[Advertisements⬇️]

HASKE CHAPTER 19 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 • HASKE • CHAPTER 19


 • Ajiyar zuciya ya sake yi a karo na uku, bakinsa yana mashi nauyin fadin abinda ya zaba. Chan kasan makoshinsa yayi magana, amma dayake qanshin gari Laila da Ammi sun ware kunne. Tsab sukaji meya ce.”Zan aure wancan!””Mene?” Umma tace
 • “Nace zan aura wancan din na yarda” “Wooow” Banan tayi ihu. Su kuma fuskan su ya nuna rashinjin dadi. Ba abinda suka so be kenan. Sai a lokacin suka kara raina kansu da makircin da suka kulla. Bilal ba karamin soyayya yake ma Haske ba wanda yafi karfin tunani mutum. Wannan dole sai sun hada da bin boka, dama suna tunanin zasu iya fltar da ita ba tareda anje haka ba. Koda yake Ammi tace su dakata. Idan ta Laila ne da tuni ankai hoton ta wajen boka. Zura takalmin sa yayi ya tafl, Umma ta danji tausayin sa sabida tana bala‘in san yaranta bataso taga bacin ransa. Amma kuma wannan shine rufin asirin su. Ta lura wannan matan zasuyi shela da ita a gari muddin basu samu abinda suke so be.
 • Balle kuma babu aibu wajen auren Banan, dama chan sunyi soyayya abu kadan zatayi mashi zai tuna da soyayyar su komai yayi daidai. Kai tsaye ya wuce gida, dama yanada customer da zasuyi business daga US amma bai je ba. Bashida karfin handling komai yanzu balle yanada zuciya kam yayi masu rashin mutunci. Afalo yaga Haske ta fito daga dakinta, harara ta watsa mashi tareda dogon tsaki saita wuce abinta. Tafiya takeyi tana karkade karkade ta tamke fuska tamau. Tausayin ta ya mamaye shi, datasan abinda Laila tayi yanzu da batayi haka ba.
 • Yadda yabardakin haka ya tarar, zanin gado ba’a gyara ba sannan babu kamshin tararen wuta. Shi dama tun asali baya ta’ammali da kazanta. Har zai gyara da kansa saiya lura raini ne da iya shege. Fita yayi ya duba dakinta bai ganta ba, sai yaje kitchen ma haka. Kara yaji (a laundry room sai ya shiga. Wanki takeyi da washing machine, tana ganin sa ta harde gira. “Ke meye haka? Meyasa baki gyara min gado ba?” “Banga dama ba” “Kinsan Allah bazan lamunta ba! Tun wuri ki canza kaM na dauki mataki akanki” “Baka isa kamin abinda Allah baiyi min ba, ehe” tace tareda murguda mashi baki. Kallon mamaki yake mata wai yau Haske take masa diban albarka haka abinda ko kemn ya aureta batayi. “Okay i have news for you! Aure zanyi with the help of Laila da Ammi sunje wajen Umma” gabanta yayi mummunan faduwa dataji haka. Bawai auren take tsoro ba. A’a sunar Laila dataji ne. Yanzu kuma kazaM yakai haka. Lallai Bilal yayi nisa. “Idan zakayi aure Mallam kayi abinka like a man. Karka fake da cewa Laila ta saka ka. Ribar me zata samu idan tayi haka? Please go lie to someone else” saita juya mashi baya. Karkada kai ya yi saiya fice, gadonsa yaje ya gyara tsab tunda ya iya balle ta wulakanta shi. Ita kuma taje ta dauki waya domin ta kira Laila. Lokacin tana napep gwiwa yayi sanyi bata samu yadda takeso ba. “Hello tawan! Please zan gaya maki abu karki ji haush!” “Okay ina ji”
 • “Dama Bilal ne yace zaiyi aure, wai kuma ke ce sila! Can you imagine” “Innalillahi baga halinsa ya nuna ba tun kafln aje ko’ina, wai nice yanzu zan samu mashi mata. Toh ribar me zan samu… Mts“ “Shi nagani wallahi. Nasan za kice saida kika hanani auren say wallahi ban taba tsammani zai min haka a farkon auren muba” “Ke ce bakya bin shawara, da kinayi da baki aure shiba” “Yanzu it’s too late for that, Kishiya ba abin tsoro bane kawai fatan Allah ya hada kanku. Rashin mutunci dayake maki ne abin yafl bakanta mani rai” “Wai ya zauna baida abin fadi sai aibanta ki, bayan yasan yadda muke dake. Gaskiya namiji kanin ajali ne, idan bai Kasheka ba zai naksa ka” “Sosai ma kuwa, yanzu karki raga mashi. Yana maki ki rama” “Noooo gaskiya i don’t think so. Wallahi yanzu ina mashi zuciya duk bana jin dadi. I miss him ni bazan iya ba” “Amma anyi gaula, kishiya zaifa maki ! Shine zaki tarairaye shi maimakon ki ci kutumar uban dan iska” “Wai Umma tace mashi yayi!” “Yasa nace maki daga shi har ita karki raga masu!” “Anya Laila she’s like a mum to me” “Wani mum kuma? Bayan Ammi bakida wata. Shiga fllin yaki zakiyi da ita tasan waye babba a rayuwar Bilal. Dole tasan iyakar ta. Anfa daina raga ma uwar miji. Cin ubanta a keyi sosai har sai takaici ya kashe ta” “No please bai dace ba, aljanna nake nema kuma bazan same shi haka ba. Dole akwai trials and tribulations a hanyar haka ….. Sai anjima zamuyi waya later” Wanki datayi ne ya bushe sai ya soma kara shine ya dakatar masu da maganar. Laila cizan yatsa ta soma yadda Haske ta soma zillewa. Kawai kafln ta kwanta zata bita whatsapp da shawarwari akan yadda zatayi ma Bilal harya saketa da kansa. shi kuma Mallam ranar a shagon Saifya wuni, yaje biko tunda shi yaki zuwa. Kodaje baya nan haka yayitajira na kusan awa biyar. Saif yana ganin sa dattijo akan benci duk ya muzanta. Gwiwa biyu ya duka ya gaida Malam. Da fara’a mallam ya amsa kamar babu abinda ya faru. “Mun san mun maka lam amma mutuncin Laila yana dakin ka, kayiwa Allah ka maida ta” shiru Saifyayi, baisan zancen Laila amma kuma yana bala’in ganin mutuncin Malam. Dukda bazai haife shi ba zai girme shi sosai. Okay Baba babu damuwa, yau ta shirya in she Allah zan biya na dauke ta” “Nagode sosai zanyi mata fada sosai bazata sake maka laifi ba”
 • “Nagode Allah ya daidaita tsakanin mu”
 • “Amin bari na tafi” .Daddy rufe kofar yayi yana hawaye, dakinsa ya wuce ya zauna. Tagumi yayi sai tunani yake yi. Meye ya taba ma Hadiza datake masa haka. Abinda take fatan ma Haske gashi ya fado mata.
 • Meyasa batada tausayi ne, an bata amana gashi taci ko ajin ta. Yanzu kuma Fijr nada ciki babu wanda ya sanar dashi. Amma komai ya kare daga yau. Daga ita har Fijrzasu bar mashi gida.Yadda Haske ta tafi hakanan suma sai sun tafi, yana cikin haka ne sai yaji motsin gate. 03 sauri ya mike saboda yanada tabbacin cewa Hadiza ce.
 • Tana layI’ tana tafiya ta shiga falo, kerere ta gansa ya saka hannu daya a aljihu. Bata kawo zancen haihuwa ba tunda hatsabibi yace sai sanda tayi aure. “Daga ina kike?”
 • “Yaushe kuma muka fara wannan Zailani?” Kafin ya amsa kukan jaririya suka sakeji, Lantana ke mata wanka shine ta soma kuka. Anan Ammi ta zaro id. tareda zubewa k. sa “Dan Allah kayl hakuri, wallahi…” “Na sake ki saki daya” Nan ta sake fashewa da kuka tareda rike mashi kafa,jij|gashi takeyi kamar ba ita taso masa rashin kunya ba. “Ki kwashe kayanki kap dana Fijr ku tafi kafln na dawo, banso na sake saka ku a idona har abada” ya fada yana nuna mata hanyar kofa “Dan Allah kayi min rai, banida wajen zuwa. Ka yafe min akasi aka samu” “Billahil azim na dawo na sameku yan sanda zasu rabamu dake. Kinga akwai yara tsakanin mu tunda rai da arziki gwara ki tafl” fige kafarsa yayi saiya dauke key dinsa akan centre table. Fita yayi ya basu waje, nan da awa biyu zai kira mai gadi idan basu flce ba yazo da yan sanda. Da sauri taje dakin Fijr domin taga ko gizo ne, anan taga har anyi wrapping din yarinyar a tsumma tunda basuda kaya k0 daya. Fijr lokacin tana wanka ita ma a bayi. Lantana ta dauko mop da bucket tana goge dakin, dayake tanada sabon reza wanda ta siya da safe zata yanke farce. Anan tayi amfani dashi domin ta yanke cibiya. Hawaye bai bar idon Ammi ba, yau itace da shege é matsayin jika. Kan gado taje domin ta dauki yarinyar. Aikam fara sol mai kyan gaske. Hasken Lantarki maganin duhu. Anan ta sake barkewa da kuka, tana rike da yarinyar ta fi ta taje dakin Anisa. Bata gida suna hadda saboda weekend ne. Tsohon durowa dinta na kayanta tana yarinya ta mo dashi. Dama akwai masu kyau wanda bata bada ba.
 • Ga kuma su rigunan sanyin ta farare da mayafln su duk a ninke. Nan ‘a saka majaririya da bata san duniyar datake ciki ba. Nan ta soma bude ido taji dumi da kaya ajikinta. Baza’a ce kallon Ammi takeyi ba amma idonta ya sarke dana Ammi. Yarinyar nan da nan ta shiga ran Ammi, gashi kuma tanada girma. Haka Ammi tasata a gaba tayita kuka, yanzu batasan inda zasu ba, ga Fijr na jego she needs a home more than Anything. Tafi minti sha biyar sai shesheka takeyi. Chan cikin ranta tasan abinda takeso tayima Haske shine ya dawo mata. Yanke Shawara tayi suje gidan Binta, tunda bazata iya zaman Zaria ba tunda tana aiki gobe Monday. Bata ce ma Fijr komai ba, batamasan abinda zatace mata ba. Lantana ‘a aika ta gaya mata ta soma kwashe kayanta zasu tafi. Fijr tasan dama za’ayi haka, ninke kayansu sukayi tsab Lantana ta tayasu fita da abinda suka kwasa. Ammi ne ta goya babyn, sannan ta tukasu suka tafi gidan Binta. Su biyun bakajin komai sai sautin kukan su cikin mota. Hajia Binta ta gansu da kaya ninki ninki, bata lura da goyon Ammi ba saida ta kwance ta mika mata. Anan ta barke da kuka mai tsuma rai, Binta ta fahimci komai a haka, Kawai tana fatan wannan ya zama sanadin shiriyan Hadiza. Anty Umma mai aiki ta kwashe kayan su, dakin da Haske ta bari nan aka kai masu kayan. Su dai suna falo sunata kuka musamman Ammi, kunyar duniya ke dawainiya da ita. Duk abinda ta nufa ma Haske ya dawo mata. Gashi ba’a sake Haske ba ita an sake ta. Shekarar ta kusan arba’in da biyar shine zatayi zawarci. Cikin shesheka ta soma magana.
 • “Binta ya sake ni! Alhaji ya sakeni dukana kawai ne baiyi ba” Fijrta sake kidemewa, batasan Daddy yana dauki tsatsauran ma‘aki haka ba. “Fushi ne, kiyi hakuri idan ya huce za’ayi magana” “Allah yasa, wallahi inaso na koma dakin mijina” tace tareda jan majina. Anty Umma ta kawo masu abinci, dama suna tafe da yunwa, Ammi ta kasa ci Fijr aka tursasa mata taci. Sannan aka hada mata shayi mai kaurin gaske.
 • Binta ta kira Umma domin ta daura garwan ruwa, katon tukunya ta daura akan gas sannan aka bata kudi da list taje tayi siyayya a kasuwa. Daga su pad, kayan yara, feeding bottle, abincin yara, glucose, sabulai, pampers, bahon wanka duk kuma Binta ta bada kudin. Sannan ta umurci Fijr dataje ta kwanta Saboda gapyar halhuwa, anan Ammi ta sake barkewa da kuka. Naka sai naka babu mai iya maka wani abun. Lallai Binta mutum ce kuma yar halas. Babu haufi da ita ce korar su zatayi karsu shigan mata da shege cikin gida, ammajibe yadda take mata hidima. Kunya ya sake mamaye ta tama kasa kallon Binta. lta ko sai faram faram take dasu tanaso komai yayin daidai, da kanta ta shiga makwabta ta saka yaran gidan suka tsinkan mata dalbejiya. Gidan sunada itace daban daban kamar su Gwaiba, mangwaro, kwakwa haka, sannan ta cema Fijr taje dakinta domin ayi wankar a chan tunda babu babban baho Kam Umma ta dawo. A bathtub dinta ta cuda Fijryadda ya dace kaflnjikinta yayi tsami, itama taji dadin wankan sosai duk an gasa ta yadda ya dace. Sun fito kenan sai ga Anty Umma ta dawo da kayan da aka aike ta. Ita daiAmmi sai raba ido takeyi tana kallo, tunani kaca kaca takeyi, tasan dai bazasu dauwama gidan nan ba. Fijr tana kwance sai ga lsi ya kirata, har yau kuma bata taba dagawa ba. a Sanda Laila ta koma gida motar Saiftayi arba dashi. Taji dadi sosai saboda zaman gidan shi Dukda babu dadi yafi nasu. Bata shiga tsakar gida ba illa zauren su domin ta soma tattara kaya, dama komai nata a kimtse yake tundajiya Haske ta saka ta a kwana. Kaninta dake bakin zauren akace idan Laila ta dawo taje ana neman ta, Gwiwa babu kwari taje tasan zata sha fada sosai. Chan kurya ta zauna a kasa tareda sunkuyar da kanta. Mallam ne ya soma magana ya bama Saif hakuri, anan Saif yayi magana shima. “Bawai bana san zama da ita bane, amma bin maza takeyi!” kowa yayi mamakin maganar har Laila. Sabida batasan sanda tabi kowa da auren sa ba.
 • “Wallahi karya ne” saita fashe da kuka “Da idona naga chats dinki satin auren mu, Khadija tana maki nasiha akan ki bari. Kuma idan ba namiji ba ta ina kika samu kudin dana gani” “Innalillahi wa inna ilayhi rajiun! Yanzu Laila ina gudun magana shine kike so ki hanani shiga makota” Baaba tace tana matse kwalla. Mallam dai banda kwafa baya komai. Ita kuma Laila gabanta ke fadi sosai, batasan me zai biyo baya ba. Duk ta kidime karya saketa. ” Wallahi Mallam ba karya nayi ba, wai ace satin auren mu take a bin maza hotel Wai tana tara kudin biki flsabillahi ” “Ni yanzu banida abin cewa, duk wanda Kaga an bashi hakuri toh wallahi an cuce shine, amma fa hakurin zan baka, tunda ka hakura ka aureta Allah ya baka daman jure sauran abinda zai biyo baya” Anan Mallam yayi masu nasiha mai shiga rai akan rudin duniya, sannan kuma da hakkin aure da kuma fa’idansa. Sosai yayi masu fada sannan Saif yaje mota yana jiran Laila. Baaba sai sababi takeyi kamar zata ara baki, fada tayi mata har saida tayi Kuka. Murna yayi sosai koba komi ya zubar mata da mutunci a idon iyayen ta, kuma yanzu koda takai karar sa babu mai yarda da ita. Awannan lokacin auren ya fita kanta, saidai babu yadda zatayi dole ta zauna. Babu wanda yace komi a mota har yakai gida, mamaki tayi daga ginin sa harya kai linta. Dakinta ta shiga inda ya shiga bangaren Sameera. Saida yaci yayi Nat sannan yace mata ai da Laila yake, tayi mata murna wanda saida taje ta duba ta. Koda ta isa tanata kakkabe dakin kura yayi yawa. Anan suka gaisa sannan Sameera ta Koma nata sashen inda ita ta cigaba. Bayan nan Sameera ta aika mata da abinci, taji dadi sosai saboda batada cefane balle 
 • kudin kirki. Bayan lsha Saif ya aika taje dakln Sameera. Wannan Karon ya gane yayi abinda ya dace. Fada yayi masu akan su hankaltu dashi sosai, baya san raini. Duk wanda bata iyawa saita bi gabas. Haka ya gama surutai babu wanda tace uffan. Daga nan Laila ta koma dakinta, takaici bai barta tayi ma Haske magana ba, banda kuka data kwana tana rerawa. Baaba tace idan ta kashe aurenta saidai tabi duniya amma karta koma gidan. 
 • Sannan Saifya cinye mata kudi babu halin magana, kuma ya saka tabar aikinta gashi babu gidan kajin. Tayi dana sanin barin sa daya yaudare ta akan aiki. Ko Haske data aura mai kudi tana zuwa aiki balle ita. Dayake ta iya gullisuwa, anan ta yanke shawara zata soma yi (ana siyarwa ma yan lalle, kafin wani kudin ya shigo mata ta koma babban sana’a. Zaman rashin dalili bazai flshe taba. Bayan kwana hudu… 
 • Iyayen Banan sun tura neman auren ta kamar yadda ta tursasa su. A wajen Umma ta koma ta karba number dinsa saboda fafuryaki bata. Daga nan yayi mata albishir da cewa tunda ita takeso tayi auren dole su zasu tura.Taso taki amma kuma ta tuna bashida abinda zai rasa a rashin aurenta. Balle zamani ya canza yanzu an goge. Haka sukeje babu girma babu arziki falon Abban Bilal. baima san da zuwan su saidai suka shammace shi kawai. 
 • ‘Daki ya koma yayita ma Lubna fada akan abin, ya nuna mata rashin amincewan sa kuma baiji dadi ba. Anan ya kira Bilal domin yaji ta bakinsa, idan yace bai so nan take zai fasa. Yadda yayi tambaya Bilal ya dago an tsare Umma ne, babu dadi ya mara mata baya. Saboda yasan zatayi fushi sosai a bayan idan Abbansa, anan Alhaji Bello Kamfani ya saka su yayita masu fada. Sun tozarta shi wajen baban Haske. Ace aure ko wata biyu bai cika ba har ana tunanin sake wani. Abun baiyi kyau ba ko tsari. Sannan babu girma a ciki. Hajia Lubna bada hakuri ta somayi, tasan tabbas batada gaskiya. Kuma batada bakin magana daya wuce hakuri. Koda Alhaji Bello ya koma falo yaji haushin ganin magabatan Banan, ta ina mace ke bin namiji neman aure? Suma dai hakuri suka bada tareda nuna cewa Banan ce take ganin idan ba’a yi haka ba hankalin ta bazai kwanta ba. Alhaji Bello ya yanke aure wata shida. Rai bai so ba suka tafi saboda bataso yafi wata biyu. Jira yaso su bada kudin sadaki karshen rashin hankali yace ya fasa. Banan bataji dadin abin ba amma hankalin ta yadan kwanta, idan akayi hakuri zataga kanta a dakin Bilal sannu a hankali. Bilal was indifferent akan labarin, ya riga ya fawwala ma Allah komai, Allah ne gatan sa yanzu kuma shine zai fitar da shi daga wannan abu. Haduwar sa da Haske ya bala’in canza shi, yanzu ya koma mutumin da za’a iya alfahari dashi. Mutumin da idan ya Kalle kanshi a madubi bazaiji haushin wani abu dayake yiba. Yanzu zai iya buga kirji yace yana kare hakkin Allah da manzan sa. Shi karin kansa yana jin dadin yadda ya canza, idan da chan zai biye ma Banan suyi masha’a dukda ba yau suka fara ba. Ita ce matar daya fara sani a matsayin mace, amma kuma bashi bane iarkon nata. A lokacin bai damu be. As long as zata soshi bai damu ba. Amma tun da ya kasance da Haske ya gane bambanci tsakanin mace mai kintsi da kuma kofar gari. Yanzu Haske ta sauko ta rage mashi zaf‘m kai, saida su Ammi sukayi kwana 3 kafin aka fade mata abinda ya faru. Shima saboda za’ayi family meeting ne anaso kowa ya hallara a Zaria harta Fijr dakejego. Sun hadu a falon Vaya Ali dake Gwargwarji dake Zaria, shine babban wansu Hadiza, Babu arziki ta kira shi tana mashi koraR Ta kusan shekara biyardataje gidansa balle tasan halin dayake ciki kona iyalan sa. Bata san yawan yaransa ba balle adadin matansa, kuma shine ya taimaka mata ta samu admission a ABU datake tinkaho. Yau yayi mata rana sabida shine ya roke Daddy Zailani alfarma akan yazo ya saurare Hadiza kila akwai wani explanation da ba’a sani ba.lmran Shima yaji labari ya dawo daga Jos, kowa ya hallara Bilal yakai Haske. Bai shiga ba saiya tafi wajen wani abokin sa lecturer a Nuhu Bamalli Poly idan an gama sai ya dawo ya tafi ita. Duka iyalan Alhaji Zailani, sai Hajia Binta da Mijinta Engr Muktar. Ammi tana ganin yadda Zailani ya dake ta sake shanjininjikinta. Chan gefe ta zauna kamar mara gaskiya, duk ta muzanta ta soma flta hayacinta. Wai ace batayi zawarci ba saida tsufan ta, idan Zailani yace bazai maida taba ina zata saka ranta? Kawar da tunanin tayi saboda bataso ta kawo wani negative thought, zai mayar da ita kuma mutuwa zai rabasu. 
 • Fijr kuma tayi bulbul ita da babyn, Hajia Binta na yin mata hidima sosai flye da yadda tayi deserving. Ta yanke shawara cikin ranta koda Daddy zai mayar dasu Allah ya amfana amma taga wajen zama. Hajia Binta tafi mata Ammi sau dubu. Ji tayi dama itace ta haife ta saboda tanada dadin sha‘ani. Ammi Hadiza kallon Haske take yi mamaki fal fuskanta, taga dukkan alamu tanada shigan ciki. Amma bari ta kashe wannan wutan daya fito mata, tana komawa dakinta zata koma Gwoza domin ayi aiki. Idan tana raye bazata haifa cikin ba kuma saita bar gidan ta tsiyace kamaryadda ta dauki alwashi. Anan wani dabara ya fado mata. Yadda Hafsat ta mutu ta aure Zailani kawai ta kashe Haske sai Fijr ta maye mata gurbi. Guntun murmushi tayi saboda taji dadin dabarar ta, kawai zata bari idan Haske ta kusan haihuwa ta mutu wajen haihuwa kamaryadda boka zai taimaka. Idan yaso babu wanda zaiyi suspecting dinta. Daga nan kuma za su ci karen su babu babbaka. Gyaran murya Yaya Ali yayi sai kowa ya mayar da hankalin 5a akan shi. Anan ya bude taro da addu’a na neman tsari da kauda shedan. Saiya tambaya Fijr waye uban yarinya, anan ta zayyana masu Isi ne kuma yanajin labarin ciki ya gudu, Anan aka rinkajimami. Sai akace za’a nema wani cikin dangi da zai rufa mata asiri. Ammi bataso ha, a yanzu tafisan Fijrta aura Bilal tunda yafl kudi. Sai kuma batun sunaryarinyar, Fijr tace ayi ma Ammi kara a saka mata Hadiza. Anan Ammi ta botsare akan saidai a saka sunar Hafsa amma ita baza’a saka sunar ta ba ma shegiya. “Wallahi Ammi sai an saka, sunar uwata za’a saka ma yata” “Babu wanda zai yi haka, ehe. Saidai Hafsa ko Binta ko kuma wani dangi amma kowa yasan Hadiza ba shegiya bace kuma babu wata shegiyar da zata gaje ni” Anan aka dakatar da Magana tukun Yaya Ali yace ayi maganar auren Hadiza da Zailani. “Yanzu ni Hadiza kin saka na tara mutanen nan masu mutunci, ki tabbata bayanin da zakiyi masu yanada muhimmanci” “Yaya kayi hakuri dani, nasan inada laifi sosai. Amma a yafe min. Dan adam ajizine. Zailani ya yafe min ya mayardani dakina. Inaso naje na rike yarana” tace tana kuka. 
 • “lea na gama zama da Hadlza, wanda mukayi Allah ya bamu ladansa. Yanzu kowa ya kama gabansa. Na yarda Fijrta dawo gida ta zauna amma ke keyi hakuri tukun” 
 • “Dan Allah kayi hakuri, nasan ka dade kana hakuri dani. Amma daga wannan baza‘a kara ba zan canza” “Ni yanzu gaskiya na gaji da wannan sirrin da aka boye ma yarinya, ko babu komai zata rinka ma mamanta addu’a. Amfanin yara kenan suyi mana addu’a bayan ranmu” “Kana tunanin ya dace yanzu kuwa?“ Engr yace “A bari ta kara shekaru mana” Binta tace “Wani girma kuma yarinya da aurenta” Yaya Ali yace Shima ya gaji da rufe sirrin. Charko Charko idon Ammi yayi, tana ganin kila Shamsiyya ta tashi tayi mata dukan tashi ki sha gishiri. Ita kuma Fijr ta san abinda za’a ce. Tana bama yarta glucose daga feeding bottle duk ta kosa a fasa kwai. 
 • “Ai yafi kyau wanda ta riketa tayi bayani” Daddy yace. Zaro ido Ammi tayi tana karkada kai. Batayi ma Shamsiyya rikon arziki ba batada wani abin cewa. Hawaye kawai ke malala mata daga idanu. ldanta yayi zazur kamar garwashi sunyi kanana. Baki yana rawa ta soma magana. “Dan Allah Shamsiyya ki yafe min, na dade ina musguna maki” wulla ido Hajia Binta tayi gefe sai tayi magana cikin ranta, ‘OH please! Munsan karya kike’ “Shamsiyya bani bane na haife ki. Hafsat twin sister dina itace mahaifiyar ki. Daddy dinku mijinta ne. Ta rasu tana nakuda zata haifa wani yaron. Anan duka aka rasa su” Banda kuka babu abinda Shamsiyya keyi, yanzu komai yayi mata daidai. 2+2 ya beta 4. Da chan maths din yaki haduwa. Ta rasa dalilin da Ammi take mata haka. Sau da dama daga nesa tana lura da yadda sauran yaran gidan ke relating da ita, ita ma saita kwaikwaya. Koda yaushe tana tunanin laifln daga wajen ta ne. Ashe ba haka bane. Ammi ta tsane ta saboda kishi, kishin da matar da bata raye. Kallon Ammi tayi tana kuka, magana ta soma ranta yana kuna, 
 • “Sau da dama ina tunanin wani laifin nayi maki, tun ina karama na dauka wani abu na fada wanda bai dace ba yasa kike min haka. Na kasa saisaita tunani waje daya na gane asalin dalilin dayasa uwa ta tsane yana” “Ga kama munayi babu yadda zance bake kika haifan ba amma kuma kina musguna min. A shekaru kadan kin azabtar dani wanda yafi karfin na mara galihu. Kinci zaraflna, kin dakeni, Kina bina da wasu mugayen fata. Duk ba komai bane saboda n’I yar kishiyar ki ne” “Kishiyar da baku hada miji ba, matar da saida ta mutu kika aure mijin ta. Inace dan uwa shike rufawa dan uwansa asiri. Amma ke kam an samu akasin haka. Kece kike so kiga na lalace kece kike so kiga nabi duniya, kece kike so na tagayyara cikin gari” “Babu irin fatan da bakiyi min ba, kece kike cewa in sha Allah sai nayi tsintar bola, in sha Allah sai nabi titi ina bin maza. Ammi for what? Me Hafsat ta mik’I da kika sauke laifin akan amanarAllah da aka mika maki!” “I’ve lost my selfesteem and self confidence saboda abinda kike min, nine kullum ina bin mutane inaso suyi kawance dani. Nice da ance ana sona kamar anmin duniya. Ni ce seeking relevance daga waje saboda bana samu a gida. Ko magana mai dadi baya hadamu balle kisan yadda na tashi ko matsala na. Kawai kiga na susuce, sau da dama ina gwammace mutuwa da farkawa naga kaina cikin gidan ki” “Babu komai duk da haka bai hana ni tunanin wata rana zaki soni ba. Ina da hope din cewa wata rana nima zakiyi alfahari dani. Nima zaki Kalle ni kamar yadda kowace uwa take kallon yarta. Nima zaki zame mani wanda zata share min hawaye ki kare min hakki na… ” Kuka ta barke dashi sosai, bataji dadin yadda aka boye mata ba. ldan so samu ne data 
 • Zauna a Zaria wajen kakannin ta yafl mata kwanciyar hankali. Hajia Binta saida ta matse kwalla, Shima Imran kukan yakeyi. 
 • Ammi bakinta yayi murus,jibe yadda Haske take gaya mata magana, “Nidai nasan ban kyauta maki ba, kawai ki yafe min” Daddy idonsa yayi ja, na maza yayi daya barke. Hafsa yake tunawa. Yasan sun zalunce ta, sun ci amanardata bar masu. Wata kila shine Allah yajarrabe su da Fijr. Tashi yayi yaje inda Shamsiyya ke zaune, kuka kawai takeyi babu tsayawa. Hannun sa yasa yana bubbuga mata baya, bai ce komai ba saida yaga ta daina sarkewa da kukan saiya koma mazaunin sa. “Shamsiyya ba Hadiza ba kawai harni, we all failed you. A idona akayi haka kuma na kasa tsayarwa sabida Hadiza ke lura da gidan lokacin. Daga baya kuma it was late. Dan Allah ki yafe mana” 
 • “Karku damu Daddy na yafe maku, Allahu gafurur rahim, nima inaso wata rana ya yafe min” “Almura” Ammi tace cikin ranta. Watau Shamsiyya tayi saurin yafewa sabida ace tanada hankali. Da badin tana neman komawa dakinta ba ai babu abinda zaisa ta roke ta. Kuma ta samu hali zatayi wanda yafi dubun sa. “Bilal yace kinje gidan Mum dinsa kince nayi ciki ya sake ni ko yayi aure? Please Ammi kece min ba da gaske bane!” Wuri wuri tayi da ido, kana ganinta kasan batada gaskiya. “Allah ya tsine maki Hadiza bakiji dadin halinkii ba” Wata gwaggo dinsu

  tace. Anan Yaya Ali yace Amin. Kowa ya soma tofa albarkacin bakinsa akayi mata wankin babban bargo. Ana maganaryadda Fijrtayi ciki amma bai isheta ishara ba. Dataga kamar basuda niyyar bari kwashe kafanta tayi fuu kamargudun iska. Wannan kenan! 


[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]