[Advertisements⬇️]

HASKE CHAPTER 17 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

 • HASKE


 • CHAPTER 17

 • Leggings ta saka 3 quater sai vest, taflya takeyi bankam bankam a warwatse kamar budurwar kauye. Tana tafe tana tunanin zuci, wata sa’in ma yana fita waje ‘Yau saina ci kutumar ubanki, shegiya mara zuciya’ Su kuma su Laila yau bata karaya ba, ta dauki alwashin saita fada mai ya kai ta. Bazata yi koran baki ba ta tafi. Ajira ya huce shi ke kawo rabon wani. Idan tayi wasa har Haske zata dauki juna biyu ta kuma hada alaka da Bilal. Kuma a haka zata rinka bambamran shi ta wajen kudin abincin yaro. Gwara ta tafi tsigau tsiyau kazar mayu. Dole a gaggauta fidda ita yanzu ko ana ha maza ha mata, balle taga Bilal ya soma saukin kai baida niyyar cin uwarta saima tarairaya. Ganin Banan a gefe ya bata hope na cinma burinta.
 • “Ke kam bana hanaki zuwa nan gidan ba?” Ammi tace tareda nuna mata yatsa.
 • Ammi wallahi ba haka bane! Alheri nazo maki dashi” Laila ta chapke. Dafa kai Ammi tayi sabida ciwon kan da ta saka mata.
 • “ku wani irin jakai ne? Duk kawayen Shamsiyya basa bibiyata sai ku? Wai uban me kuke nema wajena? Wannan wani irin rayuwa ne? Naji labarin har ankon biki shiya siyan maku! Toh sai me? Kanku farau?” “Dama nazo ne akan yadda za’a fidda ….. ” shiru tayi saboda marin da Fijrta wanka mata. “Bana ce karna dawo na same kuba? Amma dayake gidan ubanku ne kuka tsaya? Yau koni ko ku? Tunda kun zama jakai bakwa jin magana, yanzu zan aika majiki manzansa mai isar mashi da sako, saina maku dukan tashi ku sha gishiri, yau sai kunji na mai dan wake“ saita wanka ma Banan mari ita ma.
 • “Mallam Adamu karka kuskura ka bude gate yau” ta Kalle bakin gate tayi mashi magana, kuma yasan halinta batada kunya yasa ma baya shiga sabganta. Ita kuma Banan ta raina Fijr tana tunanin zasuyi mata taron dangi.
 • Zuwa tayi ta dake Fijr, ‘Dan ubanki ni zaki mara’ Laila data san halin Fijrtana gefe tana raba ido. Ko mari dari zatayi mata bazata rama ba kafin ta zuciya ta kusan kashe ta. Ba yau Fijrta taba dukanta ba, lokacin suna primary tayi ma Haske rashin kunya sai Laila ta zuciya ta mare Fijr, sauran dai sai labari. Dariya Fijr tayi dataga karfin halin Banan, finciko ta tayi ta gashin ta, sai ta sakata a hammata ta dukunkune. Anan tayita kilar ta, tun Banan na kokarin ramawa har ta soma roko
 • “Anty dan Allah kiyi hak‘uri wallahi zamu tafi” “A’a ban gama isar da sakon ba tunda har kina magana” “Wallahi Laila tace muzo banso zuwa ba” “Ai baki daku ba Hajiata tunda har kina magana” Kuka Banan keyi amma Kota saurare ta, tasha matsa gashi sai dimarta akeyi. Ita kuma Laila rugawa tayi wajen mai gadi tana zazzage mashi jakartal Kudi take hadawa domin ta bashi saiya barta ta fita. Da ido Ammi tayi ma Fijr nuni Laila ta gudu. Anan ta saki Banan wanda take kuka wiwi, mascara da eyeshadow duk ya chabe haka yayi ma fuskan dama dama. Gashi high-heels data saka kafa daya ya karye, saboda take kafar Fijr tayi domin ta samu balance sosai. Daga baya Laila taji an shaketa ana fincikarta, saida suka koma tsakar gida saita wurga ta kasa, zama tayi daram kanta tayita duka. Daga mari har naushi babu wanda bata aika mata.
 • “Bana hanaki zuwa gidan nan ba? Ko bakida labari Haske tayi aure ne? ” Wallahi da kin tsaya kin saurare ni zaki san da alheri nazo maki, akan auren tane?
 • “To ni ina ruwana da auren? shi nakeso nayi nima na tafi, baki dandara ba tunda har kina min magana kenan”
 • Takalman Laila ta flzgo ta cigaba da dukan ta dashi saboda hannunta ya soma zafl. Kuka Laila takeyi sosai duk an soma fasa mata jiki gashi marin farko ya fasa mata baki. Jini duk ya bata mata jiki, numfashi kasa kasa ta soma yi saboda ta wahala. Salati ta koma yi saboda ta gwammace ta mutu data cigaba da zama cikin halin nan, balle ta hange mutuwa yanzu. Gwara tayi mutuwar shahada kila ta shiga aljanna. Anan Fijr ta kyale ta. “Tashi ku Fita ko ayi part 2” da sauri suna rige rige suka fita, shades din Banan mai kyau da tsada Versace ne sai Fijr ta dauka. Babu dama Banan tace a bata abin ta. Fijr na dariya tayi magana. “Sai ni Katarina baban iska( Hurricane Katrina), na dau mutum na dau kayansa” “Shegu” Ammi tace yayin da suka koma daki
 • Fafur Banan ta hana Laila shiga motar ta, a cewarta Laila plan tayi da matar Bilal domin aci ubanta. Babu rantsuwar da batayi mata amma taki ji. Shiga abin ta tayi ta tsere a sittin. Babu sarki sai Allah Laila tayi titi a guje kafin Fijr ta fito ta sameta, zafi taji a kafanta ashe kwalba ta taka. Takalmin ta yana gidansu Ammi ta mance dashi wajen tsoro. Zubewa tayi a kasa tareda rike kafar. Kuka ta barke dashi saboda ya shiga waje mai bala’in zurfi. 
 • Jini ya rinka futa kamar ana layya. Da kyar ta samu ta fizge waje wanda saida ta dauke wuta na wajen dakikai 10, hawaye masu dumi ke malalo mata a fuska, duk ta susuce ba kamar yadda ta fita ba. 
 • Zugi kafar ke mata sai rawar dari takeyi, ta soma fita hayacinta amma babu wanda ya tsaya taimaka mata kowa yazo a mota wucewa yakeyi. Masu tafiya a kafa yara ne suma sunaji da kansu. 
 • Daga baya wani mai napep yazo, shine yace zai kaita gida amma dubu daya. Haka ta yarda babu yadda zatayi suka tafl. 
 • Kafin su isa gida saboda nisa ta flta hayacinta, dayake kwatancen datayi mashi baida wuya daidai kofar gidansu ya ajiye ta. Da sauri ya shiga ciki domin azo a taimaka mashi. Sameera ce tana ma mutane lalle a tsakar gida, “Salamu alaikum kuzo ku tayani ina ganin ta suma” 
 • “Wa kenan!” “Ina ganin nan take? Kwalba ya soke ta” 
 • Ba Sameera ba har wasu masu lalle suka fita domin ganin kwaf. Laila ce cikin napep bata san an kawo gida ba. Hayaniya taji saita soma raba ido amma yayi mata nauyi ga azabtacen ciwon kai. 
 • Chemist dake gefen gidansu watau shagon matan da sukayi zage zage da Saif kwanaki aka wuce da ita. Matar nurse ce kuma sun same ta, babu maganin anesthesia haka aka soma dinkewa. Yayi tsami sosai kafan kuma tasha kuka, Sameera saida tayi kwalla sosai. Shima mai Napep yaji tausayin ta. Daga nan aka bata wasu magunguna suka tafl. Anyi total din komai an bada receipt, Saif idan ya dawo zai kai kudin. Sameera ta shiga ta ita har uwardaka ta kwantar da ita. Sannan ta bama mai napep kudinsa daga kudin Laila a jaka. Mamaki take yadda bakin Laila ta fashe, ga kayanta sun somawa barkewa. Wani irin kwalba ne mai ma mutum kaca kaca. Ko mai chemist saida tayi maganar ciwon. Bata amsa ba saidai wuri wuri da idanu‘ Sameera ranta na bata kila dambe tayi amma ba tace komai ba. 
 • ‘Dakinta ta wuce ta zuba mata abinci, shinkafa da wake ne da catfish. Sai kuma kunun aya mai uban sanyi. Laila salati kawai takeyi saboda abin yana mata kamar mutuwa yazo. Gashi ta kira Saif yanajin maganar kudi yace bai aike ta ba kuma bazai biya ba. Daga nan ya watsa ashar ya kashe wayan shi. Abin duniya duk yayi mata cinkoso Sannu amarya, tashi kici abinci” Abinci ya fitan mata akai, da ace ta samu biyan bukata ne yauwa‘ Amma taci wahalar banza kuma Haske tana zaune daram dakin mijinta. Tallabo ta Sameera tayi domin ta zauna da kyau. 
 • Anan ta taimaka mata domin taci, tanayi tana bata ruwa har ta kusan cinyewa. Suna haka ne wayanta ya soma ruri, sunar Haske ta gani baro baro wanda bakin ciki ya turnuke ta. Saida ta runtse idon domin haushi kaf‘ln ta daidaita kanta ta dauka. 
 • “Tawan ya kike” tace cikin takaici “Lafiya lau dama wani workshop ne na skills acquisition inda akwai catering, make-up, dinki da kuma events decoration, idan ka fito best kuma za’a baka hannun jari shine nace da zaman banza gwara kiyi” Tura min link din zan duba anjima ni bani jin dadi yanzu” “Subhanallah! Meke damunki ?” Wal da ido Laila tayi saboda ta lura Haske na jawo mata Bad luck duk sanda ta nufe ta da abu yana dawo mata. Na fadi akan mashin ne, kuma saina taka kwalba” tace a dakilce. Sameera ikon Allah take kallo, kana ganin Laila kasan dambe tayi amma tayi shiru. Innalillahi! Are you alright? Kinje asibiti? Meyasa baki fada min ba? 
 •  Eh naje kuma yanzu haka cin abinci nake Bari Bilal ya dawo muzo mu gaida ki, please don’t stress yourself ki kwanta har sai nazo” “Karki damu wallahi, ga Maman su Mubina” Nidai sai nazo. What are friends for? I love you Laila kuma bazan samu kwanciyar hankali ba saina ga halin da kike ciki. Idan wani abu ya faru dake bazan taba samun natsuwa ba har ga Allah” saita fashe da kuka ta wayan. Wulla ido Laila tayi tana magana cikin ranta, ‘Munafuka salan ace kinyi abin arziki, yanzu zaki zo min gida da mijin ki yana tarairayan ki kuna min salo… Shegu kawai….Wallahi saina fidda ki yadda nake cin ubana kema sai kinci …… Yar iska mai siffan mayu’ ‘ 
 • “Okay Tawan sai kinzo ina jiranki” 
 • Banan daki ta koma straight ta hau ka gado, kuka ta rinka rerowa na abinda ya faru. Tunda take ba’a taba mata irin dukan nan ba, kamar yadda Fijrta dauki alwashin saita masu dukan tashi ki sha gishiri shine tayi masu. Jikinta yayi bala’in tsami kamar an watsa mata barkono sai zugi yake mata. Sai kuma ta tausaya ma Laila dan. Tafl jibguwa ainun. Yanzu yadda aka koresu daga nan ta ina zata samu Bilal. Anya tazo Naija da kafar dama kuwa? 
 • Saida ta huta kadan ta wuce bayi ta sakar ma kanta ruwan zafi kamar ana fige kaza. 
 • lta kuma Ammi zata gidan kawarta Hajia Zainab, hankali kwance ta shirya ta fita abin ta. Data isa wajen ne sai Hajia Zainab tace zasu anguwa wajen matar commissioner  
 • Taji dadi sosai koba komai zatayi maula. Katafaren gida ne mai yawan furanni a gaban gate din. Sannan cikin ma abin kallo ne. Ta ayyana a ranta yadda zata kulla aminta da matar saboda ya kamata ta shiga cikin manyan matan Kaduna ana damawa da ita. Sun zauna a falo ana motsa baki da kayan ciye ciye na zaki da kaji. Matar ta fito inda suka rungumejuna da Hajia Zainab. Ashe sunyi sakandire tare na Queen Amina dake Kaduna. Head girl ashe da gaske zaki zo?” Hajia Aisha tace. 
 • “Wallahi kuwa zanzo zumunci, ga kawata Hadiza” Kallon juna sukayi da Aisha da Hadiza akayi murmushi, “Ina wuni mun same ku lafiya?” Ammi tace. Lafiya lau, ya gida?” Alhamdulillahi” 
 • Head girl wallahi naji dadin ganin ki!” 
 • Suna cikin haka ne sai Banan ta fito zata garden domin ta sha iska tunda ta kasa barci. Sandarewa tayi dataga Ammi a falon. Mika hannu tayi tana nuna Ammi tana hawaye. Mommy me kike yi da wannan matar? Itace sanadiyar shiga halin danake ciki” Ban gane ba, wani mata kenan?” ita kuma Ammi cikin ta ya duri ruwa. Tabbas yau kwanan cell ya kamata. 
 • “Wannan matar mana mai blue veil, kinsan cewa kuwa yarinyarta ke auren Bilal. Bilal dina tun muna University of Abuja kaf‘ln na bari na koma UK” 
 • “Ke banda abin ki matar mutum ai kabarin sa. Ba Bilal dinki ba koda saka maku rana akayi idan ba mijin ki bane bazaki aure shi ba.” “Amma mommy….” 
 • “Please tafi idan na gama dasu zanzo muyi magana” Garden ta nufa kamar yadda tayi niyya. Ranta ya sake baci wai mum dinta na aminta da makiyan ta. 
 • Ammi ta soma nazari kodai sunzo neman taimako ne akan yadda ya za’a tarwatsa auren. Domin Laila ta soma magana yadda za‘a fidda wata amma bata karasa ba dambe ya kaure. Daukar wayanta tayi kamar zatayi waya saita fita waje neman service. Anan ta soma raba idanu, sai chan ta hange Banan ta saka kafa daya akan daya tana jijiga. Sannu a hankali ta isa wajen. Mugayen kallo Banan ke binta dashi ita kuma murmushi tayi mata. “Mayar da wukan bakin ki, da alheri nazo” 
 • Zama Ammi tayi a kujera tana murmushi na mugunta, “Kince kina san Bilal koh?” 
 • “Is it not obvious?” “How can I help?” 
 • “For real??? Like da gaske kike zaki saman min yadda zan mallake shi?” “Yarinya ni ba sa’arki bace, idan nace zan taimaka maki da gaske nake” 
 • “But then why, meyasa zaki taimaka min na samu mijin yarki?” shiru Ammi tayi tana nazarin Banan. Sai tayi magana. 
 • “Can i trust you? Ina fada maki sirri karki tona?” “Eh bazan fada ba wallahi” 
 • “Shamsiyya ba yarinya na bace, yar sister dina ne data rasu. Banda dangi babu wanda ya sani” Ware ido Banan tayi, bawai na jindadi ba kawai na mamaki. Wai ace yarinyar sister dinka data rasu itace abokiyar hamaiyan ka. “Okay na gane yanzu, please ki taimaka min na samu Bilal, xan baki kudi masu uban yawa” “Kudin ki baya wani damuna kamar naga Shamsiyya ta watse a duniya” Alright bari na kira Laila na sheda mata” “Laila kuma? Inace kawar Shamsiyya ne?” Anan Banan ta bushe da dariya tareda Iabarta komai, mamaki Ammi tayi sosai sabida kamar kawar arziki. “Wow! Ashe yan team dinmu nada bala’in yawa? Karku damu zan share mana hawaye. Shamsiyya zata kwashe kashinta a hannun ta” Saida Banan ta mike tsaye tayi dab saboda murna. Anan sukayi exchange din number. Kuma Ammi ta bata hakurin akan Fijr. Tace ta rinka zuwa gidanta koda yaushe amma kawaii taji tane tana bala’in tsoron Fijr kuma zata nisance ta. Daki Ammi ta koma inda su Aisha da Zainab anata hira, “Har kin gama wayan?” Zainab tace Eh Babansu Fijrne” 
 • Basu bar gidan ba saida Aisha tayi masu sha tara da arziki. Babu wanda ya kai Ammi murna saboda ta kashe tsuntsu biyu da dutse daya. 
 • Da yamma Bilal yakai Haske gidan su Laila, ba’a san ran shi ba saida ta nuna taji haushi sosai aka tafl. A hanya an siya fruits kala kala, grapes, Apple, pineapple, Banana, Watermelon da sauran su. Kuma sun biya Yahooza da Habib Yogurt. 
 • A lokacin Laila tana barci suka isa, Ledeju hudu suka shiga dashi cikin gidan. Kuka Haske tayi yadda taga bandeji a kafan Laila ga kuma plaster a bakin ta da wajen hannayen ta inda ta jibgu. Rugumanta tayi tana mata sannu tareda tambaya ko akwai abinda takeso. Sai tace dama Saif bai dawo ba kuma ga receipt na magani. Dama Bilal baisan zaman dakin da sauri ya fita domin ya biya Kuma bai sake komawa ba. 
 • Dakin Laila kaca kaca kamar na bola, Haske ta tattara komal‘ ta tayata gyarawa. Sannan ta shiga kitchen tayi mata wanke wanke. Kusan awa daya sai Bilal yace ta fita su tafi. Taso tayata da girki amma Bilal yace Kota zaba shi k0 Laila. Anan ta hakura saita soma saka gyalenta. Wayan Laila yayi kara inda Haske ta mika mata. 
 • “Besty na” taga an rubuta bata damu ba at all. “Please kije waje gani nan zuwa bari na dauki wayar nan?” Laila tace a wulakance 
 • “Ai ba damuwa dama taflya zanyi, Allah ya kara lafia?” saita f‘ice 
 • “Hello Besty, dan Allah kiyi hakuri wallahi bansan za’ayi haka ba!” “Karki damu, albishirin ki ?” Goro! Kuma fari tas” 
 • Dariya sukayi su biyu sai Banan ta bata labarin yadda Ammi tazo gidan su gashi sun dinke. Shewa Laila ta rinka yi tana murna. Ta bala’injin dadin zancen harda karbar number din Ammi wajen Banan. 
 • Dole ta rinka azalzala ma Ammi akan daukan mataki na gaggawa yadda za’a fidda Haske daga gidan tunda bana ubanta bane. Wannan kenan! 


 • Hmm 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]