,hadin su humra,sabulu,man shafawa man kitso da sauransu dukka suna
koyawa,sosai take jin dadin makarantar hakanan ta maifa hankalinta sosai tana dauke duk
wani abu da aka koya mata,har ya zuwa lokacin ba’a debo kayanta daga gidan mukhtar ba
din baki daya ta tsane su ta tsani ganinsu,hakan ya sanya umna halima tace idan an tashi
daukosun a wuce da su gun masu saida furniture a siyar kawai.
ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA”
Kusan a yanzu ya zame mata al’adarta,takan kwashi lokaci mai tsawo kwance cikin
nazarin da tunani kafin bacci ya samu nasarar daukarta.
Yauma kamar kullum tana kwance ruf da ciki,duk da cewa dakin babu hasken fitila
amma idanunta a bude suke tar,kwanyarta na aikin sarrafa tunane tunanen dake bijiro
mata daya bayan daya.
Zumbur ta miqe sakamakon motsin da take ji can qasan mararta,wanda wannan shine
karo na barkatai da take jin hakan cikin wannan satin,sau tari takanyi kasaqe tana sauraran
motsin har zuwa sanda zai lafa mata, hakan ce ta faru wannan karon, bayan motsin ya lafa
sai ta koma ta kwanta rigingine tana mai lumshe idanunta,tana tunanin gobe zata sanarwa
9
mama don tana zaton ba lafiya saboda bata taba jin irin hakan ba.
Qarfe takwas na safe tana tsakar gidan tana shara bayan ta kammala duk wani aiki na
gidan qannanta sun wuce islamiyya wadda suke shiga tara zuwa biyat da rabi na
yamma,tunda tazo ta koma al’adarta ta da,tun kafin tayi aure ita ke hidimar gidan duk da
qarancin shekarunta a lokacin,sai abinda yafi qarfinta ne kawai wanda ba zata iya ba take
barma maman nata shi,to hakan ce ta kasance wannan karon,duk da maman na hanata kai
bama ita ba har su haliman idan suna nan basa yarda tayi komai,amma takan qiya saboda
hakan na matugar debe mata kewa da sata jin qwarin jikinta.
Tana daga rumfarta zaune amma tana iya hango duk abinda ke faruwa cikin tsakar
gidan kasancewar labulen falon a dage yake don ta samu iska ta shiga inda take,da idanu
take bin duk wani motsi na sumayyar da kallo,tausayi da qaunar diyar tata na ratsata, sai
kuma wasu ‘yan sauye sauye data ke ciga da gani tattare da ita,har sai da ta kammala
komai sannan ta shigo falon
“Wash” ta fada wanda ha kan ya sanya maman juyawa ta kalleta
“Lafiya dai ko?”
“Lafiya lau, kawai gajiya nake ji da kasala mama” shiru ta danyi sannan ta sake
dubanta,tunani ne fal cikin zuciyarta amma bata aminta da abinda zuciyarta ke kawo mata
ba don bata jin hakan zai yiwu
“Bakijin komai ajikinki sai kasalar kawai?” Dan shiru tayi sannam tace
“Ummmm,wani lokaci inajin motsi mama har nace zan gaya miki ko zanje asibiti,sai kuma
naji motsin ne kawai baya ko ciwo cikin nawa” ta fada cike da quruciya dake nuni da rashin
sanin abinda ke faruwa da ita
“Tun wajen yaushe kike jin hakan?” Ta tambayeta tana dubanta da saka ran jin amsa
“Eh wajen kwana goma kenan”
“Lallai kuwa ya kamata mu koma asibiti” maman ta fada tana jinjina kai cikin qarafafawa
wanda hakan ya bawa sumayyan tsoro,take hantar cikinta ya kada,kodai wani babban ciwo
ke shirin samunta?,gaza yin shiru tayi saboda tsabar tsoro
“Mama!… bani da lafiya ko?” Ta fada kamar zata saki kuka,murmushi ta saki don kwantar
mata da hanakali, bugu da qari itama bata da tabbas din abinda take zato kansa
“Lafiya lau kike,dauko min wayata na kira malam in sanar da shi idan yaso sa muje kiga
likitan”
“To” ta fada jikinta a sanyaye qirjinta na bugawa duk da maman tace mata lafiyarta
lau,dakin gadon maman ta shiga ta fiddo wayar ta dawo ta miqa mata sannan ta samu gefe
ta koma ta zauna.
Cikin abinda duka bai wuce awanni biyu ba isar su asibitin da shiga dakin ganin
likitan,umartar ta yayi da tahau wani dan gado wanda kusa da shi na’urar daukar hoton
ciki ne.
“Allahu akhbar” shine abinda likitan ke fadi yana jinjina kai tare da girmama iko na
ubangiji.yaro ne kwance cikin mahaifarta ga motsi nan yana yi ga bugun zuciyarsa da
komai,dukkansu ba wanda idonsa bai gani ba daga sumayya har mama,mamaki fal
zukatansu tare da girmama lamarin buwayi gagara misali,sai da ya kammala komai har
EDD sai da ya duba mata sannan yace ta sauko ya koma kan tebur dinsa ya soma rubuce
rubuce.
Magunguna ya rubuta mata wadanda zasu qara mata lafiya sannan ya bata wasu gwaje
gwaje da ya kamata ace a wannam stage din da cikin ke da watanni hudu da sati uku tayi su
“Likita lafiyarsa qalau”furucin ya subuce ya fita daga bakinta jikinta a sanyaye, murmushi
yayi yana dubanta
” lafiya qalau komai yake, babu wata damuwa tattare da shi”sai da ya bata amsar sannan
kunya ta kamata ta sadda kai qasa,batasan cewa tana bala’in qaunar abinda ke cikin nata
ba sai yanzu,wani qwarin gwiwa karsashi da soyayya take ji cikin ruhinta,banu shakka
wannan karon tanajin zata iya yaqi kan cikinta a shirye take.
Basu bar asibitin ba sai da suka kammala duk wani gwaji suka siyi magungunan suka
nufi gida.
Har yanzun maman ta kasa cewa komai kamar yada sumayya ta kasa magana, sam
basuyi zato ba, basu tsammaci akwai sauran ciki jikin sumayyan ba,ZAKARAN DA ALLAH YA
NUFA DA CARA ko ana muzuru ana shaho sai yayi kenan. Hakanan sumayyan ke jin
zuciyarta fes da ita, bini bini ta saki murmushi tare da shafa cikin nata,maman na ankare da
ita,tausayinta ya dinga ratsata,haqiqa babu dan halak din da zai guji haihuwa,babu wata
halitta da bazato ganin jininta ba,dole dan adam ya koka idan ya rasa baya wato ‘ya’ya,abu
ne mai ciwo da cin zukata,Allah kuma maji roqo da addu’ar bayinsa ne,a yau gashi duk
yadda akaso rabata da rabon da Allah ta bata amma hakan bai yiwu ba,ya riga ya QADDARA
yana cikin QADDARARTA haihuwarsa da dadi ba dadi,saboda hikimarsa sai ya bawa yaron
kulawa ta musamman,ya boyeshi daga kallon idanuwa,ta yadda ko mahaifiyarsa bata san
da zamansa ba sai yanzu da buwayin sarki yaso ta sanin.
Tun daga sanda suka koma gida daga asibitin maman ta fara bata kulawa ta
musamman,ta hanata yin komai komai qanqantaraa,duk da babu wani ciwo ko laulayi da
sumayyan keji,lafiya qalau take jin jikinta. Malam na dawowa maman ta sanar masa,sosai
shima ya jinjina lamarin yana qara girmama isa da buwaya ta ubangijito ita kanta
sumayyan ma alokacin ba’a zaci zata kai ba bare d’an dake cikinta
“Yanzu ya zama dole a sanarwa uban yaron saboda yasan da zaman cikin” inji mama.
“Wannan ya zama dole ai,zan sanya abubakar yayimin kiransa ko zuwa gobe ne” cewar
malam.
****
****
****
Kansa na duqe amma gumi tsatstsafo masa yake har ta kafar farcensa, babu shakka baya
ga girman tsohon da yake gani da kuma farin sani da yayi masa kan wane shi da tashin
farko zai qaryata batun da a yanzun yake gaya masa.
“Amma ga wadan nan ka duba hoton cikin ne da aka yi mata a jiya,idan ma duka basu
gamsar ba kana iya zuwa gobe sai kuje da ita da su halima wani asibitin a sake gwada
maka har da watannin cikin” malam ya fadi yana zube takaddun scanning da komai da
komai a gabansa,jikinsa na rawa ya dauka ya soma dubawa,tsaf daya lissafa watannin cikin
zuwa yanzu dai dai suke,sau taji wani abu na zaga shi,madaukakin farinciki ya wadatu a
Zuciyarsa
“Na gode maka ya Allah da baka bata damar salwantar min da ciki ba” ya fada cikin
zuciyarsa idanunsa a lumshe,duk da zuwa yanzu yana mamakin me yasa ta aikata masa
haka?,zuciyarsa kuma na kokwanton ita din ce da kanta?,wani sashi na zuciyarsa kan gaya
masa ita dince mana,tunda kaga shaidu na magungunan cikin dakinta, kuma a baya likita
ya tabbatar da ta sha din.
Sallamarta ita ta katse dogon nazarin da yake,sanye take da dogon hijabi har qasa mai
hannu wanda idan zata shigo wajen malam din haka take sanyashi,din yanzu baki daya irin
wannan shigar tafi mata armashi,duk da dama yana daya daga cikin dressing dinta tun a
da,sam bata ma san da zuwansa ba,tazo ne karbar rubutun da malam din yace mata zata
dinga sha daga tsakanin magariba zuwa isha’i,gefe ta samu kusa da malam din ta zauna
har ya zuwa yanzu bata luta da mukhtar din ba dake satan kallonta,abu biyu yake ji
dangane da ita,haushin yunqurin zub da masa ciki da kuma qaunar jininsa da take dauke
da shi.
“Ka duba su da kyau gasunan” inji malam,wanda maganar da yayi ce ta ja hankalin
sumayyan ta lura da mukhtar din,da sauri ta dauke kanta bayan sun hada idanu,qasa qasa
tace
“Ina yini” kamar wadda aka tilasta ta fada,tasan dole ne ma ta gaidashi saboda malam
dake gun
“Lafilya qalau.ya jiki naki”
“Alhamdulilla” ta fada da qyar tana jan tsaki cikin zuciyarta tare da fadin
“Me ya shafeshi dajiki na ji da nake mai laif”
“Malam rubutun nazo karba” ta fada a hanzarce don so take ta bar falon ba zata juri zama
cikinsa ba
“duba gefan akwatincan ki dauko min farar gorar can” ya fada yana nuna mata,ta miqe ta
isa gun yayin da idanun mukhtar din ke kanta,baki daya yanayinta ya nuna mace mai ciki
ce,cikin ma da ya soma qwari.
Cikin wata silver mai dauke da rubutun yasin da ayatul kursiyyu ya fara zuba rubutun ya
bata ta shanye sannan ya dura mata wani cikin jarka ya miqa mata,a hanzarce ta karba ta
fice a dakin.
Kasa tsaiwa tayi a falonsu sai data dire zuwa dakinta ta ajiye rubutun gefe ta zauna
saman gado dafe da kanta,kuka ne ya kubce mata wanda ba zata iya fadar dalilin sa
ba,sosai ta koka sai data ji sanyi cikin ranta sannan ta rarrashi kanta.
Cikin kunya da nuyin da ada bai jisu ba sai yanzu suke saukar masa ya dubi malam
bayan sun gama tattauna abinda zasu tattauna din
“Malam ina son jin abinda ake da buqata wanda zatabyi amfani da shi” kai malam din ya
gyada yana nazarinsa,duk ya fara qarewa kamar wani kudin guzuri,addu’a yake masa cikin
zuciyarsa Allah ya yae masa abinda ke damunsa
“Babu wani abu da muke sa buqata,yadda sumayya take diyata kaima d’a na nae,tunda ko
babu komai alaqa ta sake qulluwa darajar abinda take dauke dashi” nauyinsa ya sake
kamakashi,ya sadda kai qasa
“Na sani malam,amma ka fini sanin haqqina ne yanzu in ci da ita har ta haife abinda take
dauke da shi,don Allah a fadamin na sauke haqqin da ya rataye a wuya na” dan shiru
malam din yayi sai daga bisani ta numfasa
“Shikenan,kaje ka kawo duk abinda kasan zaka iya”
Kanshi a qasa ya masa godiya sosai, karamcinsa na sake daureshi.yadda malam din ke
mu’amalantarsa kamar ba wanda ya sakar masa diya ba,sakin ma kuma mai kankat.
Cikin mota jikinsa yayi sanyi baki daya,da gyar yake iya tuqi,a yau ji yake ina ma bai saki
sumayya ba duk har yanzun akwai haushi da zargin yunqurin zubar masa da ciki da
tayi,mai yasa baiyi haquri ba ko ya dauki mataki wanda bai zama na rabuwa ba,a lokacin
baisan me ya sanya yaji rabuwa da ita ne kawai maslaha a rayuwarsa ba tunda har bata da
buqatar hada zuriya da shi
“Ke kika jawo sumayya,me yasa?,me yasa kika aikata abinda ya zama silar datse
alaqarmu?” Haka ya dinga fada yana tafe yana tambayar kansa.
Tamkar wanda qwai ya fashewa a ciki haka ya faka motar sannan ya rufeta ya nufi cikin
gidan,sosai yayi mamakin ganin qofar falon a bude sabanin dazun da take a kulle,sai yayi
zaton ko ‘yan uwan zainab sunzo kwasar kaya bayan fitarsa a gidan saboda har yau sunqi
kwashe kayanta
“Sannu da zuwa my mukhtar” yaji muryar zainab na ambata,da sauri ya maida idomsa
inda yake jiyo muryat,zainab din ce ta qure ado sanye sa wata matsiyaciyar doguwar riga
wadda ta bayyana suffarta baki daya,fari take masa tana sake takowa kusa da shi,da sauri
ya daka mata tsawa
“Ke wacce iriyar maca ce,wato da na hanaki bina kasuwa shine kika sauya salon biyoni
gida,to ina gargadinki wallahi ki gaggauta ficewa daga gidan nan don gamuwarmu ba zata
yi kyau ba,don na tsani kowacce mace tunda sumayya ta ha’ince ni taso cutata ba don
Allah ya riga ya rubuta mai taka doron qasa bane” maganar sa ta qarshe ita ta
girgizata,idan har tayi dogon nazari da tsinkaye yana son ce mata cikin sumayya yana nan
zata haifeshi nan gaba?yana nufin ita ta tashi banu riba?,ita tayi biyu babu ko daya?,bata
samu sukunin tambayarsa ba ya daka mata wata tsawa wadda ta dawo da ita hayyacinta ta
soma dubansa tana kada kai
“Wallahi bazanyi biyu babu ba mukhtar,kana nufin taci riba?” Sam tunaninsa bai kai ga
fassara maganarta ba,burinsa guda kawai ta fice masa a gida a yanzun kadaici yake da
buqata,ganin zata bata masa lokaci ya sanyashi fincikar hannunta ya watsa ta waje,sannan
ya dawo ya yibi mayafinta da jakarta ya wurga mata har kan fuskarta ya kulle gidan.
Dawowa yayi ya zube saman kujera yana maida numfashi zuciyarsa na ci gaba da tuhumar
sumayya,ta zamo silar yankewar duk wani jin dadi nasa,wayarsa ce ta soma takura masa
da ruri ya dagata ya duban sunan mai kiran.yaya yahanasu ce,baya da buqatar qarin
matsala akan wadda yake ciki,saboda haka ya kashe wayar baki daya ya ajiye
“Wallahi ban tafi kenan ba zan dawo,na dinga bibiyar rayuwarka kenan saboda ni da kai
kadai zan rayu” ya jiyi zainab na aiko masa da maganar daga inda take,tsaki ya ja don ya fara daukarta a matsayin mai matsalar qwaqwalwa Siyayyar dukkan wani abun buqatuwa ga sumayyan shine abu na farko daya somayi
safiyar washegerin ranar,kai hatta da man goge baki bai rage ba cikin siyayyarsa,sannan ya
dora kudi dubu goma akai.
Sanda kayan suka iso gidan tashi tayi ta bar wajen ma baki daya ta koma daki,yadda
bata da buqatarsu haka bata da buqatar ganinsu,kuka ne sosai ya kubce mata,har yanzu
mamakin mukhtar take da har ya iya amincewa da ta aikata mummunan laifi irin
wannan,ba wannan take buqata ba,baki daya mukhtar ya gaka rushe duk wani tanadi na
raino da suka ciwa yaran da zasu haifa buri,itakam mai yayi saura,ba gwara ya qyaleta ba
baki daya tasan cewa ta rasashi har abada?,dukkan wata kulawa a yanzun da zai nuna
babu wani zaqi da zata mata ballantana ta burgeta.
Tun daga lokacin ya zamto duka qarshen wata zai mata siyayyar dukkan wani abu,tun
daga na ci zuwa na bugata,duk da malam na hana wasu abubuwan amma sam bai yarda
ba,yana jin haqqi ne a kansa kuma nauyi ne da ya rataya wuyansa ya kula da ita saboda
yaronshi da take dauke da shi.
Kusan duk zuwansa yakan tsaya ne daga sori,su gaisa da mama da sauran yaran ya
bada saqon ya juya, baki daya gashi nan dai a tafe ne,amma sam babu wani abu dake
faranta masa illa idan ya tuna ya kusa daukan ‘yarsa ko dansa.
Ta bangaren yaya yahansu kuwa sanda taji labarin sakin,sosai na zainab ya faranta
mata,sai a lokacin ta dinga tuna abinda zainab din ra dinga yi musu,.ta tabbatar har su ta
hada ta asirce shi ya sanya suka gaza tabuka komai,jikinta kuma yayi sanyi da sakin
sumayya,ita kanta ta dunga tunanin anya abinda mukhtar ya gaya mata ya faru ba tuggun
zainab din bane?,tilas ta bar batun tunda abinda ake gudu ya riga da ya faru,amma lokacin
da ya sake dawo mata da batun cikin na nan wani farinciki taji ya mamayeta,tana da
muradin zuwa taga sumayyan amman kunya ta hanata,ta na ganin kowa yasan gallazawar
sa ta yiwa sumayya,da wanne ido ‘yan uwanta zasu dubeta?,sai a yanzun take sake
tausayin dan uwan nata ganin yadda ya sauya kamar ba muntarinsu ba.
****
****
******
Hakanan yau ya tashi da muradin ganin cikinsa,amma ya kasa tantance cikin yake son
gani ko sumayyar duk da zuciyarsa tafi afuwa ga cikin yake son gani,don rabonsa da
ganinta tun randa malam ya gaya masa zancan cikin na nan a falonsa.
Saura kusan kwanaki bakwai lokacin da yake mata siyayyar ya cika,amma duk da haka
da yammacin ranar ya shiga store din da ya saba siyayyar,shugaban gurin na ganinsa ya
san me dame yake buqata,shi ya sanya aka hada masa komai sannan akayi total ya biya ya
karba ya fice.
Qarfe biyar a qofar gidan tayi masa.yana sanye da wani yadi mai qarancin kauri ruwa
bula mai haske wanda aka yiwa aiki da ruwan bula mai turuwa,duk da sauyawar yanayinsa
da rama amma hakan bai hanashi kyau ba,sam rayuwar gidan bata masa dadi saboda a
yanzun shikewa kansa komai,hakan ya sanya ya nemi wani saurayi wanda ke zuwa ya masa
share share.
Halima ce ta soma ganinsa,ta yiwa mamansu magana aka bashi izini ya shiga,duk da
yaran yanzun basa sakewa da shi kamar da, hakan baya masa dadi sam don baiga abinda
su ya shiga tsakaninsu ba.
Cikin girmamawa ya gaida maman ta tambayeshi su yahanasun ya amsa mata duk
lafiya qalau shi kuma ya tambayi masu jiki(wato sumayya), ba wata hira dama tun da can ke
shiga tsakaninsu ba daya wuce gaisuwar,hakan ne ya sanyashi ya miqe bayan an gama
shigo da kayan ya musu sallama ya fice.
Sai ya kasa tafiya ya tsaya a soron.yana da muradin ganin cikinsa gashi ko gilmawarta
bai gani ba bare yaji muryarta, hakan babu wanda ya masa zancanta,jingina yayi da bangon
soron hannunsa harde a qirjinsa yana tunanin ta yadda zai ganta din,cikin ikon Allah sai ga
zainab ta fito tana sanya hijabinta zata shagon kusa da gidansu ta karbo klien zata wanke
kwanukan da suka kammala abincin dare da su
“Yauwa zainab,don Allah taimaka min ki fito min da yayarki mu gaisa” ya fada yana gyara
tsaiwarsa,mamaki ya cikata,kamar tace wani abun kuma sai ta fasa ta juya ta koma ciki.
A dakin sumayyan ta tarad da maman tsaye kanta tana mata fadan rashin fitowa su
gaisa da mukhtar,tundanko banza dai ai uban d’anta ne,abinda ya faru kuma babu wanda
ya ruga ya gogeshi cikin KUNDIN QADARARTA, hawaye ta soma gogewa abinda maman bata
so kenan
“Amma mama meye amfanin fitar tawa mu gaisa,tunda dai lafiya qalau nake”
“Na san da wannan,ko banza ai ko baya ta taki zai so ya tabbatar da lafiyar abinda ke
cikinki ko” maman ta fadi
“Shikenan kiyi haquri mama zan dinga gasheshi” tausayinta ya kamata,tana shirin yin
magana zainab din ta shigo ta fada mata abinda mukhtar din ya buqata
“Kin gani ai,sai kije ku gaisa” ta fada ta juya tana ficewa,hajibinta ta janyi dake rataye jikin
sif ta zura sannan tayo waje.
Tunda ta fito ya zuba mata ido yake kallonta,sosai wannan karon cikin ya fito fiye da
waccan karon,hatta tafiyarta ta soma sauyawa,kanta ma qasa din bata son hada ido da shi
har ta qaraso,daga can gefe guda ta tsaya sannan tace
“Ina yini” ba tare data daga kai ta dubeshi ba
“Lafiya lau,ya jikin naki
“Alhamdulilah” ta fada cikin sanyi,sai shiru ya biyo baya kowa da abinda ke saqawa cikin
Zuciyarsa.tsaiwar ta fara mata tsauri har ya lura da haka,sai ya waiwaya ya gangaro mata
wani dutse da suke tokare qofa da shi ya furta
“Ga guri zauna” bata musa ba ta zauna din don tana da buqatar hakan
“Me yasa sumayya?,why?,kinga ayanzun kin zama silar da zamu raini yaronmu a
mabanbanta gurare abinda ko a mafarki ban taba hasashen faruwarsa ba”ya furta wani
daci na zagaya harshensa, idanuwansa na sauya launi,da sauri ta daga kai ta watsa masa
fararen idanuwanta,take wani bacin rai ya soma bijiro mata,wato har yanzun zarginta yake
kenan?,dama abinda yake son gaya mata kenan da har ya fiddo ta tana zaman zamanta
tana lallaba rayuwarta.
Qin tankawa tayi sai ma yunqurin miqewa da ta soma yi saboda bata ga alfanun ci gaba
da tsaiwa a gabansa ba,ganin tana niyyar wucewa ba tare da ya gaya mata abinda zaya fadi
ba yace
“idan nayi lissafi dai dai cikin ya kusa shiga wata na tara,zuwa yanzu ya kamata ace anyi
siyayya,ki rubuta duk abinda kike da bugata jibi zan dawo na karba in sha Allah”
“Ka kawo duk abinda kake ganin zaka iya” ta fada tana mai shigewa gidan ba tare da ko ta waiwayoshi ba zuciyarta na suya,idanunta na zafi.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]