[Advertisements⬇️]

HASKE CHAPTER 21 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 • HASKE


 • CHAPTER 21

 • Bayan wata biyar

 • Kwanci tashi babu wuya wajen Allah, cikin Haske yanzu ya fitowa kowa yana ganin sa. Bilal yana nuna rawar gani sosai domin yaga bata rasa komai ba. Yama bukaci tabar aiki amma tace ‘An idle mind is a devils workshop’ kuma ba wani aikin wahala takeyi ba. Gwara ta rinka fita tana motsa jiki. Ummansa itama tayi farin ciki sosai dataga cikin. Saidai tun bayan da Banan taje ta karba number dinsa bata sake waiwayen taba. Duk wani fadanci da magiya yanzu ta watsar, bama nan gizo ke saka ba sai da suka hadu a wajen biki. Nan taga asalin halin Banan.
 • Dinki tayi mai bayyana kirji, gashi ta saka push-up mai uban kauri, nan rabin kirjinta a waje kamaryadda turawa keyi. Saboda wajen 8 inches akayi yankar ta gaba, baya kuma 11 ne watau show me your back. Bata saka mayafi ba sai kisto datayi da gashin kanti, sannan takalmi shima 6 inches ne tana tafe kamar agwagwa. Hankalin kowa yana kanta ita kuma sai dariya takeyi tana rangaji dakai. Anan akayi ta tsegumin akan wanda zai yarda ya aureta, Umma bata nuna ma yan ‘bikin tasan Banan ba. Kawai ta soma defending dinta haka nan. a
 • “Toh ai saka kaya daban, halin mutum daban. Hali zai kwace mace gidan aure.Yanzu masu saka nikab sai kiga basuda kirki” Babu wanda ya kulata saboda kana ganin abun kasan babu hankali a ciki, anan aka saka waka. Banan ta fito ta bude taron da rawa.
 • Aikam ta iya daga Soko,Aje, Penalty da Boda Luku babu wanda batasan yadda rawar zaiyi armashi ba. Wata ta sake tsaki tayi magana. “Na gaya maku wancan asalin yar iska ce batada kintsi. Gaja kawai”
 • Allah dai ya shirya” Umma tace Taso ta kira Bilal akan maganarya bincika halin Banan, sai kuma ta rasa ta inda zata soma. lta ce tace ya aureta mutumiyar arziki ce, yanzu kuma batasan ta inda zata fara cewa ga akasin haka ba.
 • Ganganci tagani nata, ta yanke hukunci babu bincike. Sai ranta ya bata kila fa asiri sukayi mata. Tunanin ya mafi kwanta mata inda ta tantance hakan ne. Auzubillahi tace cikin ranta tana fatan ya karye kila Bilal ya kore Banan da kanshi.
 • To datake daman yar ajinsu Umma a islamiya na Almannar ke aure, kuma asabar ne saida umma ta biya makaranta. Da Hijab dinta taje reception din. Banan tana ganinta kamar zata kashe kanta dan haushi. Mirsisi tayi kamar bata ganeta ba dukda saura wata daya auren ta da Bilal.
 • Kwata kwata bataso ta alakanta kanta da mai saka hijab cikin biki ba balle ayi tunanin sun san juna. Mamaki takeyi wai duk Umma sai ta saka Hijab kamaryar kauye. lta yanzu karan kanta batada Hijab ko daya. Sallah bawai yana gabanta bane, ita bata sallah sai tayi mugun mafarki. Haka kurum batasan annabi ya kafu ba. ldan ta wahala cikin mafarki ta tashi a firgice saita yi sallar lokacin, walau asuba ne kona azahar. Da kimono take sallah da mayafi idan ya kama, Umma kuma sai kokari takeyi su hada ido. Koba komai suyi majuna murmushi. Banan ta murtuke fuskanta tareda

  kallon gefen. Haka dai Umma ta hakura. Ana cikin haka ne sai aka saka wakar “Kiss Your Hand” tsoho ne na Wande Coal, ashe yana kai mata karo. Nan ta tashi ta soma zaro harshe tareda karkata wuya. Sai mutane suka

 • soma tafl ana ihu. Anan wasu gayu suka fito suna mata liki. Wata tsohuwa aka bama ragamar kwasan kudi, tana cikin aikinta sai ta ture Banan cikin rashin sani.
 • “Mama wannan wani irin iskanci ne ina rawa zaki ture ni!”
 • “Haba yarinya koba komai kin ce min Mama ai, bai kamata ki bini da zagi ba. Tunda kin lura zan haife ki”
 • “Bansan jin wani magana, Kina sake tureni saina sharara maki mari. Mu zuba!” 
 • Anan ta soma rawarta kamar babu abinda ya faru, tsohuwar tayi kwafa tabar wajen. Umma taga duk abinda ya wakana. Jikinta yayi sanyi ta tsora‘a da Banan. Nan ta sinna kai kasa kafin ma su hada ido tazo tayi mata nata diban albarkan. 
 • Bayan bikin saita koma gida, tana isa taga sako daga wajen Haske. Dama haka takeyi bayan sati biyu ko daya tana su snacks ta aika ma Umma, su Mommy wata sa’in harda Laila. Wannan Karon meat balls tayi da samosa mai uban yawa, sai kuma smoothie. Duk sai Umma taji babu dadi. Jibi yadda Haske ke mata dawainiya da girmamawa amma tana jin labari batayi bincike ba kawai tajuya mata baya. 
 • Fatan ta daya kada auren su yayi lasting da Banan sabida yanzu gaskiyar zance bataso, amma kuma batasan ta inda zata fara bayani akan rashin kintsi dinta ba, time will tell. 
 • Ammi tabargidan Hajia Binta bayan rashin mutunci datayi masu. Tun ana wata uku 
 • bayan fitar ta a gidan Zailani. Wata rana Maimuna daya daga cikin yaran Mommy na zauna a falo sai Ammi ta dawo daga aiki. Bayan ta amsa sallama sai tace mata sannu da zuwa. Anan Ammi ta soma sababi wai Maimuna batada kunya, da aure akayi mata haka zata rinka yi harya koreta saboda mugun halinta wai jibe yadda ta amsa gatsal babu rinsinawa balle murmushi. Magana marasa dadinji ta bita. Kuka Maimuna tasha ba tace komai ba. 
 • Bayan nan Ammi tace ta dauko mata ruwa cikin fridge, Maimuna tana kawo wa wai bazata karba ba. “Wanna ai raini ne! Ya za’ayi ki bani ruwa kerere kamar sa’anki? Yan iska yara marasa tarbiya! Sannan haka zaki kawo min babu tray babu kom Bakina kike so nasa a kan gorar? “ kallonta Maimuna tayi, tana tunani saita tafl kitchen ta dauko. Tayi yadda tace saita dawo ta ajiye mata akan table dake gabanta. Tafiya take kokarin yi da sauri kafin Ammi ta soma, sai kawai taji an jawo ta tareda sharara mata mari. “Ke dan ubanki kin isa kimin zuciya! Dan na aike ki ne zaki rinka daure min fuska! Bake ba har Binta niba sa’anku bane shashasha tambadardu, halan me kuke dashi banda kaddara bazan zauna a gidan nan ba kamarkurkuku”
 • Nan ta soma kilarta, “Dan ubanki bakisan ina hakkon kiba, da kin ganni da kin koma daki da zama saboda Kinga dodo. Shegiya ku a dole rainon turai ba’a maku fada” saita cigaba ta kai mata dundu. “An daka! Nace an daka George Bush yazo ya kulle ni” Aikam a kunnen Mommy ta dawo daga anguwa tunda ita bata aiki sai abinda ba’a rasa ba. Anan Ammi tayi mirsisi kamar babu abinda ya faru. 
 • Mommy dakin Maimuna taje domin taji mai ya faru, ba yauba yaran sun saba kawo mata korafl akan Ammi yadda take yawan masu fada da zaginsu. Yanzu sun gwammace suyi lesson a makaranta dasu dawo gida. Sannan Islamiya da wuri suke fita, basa san abinda zai dawwamar dasu balle a zage su. Hajla Bmta ta yanke shawara yau zatayi ma Ammi magana. Kota bari Kota bar gldan. 
 • Dama kara tayi mata, gashi Zailani ya hana ta shiga gidansa tun sanda ya dawo ya ganta kwance a kan gado tana jiran shi da wasu nightgown mai bayyana suffan mutun. Mallam Adamu akayi ma kashedi karta sake shiga gidan kokuma a bakin aikin sa.Ammi na duba wasu takardu Mommy ta shiga, tasha jinin jikinta amma saita dake. Anan Mommy tayi mata bayani akan korafin da yaranta keyi. 
 • “Dakata Binta ! Karki cika min kunne da zance marasa kan gado. Nasan kin gaji dani kawai basai ki fake da yaranki watsartsu ba” abin yayi ma Mommy ciwo, itama tasha kunu ta saka ma idonta tozali. Dama idan an kaita bango tana mayar da martani. “To shikenan tunda muna maki babu dadi saiki tafi inda zaki fl samun kwanciyar hankali” 
 • “Aikin banza Binta baki isa kimin gori ba wallahi. Gidan da kike takama dashi yana sakin ki shikenan idon ki zaiyi bude. Balle bakida aikin yi lokacin zaki dandana kodan ki“ “Yanzu Hadiza meya kawo irin wannan maganar flsablllahi?” 
 • “gwara ki sani ne. Kema you‘re not safe. Namiji ba dan goyo bane kuma saki yana kan kowace shegiya. Dalla fita inajin barci gobe zan tafi na barki da bakin halin ki” 
 • Mommy ta barta ranta a bala‘in bace, wai ita Hadiza tayima butulci haka. Sai dai babu damuwa duniya ce ta ishe kowa riga da wando. Kashe gari Ammi da safe ta fara tunani inda zata tafi. Sai dabara ya fado mata akan ta nema daki a staff quarters. Aikam vice principal admin taje tayita mai kuka inda aka ji kanta aka bata dakin boys quater. ‘Daki daya da bayi da kitchen. Taji dadi abin sosai basai ta kashe kudinta ba, tasan daga nan kila sun shirya da Zailani ta koma dakinta. 
 • Har yanzu dai tana business dinta na computers, babu wanda ya lura saboda kowa ya aminta da ita. Balle gatada fadin rai da nuna tafi  komai babu wanda zai zarge ta. 
 • A department dinsu kuma ta soma canza masu fuska, kawai ta tsargu kamar suna tsegumi akan mutuwar aurenta. Saita flta harkan su ta koma aiki ita kadai. 
 • Idan an kawo abu na department idan ya biyo ta hannunta babu wanda zai sani. Ko workshop akeyi akace ta kawo volunteers saidai taje ita kadai. Balle yanzu workshop ana bada kudin kashewa. 
 • Abin ya soma basu haushi sosai suma sun fara gajiya da halinta, irin yar murmushi da suke mata sun daina. lta kuma ko’ajikin tana ganin sune a kasa. 
 • Anan suka rinka kallon yadda take abubuwan ta, sai sukaga tana flta da computers tana siyarwa. Kyale ta sukayi ta cigaba hankali kwance saboda tarko suka dana mata bata sani ba. 
 • Ta dauko computers da printers zata fita dashi, balle computers din akwai  dankare akai baro baro. 
 • Tana tuki ta wuce wani waje da ake kira T Junction inda daga shi sai Gate. Sai taga an fara checking motoci ana duba boot dinsu. Gabanta yayi mummuna faduwa tana kokarin reverse sai wani mota ya tare ta Shima ya tsaya a bayanta yanaso ya fita
 • Hawaye suka soma ciko mata amma tayi kokarin saisaita kanta, duk yadda zatayi bata zata barisu gani ba. 
 • Da hannu sukayi mata alama ta karasa mana bakin gate, haka ta tafi fargaba kawai takeyi. Anan ta soma Ayatullah kursi tana neman sa’a. 
 • “Hajia Hadiza ina wuni?” “Laflya naga kuna duba bayan mota” 
 • “Yanzu harda mu tsoffin malamai” tace tana barkwanci “Har principal, in fact k0 gwamna ya shigo sai an duba.. Bude mana sauri nikeyi please” 
 • Nan take ta fashe da kuka tareda budewa, sai ga computers din makaranta cikin boot. Kallonta sukayi suka sake kallon kayan. Alama sukayi mata tayi parking. 
 • Nan aka kira principal aka sanar mashi, kan kace kwabo wanda suke wajen sun soma daukar video suna yada zance. Haka aka ingiza keyarta har admin block. 
 • Anso a kira mata yan sanda amma tayita rokon alfarma akan su yafe mata, anan aka Koreta nan take. Kuma dole ta biya kudin duka satan data rinka yi. Dama ita wannan satin zatayi arranging boys suzo ayi satan karya inda zata wanke kanta, yanzu me zata gayama yaranta da sauran yan uwa. In fact Ina zata koma tunda ance tabar boys quarters anyi mata korarwulakanci . Wannan kenan! 
 • ldan Fijr tana kaunar zuwa wajenta tana kaunar mutuwar ta,Ammi tana missing baby Hafsa saita saka akai mata. Gashi yanzu Ammi batada kayan daki ko kadan tayi fallin zawarci dashi. Lokacin farkon barinta tana sha idan taje ta kwashe kayanta ta sayar Daddy zaiyi shiga taitayin sa idan ya lura itama tayi zuciya dashi. Dataga babu sarki sai Allah shine fa ta rinka binsa tana roko kafin yayi banning dinta daga gidansa baki daya. Yanzu babu komai dakin sai katifa da fanka da ledan kasa. Gashi Ammi nada bala’in kazanta. Ta riga ta saba Haske na mata hidima sannan sai masu aiki. Yanzu ta sangarce sosai koda ta tashi sai taji kasala tayita kwanciya abinta. 
 • Abin da ke kara bama Fijr haushi wai ace maimakon Ammi ta kira Baby Hafsa kamar yadda kowa ke cewa, sai tace ‘Hassatu ko Hasse’ Fijr harta gaji da gyara mata. Yanzu haka ta yanke zuwa wajenta. 
 • Baraka ne take zuwa koda yaushe idan ta dawo hutu. lmran shima yakan je amma baya kwana. Yadda taso ta rike Anisa fafur Daddy ya hana. Ita ma Fijr taso haka sabida ta samu yar goyo da zuwa anguwa. 
 • Daga Ammi har Laila basu san Haske tanada ciki ba, tun bayan suna Haske sau biyu suka hadu da Ammi, Shima lokacin cikin yana sabo. Sanda ya girma ta koma staff quarters tabar gidan Mommy balle su hadu. 
 • lta ma Laila yanzu Saif ya sake daure mata, ya birkice mata ta rasa gane shi. Bayan fada dayake yi da yanzu ya sake sabo wanda yafl nada. Koma ya hanata, tanaji tana gani babu damarma. 
 • Gullisuwar ma ta daina yi, bayan kwana biyu take aika ma Banan neman suna, gashi ita Banan bata san abin. Masu gadi take ba suci suna godiya. shima Saif haka yake murje ido ya sha san ransa. Kullum yace bashi zai biya kudi.
 • Sun nakasa ta sosai jari ya karye, gashi babu damar taje gidan Haske ta dauki madaran ta. Ta lura katon gwangwani biggest peak Bilal ke siyan mata, kuma idan ta dauka babu damuwa. 
 • ltama Haske bata fiye zuwa gidan Laila ba tunda ta lura Bilal bayaso, kawai dai aike take mata na kayan kwalama. Sanda kuma suka hadu a gidansu Laila Baaba ce babu lafuya. Haske tana Sanye da Hijab sai Laila tayita binta da ido. Kasa hakuri tayi tace 
 • “Wai Haske ciki gareki halan?” “Ba ciki ba, baya ne” Haske tasha ta sani kawai tanaso suyi raha ne, ita kuma Laila 
 • hankalin ta yayi bala’in kwantawa. Sabida Laila ta fara gajiya, haryau batayi batan wata ba. Wanda aure bayanta duk sun dauke ciki banda ita. 
 • Yasa take addu’a kada Haske ta samu, duk su zauna a hakan. Bata hakura haka saida ta kira Ammi taji daga bakinta, anan ta sheda mata dacewa da tanada ciki kila da Fijr ta gaya. Yau Laila zata gidan Haske bayan watanni masu yawa. Murna takeyi kamar anyi mata albishir. Balle Banan tace tayi kokarin taji sirrin auren su ta gano mata meye matsalar su yadda zatayi amfani da abin sosai. Babu yadda Laila bata roke Banan akan ta yarda su zauna a gida daya da Haske ba amma taki. Tace mata tanan zata musguna mata sosai da makirci. Yadda ma duk ranar girkin Haske saita tsira ciwon karya yadda Bilal bazai iya kwana a dakinta ba. 
 • Banan taji dadin abin amma kuma bataso ta hada inuwa daya da Kishiya, bata kaunar ta balle tayi sha’awar zama da ita. A wajenta da kishiya gwara bakin miciji. 
 • Bata gaya masu zata ba, ita kadai tayi shiri abinta. Tanaso taga ya zamanta kewar su yake idan babu kowa. A kwai wasa da dariya tsakanin su ko pretending sukeyi dan mutane su sha suna zaman lafIya. Ce ma Saif tayi Haske babu lafiya, abinda yasa ya barta saboda yadda Haske ke masu dawainiya da kayan abinci. Kuma yana kyautata zaton zata dawo da tsaraba. Shi kuma yanzu da Bukola sun hada kansu, soyayya sukeyi sosai. Bayada aiki kullum saiya kashe mata kudi. Wata sa’in ita take cewa ya bari. Gashi duk kawayenta sai aure sukeyi, da kanshi zai ce please zai taimaka mata da kudi na asoebi. Abin ya nuna girma kuma Bukola ta yaba da halinsa, ya nuna Saif yasan ya kamata sosai. Hajia Mujibat dai tana kallon su tasan akwai kullaliya tsakanin su. lta batasan Bukky ta aure bahaushe saboda yawan saki. Anan ta kira Saif tayi masa bayani, balle har Bukky ta aure mai mata biyu. Kuka wiwi ya barke dashi wai yana bala’in santa. ldan suna so sai ya sake duka saboda shidai ya samu aurenta. 
 • Hajia Mujibat ta hana shi haka, saboda bazata so ace wai an Sake Bukky akan kishiya ba. Abinda bakaso ayi maka kada kayi ma wani. Anan ta basu go ahead inda har weekend suna fita hutawa k0 motsa baki. Koda Laila ta isa falon, Haske tana sanye da crop top fari sol mai zanen heart, sai gajeren skirt na Jens. Shi kuma Bilal yana Sanye da muscle shirt da three quater. Tana kwance akan cinyar sa yana mata tsifa suna rapka hira, ga kuma cikin babu abinda ya hana shi fitowa. Laila tana labe ta bayan kyaure tana kokarin taji ko suna sirri. Sai ta jiyo har an majariri daki, kusan komai an gama siya sai abinda ba’a rasa ba.Ta bala’in gigicewa tayi losing balance dinta, anan ta soma tangal tangal ta shiga ciki. “Innalillahi! LafIya Laila kamar wanda aka biyo ta?” ita kuma Laila zufa ya soma karyo mata dataga cikin da idonta. Bata boye bakin cikinta ba karara tayi magana.”Shine baki gaya min kinada ciki ba duk yadda muke tare?” “Ban gene bakisan inada ciki ba, ai wannan cikin yafi hasken rana bayyana” “Wa‘alaikumus salam” Bilal yace tunda ita ba zata yi sallama ba. Anan ta soma sosa gemu tayi. 
 • Baiko kalleta ba banda harara daya jefeta dashi, sannan yaje ya runguma Haske ya 
 • sumbaci goshlnta. Tareda mata magana cikin rada, sannan ya sumbaci cikin saiya sake watsa ma Laila harara. Duk ta muzanta saboda asalin soyayya ta gani. 
 • “Sweet bari na shirya na fita” “Okaya dawo lafIya” Hannun Laila Haske taja domin suje dakinta, suna shiga Laila ta sake magana. “Meyasa baki gaya min kinada ciki ba” “toh meye matsalar ki dani? Ke bakida ido ne? Bansan gulma!” Abin ya bama Laila mamaki yadda Haske tayi mata, ita kuma Haske abin haushiya bata kamar Laila na yin mata bakin ciki. Dukda tasan ba haka bane anma wani ya gano zai fassara a hakan. “Okay Allah ya baki hak’uri, ni kawo min kayan motsa baki” Anan Haske taje kitchen ta zuba mata yam balls da liver sauce sai Fanta. Koda ta dawo Laila tana mata dube dube cikin durawa, bata kuma fassara ba sanda ta ganta. Sabon bedsheets ta gani kuma Bilal ya siya Wanda za’a shimfida na fitar suna. 
 • “Wannan yamin kyau gaskiya ina bala’in so“ Bilal ya siya amma kuma tana bala’in kunyar Laila. Rai bai soba ta bata, gashi daga Italy aka kawo zaiyi kusan dubu hamsin a kudin Nijeriya. Zatayi ma Bilal magiya idan bai siya wani ba sai su saka mai arha ranar suna. Da sauri Laila tasa a gefenjakarta karta mance dashi, suna hira Laila na kwasan girki har sukaji motar Bilal ya fita. Anan Laila ta tambaya ina birth certiflcate din Haske tanaso tayi mashi applying abu ne zasu samu ganima. 
 • Haske ta mike taje dakin Bilal inda suke ajiye dukwani muhimmi abu walau fllin gida, 
 • takardu na makaranta etc. Laila tana labe a bayanta tana kallon inda taje, saita koma daki da gudu kamin a gane 
 • Durowa ne mai number amma Haske bata saka ba da zata flto, idan Laila ta gama hoton certificate din sai sata mayarta rufe. Bayan ta mika mata saita shiga bayi, tunda cikin ya shiga wata shida tanada bala’in fltsari. Da sauri Laila taje dakin wajen durowa, nan taga takardun gida guda uku, daya kuma sunar Haske ke kai. Anan bakin ciki ya sake mamaye ta harda kwalla wannan karan dan haushi. Wai ta tsaya wasa har Haske ta samu fili, Sannan sai taje bedside drawer na Bilal tana dube dube, anan taga kudi ten thousand dollars na business din Bilal. Duka ta kwashe da takardar gida mai dauke da sunar Haske dana Bilal daya. Tana zaune sai ga haske ta fito daga ban daki, anan ta mika mata birth certificate akan ta mayar. Koda ta koma batayi tsammani Laila zatayi bincike ba rufe drawers din tayi saita bar dakin. 
 • Ranar kamar ba Laila ba ita data saba zama har magrib yau itace kamin azahar wai zata tafi Saif yace karba dade. Haske tana tafiya dakyar dakyar irin na masu ciki abin sai bama Laila haushi yakeyi amma tasan daga yau koma zai mata fes. Wahalar datake sha yau zai wanku. 
 • Driver tasa yakaita gida tareda bata dubu biyu, yau bata iya tsayawa diban kayan abinci ba. Tsoro takeyi kamin Bilal ya dawo, Bayan azahar ya dawo da wasu kaya ninki ninki. Cradle din baby aka kawo daga Dubai. Shima yayi mamakin rashin ganin Laila amma kuma sai yayi murna tunda ta samu damar gane nan gidan ba’a santa gwara ta daina zuwa. Mai gadi ya tayashi shiga da kayan ciki shi 
 • kuma yana waya da customer wanda zai bashi 10k dollars yanzu zasu hadu a Leventis roundabout. 
 • Yana zuwa durowa yaga wayam, ita Haske tana kitchen tana kokarin hada mashi abinci tun bayan fitar Laila. A fusace yaje dakinta bai ganta ba saiya nufa hanyar kitchen. Zufa karyo masa yayi sai numfashi sama sama yakeyi. “Kin dauka kudi ne a dakina?” A’a banma san ka ajiye ba” “ina nuf‘in masu yawa, 10k dollars” 
 • “Haba Bilal me zanyi da kudin business dinka” “Toh waya dauka na duba ban gani ba” “Muje na tayaka nema” Haka sukayi ma dakin tas babu komai cikin ta, har Safe suka duba. Anan kuma yaga babu takardar gida biyu. “Ko dai Laila ce, because kafin na fita na gani” “Haba Bilal kamarya Laila! Gaskiya bana so saboda tafi karfln kudinka. Can you imagine karka bata min rai” “Toh kudina ya bace kuma mu uku ke cikin gida, kince baki dauka ba, nima ban dauka ba waya rage?“ 
 • “Sai kuma akace Laila ne, kila tuntuni basa gidan nan, am sure sawon barawo ta taka amma kar kayi mata haka please” saita fashe da kuka. “Haba Bilal tsanar har yakai haka? Sata! Satan Sata fah Bilal” tace tana kuka daya sarke mata, haka hawaye ke mata gudun famfo. Ranta yana soyuwa sosai. Bilal yayi mata cin fuska wanda bazata mance dashi ba. Idan kuma yanaso yaga zaman lafiya ya gaggauta janye zancen nan. “Yanzu Bilal inace mai gadi ya kawo cradle, amma ko tuhuma bakayi ba nan take ka laka ma Laila. Wallahi dan adam ba abin wulakantawa bane. Bakasan wanda zai taimaka maka nan gaba ba. Saboda tana talaka shine kake mata haka, Allah daya baka arziki shima zai bata” 
 • Fita yayi yaje gate ya kira mai gadi, shi yasan Laila ne. Amma daga kansa bazata sake sata ba. Daga ita har Saif yau saiya kulle su babu mai kwantar su, karyan iskanci sukeyi. Umurtan ta yayi yace suje falo. Musa mai gadi yana daga bakin kofa ya durkusa, hijab tasa idonta yayi zazur sai kuka takeyi. “Musa kaika shiga dakina dazu?” “A’a a falo na ajiye abin daka ban gashi chan” “Ka tabbata baka shigan min daki ba” “wallahi Alhaji ban shiga ba, wani abu ya bace ne halan?” “A’a karka damu sai anjima” Bayan fitan Musa sai Bilal ya kalleta wanda haryanzu bata bar kuka ba, “Toh kinji koh yanzu saura mutum daya” 
 • Tsoro ya sake bayyana a fuskar ta. bata tunanin Laila ne amma idan aka samu akasin haka bataso Bilal ya dauke mummuna mataki akan ta. “Please sweet idan itace karka yi mata wani mugun abu, you know she is dear to me, Dan Allah karka illanta ta. Nasan akwai dalilinta na yin haka, kila kudi take bukata ko taci bashi za’a ci mata mutunci a gari“ saita sake fashewa da kuka, haushi ya sake ji ya fita bai ce mata komai ba. 
 • Kal tsaye ofis dIn yan sanda ya wuce dake kawo suka nufa gidan Laila da yan sanda biyu, yau saita ci ubanta. Dama ya dade yana jin haushin ta. 
 • Laila tana zuwa ta shimfuda sabon bedsheets dinta, gashi da bala’in laushi da santsi. Nan ta shagala sai seMe takeyi kwance akai tana annashuwa. Sallama sukaji na yan sanda. 
 • Sameera da customers ana sana’a, “Sannun ku, Laila muke nema” jin sunarta dataji yasa tafl to amma sai taga yan sanda. Anan idonta ya raina fata. 
 • “Dan ubanki ina kudina?” saiya karasa wajenta tareda cin kwalarta. 
 • “Yau sai kinci ubanki harda uwarki! Bazaki sake sata ba
 • “Wallahi bani na dauka ba, na rantse!” ta soma kuka “Zakiyi bayani yau idan kika ci duka” “Ku tambaya waya dauka?” tace 
 • Sai Bilal ya saketa, kallon raini ya bita dashi. “Waya dauka?” 
 • “Wallahi Haske ta dauka” yasan makirci ne, saboda Laila mugu wa ne. Dan Sanda yace a kira Haske a waya a gaya mata abinda Laila tace. Haske tana kwance har kanta ya soma mata ciwo kamar zai fadi, Tausayin Laila duk ya mamaye ta. Gaskiya idan Bilal ya dauki tsatsauran mataki zasu samu sabani. Yanada kyau musulmi ya kasance mai uzuri. Wayan ta ya soma ruri, tana ganin sunar Bilal ta dauka da azama. 
 • “Sweet dan Allah ka yafe mata wallahi nasan aka si ne” muryan Laila taji. Ashe an saka wayar a speaker. 
 • “Ya Naji kina maganar a yafe min! Halan me nayi? Inace ke kika kwashe kudin da takardun gida guda biyu zaki sayar” 
 • “Laila ban gane ba? Me kike nufl?” ta tambaya a tsorace tareda dafa kirji 
 • “Ke kika ce tunda bakije rainon ciki ba kin soma kwashe mashi kaya kina sayarwa a 
 • hankali” Kuka Haske ta fashe dashi sabo, “Wallahi Bilal karya takeyi!” Ashe ke ya kamata na kaima yan sanda ba Laila ba” Bilal yace “Wallahi ban daukar maka kudi ba, sweet you know me mana“ “I thought I do! Ashe ke babban barauniya ce” 
 • “Wallahi ban dauka ba, kwarankwatsa” 
 • “Yau babu mai rabani dake“ murna fal idon Laila ana fada da Haske da Bilal. Bayan yanzu ya saketa zai hadata da yan sanda. 
 • “Haske ki daina karya, kila kawai sakin ki zaiyi ba tareda ya hada ki da yan sanda ba. Kawai ki flto mashi da kudin yana bedside drawer dinki” Anan Haske tayi super taje ta duba, kuka ta sake fashewa dashi. “Ga kudin amma ban dauka ba. Ni banma bi ta wajen ba tun bayan na baki bedsheets” “Gwara dai kika fada gaskiya, bafa yau kika saba sata ba. Ko sanda aka kai maki lefe kin sace Fllin Ammi sannan haka kike bin purse dina da dauke dauke” 
 • “Laila meyasa kike haka! Ki yarda ban dauka ba. Banma tuna sanda mukayi maganar file dake ba” 
 • “Wallahi da bakin ki kika fada min, ta ina zan san Bilal ya ajiye kudi ko inda yake ajiye takardun gida. Kawaii kiyi fatan kar yaranki su gaje wannan mugun hali”
 • Kashe wayan Bilal yayi yana tsaki, duk aikin Laila ne akan ta rabasu. Amma kamar ingiza shi takeyi. Sallamar yan sanda yayi tareda basu hakuri. Saiya tafl wajen motar sa. Sai ya tuna kamar an bama Laila bedsheets, anan ya koma dakinta. Ba kowa falo sai uwar daka. Saka kai yayi babu abinda ya shafe shi. A lokacin ta  dauko waya tana kokarin kiran Ammi ta gaya mata goodnews. Dama ta dauki alwashin itace zatayi sanadin barin Haske a gidan. 
 • Ammi bata dauka ba saboda ana case dinta na sata, kowa yana binta da tsinuwa da la’ana. Arm robber ake kiran ta saboda asalin sata né wannan ba irin cin kudi ka kara zero a check book babe Batada maraba da masu fashi da makami, saura kiris itama ta soma rike bindiga  Kwanciya tayi male male kamar bedsheets din ubanta, abin ya bala’in bama Bilal haushi. Hannu yasa ya rinka fin cika, “Tashi dan ubanki” da sauri ta mike tareda zaro idanu. Haka ya yaye gadon ya kuma je ya cire pillow case sannan ya dauki na duvet wanda bata riga ta saka ba akan akwati. Fita yayi abinsa ranshi yana tafasa. Dan wawanci shine ta bata sabida yanada kudin banza. Hope dai yanzu ta dauko darasi Abin duniya yayi ma Haske cinkoso, yau taga aibun muguwar kawa. Lailah ta shayar da ita madaran mamaki. Tayi kuka data dade batayi ba. Kamar kirjin ta zai fita takeji. Bata taba tunanin Laila zatayi mata haka ba. Wai ta kala mata Sata. 
 • Kuka taci tsakanin ta da Allah, Bilal ya dawo baiko kalleta ba, kudin ya gani a gefenta tana kuka. Dauka yayi ya fita domin yayi sabgar gabansa. Koba komai taga halin Laila first class. 
 • Kasa hak’uri tayi sai ta kira Laila domin taji dalilinta naso ta kashe mata aure. Laila na ganin wayar ta wulla ido. Haushi taji sosai yadda aka kwace mata bedsheets, saidai kuma tayi murnar kiran kila ya saketa ne ta tagayyara cikin gari. 
 • “Tawan “Wannan wani irin abu ne Laila? Sanin kanki ne ban dauka ba koh?” 
 • “Eh na sani!” “Why did you lie?” inda inda na karya ta soma yi “Dama saboda… Saboda ana bina bashi ne… Harna dauka kudin saina fasa, toh na mance ban mayar ba… Kuma Kinga Bilal yana sanki bazai hadaki da yan sanda ba. Shine nace haka…. Maybe kawai sakin ki zaiyi” tace cikin kuka saita cigaba. “Nikam Ga yan sanda ga saki” 
 • “Karki damu bai saken ba, Allah ya kare tsautsayi” Gaban Laila ya fadi wani bakin ciki ya mamaye ta, wai meye haka“?? Ita kenan babu cin nasara akan Haske. Wallahi bazai sabu ba. Dole yanzu ta hada da yan tsubbu “Yanzu be sake kiba?” “Eh kawai daukar kudin yayi” “Amma kina tunanin zai sake ki?” “In sha Allah bazai faru ba” “Ah lallai” “Yanzu nawa kike bukata? Ga Gold din lefena saina aiko maki ki sayar ki biya bashin“ murna Laila tayi sabida da kudin zata bi malamai Wannan kenan! 


 • Wannan hasken anyi sokuwa wlh😃

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]