QADDARAR SUMAYYA CHAPTER 19

Advertisements

_____

QADDARAR SUMAYYAH


CHAPTER 19


Goguwar dawowarta sumayyan da taji ya sanyata daga kai ta bita da ido har ta shige
dakinta.
Cikin mintinan da basu wuce biyu sumayyan ta fara jiyo qauri wanda gake da alama
da wani abu aka sanya cikim garwashi,data luta sosai sai ta fuskanci daga bangaren zainab
ke fitowa,mai da kanta tayi taci gaba da kallonta,cikin sakanmi qaurin ya buwayeta, hakan
ya sanya ta koma dakinta ta dauko burner da turaren wuta ta fito falon wanda hakan yayi
dai dai da sake ficewar fa’izan zuwa harabar gidan,jikin socket din dake daura da kayan
kallon ta jona ta cikata da turaren wuta,mintina qalilan ya danne qaurin ya koma qamshi.
Tana zaune taji bude get din gidan da qarar motar mukhtar din,wanda hakan ke
alamta dawowarsa,sai ta miqe ta koma daki ta sake feshe jikinta da turare sanna ta nufo
harabar gidan.
Turus tayi ganin zainab gefan mukhtar tamkar zata shige jikinsa tana
dubansa,hannunsa riqe da cup wanda ta cika masa da zobo wanda tuni ya fara
kwankwada,yi tayi kamar ta juya saboda takaici sai kuna taga sam hakan baiyi tsari ba,zai
kuma faranta ran zainab har taci karenta babu babbaka tunda ta riga da taga tsaiwarta.
Fuskarta ta fadada da fara’a,sannu a hankai ta soma takowa gun wanda takalmin
qafarta duj da plate ne ya dinga bada sauti,hakan shi ya janye hankalin mukhtar ya zuba
mata ido,ta masa kyau sosai,ji yake kamar ya tafi ya sureta ya daga sama yadfa suka
saba.yau ta sauya masa sosai sumayyan,da wannan tunanin ta qaraso inda suke ta tsaya
gabansa tana jifansa da murmushi,so yake take sumayyata kinyi kyau,so yake ya yaba
mata,amma wani dunqulallen abun ya danne zuciyarsa.ya sake duban qwayar idanunta sai
yaji wani bacin rai ya kamashi,murmushin da yakeson maida mata sai ya musanyashi da
hade fusjarsa tsaf wanda hakan ya baiwa sumayyan mamaki,saidai duk da haka bata
karaya ba ta miqa hannu ta amshi jakarsa tana masa sannu da zuwa.
Bai amsa ba don ji yayi ya gaza amsawar
“Wash” zainab ta fada wanda shi ya sanya su duja suka dubeta,baikai ga tambaya ba ta
dora da nata jawabin
“Ka gani ko mukhtar,kaga abinda nake gaya maka ko?,yanzu fisabilillahi duk fadin gurin
nan bai isheta ba sai ta takani saboda tsabar raini?” Mamaki fal zuciyar sumayya take
dubanta.ya Allahu,nata salon kenan?matar da tazarar dake tsakaninsu ya isa tiqa tiqan
mata biyu su tsaya shibe zata ce har ta taka ta?,tamkar dama neman abun fadan yake ya
sake tunzura yana ji ana azqlzalar zuciyarsa.juyawa yayi yana jifan sumayyan da wani irin
kallo
“Halayyar banzan da kike son koya kenan ko sumayya?,halayyar da ban sanki da ita ba?,to
bari kiji ni bazan lamunta ba,bana son tashin hankali kin sani, har sau yaushe zan huta daga
dawowata ko iskar gidan ban gama shaqa ba daga shigowarki zaki tada mana fitina?,to ki
shiga hankalinki da ni idan ba haka ba zanyi mugun saba miki”, bata data cewa,to me zata
fada ma tunda ya riga ya yarda ya hau kai kuma ya zauna?,bata baki ne kawai tsayawa kare
kai,saboda haka aladabce tace
“bansan na taka ta ba in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba kayi haquri ya mukhtar”sai
da yaja fasali sannan yace
“Shikenan ta wuce”
“Au ni ba zaka ce ma ta ban haquri ba shikenan na gane matsayina wallahi'” ta fada a zafafe
tana fashewa da kukan kirsa sannan ta kwasa tayi cikin gidan da sauri,don sosai ta shaqa
ba haka taso ya kasance ba,so tayi cikin biyu ayi daya, imma yace sumayyan ta durqusa ta
bata haquri,ko kuma tayi qoqarin kare kanta ko ta masa turjiya ya jibgi banza a gabanta
taci dariya ta more.
Da idanu sumayyan tabi mukhtar din ganin yadda ya diba shima ya bita cikin wani
tashin hankali da yaji ya rikito masa sanda ya fara jiyo sautin kukanta,wanda babu qwalla
ko daya sai tsabar ihu da iya manaqisa,kai sumayya ta kada zuciyarta ta karye,lallai babu
shakka wani sabon SHAFIN QADDARAR TA NE YA SAKE BUDEWA CIKIN KUNDIN
QADDARARTA,

sau ta lallashi kanta kawai ta shige ciki da jakar tasa ta ratsa ta cikin falon

nasu ta wuce sashen sa
A qalla ta dauki kusan minti talatin zaune kafin ya shigo bangaren nasa,fuskarsa kadai
zaka duba ta bayyana maka yanayin da yake ciki,kallonta yayi tana zaune gu
guda,tausayinta nason masa tasiri amma wani abu mai qarfi na maye gurbin tausayin da
jin haushi
“Na kai maka ruwan wankanka” tace da shi,bai amsa mata ba illa rage kayan jikinsa da yayi
ya shiga wankan kawai.
Tana zaunw taga yana shiryawa cikin yadin kaftan ruwan zuma.ya kammala ya zira
hularsa tare sa daura agogom hannunsa, muqullin motarsa da taga ya dauka shi ya
tabbatar mata da cewa lallai fita zaya yi,da hanzarinta tace.
“Ya mukhtar baka ci abincinka ba fa,kuma naga kana shirin fita”
“Sai na dawo” ya fada yana ficewa ba tare da ko ya waiwayeta ba,sai ta zube agun ta sanya
kuka,da sauri ta sanya tafin hannunta ta qunshe kukan saboda fadan da zuciyarta tayi
mata na ba kuka zata yi ba,take ta kama ambaton ‘Allahumma la sahla illa maja’altahu
sahla,wa anta taj’alal hazna iza shi’ita sahla.
Tana daga nan amma tana iya jiyo muryar zainab wanda hakan ya tabbatar mata fita
zasuyi kenan.
Kusan awa guda da rabi ta share zaune tana ambaton sunayen Allah,ya zuwa lokacin
quncin dake cin ranta ya ragu qwarai,wayarta ta soma ruri,ganin sunan mukhtar ya bata
mamaki amma sai ta daga gabanta na faduwa jikinta na gaya mata ko dai ba lafiya ba,a
daqile ya amsa sallamarta sannan ha dora
“Ya zuwa yanzu nasan abinda kika girka tun yamma yayi sanyi, ina so ki tashi ki hada min
fried rice nan da awa guda ina bisa hanya” bata da hurumin da zata musanta masa tunda
iko yake da ita,biyayya a gareshi kuma tilas ne matuqar bai sabawa mahaliccinta ba,tuni ya
katse wayar don haka itama ta aijiye ta nufi kitchen kai tsaye.
Komai suna da shi alhamdulillah tunda yanzun kam arziqi ya zaunawa mukhtar din
gwargwado,da hanzarinta ta shiga hada komai,cikin abinda yai qasa da awa daya da rabi ta
gama tunda ba wata mai yawa bace can,bugu da qari kuna ta horu wajen aiki.
Dakinta ta wuce ta debo kayan baccinta ta koma sashen mukhtar din,cikin toilet dinsa
tayi wanka ta shirya tsaf,wannan duka cikin karatun anty dije ne,falonsa ta koma ta kwanta
saman doguwar kujerarsa,a hankali tunani yayi awin gaba da ita tanayi taba sauke ajiyar
zuciya.
Tarayyarsu da mukhtar tun farkon aurensu kawi yanzu,bata taba sanin so ba sai a
kansa,da shi ta saba da shi ra qarasa mallakar hankalin kanta,dashi ta qarsa cikasa
kammaluwar hankali da rayuwarta,ta yaya zata iya jure wani baqin lamari daga gunsa ta
farad daya?.ya zata iya lamuntar juya baya daga gunsa,idan ma har laifi ta masa a yau kam
zata kawo qarshen horon da yake mata.
Tana tsaka da tunanin ta jiyo muryarsu suna shirin turo qofa,hakan ya sanya tayi
hanzari foge qwallarta,tare suka ahigo manne da juna,sai ta kauda kanta daga saitinsu din
ragewa kanta kaifin kibiyar mashin da ta soketa,ba haka zainab taso ba,wacce iriyar
mayyace yarinyar mara zuciya,ita miji bai bata mata rai tayi fushi da shi ne,sai ta zame
jikinta daga na mukhtar tana masa sallana hannunta dauke da leda mai dauke da tambarin
SS store.
Wuceta yayi kamar bai ganta ya ya shiga daki fuskarnan kamar ta mayunwacin
zaki,tamkar ba shine ya shigo yanzun yana dariya ba,jikinta sai ya mutu murus ta kasa tashi
har aka kusan cin minti talatin sannan ta yunqura ta tashi.
Gefan gado ta sameshi yana waya wanda da alama da zainab din yakeyi ya ilahi ba
yanzu suka rabu ba kuma?,sumayya ta fada a zuciyarta,kafin ta qaraso ciki ya kashe wayar
yana qoqarin kwanciya
“Yaya kace na maka fried rice kuma naga kana shirin kwanciya baka ci ba” a banzace yace
“Bani zanci ba,don ni naci abinci gidansu zainab na cika cikina,ita zaki kaimawa ita ke
sha’awar ci” shiru tayi ta tsaya cak kamar an kafata,me kenan?,wannan zallar wulaqanci
ne,dama saboda cikin zainab din ya tasheta tara saura na dare ta hau sanon girki?
“Ko ba zaki bane ni na taso da kaina na kai mata?” Ya fada yana daga kwancen,tabbas da ta
iya rashin kunya yau da zata yiwa mukhtar ko yaya take, saidai kowanne tsuntsu ance
kukan gidansu yakeyi, tunda ta taso gidansu dai dai da rana daya bata taba katarin ganin
innarta ta yiwa malam musu ba duk girma da wuyar umarnin da ya bata,sai ta kada kai da
dauki flask din ta nufi sashen zainab din.
Har ta rufe qofar falonta amma ta qwanqwasa mata saboda cika umarnin mukhtar
din,minti biyu tsakani aka bude,tana sanye da kayan bacci,kallonta tayi daga sama zuwa
qasa sannan ta yatsina
“Ya akayi”
“Abincinki” ta bata amsa a qaice
“Mtsweeew,bazan iya ci ba gaskiya” bata jira sauran abinda zai biyo bakinta ba ta juya,taku
na shida cikin na bakwai taji tace
“Kawo dai na taimaka miki na dandana kada kiyi wahalar banza” idan kujerun dake gun
sun amaa to itama ta tanka,banza ta baiwa ajiyarta taci gaba da takunta,sai ta tsinto
muryarta
“A sannu dai yarinya,kishi da zainabu abu babu dadi,hattara wlh da ni,yanzu kika fara gani
sai kin fice sa qafafunki” ta fada tana qoqarin maida qofarta
“Ni nafi qarfinki,na kuma fi qarfin ire irenki, irinki dubu ma wallahi saidai suga sumayya su
qyale” cike da mamaki tace
“Au haka kikace?,bari Allah ya kaimu gobe zaki amshi sakamakon wannan diban albarkar
da kika yimin hannun mukhtar,sai nasa ya dakaki wlh cikin gidan nan” tsaki sumayyan ta ja
sannan tace
“Mukhtar ne taqamarki ni kuwa Allah na riqe,da ni dake maga wanda yayi riqo da
kakkaurar igiyar da bata tsinkewa” daga haka ta juya ta barta gun sake da baki tare da saqa
mugun zare sake tada qaimi a kan sumayyan, babu shakka sai tasa an mata daurin butar
malam yadda zata zamo qarqashin ikonta kamar yadda ta soma maida mukhtar.
Ta jima tsugunne gaban gadon tana zubda hawaye tare da roqon ya yafe mata idan ta
masa wani laifine da ya canza shi.yana jinta zuciyarsa na masa suya yana tuhumar kansa
na dalilinsa na quntatawa sumayyar,saidai wani sashe mai qarfi na zuciyarsa na gaya masa
yayi dai dai,da wannan ya shareta har ta gaji da tsugon nan ta miqe.
Bata bari tayi asarar daren ba,alwala ta daura,ta kuma duqufa qwarai wajen roqon
ubangiji ya kawo mata haske.ya tsaresu ita da mukhtar din,tana yi ta zubda hawaye masu
dumi,lallai sai yanzu tasan meye rayuwar aure,ashe a baya duk wasa takeyi?kallon kitse
take yiwa rogo?,ya jima cikin bargon yana kallonta,tausayinta na son tasiri cikin zuciyarsa
amma hakan ya gagara,a haka bacci yayi awon gaba da shi.
**
“WATA RAYUWA…
Wata bahuguwar rayuwa mai ban mamaki ta soma yi cikin gidan wadda ko cikin
nafarkai mafarkinta bai taba biyowa ta irin wannan bigiren ba.
Zainab ta zama tauraruwa mai wutsiya cikin gidan,a zahiri idan kayi naxari da tsinkaye
ba zaka kawo ita ke sarrafa lamuran gidan ba,saidai ga duk wanda ya taba katari da fadawa
halin da sumayya ke ciki tashin farko zai fuskanci inda zaman gidan ya sanya gaba.
Ta bawa asiri amanna,kusan shi ya zame mata jagorar zamowarta mata ga mukhtar
din,baya ga haka,macace mai tsananin kissa wadda ta cakuda ta da asirin take matuqar
tasiri kan mukhtar din,cikin salo da sanabe zata bashi umarni kai tsaye zaya aiwatar.wanda
idan kai dake gefe ka kalla zakayi zaton tsabar iya biyayya ce da iya zama da miji,saidai ina
sam ba haka abun yake ba,asiri ke yawo kan qirji da qwaqwalwarsa,du kkan wani lamari da
ikon sarrafawa na hannunta,abu GUDA DAYA TAK da yayi mata karen tsaye cikin tafiyar da
aikinta shine SUMAYYA,ta kasa maida ita qarqashin mulkin nallakarta,wanda hatta su yaya
yahanasu yanzun na qarqashin ikonta,suna jin zafin yadda take mulkasun amma koda
kudi basu isa suyi qorafi ba,saidai a bayan idonta suyita zagi da qorafi iyakarsu kenan.
Abu guda data fuskanta shine,sumayyan ta lazumci karanta qur’ani,alwala ta zama
abokiyarta,qur’ani ya zama abokin hirarta,koda wani abu ya tsorata ta abu na farko dakw
fitowa bakinta shine SUBHANALLAH KO BISMILLAH, bata mantawa akwai ranar da aka
kawo mata yaronta da ta haifa da bashir wato nafi’u,yaro ne maras ji sosai suka batawa
mahaifinsa tarbiyyar yaro tunda yanzun haka yana hannun mama amarya ne mahaifiyat
zainab.yana wasa da macijin roba,daidai fitowar sumayya ya wurga mata shi wanda sam
bata ma kula da yaron na gurinka ba, sosai ta tsorata amma abinda ya fara fitowa daga
bakinta shine BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM,daga haka ta shige zainab din na taya dan
nata dariyar yadda ya tsorata sumayyan kallo basu isheta ba.
Kusan babu wanda yasan halin da take ciki banda anty dije itama don tana ganin ita
daya hankalinta bai kai mizanin sarrafa matsalolin irin wadan nan ba ita daya,tana amfani
da shawararta kuma ta qaruwa tare da ganin nasarori,duk da ayanzun ta tattara lamarin
mukhtar tana biyarshi da addu’a,sau tari wani lokacin ko ganinta ta fuskanci baison
yi,abinda tafi daga mata hankali kenan,wasu lokutan kuma sai ka ganshi kamar ba shi ba
ya koma mata yaya mukhtar dinta.
Duk abinda ta gani tana dorashi ne kan mizanin nan da hausawa kance AURE IBADA
NE ta yadda kumma tayi imani da hakanne,don sau tari anty dije na maimaita mata kalmar.
Su biyun ne zaune cikin talon kowa na sabgar gabanta,sumayya na guga saboda
socket dinta ya lalace ya tilasta mata fitowa falon don yin gugaryayin da zainab ke zaune
saman kujera qafa daya kan daya kamar yadda ta saba zama kenan cikin izza da nuna ita
watace,gama share falon da mopping dinta kenan ga zauna don ta huta,duk wanda ke da
girki shike wannan aikin, ba laifi zainab din nada tsafta dai dai gwargwado.
Sallamar da ake zabgawa daga harabar gidan shi yaja hankalinsu,zainab ce ta miqe
tare da aijiye remote din hannunta ta bude qofar ta fita,fadima ce ita da jamila diyar yaya
yahanasu,bakinsu a washe suka soma takowa zuwa inda take
“Ku tsaya daga nan da Allah ku cire takalmanku kada ku batawa mutane waje yanzu na
gama mopping” da fari jamila tayi dum amma ganin fadima ta tsugunna ta cire nata ya
sanya itama dole ta cire,juyawa tayi fuska a cusgune su kuma suka bi bayanta.
Zama tayi kan kujerar ta maida qafarta yadda take,suna shirin zama saman kujerar da
sauri tace
“A’ah,da Allah ku zauna a qasa,ai carfet ne,idan kuma baku iyawa ku tafi can ga nata
kujerun can ku zauna a kai” tsabar qin da suka yiwa sumayyan suka gwammaci zamaa
qasa,suka gaidata ta amsa da qyar,ko kusa baau dubi sumayya dake guga ba,haka suma ko
qurar data kwasosu bata kalla ba
“Dama yaayaa ce ta aiko mu gun yaya muntari” inji fadima,wani kallo ta watsa musu
“Bacci yake,ku fadi saqon sai na gaya masa idan ya tashi” shiru suka dan yi sannan suka
dubijuna alamar basu son fada,hakan yasa ta dubesh kai tsaye
“Sai ku tashi ku koma da saqonku,ko kuma wadda ta aiko kun tazo da kanta”
“Yaaya yahanasun?” Suka fada tare cikin mamaki
“Eh,ita din mana,to meye?,kunga ku tashi ku bani guri da Allah,muta ne sai shegen binbinin
tsiya haba” ta fada tana jan tsaki tare da mai da kanta gun t.v.
Zuciya ce ta zowa jamila wuya,bayan sun miqe sai ta kasa shiru
“Kema halin fa’izan gareki?,lallai akwai butulu a duniya da yawa,to wlh bari kiji,.baki isaki
shiga tsakaninmu da dan uwanmu ba wallahi”kallon banza ta yi mata sannan ta saki
murmushi tana kada qafa
“A’a’ahhhhhh…yaro man kaza,quruci dangin hauka”
“Ke za’a gayawa wannan ai mahauk…
“Idan kika sake bakinki ya qarasa wallahi sai na tashi na tsitstsinka maki mari,na kuma
tattaka ki naga wanda ya tsaya miki..” Ganin yadda ta yunquro kamar zata sanya musu
dukan ya sanya fadima ta janyeta suka fice jamilan na ciccika baki tana cewa “ai umman
zata zo naga uban da ya isa ya hanata ganin dan uwanta, mata duka sai shegeb butulci duk
wadda ka yiwa rana sai ta yi maka dare” itakam sumayya na gefe,ci kanku bata ce ba balle
ta dago ta dubi abinda ke faruwa,tana jin zainab din na ci gaba da banbaminta mai kama
da jirwaye da kamar wanka
“Ni wallahi babu wata yar miji da zata shiga rayuwata tunda ba ita ke aurena ba,idan da
can an saba muku toni wallahi bazan lamunci a dinga tatsemin miji ba” ita dai ko kallo bata
isheta ba,cikin hakan mukhtar ya fito sanye da doguwar riga jallabiya
“Ke dawa haka ina daki ina jiyoki?”
“Ni da danginka mana,haka akeyi basu da aiki sai zuwa roqo tsakani da Allah?” Zancan sai
ya baiwa sumayya mamaki, iko sai Allah, ke kudin nan ba naki bane,kuma wanda suka roqa
din ai dan uwansu ne ko?.
Tsaki yaja yana zama kan daya daga cikin kujerun
“Kudi take so zata biya kudin makarantar yara,na kuma gaya mata tayi haquri ribar
hannuna na baki zaki fara saida mayafai,kasuwa kuma yanzun sai a hankali ba kamar da ba
amma ta qi yarda,gwara da suka tafi din don ko sun sameni ba ni babu abinda zan iya
bayarwa”
“Ato nidai na kora musu jawabi” ta fada tana tafa hannuwa
“Samamin ruwan zafi du Allah” ya fada yana kashingida.
“Gaskiya muntari na fara gajiya, aikin gidan nan fa akwai wuya kawai ka sama min mai aiki”
ta fada a shagwabe, murmushi ya danyi sannan yace
“Kada ki damu,kafin a kama azumi za’a samar mikin ki bada cigiya”fari tayi da ido cikin
salo” kai dear na ko gode..bari na kawo maka”‘miqewa tayi tana wani rangwada tare da
sakin wani dan qaramin fito na jin dadi,a duniya bata da burin wulaqanta sumayya,tunda
ita taqi samuwa to ko ta hanyar mukhtar din kawai ya isheta tunda tana cimma burin
cusguna mata.
A hankali idanunsa ya sauka kanta,tana gefe daya tana guga abinta, sai ka rantse bata
cikin falon ko batasan meke faruwa ba,saidai can qasan zuciyarta ita kadai tasan meke
nuqurqusar zucida da gangar jikinta baki daya, baki daya ba mukhtar dinta take ganin ba a
yanzun,siffar ce kadai tasa,rabon da ta sanya shi idaunta kwanaki uku kenan,idan yaso
yana iya daukar kwananta ma ya kaiwa zainab din,saidai ci kanka bata taba ce masa,ta
debo idanu kawai ta sanya musu.
A nutse yake nazarinta wani abu na fisgarsa,sosai yaga ta fada ta sake haske,qirjinta ya
sake cika sosai sai hancinta da ya sake fitowa saboda rama,riga mai dogon hannu da skert
ne a jikinta na wani yadi mai roba,kanta na kame da ribbom don ta jima rabonta da kitso
“Sumayyah” ya furta a hankali ba tare da ya san kalmar ta fito ba,sarai ta jishi amma sai
tayi zaton gizo kunnenta yake mata,saboda haka tayi banza da shi
“Sumayya ba zaki kula ni ba?” Ya kuma fada a tausashe,sosai muryar ta bugeta, murya ce
irin wadda yake mata amfani da ita a zamanin BAYA, hakan ya sanya ta gaza daurewa,sai ta
daga idanunta da suka cika taf da qwalla ta azasu kansa,kallon kallo suka farayi kowa
zuciyarsa da gangar jikinsa na shirin motsa masa soyayyar dan uwansa da suke tunanin
sunyi bankwana da ita.
Muryar zainab dake takowa daga kitchen ta raba tsakaninsu,sai ta gaza ci gaba da
gugar ta zare socket din ta tattara kayanta ta wuce dakinta, kan gado ta fada ta saki wani
marayan kuka,zuciyarta da jikinta na azabtuwa da qaunar mukhtar da kewarsa.
***
****
****
Da izzarta da bacin rai ta diro gidan tun qarfe tara na safe,saidai ga mamakinta tana
qarasowa cikin falon ta qwala sunan zainab din wadda ta fito cikin kayan bacci sai ta nemi
duk wani bala’i da ta tanada ta rasa,hasalima ma sai ta fara gaida zainab din,sheqeqe tace
da ita
“Lafiya?,me kika zo yiwa mutane a gida tun farar safiyar nan,ko farkawa masu gidan basu yi
ba?”
“Haba ko hutawa ai nayi ko zainabu abu”
“Hutu kika zo yi gidan da ba naki ba?” Ta fada tana rungume da hannunta a qirji
“A’ah..to…to daka jiya na aiko yara zasu karbi kudin makarantarsu ne sai kuma basu samu
ganin kawun nasu ba,shine ni na biyo sahu,saboda koda yaushe za’a iya korarsu daga
makaranta” gyara tsaiwarta tayi
“Au basu gaya miki rashin mutunci da rashin tarbiyyar da suka zo suka yimin ba?” Duk da
cewa tasan komai amma sai ta samu kanta da gaza nunawa
“Su su fadiman?”
“Eh su din fa,don haka ina mai sanar miki cewa sun jaza miki,ba zaki samu damar ganin
mukhtar ba, bacci yake koma ba haka ba wallahi ba zaki ganshi ba,ki tashi sawunki a likkafa
ki tafi,babu mai matsawa mijina da shegen roqe roqe” idanu yaya yahansun ta zuba
mata,tana so tayi masifa amma ta kasa,kamar an wanke zuciyarta haka takeji.
Tunda ta idar da sallar walha ta bingire da baccin da batasan sanda ya dauketa, muryar
zainab din ta dinga jiyowa sama sama wanda shi ya farkar da ita,bata da niyyar fitowa
amma tilas ta fito din sabida yunwar da ta tashi da ita.
Zainab din na tsaye kan yaya yahanasun tana zubda shika shikan rashin mutunci.yaya
yahan tayi muqus kamar ba ita ba sai idanu da take bin zainab din cike da mamaki ba tare
da ta iya tankawa ba,fes sumayyan ta fuskanci meke faruwa tunda na jiya ma gaban idonta
akayi,sosai taji ranta ya baci,a rayuwarta ta tsani wulaqata babba sam,a kwanakin
quruciyarta har kuka idan taga babba cikin wata iriyar rayuwa,ko ba komai ko bata girmesu
ba yaya yahanasun ai tsatson mukhtar ce duk lalacewarta, ranta taji yana baci hakan ya
sanya ta gewaye ta bayan kujerun ta bude qofar da zata sadata da falon mukhtar zuwa
dakin baccinsa kai tsaye ta shige,wanda hakan shi ya ja hankalin zainab,da sauri ta fara
kiranta da niyyar tsaidata saidai ko qurar data kwaso bata kalleta ba bare ita,hakan ya
sanya ta rufa mata baya,tana shiga falon ta bame qofar dai dai lokacin da zainab din ke
qoqarin sanya qafarta a falon,tana iya jiyo hayaniyarta akan ta bude qofar kada ta tasar
mata miji,banza ma ta fita saboda haka ta nufi dakin gadon.
Kan side bed drower idaninta ya fara sauka sanda take qoqarin isa ga mukhtar din
wanda ke daga can saman gadon yana barci,garwashi ne tare da wani qullin tsumma a
kai,a hankali ta taka zuwa inda kayan suke,idanu ta zuba musu tana nazarinsu,babu
alamun turaren wuta zata sanya don bata ganshi ba,hakanan taji bata aminta da qullin ba
musamman da taga launin wani irin tarkace dake ciki,sai ta kunce qullin bakinta dauke da
addu’o’i ta tura bandakin mukhtar din ta shiga,cikin masai ta zazzage dukkan maganin tayi
plushing dinsa.
A hankali ta soma ambaton sunansa hannayenta harde a qirjinta fuskarta a dinke
tsaf,idanunsa ya soma warewa kanta kafin ya gama budesu baki daya cike da mamaki,ya
manta rabonsa da ya ganta cikin dakin,zai ambaci sunanta ta dora yatsanta kan lebanta
sannan kai tsaye tace
“Tashi” ba musu ya yaye bargon ya tashi,sai ga taka zuwa gefansa ta zauna,idanunta sosai
cikin nashi ta soma magana muryarta can qasa
“Wacece yaya yahanasu a gunka?” Cikin rashin fahimta yake dubanta,sai kuma ya bude
bakinsa a hankali
“Yayata ce”
8:24 AM EO
“Zainab kuma fa” hade rai yayi yana jin qin wani abu da zai taba martabarta cikin ransa
“Mata ta ce”
“Cikinsu wa zaka iya sauyawa” take yaji zuciyarsa ta harzuqgo
“Kinga…bansan.”
“Riqe maganarka tukun” itama ta katse shi
“Ka tashi ka wuce kaje tana son ganinka yanzun nan” ta fada kanga tsaye cikin bashi
umarni tare da miqewa abinta tana shirin ficewa,binta yayi da ido cike da mamakin yadda
yau ta dumfareshi kai tsaye a yau din tana kuma bashi umarni,hakanan yaji ya kasa
musanta mata,sai ya sauko da hanzari ya zura takalminsa yabi bayanta.
Bakin qofa suka tadda zainab,ga mai hankali kallo daya zaya yi mata ya gane
hankalinta a matuqar tashe yake,ita kadai tasan wahala da kuma kudin da ta kashe kafin
samuwar maganin,a yau akeso ta yiwa mukhtar din ya kuma shaqi hayaqin sosai,kusan sai
yau ta samu wannan damar,amma ta fuskanci tana neman bare mata,saboda haka suna
fitowa ta fada dakin don duba abinda ke wakana ba tare da ta kuma bi ta kan su yaya
yahanasun ba.
Tana bayansa har suka qarasa inda yaya yahanasu taje zaune tana kallon ikon Allah,a
mutunce sumayyan tace
“Yaya ina kwana?”
“Lafiya” ta amsa babu yabo ba fallasa,tana son ganin kyawun kyautatawar data mata idan
da hali ta mata godiya amma sai ta kasa,dama sumayyan ba domin ita tayi ba,tayi ne
domin girman Allah da kuma girman da zumunci ke da shi a wajen ubangiji,hakanan ko ita
ba zata so ace yau yaya abbakar ya auri wata da zata rabashi da su ba,ko ita ta haifa ya auri
wadda zata rabasu din,kitchen ta wuce ta soma hadawa kanta dan abinda zata iya ci,ko
kafin ta kammala ta fito ma falon babu kowa da alama ta tafi,sai ta zauna ta fara kurbar
ruwan shayinta.
Kamar daga sama zainab din ta fito tana banbamin masifa kamar zata ci baki mukhtar
na biye da ita yana son shan gabanta amma ya gaza cimmata,qerere tayi a kan sumayya
wadda ko mutuncin kallonta bata samu ba
“Uban wa ya saki ki tabamin turaren wuta na?” Sosai abun ya bata mamaki, har tana iya
bude baki tayi cigiyar kayan data tabbatar ba na Allah bane?,qare matsota tayi tana huci ta
kuma maimaita tambayar tata, ganin zainab din na qoqarin kai hannunta jikinta ya sanya
sumayyan dubanta
“Kada ki soma,don fankan fankan bata kilishi wallahi kika dakeni bazan dubi girmanki ba
tsaf zan rama” idanu ta zaro tana nuna qirjinta
“Ni zaki daka don ubanki,to dokeni din'”
“Wai meye haka ne zainab ba tun cikin daki nake miki magana ba?,ke sumayya tashi ki
koma dakinki” wani kallo ta watsa masa sannan ta dakata da shan tea dinta
“Kayi haquri amma bata isa ba wlh don yanzu na fito ban kuma kammala uziri na ba,kana
iya janye matarka idan na gama na tafi ita ta fito” ta fada tana ci gaba da kurbar shayinta
duk da wata iriyar tafasa da zuciyarta ke mata,jinta take dai-dai sa su baki dayansu,banda
daraja da girman sa da take gani babu abinda zai hana ta yayyaba masa baqaqen
maganganu masu zafi
“Muje nace zan biyaki kudin ko?” Sai ta sauke ajiyar zuciya,dama abinda yafi damunta
kenan,don sake samun wani maganin wannan da sauqi
“Allah ya ceceki” ta fada tana huci sannan ta juya tabi mukhtar din,cak shayin ya tsaya
mata a wuya,ambaton sunan Allah ta dinga yi don ya kawo mata dauki,tabbas sai yau ta
tabbatar mukhtar dinta ba cikin hayyacinsa yake ba,kayan karin da bata gama ci ba kenan.
****
Wani nannauyan bacci ne ya dauketa tun bayan kammala sallar asuba, hakan ya sanya
bata tashi ba sai wajen sha daya saura na rana saboda zafin rana da ya fara hudo labule.
Da wata mahaukaciyar yunwa ta farka,saboda haka bandaki kawai ta shiga ta wanko
bakinta ta shiga kitchen don samarwa kanta abinda zata ci,don bata sa aka ba tasan ba
samun abun kari zata yi ba,haka ne yake faruwa duk ranar girkin zainab din,shi kansa mai
gidan wani lokaci sai dai ya fita haka.
Sam bata lura da meke faruwa ba sai data shiga cikin kitchen din sosai,nafi’u ne yaron
zainab tsaye dare dare kan stool yana sauke dukkan farantanta na tangaran dake jere cikin
glass drower dinta yana sakinsu qasa daya bayab daya suna tarwatsewa.
Da sauri ta qarasa ciki tana kiran sunansa cikin tsawa,ko gezau baiyi ba bare ya fasa
aikata abinda yakeyi din,hannunshi ta riqe gam kana ta saukeshi daga kan stool din tana
dubansa ransa a bace
“Baka da hankali?,ko bakasan me kake yi ba?,ko bakasan abin amfani kake lalatawa
ba?”,cikin rashin kunya yace mata
“na sani mana”abun sai ya bata haushi ta kama kunnansa ba tare da ta murde ba tace
“wato tsabar rashin ji ne kenan ko?”
“Sakarmin kunnena ail kema bake kika siya ba,kuma Allah ya isa na da tabamin kunne da
kikayi” sosai yaron ya bata haushi da mamaki,ta sanya tafin hannunta ta buge masa
baki,wata qara ya saki kamar wanda aka sanya wuqa aka yanke masa maqogaro yana fadin
“wayyo bakina wayyo mama ta fasamin baki”.
A hautsine ta fado kitchen din tana kiran sunanshi,da sauri ta qarasa inda suke tsaye ta
ture sumayya tana fadin
“me kika yi masa?,me tayi maka nafs(da yake haka take kiransa)”
“Bakina ta dakarmin mama duba ki gani”hannunsa ta sauke tana duba bakin,babu wani
abu da yayi tunda duka duka dukan data masa ba wani mai zafi bane,waiwayawa tayi ta
dubi sumayya dake tsaye rungume da hannu tana dubansu
” dukarmin yaro kikayi saboda bakisan ciwon haihuwa ba ko?,to wallahi sai na rama
masa”‘sai kuwa tayo kan sumayyan gadan gadan.
Ko alama bata motsa ba har ta qaraso inda take,ta daga hannu da niyyar zuba mata
mari caraf ta kama hannun nata ta yarfar da shi gefe,sannan cikin bacin rai tace mata
“Bansan ke din wace iriyar uwa bace, ban kuma san irin tarbiyyar da kika bama yaronki
ba,amma bari na gaya miki,matuqar irin wannan tarbiyyar ita kika bashi to ba shakka kin
cuci kanki,abu na gaba duk iya zaluncin da zaki aikata cikin gidan nan kiyi,Allah na sane da
ke,amma kada ki soma gigin daukar hannu kice zaki dake ni,don baki haifeni ba,ba kuma
kisan ciwo na ba kamar yadda kika ce bansan ciwon haihuwa ba,kuma kema ba Allah kika
yiwa fadanci ba ya baki,ganin..hun da zainab din ta qwalla gami da dora hannu bisa
ka ya dakatar da ita daga maganar da takeyi,sai tayi sororo tana dubanta tare da tunanin
ko zainab din nada ciwon hauka ne dake tashi lokaci bayan lokaci?.
Sam bata fahimci tarko bane ta dana mata sai data ga shigowar mukhtar cikin kitchen
din a rude,ashe tuni taga giftawar inuwarsa ita zainab din,binsa tayi da kallo sanda ya nufi
zainab,ta manta kwana nawa rabon da ta sanyashi cikin idanunta,ranar qarshe kawai zata
iya tunawa da bata kuma ganinsa ba sai yau,itace randa ya rufeta da fada tamkar zaya
daketa,sabida tayi dan wake abincin dare,ita kuma zainab tace sam bazata ci ba ai dan
wake ba abinci bane,.ya umarceta ta shiga kitchen ta yiwa zainab din shinkafa da miya qarfe
goma na dare,umarnin ya yi mata tsauri saboda haka bata ko tanka ba ta wuce dakinta tayi
kwanciyarta bayan ta kulle qofarta,don tana da yaqinin zaya iya biyota,ilai kuwa ya biyo
sahun nata.yayi bugun duniya taqi ta bude masa,hakan ya sake harzuqa shi, haka ya koma
tare da ci mata alwashin sai ya sabar mata,to tun daga ranar rabon data karbi girki ma cikin
gidan,saidai idan sun kammala a barshi a kitchen,idan tana da sha’awarci ta diba,idan
bata ga dama ba ma ko kallo bai isheta ba.
“Wato ke kin zama ‘yar iska mara mutunci ko?” Ya fada yana nufota cikin huci bayan
zainab ta gama tsara masa qarya kan abinda ya faru,hannu tasa ta toshe bakinta saboda
yadda taji kanta ya mata dummm,kalmar ta yiwa qwaqwalwarta tsauri haka nan ta yiwa
kanta nauyi,jita mukhtar ke kira da ‘yar iska?,kalmar da babu wani mahaluqi da ya taba
jifarta da ita?,da sauri ta juya ta fita daga kitchen din cikin sassarfa saboda kukan dake
shirin qwace mata ba wai don mukhtar din dake nufota ba
Yau babu tantama abinda ke mata kaikawo a zuciya ya tabbata,mukhtar ya daina sonta
ya daina mararin ganinta,wannan wacce iriyar rayuwa ce?,haka mata keji duk sanda suka
samu juya baya daga wajen mazajensu ba tare da haqqinsu ba?,me yakai wannan zunubi
shiga tsakanin ma’aurata?,shiga tsakanin masoya?,masoyan da suka gina zuciyoyinsu da
qaunar juna,tsaftatacciyar qauna ta fisabilillahi. Wani mugun amai mai zafi taiji yana taso
mata,da qyar ta samu ta isa bandaki,ta dinga kakarin aman tamkar hanjin cikinta zai
fito,saidai banda wahala da yunquri babu abinda abinda ya fita din saboda babu komai
cikin cikin nata,don a yanzu ba kowanne lokaci take yarda da abincin zainab ba. Haka ta
gama wahalarta sai yawu kawai data fitar ta sakarwa kanta shower tana wanka tana kuka
har ta kammala sannan ta dawo cikin dakin iska na dibarta ta zabi doguwar riga ta sanya ta
koma saman gadonta tayi dai dai,jinta take wani iri daban,zazzabi taji na son rufeta, haka ta
yunqura ta sha paracetamol ta dawo ta kuma kwanciya,tunani ta shiga mai zurfi lokaci
lokaci tana dauke hawayen dake bin kuncinta.
Kamar daga sama ta dinga jiyo sallamar zainab qanwarta,daurewa tayi ta miqe ta dawo
bakin qofar dakinta don ta sanar mata tana ciki kada zainab tayi qaryar bata nan,sai data
tabbata zainab din taji sannan ta koma bakin gadonta ta zauna har ta shigo. Kallo daya ta
yiwa sumayyan tace
“Lafiya kike kuwa anty” qoqarin qaqalo murmushi tayi sannan ta dan ja tsaki
Qalau nake.yau ne kinga na tashi bana jin dadin jikina da bakina gaba daya”
“Yaya kamar fa kuka naga kinyi” sai ta basar ta hanyar fadin
“Barni kawai,nida mukhtar ne ya matsan sai da nasha magani,ni kuma kinsan bana son
qwayoyi” sai zainab din ta gamsu da maganarta ta zauna tana fadin
“Kamar kuwa mamanmu ta sani kinga tace sai na tsaya tayi dambu mutuminki na kawo
miki”,ba jira kuwa ta sanya hannu ta janyo flask din ta bude ta soma ci. Sosai taji dadinsa
cikin bakinta,sai data ci fiye da rabi sannan ta ajiye.
Bata sake fitowa daga dakin ba ranar,kusan yini sukayi ita da zainab tana mata ‘yan
gyare gyare cikin dakin, koda ta yunqura don sama mata abinci sai tace azumi ma takeyi,a
nan take gaya mata mama tace taje ta yiwa anty dije sallama zasu koma abuja ita da mai
gidanta,gwamnatin tarayya ta qara masa matsayi,duk sai jikinta yayi sanyi, bata son
rabuwa da anty dijen,idan ta tafi bata da gun wanda zata je su shawarta matsalarta
kenan,anty dije zata tafi ta barta a sanda alamu ke nuna matsalolinta qara qarfi suke. Sai
taji zuciyarta na neman raurawa amma sai ta aro dakiya da juriya ta yafa wa kanta gudun
kada zainab din ta fahimci wani abu.
Sai yamma lis zainab ta tafi ko banza ta debe mata kewa sosai kuwa,a ranar ta sanar
da mukhtar tana so taje wajen anty dijen washegari,saboda jibi zasu tafi,Allah ya dorata a
kansa ranar tambotsan nasa da sauqi,don a dakinsa ma ta kwana duk da zaman kurame
sukeyi.
****
****
Tun goma na safe ta kammala shirinta tsaf cikin shadd ja wadda aka yiwa adon stone
work baqi,ita kanta sai data tsaya ta kalli kanta,duk damuwar da take ciki amma sai taga
ramarta bata fito kamar baya ba,mamakin yadda ta qara haske da cika takeyi,haka ta yafa
baqin mayafi a kanta ta saqala baqar jaka ta fito.
A harabar gidan sukayi clashing da su kasancewar harabar ba mai girma bace,tilas
idan zata wuce din su ganta.yana zaune cikin mota zainab na tsaye riqe da murfim
mota,kudade ta yanka masa zai bata shine ta biyoshi amsa,tana karba ta juya tayi ciki
abinta,zuwa lokacin sumayyan ma har takai ga ficewa daga gidan.
A hankali yake bin bayanta,sosai ya rage gudun motar yana tafiya a hankali don baison
ya wuceta,tafiya take cikin nutsuwa,idan ka kalleta sai ka rantse da Allah bata taba aure
ba,sosai shaddar ta haska jar fatarta,ga komai nata yayi mata cif a jikinta duk da da
shigarta babu inda ta bayyana tsiraici,a haka har suka kai bakin titi.yana so yace ta shigo ya
kaita amma kamar an masa shamaki da ita haka yakeji,haka ya karya kan motarsa ya
wuceta ya hau kwalta sosai. Itakam sai a lokacin ne ma ta lura da shi,da idanu ta rakashi
sannan daga bisani ta dauke kanta tana hadiye wani abu mai d’aci.
Sosai ta lula tunani tsaye a bakin titin wanda hakan ya sanya ta kasa ankara da horn
din da yake ta zabga mata, murmushi tayi ta qaraso gaban motar bayan ya sauke glass din
“Wa nake gani kamar abdur rahman cikin mota?”ta fada tana duban motar samfurin vibe
fara qal da ita,sosai motar ta mata kyau
Murmushi yayi yana fadin
“Eh mana.ya son ranki?” Cikin dariya tace
“Fes wallahi”
“Ina zuwa haka da safe?”
“Zani gidan anty dije ne zamuyi sallama suna shirin bar mana kano su gudu abuja”
“Shigo ciki ma qarasa maganar ai hanya ta ce indai gidan da take har yanzu shine” ya fada
yana bude mata mazaunin gaba
“Rufan asiri nan ai na qanwata ne,nan ma ya isa” ta fada tana shiga baya
“Yayarki dai,kina nufin nidin ban girme miki da wajen shekara uku ko hudu ba?”
“Jimin mutum da shegen son girma,shekara hudu kakar wata shekara arba’in, kai uku ne
ma”
“Ko second daya ne dai na fiki ko?” Ya fada yana dariya,don sun saba da wannan caftar
indai shi da sumayyan ne,itama dariya ta saki sannan suka shiga gaisawa a mutunce,ta
tambayeshi mutanan gidan da kawunsa wanda qani ne ga mahaifin mukhtar.
“Kinsan tun ranar nan naso kawowa yaya mukhtar mota ta ya gani da kuma takardar
zanen filin da zamu fara gina islamic clinic to ban samu dama ba”
“Da kyau masha Allah abdhr rahman,Allah ya sanya alkhairi ya kade fitina, kace yanzu sai
bude asibiti”
“In sha Allah duk da aikin ginin ba qaramin abu bane, har kwantarwa nake sa ran zamu
dinga yi,zamuyi amfani da likitancin musulunci da kuma na’urorin bature”
“Kace mun kusa fara kiranka alhaji abdur rahman”
“Da ba alhajin bane?,mijinki zaki cewa haka,gashi har yau ya kasa zuwa ko ina,ya zama sai
a hankali wallahi” sai ta danyi shiru tana sauke boyayyar ajiyar zuciya don ha taba mata
inda yake mata qaiqayi
“Ina fata kina ci gaba da addh’o’inki ko?”
“Babu abinda na fasa abdur rahman,sauqin ne sai a hankali”
“Haka ne,kada ki gaji,kinsan ita cuta farad daya take shiga sauqi kuma samuwarsa sai a
hankali,Alah ya yaye ma dukkan musulmi baki daya”
“Amin abdur rahman,na gode” haka suka ci gaba da hira jifa jifa yana kwasarta da
tsokana,har qofar gidan anty dije ya sauketa sanna ya mata kyautar dubu uku,da fari taqi
karba sai da ya bata rai sannan ta amsa tayi godiya tare da bashi saaon gaisuwa gun
qanwarsa bahija da mamarsu.
Anty dije taji dadin ganinta sosai,nan suka wuni suna hira,ta tayata hada ragowar
kayayyakin da bata kammala hada kansu ba,tuni yaranta sunyi gaba don su qarasa
kammale gidan kafin isowar maman tasu. Suna hada kayan tana mata nasiha mai ratsa
jiki,idanun sumayyan ya hada qwalla har ta kai ga gangarowa,ta share qwallar tana fadin
“Yanzu shikenan anty?,gurin wa zan dinga zuwa” sosai ta bata tausayi.yarinyar da dududu
bata wuce shekara sha tara ba amma ta hadu da kaidin kishiyoyi kala kala,sai ta saki
abinda take ta koma gefanta ta zauna
“Kina da Allah sumayya,baya ga haka akwai waya hannunki, duk abinda ya shige miki duhu
ki kirani ki tambayeni, koda babu kudi a ciki kimin plashing zan kiraki da yardar Allah,ki
ninka haqurinki kawai,domin duk wata mace da kika ga ta zama wata gidan mijinta ki
tambayeta wanne irin haquri ta hadiya kafin ta kai ga cimma wannan matakin”
“To anty na gode”
“Babu godiya, ke diyata ce kamar su yasmin kike a gurina…amma sumayya yanayin jikinki
kamar ya sauya?,ko baki kula ba?” Ta fada tana kallonta
“Me kika gani anty?”
“Bakya jin wani sauyi a jikinki?”
“Babu abinda nake ji” ta fada tana kallon anty,shiru ta danyi sannan tace
“Shikenan…koyaya kika ji wani abu kada ki zauna,kije asibiti”duk da bata fahimci abinda
take nufi ba amma ta amsa mata da to.
Ana gab da sallar magariba ta koma gida,a gajiye ta koma,bandaki kawai ta fara shiga
tayi wanka ya daura alwala,sai da ta kammala sallahr magariban sannan ta fita,cikin
kitchen taji motsinta sai ta tura qofar ta shiga,tana tsaye tana hada food flask na abincin
mukhtar,qarasawa tayi kusa da ita ta mata sallama, kai kawai ta daga ta dubeta ta maida
kai taci gaba da abinda take ba tare data amsa ba,ita din ma bata damu data amsa ba kai
tsaye ta jeho mata tambayar da ta fito da ita
“ina abincina zainab,banga flask dina ba”
Dagowa tayi sosai ta sake kallonta,sai ta saka wata dariya data sanya dole sumayyan ta
tsaya tana kallonta cike da alamar tambaya, sai da ta tsagaita don kanta sannan tace
“Ince ko baki samu labarin baki da abinci a gidan nan ba” jin maganar tayi banbarakwai, ba
kuma ta fahimci inda ta sa gaba ba,saboda haka taci gaba da kallonta,dauke kai tayi daga
bisani sai ta nufi dan qaramin store din dake kitchen din da niyyar fiddo da ko indomie ce
ta tafasa,sai ta tarad da store din a garqame da kwado,waiwayowa tayi ta sake duban
zainab din
“Naga alamun baki fahimta ba,amma bari nayi miki bayani dalla dalla,mukhtar ya soke
baki abincinsa,walau ni na dafa ko ke ika dafa kin fahimta ai yanzu ko?” Sosai maganar ta
daketa,sai ta kasa furta komai baya ga wani abu da ya tokare maqoshinta, bata fahimci me
hakan ke nufi,tilas ta jira dawowarsa tunda shi ya ajiyeta ba zainab ba,wannan maganar ba
tata bace. Wuce zainab din tayi ta nufi sashenta ta dauki tukunya ta tari ruwa ta dora kan
gas tare da jefa lipton,tilas ta sanya wani abu a cikinta ba don haka ba abinda take ji cikin
zuciyarta bata jin wani abu mai suna abinci zai iya wucewa ta maqogoronta.
Hannayenta ta harde saman qirjinta tana jiran ruwan ya tafasa,tamkar zata fadi haka
take ji,ga yunwa ga bacin rai,tana kammalawa ta juye a cup ta nufi daki,bata ko bi ta kan
qananun habaicin da zainab keta jefawa cikin waqe,don yanzu bata ita take ba ta kanta
take. Tea ta hada da kayan shayinta wanda dama a dakin suke.
Ko rabi bata sha ba ta soma yunqurin dawo da shi,sai data amayar da shi tas sannan ta
dawo ta zube qasan carfet din dakin cikinta naci gaba da juyawa,rasa abinda ke mata dadi tayi,fashewa tayi da kuka tana kiran sunan Allah.

Advertisements

_____

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

QADDARAR SUMAYYA CHAPTER 30

Advertisements _____ QADDARAR SUMAYYA CHAPTER 30 Ba yadda ummee ta iya wani lokaci haka take …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *