HASKE CHAPTER 27

Advertisements

_____

HASKE

CHAPTER 27Ba Haske tabar gidan ba sai wajen sha daya, tayi hamma ta gaji amma ko ruwa bata kai
mata ba. Dama batada pure water na borehole take sha. Ko sanda Ajwad yayi kuka daya
farka ta sauko shi ta rungume tana bashi nono. Har lokacin Laila bata ce komai ba banda
bakin ciki dake dawainiya da ita. Wai ace ta riga aure amma har yanzu shiru. Balle yaron
nada masifar kyau ga girma abinsa.
“Bakiga na haihu bane?” Haske tace. A dikilce Laila ta amsa da “Uhmm sannu.. Nazo
magana sai na mance…Kinsan halin rayuwa” abin baima Haske dadi ba amma kuma Laila
is going through matsala masu yawa. Bataso tayi san kai komai ya zamana akanta, bataso
1
abinda Laila tace ya zamto gaskiya komai idan ba Haske bane ba’a yi.
“Sunan sa Bello Abban Bilal amma muna ce masa Ajwad”
“Allah sarki” saita tashi ta shiga da kayan shayin ciki. Sanda zata tafi har mota Laila ta
rakata. Sai raba ido takeyi ko zata bata kudi amma batayi ba, “Shegiya” ta ayyana a ranta
saita koma ciki da Sauri sabida Officer ya kyallara ido ya ganta. Data san bazata bata ko sisi
ba da ko kofar daki bazata ba.
Su Bukola an isa asibiti inda aka shiga da ita emergency saboda ta galabaita. Saif sai
yawo yakeyi, baiso Bukola ta mutu sabida kashin sa ya bushe. Dama yanzu da ita yake so
yayi kame kame yayi mata wayo ya rinka karbe mata kudi. Idan ta mutu kuwa zaiyi biyu
babu.
Bayan an fito da ita inda aka ce an cire cikin, kuma barin yan biyu tayi. Murna ya nuna
karara har saida kallo ya koma kanshi. Anan daya lura ya soma inda inda. Basarwa yayi ya
hade fuska. Anan aka ce dole a kwantar da ita na ranar zuwa gobe, ya kira wanda zasu
zauna da ita. Hajia Mujibat ya kira. Anan tazo cikin minti 30 hankali a tashe. Kuka takeyi
wiwi dataga karin ruwan. Ita tafi san Bukola cikin yaranta.
Anan tace ma Saif karya damu zata lura da ita sannan zata tafi da ita gidanta har ta warke.
Baiso ba ya fara zuciya tunda idan bata nan bazai ci mai kyau ba. Kuma yaso yayi jinya koba
komai idan yan dubiya suka zo zasu bashi kudin wanda zai danne. Sannan kuma su kayan
abinci ya cinye, mai ciwo inashi ina wani cin abinci? Dama dama shayi amma wani kaza ko
snacks duk nashi ne.
Kuma yana kyautata zaton yan customers zasu zo dayawa irin masu kumban susa sosai
suyi hadarin kudi. Harara ya rinka watsa ma Maman Bukola a kaikaice saboda haushi. Ya
tabbata da gayya zata kwace mashi business saboda shegen san kudinta
Bilal yana zaune a farfajiyar gidan yana jiran Haske, koda zai shiga Mallam Adamu yace
bata nan. Mommy ita ma tana falo tana jiranta, driver ya ajiye ta ya tafi. Mamaki takeyi akan
fitarta da safe tana jego, yanzu kwanan ta ashirin da haihuwa bai isa ta fara fita ba.
A tsakar gidan suka hadu da Bilal, murmushi yayi mata wanda ya dade baiyi mata ba. Ita
jin dadi lallai ya soma santa kila ma ya
da
ma murmushin ta mayar masa, anan ta s
ta dakinta. Mike wa yayi ya karasa wajen ta tare da mika hannu ya karba Ajwad. Anan wajen
ya fara wasa dashi. Shiru sukayi babu abinda suka ce, ta lura baiso ya shiga ciki saboda
Haisam. Abin dariya ya bata saboda batasan Bilal da tsoro ba.
“Muje daga ciki”
Shiru yayi kamar bai jita ba yanda saida ta sake maimaitawa, anan saiya bita sannu a
hankali zuwa falon. Ganin Mommy da tayi yasa gabanta ya fadi. Tasan tayi laifi kuma bata
jin magana. Gabanta ya cigaba da duka uku ukujikinta yayi sanyi.
“Ina wuni Mommy?” tace ba tare da ta kalle idanta ba. Mommy ta lura da rashin
gaskiyarta saidai bata kawo Laila ba. Duk mai hankali bazai kara ta’ammali da Laila ba. Ita
karin kanta sun shiga filin yaki da Laila kuma ranar lahira sai an masu shari’a sabodata
cuce Shamsiyya.
“Lafiya lau Shamsiyya, ya kwanan Ajwad?”
“Lafiya lau, sau biyu ya barka cikin dare” tace tana barkwanci
“kokuma sau biyu kika iya farkawa kika duba shi”
“Ina wuni Mommy?” Bilal yace
“Lafiya lau, zauna mana ka tsaya”
Bayan Bilal ya zauna sai ta kalle Haske, “Ina kika je ?”
“Dama.”
“Dama mene shamsiyya? Inda kika je baida suna ?”
“Daga gidansu Laila nake!” ta fada a sanyaye
Ba Mommy ba harta Bilal saida ya dalalo ido dataji ta ambaci Laila, saidai baice komai ba.
“lyayen ta sun rasu ne?” Mommy tace

“Aa” ta amsa a daburce, sai yanzu taga wautar ta. Data bari bayan kwana biyu kafin ta
yafe mata tukun.
“Mijin Laila kenan ya rasu?”
Aa”
“Kishiyar Laila ko yaransu?”
“A’a Mommy”
“Ita kanta Laila ta rasu kenan?”
“Innalillahi Mommy babu wanda ya rasu”
“Alhamdulillahi, meye gaminki da ita?” tace tareda kafa mata ido. Zufa Haske ta soma
sosai. Gwiwa dinta yayi sanyi, gefen kujera ta samu ta zauna. Anan ta bude baki zatayi
magana, hannu Mommy ta daga mata bataso taji.
“Bani so naji meya kaiki! Abu daya nakeso ki gane. Kinsan ke ba yarinya bace koda
shekarunki basuda yawa amma yanzu kinada yaro. Ya kamata ki rinka amfani da hankali
idan zakiyi wani abu. Laila itace sanadiyar da yaron nan zai tashi ba tareda iyayen sa ba,
baiji ba bai gani ba anyi depriving dinsa daga wannan damar. Kema kin tashi babu uwa,
kinsan rashin samun iyaye duka a gida yanda yake bata maka kai psychologically, amma
still saboda rashin tunani naki shamsiyya kika koma kina aminta da ita” hawaye take
gogewa da haban gyalenta.
Shiru Haske tayi tana hawaye, meyasa bazasu fahimci inda ta dosa ba. Da sun bari sunji ta
bakinta su gane komai. Tanada tabbacin cewa mommy tafita saukin kai, kuma zata
taimakawa Laila a yanayin datake jiya. Watau kenan jiya data kai Laila ta kwana gidan
Mommy korarta zatayi? Ran Bilal tafasa yakeyi kamar mene, yanzu harta koma wajen Laila?
Wai meke damun Shamsiyya ne kamar anyi mata asiri? Sai wani zuciyar yace mashi babu
asiri iskanci ne. Ya za’a yi ta yafe ma Laila, ya kamata tafi shi fushi da ita amma harsun
dinke. Muryan Mommy sukaji tana magana.
“Wani uzuri gareki da zaki ce kun koma aminta, are you stupid Shamsiyya? Ko kinada
amnesia ne? Har kin manta yadda ta dauki alwashin saita rabaki da gidan aurenki, kuma ta
samu nasara shine bazaki hankaltu da ita ba. Those who betray you once will do it again,
bature yace haka. Haba Shamsiyya wanna ai shashanci ne, maraici ba rashin hankali bane.
Kina ganin Hafsat da tanada rai zata yarda da wata kawarki Laila. Ran farko zata gane ba
kawar kirki bace ta rabaku… Eh na gane ta taimaka maki amma yanzu kowa ya kama
gabansa”
“Mommy dan Allah kiyi hakuri, wallahi Saif ne ya saketa batada wajen kwana, sai tazo nan
Fijr tayi mata cin mutunci itama ta koreta. Naje duba ko tana lafiya ne… Bance zanyi
kawance da ita ba.. ‘m just trying to help” saita fashe da kuka wiwi. Meyasa baza’a mata
uzuri ba bayan abin arziki tayi. Nisa Mommy tayi, yau da Yasmin ne babu haufi saita shiga
jikinta da Bulala, amma wannan amana ce babu yadda zatayi da ita. Bilal ya soma magana.
“Kinsan duk problem din da muka samu a cikin auren mu ya jibanci Laila? Har marina
kikayi akanta amma shine kika sake sauraren ta. Idan bakiyi kawance da ita ba mutuwa
zakiyi ko menene? An saketa and so? Kema ba’a sake kiba? Maimakon kiji dadin Allah ya
fara bin maki hakki shine kika barta cikin gidan nan, sai tayi sanadin da Daddy ya koreki
tukun zaki huta, because am sure kinada niyar barin ta cikin gidan nan”
“Ni na taba ganin irin wannan bala’i? Wai ace duk abinda take maki bakya gani? Sai kinyi
wani auren ta kara fito daki koh, zaman nan gidan kike so? Baya babanki zai sake aure
bakisan irin zaman da zakiyi da matar ba. Maimakon ki rufa wa kanki asiri a’a kece dadi
kawance, jibe yadda ta hada kai da Hadiza za’a maki kishiya.. Duk fah kin mance. An
saketa hankalin ki ya tashi kamar ni aka saka ko Hafsat” Mommy tace cikin takaici. Idan
ba’a idon Haske akayi ba zata rantse ba Mommy take magana ba. Dukta canza farad daya
sai ruwan bala’i takeyi.
Suna zaune sai Bilal yace zai tafi, bakin ciki yake ji mara mitsaltuwa. Zakaga fushi a fuskan
sa karara ba kamar yadda yazo ba. Mikewa tayi domin ta raka shi sannan kuma ta bashi
hakuri, ba abinda yake tunani bane. Kawai taimakon Laila tayi amma ba wani serious
kawance zasuyi ba. Tafiya takeyi da kyar saboda yunwa, cikin azama ta fita da kyar ta
tsakura biredi saita kurba shayi kadan. Yasa ta siya kayan shayi domin tasha itama gidan
Laila amma kuma baayi mata tayi ba.
5
Sun isa wajen motarsa ya shiga ya zauna, bai tada ba sannan bai ce mata komai ba. A
yanzu yanada shakku ko yanaso ya aureta. Yana san mutane masu amfani da hankali. Ina
amfanin ya aureta kullum suyita fada akan Laila. Zuciyar sa yana mashi wasi wasi sosai. Sai
kuma ya tuna yanaso ya nuna ma Haisam ba’a raba mace dashi.
Karar Gate suka ji, motar Haisam ya danno kai. Anan gaban Haske ya sake faduwa. Tasan
yanzu za’a sake fada. Magana ta soma cikin tsoro.
“Please ka tafi kafin ya karaso, i don’t want any trouble”
“Ba inda zani sai kace ba namiji ba'”
Suna tsaye har Haisam yayi parking, kamar yadda suke zato haka yaje wajen su. Fuska a
daure ya soma tsuma.
“Me kike yi haka? Bana rabaku ba? So kike ya sake yaudaran ki?” yace yana nuna yatsa.
Murmushi Bilal yayi, tabbas Haisam baisan asalin halin Haske ba. Duk wanda ya sani bazai
so yayi ta’ammali da ita ba.
“Maman yarona ne, munada alaka har duniya ta nade” Bilal ya amsa.
“Badai kai nake magana ba malam”
Saiya kalle Shamsiyya wanda ba tace komai ba, rage murya yayi ya soma magana, “Shams
meyasa bakya jin magana? Nace ki fita harkan sa rudan ki zaiyi. Why can’t you see?”
Dariya Bilal ya bushe dashi, tabbas Haske idan anaso taga abu bata gani. Kamar tanada
problem a brain dinta. Amma kuma ba matsalar shi bane. Ya lura Haisam yana mata so fiye
da yadda shi yakeyi. Soyayyar ko Ajwad zai samu kulawa. Bazai iya zama da Shamsiyya ba
muddin tana mu’amala da Laila. Kuma yasan dole tayi, gudun kada a cigaba gwara ba’a
soma ba. Ta sake zaban Laila akan shi tunda har taje gidanta. Shi yanzu peace of mind yake
so. Gwara ya hakura da ita, yana bala’in santa amma rabuwar su zai fi kawo mashin
natsuwa. Ko kadan Haisam baici gasar ba, kawai yafi san nashi kwanciyar han kali ne.
Badai shamsiyya ba, gashi gata. Duk rawar kan nan zai bari idan ta cusa mashi wani bakin
ciki. Aurenta punishment ne ba victory ba. Kallon su yayi su biyun yana dariya, “Calm down
Gamji, I don’t want your woman either. Gata gaka Allah ya sanya alheri”
“Saboda Laila zaka mance da Soyayyar mu?” tace tare da hawaye.
“Banyi komai ba, ke kika yi da hannun ki. Banda energy din ja da ita. Gwara na baku
waje”
“Wallahi taimako ne, koda ta tambaye ni kai bance mata komai ba” ta fada a rude.
Murmushi yayi, Haske is naive amma ta kasa gani.
“Karki damu, ga Haisam zai lura dake fiye dani”
“Amma ina sanka ai.. Kaina baban yarona… Karka sak√© guduna'”
“ke kika guje ni da farko, remember? Yanzu kuma kin sake. Bansan meke damun kiba…
Maybe kinada reasons din haka but bari na gaya maki Laila ba kawar arziki bace”
“She said she is sorry, har kuka tayi”
“Kukan banza, ni banyi maki kuka ba? Sau nawa ina rokon ki akan ki yarda dani, pick me.
Amma me kika yi? Marina kika yi kika tafi”
“Waye Laila?” Haisam ya tambaya saboda bai ganewa. Kallonsa Bilal yayi, takaici kawai
ke dawainiya dashi saboda kana ganin yadda Haske ke defending Laila.
“Besty din Girlfriend dinka ne, with time ba baki nake maku ba amma zata shayar dakai
bakin cikin ta… Shamsiyya nada taurin kuma ni na yafe da soyayyar ta, gaka ga ita”
Kallon Haske Haisam yayi saboda yana bukatar karin bayani, a hankali ta soma magana,
“Laila tayi ma Bilal sharri shine nace ya sake ni” saita fashe da kuka.
“Innalillahi wa inna ilayhi rajiun” Haisam yace saiya dafa kansa. Jingina da motarsa yayi
duk jikinsa yayi sanyi. Baiji dadin yadda baisan kan zancen tun farko ba. A hankali ya soma
magana.
“Shine zaka hakura da ita? I thought she’s sorry”
Runtse ido Bilal yayi, zuciyarsa bai bar mashi daci ba. Sunar Laila kawai yana saka shi
cikin tashin hankali balle ace wata rana tazo gidan sa. Baisan irin abinda zaiyi ba. Sau da
dama yana so yaje gidan Laila yayi mata wani mugun abu, ya shayar da ita bakin cikin data
shayar dashi amma kuma saiya fasa.
“Bazan iya zama da Shamsiyya ba, har Laila ta samu damar dawowar rayuwa ta, bayan
duk abinda tayi… Bazai yiwu ba… Bani babu ita koda zai zame min sanadin mutuwa na..
Bawai na tsane Shamsiyya bane amma bazai yiwu bayan anci min da iyayena mutunci
akan Laila sannan suna aminta”
“Daga yau bazan kara ba, wallahi” tace tana kuka.
“Da bansan halinki ba, dana yarda.. Amma yanzu Allah ya amfana… Bazaki sake gani
naba for now… zansa driver yazo ya rinka kawo min Ajwad har nayi calming down… Allah
ya baku zaman lafiya keda Haisam, ya kawar da tsautsayi da mugun kaddara”
Rufe kofar motarsa yayi ya soma tafiya, bazai bari a sake shayar dashi wani bakin ciki ba
Shiba Shamsiyya bane balle ya zama naive yasan zata sake kuma auren su bazai lasting ba.
Maybe Haisam yanada hakurin da shi bashida shi.
“Bilal don’t go! Please!! Bilal! Bilal!” tayita fadi tana kuka, harda dukawa kasa. Wani zafi
da daci takeji amma ko gezau. Tuni Mallam Adamu ya bude mashi Gate ya fice abinsa.
Haisam baisan ko dadi zaiji ba kokuma tsoro. Waye Laila da zamanta a rayuwar Haske ya
tsorata Bilal da gwara ya kyale ta? Koma waye ita bazai yi irin na Bilal ba, ba zai bari ta
kusanci Haske ba balle ta samu ta raba su tunda ya lura ance batada tsoron Allah.
Koda suka komai ciki daki ta wuce shi kuma yaje wajen Mommy, yana so yayi mata
albishir da cewa su soma shiri saboda zasuyi aure. Ita Haske daki taje saita hada ruwan
shayi daga flask dinda ke wajen, tana sha saita soma jin dama dama. Komai ya soma
zuwan mata da kyau.
Anya ba gaskiya bane Laila mugun kaddara ce a rayuwar ta? Sai kuma wani zuciya ya raya
mata wannan shedan zur ne da camfi, duk abinda ya faru da ita babu saka hannun Laila,
tun kafin a haife ta an riga an kaddara. Kamar yadda ta gaya masu ba kawance mai zurfi
zasuyi ba, sama sama ne abin. Zata rinka duba Laila na kwana 2 harta samu aiki, sannan
saita fita harkan ta kamar yadda kowa yace. Itama ta gaji da korafi da kiranta jaka da akeyi.
Haisam da fara’a ya soma magana, amma yadda Mommy tayi ya bashi mamaki. Dakewa
tayi sosai kamar bataji dadin maganar ba.
“Mommy lafiya?”
“Kai yanzu duk duniya Shamsiyya kake so? Duk hankalin ka? Wallahi ina gudun maka
bakin cikin da zata shayar da kai akan wancan mara tsoron Allahn!”
“Laila wai?”
“ita fah, Haisam ka dade kana shan wuya. Bana so wani abu ya sake faruwa dakai. Daga
kai har shamsiyya yarana ne. Ina son what is best for you. Zaman Laila a rayuwar ta ba
karamin hatsari bane, ko an rabasu bata jin magana. Na rasa wannan bala’in amma idan
kace kanaso har ga Allah zan maku fatan alheri sannan zan cigaba da taya shamsiyya da
addu’a kila wata rana za’a dace”
Shiru Haisam yayi yana tunani, meyasa Shamsiyya bazata yi amfani da hankalinta ba
tunda ya nuna cewa Laila mugun abu take mata. Duk yadda Mommy ke santa amma jibe
yadda ta Soma fita mata kai, Bilal shima yace ya hakura. Kowa gudun ta yakeyi. Yanzu
saura shi, wanda yasan yana cikin tsaka mai wuya! Yanzu meye abin yi? Wannan kenan!
Bayan wata uku..
Kamar yadda Alhaji Shehu yayi alkawari aikam ya cika, ba kashe gari yaje ba saida ya sake
bashi karin kwana bakwai, da baiji komai ba yayi odan yan sanda da mutane wanda zasu
kwashe kayan wajen. Koda yaje bai ga wani kayan kirki ba. Da Saif ya kira manajan shagon
akan ya lura da komai saboda bazai samu damar zuwa ba matarsa babu lafiya. Aikam nan
kowa ya ja abinda zai iya dauka suka kai fanteka aka siyar. Nan kowa ya fanshe kudinsa yayi
gaba, kusan duka karafan da langa langa aka siyar. Manajan yafi samun ganima tunda
kusan dubu dari da hamsin ya tashi dashi kuma a hakan yan fanteka sun cuce shi.
Saif kullum yana kan hanyar zuwa gidansu Bukola, tunda taje batada lafiya bata dawo ba,
kuma ya lura kamar bariki suke so suyi masa bazata dawo ba. Yau ko gobe ake ce mashi.
Sanda aka tambaye shi inda motarsa yake, bai masu karya ba ya fadi komai. Sun jajanta
mashi sosai har Hajia Mujibat ta ranta mashi 50k domin ya rage zafi ya fara business.
Dayake baida kan gado ya saba cin dadi haka yake zuwa ya siya nama a Taraba yaci tareda
farm fresh babban roba ya lashe baki. Amma zara bai barin dami, kwanci tashi kudin suka
soma karewa, koda yake ya siyan ma Sameera buhun shinkafa, ita kuma Laila ya diban
mata local biyar ta rage zafi.
Itama yanzu ta samu shiga, wani private nan gaba dasu kadan suka dauketa aiki, wata
Anty din yan Nursery zata maternity leave, Sai suka dauke Laila na wata uku, anan kuma
idan an samu gibi saita zauna kokuma shikenan. Ana biyanta dubu takwas tunda batada
experience din teaching sannan za’a kara mata according to her performance. Dayake
yaran shekara 4 take koyarwa. Kusan kowane yaro ana kaisa da lunchbox inda ake saka
mashi abinci.
Laila kam lokacin break kafin su soma ci zata saka su suyi layi biyu. Masu dankalin
turawa, indomie da kwai sai su snacks gefe daya. Sannan kuma dayan layin masu shinkafa,
ko taliya nasu daban. Haka zasu zo daya bayan daya tana tsakura tana ci tana rufe ido. Idan
takai wajen masu shinkafa ta rinka korafi tana cewa ‘wai ku ba kwa cin dankali ne? Kuce a
rinka soya maku dankali da plantain ko na rinka zane ku’
Yara kanana hankalin su duk ya tashi, idan suka ga shinkafa suyita kuka suna basa so
suna botsarewa saboda tsoron masifan Laila. Sunsan zasu sha masifa har karshen ranar
Fannin karatu kuwa banda wake wake na’l went to the market, I went to the shop, i saw a
little fine girl in my father’s shop’ suyita gabza rawa. Idan Headmistress tazo sai tayi karya
tace yanzu suka gama classwork, kokuma ta dauko English da sauri ta fara masu tana
tafiya ta rufe. Idan basa waka toh suna barci kowa tace ya kwanta akan table kanta yana
ciwo.
lyaye suka soma korafin yadda yaransu suka canza, saidai gaskiya tana kokari wajen
turanci. Bata yarda suyi Hausa yanzu bakin su ya nuna da harshen turanci. Anan tayita kuka
tana cewa sharri ake mata tana aikinta. Sannan ga fankama bata magana da sauran
malamai. Saboda taga tafisu yarinta. Tana tafe tana karkade karkade.
Saida tayi kwana uku da zuwa gidanta bayan sakinta kafin suka hadu da Saif, sun sasanta
sosai saboda a lokacin harta samu aiki. Shima yaji dadi saboda zai samu nashi kason. Dubu
biyar tace za’a rinka biyanta tayi mashi karya. Kuma albashin farko ta bashi dari biyar.
Sannan tayi cefane harda kayan ciki. Yanka hudu ta saka mashi inda yayita jindadi yana
gode mata. Yanzu ya soma respecting dinta fiye da tunanin ta tunda bata dogara dashi.
**
Bata kara zuwa gidan Laila ba. Duk da abin yana mata ciwo. Fijr ta kama Haske tana waya
da Laila ta wayan Saif. Anan taje take gayama Daddy Zailani. Lokacin yana zaune a falo
yana kalaci da Amarya Anty Fadila. Shima abin yayi mashi ciwo, kamar yadda duk wani mai
hankali yana ji ranshi zai baci.
Haske taji sanda Fijr tagaya, tana jiran Daddy yayi mata magana kila shi zai fahimci ta
idan tayi bayani. Saidai kam baiyi ba. Kallonta yakeyi da abin tunda tanada hankalinta.
Abin yafi bakanta mata rai watau silent treatment, duk ta muzanta ta daina kuzari. Magana
sama sama yake mata ya rage mata fara’a. Saboda haka saita dauki alwashin bazata sake
zuwa gidan Laila ba, tadai aika mata provision da kayan cefane sau biyu cikin yan
watannin. Sannan ta hada mata 2k da atamfa wanda aka kawo mata sanda ta haihu, tasan
Laila zata fi bukata kuma zata gode mata.
Batun aurenta da Haisam kuma saura kwana 3, ya roke ta alfarma akan ta fita harkan
Laila tunda shi yafi alheri. Dariya kawai takeyi cikin ranta idan yana bayanin yadda baiso
yayi alaka da Laila. Suda sukayi aiki waje daya kuma sau nawa suna hira da ita, yasan dai
Laila is harmless bazatayi kisa ba she is sure of that, kawai dai bazaka rabata da kananan
gulmace gulmace ba, amma idan kasan halin mutum sai kaci maganin zama dashi.
Tadai yi mashi alkawari bazata sake ta’ammali da ita ba tunda baya so, ita ma tayi ma
kanta alkawari bazata sake barin Laila ta raba mata aure ba. Tana kyautata zaton cewa idan
tayi auren nan ta kuskura ta fito bazata sake auruwa ba, yasa zata lallaba ta zauna koda
babu dadi. Kafin a soma kiranta annoba.
A hankali ta soma cire Bilal daga ranta tunda da gaske ya hakura da ita. Abinda yace haka
direba ke daukar Ajwad su kai mashi, wata rana idan Fijr zata aiki sai ya aika mota su tafi
tare, a shagon zai zauna yayi wasa da babyn sannan kuma Hafsat tana gefen sa. Bayan
kusan awa da haka zuwa biyu sai ya aika a mayar.
Haisam Shima yana bala’in kokarin ganin cewa duka hankalin Haske yana kanshi, kuma
cikin ikon Allah yana samun nasara. Da kanta zata kira shi a waya suyi hira sosai. Shiru
shirun yanayin su ga mutane ne amma idan suka hadu kamar suda suke, basa isar juna.
Posting dinsu ya fito daga shi har Chiquita, ita an kaita Katsina shi kuma Kano. Babu wanda
yayi zaman camp sunyi redeployment zuwa Kaduna, ita taso taje Abuja sabida kwata
kwata bata jin dadin zama gida daya da Haisam. A gaban ta zai sha wayan sa da Haske yana
kashe murya da kalamai ko gezau.
Mommy ta sake mashi magana akan Haske, sai ya sheda mata eh yaji ya gani yanaso tayi
ma Mum dinsa magana a tura a haka. Koda Yasmin taji hankalinta ya tashi, taje tana mata
kuka, hakuri ta bata saboda wannan karan zabin Haisam zatabi koda bata so. Fatan
daidaituwa a tsakanin su takeyi.
Ankai kayan gaisuwa da sadaki da lefe, Haske batasan wani hayaniya tunda ba budurwa
bace. Shima Haisam ya yarda da zancen, saboda haka yinin biki kawai za ayi, sai kuma
maza walima bayan daurin aure.
Lefe akwati shida akayi mata na kayan alfarma, sannan ya kama masu gida three
bedroom, kayanta na wajen Bilal aka kwaso. An canza na canzawa wanda kuma batayi
amfani dashi ba aka bar mata. Kamar kujeru kuwa Sanat akaje suka siya sai aka siyan mata
sabo wajen su. Komai nata aziman kashar kashar jira takeyi ayi aure domin ta tare.
Kamar yadda Haisam ya roketa akan tayi hakuri karta gayama Laila, abin yanata
tsungulinta amma ta danne. Tadai ce bayan ta gama amarci idan tayi watanni zata sheda
mata. Fijr tayi rawar gani sosai, babu yadda bataso ayi dinner ba amma aka ki. Wancan
auren bataji dadinsa ba saboda tana hanyar zuwa Maiduguri.
DJ mai piano ‘Ayaga’ ta kira masu, tun daga ranar saka lalle zaiso ya soma har ranar biki
Ya samu lakabinsa Ayaga sabida idan kika fara rawa sai kin kusa yaga zaninki. Ta riga ta
koya tambolo da shaku shaku wanda zata gwangwaje da kyau. Sannan ita zata ma Haske
make-up, mommy, mum din Haisam da Anty Fadila. Sauran tace suje wani wajen batada
lokaci. Yadda take hada hada kai zaka ce wannan ne farkon auren Haske.
Tare da ita akayi jere, itace take ma zuwa kasuwa. Sannan kuma a wajen ta Haisam ya
samu idea na abinda Haske keso wajen lefe. In dai kana neman yar uwa mai rufa maka asiri
toh Fijr ne abokiyar tarayya dinka.
Ranar auren ranar Asabar ya fado, wajen sha biyu da rabi aka daura auren Shamsiyya
Zailani Abubakar da Haisam Adam Mijinyawa bisa sadaki dubu hamsin. Duk abokan arziki
sun halarta harta mahaifin Bilal. Gidan baka ganin komai sai yadda kowa ke murna da
annashuwa. Bikin dangi akeyi tuwansu miyansu.
Ammi bakin ciki takeyi sosai, wai ace Shamsiyya ko fallin zawarci batayi ba harta samu
miji ita data fita kyau saidai tsufa tana zaune babu labari. Gashi Dr Mahmoud bayan dubata
dayake yi yaki bata fuska tace tana sanshi. Kwarjini yake mata sosai ya cika mata ido.
Ayyanawa a ranta tayi gwara taje wajen bokanta na cikin Kaduna yayi mata aiki. Dan
gaskiya tana sanshi balle yanada kumban susa. Dab da bikin sai neman Haisam takeyi tana
gaya mashi lallai karya aure Haske saboda tayi gantali har suka koreta, sannan tayi yawon
karuwanci. Ba wai wai bane da gaske abin ya faru. Bonanza tayi ma yan KASU da kanta
kowa ya kwasa rabonshi. Shi kam dakewa yayi yace ta koma KASU tace duk wanda bai
karba nasa rabon ba yayi maza yazo ya karba saboda idan tayi aure an rufe.
Sakin baki tayi a wajen, sai kuma ta watsa mashi harara watau ita zaiyi ma bariki. Abin
baima dameshi ba. Haushi taji sosai yadda take ganinsa da hankali ashe fanko ne. Imran
kanin Haske shida Abubakar yaron Mommy suka tsaya tsayin daka domin walima ya tafi
yadda ya dace. Anko sukayi farin geztner daga sama har kasa su ukun da Haisam. Abin yayi
armashi sosai gwanin ban sha’awa.
Ranar daurin auren ne Ammi taje wajen boka, tun safe taje ko sanya alheri batayi ma
Mommy ba. Koba dan Haske ba saboda ita ta rike Haisam. Abin baima Mommy ciwo ba
tasan halin Hadiza. Gobe idan yan zaria zasu tafi zatace ta tarkata ta bi su. Sunyi zaman ya
isa haka Allah ya amfana.
Da malamin tsubbun ya duba kasa ya soma surkulle, sai yace zata kawo zakara wanda
suka shekara guda uku. Sai agwagi guda shida maza uku mata uku, sai bakar zabuwa. Dasu
za ayi mata aikin zata samu kan Dr Mahmoud. Murna ta somayi sosai saboda sanda aka
kawo lefen Haske ta sace dan kunnen zinare. Ba’a lura ba tunda bataji ana cigiya ba. Yanzu
shi ta siyar ayi aiki. Tana kyautata zaton a tadin farko Dr Mahmoud zai mayar mata wanda
ya ninka.
Harta mike zata tafi sai ya dakatar da ita, anan yake tambayanta meye tafi so a rayuwar ta,
ko tanada abinda yake damunta. Tace gaskiya tana so taga karshen Haske. Yanzu batada
wani kwanciyar hankali tunda taga Haske sai gaba takeyi. Anan yace to taje ta magance
matsalar ta na Haske idan tayi haka Mahmoud nata ne.
“Magance matsalar?” tambayar kanta tayi amma ta rasa amsar. Sai daga baya ta fara
tunanin idan Haske na raye bazata taba samun duniya ba balle kwanciyar hankali, Laila ta
fado mata a rai saita nufa hanyar gidan.
Da Laila taji auren Haske kamar tayi hauka, gashi Ammi tace mata zuwanshi turai kamar
yana shan jini. Kudi yake barazana dasu sosai dankam zai kara da Bilal. Anan Laila ta soma
ma Ammi rashin kunya akan meyasa bata fada mata ba. Zage-zage suka soma kamar zasu
kara dambe, dan saida ta kira Ammi tsohuwar Banza. Nan dai Ammi ta bata hakura domin
ta samo masu mafita. Idan Haske tana raye dan tsubbu yace bazata aure Dr Mahmoud ba.
Idea kala kala suka rinka kawo wa har suka samu mai kyau wanda bazai wargaje ba. Dari
biyar Ammi tabama Laila saita tafi zata dawo ranar da zasuyi aikin.
Ranar daurin aure wani cousin dinsu Fijr yace Ayaga bazai yaga ba saboda su yan sunna
ne. Aikam Fijr ta soma ruwan bala’i babu mai hanata yagawa. Ita ta riga ta dauki alwashin
rawa kuma zatayi. Babba ne yanada yara uku, amma babu abinda yasha mata kai yana fadi
tana fadi har saida Alhaji Zailani ya bashi hakuri yabar Fijr tayi abinta.
Dama tayi gayya sosai na customers dinta, anan ta soma rawa abinta anata manna mata
kudi. Balle tayi kyau sosai abinta. Ta saka bra mai kyau kirjinta ya daina yanayi da kamar
ana rungumar agwagwa. Dinkin ta ya zauna mata dagwas. Kowa ta burgeshi kuna hada ido
tana watso maka murmushi, gashi ta saka hakori duk da bataje ba.
Da yamma aka kai Haske gidanta na Dendo Road, Mommy ta kaita tare da Anty Fadila. An
mata nasiha sosai akan aure, Mommy ita kuma banda ta kula miji yafi kawa bata cewa
komai. Aljanna take nema kuma a kafan mijinta zata samu ba’a kafar kawarta ba. Dan Allah
ta kula ta daina daukar jita jita tana bin maganar mutane fiye da na mijinta. Karta bari a
maimaita abinda ya faru a gidan Bilal. Ta rike maraicin ta tasan me takeyi, sannan ta tuna
tanada yaro wanda sakarcin ta yasa ubansa ya guje ta.
Magana akayi mata mai shiga jiki sosai, ta dauka kuma tayi alkawari zata fita harkan Laila.
Ko provision bazata sake aika mata ba. Koda sun hadu a kasuwa sama sama zasuyi in sha
Allah. Mommy taji dadi tare da shin mata albarka. Anty Fadila ma haka. Ba’a kwana ba
tunda rana kowa yazo ya kalla dakin ya tafi.
Gogan ango sai bayan isha ya shigo gidan, shida Abubakar ne da wani abokinsa Mubarak.
Suma sukayi masu nasiha sai suka tafi. Haisam mamaki yakeyi kawai, yau da za’a ce zai
aure bazawara kuma age mate dinsa bazai taba yarda ba, bai saba faruwa a arewacin
Nijeriya ba. Amma komai nufi ne na Allah, wannan kuma zabinsa ne kuma yaji dadin
abinda yayi. Ko sau daya bai taba nadamar aurenta ba. Kuma yaji dadin yadda tazo da
Ajwad yana san yaran kamar wanda shiya haifa.
Hira sukayi kadan inda tana gefen sa harya gama kallon network news, baya missing abin
yana san kallon labaran gargajiya yasan inda kasa ta dosa. Daga nan kuma suka koma daki
inda suka kwanta. Wannan kenan!
Ranar kin dillanci..
Haske tana jin dadin kasancewa tareda Haisam, yana bala’in kokarin yaga bata rasa komai
na fannin zamanta kewa ba. Saida yayi sati daya baije ko ina ba saidai ya fita masjid. Ko
cefane Imran ke yin masu ya kawo. Shi yanzu yana gefen amarya. Yadda yake zumudi yana
tarairayan ta har tunani take tana mamaki. Batasan zata samun wannan matsayi nan a
wajen sa ba musamman tunda ta taba aure. Anan ya kara mutunci a idonta kuma ya nuna
zurfin hankalin sa.
Makwabtar su duk suna tsammanin shine uban Ajwad balle unguwa na masu dashi kowa
harkan gabansa yakeyi. Mutum daya ta shigo mata ma. Mommy duk sallah saita bita da
addu’a. Kwana biyun nan idan ta tuna Haske sai gabanta ya yanke ya fadi ras. Ta rasa
meyasa yake mata haka. Banda Innalillahi wa inna ilayhi rajiun bata ambatan komai.
Yasmin ta lura tana cikin damuwa inda ta kira Haisam ta sheda mashi tunda sunfi kusa.
Anan yayi fitar farko domin yaje yaji dalili, sakata a gaba yayi yaji meke damunta. Bata ce
mashi akan Haske gabanta ke fadi ba kafin ya tayar mashi da hankali. Sai tace mashi haka
kurum bata jin dadi. Addu’a sosai ya bata wanda zata rinka yi domin ta samu natsuwa.
Ranar da Haske ta cika kwana bakwai, tana zaune kan sallaya ta idar da sallar magrib.
Haisam bai dawo daga sallah ba. Wayanta ya soma ruri. A natse ta dauka ta kara a kunne,
sai tayi sallama tana sauraro. Gefenta Ajwad ne ya farka yana wasa da kacau kacau dinsa.
“Besty nice” taji muryan Laila. Gabanta ya fadi saboda batayi zato ba. Bata amsa ba ta
shiga tunani saida Laila ta sake magana.
“Hello! Besty kina jina”
“Eh, ya akayi”
“Lafiya lau…Ya ango?” zugum tayi ta soma tunani a ina Laila ta sani tunda bata fada
mata ba.
“kinyi shiru kina mamakin nasan da maganar koh? Ai abin duniya baya boyuwa”
“Haka ne kam..Ni bari naje zan shiga kitchen kafin mijina ya dawo”
“Sorry besty alfarma nake nema”
“Na me kenan?”
“Balance sheet Zaki koya min, inada interview na aiki gobe da zani”
“Ki duba Google mana”
“Banda babban waya kuma Saif kinsan ya kwace nawa, i won’t bother you idan nasan is
not serious”
“Laila no offense amma bazan iya ba, bawai yin kaina bane ance na daina mu’amala
dake you’re bad luck… Ki nema wanda zasu maki”
Kuka Laila ta fashe dashi sosai, “Haba Haske dan Allah ki taimaka mani… In sha Allah daga
yau bazaki sake ji daga gareni ba har muddin rayuwata”
“Kin tabbata Laila, wannan shine abu na karshe da zanyi maki”
“Na rantse da Allah bazan sake neman wani abu daga gareki ba”
Tunani Haske tayi yadda zata fita, text tagani ya shigo daga Haisam. Yace zai duba
Mommy sharp sharp, Napep ma ya hau saboda yayi sauri baiso ya dawo gida. Ita ma saita
dauki Ajwad tasa shi a mota, a baya ta saka shi tareda seat belt tunda ya soma zama
abinsa.
Harta kunna injin motar sai Laila ta sake kira wai tana kofar layin su, tazo ta sameta.
Bataso ta karaso saboda tasan Haisam bazai soba. Abin yayi ma Haske dadi Laila ta nuna
tanada hankali. Fita tayi da Ajwad sagale a kafadarta suka tafi. A bakin gate mai gadi yace
tunda ba zatayi nisa ba a bashi Ajwad suyi wasa. Dayake yaron baida kiyuwa har Haske
mamakin sabonsa da mutane takeyi.
Tana tafi sauri sauri, gudu gudu tasan da yardan Allah zatayi ta gama kafin Haisam ya
dawo. Bazai masan ta fita ba, Balance Sheet ba wani abin wuya bane kuma kamar yadda
Laila tace ta samu aiki duk wani kamfani ana bukatar a gane duka transaction dinda akayi
end of month dana yearly, vital information ne.
Tana tafe harta wuce T Junction na farko kafin takai bus stop. Sai taga irin motar Ammi,
Corolla S ne silver. Bata kawo komai ranta ba ita tana murna daga yau zata rabu da Laila,
balle Ammi ta koma Zaria yanzu kamar yadda Mommy tace. Ita ma karin kanta yanzu dan
kwana biyun nan da basa harka tafi samun natsuwa. Tanaso su cigaba a haka.
Su Ammi da Laila ana mota an boye ta ciki da zata wuce, dariya sukeyi suna jin dadin tun
kafin abin ya wakana. Laila ce ke mazaunin direba tunda garin kankanba ta taba saka
saurayinta ya koya mata. Sun saka seat belt Sai ta kunna injin.
“Don’t miss” Ammi ta jaddada mata.
“Haba dai sai kace ba yar halak ba” tace tana dariya. Da gudu Laila ta nufa inda Haske
take tafiya a 180, Haske tana tafiya taji gudun mota. Ta waiga kenan sai taga Laila cikin
motar. “Laila” ta furta tsoro fal ranta. Kan kace kwabo kuma ta dauketa da motar. Saida
tayi tashi ta hau kan motar sannan ta ganganra ta fadi. Sai kuma ta takata da motar kana ta
tafi da sauri suka barta a wajen murna fal ransu.
Mai gadin gefen wajen wanda yaga abinda ya faru yazo da gudu, yana zuwa tuni ta suma
tareda fita hayacinta, jini ya soma kwarara mata daga baki da hanci da kuma saman kanta.
Sannan cinyarta ya tsage. Gashi dukta gurje wani abin sai likita ya gani. Mai gidan ya kira
akazo mutane suka fara taruwa yan unguwa wanda zasu wuce Isha. Haisam ya dawo a
Napep sai yaga taruwan mutane. Gabansa yana mugun fadi yace bari ya tsaya ya gani, idan
hatsari ne koba komai shi Dr ne zai bada taimako.
“Innalillahi wa inna ilayhi rajiun”
Hannu ya saka akai saiya karasa wajen nan, “Shamsiyya me kike yi anan? Waya maki
wannan aikin? Innalillahi!” yayita magana
2
“Kasan tane?” mai gadin ya tambaya.
“Matatace” ya amsa da kyar hawaye masu dumi suna gangaro mashi.
Anzo da mota aka sakata, 44 barracks dake kusa aka kaita. Emergency room aka shigar da
ita, Haisam zai shiga suka hanashi. Dadin abin wallet dinsa yana hannun sa. Anan ya nuna
masu ID card na Nigerian Medical Association kuma shine mijinta. Oxygen ke manne
fuskanta tana cikin coma. Anyi damaging brain dinta. Kawai tanada taurin raine wasu nan
take zasu mutu. Ita ma sai dai addu’a amma tanada raunuka internally da externally.
Bayan fitan Haisam daga gidan Mommy jikinta ya sake sanyi ta rasa meke mata dadi,
haka ta kira shamsiyya, ashe an bar wayan yana gefe babu abinda ya same shi. Dayake mai
gadin yana wajen saiya dauka. Shine yake mata bayani ai mai wayar mota ta taka ta, yanzu
haka suna 44 da mijinta. Bata karasa jiba ta fadi kasa sumammiya.
Yasmin dake gefen Mommy taga ta zube kasa, cikin tashin hankali ta dauki wayan. Abinda
aka gayama Mommy itama aka gaya mata. Anan ta sake wayan saita shiga bandaki da gudu
ta debo ruwa. Watsa mata tayi saita farfado. Tana ganin Yasmin sai komai ya dawo mata
sabuwa. Fashewa da kuka tayi ta fita zata asibiti.
Babu hijab kuma kallabinta ya fadi sanda ta suma, Yasmin ta lura da inda zata kuma duk
cikin rudewa ta fita babu kaya. Ita ma mayafin ta dauko da hijab da kuma slippers na
Mommy. A bakin mota taga mommy ta tsaya, ita bata shiga ba ita kuma batayi komai ba. A
sandare kamar itace. Dafata tayi inda tayi firgit ta tashi.
“Mommy ga Hijab” saita mika mata. Yasmin ta shiga mazaunin direba sai mommy tana
baya. Tashin hankali kawai ke dawainiya dasu, a hanya kafin 44 Daddyn Yasmin ya kirasu ya
1
dawo bai gansu ba. Bayani ta soma mashi akan hatsarin.
“Ajwad fah ?” ya tambaye ta
Sai a lokacin ta tuna dashi, bata san ko dashi aka yi hatsarin ba kokuma Haske kadai ne.
Kallon Mommy tayi ta gefen ido wandan ita hawaye daya bayan daya yake bin mata ido.
“Muje gidanta mu duba Ajwad ne?” Mommy bata amsa ba, hawayen ta take abinta.
Tashin hankali mara mitsaltuwa take ciki. Dama tun shigan satin take samun bad feeling.
Saidai yanzu bata kawo Laila ko Ammi ba, itama bata tsammani zasu iya kisa saboda
duniya.
A reception Yasmin tayi tambaya akan matar da aka kai yanzu wanda tayi hatsari, sai aka
ce tana cikin emergency bata fito ba. Ana kokarin a kara mata jini, Type B yana wuya ba’a
samu a bloodbank ba. Murmushi Yasmin tayi saboda ita ma B ce. Anan aka wuce da ita
akayi yan gwaje gwaje sai aka diba.
Engr Muktar yayi ma Zailani waya ya sanar dashi, ya dawo daga Isha kenan. Doka salati
yayi mai karfi idansa ya canza kala. Shima yanzu zai rasa shamsiyya kamar yadda ya rasa
mamanta. Anty Fadila tazo da sauri taji ko lafiya, yanayin sa kawai ya nuna yana cikin
damuwa. Da kyar ya iya bude baki ya gaya mata, itama tashin hankali ta shiga.
A cikin yan watannin da tayi da Haske sun bala’in shiga ran juna, suna ganin girma da
mutunci juna kuma kamar yarta ta dauketa. Tsakar gida taje domin ta kira Fijr, tun bayan
biki yaran Mommy Abubakar ke zuwa zance. Kamar yadda Haisam ya mayar da gidan
Mommy nashi haka Abubakar ya mayar da tsakar gidan Zailani. Suna garden ana gabza
hira.
Ganin Anty Fadila da tayi tun kafin tayi magana ta mike tsaye, “Anty Lafiya?”
“Shamsiyya tayi hatsari a kofan layin su”
“Innalillahi wa inna ilayhi rajiun” da Fijr da Abubakar suka fada.
“Muje asibitin.. Ina ne?” Abubakar yace
“44 kuje zanzo da Daddyn ku”
Su Anty Fadila saida suka biya gidan Haske domin su debo kaya, Anan suka ga mai gadi
sai safa da marwa yakeyi da Ajwad a hannu. Ihu yakeyi yaki shiru. Tausayin yaron ya
mamaye Anty Fadila harta soma kwalla. Karbansa tayi sannan Daddy ke masa bayani akan
Shamsiyya tayi hatsari. Ya lura da gida please.
Bedroom din Shamsiyya ta shiga, ganin shi da tayi ya burge ta. Koma yana mazaunin sa.
Anan ta kwasa kaya kala uku duka dogon gown simple. Ajwad ne ta deban masa babban
jaka na duka abinda yake bukata.
***
Duka yan uwan Shamsiyya an hallara a asibiti, mata masu saurin kuka sai yi sukeyi
musamman Mommy. Fijr ma tana daga gefe ana kuka. Engr Muktar da Daddy Zailani suna
tsaye duk Dr daya fito suna tambaya me ake ciki. A haka ma babu wanda ya basu wani
kwakkwaran amsa.
An shafe fiye da awa hudu kafin wasu leburorin asibiti suka fito da ita akan gado mai taya.
Anan hargitse ya soma. Duk zatonsu wani karaya ne saida sukaga bandeji a duka jikinta.
Fuskanta kawai ne babu komai. Kuka sukeyi har wajen dakinta.
Anan aka sake gyara mata gadon da kafa aka sagala shi sosai. Oxygen dinnan yana nan
makale a hancinta. Idan Kaga kana numfashi da kanka ka gode ba sai karfen bature ya
taimaka maka ba.
Kukan Ajwad yafi daga masu hankali, an siya SMA aka bashi amma yaki karba. Haka aka
roke Fijr alfarma tunda tana shayarwa ta bashi nono. Da farko yaki karba, amma daga baya
ya amsa. Yana sha yana kallon kwayan idanta har yayi barci. Anty Fadila ta karbe shita
goya a bayanta tsam. Haisam kam dakyar yake wani abu, koda ya shiga tiyata din kallo
yakeyi baiyi komai ba. Idansa yayi jazur kamar garwashi. Shi kadai yasan meke damunsa.
Idan Shamsiyya bata farka ba zasu shiga kotun babban duniya da wanda suke da saka
hannu akan abin.
Malaman asibiti suka ce kowa ya tafi sai mutum daya wanda zai kwana, anan aka soma
rige rige kowa naso ya kwana. Mommy ba tace komai ba amma kana ganin yanayinta kasan
babu inda zata tafi. Tana gefen Shamsiyya ta janyo kujera, yadda bakinta ke motsi kasan
addu’a takeyi. Hawaye kawai takeyi fargaba fal ranta. Bataso a maimaita na Hafsat.
Daga karshe an yanke Mommy da Yasmin zasu kwana, Fijr tayi kukan duniya amma ance
yanzu dole ta hakura. Koba Hafsee ga Ajwad yanzu yana bukatar uwa. Ita zata rinka shayar
dashi har aga abinda Allah zai yi.
Haisam baice kala kus ba, yana daga gefe yanata kallon su. Da zasu tafi saiya dakatar da
Abubakar, yace ya shiga motar su Daddy Zailani yaje gidansa ya dauko mashi mota. Idan ya
kawo saiya shiga nashi ya tafi. Haka kuma yayi, sai Haisam ya shiga motarsa wanda anan
zai kwana. Baiso yayi nisa da Shamsiyya kafin wani abu ya faru da ita.
Bayan kwana 10..
Babu abinda ya canza wajen Shamsiyya, har yau bata farka ba. Saidai ciwon jikinta wasu
sun soma warkewa anata rage bandejin. Ko tari batayi ba. Anyi filing abin wajen yan sanda
saboda aikin hit and run ne.
Yasmin tayi rawar ganin sosai, ta cire wani kishi datake yi akan Haske tana lura da ita. Duk
wajen basa wani katabus. Ita take bin kowa da abinci dan idan ka biya ta kansu bazasu
ciba. Sanna kuma ita take monitoring Haske, idan ruwa ya kare ita zata kira Doctors, duk
wani abu daya jibanci Haske ita ce. Sannan ta goya Ajwad tareda dawainiyan sa. Fijr bata
iya komai, kuka takeyi. Ta rasa meyasa duk tayi sanyi, tausayin Haske take sosai.
Duka cikin mutanen da suke wajen daga Mommy sai Haisam zakafi tausayawa. Basa
magana, komai a hankali suke yi. Zakaga pain a idanun su. Haisam sai an roke shi yake
zuwa gida, shima da rana zai je yayi wanka ya canza kaya. Barcin dare kuwa har yanzu a
mota yakeyi. Shi yaga samu shi yaga rashi. Finally ya samu Shamsiyya kuma yana kan
hanyar rasata. Abinda yafi daure mashi kai shine meta fito yi cikin daren kuma ina zata?
Yasan bazai samu amsar ba saita farka
Kowa yana zargin saka hannun Ammi da Laila amma akayi shiru, ita kuma Ammi koda ta
koma wajen boka babu wani labari. Bata ma sameshiba ya takarta kayansa ya koma
kauyen su. Anan tayi zugum takaici kamar zai kasheta. Gashi yanzu batada tudun dafawa.
Laila itama tana zuwa aikin ta yanzu kamar yadda ta saba, bata aikin komai sai waka da
barci. Batayi nadaman abinda sukayi ba ko kadan. Dama ta dauki alwashin ita ce karshen
Haske. Yanzu batada saurin matsala ta ida nufin ta.
Sara kanta taji yana mata, ga bala’in nauyi kamar ba nata ba. A hankali ta bude idonta
saita rufe kuma da sauri. Hasken lantarki ne ya cika mata su. Batasan inda take ba amma
tana kyautata zaton tana duniya ne. Kokarin motsi da jikinta tayi amma ta kasa. Komai
yana mata ciwo kuma yayi tsami. Muryan wajen ta tsinta, tasan muryan masu magana.
Na Fijr ne dana Daddy, sai kuma Bilal. Sake bude idanun ta tayi kuma ta rufe da sauri.
Magana suke wanda bata fahimta ba. Ta kusan minti goma sha biyar.
“Ruwa” ta furta wanda makogwaron yayi bala’in bushewa. Basu amsa ba tunda kasa kasa
tayi magana, kuma basa tsammani zatayi. Ance masu zata kusan wata daya a haka. Yanzu
haka sun canza mata asibiti zuwa private na Dialogue.
“Ruwa” ta sake fadi. Wannan karan Fijr taji magana, data kalla gefen sai taga ido rufe ta
abbatar gizo ne.
“Ruwa dan Allah”
“Haba wallahi naji magana…ta farka” Fijr tace cikin murna saita mike da sauri.
“Doctor ta farka” Bilal ya kwala ihu. Daddy yana bude roban swam ya mika ma Fijr. Anan
ta taimaka ta bata tayi gulp uku saita ture baki. A hankali ta soma kallon su.
“Bilal” tace a hankali. Murmushi yayi mata irin na kwarin gwiwa. Runtse ido tayi saboda
abinda ya faru ya soma dawo mata. Laila ta gani cikin motar Ammi kafin komai yayi mata
duhu. Tabbas tagani ba gizo bane, Laila ce. Besty dinta. Hawaye sirara suka soma zuban
mata.
“Shhhh zaki warke karki damu” Bilal yace.
“Me kukayi mata” Dr yace
“Ruwa ta bukata kuma na bata” Fijr ta amsa. Anan doctor ya soma dube dube yana ganin
progress dinta. Sai ya yanke cewa ta soma samun sauki yanzu tunda ta farka. Kumburi na
kanta yana sauka shima kuma BP dinta ma haka.
Haisam yana motarsa yana jin karatun Alquran da kira’ar Shuraim. Idan yaje ya dubata,
saiya koma motarsa ya zauna yana kuka. An mashi nasiha akan ya daina amma yaki. Har
mommy ta roke shi alfarma bai saurare taba. Idan ba idon Haske ya gani a bude ba bazai
hakura ba. Ya dauki duk wani san duniya ya daura mata, mutuwar ta barazana ne a
ruyuwarsa. Baya tunanin zai iya jure rashin ta.
Yasmin ya gani tsaye a gefen sa, dama ta kawo abinci kuma ko tabawa baiyi ba. Share
hawaye ya maza yayi tareda sosa kansa. Murmushi yayi kokarin kakalowa amma ya kasa,
“Yanzu zanci wallahi” yace sai kuma hawaye ya cikar masa ido fal. Baijin cin abinci, daci
yake ji cikin ransa amma ko saboda wanda suke kusa dashi zaici.
“Ta tashi” ta fada. Ware idanu yayi sosai, zakaga jin dadi karara a idansa. Da sauri ya zura
takalmi ya rufe kofa. Gudu ya soma har dakin. Aikam yana shiga idanunsu suka sarkafe.
Mommy tana gefenta, bata ce komai ba sai hamdala.
“Shams.. Dan Allah ki tashi” yace yana hawaye. Zuwa bakin gadon yayi ya rike mata
hannu wanda akwai bandeji. Rufe idanu tayi kamar bata gane shiba. Da sauri ya kalle yan
dakin domin suyi mashi bayani ko tayi losing memory dinta ne. Ita kuma kunya yake
dawainiya da ita. Yaushe yanuwanta zasu daina shan wuya akan wawancin ta? Yaushe zasu
samu hutu akanta? Musamman Haisam he doesn’t deserve this stress! Allfor what? Kawar
da batada amfani! Kawar da bata kawo mata komai sai tashin hankali! Yaushe zatayi
hankali ne? Kaico ta soma da hali irin nata! Hawaye ya cigaba da gudun mata a fuska.
“Shams nine Haisam baki gane niba ne? l’ve longed for your presence, dan Allah ki bude
ido ki kalle ni” shima kukan ya cigaba. Kallonsa Bilal yayi, tabbas Haisam shiya dace da ita.
He can never love her yadda Haisam yayi. A hankali ta bude idonta ta daura akan nasa,
yadda ya rame yayi baki ya sake bata tausayi. Yanzu ita ce ta jawo mashi haka. Ga kuma
1
Mommy gefe, nata kunyar yafi yawa. Wai yanzu duk ita ce silar wannan.
“Shamsiyya kiyi magana mana, please say anything
“I’m so sorry” ta furta kadan kadan wanda magana yayi mata nauyi. Duk ta galabaita
jikinta yana ciwo. Amma she owes him that much.
“Shhhhh don’t be, nasan ba laifin ki bane” yace saiya saka hanunsa a fuskanta yana share
mata hawaye. Tausayin ta kowa yakeyi, Bilal ne ya soma magana.
“Kinsan abinda ya faru… Like zaki iya tunawa?”
Tsit dakin yayi ana jiran me zata ce, Anty Fadila ta shigo da Ajwad goye a bayanta. Taje
gida domin ta dauko dinner wanda Lantana ta dafa. Yanda taga sunyi charko charko itama
ta tsaya, duk zaton ta mutuwa Haske tayi.
“It’s my Fault” Haske ta fada.
“Karki ce haka Shamsiyya, azzaluman mutane marasa tsoron Allah ne sukayi haka”
Zailani yace.
“Laila ce… Am so sorry… Kun gaya min naki ji… Dama akwai ranar kin dillanci” tace saita
fashe da kuka. Salati kawai ake yi a dakin, dacin da Bilal yakeyi yafi na Haisam. Kallon
Haisam yayi rai a bace yana masifa.
“Ya akayi ka barta kusa da ita? Bakada hankali ne?” yace a fusace. Kuka Haisam ya
somayi. “Wallahi masallaci naje saina biya wajen Mommy. Kafin na dawo…”saiya sake
fashewa da kuka.
“Duk ba laifin kowa bane, stop shifting blame..Ni ce bana jin magana… Ni ce mai sauran
yarda… Dan Naga bazan iya abu ba ina ganin kowa ma Haka yake…Duka laifin nawa ne
kuma am deeply sorry” saita fashe da kuka. Mikewa tsaye Mommy tayi, kallon Haske tayi
tana kuka.
“Yau ga ranar abota, abinda kike nema wajen Laila kin samu… Allah ya barku tare… Kin
tsallake maganar kowa sabida tsabaragen taurin kanki.. Na rasa a inda kika gada haka?
Kowa yana nuna maki fari bakya gani… Sai kace bakida hankali ko bakida ilimi. Wannan
wani irin kawance ne? Kin cuce mu kin cuce kanki” saita fashe da kuka.
“Kiyi hakuri Maman Yasmin” Anty Fadila tace itama hawaye takeyi.
“Kamar ya nayi hakuri.. Duk wanda aka bama hakuri ai an cuce shi… Yanzu ko tausayin
maraicinta batayi sai ta rinka abu recklessly, ta mance tanada yaro. For what possible
reason” saita cigaba da kuka tana share hawayenta da hijab.
Haske rintse ido tayi, tasan batada gaskiya kuma batada bakin magana. Amma alfarma
take nema akan su yafe mata. “Mommy kiyi hakuri dan Allah ki yafe min, I know I’ve caused
so much pain on you”
Kallonsu duka ta rinka yi daya bayan daya, tasan ta sakasu cikin tashin hankali wanda
batada bakin wanke kanta. Existence dinta banda bakin ciki baya kawo masu komai,
kullum suna hidima akanta suna kokarin suganta cikin jin dadi da walwala. Kamar yadda
Mommy tace ne, she’s reckless kuma batada tausayi. Tana abu bata tausayin yadda na
kusa da ita zasu kasance. She is also selfish babu haufi, kanta kawai ta sani.
“Ku yafe min?” ta sake maimaitawa. Babu wanda yace komai ana kuka kawai. Allah ya isa
suke bin Laila dashi kuma cikin ransu, kallon bilal tayi wanda kasan yana cikin bacin rai.
“Bilal please forgive me, nasan akan Laila na shiga hakkin ka?” murmushi yayi mata,
“Just get better”
“Fijr!” tace tare da kallonta. Ita kuma fashewa da kuka tayi, ta rasa dalilin da maimakon
taji dadi sai taji babu dadi.
“Get better Anty, Ajwad yana missing dinki” Fijr tace tare da share ido.
Haka tabi daya bayan daya dake cikin dakin tana rokonsa gafara, data kai kan Mommy
kallon juna suke yi, kafin tayi magana sai mommy tayi, “Shamsiyya na yafe maki, amma l
want you to get better muje muci uwar Laila” mamaki kowa yayi a daki. Mommy ba mace
bace mai ashar a bakin ta. Lallai kam kashin Laila ya bushe.
Haisam shine na karshe, hawaye yakeyi sosai zatayi magana ya dakatar daita.
“Promise me zaki warke mu koma gidan mu domin cigaba da rayuwar da muka fara,
promise me Shamsiyya!” runtse idanu tayi. Batasan me zata ce mashi ba. Yafiyan sa kawai
take nema.
“Haisam ka yafe min dan Allah, ka hanani kuma ban hanu ba. Na fita ba tare da na
tambaya ba. I caused so much pain on you… Jibe yadda ka koma akaina… For what?” saita
fashe da kuka.
“Nace maki you don’t get to talk, hear me first… hamsiyyal love you fiye da tunanin ki..
Na rasa ki da farko yanzu banso na sake rasa ki, this is my second chance at love, ki warke
mu koma gida… This is not goodbye, ki taimaka min dan Allah ba dan halina ba”
“I feel so much pain, jikina yana bala’in ciwo… Da kyar nake magana… Da kyar nake
maku magana yanzu” ta fada chan kasa. Muryanta daya soma dishewa. Da sauri Mommy ta
tashi taje wajenta. Rufeta da bargo tayi tana gyara mata kwanciyar.
“Ya isa haka mana, tunda ta gaji maganar ya isa… Ki kwanta kiyi barci please” saita shafa
mata kai tana murmushi.
“Yau zan kwana anan zan dubata” Haisam yace. Babu wanda ya musa mashi saboda ya
cancanci hakan. Nan take Bilal yayi ma DPO text akan samun lead na case din.
Sun taba hira kadan suna yi suna kallon Haske tana numfashi kadan kadan, hankalin su
ya kwanta sosai. Sallama sukayi mata sannan suka tafi gida, yaune ranar farko da Mommy
zata kwana a gida tun faruwar abin. Ko zuwa bata taba yiba.
Haisam ya jawo kujera ya zauna gefen Haske, kallon yadda take barci yakeyi. Santa yana
bala’in shigansa. Addu’a kawai yake mata domin ta samu shifa. Wajen karfe daya na dare ta
farka. Bataga kowa ba illa Haisam, tausayin sa ta sake ji. Ya kamata ace yana kwance kan
katifa yana hutawa amma jibeshi zaune akan kujera kamar mai gadi. Duk laifinta ne, ita ce
mai kunnen kashi, batajin magana. Da tabi n’a su da duk haka bai faru ba. Amma ance
.l.l 41
7:52 PM 0O *
wanda aka bashi kazar wahalar saiya fige.
“Zauj” ta fada. Baiji ba yayi nisa wajen barci. Mitsake hannunta tayi wanda ya rike shi gam
kamar wani zai kwace ta.
“Zauj… I’m so sorry… love you so…” bata karasa ba ta soma sarkewa. Anan ta fara tari
wanda yayi sanadiyar farkawan sa. Tana tari tana ta bala’in kwarewa.
2
“Shams… Talk to me! Me ke damun ki? Na kawo maki ruwa ne?”
Girgiza mashi kai tayi, a hankali kuma tarin ya soma ragewa. Dama ECG da aka saka mata
sai sama kasa yakeyi. Sai kuma yayi layi daya tare da kara. Salati tayi sai HASKEN
idanta ya mutu.
” Ta rasu Sir” Nurse dake duty ta fada mashi. Kallonta yayi ya sake kallon Shamsiyya
wanda bata motsi ko kadan. Da sauri ya fita ya bar dakin. Varenda ya samu ya zauna sai ya
saka hannunsa a saman kansa. Salati ya somayi yana kuka. Wannan kenan!

Advertisements

_____

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

HASKE CHAPTER 24

Advertisements _____ HASKE CHAPTER 24 Hakuri shine gishirin zaman duniya amma ga Fijr kuwa barkono …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *