HASKE CHAPTER 24

HASKE

CHAPTER 24Hakuri shine gishirin zaman duniya amma ga Fijr kuwa barkono shine nata. Akan gado ta
ajiye Hafsee saita Kalle Lantana, “Watsa mata ruwa muga…ina zuwa”
Hanyar kofa tabi da sauri tana zancen zuci, batasan meya faru ba amma tana kyautata
zaton cewa Laila ce sila, in fact bama taso taji komai saita hukunta ta daidai laifin ta koma
fiye. A gefen Mallam Adamu ta dauko belt din injin nika wanda yake bama yara tsoro dashi.
Inda Laila tabi itama ta nufa da sauri tareda sarsarfa.
Ita kuma dataga tayi nisa saita rage tafiya, rangaji takeyi tana juyi kamar reshen bishiya,
murna fal ranta yau tayi abin kai wai fitsari da kumfa. Napep sunyi wuyan gani anguwar
masu dashi, tana tsaye tana jira wanda zai gipto idan taci sa’a. Saita soma dirga kudinta 7k
cip.
Tana murmushin jindadi hankalinta yabarjikinta. Taji tafiya ta bayanta amma bata kawo
komai ranta ba. ‘shuu’ taji Fijr ta Zabga mata belt din injin. Anan ta makale baya tareda
sakin kayan hannunta. Mari ta kuma sharara mata guda biyu masu kyan gaske domin sun
zauna daidai kan fuskan.
Sai Fijr ta finciko ta tareda shaketa gam, firfito da idanu tayi fatsari ya soma zuban mata.
Dama zata shiga bayi kenan Banan ta kirata a waya. Jijiga ta Fijr tayi tana mata tambaya.
“Uban me kika mata haka?”
“Ba da

ke nakeyi ba? Nace meye kika mata harta suma rai yana wajen Allah? Halan kin

nuna mata first class halinki kenan?”
Zabga mata belt din Fijr ta soma yi ta ko’ina, banda ihu babu abinda Laila keyi. Taki
magana sabida tasan idan Fijr tasan asalin zancen zata kashe ta.
“Anty Dan Allah kiyi hakuri, lafiya lau nabar gidan”
1
“Zakiyi bayani malama, bari na gama aika ma jiki manzan sa mai isar mai da sako”
Saita ture mata kallabi domin ta fincika gashin ta har gida, takaici taji dataga kan duk ya
gwaigwaye kamar an gama cizgan giginya ko mangwaro. Mari ta sake sauke mata saita
murde mata hannu ta soma janta.
“Muje kiga yanda kika barta sai kiyi min bayani da kyau” tirje wa Laila tayi ta soma
kokawa da Fijr bazata ba. Anan ta sake zabga mata belt din, darewa tayi tana lankwasa
baya sai tayi kokarin amfani da dayan hannunta domin ta sosa wajen. Zafi takeji kamar an
barbada mata barkono. Nan take zazzabi ya sauko mata.
“Ikon Allah ! Dani zakiyi dambe?” sai Fijr ta saketa Sanna ta cire kallabin ta tayi dammara
dashi.
“Toh shikenan mu kara.. Wanda ya fasa tsakanin ni da ke kada Allah ya raga masa” saita
nufa Laila da naushi. Anan ta sakata a hammata ta kuma take mata kafa sabida balance
saita soma duka. Banda ihu bata komai, ita yanzu numfashi Yama soma gagaran ta kamar
Fijr ta saka mata barrier da iska.
Abin bai ishe Fijr ba, sai ta janye belt din injin. Dukan tashi ki sha gishiri tayi mata. Tunda
take bata taba samun galaba ba kamar wannan, duk sauran dukan da takeyi saboda
nishadi ne da keta. Amma wannan karan zallan bacin rai ne. Haske ta dade tana shan
wahala kuma idan tana raye no one would hurt her again, wannan alkawari ne ta dauki ma
kanta, Haske marainiya ce kuma itama tanada ‘ya da zataso bayan ranta a tayata da raino.
Wani hawaye siriri ya zuban ma Fijr, bakin ciki kawai ke mata dawainiya balle ta tuna
yanayin dataga Haske. Shirun Laila yasa ta saketa, ta bala’in galabaita har hawaye sun kafe
daga idanta
Ga layin belt kacha kacha duk jini jini a jikinta, anan Fijr ta sake finciko ta domin su koma
gida. Aikam roko takeyi dakai saboda bata iya magana, numfashi bai fi sau daya takeyi ba
every 15 secs. Tirgewa ta sakeyi, anan kuma Fijr ta sake zuciya ta zabga mata belt din saita
kama mata haban zani. Janta takeyi kamar akuya.
Kota kan kudin batabi haka tabarsu kan titi da gangan kowa ya rasa, dabara ya fadoma
Laila saita ganna ma Fijr cizo. Tana sakinta saita ruga a guje. Dabu daya ta iya dauka ko
jakarta bata bi takai ba. Haka Fijr ta rinka binta ashe ta iya sport sosai tana Relay race
lokacin a secondary.
Kan kace kwabo Laila ta soma yin mata tazara, sakin jiki tayi tsakanin ta da Allah. Anan
Fijrta tsaya ta barta saita yi magana da karfi, “Ki gudu dan ubanki, har gida zan biyoki ai
ban gama dake ba” saita juya
Tas ta kwashe komai tasa a jakar ta tafi dashi, har gida zata mayar mata idan taje bata
kashi. Karar kukan Hafsee taji tun daga wajen gate, da sauri ta karasa ciki har Daddy ya
dawo. Haske ta farfado amma bata hayacin ta. Sai sumbatu takeyi.
Lantana da Daddy suna kokarin sakata cikin mota bangaren baya, Hafsee tana hannun
Anisa tana ihu bawai tasan meke faruwa bane kawai kiriniya ya motsa.
“Alhamdulillahi bata mutu ba?” tace a fili. Kallonta Daddy yayi zai tambaya ina taje amma
kuma ya fasa. Shiga yayi zai tafi taje itama zata.
“Ki zauna dasu Anisa magrib yayi” bai sake cewa komai ba saiya tada motar inda ya fita
gate da an riga an wangale. Haka ta karba Hafsee ta saba a baya, kallabin kugunta data
mance mayar dashi kanta tayi amfani dashi tayi mata irin goyon maneji.
Hankalin Zailani yayi mugun tashi saboda harya isa dakin Haske bata farkaba. Saida
shima ya shiga bandaki ya debo ruwa mai yawa ya sheka mata, Lantana yayyafa mata tayi
wanda baima wani taba ta ba. Tari Haske tayi tareda firgici, anan yayi hamdala shine suka
nufa hanyar asibiti.
Al-mansur private ya kaita, tun a hanya yayima Doctor Kola waya gasu nan zuwa. Nanda
nan aka fito da gado da oxygen aka sakata suka wuce da ita. Taimako na gaggawa aka bata
inda aka gane zuciyar ta ne ya buga.
Bata samu Napep ba saida tayi gudu mai bala’in nisa, kowa kallonta yakeyi ana sha hauka
tayi. Ga kaya fes fes dai a jikinta kuma ba’a Santa ba. Wasu suka soma tunanin kila sabuwar
hauka ne tayi wani mugu abu shine tabi duniya. Ga gashi kamar na kolaman kaza.
Dakyar wani mai napep ya dauketa data hasko mashi dubu daya, a napep banda kuka
batayin komai. Ta rasa meta ma Fijr data tsane ta haka. Maimakon suyi hadaka suci uban
Haske tunda yar kishiya ce, a’a wai Haske ne ake kwatar ma yanci haka.
2
Sai a lokacin ta tuna bata tambaye Saif ba kafin ta fita gabanta ya sake fadi akan karyan
da zata zabga mashi. Sun Kai gidan mai napep yace bazai bata canji ba shi drop ya dauke
ta. Anan suka soma gardama. Zaginta ya soma yace idan bata fita saiya yaga mata kaya,
haka babu arziki ta fita tareda binsa da Allah ya isa.
Koda ta isa motar Saif ta gani inda gabanta yayi ras, saita soma tangadi tana tafiya a
karkace kamar tayi accident. Shima daga shi sai three quater blue da bakar singlet yana
zaune a dakinta yana cin kaza gurguwar kan hanya. Wani yayan Bukola yazo daga Lagos
shine ya siyan mashi ya kaima matansa, dama koda ya iske Laila bazai bata ba.
Da sallama ta shiga ko amsawa baiyi ba balle ya kalleta. Ita dama yayi magana tasan ta
inda ta dosa. Anan ta wuce daki ta daura tawul ta wuce bayi, babu ruwa flask kuma heater
ya kone gashi kalanzir kwalba uku daya siya tun ranar da bukola tazo ya kare da safe.
Haka ta wuce bayi ta watsa ruwan sanyi, kamar an gaya ma ruwan domin yaci zalinta. Yayi
mata bala’in sanyi harda tsandara ihu ikin bayi, koda ta fito tana rawar dari kamar zata
mutu. Jikinta ya sake kumbura sannan ta soma al’adanta na wata wata. Aikam ta shiga
uwar daka kenan Saif ya bita.
“Zo ki fita!” yace babu wasa fuskansa. Baki yana rawa tayi magana, “Dan Allah Saif
accident nayi wallahi kaji tausayi na”
“Nace zo ki fita kokuma ki fada min bulo nawa ubanki ya taimaka min dashi sanda nayi
ginin nan”
Kuka ta fashe dashi, bata saka kaya ba balle pad, dama akwai ragowa data dauka gidan
Haske tunda ita bata amfani dashi. Zatabi hanyar durowa ya ingijeta waje.
“Waje nace ki fita ki koma wajen kawaliyar ki domin su baki masauki
“Haba Saif karka min haka ko kaya ka barni nasa mana.. Bakada tausayi ne?” saita nufa
hanyar durowa kuma cikin gadara zata dauki kayan. Zabga mata mari yayi da karfin gaske,
‘dim’ ta gani ta wajen idanta dishi dishi kamar ta makance. Saiya finciko ta wajen falon ya
wurga. Balangu baiga wuta ba, tafashe baiga wuta ba, soyaryen nama baiga wuta ba, tsire
shine sukayi ido hudu da wuta kuma kalan azabar datake ji kenan.
” Dayake na maki kamada lusari koh ai dole kimin karya da rainin wayo haka… Kinsan
Allah ki fita tun kafin naci zarafin ki cikin daren nan….Albarkacin Malam kike ce dana dade
da sakinki. Keba kyau ba, keba haihuwa ba, keba iya kwalliya ko tarairayan miji ba. Banda
shikashikan rashin kunya baki komai shine kike so na raga maki? “
Bata so a sake bugunta, tana ganin duka daya za’a mata zata iya hadiye rai ta mutu, ta
bala’in gajiya kamar tayi jinya na wata shida, duk kasala takeji kamar zatayi amai sabida
bakinta wani daci yakeyi. Hawaye ta soma yi tana tausayin kanta. Wai meyasa mutane
basuda imani ne? Jibe yadda ake mata kamar wata dabba ba mutum ba sabida anfi
karfinta. Abu daya ta sani kuma Allah zai bin mata hakkin ta, wani shari’a sai a lahira.
“Kaida Allah, an baka amana na shine kake cin zalina” tace cikin kuka ta fita. Tana saka
kafa a waje daga ita sai towel wani sanyi ya kwararo mata. Sakata yasa ya rufe dakin sai
yayi kwanciyar sa.
“Sai dai idan gobe ki shigo amma yau kisan nayi”
Dakin Sameera ta wuce da kyar sabida cinya dinta yana ciwo anfi zabga mashi belt, gashi
yanzu tafi gani da ido daya. Sameera tana sallah isha lokacin sai Laila ta tsaya tana jiranta.
Dama raka’ar karshe ne saita juya ta soma kallonta, tana ganin yanayin ta tasan sunyi
sana’a. Anan Laila ta duka har kasa tana kuka, “Anty dan Allah ki taimaka min da Pad da
kaya”
“Ikon Allah yau kuma nine Anty” Sameera tace cikin ranta. A fili mikewa tayi domin taje ta
duba, yanzu kwana takwas kenan datayi batan wata. Yarta Sadiya watan ta goma sha uku,
kawai tunani Sameera takeyi kamar tanada shigar sabon ciki.
Cikin sa’a ta samu ragowar Always guda uku da sabon pant, saita dauko mata atamfa riga
da zani. Jikin Laila duk shedan duka ta soma tunani kodai Saif ne, amma kuma bataji karar
ihu ba. To a ina ta samu wannan tabo? Sai ta tuna tun safe tabi wasu mata ko sallama
batayi mata ba ta fice abinta. ‘Bariki alalen gero idan baka iya ba sa ya chabe maka”
Anan ta bata izini inda ta shiga uwar daka dinta a karo na farko, canja kaya takeyi tana
kare ma wajen kallo. Ya bala’in haduwa kamar banata ba. Kudi tagani masu yawa akan
durowa. Saita soma tunani gwara ta dauka koda dari biyar ne domin rage wani zafin. Dari
takwas ta kare da dauka yan dari biyu. Haka ta dauka tasa a gefen zaninta. Ita kuma
Sameera tana sane da kudin an kavwo mata ne zata hada kayan souvenirs.
Daga nan Laila ta soma mata bincike durowa bayan durowa tana kallo, anan sai ga Abul
Khair ya shiga ciki da gudu, “Anty Amarya ance idan kin gama kizo kici… Anty me kike
nema?”
Hannu ta saka a bakinta alamar yayi shiru, saita yi mashi dakuwa sannan ta saka hannua
wuya alamar zata yanka shi idan yayi magana. Saita soma magana, “Muje dama yanzu zan
fito” yadda Sameera dake falo zataji.
A falo taga an saka mata abinci, ranar Sameera shinkafa da wake da mai take jin ci. Haka
Laila ta tabe baki duk zaton ta zataci miyan dagedage ne da nama. Amma kuma taci sosai
tunda tana fama da yar gusau.
Duvet mai laushi da pillow Sameera ta ajiye mata akan 3 seater domin ta kwana wajen,
sai tace mata saida safe zasu kwanta da wuri gobe akwai school. Bayan ta gamaci ta kai
kwano kitchen domin ta ajiye. Anan ta soma dube dube tana kallo tareda bin Sameera da
ashar na rashin dalili. Har taso ta kunna gas kadan idan Sameera tazo ta kone kurmus,
saita tuna batada masauki sai nan kafin ta koma nata dakin.
**
Anyi ma Haske karin ruwa tareda alluran barcin, ana saka ran zata farka wajen 10. Sai su
Lantana suka koma domin dauko kaya, ita ma Mommy ta samu labari taje wajen domin ita
ta canje Lantana inda daddy zai mayar da ita.
“Uhmmm hmm” Ammi tace batada niyyar tashi balle ta nuna ta damu, Mommy abin yayi
mata ciwo saboda ciwo yana kan kowa. Yau Kaine gobe waninka. Sanda Haske ta tashi ta
soma magana, mommy duk zaton ta ruwa take nema saita kai mata. Damtse bakinta tayi
taki sha saboda ba abinda take nema ba kenan. Kasa kunne Mommy tayi sai taji;
“Bilal”
Kallo ta bita dashi, bata san dalilin zuwanta asibiti ba kawai ance zuciyar ta ya buga.
Amma neman Bilal nameyi takeyi?
“Mijina” ta fada wannan karan da dan karfi. ‘Kin makaro’ Mommy tace cikin ranta. Zuwa
tayi dab da ita ta rike mata hannu. Matsawa tayi idan Haske ta sake bude ido fiye da nada.
“Bilal baya nan… Bari Kisha ruwa tukun” saita kai mata ruwa bai, “Karbi yi maza” ita ma
tana san ruwan saita sha fiye da rabin kofin kafin ta sake cire bakinta.
“Mommy ina Mijina?” tace tana hawaye.
“Zaki iya tuna abinda ya faru da rana?”
Runtse idanu tayi ta cigaba da kuka, komai fes take tunawa bata mance dibar albarkan
datayi mashi ba. Abinda yafi sosa mata rai shine yadda ta zabga mashi mari. Hannun ta
soma mitsikewa tana dana sanin abinda tayi.
“Mommy please ki kira min Bilal na roke shi gafara.” kallon yanayin ta Mommy tayi.
Gafara name kuma bayan shine da laifi?
“Mommy ki taimaka min na gane gaskiya, Bilal bashida laifi ashe duk makircin Laila da
Ammi ne… Mommy ki tayani bashi hak’uri kafin na rasa shi… Bazan iya rayuwa batare dashi
ba, ya dawo mu raina yaran mu”
Jikin Mommy yayi sanyi, batasan me zatace ba. Haske batayi amfani da hankali da ilimin
taba. Jibe yadda ta yanke aurenta babu abinda ya shafe ta. Mutane suna tsintar kansu cikin
rayuwa wanda yafi nata kuma suna hakuri, aure ibada ne kuma aljanna sai anyi jihadi.
Murza mata hannu kawai tayi batace komai ba. Suna haka sai Daddy ya shiga.
“Harta tashi? Alhamdulillah” saiya karasa wajen. Kallonsa tayi tana kuka, “Daddy ka
taimaka ka bama Bilal hak’uri dan Allah. Wallahi sharrin Laila ne da Ammi”
wannan abu yanzu da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa. Shima shiru yayi sai daga
bisani ya Kalle Hajia Binta, “Bakiyi ma yarki bayani bane halan ta mance yadda ta tozarta ni
dazu!”
Runtse ido Haske tayi tanata kuka, tasan ita mai laifi ne kuma dama dan adam tara yake,
how do they expect her to be perfect? Su basa kuskure ne? Koko komai sukeyi daidai? Ita
ba alan musuru ba ta ina zata gane Laila muguwa ce kullum tana kiranta da Besty, abu
daya ta sani Laila nada san banza and we all aren’t perfect, amma not in a million years tayi
tunanin Laila binta da sharri take koma tana bakin cikin aurenta. Bayan itace ta rinka
zugata wajen Bilal, sannan data biye ma Laila da tun kafin aure ta bashi kanta.
“Dan Allah Kuyi hakuri, idan Bilal ya yafe min komai zai daidaita”
Daddy ya fito da waya daga aljihu domin ya kira Bilal, Mommy kuma ta soma bude flask
zata hada mata shayi tasha. Sunji dadi babyn yana lafiya babu premature delivery babu
komai.
Not reachable yaji inda ya tabbata wayan a kashe yake. Shi kuma Bilal yana zuwa gida
yace ma Mallam Musa karya bari kowa ya shiga duk wanda yazo yace tunda ya fita bai
dawo ba.
Haka ya koma daki yayi tagumi yana tunanin yadda Haske ta iya watsar da komai nasu,
duk yadda suka tsara rayuwar su akan kawa, kawar ma Laila. Waifa Laila dai!
Wani Jallabiya dinsa sabo Brown mai hula yasa da zashi masallaci, ya saka hular babu
wanda ya gane shi kuma ana idarwa ya fita. Shi yafi jin dadin sallah cikin jam’i dayayi a
daki abinsa. Da sauri yayi tafiya zuwa gida baiso yan unguwa suyi mashi magana.
Kashe gari haka Haske tayita saka bala’i sai an kira mata Bilal, anan aka bata waya domin
ta gwada da kanta, taji switch off hankalin ta ya kara tashi. Sai da safe da Fijr taje asibiti taji
yadda akayi, Shima Mommy take bama Babban wansu labarin yadda akayi ta waya.
“Ke kam Anty dan rashin hankali dan kawa kika kashe aurenki? Kawar bana arziki ba sai
Laila sai kace makauniya bakya gani?”
“Fijrr”
Mommy tace domin tayi shiru karta kara tada ma Haske hankali, Doctor yace ayi mata
abinda take so kafin jininta ya kuma hawa. Amma yanzu kam abinda take so bamai yiwuwa
bane.
Dama tace ma Daddy idan zai dawo ya kai mata wayanta, anan ta hau WhatsApp zata yi
mashi sako, taga baya existing ashe yayi deleting number dinsa daga duniyar WhatsApp.
Sai tayi mashi text yakai kala goma na ban hakuri yazo ta yarda dashi yanzu dari bisa dari.
Anzo maganar cin abinci tace bazata ci ba sai taga mijinta. Babu darun da ba’a yi da ita ba
saita fashe da kuka tana shesheka.
Daga nan tace zaman asibiti ya isheta a mayar da ita gidanta, kokuma a kawo mata Bilal.
Daddy da kansa yaje gidan aka ce bai dawo ba tun jiya. Anan Haske ta shake shiga cikin
tashin hankali,tunani kala kala kardai ace yayi accident ko wani mugun abu ya faru da shi.
Kanta ta soma jijigawa tana fizge fizge, Tuni ECG din ya soma hawa da sauka kasa alamar
disturbance jikinta. Babu arziki akayi mata allurar barci dan tana barazanar saka kanta da
danta cin halaka.
Haka akayi kusan kwana 8 babu Bilal babu alamar sa, har Immigration anje an duba ko ya
fita Kasar akace passport dinsa na nuna bai fita ba. Hankalin kowa ya tashi musamman
Haske. Dama bayan kwana biyu yace ma Mallam Musa ya kira abokinsa yazo ya dauki
motar sa ya mayar gidansa koda an leka gidan baza’a ga komai ba.
Mallam Musa ke siyan masa abinci ko a Zaria Road ko a Chicken Republic ko Chinese
Restaurant. Yana kokarin cire Haske sannan ya dauki kaddara, baisan meyasa ta guje shi ba
amma yana fatan Allah ya mayar mashi da wanda yafi albarka. Tsakanin shi da Laila
wannan shari’a sai a lahira amma kuma randa zasuyi ido hudu zata sha mamaki.
Auren Banan kuma yana nan bazai fasa ba, koba komai saboda shima ya shayar da ita
bakin cikin datayi mashi. Yasan bada dadewa ba Laila zata nuna mata halinta.
Haske bayan an sallame ta da kanta taje gidanta amma ba’a amsa ba tayi bugun duniya
Mallam Musa yana jinta yayi banza. Umurnin da Bilal ya bada kenan koda Haske taje kada
ya bude duk da baya tsammani zata bayan diban albarka da tsanar datayi mashi farad
daya. Kawai bai so taje ta sake mashi rashin kunya ne, dab yake kafin zuciya ya debe shi ayi
abin kunya.
Ita kuma batada wani sana’a yanzu sai kuka, dashi take kwana dashi take tashi. Tayi baki
ta rame sosai kashi da rai jijiya da wahala. Mommy tana hanyar gidan kullum kokuma ta
waya tana mata nasiha. Akan ta fawwala ma Allah komai domin shi yasan daidai, balle
dama a duniya sai anyi maka jarrabawa kafin ka gane darasin, Allah yasa ta canza akan
gaba.
Duk maganar nan da ake mata baya shigan ta, kawai Bilal take so ya maida ta dakinta. Ta
yarda achan saiya hukunta koma menene ko dukanta ya rinka yi yafi mata wannan zaman.
Gabanta sake faduwa yake yi idan ta tuna zaman zawarci takeyi, wai da gaske bafa wasa
bane tabbas aurenta ya mutu.
A kwana a tashi har satin auren yayi, Saif ya gama gininsa tsab sai san barka. Tun farkon
shigan satin ya tafi Osun da Bukola inda zasuyi auren. Yan uwansa ranar daurin aure zasu
je. Sun dinka anko kala uku wanda zasu gwangwaje shida Bukola leshi daya dinkin ne ya
bambanta.
Akwai purple, blue da fari. Hular sa irin an karkata dai. Duka danginta sunata yabawa da
kyansa kuma yanata barnar kudi, duk kudin pure water da baya amfani dashi yanzu ranar
su yazo. Alhaji sama Alhaji kasa ake ce ma shi, dama idan kaga bayarabe yace maka Aboki
bakada ko sisi. Aboki shine coblar ko mai tea da biredi, Alhaji kuma mai farare bugun
Abuja.
Shima Bilal sai satin Bikin ya kunna wayarsa, anan yaga msgs kacha kacha daga kusan
kowa nashi. Haske dana Umma nasu yafi yawa. Ko karanta na Haske baiyi ba yasan cewa
zagi ne Laila zata zugata tayi mashi. Tas nata yayi deleting bai bude ko daya ba balle yaji
haushi. Ya duba na Umma inda take masa fatan alheri duk inda yake.
Abin mamaki duka Text din Banan, banda na tambayansa kudi babu ko ya lafiyan sa.
Wannan na karshen ce masa tayi zatayi events kala biyar; Bachelorette Party, Kamu,
Mother’s day, Dinner da Polo. Ta bangarenta wajen Alhaji Bello take zuwa karbar kudi tun
da bata samun Bilal.
Daren da za’a shiga ranar auren Haske ba tayi barci ba, kuma taiji labarin auren yana nan
babu abinda aka daga, da kanta take shiga Instagram tana kallon video da Banan ke
posting. Biki takeyi sosai na zamani.
Kuka takeyi sosai, batama performing sosai a wajen aiki inda aka tace masu batada lafiya.
Anan supervisor dinta suka bata hutu ta dawo sati mai zuwa, akwai sabbin yan bautar kasa
da aka dauka yanzu sunada ma’aikata sosai.
Yanzu tana samun dama tayi kuka sosai abinta, ran auren tafi shiga tashin hankali wai
Bilal dinta ne zaiyi aure. Wajen sha daya na safe ta tafi gidan su. Ta kofar baya inda kitchen
yake tabi yadda mutane basu da wani yawa kuma basu santa ba taje. Dakin Ummansa taje
ta zauna.
Umma tana ganinta ta tausaya mata ainun, amma itama yanzu batasan inda yake ba.
Kawai sunsan idan yana fushi haka yake zama quiet na kusan wata koma kasan haka
domin yayi tunani kuma harya huce. Saboda idan ya zauna cikin mutane zai sauke masu
haushin sa yana zage-zage da rashin mutunci.
Suna cikin haka ne sai sukaji magana yana tashi, “lyye Ango kasha kamshi, angon Banan
bada kanka a sare” tare da guda yana tashi. Runtse ido tayi gabanta yana fadi, yau koma
menene saita koma dakinta, ta dauki alwashi har kasa zata duka tana mashi kuka.
Dayake bai yi tunanin ganin Haske ba kai tsaye dakin Ummansa ya shiga, yazo ne ya gaya
mata tayi hak’uri ba zai iya auren Banan ba. Haske ma wanda ya yaba da halinta tayi
breaking heart dinsa balle Banan. Bayaso ya aureta ya kuma saketa tunda ya san dakyar su
yi sati biyu, zuciyar sa nada yanzu ya dawo abu kadan ke kullar dashi.
Da sallama ya shiga bayan ya matsar da labule, saida ya zauna a kujerar mirror sannan
yaga wanda ke gefen Umma, badin yayima Haske farin sani ba bazai taba cewa ita bace. Da
Haske da Umma aka amsa sallama, yana cikin gaisuwa da Umma yaji sautin kukan Haske.
Shima yayi duhu ya rame, Umma sa ta tausaya masa kuma ta fatan ya maida Haske dan
harga Allah tana santa a mtsayin surika.
Mamaki cikin rana yake yi meta zo yi anan bayan tace bataso ta hada dangi dashi, yanzu
kuma tazo. Koda yake ita ba matsalar bane. Abinda ke cikin sa ne ya hada alaka dashi.
Kuma ya bude account wanda zai rinka ajiye mata kudi na amfani, idan ma bataso ta raina
dan bai damu ba zai rike abinsa ya zama masa uwa da uba, kuma Umman sa zata taya shi.
Shiru yayi yanaso yayi ma Umma magana cikin sirri, kuma bai so yace ta tashi suyi siri
Haske ta dauka zancen ta zasu yi, dabara ya fado mashi sai yayi ma Umma text.
“Umma kamar wayanki yayi haske, ki duba ki gani” sai ya mika mata wayan dake gefen
sa. Tana karba ta duba nazari ta soma, tayi kusan minti uku batace komai ba. Sai ta daga
ido ta kalli shi sai ta sake karantawa. ldan idanta bai mata gizo ba ya fasa ne, amma akan
wani dalili?
Mikewa tayi ta wuce dakin Abbansa domin ta nuna mashi text din, sannan kuma ta basu
waje. “Ina zuwa yanzu zan dawo.. Jirani”
Bayan tafiyar ta shiru banda sautin kukan Haske, idan ma bazai tambaya ya lafiyarta ba
yaci ace ya tambayi lafiyar abinda ke cikin ta wanda ajiyar sa ne. Dama yace mata zata yi
kuka akan Laila gashi yanzu idanta har zafi yake mata sabo da kuka. Kullum tana cikin shan
magani saboda ciwo. Watau har zai ce ya daina santa kenan! Ashe karya ce yalke mata idan
har cikin karamin lokacin nan ya daina.
“Dan Allah Sweet kayi hakuri” kallon gefe da gefe yayi yaga ko shine take cewa Sweet.
Magana ta cigaba wanda wannan karon ya gasgata tunanin sa.
“Na gane kuskure na, na gane komai yanzu. Na gane cewa abinda kake fada min gaskiya
ne. Please sweet ka yafe min muje mu raina yaran mu tare. I promise to be the best wife, na
rantse bazaka yi sani ba. Na gane irin soyayyar da kake min gaskiya ne”
Tunani ya soma, ganin yadda ta lalace ya bashi tausayi amma kuma wanda zai iya tafiya
daga gidan aurensa akan kawa ba wanda zai iya yarda dashi bane. Yanzu ya fara dawowa
daga soyayyar ta. Bai iya tsammani yanaso ya zauna da ita. Zama shi kadai yanzu ya fi
mashi kwanciyar hankali. Kuma ya gama auren Shamsiyya koda tana suma tana farkawa
ne. Danna wayarsa na rashin dalili yakeyi ko kallonta balle ya nuna ya gane dashi take
magana.
“Dan Allah fa nake rokon ka badan halina ba.. Haba Sweet ko Allah wanda ya halicce mu
idan muka nema gafara yana yafewa please ka tausaya min, wallahi bazan iya rayuwa
batare da kai ba”
“zan mutu fah” tace sai ta fashe da kuka.
Tsam ya mike ya fita daga dakin ya tafi wajen Abbansa da kansa domin ya fada da gaske
bazai iya auren Banan ba. Anan yaga Alhaji Bello yanama Umma fada, itama ta gaji da boye
sirri nan ta tona asalin halin Banan. Anan yace mata Allah yasota da anyi auren da ya dauki
mataki akanta.
Kiran iyayen Banan yayi ya sheda masu ga abinda suka dauka tareda basu hakuri da fatan
alheri. Banan tana daki tana sisinar hodar Iblis ga waka yana tashi kamar zai fasa kunnen
mai sauraro, a lokacin Babanta ya kirata ya gaya mata. Sam bata yarda ba duk zaton ta
hodar ke mata karya. Dariya kawai takeyi ta cigaba da sisina cikin kwarewa, idanunta suka
kada kwakwalwarta ya soma chaji. Rawa ta tashi ta soma sannu a hankali tana layi kamar
zata fadi tareda tambele. Ta dauki alwashin idan ya sake jikinta zata wajen dealer din ta
zageshi saboda ya saida mata mara kyau, saboda haka kurum bazata rinka ganin kamar
ance an fasa aurenta
Nisa Alhaji Bello yayi sai ya sake tambaya Bilal ko yanaso aje gidan su Zailani ayi masa
bikon matarsa, sai yace baiso Allah ya zaba mashi mafi alheri.
“Amin Summa Amin” wannan kenan!

About Ismail

Check Also

HASKE CHAPTER 25

HASKE CHAPTER 25 Sati daya cip Saif yayi a dakin Bukola bayan nan ya koma …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *