[Advertisements⬇️]

HASKE CHAPTER 20 - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 • HASKE • CHAPTER 20


 • Bayan kwana Blyu…
 • Fijr ne take sanye da maroon shadda wanda yasha aiki, tayi daurin gwargwaro wanda ya zauna mata a akai. Ga make up dinta Shima abin kallo ne. Zara zaran idonta take wullawa fuskanta babu komai sai zallan farin ciki. Yaune sunar baby, tun ranar da akayi meeting Daddy da kansa ya aika direba gidan Mommy domin a kwashe mata kaya. Taso abin saboda zama daki daya da Ammi yana bala’in takura mata.
 • Ammi batada aiki sai sumbatu tana zance marasa kan gado ciki ciki gashi kuma ta rinka shure shure kenan cikin dare. Taji ciwo sosai yadda Fijrzata tafi banda ita. Zailani ya nuna mata da gaske yake akan batun rabuwar su. Ga kuma kewarjaririya, yarinyar tanada shiga rai saboda tanada bala’in fara‘a. Haka kurum saita rinka murmushi abinta. Idan Zailani baya nan bayan Ammi ta tashi daga aiki ta kan biya ta gidan domin taga babyn.
 • Babu wuta ta siyan mata abubuwa, kunyar ya riga yazo saidai a guji na gaba. Mommy ita ma tayi rawar gani, Haske ma haka ta sakejiki babu abinda Fijr ta rasa. cradle mai tsadar gaske ta siya da kayan yara. An nuna ma Fijr kara sosai. Da safe ranar da sukayi bakwai Daddy ya kira Fijr bayan asuba. Ya roketa alfarma akan a mayar da sunar Hafsa tunda itace mai rasuwa. Dannewa tayi ta yarda a haka saboda Daddy yafi karfin ya tambaye abu wajenta kuma taki. Musamman yadda ya dawo da ita gidansa bayan tayi abin kunya.
 • Haka yarinya taci suna Hafsat, kuma Fijr tace haka za’a kirata baza’a boye ba. Tunda dai asalin mai sunarta rasu. Kuma da gangan tayi saboda Ammi, tasan duk sanda aka ce Hafsa sai gabanta ya fadi. Rawa take ma babyn tana cewa “Hafsa ta tafi Hafsa ta dawo, kin zama duwawun karfe babu yadda za’ayi dake”
 • Ba taro akayi ba kawai su Haske ne da Ammi sai mommy da yaranta ana falon. Kunyar mara kunya asara ne kuma Fijr bata kunyar abinda tayi. Wani yaga yadda take ma babyn rawar gani zaiyi tsammani cewa da aure akayi cikin.
 • Ranar Daddy yana gidan koda yaga Hadiza bai damu ba, yasan suna taje kuma da yamma zata ware. Ita kuma da biyu taje. Sabida ya ganta kila ya tausaya mata. Tursasa Fijr tayi akan ta sheka mata kwalliya harda saka mata eyelashes.
 • Haka yayita saka mata ido yayi ruwa, da gangan Fijr ta saka mata gum mai yawa. Gashi ta saka wani leshi mai uban tsada green and yellow, bata ma gama biya ba a wajen aiki taci bashi da takalmi. anzo da abinci za’a kaima Daddy, nan ta soma salo tana fadin ga adadin yadda yakeso. A’a yafi san mayonnaise akan salad cream. Baicin green beans irin dai ta san halinsa haka.
 • Daga nan tace zata kai masa dinning. Dama Haske ce zatayi saitaje wajen tareda dan ingije ta. Tun zuwan shamsiyya gidan Ammi ke binta da magayen kallo, data gifta data watsa mata harara.
 • Kuma abincin ranar gabadaya Shamsiyya ta dafo duka takai a babban cooler, Ammi ana yauki harda saka takalmi mai tsini. Kwas kwas kwas Daddy yaji tafiya. Dama yana duba jaridar Daily Trust ne.
 • Daga kai yayi ya ganta saiya murtuke fuska tamau, ita kam bata hakura ba. Murmushi ta sake yi saita yi sallama. Kashe murya tayi kai zaka zata shekarar ta goma sha shida. “Daddyn Fijr ga abinci” tace tareda rausaya kai 
 • “Uhmm hmmm” 
 • “Bari naje na kawo ruwa sai nayi serving dinka” bai kula ba illa satar kallonta ta cikin tabaran idansa. Ita kuma ta tafi tana juya jiki kamar reshen bishiya. A yau idan taci sa’a zata koma dakinta. 
 • Ta dauko zobo a jug tareda kofuna biyu, idan yaso saita taya Daddy hira suna cin abinci. Atleast koda friends su zama tunda dai akwai yara tsakanin su. 
 • Tana cikin taflya ruwan idonta ya tsananta, ji take kamar ta fada cikin yashi. Kan kace kwabo tayi losing balance dinta ta turgude. Anan ta watse kasa kamar sabuwan hauka. Zaman dirshan tayi kamar na yan bori. 
 • Ji kake tas tas tas zobo rodo ya sheka mate a jiki. Ga kofuna suma sun fashe. Disaster tayi creating wanda saida kowa ya fito domin yaga meke wakana. 
 • Daddy ko kallonta baiyi ba, da farko tasha zai je ya daga ta sai tayi zama jikinsa tana mashi salo. Kafarsa ya dauka yabarwajen. 
 • Charko Charko kowa ya tsaya yana kallonta. Babu wanda yakeso yaje tabata kafin ya shafi zobo a kaya. Balle ma Haske farin leshi ta saka sol. Fijr ne ta soma magana. “Toh Kinga dai yanzu Ammi sai kiyi kokarin tashi tsaye babu wanda zai so ya taba ki ya shafl zobo” kallonta tayi cikin takaici. Duwawun ta yana mata ciwo sosai kuma tana bukatar tallafi.  Da gaske Ammi haka zakayi kokari ki tashi ko ki kwana a wajen nan” 
 • “Lantana zoki taimaka min” Ammi ta umurta, Lantana tana tura baki ta taimaka mata. Sannan ta gyara wajen tsab. Mommy dai na daga gefe tana mata sannu sannu. Haka Ammi ta koma ta canza kaya tareda yin wanka. Sai Lantana ta tafi dauraye nata. Nan aka soma ruwa wanda babu damar shanya, dole aka barshi cikin bucket. 
 • Fijrta bata wasu daga cikin tsoffin kayanta wanda basuda aminci. Ammi tayitajuya kayan tana kallo. Ta raina shi balle ga Haske cikin kayan alfarma. “Fijr canza min ki bani leshin ki na salla, bansan wannan” “Ni gaskiya Ammi kiyi hakuri wallahi” “Yanzu bazaki bani ba ina mamanki” “Emotional blackmail! Gaskiya bazai yiwu ba!! Kinsan kinada kyasfi kafin na kwasa. Gwara wannan daga kin cire saina mayar tsumma” “Ni kike gayama haka gaban mutane. Kyasfi wani mugun ciwo ne? Ai kowa nayi” tayita sababi ita kuma Fijr ko gezau “Nidai Ammi saidai ki siya” “Nawa toh” “Yauwa yanzu naji bayani, dubu sha biyar danma ke kika haifan” kallonta Ammi tayi tana mamaki. Da dukkan alamu batada hankali. “Halan bakida hankali ne Fijr? Anya kinaso kiga annabi kuwa??” “Nifa ina zaune kike so ki siya kayana, banfa matsu ba kece bakida kaya” “Ni dubu uku gareni” “Saidai na samo maki wani amma wannan yafi karfin ki”. Haka ta samo wani atamfa mai dan kyau, yafl dubu uku wajen Fijr amma batasan dinkin tun asali. Sau daya ta taba sawa kuma neman yada kai takeyi dashi.
 • “Dinyan makaho ya nuna a hannun sa” Fijr tace tareda mika hannu domin Ammi ta bata kudin ta. Rai bai soba ta bata yan dari biyar guda shida. 
 • Haka ta saka kayan, duk cikin dakin ita ce taf‘l kamada karamar mutum, danko Lantana 
 • Haske ta kai mata kwancen kaya. Duk ta muzanta tana jin babu dadi. Anan ta cigaba da bin Haske da mugayen kallo. 
 • Mommy tace su koma falo domin suyl kallo. lta kuma Fajr batada wani matsala yanzu. Sam maza sun flta kanta. Daga Isi har Ghali. Soyayyar Hafsat takeji yana shiganta sosai. Sai dai ta sakata a gaba tayita kallo, tanaso yarinyar ta fita daban daga yadda take kokuma Isi. Idan so samu ne tana so yarinyar tayi yanayin Shamsiyya. lta yanzu zancen aure yama fita a kanta, kawai ta samu abinda zata rinka yi ne wanda zai rinka samo mata kudi. 
 • Kashe gari… Tsaye yake Sanye cikin wani kodardiyar kwabdeden jumperwanda ya kusan kaurinsa, dinkin tazarce ne akayi masa a kan material din mai kwabo kwabo. Ya sanya wani hula kamar zaiyi dakwan rama. Bakar leda ke hannun sa na viva wanda daga dukkan alamu kayansa yake ciki, Kafarsa kuma takalmi ne kambas fari wanda yayi mada mada kamar wanda yayi kwambe cikin laka. Kana kallon sa kamar mara hankali kokuma wanda damuwa yayi masa yawa, wayar hannu sa asalin China mai suna Rokea daure yake da lobari kuma bayada baya sai zallan 
 • batir a bayyane. Sannan kuma duk rubutun ya koke saidai idan kasan asalin kan wayar. 
 • Zufa yakeyi sosai duk wajen bayansa, da hammata sharkap yake. Mari yake kaiwa da gwauro a bakin kofar gate din. Mai gadin ne ya dawo Mallam Adamu. “Na mance ban tambaye ka ba, Yama sunar ka?” “Isi… Isi… lsiyaku Mohammad… Tamin farar sani. Wallahi ta sanni..” yace cikin damuwa. A hanya Mallam Adamu ya ga Lantana sai yace mata tayi ma Fijr iso tayi bako. Fijrta hakince kan gado tana kallo a laptop din Imran, film din Sugar take kallo Nigerian series, babbaka dariya takeyi Princess tana bala’in burgeta kuma tana mata yanayi da ita. Duk sunadajiki kuma suna san wild life, gashi duk sunyi cikin shege. “Assalamu alaikum, Anty Fijr kinyi bako” pause tasa a film din saita gyara zaman ta. Baby Hafsa saida tayi kara kadan saboda an taba ta..”Bako kuma? Ni ai bana expecting kowa” “Isi ne ko menene yace wai sunar sa” Gabanta ya fadi saita zaro idanu tareda dafa kirji “Isi kika ce! Kin tabbata? ” Wallahi Mallam Adamu yace yana bakin gate ” ” Tohje ki nagode ” 
 • Bata tashi ba asali ma batada niyyartashi, tunani ta soma yi akan yadda zata yada kai dashi. Yanzu kwata kwata ya fitar mata a kai. Baya gabanta baya burgeta. Da chan batada wanda takeso ta kasance tareda shi bayan Isi amma yanzu komai salap yake mata.
 • Ta shafe kusan minti arba’in da biyar bata bar inda take ba, gashi yau babu kowa a gidan jiya yan suna Mommy har 10pm tana gidan. Su kuma su Haske da Ammi yau ana aiki. Daga ita sai Lantana da Baby Hafsa, Anisa ta tafl makaranta na Uncle Bado, Daddy ya tafi aiki. 
 • Dogon tsaki ta doka saita sungumi mayafin, riga dinkin boubou dakejikinta. Tana taflyarta na gado bankam bankam rai a bace. Duk haushin Isi zata sauke mashi. 
 • Cin sa’arsa daya tanajego data hau ruwan cikinsa tajibga banza, a hakan ma bawai ta dauki alkawari bane bazata yi dambe ba, kawai tanaso tayi wajen sati biyu zuwa uku saita koma yi sosai, 
 • Gate ta bude ta soma waige waige sabida bata gane lsi ba. Kullum yana cikin saka gwanjuna na riga da wando, sai kuma yayi aski mai layi layi kamar dan tasha. Wannan kam daban da kayan hausawa. 
 • Murmushi ya soma yi dayaga Hasken Annuri dinsa, ta bala’in canzawa ta kara gogewa. Sheki takeyi yanzu ga kuma class a tareda ita. Hakora uku babu a bakinsa yasa ta sake rashin fahimtar waye. Ga kuma gemu buzu buzu a fuskan sa. “Baba wa kake nema?” tace cikin ladabi 
 • “Haba Fijr kamar ya wa nake nema!” 
 • Sai a lokacin ta gane shi, duk ya tsofe ya lalace kamar ubanta. Balle dama ya bata shekara goma sha biyar. 
 • “Dankari makari salatin maguzawa! |SI!!! Kaine ka koma haka kamar mahaukaci”
 • Sosa keya ya somayi, anan fuskan sa ya canza kamarzaiyi kuka. Allah kadai yasan wahalar daya sha bayan rabuwar su. “Kiyi min izini na shiga ciki na zauna, idan naci abinci saina baki labarin abinda ya faru dani. ” Allah ya amfana! A kara gaba! Umma ta gaida Aisha” “Dan Allah karki yi min haka, wallahi daga Kano nake tun safe a gajiye nake” “Nina gayyace ka halan?” “Kinki magana dani ya zanyi dake” Bawai Tausayin sa taji ba, kawai tana so su karkare magana ne. idan ta biye mashi zai rinka zuwa kullum yana damunta. Matsa mashi tayi ya shiga cikin gidan. 
 • Bai taba shiga ba saidai ya saba rakota bakin kofa, cikin ya burge shi sosai. A wajen karamin garden ta saka Mallam Adamu ya ajiye mashi tabarma. 
 • “Ga famfo chanje ka sha ruwa kayi min bayani, sauri nakeyi“ 
 • Gwiwa babu kwari yayi haka, mamaki yakeyi yadda ko murmushi taki mashi. Bayan tace bazata iya rayuwa batare da shi ba. Gashi kuma yazo tana mashi fuska. Watau duk msg dinda take aikawa groups na Facebook wanda yake ciki duk karya ne. Ashe soyayya karya ne. “Ina jinka” “Wallahi na sha wahala, banje Kano da kafar dama ba” “Allah sarki” tayi fari da ido. Kuka ya fashe dashi kafin ya cigaba da Magana. 
 • “Dama shagon waya na kama, ashe wani ya sace wayan wani soja ya kawo kamar nashi ne saina siya. Yan SARS sukayi tracking zuwa shagona ….. Anan…. Anan suka…. dinga Dukana sukayi min kamar ganga… Sannan kuma… Kuma suka tura ni cell bayan sati daya kuma zuwa prison harna tsawon wata biyu….. Kayan shagon aka siyar na fito ” kuka ya sake cin karfinsa. Wiwi ya barke dashi Wannan karan. “Maganin ka kenan bayan kaci kudina ka gudu kai me wayo kayi aure” 
 • “Dan Allah kiyi hak’uri, yanzu haka bayan na fito daga cell ashe gidan da muka kama ba mai gidan muka biya kudin ba, yan damfara ne yanzu an kore mu, Basai kin fada ba nasan hakkin ki ne” 
 • “Amma Naji dadi wallahi, su kuma hakorar a ina aka cire maka su?” murna karara fuskanta tanaso taji. 
 • “Duka a prison dinne, yasa nakeso ki yafe min ko zan samu saukin rayuwa” 
 • “Amma da zanga wanda ya cire maka hakori, da kuma wanda ya sayar maka da wayan sata dana basu kudi” 
 • “Nidai kiyi hakuri ki yafe min koba komai naga haske a rayuwa na” ” 
 • “Tashi ka tafi naji, zanyi tunani” Shiru yayi sabida yunwa yakeji, rake yasha a hanya. Baida ko sisi sai dari bakwa’l wanda bazai maida shi Kano ba. Gashi matarsa itama tanada ciki. Yana tunanin kila idan Fijr tana da sauran burbushin sanshi saita bashi kudi like old times. Da kanta taje gate ta wangale kofa, da hannu tayi mashi alamar ya fita. Bai tambaya ya cikin ba kuma ba tace mashi ta haihu ba. 
 • A bakin gate ya tsaya yanaso yayi mata magana cikin rada, kafln ya ankara ta sharara mashi mari. Saida yayi superya soma tangal tangal saboda zafi. “Idiot ka dawo nanda sati biyu idan ka haifu” Haka ya tafi yana dafe da gurin sabida bala’in zugi kamar an mare shi da karfe. a 
 • Ammi Hadiza tana ofls sai tunani takeyi, ta dauki loan da ake bama ma’aikata ta siya mota. Saboda tana kishi da Haske dole ta siya wanda zaiyi kwatankwacin nata. Gashi Daddy bai riga ya damka mata takardun sabon filin da ake tunanin Haske ta dauka. Yanzu kuma aure ya mutu, ko sauraron ta bazai yiba. 
 • ‘STEP 8’ suna project na renovation tareda Old students association. Anyi team na malamai da zasu rinka lura da aikin, daga ciki akwai Ammi Hadiza. 
 • Za‘a gyara computer lab, za’a canza computers daga tsoffln zuwa MacBook. Sannan kuma AC suma za’a canza. Bayan nan kuma duk wani ofis dake da computer na malamai za’a canza zuwa MacBook. 
 • Awani store aka mayar da tsoffln computers din wanda Ammi keda makullin shi. Wani dabara ya fado mata, ta rinka dauka tana siyarwa a Makarfl plaza ko Royal saita soma biyan bashin ta. Bayan nan sai ta kama haya kuma koda 2 bedroom ne, idan yaso da karfln tsiya Anisa ta dawo wajenta da zama. 
 • Koba komai Daddy zai dauke kudin cefane na Anisa daga nan zata rage wani kafan. Computer masu monitor, CPU, keyboard, mouse da printer ta faki idon mutane taje store ta kwasa guda uku. A boot tasa sannan ta cigaba da aikin gabanta. Wajen 2 da aka tashi saita fita dashi, gabanta yana duka uku uku kamar zai fita. Babu wanda ya tsaida ta, bata tsaya ko’ina ba sai royal. Haka ta sayar tareda masu 
 • alkawari zata rinka kawo masu wani domin yanzu aka soma business, Wannan kenan! 
 • Gullisuwa datayijiya yayi bala’in kasuwa, ashe itama Sameera acici akwai kwadayi. Nan tayi mata cinikin dari da Hamsin. Sannan da kanta tabama Laila roba transparent domin tasa kuma wanda Laila ke da shi. Sannan ta ajiye a gefen yan lalle. Haka ranar akayi ta lalle ana lashe baki, wasu ma suka siya suka tafi dashi. Wasu kuma bayan sun tafi suka aika yara domin a siyan masu. 
 • Yau Saifa dakin Laila yake tun asuba ya dawo, yana kara barciyaji kamshi yana tashi. Murmushi yayi cikin magagin barci, duk daukarsa dakin Sameera ne tana masu pancake dinta mai dankarin dadi. 
 • Toh dayake Sameera tanada duvet mai laushin gaske, dayajanyo yaji bargon ba wani taushi saiya gane inda yake. Barcin kawai ya kaurace mashi daga idanu. Mamaki yakeyi wai yau Laila take masu abinci haka. 
 • Sanye cikin gajeren wando da singlet baki yaje falo, shi baya ta’ammali da farin singlet ko kaya, ‘Fari akwai tonon silili’ yake cewa. A zaune ya ganta tana kirga gullisuwa bayan ta soya. 
 • Shima kamewa yayi a kujera ya zauna, saiya soma kallon TV dake aiki. “Ina kwana ?” “An tashi lafiya?” “lafiya lau” 
 • “Kawo min abinci” Jiya dazai dawo ya siya biredi da madara ya bama kowace matan shi, ita kuma harta saka ruwa a flask. Yasha citta da na’a na’a wanda Sameera ta soma shukawa. 
 • Haka ta kai masa ta ajiye masa a gaba, bata bashi gullisuwar ba ta killace abinta. Da gefen ido yaketa kallon movement dinta, yana ganin ko tanada hankali ashe batada shi. Yanzu dan mugun hali shine ko hakkin ido bazata bashi ba, kuma a duniya yana bala’in san gullisuwa tun yana yaro. Dan madara madaran da gardin tada mashi lissafi yakeyi. Ga kuma dan mai mai a bakinsa. 
 • Yana tunawa miyau na tsinke masa ga kamshi ko’ina. Sai ya tuna rashin kunya irin na Laila, uban wa ya bata izinin soma sana’a ba tareda ta tambaye shi ba. Salan ya hanata a kirashi mugu. 
 • “Meye wancan a robe?” ya fada tareda basar wa kamar be gane ba. Da fara’a ta soma magana. “Damajiya na soma gullisuwa tunda yafi zaman banza” “Ah lallai toh a bamu ala koro mana” yace yana washe hakora. Bazai iya mata fuska ba 
 • saboda miyau sai tsinke masa yakeyi. Murtuke fuska tayi. 
 • “Ai iya kudinka iya shagalin ka, babu wani ala koro, babu wani family and friends, nima nan Monica(Money ka) ce” saita murguda mashi baki. Kallon hadarin kaji yayi mata, har zai 
 • hasala sai yaga bazai kai shi ko’ina ba. Rage murya yayi yana marairaicewa. 
 • “Meye gullisuwa ! Ina mijin ki bazaki iya bani ba! Maimakon ki nema albarkan k0 kya samu kasuwa! Wallahi bakiji dadin halin kiba. Shegen mako kamar kwalta ba’a bambaranki” Tana tura baki ta dauko guda biyar ta bashi, dama yankan goma ne tayi. 
 • “Hamsin kenan! Wallahi saika bani kudina haka kurum zaka nakasa ni” dariya ya bushe dashi sabida saidai ta dake kudinta shi kam banza yaci. “Rabin raina nine Destiny dinki kike ma haka akan abin duniya” yace cikin izgili “Alkuran saika bani kona cire a kudin cefane” “wannan keya shafa saboda dama nawa xan baki!” Haka yaci gullisuwa ya hada da biredi yasha tea, yaji dadin abin sosai. Bin roban yake da ido yana so ya kara. Ita kuma taki tashi tana zaune, koda zata kitchen dauko kofln shayi 
 • haka ta dauki robon saboda tasan halinsa. 
 • Haka ya hakura ya gama ci. Wanka ya shiga ya fesa kwalliya. Sabuwar kaya yasa  daga shagon dinki. Boyel ne army Green, saiya saka Light green hula wanda yasha wanki yana sheki. Takalmin sa cover shoe Prada ya bada jiya aka goge mashi na masu yi. Haka ya feshe turare kala uku wanda ya boye a motarsa, yayi kyau sosai saboda yafi minti biyaryana taje sajensa da gashin kansa. Ko Laila saida ta yaba da kwalliyar. Destiny biki zaka halan?” 
 • “Uhmmmm wannan yafi biki, sa’a zan nemo” “Allah ya taimaka, wallahi kayi kyau har na soma kishin ka” “Tukunna dai”yace cikin izgili ” Allah koh! Kace haka zaka rinka wanka kana representing dina? “Sosai… Ni saina dawo””Allah ya bada sa’a” 
 • Dari da hamsin ya ajiye kan centre table na cefane, shi dama idan baya dakinki bai baki ko sisi. Sannan kuma babu kayan miya babu man gyada, rabin kwalba ta siya na soya gullisuwa. Ko kallonta baiyi ba yayi gaba. A tsakar gida yaga Sameera, itama taga yadda yayi kwalliya kuma ya Burgeta. Murmushi suka yi saita gaida shi. Masu gini sunzo sun soma, anan ya basu 5k yace idan suna neman wani abu su kira shi. 
 • Haka ya tafl yana nishadi, babu komai a ransa sai tsantsar jin dadi. A gurguje yaje shagon ruwan sa, suna aiki her an soma distribution, baida mota na kai ruwa saidai kullum ayi hayar a kori kura safe da yamma. “Mujibat Bolarinwa Restaurant” ya tsaya, nan ya shiga yana fankama kamar shi wani ne. Kamar tin sati uku da suka shude kullum sai yaje yaci abinci a wajen. Da biyu yake zuwa. Hajiya Mujibat mace yar kimanin shekara 58, tanada yara takwas duk sunyi aure saura biyu na gabanta yan biyu ne mace da namiji. 
 • Da Bukola da Olabode, yan kimanin shekara ashirin da biyar. Bukola ko Bukky tana da bala’in kyau, yar gayu ce ga kuma diri. Sannan itace yanzu ke handling business din. Hajiya Mujibat kawai dai tana zaune tana karban kudi ne. Waiters ne suka zo kansa, “Sannu Sir! Me za’a kawo maka?” 
 • “Sakwara malmala uku, sai miyan vegetable da naman dari bakwai” watau ya kashe dubu kenan zama daya saboda sakwara dari dari ne. 
 • Yana zaune yana kallon Bukola ko Bukky kamar yadda Mamanta ke cewa. ‘Yar nema saina aure ki” yace cikin ransa. lta kuma sai safa da marwa takeyi tana Kokarin komai ya tafi daidai. Dayake tanada dan rawar kai idan tana abin ta. Kara burgeshi yayi ashe yana san 
 • mata masu rawar kai ba sanya sanya ba kamar Sameera.
 • Bayan an kawo mashi sai yace a hado da gwangwanin Maltina, yana ci yana sha yana rangaji dakai. Bukky ne tazo wucewa, dama sun saba gaisawa. “Hello !Ya kike?” “Lafiya lau Sir, a kawo maka wani abu ne Sir?” ” A’a nagode, amma basai kin ce min Sir ba, sunana Saifullahi nice meeting you” saiya mika mata hannu su gaisa. Bata mika nata ba ta soma magana. “Mu a yaren mu idan mutum ya girme mu muna ce masa Uncle k0 Sir saboda girmamawa” “Okay na gane babu damuwa, ya sunan ki na asali” “I’m Bukola Sir” “Nasan wannan ina nufin asalin sunar ki” tunani tayi sosai bata gane ba. Chan saita dago. “Sir kana nufln sunana na Islam?” “Eh shifa na muhammadiya” “Aminat ….. Aminat Bukola Bolarinwa” tace tana murmushi wanda dimples dinta ya lotsa kuma ya kara mata armashi. “Okay anjima Aminat zan iya dawowa na dauke ki muje date,just ni da ke muje duk inda kike so. Let’s get to know each other better” Yadda ya chakare yayi kyau, ya burgeta sosai. Bazata iya ce masa a‘a ba. “Okay karfe 7 nake tashi. Kazo lokacin” saita taFI tana rausaya. ‘Da gaske na tako sa’a’ ya fada cikin ransa 
 • Tun cikin nan Bilal yake tarairayan Haske, yana bala’in san yara. Musamman ma tagwaye, yana kyautata zaton tunda su Ammi yan biyu ne Shamsiyya kila ta haifa. Yana so ya saka sunar Hajia Lubna sai kuma ya bama Haske damar ta zaba suna daya. Ita kuma tunda taga an saka ma baby Hafsat sunan mamanta kuma Ammi bazata maji dadi ba, saita yanke shawara idan sun samu tagwaye kokuma wani lokaci zata saka ma yarta suna Laila. 
 • Baya wani san tuwo balle na alkama, amma tun da Shamsiyya tana so haka yake hakura suci da miyan kuka. Da yake best food dinsa shine macaroni da sauce sai samosa. Toh tana yin masa nasa daban.
 • Suna yanzu fahimtar juna, bai taba mata maganar auren ba itama batayi ba. Saidai zataga wayansa yana kara amma yana kallo yaga wani number haka sai yayi tsaki yaki dauka. Bayan aiki ta biya wajen Laila domin taga yadda ta ke, saida ta biya central market domin tayi ma kanta cefane. Koda taje gidan Laila tana tsakar gida tana bada gullisuwa. Anan ma Haske taga ginin gidan a karo na farko. 
 • Sun shiga cikin dakin Laila sai kallon Haske take yi, ita a saninta idan Haske tanadajuna biyu zata sanar da ita. Kuma bataso ta tambayeta kafin ya zamanto gaskiya. ita data rigata aure batada ciki balle Haske sabon shiga. 
 • Suna cikin hira sai taji Haske daga kasuwa take, haka tace suje boot domin ta gani. Bata soba amma tunda Laila ce babu damuwa. She is her best friend. Anan Laila taga cefane makil kamar na gidan biki. 
 • Saida ta diba dankali, dama roba biyu Haske ta siya aka saka a leda daban daban, 
 • sannan kuma ta diba nama, kayan miya, kayan salad da kuma kwai. Ko ajikinta ta kwasa ta wuce gida. 
 • Anan aka zo siyan gullisuwa, sai a lokacin Haske ta lura tana siyar wa. Aikam ya biya mata rai. Ta lura Laila batada niyyar mata tayi. Anan ta dauko wallet dinta ta mika dari biyu. Guda daya Laila ta bata a matsayin gyara, tayi godiya daya taci saita saka sauran a jaka zata tafl dashi. Sai tabama Laila dubu daya domin ta karajari tayi ciniki sosai.
 • Har mota Laila ta rakata, taji dadin kudin sosai saboda gobe zata soya gullisuwa ta saka a roban takeaway domin ta aika ma Banan. Dole su kulla aminta sosai kafin ta shiga, balle Haske sai fresh takeyi, wata shida yayi mata yawa sosai. Yanzu tsoronta kada Haske ta dauki ciki, idan taji wannan muguwar labari tabbas zatayi 
 • hauka. Yasa gudun ba’a cigaba ba gwara ba’a soma ba.
 • Dole ta rinka samun information akan Bilal wajen Haske na abinda yakeso tana fada ma Banan, sabida idan ta shiga gidan ta kece ma Haske zara. Dole bakin ciki ya kashe Haske har ta bar gidan tunda ba na ubanta bane.
 • Haske tana cikin mota sai wayanta ya soma kara, a speaker tasa ta soma magana. “Sweet ya kake?” 
 • “Maman twins ko triplets ne duka ni inaso” 
 • “Zolaya koh!” “Kina ina ne na dawo ban ganki ba” ” Na biya kasuwa ne daga nan naje ganin Laila, hope you don’t mind?” shiru yayi da yaji ta ambacin Laila. 
 • “Uhmmmm don’t worry sai Kin dawo” saiya kashe wayan. Zuciyar sa yana masa zafi. Ya rasa yadda zaiyi maganin Laila yaji dadi. Yanzu dai yaji dadi Haske ta gane Ammi almura ce kuma bata kaunarta. Saura Laila. Wannan kenan! 


 • Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]