[Advertisements⬇️]

HASKE CHAPTER 25 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HASKECHAPTER 25

Sati daya cip Saif yayi a dakin Bukola bayan nan ya koma yana raba masu kwana daya
daya kamar yanda yakeyi tun asali. Koda yake ana raba dare ana jinya, wajen sha biyu Laila
zata soma ciwon karya tayita kurma ihu tana jefa duk abinda ta gani wai rafanai gareta
dole ayi jinyarta ana mata rukiya. Ita fa wai kada Saif ya kasance kusa da matarsa.
2
Dayake ya fita iya shege banza yake da ita kuma ya hana Bukola fita. Sameera ne take
zuwa duba ta, itama takaici ya ishe ta sabida an hanata barci. Ranar karshen amarcin sa,
tun bayan Isha yake rike da ita. Jira yake ta soma suyi fito na fito, haushi ya turnuke shi
sosai sai mazurai yakeyi, tana fara ihu ya zura takalmi yaje. A lokacin har Sameera ta soma
bude kofa, a hanya suka hadu inda yayi mata alama da hannu akan ta koma. Laila na
ganinsa ta rinka fizge fizge na karya tana zare ido.
“Sannu koh”
Yace tareda binta da kallon wulakanci sai ya wuce Kitchen, duk zaton ta zai dauko ruwa ne
ya bata. Harta soma gyara rigar ta domin jikinta ya bayyana wani sansa na kirjinta daga nan
ya kalle ta zai mance da Bukola. Fitowa yayi da muciya. Anan ya soma auna mata. ‘Qum
qum qum’ karar da kake ji yana tashi.
“Zaku fita ko bazaku fita ba”
Banda ihu bata komai, shikam bai fasa auna mata ba. Dataga babu sarki sai Allah kuma
bashida imani. Sai ta soma magana.
“Wallahi zamu fita, dan Allah kayi hakuri… Zamu fita ta hanci…Kaji tausayin mu yanzu
zamu tafi”
4
“Ai babu kalmar tausayi tsakanina daku, yau saina rama duk abinda kuke min…” sai ya
cigaba da kai mata duka da muciya. Hawaye takeyi sharbe sharbe dukta galabaita gashi ya
danne ta babu alamar gudu. Sameera na daga daki tana

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

jin ihu, ita ma Bukola tunda take

batada ganin yadda abin yake ba sai gidan Saif. Addu’a kawai ta rinka yi tana jiran ya dawo.
“Sun fita, ni ce yanzu! Wallahi Laila ne babu aljani ko daya ajikina ka kyale ni dan Allah”
“Dan Allah ka daina dukana haka Wallahi sunana Laila Mohammad”
Lagalaga yayi mata jini da majina dakyar take numfashi saiya wurgar da muciyar kasa ya
fice ko magana baiyi mata ba. Anan tayita numfashi sama sama tana kuka har barci ya
dauketa. Shi kam tunanin rashin mata haka da baiyi ba tun farko yakeyi, Yar iska kawai’ ya
fada cikin ransa.
Sanda Bukola zata koma aiki ranar farko saita bama Laila Danmukulli domin ta ajiye
mata. Aikam bayan tafiyar ta Laila ta bude ta shiga ta bincike mata shi tas. Bukola irin
mutanen nanne masu gane idan an taba masu abu. Tasan yadda take ajiye kayanta kuma
kana matsarwa zata gane.
Laila bata dauki wani abu ba banda tsame nama datayi daga tukunya na kaza da ganda.
Sai kuma tadan zazzaga madara a Leda kafin ta fita taje dakinta ta hada shayi mai uban
kauri wanda ta mance yaushe rabon data sha.
Bayan ta fita daga dakin ne ta tuna bata dauki lipton ba, dama tanada raguwar siga.
Wajen Sameera taje domin ta tsammata. Anan ta bata guda biyar. Yanzu babu abinda ya
sha mata kai halinta na roko har wajen Sameera. Tunda yanzu babu kawance da Haske
balle ta rufa mata asiri, wata sa in tana missing dinta. Yau itace rokon Maggi, kayan miya
wata sa’in har kudi.
Dari takwas dinda ta dauka Sameera tana ankare kawai tayi mata kawaici ne amma abin
yayi mata ciwo. Wajen cin awara da gyada ta karar da kudin, sai kwalban kalanzir data siya
dashi. Da Bukola taga yadda akayi mata ta’annati abin bai mata dadi ba, kashe gari sai
tabama Sameera mukulli. Aikam Laila ta shaka sosai inda ta rinka jefinta da habaici.
Kananan maganganu take watsawa kala kala idan ta ganta.
“Yarbawa masu kwalo kwalo, da duwawu suke tuka tuwo” shine wakar datake yawan yi
idan tana tsakar gida. Ko ajikin Bukola saboda tafi Laila hauka, abinda Laila keyi jahilci ne.
Amma tana rokon Allah ya rabasu saboda idan ta kama Laila bazata mata da kyau ba. Sai
dai cikin ruwan sanyi zata rama.
A kwana a tashi babu wuya wajan Allah, suna zaune gidan dai su uku. Wata rana Bukola
tayi sakwara da miyan agushi. Dangin karfi tako kirba shi yayi laushi sosai. Sai ta saka a
cooler biyu domin ta bama Laila da Sameera.
“Abul Khair dan Allah zo na aike ka” Bukola tace mashi, wasan shi ya cigaba kofan daki ko
kulata baiyi ba. Sameera ta fito famfon waje domin diban ruwa. Kunya ya kamata sosai
saita kalle shi ko baiji bane.
“Abul Khair kazo mana” Ta maimaita.
“Abul Khair bada kai akeyi ba?” Sameera tace cikin tsawa. Karkabe hannunsa yayi saiya
mike, kallon Sameera yayi sai ya soma magana.
“Anty ne tace na daina ma Anty Amarya magana, koda ta aike ni naki zuwa wai mayya ce
zata kashe ni”
“Waye Anty?” Sameera ta tambaya a razane.
“Anty Laila”
“Ikon Allah” Bukola tace.
Jan hannun Abul Sameera tayi suka nufa dakin Laila, buga kofa sukayi tana jiranta. Bukola
na daga bakin kofa tana kallon su. Fuska a yatsine ta fito tana harara.
“Lafia?” tace
“Dan Allah ban haifar maki yaro akan kiyi mashi tarbiya ba! Ya zaki ce masa karya amsa
aiken Bukola mayya ce? Wannan wani irin abu ne?”
“Toh aiba karya nayi ba, mayya ce”
“Wannan matsalar ki da ita ce, ki daina hada min yarana cikin kishin ki, na dai gaya maki
banso gwara ki bari”
“Idan ban bari ba kiyi kutumar uban da zakayi Sameera, kinyi asara in dai zaki hada kai
da bayarrabiya..Jibe ma yaranki munana masu sifan yan wuta, ai gwara bari da
haihuwan su” saita doka tsaki.
Kallon ta Sameera tayi cikin mamaki, “Idan fitsari banza ne Kaza ma tayi mana, idan
haihuwa banza ne ke kiyi mana inace kina da miji kuma mace kike”
ita kuma Bukola ta karasa wajen cikin fushi. “Meye haka Laila meyasa zaki zage ta? Daga
tace ki daina hada yaranta cikin haukan ki sai zagi”
“Kehhhhh! kwalo kwalo banyi dake ba, gwara ki tafi kamin na hada dake duka naci
ubanku. Wallahi bana raga ma kishiya cin ubanta nakeyi saina ga ajalin ta.. Ehe” Ta fada a
tsawace
Sameera butulcin Laila take kallo amma ta kyale ta, janye Abul khair tayi suka tafi. Bukola
ji tayi kamar ta koda mata mari amma kuma zai kaisu ga dambe kuma raini zai shiga
tsakani. Da kanta ta kaima Sameera sakwara ta fasa bama Laila. Kuma taga Laila bata wani
sana’a namanta yafi yawa. Ita ta cinye abinta tana lashe baki.
Daren bayan Saif ya dawo ya gama cin abinci yana sambatu, sai yace yanzu gaskiya bazai
iya daukar nauyin su uku ba. Ita datake amarya zai iya lura da ita, Laila da Sameera su
kama sana’a. Da sauri ta chapke tace banda Sameera tasan gashin kanta ya kamata a daina
sangartar da Laila. Yasa taki fita ta nemo nata. Su a yaren su mace har dako tanayi domin ta
samu kudi. Kawai yanzu Laila ne za’a daina ciyar da ita har sai tayi hankali. Ai yayi mata
kokari ya bata muhalli, kuma yana biyan kudin wuta dana ruwa. Sannan kuma idan tana
3
ciwo yana kaita asibiti amma maganar abinci ya dauke.
Yayi na’am da shawara sabida dama baisan ciyar da Laila, batada godiyan Allah ga korafi.
Sameera ko saboda yaransa zai yi haka. Sai ya tara su a dakin Bukola, falonta babba ne
dan yafi duka nasu. Gashi set din kujerar ta manya ne leather seat sky blue, labule ma blue
da ratsin gold. Sannan tiles gareta sai rug mai laushin gaske. Daga chan kurya kuma
dinning table ne mai takwas.
Abin yayi ma Saif dadi sosai saboda banda gidan mutane bai taba ta’ammali da shi ba,
yasa yanzu baya cin abinci akan kujera sai dai yayi kerere akan dinning. Balle ita Bukola
bata cin abinci da cokali sai mai yatsu. Shima yanzu ya koya sanabe duk da baya so amma
komai nata burge shi yakeyi. Balle aurenta yasa ya samu inda yake masu dealer na ruwa
babban shago. Abin yayi mashi armashi kuma yana da tabbacin ya kusan zama Dangoten
(2
Rigasa.
Duk sun taru sun zauna, yana kan 3 seater yace ma Bukola ta zauna gefen sa tunda ita ce
amarya, ita taso Sameera ta zauna amma yaki. Laila riga vest ke jikinta da wani wando
1
leggings duk ya soma gashi. Dayake taga Bukola na san saka irin kayan.
Tana taunan chewing-gum kas kas kas babu abinda ya shafeta, sai ya soma magana.
“Yanzu akwai sabon gyara dana kawo cikin gidana, mai so ya zauna wanda baiso Umma
ta gaida Aisha” babu wanda ya gane zancen sai Bukola.
“Ina nufin kowa yanzu zata soma ciyar da kanta, banda amarya”
“Ai mun saba” Sameera tace cikin ranta tasha wani abin daban ne. Laila ne ta ware ido ta
soma masifa. “Banga neba ? Sai kace yarbawa” sai ta watsa ma Bukola harara.
“Ai mutane ne kuma ba laifi bane dan kin taimaka ma mijinki” Bukola tace tana
murmushi. Laila ta makale murya ta soma karairaya.
“Haba Destiny, karka yi haka kamar ba cikarken bakano ba. Haba wannan ai ba girma
bane”
“Dalla rufe min baki! Girma! Naga dutsen dala ban tsorata ba. Daga yau bazan bada kudin
cefane ba, musamman ke Laila bazan baki ko sisi ba. Dama dama Sameera zan rinka bata
wani abu saboda yaranta amma ke kinki haihuwa ko amai na karya ban taba ganin kinyi
ba. Yasa zan daina”
Idonta ya raina fata, saita saukar da murya. “Haba Destiny yanzu ina zanje na samu
abinci? Bin maza kake so nayi?”
“Ai ba yau kike fara ba”
Saiya juya gefen Bukola ya soma bata labarin yadda tabi maza kafin auren su. Bukola harda kukan karya tana jan majina.
“Anty Laila baki kyauta mashi ba, dan Allah ke daina bin maza haka ki hakura da namiji
daya, ashawo ba sana’a bane mai kyau kina musulma… Kai ma Sweetheart bai kamata ka
fada mana ba daka rufa mata asiri “
“Ai ba karya nayi mata ba a gabanta na fada yasa kukaga ina dukanta kamar ganga” yace
cikin takaici. Anan kunya ya kama Laila tayi shiru ta sinna kai. Duk bakin rashin kunyarta ya
mutu murus. Daga bisani murya kasa kasa tace, “Zaka bani kudi da zan fara sana’a?” bai
tanka ba saiya soma canza Channel. Dama Bukola tazo da plasma babba an makala a
bango.
“Saifullahi dan Allah ka rufa min asiri kafin ka jawo min raini wajen kishiyoyi na” tace
tana kuka. Bukola tana dariya ta soma magana, “Haba ai kinada kwanan abinci wajena
kafin ki samu abin yi” Daga nan ta mike ta dauko purse dinta, dubu biyu ta bata “Ga
wannan ance kina gullisuwa da, yanzu sai ki soma kina rufa ma kan ki asiri.. Amma rance
(1
ne zaki biyani'” tace cikin raha. Sameera dai bataga amfanin zuwanta meeting dinba.
Bayan kwana biyu Laila tana barci Bukola tazo ta buga mata kofa, da magagi ta karasa
wajen tana hamma. Bakin durum na ruwa Bukola ta nuna mata.
“Anty Laila dama ruwa zaki debo min ki cika min durum dincan zanyi amfani dashi
anjima” kallon durum din Laila tayi sa ta kalle Bukola, bata gane zancen ba.
“Ni zan debo maki ruwa?”
Marairaicewa tayi tana juya jiki, “Toh Anty Laila inace kin yarda zan baki abinci? Ai dole ki
tayani da aiki.. Please kiyi sauri kafin su dauke ruwan” sai ta tafi ko sake kallonta batayi
ba. Takaici ya cika Laila ta koma daki.
Gashi batada wani kudi a hannun ta duka jarin tayi tuwan madara da gullisuwa. Yanzu
kuma idan taki Bukola zata iya mata bariki taki bata abinci. Bata tashi ba sai bayan minti
talatin wai ita siyasa. Aikam bayan ta gama jida tana haki taje dakin Bukola, ranar Saif yana
wajen Sameera.
“Bukola na gama fah” ta fada cikin gadara. Bukola tana kwalliya zata aiki tayi banza da
ita. Laila na waje tana jira, saiga Bukola tazo fuska a murtuke zata fita. Rufa dakinta tayi
tasa makulli, saita kaima Sameera Key.
“Anty Laila Dan Allah idan na saki abu ki rinka yinshi nan take kuma cikin dadin rai..
Fisabililahi nace ki deban min ruwa kina ta kumbure kumbure bakya murmushi, idan ba
2
zaki yi ba sai saiki gaya min… Gaskiya Anty ki canza”
Saita tafi tana dariya cikin ranta, da karan bana ake maganin zomon bana, Laila kam jira
take a bata abinci amma bata gani ba. Ga cikinta yana neman hadewa da bayanta. Haka ta
koma dakinta rai a baci ta soma lasan tuwan madara… Wannan kenan!
***
Tun shigan satin take jin ciwon jiki, kuma yazo daidai da satin haihuwarta. Dama ta dauki
maternity leave a wajen aiki yanzu tana gida. Haryanzu dai babu zancen kirki tsakanin ta
Bad. Sau daya yaje gidan kuma yakai mata kayan Baby ne. Shima da kyar ya iya cewa ya
jikinta wani rana zata haihu.
Har yanzu bata fasa mashi text na ban hakuri ba kuma shima bai fasa shareta ba. Koda
sama da kasa zasu hadu bazai sake zama da ita.
Kawai ta bar komai idan ta haihu zai shiga taitayinsa zasu shirya. Ta riga ta hada Jakarta
na haihuwa kawai dauka zatayi su tafi dashi idan haihuwa ya matso.
Fijr ne ta lura tana ta cizan lebe sai zagaye gida takeyi sai ta tambaya ko haihuwar ne.
Anan tace tana ganin shine, sai suka kira Mommy domin su sheda mata. Ammi tana gefe
tana sauraro, anan ta yanke shawara idan tabar Haske ta haifa dan ta shasu misila.
Daukar gyale tayi ta nufa hanyar gidan su Laila, tunda sunyi baram baram da Banan tace
gurguwar shawarar su yasa Bilal ya fasa. Harda kalle Ammi da mari tayi, wanda Ammi tun
kafin ta zama budurwa rabon da a mareta dan Zailani bai taba ba.
Laila na cikin jin takaicin Bukola sai ga Ammi tazo, anan take sheda mata shamsiyya ta
kusan haihuwa. Laila tayi bakin ciki sosai amma babu yadda zatayi. Shine Ammi tace suje
asibiti a boye su kasa su tsare. Har Laila zata fita sai ta tuna Saif yace ko uwarta da ubanta
ke ciwo ta sake fita saiya saketa.
Nan dai Laila tace ma Ammi taje asibiti tukun, koda Haske ta haihu babu damuwa still
bazata iya kwakulan Bilal ba. Zata faki idon taje ta sace yaron saita aijiye a bola ko gidan
marayu inda kowa zai rasa. Ammi tayi na’am da shawarar inda ma tafiso a sace babyn
yadda Haske zata rinka samun firgici ta shiga tashin hankali har muddin rayuwar ta.
Anan Laila ta roke Ammi ko zata samu wani abu hannunta don ta siya awara saboda
yunwa takeji. Naira dari ta bata tare da kiranta mayya. Ita kuma babu daman rokon
Sameera tunda ta kira mata yara ma su siffan yan wuta ta daina mata magana bayan
gaisuwa.
Haske tayi ma Bilal kiran duniya amma bai dauka ba, sai tayi mashi text inda take sanar
dashi batun alkawarin su akan zai shiga dakin Labour da ita. Tsaki yayi saboda wannan
alkawari ya daukar ma matarsa ne, yanzu kuma basu da gami banda abin cikin ta.
Bayan awa daya da mashi text sai ta shiga labour gadan gadan dole aje asibiti. Yanzu Fijr
ta iya mota sabida haka ita ta tuka su inda Mommy zata same su achan. Shi kuma Daddy
yana Madina wajen aikin sa.
Sai ya tura Anty Fadeela domin ta lura da ita, yanzu auren su saura sati uku. Tun a waje ta
zame masu uwa. Tana kiran Haske lokacin datake yayin daina cin abinci tana mata nasiha
aka daukar kaddara.
Anje asibiti inda aka ce dole CS za ayi mata batada isarshen lafiya. Haka aka tafi da ita
ciki. Fijr da Mommy anata kuka tareda addu’a suna tsoron kada su rasa ta. Ammi ta dawo
asibiti tanata raba ido tareda mugayen addu’a cikin ranta, Allah yasa likita mai yin
operation barci ya kwashe shi cikin aiki. Mommy ta kira Umma a waya. Ita ce ta sanar da
Bilal halin da ake ciki.
Yana Abuja lokacin sabida anan yanzu yake zama, baiso ya hada hanya da Haske. Sanda
ya isa an fito da babyn kenan saura Haske ana gyara ta.
Yaro ne babba 4.5kg fari sol kamar mamansa, saidai fuskanshi tsab kamar na Bilal. Anan
ya karbe shi yayi mashi kiran sallah tareda addu’a. Yaran ya shiga mashi rai ainun, sai yaji
dama a gidansa za’a raine yaron. Kokuma yayima Haske kyauta akan wannan abin arzikin
datayi mashi, sai wani zuciya ya tuna mashi itace ta guje shi gwara ya mance da ita. Those
who betray you once will do it again.
Anan aka soma Murna Fijr sai fara’a take yi, Mommy ma haka ana jiran Bilal ya bada yaron
a dauka. Wani Doctor ya fito daga theater sai Ammi tayi mashi magana.
“Ta mutu ne?”
“A’a Hajia bata mutu ba, lafiyan ta lau yanzu zata fito bayan wasu hours zata tashi sabida
allura da mukayi mata” yace cikin fara’a.
“Hadiza bakiji dadin halinki ba” Fijr tace kasa kasa, amma dayake Fijr babu siri kowa yaji
me tace. Mommy ta kalleta irin bana hanaki rashin kunya ba.
Bayan wasu hours.
A hankali take bude idonta, komai yana dawo mata kadan kadan. Ta tuna cewa ta shiga
Labour. Surar namiji ta gani a gabanta dirarre. Bata gane ko waye ba amma yanayin sa ya
nuna ta sanshi. Murna fal ranta Bilal yazo dubata.
Sanye yake cikin kaya na alfarma, kaftan bai kai gwiwarsa ba, sannan yanada gajeren
hannu. Sky blue gezner sai sheki yakeyi. Turaren sa ya bada koina tana kokarin tantance
sunar sa. Ga gemunsa ya kwanta lub lub. Sake ware ido tayi inda ta kalle mutumin da kyau.
“Haiisam” tace da kyar.
Runtse ido tayi sabida ta soma hauka ko ganin gizo, ba Haisam ya kamata ta gani ba. Bilal
ne yake mata gizo. A hankali ta bude ido, murmushi yake mata mai laushi.
“Haiisam” ta sake maimaitawa.
“Ki daina magana bakida karfi a jikin ki sosai” Saiya Kalle sauran yan dakin. “Bari na
canza mata ledan ruwan”
“Me kake yi anan? Ina Bilal?”
“Sanda nazo Bilal ya tafi, ni kuma jiya na dawo cikin dare, yau naje wajen Mommy sai aka
ce tana nan wajen shine nazo” yace cikin yanayin ko’in kula. Basarwa yakeyi yanayin
maganar sa abin kallo ne balle shi karin kansa, ya bala’in haduwa kamar bashi ba. Aikin sa
ya soma gadan gadan cikin kwarewa. Yanda yakeyi kamar ba Haisam din da ba. Ya manyata
ya canza sosai ga bala’in kwarjini.
Binsa da kallo takeyi babu giptawa, kamar tana neman abu ajikinsa. Shima yanaji a
jikinsa tana kallon sa. Amma bai nuna ya lura ba. Mommy ne ta karasa wajen gadon tana
murmushi saita rike mata hannu.
“Shamsiyya bakiga yaron ba, Allah dai ya raya”
“Gaskiya Babyn ya hadu, da akwai aure tsakanin mu babu abinda zai hanani jiransa
kuma koda nayi aure saina kashe sanda ya girma na aure abina” Fijr tace tana dariya, kowa
a wajen ya murmusa banda Haisam. Gefe yaje ya tsaya saiya saka hannunsa cikin aljihun
wandonsa.
2
Shiru yayi yana tunani kana ganin yanayin sa kasan cewa hankalinsa baya ma dakin.
Karar wayansa ya dawo da hankalinsa, cikin yanayin sa na natsuwa ya fito da hannu daya
daga aljihu tare da Wayan.
Murmushi kadan yayi saiya kara wayan a kunne, “Chiquita (Cute da Spanish)”
“Na’am YaHaisam har yanzu kana asibiti dinne?”
“Eh amma yanzu zan tafi”
“Okay ka jirani ga direban Daddy zai ajiye ni”
“Be safe” saiya kashe wayan. Mayarwa yayi cikin aljihun sa, Haske kuma tana binsa da
3
kallo. Ya canza mata sosai, gashi kota kanta baibi ba.
Fijr ta dauki Babyn ta kaima Haske domin su gana, “Bilal yace zai dawo anjima” tace
mata. A lokacin ta sake runtse ido, hawaye sirara suka sauko mata daga idanu. Da gaske fa
Bilal ya daina yayinta. Kodai ya samu wata ne? Tambaya tayi ma kanta wanda tasan babu
wanda zai amsa mata shi.
Fijr ta taimaka mata domin dajingina bayanta a gefen gadon, ita ma kallon babyn ta
soma, tabbas ya zizaru wajen fasali. Murmushi tayi yayin da sanshi ke ratsa mata duk
ilahirin jikinta.
“Anty yanada kyau koh?”
“Uhmm” tace saita cigaba da mashi addu’a wanda takeyi cikin ranta.
“Prince Charming kike ji, ai yana soma girma zan samo mashi tallan pampers shima yayi
kowa yagan shi” ta kara.
Fijrrrr” Mommy tace tareda tafa hannu tana ware ido. Murmushi Haisam yayi saboda
shi baiki Fijr ya Sakata a gaba yayita kallo ba, koba komai zaita kwasan dariya.
Sallama sukaji inda kowa ya mayar da hankalinsa bakin kofa, Yasmin ne ta shigo ciki rike
da katan cooler na abinci.
“Yauwa yar albarka shikenan koh akwai saura?” Mommy tace.
“A’a akwai sauran yana mota” ta amsa da ladabce. “Ina wunin ku?” ta kara
Kallon Haisam tayi inda suka sakar ma juna murmushi “Chiquita’ ya fada kasa kasa yanda
ita kadai zataji.
“Bari muje na tayaki” Fijr tace saita mike tsaye. Da sauri Haisam ya dakatar da ita “No
haba bari naje” saiya fita a inda Yasmin tabi bayan shi.
“Sun dace” Fijr tace tana murmushi.
Tare suka jera inda suka dawo da cooler na miya sai basket na kwanoni da cokula, sai
kuma katan din ruwa na Faro. Ammi ce ta ajiye Hafsee dake jikinta ta mike domin ta zuba.
2
Anan ta zuba nama san ranta babu abinda ya shalleta.
“Toh ni bari na tafi” Haisam yace. Kallon inda Haske take yayi, “Maman Baby” yace mata
tareda nodding. Saiya shafa ma Hafsee kai ya tafi.
Yasmin dake kofa tana tsaye ta bin masa baya, rangwada takeyi abinta ta saka kimono
plain peach wanda aka saka lace mint green a kasan kayan da hannu sai wuya. Dogon riga
green ta saka a ciki sai ta daure rigan da igiyan sa.
Tayi kyau abinta kana kallonta zaka samu nishadi. Tafiya sukayi kadan babu abinda suke
cewa. Ita ta soma magana.
“YaHaisam dazu ance kazo ina barci”
“Eh Chiquita nazo gaida Mommy sai naji Haske ta samu karuwa”
Tabe baki tayi ta soma fari da ido, magana ta hau yi cikin shagwaba, “Yanzu Yaya bama ni
kazo gani ba?”
Dariya yayi mai sauti saiya kalleta, “Chiquita iyayen rigima, ina ce ke kadai kinsan da
Zuwa na. Kawai nayi missing Mommy ne amma gabaki daya Family na zo gani… Happy?”
Kakalo murmushi tayi saita girgiza kanta, batasan meyasa yake nokewa kamar bai gane
halin datake ciki ba. Meyasa bazai ce dominta yazo ba? Bata kai bane koko me yake nufi?
Kullum yayita mata kirki amma kana gani kasan matsayin yar kanwarsa ya dauke ta.
Meyasa bazai bata wani matsayi daya wuce wannan ba.
Har motansa ta rakasa inda ya shiga saita rufe mashi. Taso ta basar amma ta fasa, Allah
kadai yasan yadda zuciyarta ke mata radadi da bazanar fashewa akan soyayyar sa. Da chan
tana ganin gangancin yanmata masu kiran saurayi kokuma su nuna masu soyayya. Idan
aka saka mata wuka a wuya bazata iya yiba, magana ma da saurayi wahala yake mata.
Sai kayi mata kira uku kafin ta dauka kuma bazata wuce eh ko a’a ba. Amma ga Haisam
kuwa da kanta take neman sa ta WhatsApp, kiransa da sauran nuna alamar kulawa. Inda
abin yazo mata da sauki dan uwanta ne kuma abin bazai yi muni da kyau ba. Tawa ta
sameni ina san maso wani’ ta ayyana cikin ranta.
“YaHaisam to ni bari na koma…. We will talk later?” saita juya. Ta soma tafiya wajen taku
biyar sai yayi magana.
“Chiquita”
Tsayawa tayi cak kamar mai amfani da battery, muryansa kawai takeji yanzu bata waya
ba yana kara mata sanshi cikin ranta. Juyawa tayi fuskanta babu yabo babu fallasa
“Na’am Yaya”
“Zanzo anjima…. Sai muyi labari.. Okay!”
Dakai ta amsa sai tayi murmushi wanda ya bayyana hakoranta. Shi kuma ya kunna
motarsa ya tafi. Da kyar ta karasa dakin duk ilahirin jikinta yayi sanyi, saita ta tsaya bakin
kofa ta share idonta sabida ya cika fal da hawaye. Bata san ganganci daya kaita har ta fara
san Haisam ba. Gashi bai ma san tana yi ba, bama shi ke bata tsoro ba face tasan kalar san
dayake ma Shamsiyya. Saidai yanda ya nuna bai san tana dakin ba ya burge ta, kila yanzu
ta fice mashi daga rai. Wannan kenan!
**
Taso ta kaima Sameera Gullisuwa domin ta ajiye mata kusa da ita koba komai zata fi
samun ciniki a haka. Sai dai har yanzu Sameera bata wani sake mata fuska ba, idan bai
kama dole ba bata ce mata komai.
Dabara ya fado mata saita ce bari ta daura akan karamin kujera na kitchen, sai ta kai waje
yanda zata fi samun customers sosai. Duk me so zaiyi sallama ta fita ta bashi.
Sameera ta shimfida tabarma zata soma ma wata mata lalle, sai Laila ta fito sanye da riga
top sai zanin atamfa. Sannan ta saka kallabi ta daure shi akan goshi. Tafiya takeyi kamar
balbela tana kumbure kumbure. Idan Sameera bazata mata magana ba ita ma zata fita
harkan ta.
After all kishiya ba abin ayi ta’ammali da ita bane, balle ma ta kusan sanadin barin
Sameera a gidan. List gareta kuma ta gama da Haske yanzu, saita maida hankali akan
Sameera sannan kuma Kwalo Kwalo. Idan yaso zata rage daga ita sai Destiny inda zasu sha
madaran soyayya. Babu haufi makircin kishiyoyi ke kawo mata matsala, idan suka tafi
komai nata zai zama aziman.
Ta ajiye kenan ta juya zata soma tafiya, ‘Kip rukukus’ taji kara inda ta juya da sauri. Akuya
ne ja mai baki ajikinsa ya ture robon. Da sauri ta ruga kafin ya soma ci amma ya rigata.
“Kutumelesi! Butan Shayil Aikam yau zan hallaka ka!” ta fada cikin masifa. Zuwa wajensa
tayi ta soma ture shi amma ko kulata baiyi ba. Cin Gullisuwa ya rinka yi abinsa. Itace bata
5
gane shiba amma Officer ake kiransa. Ya saba ma mutane barna cikin gari.
Idan aka aike yara siyan alayyahu haka zai hankade su ya kwace ya ci, sannan kuma kana
tsaye a titi da kudi a hannunka zai iya fizgewa yaci naci yabar na bari. Gashi baya zama a
kasa, idan masu zaman majalisa suka fito suna zaune, haka Officer zai zauna gefen
tabarman su babu abinda ya dame shi wata sa’in har gogan jiki yake da mutane.
Gashi bai jin duka, duk abinda zaka kwada masa bazai matsa ba, abinda yaga dama
yakeyi, shine ma zaiyi kokarin dambe dakai. Gashi mai akuyar wata dattijuwa ne aka bata
akuyar tun yana karami daga kauye. Idan yayi barna haka zatayi ta bada hakuri, mutane
dai suna zaginsa kuma an shawarceta akan ta siyar.
Da kyar Laila ta samu ta kwace roban, yaci fiye da rabi. Sauran kuma duk kasa yana kai.
Ranta yayi mummunan baci saita wuce cikin gida domin ta dauko tabarya. Zata nuna
mashi ta fishi hauka. Koda ta dawo bai tashi ba yana cin sauran wanda ke kasa abinsa.
Auna mashi tayi a jiki inda ya dago ya kaleta, baya ya somayi da jikinsa. Murmushi tayi
tana ganin ta samu galaba a kansa. “Dama yau nace saina hallaka ka, daga ni bazaka sake
ma wani barna ba” saita sake nufan sa.
Bubbuga kafansa yayi a kasa saiya ruga da gudu ya nufeta da tunkuye, anan ya zubar da
ita a kasa ta fadi warwas tana numfashi. Duk abinda akayi a idon yan anguwa. Kowa yana
ganin ganganci akan dambe da dabba. Balle officer ya buwaye kowa.
Kofaton sa yayi amfani dashi ya taka mata kafa saiya soma kallonta, wasu samari da
sukaga abinda ya faru suka kai mata agaji. Ture Officer sukayi sunata kilarsa. Da kyar yabar
wajen yana ihunsa.
“Kema Hajia aida baki biye masa ba, idan ya maka barna kyale sa kake kokuma ya gotar
maka da kashi” daya daga cikin su yace.
Girgiza kai tayi alamar tagane saita tashi da kyar zata tafi, a karkace ta soma tafiya sabida
harya gotar mata da hakarkari. Tana tafe tana dingishi, samarin suka taimaka mata da
kujeran zuwa cikin gida daga kadan suka tafi.
Batace ma Sameera komai ba ita ma bata tambaya meya faru ba, kujerar daki ta zauna.
Anan ta fara hawaye sirira saboda zafin dake bin duk wata ilahirin jikinta. Numfashi take
kadan kadan tana jira Destiny ya dawo yaje har gidan mai akuyar yaci masu uwa.
Ranar bataci wani abin kirki ba banda awara data sake zuwa ta siya a gida biyu tsakani.
Gashi yanzu Abul Khair data hana ya kula Bukola yayi mata fuska shima balle ta aike shi.
Abu ya fado mata gwara ta karbi number din Bukola saita rinka tambaya akan me zata dafa
masu kafin ta dawo.
Sai kuma ta yanke shawara taje wajen Sameera ta karba key tayi masu tuwan shinkafa da
miyan taushe.
“Sameera bani Key din Bukola”
“Tace a baki ne?”
“A’a amma abu zan mata” tace cikin rashin kunya.
“Bukola ta bani key Bukola zan bamawa idan ta dawo”
Fuuuu ta tafi kamar guguwa batace komai ba, Sameera yanzu tana shigan mata hanci.
Amma ta kusan fyace ta. Suna dab da goga kirji kuma karta ga tanada girman jiki dukan
tsiya zatayi mata. Ranar bin gado da kujera tayita yi yunwa yana dawainiya da ita. Gashi
2
yanzu babu jarin Officer ya cinye tas.
Sameera wajen la’asar ta shiga kitchen domin tayi abinci, ranar Saif ya bata dari biyar na
cefane. Mubina tace tana san cin dambu na shinkafa da soyayyar kifi. Dama duk cikin yaran
yafi santa. Kudin bazai isa suci waja waja ba amma kuma kadan zata kara tunda tanada
shinkafa da aka barza.
Dama tanada wanda ke zuwan mata kasuwa idan bazata iya ba, wata makwabciyar su ne
wanda take sana’a na awara, kullum sai taje ta siya waken soya da sauran abinda zatayi
amfani dashi. Tanada mutunci yan unguwa suna bata kudi domin ta taya su, lada kadan
zaka bata.
Sai Sameera ta bata kudi domin ta siyan mata kifi manya guda uku, sai zogale, gyada da
kuma ginger. Bayan ta gama aikin saita gyara dakinta ta bishi da turaren wuta, daya turaru
saita fito da kaskon bakin dakinta domin shima yayi dan kamshi
Bayi ta wuce tayi wanka, yau tanajin gayu sosai. Make up ta fesa harda jan gira dama ta
iya a wani biki ta koya kawai batayi ne. Sabon dinki tasa na atamfa Da Viva mai green, blue
da pink. Offshoulder ne dinkin kuma ya amshe jikinta, sai tayi daurin da ake yayee na
turban.
Dama bayan asuba Saif yabar dakin Laila ya koma na Sameera kamar yadda sukeyi, Laila
babu abinda ya shafeta kayanta na jiya shike jikinta babu wanka balle ta canza su. Gashi
har yanzu gashin kanta a gwaigwaye. Duk abin ka yanzu baka ganin gashin kanta tana
tareda kallabi wanda da chan bata sawa. Har magrib zata iya fita kofar daki ta dauki
mopstick babu kallabi.
Bukola ta fara dawowa taje dakin Sameera domin ta karba key, tunda tayi auren sau
daya ta shiga dakin ranar Sameera tana zazzabi. Ita a bakin daki take jiran ta har ta fita suyi
maganar su. Yauma haka tana tsaye Sameera zata dauko mata key, sosai tayi mata kyau
inda tayi magana.
“Anty yau zaki kashe shi fa! All these finesse da chakarewa karki hanashi dawowa wajena
gobe please”
“Ai ban isa ba” saita mika mata key din, murmushi sukeyi ma juna sosai saboda akwai
mutunci tsakanin su. Bukola ita duk yadda kabi da ita haka zata maka. Idan kirki toh idan
rashin mutunci kazo wajensa.
Laila na daga daki bakin ciki kamar ya kashe ta, sai tace gwara ta rabasu kafin su hade
mata kai cikin gidan. Ta window ta leka ta kalle Sameera taga kyan datayi.
“Ko kyau” tace tareda tsaki.
Bukola ta koma dakinta sai ta shiga wanka, tana fitowa saiga Laila zaune akan kujera
harta kunna TV tana kallon Telemundo. Hade girar sama dana kasa tayi ta soma magana
cikin masifa.
“Anty Laila lafiya kika shigo min daki ba tareda izini ba?”
“Dama nayi sallama sai baki amsa ba shine nace kila kina bayi ne” ta fada da fara’a.
“Amma dai da kin jirani a waje mana, a musulunci ina aka ce ayi haka?”
“Ayya ban zata haka bane, ni banma dauka wani abu ba”
“Anty gaskiya karki sake shigo min daki ban baki dama ba, idan ban amsa ba kije ki dawo
sanda kika ji motsi na saiki zo tunda ba mutuwa nayi ba”
“Toh kiyi hakuri” Abin yayi ma Laila ciwo da Sameera ne data zageta amma wani abu a
ranta yana cewa idan ta zage wannan nata ya kare, bayan ita datake neman su hade ma
Sameera kai.
“Anty ki tashi ki fita tunda dai ban baki dama ki shigo ba” ta fada ko kallon Laila batayi
ba.
Rawar baki Laila ta soma gabanta ya fadi, har ita Bukola zata nunama bariki. “Dama nazo
ne nace ko zaki rinka barin min key saina rinka mana abincin rana kafin ki dawo”
“Allah koh! Na bar maki key ki tsame min nama ko ki deban min madara… Do you think
am stupid? Besides sai kace an tsine min nabar ma kishiya tayi min girki lafiya na lau ” tace
saita kalleta. Anan jikin Laila yayi sanyi ta soma tir da hali irin nata gashi ya kawo mata raini
gaban kishiya. Zufa ya soma karyo mata duk AC dake dakin, ita Bukola bata ta’ammali da
zafi saboda tanada hips sosai ga dukiyar Fulani yalwatacce bataso tayita zufa.
“Ki amsa ni mana? Wani bincike kike so ki sake min? Look Anty Laila idan bana cikin daki
bazaki taba shiga ba. Kuma ko ina ciki zan rinka binki da kallo duk abinda kike yi”
“Kiyi hakuri Bukola tsautsayi ne… Kuma wallahi ban daukar maki kudi ba” tace a hankali.
“Anty ba’a tsautsayi da sata, a garin mu muna cewa Ole buruku. Kuma bana ajiye kudi
haka komai na banki. Sannan kuma ga ojikokoro… Uhmm meye ma ma’ana abin” saita fara
2
tunani tana yarfi da hannu.
“Ehen yauwa na tuna, kwadayi baida amfani Anty Laila….Yanzu ki tafi nina gaji inaso na
huta sosai” saita nuna mata kofa
Laila kasa mata magana tayi ta soma tafiya, Bukola dai dariya takeyi cikin ranta. Har ta kai
kofar daki sai Bukola tayi magana.
“Anty”
Juyawa tayi ta kalle ta, “Na’am”
“Bari na baki indomie ki dafa”
Saita wuce kitchen ta dauko super pack daya ta bata da kwai daya, anan fuskan Laila ya
washe kamar ba ita taso kuka ba. Harda rinsinawa kasa tayi.
“Nagode sosai Allah ya saka da aljanna”
“Ba komai Anty ai ana tare”
“Ai da kin dena ce min Anty, ai mun zama daya.. Zaki iya ce min Laila ko Lailus”
“Karki damu Anty mu a yaren mu idan mutum ya fika wani matsayi ka bashi girman shi,
duniyar guda nawa ne… Kin rigani auren Saif yasa dole nace maki haka” dariya Lailus tayi
taji dadin maganar nan.
“Kince kin gaji dana dawo anjima na tayaki hira tunda Saif yana wajen wancan” saita tura
baki tareda nuna dakin Sameera. Hade fuska Bukola tayi sosai kamar bata taba dariya ba,
ita bata san gulma. Idan akayi nata bata so yasa take kiyaye yin na wani. Balle anyi ma
yarbawa shedan gulma.
“Eh na gaji, idan kin fita ki janyo min kofa”
Laila taji haushi, tana tunanin idan aka kawo chapter din Sameera zasu rashe su kwashe
mata albarka. Haka ta fita ta koma dakinta. Tana kitchen taji motar Saif, bata fita ba ta
cigaba da dafa indomie dinta, dama tayi dabara ta gyara heater anan ta tafasa da kwan.
Saita tsiyaye ruwan, haka kurum bazata kunna risho ba kafin tayi barnar kalanzir.
“Gaskiya kin yi kyau” Saif ya fada daya ganta, da gudu Laila taje window harda bigewa
domin ta sake gani. Tsaki ta kara buguwa amma bata bar wajen ba, ledan hannunsa
Sameera ta karba, kankana ne gida biyu sai yace ta kaima Bukola. Har cikin ranta bataji
dadin yadda ba’a siya da Laila ba.
Bayan ta bama Bukola ta koma dakinta, Saif yana bayi har bayin ya soma sirarowa da
wari. Kitchen ta nufa ta raba nata kankana ta saka cikin plate domin ta kaima Laila.
Sallama uku tayi kafin Laila dake falo ta amsa, tanajin kacau kacau na cokali amma akayi
banza da ita.
Datazo bakin labule ta yayee fuska a murtuke, murmushi Sameera tayi saita mika mata,
“Gash”
“uhmm” tace ko godiya ta karba ta juya ta tafi. Abin yayima Sameera ciwo taga wautar ta
akan zuwa tun farko. Koda ta koma daki kamar ba nata ba, sabon turare ta kunna na sanda
1
saita daga labule iska ya gauraye wajen. Wannan kenan!
Dayake Dr Pratab Punjabi yazo daga Indiya, shi ne yayi ma Haske CS dinta, sannan
Badman yayi masu hadarin kudi sosai inda aka bata best intensive care a asibitin na
Dialogue. Cikin kwana goma har ta soma warwarewa sosai.
Batayi wankan jego ba saboda surgery amma tana samun kulawa yadda ya dace. Kullum
Haisam sai yazo sau daya, idan yana wajen yana canza mata ruwa kuma yana mata allura
na hannu idan ya kama. Suma yan asibitin sun san makarantar dayayi har sukayi mashi
tayin aiki a wajen saboda sun lura yanada kwanya.
ldan yazo zakaga Doctors ana mashi tambaya akan yadda suke magance wani matsala a
turai, anan zai masu bayani akan hanya mafi sauki. Abin ya kara burge Haske sosai, ga
kamala ga kuma ilimi. Uwa uba yanzu ya iya fesa kwalliya, idan ya saka kaya kamar danshi
akayi abin. Baida maraba da model na kayan maza sabida kana gani yanzu yana yana zuwa
gym.
Sannan wani turare dayake sawa mai kamshin gaske ga kuma sanyi, kullum akwai bakin
tabaro a idansa har sa ya shiga dakin yake cirewa idan zai gaida mommy. Idan bata wajen
barin abinsa yakeyi.
Ammi itama tana zuwa jefi jefi idan taso gulma, bala’in burgeta Haisam yakeyi. Ya taba
rage mata hanya sannan ya biya Ostrich bakery ya siyan mata cake da meat pie. Abin yayi
mata dadi sosai inda ta fara mashi kwadayin Fijr. Zasu dace sosai, ita bata masan ya taba
san Shamsiyya ba.
Ko sau daya bai taba jan Haske da hira ba koda wasa, abin kam yayi bala’in mata ciwo.
Baisan aurenta ya mutu ba tunda Bilal yana zuwa kusan kullum. Idan Bilal ya shigo saiya
fita yabar wajen, shi ma idan yana ciki sai ya fita ya bada waje.
Kamar yadda yace zaije wajen Yasmin haka kuwa yayi, amma bai yi wani magana sosai
ba. Dama ba yanayin sa bane saidai kai kayi yana dariya. Sun shafe awa kusan daya tanata
mashi surutu, anan ya sake karanta inda ta dosa. Tunani yakeyi yanda zai soma fada mata,
shi ya rufe babin soyayya saboda bashida amfani. Zaiyi aure dan aure amma banda
soyayya.
Kuma bai kamata Yasmin ta aure wanda bai santa ba, yarinyar tanada natsuwa da
hankali, kamar kanwarsa take idan wani ya bata mata rai shi mai kwatan mata hakki ne
balle kuma ace yanzu shine zaiyi mata haka. A hankali yanzu yake so ya wayar mata kai.
Gashi yafi san zama gidan Mommy akan nasu, har yau bai mance da Ladidi ba. Yafi samun
natsuwa wajen Mommy, amma Yasmin ta rinka damunsa kenan. Yanzu idan yaje sanda
yakeyi sai yaje dakin Abubakar yayi kwanciyar sa, idan kuma taga motarsa zata bishi ta
soma tambaya ko yaci abinci bari tayi mashi girki.
Ta iya daga su snacks da abincin gargajiya, ko baijin yunwa saboda karya bata mata rai
zaici. Wata sa’in harda takeaway take masa. Shima yana biyawa Kanti Plus Store ya siyan
mata tsaraba ko Chocolate, turare kokuma Pouch na wayanta tunda tana san abin kuma ya
lura kusan kullum saita canza. Idan ya shirya zai fita zata ce suje tare wallahi bazata takura
mashi ba kawai bata san zaman gida batada kawa ko kwara daya a Najeriya tunda banan
suka tashi ba, dama dama suna shiri da Fijr kansu kusan daya.
Ita Yasmin tana jin labarin yadda yake yawan zuwan asibiti, kishi takeyi sosai yasa takeso
ta rinka binsa, idan yaso Haske zata gane suna dating saita fita harkan sa tunda shi yaki fita
nata. Idan ya kama da kanta zata roke Haske akan tabar mata shi tafi sanshi kuma bazatayi
hurting dinsa ba. Amma kuma maraicin Haske yana bata tausayi, ita da zata iya fita harkan
Haisam harga Allah zatayi. Amma abine daya jibanci zuciyarta kuma batada yanda zatayi.
Zuciyarta ta fara sanshi, batasan yanda zata bata hakuri akan ta gane bazata same shiba,
wahala kawai zasu sha idan bata daina. Kawai abin da ta sani idan iyaye suka lura za’a iya
saka shi ya aureta. Amma kuma bata so a takura mashi akan ya aureta bisa dole, da
soyayya aka haifeta kuma tana fatan dashi zatayi aure.
Ranar da Babyn yayi Bakwai ba’a yi taron Suna ba sabida Haske tana asibiti duk da bawai
tana ciwo bane sosai, Alhaji Zailani ya roke alfarma akan asa ma yaron Sunar baban Bilal
saboda su dan wanke rashin mutunci da Haske tayi.
Bilal yaji dadi sosai inda Babyn yaci suna Bello amma ana mashi lakabi da Ajwad. Ajwad
yazo ma mutane da soyayyar sa saboda babu mai kinsa harta Ammi, tana samun nishadi
wajen kallon sa. Haka yake kafa mata ido yana murmushi, saidai batun sace yaron akai
gidan marayu bata fasa ba.
Ko barci Ajwad keyi zakaga wani gefen sa yana gadi, kamar ansan abinda ke ranta. Shima
Haisam kullum saiya dauka yana kallo, ji yake a ransa dama na su ne shi da ita amma kuma
yasan kaddara ta riga fata.
Chan kasan ran Bilal yana kishi idan yaga Haisam a wajen, eh yasan dan uwanta ne
amma baisan ganinsa kusa da ita. Bawai ya tsaneta bane, kawai ta fice mashi daga rai ne.
Duk wani santa dayake yi yanzu ya nema abin ya rasa. Kawai dai jininsa bai hadu dana
Haisam bane
Randa tayi kwana goma cip a dakin tana barci Haisam ya shigo, Mommy itama tana daga
gefe tana lazimi akan sallaya, Haisam ne ya shigo hannunsa cike da kayan kwalam kaji da
drinks. Murmushi tayi tana kallon sa, shima abinda yayi kenan yasan zatace dama bai kawo
ba, amma dayaga batace komai ba sai yaji dadi.
Ita kuma batasan ko ya sani ba amma dai yadda ya fita harkan Shamsiyya yayi mata dadi,
balle taga suna shiri da Yasmin koba komai za’a bar Haisam cikin family.
Yana cikin wasa da Ajwad sai ga Bilal ya shigo, suna kallon juna suka watsa ma juna
mugun kallo. Haisam ya rasa matsalar Bilal dashi, bayan yana auren Haske meye kuma duk
ya damu haka. Ajiye Ajwad yayi sai mike tsaye.
“Bari na baka waje ku gana da matarka da family dinka”
“Are you trying to provoke me?” Bilal yace cikin fushi.
“Bangane ba?”
“Kana kiranta matana domin ka bata min rai bayan kasan abinda ya faru” Shifa Bilal
yasha izgilanci yake masa saboda yaji Haske ta guje shi lokacin.
“Baida labarin kun rabu, randa ta haihu ya dawo kuma ba’a yi maganar ba” Mommy tace
a sanyaye.
“Ohhh” Bilal yace saiya sake watsa ma Haisam harara.
“What happened? Me kayi mata??? Did you hurt her??? La haula dama Shamsiyya
batada aure?” saiya dafa kansa.
“Abinda ya rabamu is none of your business kanaji koh? Kuma ka daina zuwa kusa da ita
bana so” Bilal yace cikin takaici yana nuna mashi yatsa. Saiya kalle Mommy kuma.
“Mommy kice mashi ya daina zuwa wajen Shamsiyya da Yarona, bana so”
“Ku kam bazaku daina fada ba har yau?” Mommy tace. Duk abinda ake yi Shamsiyya tana
ji saidai bata bude ido ba. Tsoro take kada dambe ya kaure tsakanin su. Bilal zuciya ga
Haisam shi ma yanzu yana fadin rai.
“Ni banida matsala, naga dai shamsiyya yar uwata ce kuma babu wanda ya isa ya raba
mu. Kaine dai bakada alaka da ita. Please daga yau ka daina shiga cikin dakin nan, idan
kazo ka tsaya a waje za’a miko maka Ajwad.. Family only”
Kallon Haisam Mommy tayi cikin mamaki, shida baya magana amma ya iya fadin haka.
“Bansan rashin mutunci Dan Lele ka barshi yaga yaranshi mana”
“Okay yau kadai ne, kuma dama ta warke. Yanzu zanje ayi maganar sallamarta… Idan ta
koma gida sai muga yadda bakada alaka da ita zaka ganta” saiya matsa gefe, Yasmin ne ta
shigo ciki ta kawo abincin rana inda Bilal ya fasa magana.
“YaHaisam dama nasan zan ganka anan” tace da fara’a.
“Chiquita ban dade da shiga ba”
“Yaya Bilal ina wuni”
“Lafiya lau'” saiya cigaba da wasa da hannun Ajwad, kawai yana tunanin wanda zai hana
shi ganin Haske idan yasoyi. Haisam bai isa ya nuna iko akanta ba, ai sun taba aure kuma
sunada yaro tsakanin su. Yafi shi iko akanta.
Tunani Haske ta soma, wannan abinda Haisam yayi saboda yana santa ne koko yana
tunanin Bilal ya zalunce tane yasa yake kokarin kwantan mata yanci. Dan kam yafi hasken
rana bayyana cewa akwai soyayya tsakanin shi da Yasmin. Wannan kenan!

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]