HASKE CHAPTER 26

Advertisements

_____

HASKE


CHAPTER 26Saif ya tashi murna fal ransa, zaiyi hadaka da wasu iyamurai yan Abia. Yanzu zai koma ya
fara business din saida electronics inda Mr Osita da Mr lyke zasu rinka shigowa dasu
Plasma, Fridge, Home theater, AC, DVD, fanka, Dispenser etc daga Japan sai ya rinka masu
distributing a Kano da Kaduna.
A Katsina road shagon yake babba wanda zai dauke kaya masu dan yawa kafin su samo
babban shago inda zasu mayar permanent office, wani plaza ake ginawa wajen Leventis
roundabout inda suke hari.
Saif ya kasance mai inferiority complex, idan yana tareda mutane ya rinka kwaikwayo
yana yanayin su. Sam baiga kyau ko burgewa a yanayin dayake ba. Musamman saka
manyan kaya yanzu tunda ya soma harka dasu Osita da lyke ya daina saka kaftan.
Kasuwan barci yaje ya dizgo gwanjuna dinsa masu kyan gaske riga hudu da wanduna
biyu. Sai hula hana sallah bana gayu ba irin dai wanda iyamurai ke sakawa. Sannan ya siyo
cambas baki yana hadawa.
Idan Kaga Saif kafin yayi magana zaka rantse baya ta’ammali da Mohammadu. Gashi ya
mulka vaseline a fuska yayita sheki kamar dan wake abinsa. Uwa uba yaci zanzaro kamar
wanda zaije yakin basasa ga kuma tie ya damtse wuya. Dayake bai iya sawa ba haka yake
numfashi sama sama har sai ya gaji da azaba ya cire. Wai shi yanaso yayi looking smart da
ka gansa kaga daular.
Dayake ya canza kalar motonsa, lemon green ya fenta. Gashi dama Sienna yanada girma
haka yake tafiya cikin garin kowa yasan da zuwan shi wal wal yana jan hankali a kansa.
Yace ma kadan kenan, yayi fentin green saboda dollars green ne duk da ba yanayi daya
bane, a nasa tunanin gwara yayi announcing success dinsa. Kowa ya gane Saifullahi
Dangoten Rigasa ya danno kai.
Yau ma ya tashi tun safe zaije su gama deal din, a dakin Bukola yake kuma abin yayi
mashi dadi sosai. Yasan zai ci gangariya, koda yake kudinsa ne. Tunda ya lura yana samun
alheri tunda ya auro ta baya bari ta kashe kudinta wajen cefane sai idan bai sani ba.
Kwandan dankali biyu ya siya da crate din kwai sai ketchup.
Tun bayan asuba bata kwanta ba, zuwa tayi ta kaima Laila dankali mai uban yawa domin
ta fere masu. Kuma tace dan Allah tayi sauri sannan kuma ta ajiye mata durum na ruwa
akan tayi maza ta cika. Sai tace mata anjima idan ta tafi aiki taje lungun dakinta ta baya
domin ta share mata kura da datti ya soma yawa.
Laila taji haushi sosai inda ta dake kamar bata taba dariya ba, anan Bukola tayi magana.
“Anty Laila wallahi banso ana min aiki ana hada rai. Allah ya baki hakuri” saita kwashe
dankalin zata fita. Da sauri Laila ta tare ta.
“Haba Bukola ba fushi nake yi ba wallahi. Kaina ke ciwo” saita kakalo murmushi.
“Karki damu Anty ba damuwa kije”
“Wallahi zan iya” saita karba. Ta lura idan bata taya Bukola aiki ba, hanata abinci takeyi
gabaki daya ranar koda tazo ta tayata daga baya.
Sameera tayima text akan karta damu da neman abinda su Abul Khair zasu dashi
makaranta. Dayake cikin Sameera yanzu yana bata wuya musamman da safe. Koda yake
Bukola itama nada shigan ciki amma bata gayama kowa ba har Saif.
Sameera taji dadi sosai inda ta sake kara barci bayan tayi masu wanka da asuba. Bukola
roba babba ta cika bayan ta fere, kuma Nepa sun mata kirki sunbar wuta inda ta saka a
deep trier dinta yayi mata saurin suya.
Tazo da hantan kaza daga shagon mamanta, anan ta yanka shi kanana ta hada da kwai
da kayan miya albasa, tarugu da garlic. Kafin kasani gidan ya gauraye da kamshi. Ta raba
gaba daya gidan harda Laila.
Tana kitchen sai ga Saif, murmushi sukayi ma juna inda ya dauki cokali ya soma dandana
sauce din sai ya dauki dankali da aka sauke daga wuta guda hudu, aikam ya kona hannu.
Maimakon ya mayar kwanon saiya maza ya tura bakinsa. Abin yayi kyan suya kashar kashar
duk miyansa yana bala’in tsinkewa.
Aikam nan ya rinka soya mashi wuya a hankali, ihu ya fara yana zillo. Dankali kuma a
hankali yake tafiya, daya kai wajen kirjinsa saida yasha mamaki. Idanun sa suka kawo ruwa
sosai aikam anan ya burka tusa mai uban kara.
Tusan ya bakanta ma Bukola rai, ita batasan abin kwata kwata. Dama ya saba mata ko
kunya irin tana amarya babu abinda ya sha mashi kai idan ta kamashi suna zaune suna
kallo a falo zai banka mata. Gashi tanada kyankyami batasa kazanta kusada abincin ta.
Nanda nan sai amai ya soma mata kakari ita haka yanayin ta yake.
“Haba meye haka zaka mana tusa cikin kitchen?” da kyar ya iya magana yana nishi, ga
azabar dayake ji ga kuma tayi mashi maganar tusa. Kunya yaji sosai saboda bai taba
tsammani zata damu ba. Wai shi a dole idan ya banka mata itama ta rama ayi dariya a wuce
wajen.
“Bakida tausayi ne? Bakiga na kware bane?”
“Ni dai gaskiya banason haka! Yanada kyau ace mutum yanada kunya duk da ni matarka
ce. Ya kamata kayi excusing kanka” dayake bata kallon idonsa ta juya mashi baya. Kallon
sama da kasa yayi mata ‘Ahhh Lallai’ yace cikin ransa saiya fita.
Bayan sun karya shiya ajiyeta a shago saiya wuce nashi sabgan gabansa.
Yaje banki ya ciro miliyan daya da rabi wanda zai bada nashi Kenan. A ledan viva aka saka
mashi yan dubu guda sha biyar. Ya fito daga motarsa zai karasa inda shagon yakeyi tunda
bai samu yayi parking gaban wajen ba akwai wasu motaci.
Ya fito zai rufe motar sai yaji an tallabe mashi keya tare da kwace ledan ‘Wuf
” Heeehooo Barawooo”
ya fada da karfi saiya saki makulli a kasa yabi mutumin daya kwace kudin. Dayake bai rufe
motar ba haka ya tafi. Ashe su biyu ne sai dayan ya shigan motar ya taka yabi hanyar dasu
Saif suka bi. Zuwa yayi da mota kamar zai kade Saif dole ya matsa ya canza hanya. Sai ya
bude ma dayan kofa ya shiga suka tafi.
Haka Saif yayita rero ihu yana kuwa yana binsu, gudun famfalaki yakeyi kamar kafansa sai
tsinke duk ya gaji. ‘Fal fal fal fal’ kawai yake wurga kafansa gaba. Zufa yakeyi amma yaki
daina gudun. Gashi motar ta tsere masa sosai saboda ma Go slow ne da bazai gani ba.
A hakan ma daga baya ya daina ganin motar, abinda yasa ma yake iya hange daga nesa
saboda kalar fentin. Haka yayi zaman dirshan a kasa wajen Leventis. Daga hannunsa sama
yayi yana kallon sararin samaniya hawaye masu dumi suna gangaro mashi daga idanu.
“Annabil Annabi! Annabi!!”
Saiya aza hannu akan kai ya cigaba kuka jabe jabe. lyakacin kudinsa kenan ya rage. Kuma
500k bashi ne bana shi bane. Wasu na annabi ne suka tsaya suna mashi magana. Da kyar ya
daina kiran Annabi ya masu bayani. Haka aka saka shi a napep inda zai je magajin gari
police station domin yayi reporting.
A police station kuka yake shabe shabe kamar anyi masa mutuwa, jikinsa duk rawa yakeyi
dakyar yake iya rike biron dayake rubutu dashi, da DPO yazo wucewa duk daukarsa an
kashe mashi uwa ko mata yanda yaketa kuka da shesheka. Sai yaji cewa sata aka mashi,
kwafa yayi yabar wajen. Bai san namiji rago mara tawakkali.
Bayan ya gama ya taka yaje shagon nasu, su Mr Osita sun jira shi har sun gaji. Anan yazo
wajen da zufa jabe jabe duk ya sake baki ya canza fasali farad daya, yanda yakejin jikinsa
kamar an mashi duka da itace. Anan yayi masu bayani inda suka mashi jaje. Saidai sunce
mashi lallai dole saiya bada wani abu kamar yadda suka bukata kokuma kawai ya bar abin.
Kuka ya sakeyi saiya fita yabar wajen saboda bashi da hanyar samun kudi. Mr lyke ya
bashi dari biyar domin ya hau achaba. Dayaje gidan ruwan baiga ana hada hada ba. Anan
ya tambayi lafiya ake masa bayanin babban injin su ya lalace. A haka za’a gyara wajen dubu
dari da talatin.
Da sauri ya wuce ofis dinsa saiya rufe, kuka yakeyi sosai yana kiran ‘Annabi’
Kiran Annabi yakeyi cikin Ofis dinsa yayi zaman dirshan kamar zai soma bori, kuka yakeyi
jabe jabe kamar karamin yaro. Ya mance yaushe rabon da yayi kuka haka, ko sanda
mahaifinsa ya rasu baiyi ba.
Bugun kofa akeyi amma yayi banza dasu, baya tunanin akwai wani abu da zai sake samun
sa dayafi wannan. Ji yake kamar zai haukace ya huta. Ba’a bar bugun ba kuma bai bude ba.
Magana yaji wanda ya sake firgita shi.
“Saifullahi ka bude mana ance kana ciki, Alhaji Shehu ne”
Gaban Saif ya fadi saboda mai gidan da yake haya ne na shagon ruwan yazo karbar
kudinsa, da kyar ya mike tsaye ya share hawaye ya bude. Alhaji Shehu dattijo ne mai uban
masifa. Baya ma mutane uzuri babu ruwan shi. Daka bari maganar kudi ya hadaku gwara
ka mare sarkin zazzau dan shi kila ya yafe maka.
“Saifullahi na biyo batun kudina ne, sati biyar kenan kayi min shiru” da kyar Saif ya bude
baki zaiyi magana amma babu abinda ya fito. Gyara murya ya sakeyi saiya soma magana,
wannan karan dakyar kake jin sautin murya.
“Ranka ya dade, Dan Allah kayi hakuri wallahi an mani sata da kudina da mota”
“Allah ya kiyaye tsautsayi amma ai bani nayi maka ba, yanzu ina laifina da wannan
kanaso na barka kenan babu ko sisi. Gaskiya zaka tashi min daga gida. Babu abinda ya
shafeni da quick notice, gobe zanzo da mutane su fitar maka da kaya”
“Dan Allah kayi hakuri kayi min rai, wallahi zan hado maka kudinka”
“Nima kayi hakuri ka barmin gidana, zaki da mai muka biyo birni. Idan ina sana’a da
bashi bazan dade a birni ba… Nina fara fita nayi arziki a kauyen mu.”
Rufe ido Saif yayi saboda kanshi yana bala’in Sara, ga kuma labarin Alhaji Shehu wanda
yaji yafiso sau dari akan shine ya fara kudi a garin su. Duk inda ya je saiya fada labari. Da
Alhaji Shehu ya gama zayyana wa tas sai ya buga babban rigar sa ya fita abinsa yana
mazurai.
Saif tunani ya somayi, ya rasa abinda yayi da bala’i haka suka rinka abko mashi. Yaga dai
yana sallah duk da bajam’i ba amma yanayi, kuma yana azumin ramadan ko yaki koya so
sabida baiso Allah ya kona shi. Toh wani laifi yakeyi haka da bala’i ya fado mashi rana daya.
Tunani yakeyi amma ya rasa gane amsar tambayar. Chan daga baya yayi dogon nazari
Saiya tuna ma’aikantasa watanshi uku bai biyasu albashi ba. Saidai kuma aiki ya gaji
haka, wata rana a biyaka wata rana ayi maka fuska ne. Shi kuma yana tara kudin ne zaiba
su Mr Osita. Rufe ofishin yayi saiya fita, babu wanda yasan an mashi sata. Su dai suna
haraban wajen suna kallon shi yana tafe kamar bashida lafiya.
Da kyar ya isa gida saboda yana famada zazzabi ga bala’in ciwon kai, koda ya iso yaga
Laila bakin daki tana jiransa, baida karfin mata magana saiya kauda kansa. Ita kuma bala’i
yana cinta yau za’a yita a wanye. Bataga dalilin da Bukola take zuwa aiki ba, dole itama
tabar zuwa kokuma babu sauran jin dadi a cikin gidan. Balle yadda Bukola ta mayar da ita
mai aiki itama saita rama ta hanyar hanata aiki.
“Wallahi a yau sai dangin Oduduwa tabar zuwa aiki kamar yadda nima na bari” tace tare
da shan gabansa. Kallonta yayi sai ya ratsa ya wuce. Da gudu ta sake binsa tana masifa,
dakin Sameera yaje ya mika mata hannu. Ta gane key yakeso tunda yana dakin Bukola ne.
Anan ta mika mashi inda ya karba ya wuce, bai bita kan Laila ba ita kuma bata fasa mashi
masifa ba har ya shiga cikin dakin ta bishi. Inda take shiga banan take fita ba. Masifa taketa
yi kamar zata ara baki.
“Laila ina tausayin ki wallahi, duk abinda take maki da wannan zaki saka mata, ina ce
abinci take baki” wulla ido tayi abin baya shigan ta.
“Ai bakin da Allah ya tsaga bazai hanashi abinda zai ciba, saboda haka dole kace mata
tabar zuwa aiki”
“Idan bance bafa”
“Aikam baza a sake samun zaman lafiya da kwanciyar hankali ba, za’a yi kutumar uba
anan gidan
“Laila lafiyan ki kuwa? Ina mijinki kike watsa min kalamai masu zafi”
“Toh ai kai ba cikakken namiji bane, inda maza suke bazaka iya zuwa ba”
Tunani ya soma kodai tasan da karayar arziki shine takeso ta kawo mashi raini, yanzu
tana ganin su tsara ne. Amma zai bata mamaki ya nuna mata koda yake talaka zai iya
dukan matansa idan sukayi mashi laifi. Kuma gidansa bazai fi karfin sa ba. Yanzu dole ya
sake zare masu ido ya nuna shine in charge.
Sharara mata mari yayi mai kyau, baida karfin dambe amma gwara ya nuna mata Bafa
tsoronta yake ba. Aikam saita wanka mashi shima, yaune rana na farko data mare shi. Da
chan sai dai ta dake shi a jiki. Idanunsa ya firfito yayi mamaki ainun. Aikam ya zuciya ya
sake wanka mata mari.
“Ke kin yi karya ki mare ni na kyale ki… Yar tasha kawai” ya fada yana nuna mata hannu.
Anan ta sake daga hannu ta Sharara mashi wani, saita sake dagawa zatayi mashi wani saiya
rike mata hannu yana mazurai. Finkicota yayi ya sakata a loko ya soma kilarta.
“Dan ubanki ni zaki mara? Halan nayi kamada tsaran ubanki?”
“Badai ubana ba saidai ubanka, shege matsiyaci”
ta fada tana nishi tare da kuka. Shikuma tsiya data kira ya sake tuna mashi lallai sunyi
sallama da talauci. Anan ya zuciya ya zage damtse yana dukanta. Itama dai tana ramawa
amma yafi samun galaba akanta. Suna cikin dambe ne sai suka fasa ma Bukola Centre
table da kuma Jug dake kai duka. Bafa su daina ba ta yaga mashi riga shi kuma ya barka
mata skirt daga ita sai underwear sannan rigarta ma ya yage.
Sameera ne ta shigo da gudu, “Dan Allah ku bari wallahi babu girma, kun maida dambe
abinci kullum sai kunyi”
“Barni da dan iska yau saina nuna mashi asalin waya aura, bana cikin matan da miji zai
juya su wallahi ubanka zanci” saita nufeshi da naushi.
“Innalillahi wa inna ilayhi rajiun! Laila anya bakida ciwon hauka? Mijinki ne fa” Sameera
tace. Aikam Laila ta nufeta tana zagi, saita dauki kwalban Jug zata luma mata.
“Dan uwarki yau zan nuna maki asalin hauka”
“Idan kika bita da jug dinnan a bakin auren ki”
Ko ajikinta ta soma bin Sameera dashi, ita kuma waje ta fita tana neman taimako. Bukola
ne ta dawo sai taga ana fita daga dakinta cikin hauka.
“Lafiya meye haka?” tace a firgice
Babu wanda ya tanka ta banda Sameera data shiga dakinta ta saka sakata tana numfashi,
hawaye ta soma saboda Laila ta ci mata fuska ba kadan ba. Amma Allah saiya saka mata, ta
window ta rinka lekawa. Ita kuma Laila sai buga kofa tana masifa.
” Dan ubanki ki bude na nuna maki asalin hauka, baka mummuna mai katan duwaiwai”.
“Laila na sake ki saki daya” yace da karfin tsiya.
“Innalillahi wa inna ilayhi rajiun” Bukola tace
Ita kuma ta tsaya cak, sai kuma tayi dariyar mugunta ta ajiye kwalbar ta soma tafiya.
Waka ta soma tana rawa tare da guda.
“lale iye yanci ya samu babu sauran bauta” tsohon waka ne da akayi zamanin su Fati
Mohammad a kannywood. Kamar mahaukaciya tsab babu bambanci harda kwaso shoki
tana makale kafada.
“Dan Allah Saif kayi hakuri bai kai nanba” Bukola tace
“Ai Barta kawai ta tafi annoba ce, idan kinsan meya kawo fadan nan murna zakiyi.. Cewa
tayi dole kibar zuwa aiki”
Kallon Laila Bukola tayi tana mamaki, bata sake cewa komai ba ta wuce dakinta. Anan
taga barnar da sukayi mata. Yanda kasan dabbobi haka suka mayar mata da daki. Ita kuma
Laila cikin minti talatin ta hada kayanta a akwati. Murna takeyi tasan idan dai an saketa ne
dole su Gwaggo su barta.
Ko kudin Napep batada shi, da suka kai kofar gida taga wasu samari na layin su ana
mutunci. Tace su bada kudin Napep din. Basu kawo komai ransu ba suka bata inda ita taja
akwati ta shiga ciki.
A tsakar gida taga Gwaggo tana jan ruwa a rijiya, kallonta tayi sai ta kalle akwatin. Anan
Laila ta soma hawaye “Gwaggo ya sake ni”
“Saki nawa yayi maki?”
Laila ta soma murna, saita sake fashewa da kuka. “Saki daya yamin bayan ya dakeni”
“Alhamdulillahi kinji dadi akwai sauran shan ruwa…Tun kafin dare yayi maki dauki
kayanki ki koma. Sai kiyi idda a dakin mijinki”
“Bangane ba Gwaggo” tace a tsorace
“Ina nufin ki tafi kafin Malam yazo, kin mance meya ce maki ne halan?? Ki rufa ma kanki
asiri dan Allah kuma ki rufa min nima kar yace nike zuga ki”
“Yanzu Gwaggo ni kadai zan koma bazaki zo muje kiyi mashi fada ba, sai kace banda
dangi banda gata”
“Ai ba tare muka zo ba. Kije bayan kwana biyu zanzo muyi magana… Amma yanzu ki rufa
min asiri ki tafi dan Allah.
“Wallahi Gwaggo banda ko sisi”
Anan gwaggo ta kwance zaninta ta bata dubu daya. Jan akwati tayi tana tafiya tare da
tunani. Gaskiya bataso ta koma wajen Saif bayan iskancin datayi ma kowa a gidan.
Musamman Bukola da Sameera. Da wani idon zata kalle su? Wani dabara ya fado mata
gwara taje gidansu Haske domin ta bata masauki koda bazata rinka mata magana ba. A
rama ma kura aniyarta, balle tasan Haske akwai tausayi idan taga halin datake ciki zata
taimaka mata. Daga nan ma plan dinta da Ammi sai suyi sosai sannan ta samu abinda zata
samu wajen Haske kafin ta gudu ta koma koda Abuja ne ko Lagos da zama inda babu
wanda ya santa, sannan tayi sallama da bariki tateda samun duniya yadda ya dace.
Wannan kenan!
Haisam ya saka Doctor ya sallame Haske akan cewa zai ci gaba da dubata a gida idan
wani matsala ya tashi. Fafur yaki yarda ta koma gidansu na Daddy Zailani saidai gidan
Mommy. Anan zai fi samun damar sakewa da ita ya kuma yi monitoring duk wani motsin ta.
Shi a nasa tunanin yanaso yama koma gidan ne dakin Abubakar inda kome akeyi a
idonsa. Baiso kwata kwata Bilal ya kebe da ita balle ya sake rudanta da wani karyan.
Mommy ne da Maman Haisam suka rinka bashi hakuri ana lallashin sa akan ya bari ta
koma gidansu tunda dai mahaifinta yanada rai kuma da rufin asiri. Abin bai mashi dadi ba
amma ya hakura, still bai fasa abinda yayi niyya ba.
Ammi taji haushin haka, taso ta zauna gidan Mommy yadda cikin dare zata dauki Ajwad ta
yarda a titi. Yasmin taji dadi ta wani fanni sannan kuma ta wani fanni bata soba. Jindadi
shine yadda Haisam zai rinka zama a gidan kullum, rashin jin dadin kuma shine yadda ba
wajenta zai rinka zuwa ba. Sai wani zuciya yace mata ai a haka ne ma zata samu ta karkato
da ra’ayin sa akanta. Idan ta rinka yima Haske hidama tana mata abubuwa Haisam zai
gane itama tana san abinda yakeso kuma zaiji tausayin ta.
Yadda takeji yanzu bataki ya aure su biyu ba tunda ya halasta a gareshi. Ita da kanta ta
dauki Ajwad ta runguma inda ta hakince a gaban motarsa sanda zasu bar asibiti. Sai ita
Haske motar Mommy ta shiga inda direba ya jasu domin su tafi. Fijr bata samu wajen shiga
ba sai motar Haisam daya rage, Ammi tace babu wanda zai shigan mata mota tunda babu
mai saka mata mai.
Haushi taji sosai saboda ranta ya baci kala biyu ne, na farko an sallame Haske duk da
koda ta zauna babu laifi. Tunda ta fara zuwa asibiti shi head din Doctors din ya burgeta.
Dattijo dan shekara 58 dan garin Gombe yaren Tangale. Yanada kamala da dattako tuni ya
tafi da duka imaninta. Yasa take zuwa asibitin ko taso ko bata soba.
Dr Mahmoud yanada mata biyu duka yan Gombe ne, dayan yaren su ne Rukayya dayan
kuma Fulani ce Halima. Yanada yara goma sha biyar cur kuma suna raye. Baida niyyar aure
a halin yanzu. Shi baida sha’awa ya tara mata barkatai. Abinda yasa ya aure mata biyu baifi
dama suna soyayya da Halima ba sai iyayenta suka ce basu amince ba tunda shiba Fulani
bane kado ne, haka akayi ta fafitika amma suka ki.
Bayan ya aure Rukayya wanda take yarensa sai Halima ta birkice ta soma ciwo har zuciyar
ta ya kusan bugawa, dole iyayen Halima sukazo domin ya agaza masu tunda yanada halin
rike mace fiye da daya. Suna zaune kamar kawaye ba’a jin kansu saidai ba’a rasa wani abu
ba na kishi. Amma zaman lafiya akeyi kuma yaran dakyar ka bambamta yan dakin wane.
Yanzu Ammi ita ta gama yarda cewa Zailani bazai mayar da ita ba tunda bikinsa saura
kwana kadan. Yasa tace bari ta soma neman bazawari koba komai ya rufa mata asiri kuma
ta samu duniya. Balle yadda taga yana hawan manjan jipajipai ga kaya na alfarma, sannan
yana jin turanci yari yari kamar rainon Queen Elizabeth.
Haka take sake baki tana kallon sa idan yazo duba Haske da safe, gashi yanzu rawar kan
Haisam yasa an sallame su. Ko fadan da akayi da Haisam da Bilal tana asibiti amma taje
neman Dr Mahmoud, ranar ta dauki alwashi sai sun yi magana. Tunda ita ba yarinya bace
bataga dalilin da zata rinka wani wasan buya da saurayi ba.
Tana Office dinsa tace masa gwiwanta yana ciwo, saiga Haisam yazo rai a bace a sallame
su. Haka Ammi ta fincika motarta rai a bace tabar asibiti. Fijr da Hafsee na tsaye batasan
inda zata ba. Ta lura Yasmin nasan Haisam kuma tasan kila zasuyi hirar mosaya yasa bata
so ta shiga balle ta takura masu. Napep ta ayyana zata shiga tunda shine abin hawanta
Haisam ne ya fito daga motarsa yaje inda take, murmushi yayi mata saiya mika hannu ya
karba Hafsee. “Muje motana akwai space ai” saiya juya bai ko kalleta ba balle ya tsaya yaji me zata ce.
Yanda suke jerawa kamar mata da miji da yaron su Yasmin ta lura, sai kuma ta tuna Haske
bala’in siririya ce kamar ita, Haisam baya san mata masu kiba. Fijr batasan matarsa na da
chan ba, amma kana ganin wannan kasan sabuwa ce.
Ita a duniya tana bala’in san kampanin Mercedes Benz kuma shine wanda Haisam ke
hawa. S Class ne sabuwa fil baka yana sheki gashi akwai tint. Sannan ma wannan yafi na
Bilal zafi. Da azama ta zagaya baya ta shiga saiya miko mata Hafsee.
Suna cikin motar kawai kallon kirarsa takeyi, ya keru sosai. A ranta ta ayyana wani miyan
sai a mokwabta, shima na chan bayan layi. Haisam yanada natsuwa sosai kuma sun dace
da Yasmin. Bazai taba ma kallon ballagaza irinta ba. Tunanin Ghali ya fado mata a rai wani
sanshi ya sake mamaye mata rai, ita har ga Allah sanshi takeyi saita runtse ido ta furta
“Masoyina.. Ina bazai yiwu ba… Kambala’i’ ita anata tunanin a hankali tayi amma kowa
dake cikin motar yaji.
Ta centre mirror Haisam ya kalleta yayi murmushi, Yasmin kuma tanata wasa da Baby
Ajwad abinta. Shi ne yaga shirun yayi yawa ya soma janta da hira. A hankali ya soma
magana cikin yanayin sa na sanyi “Chiquita raino zai maki kyau”
“Da gaske Yaya?”
“Uhmmm gashi Ajwad sai murmushi yakeyi baima lura cewa mom dinsa bata nanba”
“Ai yanzu kullum zan rinka zuwa, kafin posting dinmu na Nysc ya fito”
Murmushi yayi a ransa saboda shima baiyi bautar kasa ba, abinda ya dawo dashi kenan.
Bawai yana tunanin zai dauwama a Nigeria bane kawai idan tsufa yazo maybe zai dawo
daga US kada ace baiyi bautar kasa ba. Saboda shi harya samu aiki inda yake. Dama
shekara daya yazo yayi saiya koma na dindindin tinda Haske tayi aure.
Amma yanzu kuma komawarsa akwai tangarda, bai san ko zai iya tafiya ya barta ba.
Soyayyarta yana nan daram babu inda yaje. Tsoron sa kawai kada ta sake gudunsa kamar
yadda tayi da farko. Yasa yakeso duk wani hanya na communication da Bilal yanaso ya
yanke, out of sight is out of love.
Sanda suka isa Fijr ta leka ta window sai Mallam Adamu ya ganeta shine ya bude masu
gate. Farfajiyar gidan ya burge Haisam sosai furanni ta ko ina. Shi ne ya karba Ajwada
hannu sai kuma Hafsee ya mika mata yatsa daya tana wurga kananan kafarta tunda ta
soma tafiya.
Fijr ne take gaba tiryan tiryan suna binta har suka kai falon, saiya tsaya a wajen.
“Ka shigo mana, sai kace bako” Fijr tace
Yayi jim kamar bazai jeba sai kuma ya bita, babban daki ne aka ajiye Haske. Dakin Ammi
nada Daddy Zailani yasa aka gyara mata inda zasu wala da ita da babynta. Dayan dakinta
shima yanada girma da kadan wannan yafi shi, yayi ma Anty Fadila magana idan bata
yarda ba sai a fasa, itace ta kara mashi karfin gwiwa. Tace duk abinda Ammi tayima Haske
yafi cancanta akan ta gaje dakinta. Koba komai Ammi taji bazata soba ba. Balle tunda
yaranta tare da Anisa zasu zauna batada matsala ita kam.
Cradle din Ajwad Haisam ya ajiye shi, kowa na cikin dakin ita shamsiyya tana kwance ta
rufe ido. Tanajin sallamar shi tayi maza ta damtse ido. Ta wani bangaren taji dadi kuma taji
haushi. Dadinta shi ne yanzu kuma Bilal ya fara kishinta, shima Haisam haka. Haushi kuma
idan yanzu suna yi sabida kiyayya da suke ma juna babu wanda ke Santa a cikin sufa.
“Mommy ni bari zan tafi amma zan dawo anjima. Akwai abinda kuke so ne?”
“A’a munada komai, wallahi daka huta Allah ya saka da alheri”
“Amin”
Harya soma tafiya sai Yasmin ta mike, “Yaya muje ka sauke ni”
Kullum Haisam yana gidan yana killace da Haske, aiki yayi ma Bilal yawa yana Abuja yasa
bai samu dama ya duba Haske ba. Abin yayi ma Haisam dadi ko babu komai yasan
matsayin shi yanzu.
Bilal a wajen Ummansa ya samu labarin Haske tana gidansu ne tunda har taje. Dama yaje
shoprite na Abuja yayi ma Ajwad siyayya kamar bai san darajan kudi ba. Duk abinda ya
burge shi yake dauka. Haske itama ya siyan mata leshi biyu da material daya.
Dayake Mallam Adamu yasan shi baiyi shayin bude mashi kofa ba, haka yakjr parking lot
domin ya ajiye motarsa. Haisam ranar bai zoba tukun Mommynsa batada lafiya zai mata
allura da kuma kara mata ruwa. Yadai kira Haske yayi mata bayani.
Ita kuma tunda Bilal ya daina zuwa saita karkatar da tunanin ta akan Haisam fully. A
hankali take bari soyayyar sa yana shiganta. Tana samun nishadi idan yazo kuma rashin jin
dadinta idan baya nan. Koda baice komai ba tana jin dadin kallonsa a koda yaushe.
Ya canza sosai kuma taji dadin canjin, ya zama dirarren namiji wanda kowace mace zatayi
alfahari da samunsa. Tana sane da Yanda Yasmin ke zirga-zirga duk sabida Haisam ne,
amma its a selfish world. Idan Bilal ya guje ta bazatayi wasa ta bari Haisam yayi mata nisa
ba.
Da kanta ta karbi number din sa wai idan wani abu ya motsa ta kirashi. Ita duk siyasa
takeyi saboda koda chatting ne su soma. Amma ko sau daya bai taba ce mata uffan ba.
Tana ganinsa online wani zuciya yana ce mata tace mashi koda ‘Salam’ ne tunda shi dan
uwanta ne. Sai kuma ta fasa ta rike mutuncinta na mace wanda Allah yayi mata.
Yau daya ce bazai samu damar zuwa da wuri ba duk taji babu dadi, ranta baiso ba taji
kamar an cire mata wani bangare na jikinta, yanzu tasan ta kamu da ciwon sanshi. Saidai
batasan a matsayin daya dauke taba tunda har yau yaki ce mata komai. Sai dai kuma tasan
first love din mutum da wuya ya mance kuma itace nashi. Anan hankalinta ya kwanta. Tana
kishingide tana hawaye sai Fijr ta shigo zatayi mata sallama domin zata shago.
“Anty Shams waya sakaki kuka ki fada min sunar shi na bama uwarshi mamaki”
Murmushi Haske tayi saita share hawayen da sauri tare da gyara zama. “Babu wanda ya
isa yamin komai tunda i have the best sister”
“Okay gaya min meke damun ki?”
Tunani Haske ta somayi tanaso ta fada mata ciwon so yake dawainiya da ita amma kuma
sai ta fasa. Kafin tayi looking very irresponsible. Kakalo murmushi tayi saita soma magana,
“Kaina ke ciwo… Har kin shirya zaki tafi ne?” ta kuma canza maganar nan
“Eh Anty Sallama nazo maki”
“Allah ya kiyaye hanya ya bada sa’a”
“Amin Anty Allah ya baki sauki… Ki sha magani please”
“Toh nagode”
Bayan Fijr ta tafi saita dauki alwashin idan yazo zata jashi da hira sosai ta nuna mashi ana
tare. Ya kamata yasan cewa yanzu tana yayinshi. Lantana tace ta yanyanka su kabeji, karas
meatballs da kuma coconut drink wanda yasha madara.
Bayan an gama komai wanda duka Lantana tayi ita kawai tana nuna abinda za ayi ne.
Bayi taje tayi wanka saita canza kaya. Riga da skirt tasa dinkin peplum. Sai tayi daurin ture
Kaga tsiya. Wajen kwalliya kam tasa foundation, prima, eyeliner da kuma jambaki red. Ta
dade batayi kwalliya haka ba tun sanda take gidan Bilal.
Tana zaune sai taji karar mota, duk tunaninta Haisam ne harta soma murmushi. Dataga
Bilal ya fito bazata ce bataji dadi ba amma ba haka taso ba. Kuma yanzu tana tsoron kada
Haisam yazo yayi misunderstanding komai yasha suna soyayya da Bilal ne yace bai santa.
Ta lura Bilal enemy of progress ne, baya santa kuma bayaso wani ya sota.
Lantana taje domin ta taya shi da kayan shi. A falo ta ajiye sai taje domin ta gaya ma
Haske. A lokacin har Haske ta saka mayafi tana shirin fita. Umurtan Lantana tayi akan ta
dauki Ajwad domin ta kai mashi.
Tana zuwa falon Bilal ya ganta, anan wani sabon santa ya fara mashi sintiri. Tayi kyau
sosai HASKEN LANTARKI, farar mace bakya laifi, farar mace alkyaban mata farar mace
zinariya. Dakewa yayi kafin ta gane yana kallonta amma gaskiya ta burge shi ba kadan ba.
Sallama tayi saita zauna gefe bata kalle fuskansa ba, Lantana ta mika mashi Ajwad saita
tafi domin ta kawo mashi ruwa.
“Ina wuni?” Haske tace a sanyaye. Itama taga ya burgeta. Yayi kyau kuma ya soma kiba
kadan. Sai dai tasan shedan yake mata gizo, saboda ta fara san Haisam yayi confusing
dinta ta kuma soma yabawa da Bilal.
“Lafiya lau, yasu Daddy?”
“Lafiya” daga nan babu wanda yace komai. Ita tana wasa da yatsunta wanda haka takeyi
idan she’s not comfortable. Shi kuma yana wasa da Ajwad. Sun shafe minti talatin suna
zaune. Kallon Bilal tayi yana kara burgeta yadda yake wasa da danshi abin yayi mata kyau.
A wannan lokacin ta birkice sosai batasan wane zata zaba ba tsakanin shi ko Haisam tunda
duka sunada halin da take so a wajen namji. Karar Gate taji inda gabanta ya soma fadi. Fata
takeyi kada ya zamanto Haisam ne.
Addu’a takeyi sosai amma kaddara ta riga fata, Haisam ne ya shigo da kaya ninki ninki
shima na yara, bai lura da Bilal ba saida yama shiga cikin falon sosai. Anan ya murtuke
fuska tamau.
“Meya keyi cikin nan gidan?”
Da sauri Haske ta mike tsaye ta soma magana cikin rawar baki. “Please karka ji haushi,
yazo ganin yaronsa ne”
“waje bai ishe shiba sai ya shigo har falo”
taba rabuwa ba gwara tun
“Bai isheni ba, ni da Shamsiyya have a connection. Bazar
wuri ka sani” Bilal yace saiya ajiye Ajwad ya mike tsaye shima aga tsawon sa.
“Na shiga uku! Dan Allah kar ku yi fada” Haske tace
“Ni banda matsala, ki gayama Ex husband ya gane matsayinsa… Ajwad kawai yakeda
alaka dashi banda ke.. dan ya gane kowa zai huta”
“Atleast ni Ex husband dinta ne! Ina ruwan ka da abinda ke tsakanin mu? Ko kana Santa
ne?? sai ya soma dariya na mugunta.
“Ohhh dama santa kakeyi shine kake mazurai.. Toh batasan kanayi ba bari kaji”
2:23 PMAOO
l. 40
“Ina ruwanka da ko ina santa? Ba matarka bace yanzu! And she’s my sister i need to
protect her from fools like you” Haisam yace cikin bacin rai. Baiji dadin yadda Bilal ya gane
har yanzu yana san Haske ba.
“Na yarda am a fool, a haka na kwace ta da farko kuma i will do it again… Shamsiyya ni
take so kuma nine na dace da ita… Tafi karfin ka yaro wannan goron sai magogin karfe”
Bilal yace yana dariya.
“Let’s see yanzu ai, muga wanda shamsiyya zata zaba, you’re so confident saboda
kunada yaro zata ce zata sake zama dakai.. Zaka sha mamaki because she already knows
you’re a pathetic loser”
Nufansa Bilal yayi cikin zafin nama sai Shamsiyya ta shiga tsakanin su, kuka ta soma yi
tare da harde hannunta biyu alamar roko.
“Dan Allah kar kuyi fada, Haba sai kace yara you can’t handle your differences maturely”
“Kice mashi ya fita harkan ki, Ajwad yakeda alaka da shi bake ba. Idan ina raye bazaki
taba komawa wajen saba”
Bilal ne ya kalleta saiya sauke hannunsa wanda yaso kaima Haisam naushi dashi, kwafa
yayi saiya soma magana, “May the best man wi… Don’t be too hard on yourself idan ka
sake losing, nasan idan ka koma US zamu dade bamu sake ganin ka ba”
Ya tafi yana dariya, yanzu zai soma neman auren Haske gadan gadan, badan Haisam
kawai ba sabida yanaso Ajwad ya tashi tare da iyayen sa gida daya. Sannan kuma ya nuna
ma Haisam ba’a neman mace dashi. Shine Badman Bilal yaro da kudi abokin tafiyar
manya, kura da kallabin kitsi aganshi a kyale shi.
Shi kam Haisam naushin iska yayi yana fitar da iska mai zafi ta hanci. A hankali yaso ya
nuna ma Haske yana santa amma Bilal ya kawo mashi cikas. bazai bari ya sake losing dinta
a karo na biyu ba. Hanyar Gate ya nufa yanaso yace ma Mallam Adamu kada ya bari Bilal ya
sake shigowa cikin gidan. Ita kuma kujera taje ta zauna tana kuka, hannu biyua kumatu
hawaye masu dumi suna gangaro mata, kirjinta duka uku uku yakeyi duk ilahirin jikinta
yayi sanyi, tausayin kanta ta somayi, komai ya hargitse mata. Yanzu wa zata zaba tsakanin
Haisam da Bilal?
Assalamu alaikum, ban hakuri ga wanda suka bude Wattpad da niyyar karatu sai sukaga
hoto, lol. Please a yafe ma Ainakatiti especially Mommy kiyi hakuri please. Yanzu ki dauko
lacasera da kika mayar fridge nasan ya sake sanyi, ki shimfida sallayanki domin Kisha
karatu, I promise you this episode is worth the wait. Wannan shafin naki ne kyauta
Mommyna Allah yabar mana ke cikin koshin lafiya yadda zakiga jikokin ki, Amin.
#AshaLacasera
Napep ta hau inda ya kaita har kofan gidansu Haske, dari biyu ne kudin ya bata canjin dari
takwas. Aka ta aza akwatin sai ta wuce cikin gida. Ta karamin gate tabi, “Sannu” tace ma
Mallam Adamu yayinda take tafiya. Ya ganeta yasa bai tareta ba.
A varenda ta hadu da Lantana, fuska a yatsine ta soma magana cikin gadara tana hura
hanci. “Shamsiyya tana ciki?”
Saida Lantana tayi mata kallo sosai tukun ta gane wacece ita, a ladabce ta amsa duk da ta
girme Laila tazo ko sallama babu balle gaisuwa.
“Eh suna daga ciki, bari na gaya mata kinzo”
“Karki damu nasan hanya” saita tafi tana karkada jiki, Lantana taso tace mata ta tsaya an
canza daki amma Laila ta wuce kamar gidan gadon su. Dataje dakin Haske taga wayam,
saita fito tana kwala kira.
“Yama sunar ki! Mai aiki!!! Ke kalle ina magana!! Heyyyy!”
Tace a tsawace, ta soma ayyanawa a ranta idan zatayi zaman gidan bazata bari mai aiki ta
rainata ba. Bata cikin sakarkarun mata masu hira da mai aiki, mai aiki tana mata ubanta
zataci. Saboda ita bata dauke su a bakin komai ba, babu abinda ya shalle ta duk gidan
dataje idan akwai masu aiki ta rinka kyaran su kenan tana masu tsilla tsilla da kicipi.
Dama scolar na Ajwad da Hafsee takeyi, bata kula Laila ba ta cigaba da aikin ta kamar
bataji ba. Abin yayi ma Laila ciwo inda ta sake jin haushi sosai. Harzuka tayi ta soma masifa
“Banisan rashin mutunci fah, ina maki magana kin share ni halan bakisan koni wacece ba”
Ita Haske tana daki tana kwance, kuka takeyi kamar idanta zai tsiyaya. Sai taji kamar
muryan Laila, a’uzu tayi saboda tasan ba daidai bane, ko a mafarki Laila bazatayi gigin
zuwa ba saidai idan tana ciwon hauka. Kasa kunne tayi ta sake ji wannan fah Laila ne.
Da sauri ta tashi ta mike tsaye ta fita, sai taga Laila tana zuba masifa. “Lafiya me akayi maki
halan?” tace fuska babu yabo babu fallasa. Juyawa Laila tayi taga Haske, saita soma
murmushi.
“Yauwa Besty dama ke nake nema”
Tas’ taji saukan mari wanda Haske tayi mata, ta dago kenan saita sake sharara mata wani.
Laila ta razana batayi zaton Haske zata iya marinta ba, bude baki tayi zatayi magana sai
Haske ta dakatar da ita.
“Firstly, am not your besty. Karki kara kirana da sunan nan. Secondly, meye kika zo yi?
You’re not done ruining my life ne ko za ki cigaba? Kin cuce ni Laila Allah ya isa” saita soma
hawaye. Rawar baki Laila tayi dukjikinta yayi sanyi, amma Kuma ta dake.
“Eh duk abinda kike zargina dashi nayi maki, kuma am sorry, I truly am. Duk duniya banida
tamkar ki, kamar sister dina kike, munyi kuka tare kuma munyi dariya, daki daya muka
kwanta babu wanda yasanni kamar ki kuma kema haka, kiyiwa darajan iyayenki ki yafe
min, dan adam tara yake ba goma ba, i know am not perfect so are you, in sha Allah bazan
sake wani abu to hurt you ba, nagane kure na yanzu give our friendship another chance,
koh Allah daya halicce mu idan mukayi mashi laifi yana yafewa balle dan adam, please
shamsiyya…Nima Saif ya sakeni” saita fashe da kuka.
Jikin Haske yayi mugun sanyi, she could feel the pain a muryan Laila, koma menene kana
ganinta kasan duniya ya koya mata darasi. Taji tausayinta ainun ranta yana mata wani iri,
bata ce komai ba tana dai kallonta. Sannan tayi dana sanin marinta, ba’a solving matsala
da violence ba dabi’a bane mai kyau, wannan zafin da takeyi kwana biyu ta rasa inda ta
samo dabi’an, wata rana saurin hannunta zai kaita ya baro. Laila ce ta share hawayenta ta
soma magana
“Dama nasan da wuya ki yafe min, but please banida masauki”
“Toh ina ruwana?” tace tana basarwa, amma har ta yafe mata tunda ita batada matsala,
once ka gane kuskuren ka komai ya wuce a wajen ta.
“Akwai ruwan ki babba ma kuwa, masauki zaki bani za’a ramawa kura aniyarta ne yanzu”
Saita soma ya tsine fuska, tunani Haske tayi sosai. Tasan cewa idan ba matsala babba bane
Laila bazata zoba, koda yake ta kuma bata hakuri kuma tace bazata sake ba. Kuma gaskiya
ne Allah yana san masu yafiya. Ita bazata lya rike ta a rai sosai ba.
“Muje” tace sai ta juya inda Laila ta bita a baya, wani daki daban taga sun shiga. Abin yayi
mata kyau sosai Italian bed ke ciki, ga labule masu kyau sannan kapet mai laushi yayima
kafarta maraba da zuwa, nan take Laila taji babu dadi ranta yayi mugun baci, wai jibe dakin
da Haske ke zawarci a ciki. Wannan ai vacation ne ba ukuba ba, gaskiya bazai yiwu ba da
sake wai an bama mai kaza kai.
5
Zama tayi akan gado ta hakince, kallon wajen take sosai inda zata zauna, ‘not bad’ ta
ayyana a ranta. Haske taje kitchen ta zuba mata abincin datama Haisam, anan Laila ta
zauna taci san ranta ga kaji a gefe, nan take ta shanye kwalin five alive. Sai tayi mugun
gyatsa ‘Gaaaa’ kamar awaki sannan tayi mirsisi.
Ajwad ne yayi firgice yayi kara kadan saiya cigaba da barci, Laila bata cema Haske ta sauka
lafilya ba, bale tace ina yaron. Haske dai na daga gefe tana danna waya. Bayan taci tayi nat
sai tace zatayi wanka. Haka ta shiga bayin ta batar da mintuna kusan arba’in dan harda
kanin wanka tayi duka. Tawul din Haske da aka rataya ciki pink mai laushin gaske ta daura
abinta.
Kai tsaye wajen mirror taje domin tayi shafa, babu abinda bata shafaba tana budewa.
Murna takeyi sosai tazo gidan daula, sakin da Saif yayi mata kamar ya biya mata Makka ne,
gaba ya kaita wai gobarar titi. Yanzu zata fara zawarci ta samu kuma mai kudi a layin ta
aura, wani abu ya fado mata baga Daddy Zailani ba cikin sauki tunda yanada tsufa mai
kyau, zatayi seducing dinsa har ya aureta. Tunda batasan zaiyi aure ba, sai taci uban Haske
da Fijr da kyau, harta Ammi ta kawo mata wargi tacin mata uwa.
“Queen Laila”
Tace tana kallon kanta a mirror.
Yanzu Fijr bata dadewa, wajen la’asar take rufe shago ta koma gidan saboda Haske tana
zaman kadaici. Balle uwa uba Mommy tana wajen Mum Haisam taje dubata yau bata jeba.
Tayima mutane uku make up, sannan ta saida kayan kwalliya na kusan 10k sai tayi tutorialsta saka a YouTube saita tashi.
Bata koma gida ba saita tafi Tudun wada, wani shagon nama mai suna Taraba taje domin
ta siya, bakinta yana mata galmi galmi kuma tunda tanada kudinta saita siya. Tun a Napep
kamshi ya isheta ta bude tana ci, Hafsee ma ana mamula, ga farm fresh gefe suna basga.
Tayi ma mai Napep tayi yace baiso, anan tace idan sukaje gida zata shiga ta dauko leda ta
zuba mashi hakkin ido.
Koda suka isa bata san Laila na ciki ba, kamar yadda tace haka ta saka mashi a leda ta
bashi, addu’a yayi mata ya karba ya tafi harda yin mata ragin naira hamsin. Yana cikin masu
Napep da basuyi kusan dambe ba sun zagi iyayen juna.
Hankali kwance ta wuce dakinta ta ajiye jakarta da kayan pampers din Hafsee, dama ita
Hafsee tana ganin Lantana ta makale mata. Ta dauki ledan naman Haske zata kai mata, sai
taji dariya yana tashi, duk zatonta Yasmin ne tazo tunda ta kwan biyu bata jeba.
Murda murfin kofar tayi saita yayee labule, Haske tagani ta wangale baki ana kwankwatsa
dariya da Laila. Anan take ta soma tsuma, ita kuma Laila gabanta ya yanke ras ya fadi.
“Jar uba! Uban me kika zo yi nan gidan?” tace tareda nuna ta
“No sis, its cool. Ta bani hakuri wallahi” tace tana murmushi
“And you believed her! Are you stupid? Kin mance duk abinda tayi maki ne? Haba Anty
Shamsiyya meyasa bakya amfani da hankali? You’re the dumbest dumb person da Allah ya
bani ikon haduwa dashi” tace cikin bacin rai.
“Ai hankalin kenan Fijr be nice, ka saka sharri da alheri ladan mu yana sama, ba komai ake
hayaniya ba kamar barbarians”
“Toh ta baki hakuri me takeyi har yanzu bata tafi ba? Meye take zaune saita hure maki
kunne kuma dan tsab almuran chan bazata chanza haliba”
Hannun Fijr ta rike tana murzawa, murmushi takeyi irin na trust me nasan abinda nakeyi
saita soma magana kadan kadan
“Ermmm. Batada wajen zuwa ne, kinsan ta taimakeni da shine nima zan mata, its
temporary… Tana gane harkan komai zata tafi”
“Kutumar uban chan…wallahi bazan zauna gida daya da munafaka ba, koni ko ita cikin
gidan nan. Amma bazan hada inuwa daya da ita ba…kafin na kwasa mugun hali na bani
na lalace Allah ya kiyaye”
Haske ranta ya soma baci, meye Fijr keyi haka! Ita da akama laifi ta yafe balle ita. Ina
ruwanta? bata san rashin muhalli bala’i ne. Ka rasa tudun dafawa masifa ne. Duk wanda ya
taimakawa wani Allah zai taimaka mashi, duniyar kwara nawa ne? Ba dauwamanme bane,
lahira take nema tana so ta cika da kyau da imani. Duk wani abin lada kuma tana kan gaba
ko zata dace gobe kiyama.
“Fijr bansan rashin kunya, nace ya isa haka” Haske tace fuska babu wasa. Harara Fijr ta
banka mata sai tayi fatali da kallabin ta. Super ta soma tana tsuma masifa ya fara cinta,
“Maraba gasarshe, dama nace maki idan muka hadu zan baki mamaki… Sai nayi maki
tsirara nayi maki lagalaga” tace tana kallon Laila.
Da sauri Haske ta sha gabanta domin ta kare Laila, ita kuma har ta soma guntun hawaye
saboda tsoro. Tana dai fatan Haske ta taimaka mata kafin ta yabawa aya zaki.
“Fijr idan zaki daketa dole ki soma dukana, tunda yanzu kin daina ganin girma na”
“Anty koki matsa min nayi abinda nayi niyya, kokuma na mance an maki operation nayi
maki lagalaga kema, sannan kuma na koma na dake shegiyar chan”
Gaban Haske ya soma faduwa data lura Fijr da gaske takeyi, anan itama ta soma ja da gefe
domin ta bata waje. Fijr baji ba gani ta soma masifa da karfin gaske. A Saman muryanta
take magana tana jijiga duk wani sansa na jikinta.
“Wallahi yau tsakanin nida ke ne, banki kema ki rama dukan ba, kada Allah ya raga ma
wanda ya raga ma wani cikin mu… Dama nace sai naci bankin ubanki, kuma yau kin kawo
kanki wajena… Sai nayi maki tsirara na yayyaga ki, lagalaga zan maki wallahi karyan
iskanci kike yi.. Cikina shida a waje ga kuma yarinya, ni nayi ribar bariki.. Ke baki iyaba”
Wani Liver yazo ma Laila, ta tuna dazu tabi Sameera da gudu da kwalba ita da takeda yara
balle wannan karuwan, da gadara ta fara masifa ita ma
“Kina tunanin ina tsoronki ne zaki rinka wani hayagaga, Allah yasa wuta ke fitowa a bakin
ki kin tarashi kin samu, shege ka fasa. Wanda ya raga ma wani dan wuta.. Wallahi ubanki
zanci”
Tas’ taji an sharara mata mari wanda ya tsaida maganar da takeyi, saita finkico Laila, anan
ta soma dimarta harda tokarin cikinta. Ita ma Laila ta fara ramawa amma Fijr tafi samun
galaba a kanta. Sake ware idonta tayi ta kalle hannun Fijr dan zata rantse da itace ko rodi
ake dukanta domin zafi, bale tayi bleaching da kaya masu arha fata babu karfi abu kadan
ya yage, jini ya soma kwarara a bakinta an turgude mata hakori sanadiyar naushin data
burma mata a baki.
“Wayyo Shamsiyya ki bata hakuri wallahi yanzu zan tafi” tace tana kuka. Fijr ko jinta batayi
ba ta cigaba da kai mata duka, yanda kasan tana filin boxing Mohammad Ali ya samu Joe
Frazier. Kwalo takeyi da ita sai taka matajiki takeyi kamar tsumma, abin bai ishe ta ba ta
jawota tayita kai mata cizo duk inda ta samu.
Sannan ta kuma cigaba da kai mata duka, an dade ana dukan Laila amma na Fijr daban
yake. Shiganta yakeyi sosai har ruhinta. Kuka takeyi tana kiran Shamsiyya ta taimaka mata.
Charger na laptop din Haske ta janyo tayita zabga mata. Haske ta mike sau biyu amma Fijr
tana dunkule hannu zata auna mata, dole taja da baya tana kallo. Tausayin Laila takeyi
sosai tana tunanin yadda zata kaita asibiti a kwantar da ita. Ita kuma Laila tsabaragen
wahala taji duk wani mugunta akan Haske ya fitan mata kai, bataso ta sake alaka da
Shamsiyya balle tayi gamo da Fijr ta azabtar da ita haka.
Da Haske ta lura Fijr kisa zatayi, saita je ta hau jikin Laila ta kwanta gwara a dakesu tare
amma bazata iya ganinta haka ba. Anan Ajwad ya farka hayaniya ya soma tsandara ihu.
Kota kanshi Haske batabi ba tana kokarin ceton Laila.
“Wallahi saidai ki dakeni amma bazaki kara dukanta ba” tace tana kuka wiwi. Fijr tana
bala’in ganin girman Haske yanzu, kwafa tayi tabar Laila saita ga bakon akwati wanda
tasan na Laila ne. Dauka tayi takai chan bakin Gate tayi fatali dashi titi. Saita dawo lokacin
Ajwad baiyi shiru ba, muryan Haske taji tana mashi ihu, “Kai dalla ka fiye rigima kana ganin
ina kokarin taimaka ma kawata shine zaka fara min tsiya” sai tayi tsaki. Bawai taje wajen
shi bane tana kokarin mika ma Laila riga domin ta saka.
6
Kamar yadda Fijr tayi alkawari tayima Laila tsirara, haihuwar uwa tayi mata babu komai
jikinta. Kayanta na durawa ta mika mata Super wax irin compensation akan wanda Fijr ta
yaga dukda bana kirki bane. Fijr ranta baiso ba yadda taji Haske ta zagi Ajwad.
Shiga dakin tayi ta dauki kwalbar Pepsi ta fasa a bango, “rasss” komai ya fashe. Nuna Laila
tayi dashi kamar zata Luma mata “Zoki fita kona kashe ki”
Da gudu Laila ta fita tana kuka kafin Fijrta kasheta. Har Gate ta bita itama tana gudu tana
sharfa mata zagi. Saita rufe gate ta juya ta tafi “Aikin banza” tace afili. Tana tafe bankam
bankam kamar budurwan kauye, tunani kala kala takeyi yadda Haske take tunani kamar
jaka, wai ace mutum ya kashe maki aure saboda kafi kowa dakikanci sai kuma ka cigaba da
dariya dashi.
Ita bazata lamunta ba, bazata kuma yafe ma kanta ba taga ana yi ba tace komai ba. Babu
abinda ya shafeta koda batasan mutum ba zata taimaka mashi balle a gidansu, idan Haske
taso karta sake mata magana daga yau.
Sai a lokacin jikin Haske ya dawo ta gane Lallai Ajwad kuka yakeyi. Tana gunguni ta dauke
shi tare soma buga mashi baya, still bayi shiru ba saita soma bashi nono, anan yaki sha da
farko yana kuka, daga baya kuma ya karba, yana sha yana cire baki yana kuka. Da kyar ta
samu ya karba sosai, daga nan ya soma lumshe ido. Ita tanaso yayi maza yayi shiru koba
komai tabi sahun Laila, ko kudi ne ta bata suyi tunanin masauki koda gidan Mommy ne
kafin gobe a samu mafita.
Ita Laila zama tayi bakin kofa tanata kuka, gashi batada takalmi. Duk wani ilahirin jikinta
yana mata ciwo,ji take kamar tayi karo da tipa, yau tasan ta daku inda ta jaddada batada
maraba da jaka, kowa dukanta yakeyi. Kuma wani shari’a sai a lahira batayi ma Fijr komai
ba amma take cin zalinta. Ta saba jin Fijr na cewa dukan tashi kasha gishiri, batasan ko
yana maganin ciwo ba amma idan ta samu yanzu zata kwankwada ko zai kawo mata
saukin zafin datake ji.
Jira takeyi taga Haske ta fito amma shiru. Dadin abin canji a zipper din akwati ta saka
tanada dari takwas. Tunanin masauki ta soma amma babu inda zata, batada waya balle ta
kira kowa, abu ya fado mata gwara ta koma gidanta tayi idda anan kamar yadda gwaggo
tace, da raban zata sha duka ne data tafi tuntuni. Tayi nadamar zuwanta sosai kuma ta
tsine ma Haske albarka kala kala fiye da Fijr, sannan tayi mata fatan mugun kaba’i ya aukun
mata.
Tafiya takeyi kanta yana bala’in sara sabida hakori da aka turgudar mata dashi, saida ta
samu zani ta dafe wajen. Ciwo yakeyi sosai kamar ana mata azaba da wuta. Tana tafe tana
kuka harta ga Napep batayi nisa ba. Anan ta shiga ta tafi gidanta, kawai ta dauki alwashi
bazata shiga sabgan kowa ba, harkan gabanta zata soma kuma gobe zata fita aiki. A private
zataje ta nema aikin teaching tunda tayi karatu. Bazata iya zaman sai an bata ba
Sanda Haske ta samu Ajwad yayi shiru saita goya shi, a lokacin Fijr tana bayi tana wanka
tareda tunanin masoyi Ghali. Kusan kullum yanzu saiya fado mata à rai. Haske bin titi tayi
sama da kasa babu alamar Laila, tausayinta yayi dawainiya da ita, matse kwalla tayi
saboda dacin datake ji a ranta. Idan wani abu ya faru da Laila bazata yafe ma Fijr ba.
Al-muslim akhi muslim, Koba komai sabida wannan dabata daketa haka ba. Komawa gida
tayi tana bala’in tausayin ta, saita dauki waya ta kira Saif ko Laila tana gida, toh a lokacin
bata isa ba saboda go slow. Yace mata ai ya saketa amma baice ta tafi ba, ita kuma ta
kwashe kaya tayi gaba bayan tayi mashi diban albarka.
Tsorata Haske ta sakeyi tana ganin kada Laila ta fada hannun mugaye, haushin Fijr takeyi
sosai kamar taje ta shaketa. Kuma idan Daddy ya dawo zata kai kararta wajensa domin ya
hukunta ta. Sannan zata daina sake mata Fuska tunda batada kunya
Koda Laila ta isa kofar gidan tafi mintuna goma tana tunanin me zata ce, da wani irin ido
zata kalle su, dadin abin magrib ne bazasu ga fuskanta sosai ba. Dabara ya fado mata tace
tayi accident ne, sai kuma tayi tunanin duk randa aka daketa abinda take cewa kenan.
Karsu gane karya take, duk yadda tayi racking brain dinta ta kasa samo karya.
Ji tayi ana sinsina mata hannu an soma lasa, a firgice ta matsa tana ihu. Ashe Officer ne ya
ganta tsaye taki tafiya shine yaje wajenta. Kukan awaki ya soma saiya tafi, zaginsa tayi
sosai saita wuce cikin gida kafin ya dawo yace zasu dambata.
Bataga kowa a tsakar gida ba abin yayi mata bala’in dadi, a hankali ta sidada inda Bukola
tana ganinta ta window data mike zata dauki abu. Ita kuma Sameera bayan fitan Laila ta
fito tana haki, Bukola ne ta roketa akan ta fito komai ya lafa. Saita ce karta damu tayi
cefane zatayi masu semolina da miyan kubewa danye.
Haka ta shiga dakinta ta rufe, ta siya kyakya suya da rogo dafarfe a bakin layin su wanda
zatayi dinner dashi. Saif yaga haske yana tashi daga dakin Laila, shine ya tambaya Bukola
yanda akayi, anan ta sheda mashi cewa ai Laila ta dawo amma batayi magana ba. Shima
bai jin magana da ita tunda ta yaga mashi riga kuma ta mare shi.
Da kyar Shamsiyya tayi barci, duk tana tunanin inda Laila take. Harsu Gwaggo ta kira
amma aka ce bata wajen. Da safe ta sake kiran Saif anan ya sanar da ita amma basu hadu
ba. Taji dadi sosai saita kuma yafe ma Fij, sai dai idan komai ya lafa zatayi mata iyaka tasan
matsayinta. Anan tayi ma Saif nasiha da ban baki sannan ta roke shi akan ya mayar da
Laila, anan yace ya maidata. Yaji dadi yanda Haske ta damu da Laila koma komai zasu
soma samun abin mai kyau.
Yana dakin Sameera zaiyi brush sannan suyi kallaci, ya shiga bayi ya dauki brush din kenan
abin ya fada toilet seat, ranshi yayi mugun baci gashi ya gama kanin wanka baiyi flushing
ba balle ya dauka hakanan ya saka gishiri yayi amfani dashi.
Tunani ya fara sosai yadda zai samu kudin da zaiyi brush, gashi har yanzu bai fada ma kowa
ba akan satan, duk zatansu mota yana wajen gyara ne. Fitowa yayi sai yaga Sameera tana
cura doughnut, murmushi yayi har cikin ranshi ya samu abinci.
“Ke Sameera dan ranta min dari biyu na siya brush” yace fuska a murtuke. Hada rai itama
tayi saboda bataga dalilin da zai tambayeta kudi ba. Baya bata nashi kuma bazai karba
nata ba.
“Banda shi”
Kallon hadarin kaji yayi mata sai yayi tsaki ya tafi, dazu fah ya ganta tana dirga damin kudi.
Bayi ya wuce ya dauki sosan wankan sa ya soma gigarawa a bakinsa. “Duk ramar giwa tafi
kwando goma” ya fada a bayyane. Haka ya wanke bakinsa fes har harshen sa, sai yayi
flushing bayin ya fito, ko kallon Sameera baiyi ba itama haka.
Yanzu kudin mota yakeso wanda zai je shagon ruwa ko zai samu ya roke Alhaji Shehu, sai
yace gwara ya tambayi Bukola. Ita kuma ranar kap bata fito ba, tana daki tana murkusu
murkusu cikinta yana mata azaba. Daga bisani kuma taji jini yana gangaro mata ta soma
barin cikin.
Tayi kuka sosai saboda tana bala’in san abinta, tana cikin yanayin ne sai ga Saif ya shigo
maula. Ganin yanayin ta yasa shi firgicewa. Da kyar ta iya bude baki tayi magana, “Please
ka kaini asibiti” gabansa yayi ras baida mota baida kuma kudin amfani. Nokewa ya fara
saiya canza topic din.”My dear meke damun ki”
“ina ganin nayi miscarriage ne, dan Allah ka kaini asibiti”
“Dama kinada ciki ne?”
Bata masa shiba illa hawaye data cigaba tana rufe ido, shikuma yayi bala’in jin dadi saboda
yanzu yanda komai ya chabe baida halin welcoming kowane yaro. Ai da bai bare ba dashi
zai taimaka ya barar mata dashi.
“Dan Allah ka kaini asibiti”
Mikewa yayi yaje dakin Sameera inda ya gaya mata Bukola babu lafiya saiya fita, mai
Napep ya taro domin su shiga. Sameera ta taimaka mata da kaya sannan suka tafi. Wallet
din Bukola ya bude yaga dubu biyar, anan ya kwashe suka tafi dashi. Ita kuma Sameera
tana gida, ita ce ta gyara ma Bukola dakin tsab tayi mata mopping wajen tare da canza
mata zanin gado. Batadai yi wanki ba amma ta saka a bucket.
Laila tana kallon fitansu ta window, “Shegu” tace sai tayi tsaki ta koma uwar daka domin ta
kara barci kafin ta fita neman aiki. Tana cikin barci taji ana Sallama, ranta a baci ta tashi sai
taga ashe Haske ne, wayancewa tayi saita soma murmushi.
“Besty ke ce”
“Wallahi na kasa barci ina tunanin wani mugun abu ya faru dake”
“Uhm uhm nan na dawo straight” saita kalle gefen Haske inda taga zungureren leda. “Meye
wannan?” ta tambaya. Mika mata ledan tayi ta gani, su biredi ne babba na Paladin,
madarar Dano, Bonvita, Sugar St Lious, Top tea da indomie karami rabin katan.
“Nace bari na kawo maki kila zaki bukata”
Har cikin ran Laila taji dadi, Haske ta saba mata alheri amma wannan yana cikin wanda taji
dadi. Dama ta rage rogo zata dumama taci idan ta tashi. Anan tace ma Haske karta damu
zata fita neman aiki, bataso Haske ta raina ta tunda ta yarda ta fita sau dubu.
Haske taji dadi sosai inda tace kada taji tsoron tambayanta kudi idan tana bukata, koda
batada shi nan take zatayi budget da ita. Sun zauna suna hira yayinda Laila tasa ruwa a
heater, ga Ajwad a bayan Haske amma ko kallonsa batayi ba, balle baida rigima na rashin
dalili. Haka ta hada tea mai uban kauri ko tayi batayi ma Haske ba, ita kuma ranta yayi
mugun biyawa. Balle kuma yayi zafi sosai yana gasa mata bakinta dake ciwo.
Yanada kyau mutum yana ma mutane uzuri, sai tayi ma Laila uzuri akan cewa kila tana
zaton ta karya ne. Anan Laila ta soma bugun ruwan cikinta akan Bilal, yana zuwa koko?
Taso ta kwashe komai ta zayyana mata tas sai wani abu ya hanata. Amma idan suka sake
haduwa zata gaya mata yadda yanzu ana fada akanta, koda zata dauki shawarar Laila
yanzu sai tayi dogon nazari ta gane karya da gaskiya, wannan kenan!
Haisam yana kwance dakin Abubakar abin duniya yayi mashi cinkoso, yanaso ya gane
yadda zai magance matsalar sa na Bilal, baya so ya sake rasa Haske for the second time.
Yanzu santa yafi nada baisan ya rayuwar sa zata kasance ba. Yasmin ne ta shigo ciki, tun jiya
daya dawo ko abinci bai fita yaci ba, itace taketa zirya tana kai mashi. Yanzu haka tanaso
taji mai zaici ne sai tayi masu.
Da fara’a ta shiga ciki tana murmushi, fuskanta akwai make-up kuma ta saka kaya masu
kyau, English wears ne riga iya gwiwa sai wando wanda aka yayyanka. Rufe ido yayi saboda
bai san takura. A natse taje dab da gadon ta tsaya, tasan idansa biyu sabida yadda yake
motsa su, kallonsa tayi sanshi yana kara bin duk ilahirin jikinta, magana ta soma cikin
taushi.
“Yaya Haisam ina kwana?” yaso yayi banza amma ya fasa.
“Lafia” yace a dikilce.
“Naga tun jiya sai kwanciya kake halan bakada lafiya ne?”
“Lau nake”
“Toh meke damunka? Naga you look disturbed”
“Nace maki lafiya na lau, bakiji ne” ya fada cikin daga murya. Tsoro taji saboda bata taba
ganin fushinsa ba, koda yaushe yana murmushi koba yawa.
“Please ki fita” yace tare da nuna hanyar kofa. Baisan takura kuma matsalar sa yafi karfin
azo ana mashi chit-chat. Hawaye ya ciko mata idanu, a hankali ya soma fita kadan sai
gudun famfo. Yau itace akema Haka? Zuciyar ta batayi mata adalci ba tunda ita taja mata.
Hanyar kofa tabi kamar yadda ya umurta. Harta murda kofa saita dakata.
“A duniya Yaya me nayi maka da kake min haka?” tace cikin kuka.
“Na ce ki fita karki takura min koh?” yace a tsawace kamar yana magana da baiwarsa.
“Yaya do you think am a fool dan ina sanka? So hauka ne ko rashin galihu? Ace na zubar da
girmana na ‘ya mace amma still bazaka saurara minba! Haba yaya kana tunanin da inada
mafita bazan iya bi ba. Amma this is my only option, zakaga kamar Ina takura maka amma
bakasan yadda zuciyana ke barazanar fashewa idan na nisance ka, kaima kasan soyayya

kuma kasan how painful it is to love and be rejected “magana yana soma cikin nadama
akan abinda yayi.
“Chiquita ba haka bane, kaina ce ciwo” daga mashi hannu tayi ta cigaba da masifa.
“Please don’t Chiquita me! Kullum ka rinka min kirki kana nuna ana tare amma ba haka
yake ba. Kasan ina sanka meyasa kake kuma wasa da hankalina, yau kamin kirki gobe kayi
min ba daidai ba, what gives you the right to treat me like trash Ya Haisam? Nima fah inada
galihu kuma ban rasa masoya ba, zuciyana ta soma sanka ba tare da shawara naba”
“Chiquita I don’t want to hurt you, amma kamar karamar kanwata kike, bansan me nayi da
kikaga ya burge ki ga da namiji ba. Mutum daya nakeso a duniyan nan, ita kadai bazan iya
canzawa ba” ya fada kamar zaiyi kuka domin ya kasa kallon idonta. Ita kuma dariyar
mugunta tayi ta soma share hawayen ta.
“Nasan akan Anty Shamsiyya kake min haka, but for heaven sake yaya bazawara ce fah,
sauran wani ce. Ka barta ta koma wajen Ya Bilal mana… Please yaya I promise to make you
happy!”
“Yasmin yau ya zama rana ta karshe da zaki kirata saura.. Kika sake disrespecting dinta
ranki zai baci” yace fuskansa babu wasa.
“Kagama hauka akan Anty, zatayi dumping dinka kamar yadda tayi da farko.. The power of
first love, bazata taba zaban kaba…Kayi ka gama ina jiranka Sweetheart, am very patient”
tace tana dariya saita tafi.
Tunani ya soma kada abinda tace gaskiya ne, Shamsiyya ta kyale shi ta koma wajen Bilal.
Besides akan wani dalili zata zabe shi bayan tanada yaro da Bilal. Idan kuma yace tabar
uban yaronta is not a reasonable thing to ask. Amma abinda ya sani zai so Ajwad sona
hakika kamar shiya haife shi, yadda ba zaiyi missing ubansa ba. Sabida haka yana nan akan
batun neman auren Haske. This is his second chance at love, kuma bazai bari damar ta
kubutar mashi ba.
Ita kuma Yasmin dabara ya fado mata taje ta gayama Mommyn ta dana Haisam lallai tana
sanshi koba komai sai ayi masu aure. Idan tana raye saita kwace shi a wajen Haske, she’s
optimistic nan gaba shima zai gane tana mashi sona hakika. Kuma shima zai fara mata,
tasan zai dauki lokaci amma it’s a sacrifice she’s willing to make. Wannan kenan!

Advertisements

_____

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

HASKE CHAPTER 24

Advertisements _____ HASKE CHAPTER 24 Hakuri shine gishirin zaman duniya amma ga Fijr kuwa barkono …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *