[Advertisements⬇️]

HASKE CHAPTER 18 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 • HASKE


 • CHAPTER 18

 • Koda Saifya dawo kai tsaye dakln Sameera ya wuce tunda dama nan yake. Balko bl takan Laila ba, ita kuma Sameera a lokacin taje dakin ta kai mata abincin dare. Tuwon semovita tayi da miyan kubewa danye.
 • Laila dan shegen rowa bata tsamma Sameera kajin dasu Haske suka bata ba balle wani fruits, haka tayi mirsisi abinta. Gashi Sadiya sai zillo takeyi tanaso taci.
 • Sunji karar shigowan sa amma sunata raba ido tunda dai Laila babu lafiya. Shiru har minti kusan talatin. Abul Khair ne ya shiga dakin Laila wai Sameera taje ana kiranta.
 • Dama tabar yaranta chan suna kallon cartoon The lion Guard 3 Disney. Mikewa tayi suka tafi tare, ita kuma Laila ta kishingida tana cin abincin ta. Yau ranta fes yake kamar an biya mata kujerar Makka. Kaji ta dauko ta soma yaga tareda fruits. Tanayi tana tunane tunane yadda zata shawo kan matsalar tana Haske, idan ta fldda ta daga gidan saita maida hankalita kan Sameera domin ta koreta. Saboda dama matsalar Haske ne da tuni tayi sanadiyar sakin ta. “Assalamu alaikum, sannu da dawo wa” “Wato ke dan rashin mutunci kinaji na dawo shine

  kikayiburus dani koh? Wato har nayi lalacewar da nine zan rinka bibiyan ki? Yanzu dan kutumar uba kin zauna dakin yar iskan chan ko kishina bakya yi kin hada kai da ita! Allah ya wadaran naka ya lalace Sameera, kinyi asara” “Kayi hak’uri dama nasha tanan zaka biya shine nace sai mu dawo tare, bari na kawo maka abinci”

 • Bata tsaya taji mai zai ce ba ta mike da sauri ta nufa kitchen, shi kuma tsaki yayi yana watsa mata harara. Remote ya kwace a hannun Abul Khair sai ya canza zuwa Zeeworld.
 • Dama yana bala’in san tashan kamar ba namiji ba, balle yanzu an dawo da Twist of Fate na Pragya da Ahbay.
 • A tray ta saka cooler biyu na tuwo da miya. Sannan saita dauko plate da kuma kunun aya ta tsiyaya mashi a kofl. Duk yadda ya so ya bata rai ya kasa sai walwala da annashuwa ya soma.
 • Haka ya soma ci yana watso mata hira jefi jef’l harda barkwanci. Shap ya mance shine ya watsa mata ashar dazu. Yaci yayi nat baida niyyar zuwa wajen Laila. Sameera itama ta lura sai tayi mashi magana.
 • “Baban Abul baka tambaya ya mai jiki ba” Shan kunu yayi saiya soma magana 
 • “Wani bayada lafiya ne?” “Laila ka mance ta taka kwalba” “To ai ban aike taba” 
 • “Amma yaci ace dai ka duba ta koba komai zataji dadi” Shiru yayi yana tunani saiya mike ya fita. Ranshi a bace ya shiga dakin. Tana zaune kan 3 seater daga ita sai wani arniyan night gown iya cinya. 
 • Kallon Korean film takeyi a DVD mai suna Doctors. Tura kofa yayi sai ya shiga, ko sallama baiyi ba ya tsaya mata akai kerere. Ita ce ta soma magana a shagwaban ce wanda ya dakatar da ita. 
 • “Destinyyy tun dazu nakejiran ka wallahi kafana sai zugi yakeyi, gashi kaina ma ya soma “Ke dan ubanki nine kikejira na biya maki kudin magani?” “Haba Destiny wa zai biya min?” “kin raina kanki nine zan biya maki bayan duk kudin da yake karkashin kapet” anan gabanta ya fadi ashe yasan dashi. “Wani… Kudi ?” ta soma inda inda Inda”Ban sani ba” sai ya watsa mata harara. Zuwa yayi wajen ya kwaso kudin. Wrap biyar ne 
 • yanzu saura hudu da guda daya wanda baifi dubu biyar ba. Zaro ido tayi sabida sai a lokacin ta lura da yanayin kudin. “Me kayi min da kudin?” “Karki raina ni, dakai da kaya duk mallakar wuya ne” “Kutumelesi wallahi saika biya ni” saita mike tsaye tanajijiga. Kallon ta yayi ya soma dariya. Kana gani dambe takeso tayi dashi. “Da kika mike me zaki iya yi? Ni sa’arki ne?” 
 • “Wallahi kudin nan basu ciwu ba saika bani, karyan iskanci kakeyi shege ka fasa!” 
 • Tasss taji saukar mari, kafin ta daga kai kuma taji saukar wani. Sannan saiya hankadeta kan kujera. Hawa kanta yayi ya soma kilarta. 
 • “Nine dan iska, yau saina nuna maki karshen iskanci, na gaya maki ki hankaltu dani sabida banida mutunci amma kinki ya janyo wayan DVD  dake gefe ya rinka bin lafiyar jikinta dashi. “Ni ka daina dukana” ta fada tana kuka. Duka yakeyi kamar Allah ya aike shi ya kashe ta. Yau duka na biyu kenan taci bayan kwalbar kafanta. Anan ya yaga mata kaya sai karamin wando kawai. “Bakisan dama ina hakonki ba, shegiya yar iska” 
 • “Niba yar iska bace wallahi” daga nan ta soma ramawa. Dukan juna suka hau yi har Allah ya bata dama ta ganna mashi cizo ya dagata. Tuni ta dingisa kafar ta tayi waje ta soma watsa mashi ashar. 
 • “Shege tsinanne, aida ka tsaya na shayardakai madaran mamaki” shi ma ya fito waje amma ya ganta rike da mopstick. Sameera taji hayaniya ta fito waje. 
 • “Dan Allah ku bari mana, wallahi babu girma a abinda kuke yi” ko kulata basuyi ba. “Barni da yar iskan nan, zaki san baki iya bariki ba. Daidai nake dake. Asalin dan tasha kike gani. Ko yan maraba da Tafa sai sun mara min baya” “ka sake tabani idan ban fasa maka kaiba” Karasawa yayi yaje gabanta yana sha wasa takeyi. Anan ta zabga mashi mop akai. “Lalalala ! Dama bakida mutunci ni mijin ki kike duka?” Ta daga zata saké zabga mashi saiya rike abin. Anan ya finciko ta dambe ya sake kacame wa. Ya samin galaba akanta amma Shima yasha yakushi. Sameera ne tayi kokarin raba su inda tajanye Laila, nan suka soma tona majunan su asiri. Yace ai ba budurwa ya sameta ba ta tona yadda yake cema Sameera yayarsa da kuma duk mugayen abubuwa da suke mata. 
 • “Toh dan ubanki zoki tafu gidan ku har saina nemeki” anan gabanta ya fadi sosai. Me zata ce masu Baaba idan ta koma batayi wata uku da aure ba.

 • Bayan sati shida 

 • Aminta ya kullu tsakanin Ammi da sabbin yaranta biyu. Kullum Banan tana gidan tana mata fadanci. Suna kulla makirci kala kala wanda zasuyi Amfani dashi wajen fidda Haske. Laila akejira ta warke domin ta kaisu gidan, ita kuma sai inda inda ‘akeyi saboda bataso kowa yasan halin datake ciki. Daga Ammi har Banan basu san gidan ba, Fijr yar ra’ayi taki kaisu, Baraka ta koma makaranta. 
 • Ita kuma Laila abin duniya yayi mata cinkoso yanzu, Saif ya kwace kudinta bai barta taje dashi gida ba. Koda yaje bayan kwana biyu yace nashi ta sace, dama haka take masa sata na kayan abinci. Har lefenta ta siyar. Sannan gantali takeyi inda taje akayi mata duka. Karya yayi masu mai rai da Lafiya, Mallam baban Laila saida ya mareta datayi kokarin kare kanta akan kazafin Saif. Anan yayita bama Saif hak’uri akan ya mayar da ita. Saif yace ya hakura ta shirya kayanta bari yaje ya dawo. Aikam taflya yayi bai sake komawa ba. An kira wayansa yafi a kirga amma yaki dauka. Gashi Mallam yace karta kuskura ta fita inkoba haka ba saidai taje inda ta fito amma bazata sake zaman gidan shi ba. Duk tayi bakin kirin ta rame sosai duka aikin gidan wanda batayi ada chan yanzu takeyi. Ita kema Baaba wankin kayanta. 
 • Gashi batada shigan ciki balle ta fake dashi, tashin hankali take ciki mara misaltuwa. Babu damarta gayama Haske kafin tayi mata dariya. 
 • Karya tayi wai sun tafi Danbatta garin iyayen Saif sanda Haske taso sake dubata. 
 • Saifyanzu yana cin kudin Laila abinsa, bada dubu dari yayi aka siyan masa sabon injin sealing ruwa tareda saida tsohon. Sannan ya soma tada gininsa. Wannan karan 2 bedroom yayi da bayi biyu da falo, kitchen da store a ragowar fIlin. Yanzu tsakar gidan su duk ya tsuke sai motarsa kawai da fili kadan. Yace shida sabon amaryar sa dangin Oduduwa zasu zauna. Yarbawa sunfl iya rike miji kuma dole ya nema daya ya aura. Kila ta zame masa sanadiyar samun arziki dayake buri. Business din Sameera sai habaka yakeyi yanzu, ta fara wrapping souvenirs in bulk tana siyarwa. Na turare, kasko, sagem da mahallabiya. Haske tanada shigan ciki mai laulayi da kwadayi, daga ciki akwai farin kasa, gasharshen masara da tuwon alkama da miyan kuka. Sai tace bari taje Gidan su Laila wajen Baaba domin a gyara mata alkama akai mata nika. Balle dama tun aurenta bataje ba, daga nan sai tayi masu wuni. A kasuwan Unguwan Shanu za’a siya a nika mata, kuma Baaba nada customer din mai siyarda kuka. Jallabiya tasa baki da kallabin sa, fuskanta babu komai akai banda kwanciyar hankali. Jaka a hannu daya sai makullin meta a daya, takalmi tasa mai dan tudu Zara. Da murmushi ta shiga gidan tareda sallama. “Assalamu alaikum..” sandarewa tayi, taga mutum kamar Laila tana bakin rijiya tana scholar mai uban yawa. Gashi tayi baki sosai ta fita hayacinta. Laila ta dago zata amsa saka ga Haske ce. Anan duk ta muzanta. Hawaye ya soma malalo ma Haske daga idanu. “Meya faru dake? Ina ce kina Danbatta?” kukan kunya Laila ta fara. “Wallahi Saif baida mutunci, nafi wata daya a gida” “Shine baki gaya min ba? Yanzu akwai sirri tsakanin mu? Komai nike gaya maki amma shine zaki min haka!” 
 • “Ba haka bane banso na takura maki ne” 
 • “Kamarya takura, munfa zama daya ni da ke. Kukan ki nawa ne. Bakin cikin ki shine nawa, tashin hankali ki duka nawa ne. Dan Allah ki daina haka mana” Baaba taji hayaniya saita leko “Shamsiyya saukar yaushe?” “Yanzu nazo, ina wuni” saita rinsina har kasa ta gaida ta “Lafiya lau, ya mijin ki?” “Alhamdulillahi”
 • “Sai kikaji abinda ya faru! Wallahi kawarki bata kyauta ma mijinta” 
 • “Yanzu nakeji nima, banida labari tuntuni” Kallon Laila Baaba tayi Saboda mamaki yadt bata gaya mata ba. Sai kuma tayi tunani komai nasan sirri. Ke Laila barwankin haka ku shiga daga daki mana” 
 • Hannunta Haske ta rike suka tafi, zuciyar ta kuna yake mata sosai. Hawaye sirara ke malalan mata. Tausayin Laila take ainun, she doesn’t deserve to suffer haka. Saif yaci amanarsoyayya. Suna cikin daki sai Haske tabama Mashkura kudin taje ta siya kayan, Laila batayi suspecting ciki ba kuma ita kuma ta mance ta fada mata. Har waien yamma suna tare, a lokacin kuma an gama mata gyaran garin an nika zatat 
 • Har wajen yamma suna tare, a lokacin kuma an gama mata gyaran garin an nika zata tafi. Wani abu ya fado mata a rai data bar Laila a gidansu tayita shan wahala gwara kawai ta dauketa su tafi gidanta. Kallon Laila tayi tana murmushi, 
 • “Please tawan, idan nayi ma Bilal magana zaki yarda ki dawo ki zauna dani? Dan Allah karki ce a’a” saita dungule hannayenta biyu tana rokonta. lta kuma basarwa tayi tareda wulla ido. Uhmmmm su Baaba fah?” “Karki damu dasu, basu hanani ba idan na roka, kawai ke nakeso ki yarda” “Okay na yarda” Rungumar Laila tayi tanajindadi kamar Bilal ya amince mata, koda yake yanzu Bilal baya mata musu, abinda taga dama shi takeyi. 
 • Har bakin mota Laila ta rakata, motar Benz baka kirin mai tint sai sheki yakeyi. Hadiye wani mugun miyau tayi saboda bakin ciki. Saida ta bi motar da yatsunta tana shafawa a hankali saboda ya bala’in burgeta. A lokacin wani bakin ciki ya sake mamaye ta, wai Haske mara galihu da bata tashi ana santa ba ita take cikin wannan kwanciyar hankali da daular. Meye Haske takeda da ita batada shi. All these things supposed to be hers. Koda yake kowa da nasa kaddara, amma wannan kaddaran ne ya kamace ta. lta ce ya kamata tayi aure cikin kudi tunda iyayenta basuda shi. lta ce bata tashi cikin kudi ba, itace ta tashi tana cin dumame. Saboda haka itace yafl cancanta akan ta aure mai kudi yadda zataji dadin duniya. Haske ta shiga da niyyar zata dawo anjima, abin yayi ma Laila dadi. Koba komai zata zama sojan gida. lta ce zata rinka kaima su Ammi rahoto yadda ya dace. ldan ma Ammi tazo da wani kayan magani ita ce zata birne ko ta saka mata a abinci. ‘Dakinta na zaure ta koma wanda yanzu tana zaune tare da kanwarta Mashkura, a tsanake taketa kokarin hada kayanta. Zata kashe tsuntsu biyu da dutse daya. Koba komai tasan Haske zata ce ma Bilal ya canza mata suturu, kuma ga cin mai kyau da sha, fatarjikinta zaiyi laushi. Bilal ya isa kenan sai ga Haske, yana bayi yana wanka sanda ta shiga dakin. A bakin gado ta zauna tayi tagumi. Tausayin Laila kawai yayita bin duk ilahirin jikinta. Dukjikinta yayi sanyi, saidai kuma tasan jarrabawa Allah yajarabce Laila dashi kuma tana fatan taci nata da flying colors. Hura mata iska yayi a fuska wanda ya flrgitar da ita. Murmushi suka sakar ma juna saiya soma gage ruwan jikinsa da towel. Tashi tayi a natse taje wajen sa. Karba tayi tana taya shi amma ba tace komai. Bilal ya riga ya karance Haske, yasan idan abu yana damunta ta rinka wulla idonta kenan tana tunanin. “Sweet ya akayi?” murmushi tayi ba tace komai ba. “Me ke damun ki?” 
 • “Dama Laila ne ta komai gida! Can you imagine Saifyayi mata wulakanci wai tafi wata daya” tashi yayi tsam ya koma wajen dressing mirror. Bayaso yayi wani magana daya jibance Laila. “Sweet bakaga yadda ta koma ba, duk ta rame saika ji tausayin ta” “Allah koh!” “So I was thinking maybe, ta dawo nan ta zauna ….. 
 • Daga mata hannu yayi domin ya dakatar da ita. Fuskansa ya canza farad daya. ldansa ya canza kalla. “Karki kuskura kice zata dawo nan dan bazai yiwu ba” “But Sweet wanda ya taimaka ma wani Allah zai taimaka mashi” 
 • “Final warning Shamsiyya, karki sake min maganar nan” Mamaki tayi saboda bai taba kiran sunarta ba. Saidai idan ance sunar ta na asali. Amma yau shine yake wani daga mata murya haka. “Sweet meye tayi maka haka? Why do you hate her so much?” 
 • “Kema ki gaggauta fita harkan ta” 
 • “Wow Bilal! Na gane irinku. Kune mazan nan masu raba matan ku da kawayen su saboda selfish interest dinku, well I have news for you saboda bazai yiwu ba” 
 • “Meye matsalar ki ne? Kinada sauran kawaye a gari, ki zaba daya daga cikin su mana basai ita ba. Please baby do this for me” “Abinda na lura shine kasan she can’t be manipulated, zata fada gaskiya komin dacinta, idan abu baya taflya daidai zata gaya min shine kake tsoro koh?” “Wai ni ina ruwana da Laila, da ace tana maki soyayyar gaskiya wallahi baza kiji baki na ba amma ba‘a sanki” Anan kawaii ta fashe da kuka, Bilal yana ma Laila mugun tsana daya rufe mashi ido. Ya riga yayi nisa bayajin kira, dafin tsanarta yaci shi sosai. Amma ya za’ayi yace wai Laila bata mata soyayyar gaskiya. Duk sanda take neman kawa kuma abokiyar shawara Laila tana nan amma shine har zai iya bude bakinsa ya furta haka. Mikewa tsaye tayi cikin fushi, hanyar fita tabi kuma ta banko kofar dakin da karfln gaske. Baiko damu ba, yasan Haske batada riko zata sauko inda zai kuma fahimtar da ita akan Laila. 
 • Ita kuma Haske gado taje ta kwanta, kuka takeyi wiwi kamar ranta zai fita. Abinda Bilal yayi yake bata mamaki, prisoner dinsa yakeso ya mayar da ita kome? Yanzu bayan wannan sai me? Zai ce tabar aikinta ne kuma ta daina zuwa gidansu Mommy kuma kome? Wani zuciya ya soma raya mata maganar da sukayi kafin auren da Laila. lnda tace Bilal ba mutumin arziki bane gashi tun kafin aje ko’ina ya soma nunawa. “Ya ilahi” Ta furta tareda shafa cikin ta, gashi yanzu zata hada zuri‘a da shi. Wani sabon hawaye ya soma gangaro mata. Tana cikin tsaka mai wuya. Yanzu ya zatayi da halin Bilal dinnan. Nan gaba mai zaiyi mata kuma. Laila sai zuba ido takeyi tana jiran Haske babu alamarta, gashi har magrib ya gabato. Rai a jagule tayi sallah dukta kosa tazo su tafi. Daga baya saita kira wayar Haske taji a kashe. Anan ta bita da ashar tareda tsine mata sosai. Ammi ne ta kirata domin ta shaida mata good news. Sun yanke hukunci akan zasu gidan maman Bilal domin su gaya mata asalin waye Haske. Kuma suna so dole Laila taje. Bayan wayan tunani kala kala ta soma, daga bisani ta samo karyan data shirya rna Mallam akan Mommy ne babu laMa kashegari zata US to tanaso taje tayi bankwana. Sun aminta mata saidai ance kar tayi dare, a cikin daren ta goge kayanta tsab da gyale wanda zata saka. 
 • Haske batayi abincin dare ba ranar, kuma ta rufe kofan dakinta gam babu damar ya shiga. Babu irin rokon da baiyi mata ba amma taki sauraren sa. Haka ya tafi abinsa, tunda sukayi aure wannan shine ranar farko da suka kwana a daki daban. 
 • Da asuba ya tashi yaje masallaci, dama baya dawowa sai gari ya soma haske. lta kuma tana kokarin tayi saurin hada ma kanta kayan kalaci kafin ya dawo, yasan zatayi haka tunda bataci dinner ba saiya dawo da wuri. 
 • A kitchen ya riske ta, yana tsaye bakin kofa yana kallonta. Sam fushi bai mata kyau ba. Tana ganinsa ta hade girar sama dana kasa k0 kallon inda yake batayi ba. 
 • “Sweet fushin ne haka? Ko gaisuwa?” I’lna kwana!” tace ciki ciki wanda bata ma Kalle shiba “Haba mana meye yayi zafi haka? Kinsan halin Laila kuwa?” ya fada cikin takaici tareda girgiza kansa, sannan saiya lashe bakinsa daya bushe. “Da kinsan halin ta da bazaki min haka ba” hawaye ta soma, ranta yana mata bala’in kuna gashi sai harbawa yakeyi kamar zai fashe. Wai yau Laila ita ce abin kyama wajen Bilal, duk sacrifice din da tayi akan ta kulla su, dama dai dan adam butulu ne. Jan majina tayi tareda amfani da hannunta domin share fuskanta. “Nasan halinta Me da yadda nasan halin ka. Meye matsalar ka da ita? I know her har na tsawon shekara goma sha uku” “Hmmmm! Toh sai mene? Maybe da chan tanada kirki amma yanzu ta canza””Please ka bari banaso naji! Na gane nan gidan ka ne but duk wani mugun magana akan Laila inaso ka bari! Please dan Allah nace” Kallon mamaki yake mata, sai kace makauniya kowa yaga Laila yasan bata santa. Meye haka duk tana wani zuzuta aminta su. Zuciya yayi saiya bar wajen. Dakinsa yaje ya canza kaya, fita yayi yabar mata gidan ta zauna ita kadai. 
 • Shi bazai iya da wannan tashin hankali ba, abinda yasani Laila bazata dawo gidan ba koda tana tsw da bahuguwarjaba. Zuciyar sa sai tafasa yake masa, how can Haske be so naive. Ga abu a fuskanta amma taki gani. Koda yake hankali ke gani kuma baya tunanin suna tareda ita yanzu. Laila wajen tara na safe harta gama Shara da wanke wanke, abinda wata rana zata kai sha daya amma yau saboda taso mugunta tayi da wuri. Ita ce ma ta tada Ammi daga barci saboda kada su makara, komai takeso ya faru yau. Ita kuma Fijr tun shigan satin take fama da ciwon baya, ta siya aboniki da adararbakur tana shafawa amma sai karuwa yake yi. Ta rasa gane kan ciwon gashi yanzu kuma yau ta tashi da ciwon ciki. Wajen sha daya Ammi tazo tayi mata sallama zata fita, zaune ta ganta a kasa zaman dirshan. “Lafiya dai Fijr””Jikinaje ciwo” “Okay Kisha magani, Allah ya sawake” “Amin sai kin dawo” Banan tazo kofar gidan ta dauketa sannan suka biya suka dauke Laila. A bakin titi taje ta tsaya saboda zumudi, kai tsaye gidansu Bilal suka wuce. A falon maman shi suka zauna. Dayake batasan da zuwan suba. Hajia Lubna dattijuwa ce wanda take bala’in san yaranta, a duniya bata ganin aibun su yasa duk yadda aka kawo mata gulma akan Bilal bata dauka. ldan ta tambaye shi akan maganar zaiyi denying shikenan zata watsar da zancen. Tanadajiji dakai kuma anan ya gada girman kansa, idan zakayi mata fadanci toh zaku yi shiri sosai. Ta saka kayan alfarma mai bala‘in kyau, girar sama dana kasa a harde. A three seater ta zauna tana bin su da kallo daya bayan daya, tuni Ammi ta muzanta balle akwai ta da inferiority complex. Daga bisani ta gane Banan, sakin fuskanta tayi ta soma magana. “A’a wama sunar ki?” “Banan ! ina wuni Umma” “Laflya lau yaushe kika dawo?” “Na dan kwana biyu” “Allah sarki” 
 • Sai suka gaisa da Ammi da kyau, itama Laila ta gaida ta. Anan akayi shiru falon yayi tsit. Ba abinda ke motsi sai TV dake aiki. “Lafiya dai koh?” Hajia Lubna ta katse shirun. Ammi ce ta soma magana, anan ta zayyana mata cewa Haske tayi ciki kafln tayi aure. Kuma an koreta har wajen shekara daya da kusan rabi. Laila tace ta dawo gidansu da zama amma kusan kowane dare saita fita, balle dama dakin zaure suke babu wanda zai lura. Haka Ammi da Laila suka la’anci Haske abin tausayi. 
 • Tuni hankalin Hajia Lubna ya tashi, wai ace danta ya aure gogaggiyar yar bariki haka. Idan ita ta haife shi a yau dole saiya sake Haske. Saida Ammi da Laila suka faki idon Hajia Lubna suka tafa sunajin dadin abin. Ransu yayi fari sosai da sun sani data wajenta suka kama kafa. Anan Hajia ta kira Bilal akan Lallai sai yaje tana kiransa, yace toh bari zai je bayan azahar. Koda ya koma gida Haske ya gani a falo tana zaune. Batabi ta kansa ba ko sallama ciki ciki ta amsa. “Ki kawo min abinci daki” yace “Banyi dakai ba” tace tareda watsa mashi harara. Cak ya tsaya yana kallonta, “Me kika ce?” “Banyi dakai ba, kuma daga yau bazan sake dafa abinci dakai ba muddin baka daina zargin kawata ba””Shamsiyya wallahi ina tausayin ki! Wata rana zaki gane kuma zakiyi kuka” Wucewa dakinsa yayi saiya shiga wanka, daga nan ya wuce ya fita domin yanajin yunwa. Rich bites ya wuce yaci jollof da coslow saiya tafl gidansu.  Sallama ya somayi amma bai karasa ba saboda idonsa ya sarke da fuskan da bazai mance dashi ba. Wannan fuskan ya janyo mashi tashin hankali bila adadin. Toh me takeyi gefen Ammi da Laila, yanzu kuma iskanci Haske har yakai ta hada shi da mutane akan magana kadan. 
 • Karasa shiga yayi saiya zauna a kujera gefen Umma, ko gaisuwa da kyar take amsa masa. Kana ganinta kasan akwai magana a bakin ta. Gabansa tun a hanya yake faduwa, yanzu kuma abin ya tsananta. Baisan hukunci da Umma zata yanke be. In fact bai ma san zurfin laifinsa ba. “Ashe ban isa dakai Bilal bal” anan kuma gabansa ya sake fadi. Zufa ya soma karyo masa. Yasan shi mai laifl ne amma wanne daga ciki za’ayi masa fada akai yau. 
 • “Ashe ban isa dakai ba Bilal!” “Yau nice abin wulakantawa!” “Shine dan ka tozarta ni ka aure yar hannu yar bariki a matsayin mata?” “Ban gane ba Umma” “Ina zaka gane? Nace ina zaka gane? Kaje ka aure yar iska dukta shanye ka da ruwan bariki dole ina magana kanayi” “Wallahi Umma bansan me kike magana akai ha?” “Shamsiyya daka aura inace saida aka Koreta ta koma bariki? Gasu dai kana ganin wanda suka fada” Kallon su Ammi da Laila yayi wanda basa komai sai annashuwa. Kallon dayake binsu dashi irin kallon sunyi asara, saiya mayar da hankalin sa kan Umma. “Umma nine mijinta, kuma zan tabbatar maki da cewa ba gantalalliya bace, nima kafln auren an kawo min gulma haka amma na share” 
 • “Ina zaka gane anyi amfani da sirihin bariki an shanye ka” sai kuma ta fashe da kuka tana tafa hannu.”Na shiga uku ni jikar Sa‘adatu, yau jinina ne ke auren yar hannu. Shikenan na gama jin kunya a gari” “Toh wallahi sai dai ka saketa tun kafln ta dauki ciki mu bani” Zare ido yayi, gabansan ya cigaba da gudu fiye da yadda ya dace. 
 • “Haba Umma, wannan wani irin magana ne? Makirci ake kulla wa. Wallahi na rantse da Allah Shamsiyya mutumiyar kirki ce” sai ya fashe da kuka tareda dukawa gwiwa biyu. 
 • “Kai dalla chan sakarai ana kokarin raba ka da mai farin kafa kazo zaka kawo mana shirme” Ammi tace “Nice nan uwarta kuma daba mutumiyar arziki bace da bazan fada haka ba, family din mutunci bai dace ku danganta kanku da ita ba. Ko babanta ya kore‘a balle kai. Sakinta zakayi yanzu munajira” Tashi yayi yaje wajen Laila ya haska mata mari, “Dan ubanki ki fada gaskiya, Haske yar iska ce koko?” cikin kuka ta soma magana “Wallahi yar iska ce, kowa ya Santa a KASU” Sake haska mata wani mari yayi cikin zuciya, yau Kota fada gaskiya ko taci duka, kuma ko Ammi albarkacin Haske taci data daku. “Bazaki fada gaskiya ba saina nakasa ki” “Ko kasheni zakayi yau gaskiyar kenan, Haske yar iska ce” “Ya isa haka dukan ku, karku tada min hayaniya akan wata daban, magana daya saidai ka rabu da ita kafin ta bata mana suna a gari” “Umma dan Allah kiyi hakuri, bazan lya rayuwa ba tareda ita bane. Ta fita daban akan sauran matan da nake hulda dasu” “Ban kashe iyayena ba kuma kaima bazaka kasheni niba, ban janyo nasu abin kunya ba kuma bazaka janyo min ba. Dan haka na riga na gama magana” “Umma alfarma nake nema wajen ki, ki barni na zauna da matana tunda ina san abina yadda take” “Karya kake! Saika saketa” Ammi tace. Banan dai ta kosa ayi sakin ta soma maganar aurenta. Shiru Umma tayi tanata nazari, ta rasa me Haske take masa daya rude akanta. Bata taba ganin yayi haka akan mace ba. Ko sanda su kayi soyayya da Banan batayi tsammani zai saka kamarsa ba amma wannan ya ninka sau dubu. Toh idan bazai sake Haske ba dole ta tursasa mashi akan ya aure Banan. Ajiyar zuciya tayi ta soma kallon su, kowa yasan magana zatayi wanda ake tunanin shine na karshe. 
 • “Toh shikenan, umurni na karshe zan bada. Koka sake Shamsiyya kokuma ka aure Banan. Ya rage naka” Fuskan Ammi da Laila ya canza, ba abinda suke so ba kenan. Sunf’l san a some sakin Haske. Fata suka soma yi akan tsanar da yayi ma Banan yanada yawan gwara ya sake Haske akan ya auro wata Banan. Sunkuyar da kai kasa yayi yanata hawaye, yau shine yake cikin tsaka mai wuya. Gashi kuma akan Laila ne Haske ke masa rashin mutunci. Banda Santa da kare mata martaba baya komai amma duk bata gani. Share hawaye yayi da handkerchief, bai ce komai ba. shi bashida zabi cikin biyun. Yanzu koda ma ya zaba Haske ya lura ta soma gajiya dashi, ba zaman laflya zasuyi ba zasu rinka 
 • tashin hankali. Anan take mata suka soma fita kansa, halin su sai su bazai iya gane yanayin tunanin suba. Babu hikima idan suna wani abun. Hawaye suketa saukar masa sai ya soma magana. “Umma baki taba tambaya na abu naki ba, daga Allah da manzan sa sai ke a wajena. Banida wadda tafiki Umma…. A cikin zabin nan biyu na zaba…” Laila rufe ido tayi tana addu’a ya zaba sakin Haske, harda addu’a ta hada dashi na ayatul kursiyu. Ammi ita dai baza kunne tayi tanaso taji good news mai dadin gaske. Banan kuma fata takeyi a aureta a haka din sai daga baya ta kore Haske. 
 • Fijrtana zaune sai ruwa ya tsinke mata ta kasan jikinta, Lantana ta kira inda ta sheda mata nakuda takeyi. Anan gabanta yayi mummunar fadi saboda sun riga sun kwantar da ciki. lhu ta soma kwararawa tana sambatu, nan ta soma ma Lantana explanation kamar ta tambaya. “Wallahi ba ciki bane, ina ganin kari ne” tace tsoro fal ranta. Sai wani contraction ya kamata. Tuni ta sake tsala ihu tana flsge fizge. 
 • “Lantana kira Ammi a waya ta dawo” an kira Ammi amma tana jira a sake Haske, tuni ta saka wayar a silent tareda rejecting call din. Gashi babu driver da zai taimaka masu wajen kaisu Asibiti. Dayake Lantana ta taba aure sai ta taimaka ma Fijr. lta ta rinka taimaka mata har ta haifa yarta mace. Shigan Daddy kenan saboda ya fita tun safe, kukanjaririya yaji yana fita daga dakin Fijr. Sannu a hankali ya taka yaje dakin. Gabansa ya soma fadi na rashin dalili amma ya dake ya cigaba da taf’nya. Murda kofan yayi saiya bude, yana yayee labule yaga Fijr da Lantana tareda jaririya a hannu. “lnnalillahi wa inna ilayhi rajiun” yace cikin tashin hankali. Nan take kansa ya soma Sara hawaye ya fara malala masa a fuska. Va mance yaushe raban da yayi kuka tun mutuwar Hafsa. Bakin ciki mara misaltuwa yake ciki. “Wallahi Ammi tasan inada ciki” tace tareda fashewa da kuka. Wannan kenan! 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]