[Advertisements⬇️]

HASKE CHAPTER 16 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HASKE

CHAPTER 16
Abba ya yanke shawara akan Haisam zai koma US da zama. Zaiyi transfer na internship dinsa daga nan ya cigaba da karatu a chan. Kowa yayi na’am da maganar musamman Mommy. Koba komai zai nisanta da Shamsiyya kuma zaifi ma kowa kwanciyar hankali. Daga nan tana kyautata zaton zai samu wanda zata maye mashi gurbin Haske. In sha Allah wannan zai zame mashi mafi alheri, kuma tana sakejaddada mashi amfanin rungumar kaddara da mai kyau da mara kyau shine cikon imani. Komai yana taflya yadda ya dace ma Bilal da Haske, tsallan soyayya da kula suke nuna ma junan su. Kowa yana kokarin faranta ma dan uwansa. Idan kagansu dole su burge ka gwanin ban sha’awa. Umman sa take kai masu breakfast, lunch and dinner. Abinci mai yawa harna bakin su idan sun samu. Kuma taje bayan kwana hudu da yarsa Anty Jalila. Ta tabbata Haske bata rasa komai ba. Itama Mommy taje sau biyu, ta kai mata kayan amfani da Kuma cefane. Balle anyi mata gara tabarkallah masu yawan gaske. Ko yawan dublan da alkaki abin kallo ne. Fijrtasaka Baraka a gaba domin ta rakata gidan. Tunda taji labarin maman Haske ta rasu sai tausayinta ya kamata saboda sunata daukar alhakin ta babu gaira babu dalili. Ko Haske saida ta tsargu data ganta, tunda basa ga maciji. Amma gashi ta kai kanta cikin gidanta kuma tayita binta da ido. lta kuma kallon yanayin ta takeyi. Ya bambanta da nasu.
Baraka ce ma suke yanayi kuma idan aka ce yarinyar Hafsat ne bazata musa ba. Ta shiga ranta kadan babu laifi kuma ta ayyana a ranta zata rinka zuwa duba ta akai akai. Haske tayi masu hidima sosai da zasu tafi, daga cikin lefenta ta dauko masu atamfa turmi biyu, sai packet din lipgloss da gazar su raba.
Ammi kam taki zuwa, duk yadda Daddy yayi mata magana akai tace bazata ba. Haka ya barta da halinta. Mutuwa ne tayi masa haka, idan Hafsa nada rai bazai san wata Hadiza ba balle tayita cin mashi fuska.
Su Baaba da kannen Laila duk sunje gidan saboda ranar bikin tare aka kaisu. Baaba ta bata samiru masu seti hudu guda uku. Ruwan kwai garesu da fulawa ja. Haske taji dadin su sosai Sabida tasan Baaba ba karamin daurewa tayi ba kafin ta samu kudin su. A saman cabinet dinta na kitchen tajera wanda ya kara mashi armashi. Laila dai Saif bai barta taje ba, haka kurum dan ganin damansa ya hanata. Kuma yace idan ta fita sai dai Bilal ya aureta amma ta dawo na lahira saiya flta jindadi.
Mamakin lafuzan sa takeyi kamar wanda sukayi auren kiyayya bana so ba. Tana tuna sanda suke kaiwa dayan dare suna zance tareda kwashe ma Sameera albarka.
Amma yanzu ya daina sakin mata fuskan da zaka kai masa gulma, ko yan lalle sukayi wani abu zatayi gulma haka yake dakatar da ita. Ya canza mata sosai kamar ba Destiny dinda ta aura ba, ranar da Saifya yardar mata domin taje gidan Haske tayi murna sosai. Daukar wani zungureriyan jaka tayi, ita abinda ta sani ko Haske bata hadata da kaya ko ba saita faki idonta ta diba.Bakin ciki ya kama Bilal dayaji labarin Laila zata gidan. Bai wani santa sabida yasan asalin halin ta. Kwata kwata bata san cigaban Haske a rayuwarta. Mamaki yake yadda Haske bata dago ba. Suna dakinsa tana ninke mashi kaya shi kuma yana kwance kan gado suna hira. Siyasa yakeso yayi ma Haske akan karta yarda Laila taje.
“Babyna, bakya tunanin bai kamata tazo tun yanzu ba. Tunda badai tashi zamuyi ba”
“Ai bazaka gane wutan cikin Laila ba, bayan ta saka na tura mata kati na data. Saida nayi video call da ita, ina bin kowane waje domin ta gani””Toh tunda ta gani menene sai ta zo ta takura mana” “Gani ya koreji, besides nima nayi missing dinta, Laila tayi a rayuwa, ba kasafai ake samun irin su ba”
“Allahu” Waigawa tayi ta Kalle Bad, latiya ya canza tone dinsa kamar baisan Laila.
“Baby akwai matsala ne?” “uhmm uhmm” 
“Gwara ka fada min” “Kawai ban santa ne” 
“Tun yaushe kuma?” ta fada tareda mamaki “Karki damu a bar maganar” 
‘Daga kafadanta tayi alamar to, shi kuma Bilal saiya gyara kwanciyar sa tareda rufe ido. Tsoron sa daya karta koya ma Haske mugun hali, balle ta rigata aure lace haka akeyi. Laila ta fesa kwalliya abinta, ranar Saif bai ma da wuri ba. Yanata kwance kan gado yana binta da ido. Shi duk yana haka ne saboda idan lokacin tafiya yayi yace zai rage mama hanya. Daga nan saiya shiga shima ya kashe kwarkwatan ido tareda cin abinci. “Bari na kishingida idan kin shirya sai kiyi min magana na kai ki, kinsan za kifl samun class sosai” ya fada tareda basarwa. “Nagode Destiny kamar ka sani kuwa” tace murna fal ranta. “Karfa ki manta ki tafi baki tashe niba” ya sakejaddada mata. Wajen sha biyu na rana ta gama shiri, Destiny yana barci yana farkawa tsoro fal ransa karta tafl ta barshi. Ta shiga bayi sai bai ji motsin ta ba. Da gudu ya flta tsakar gida da gajeren wando yana raba idanu tareda cizan yatsa, harya soma tunanin irin dukan da zai mata idan ta dawo. Dankam saita yaba ma aya zaki. Sai gata ta flto waje zata dauki mop, sosa keya yayi kamar mara gaskiya saiya koma daki. Ya shiga kenan sai Sameera tayi sallama. “Assalamu alaikum” saita shiga ciki “Amin wa’alaikumus Salam” Laila tace “Ya akayi ne” Saif yace. Kallon Laila tayi alamar ta basu guri saboda ta tsaya masu sekeke amma ko gizau. Saita Kalle Saiftayi mashi ido yayi ma Laila magana. Shima turnuke fuska yayi tamau bai ce komai ba. Data lura baisan sirri saita soma magana. “Dama kumn makarantar su Abul Khairdana cika maka zaka bani, hidima ya taso min shine zanyi amfani dasu” “Yojimin wulakanci, wai muyi abu a sirri ki 20 bainar duniya kice zaki tona” yace a harzuke 
“Hmmm” tace tareda wulla idonta. “Banda abinki ina zan samu dubu biyaryanzu, kinsan yau ban fita ba!“ “Ammajiya kayi ciniki ai, kuma duba goma sha biyu ne, akwai kudin uniform dana takardu” “Yo tinda ke kika bude min kamfanin dole ki rinka bibiyan movement dina” “Kayi hakuri kudin kawai zaka miko” “Toh nace banda shi, ko kotun babban duniya za’a baza’a kwata komai gareni ba” “Kema kiji tsoron Allah Sameera, ya zaki dinka masu uniform mai uban tsada ana buhariya. Wai ace dan rashin hankali da kan gado irin naki kin dinka riga da wando da hijab. Bayan rigar kullum ana boye wa. Maimakon ki dinka dogon hijab kawai sai tayi managing sauran” “Toh Abul Khair fah? Shima Hijab kake so nayi mashi? Koko dogon hula zan dinka” tace cikin izgili “Nidai kawai ka bani kudina” “Rashin kunya zaki min dan Allah ya hore maki arziki? Sameera kibi Allah kibi ni. Karki bari akan abin duniya ki Shiga wuta. Wai ace meta bakuda tausayi sai shegen san kai, yasa kuka fl yawa a Jahannama” yace yana nuna maka yatsa 
“Ina zancen rashin kunya anan, daga nazo karbar kudina zaka zare min ido” tace hawaye fal idonta. Kallon Laila yayi, “Ke kuma ubanme kike kallo? Muna magana kinzo kina bin bakin mu da ido, Sa’idawa masu sujjada da kumatu” da sauri ta koma daki ta barsu. Rage murya yayi, “Kingane koh, akwai wani kudi danakejira ne. Ki bari anjima zan dawo na kawo maki” girgiza kai ‘ayi akan bata yarda ba. Saiya sake gyara zama yana murmushi, “Haba uwargida na, wallahi zan baki mana” “Okay kije yanzu zamu fita zan shigo na kawo maki” “Kokai fah yanzu Naji bayani” tace tareda tura baki saita tashi tsaye. “Hohoho kinfi kuturu naci, da aci bashin ki gwara a kashe sarki. Yafl ma mutum sauki wallahi” yace yana dariya. Yanzu yana tunanin yadda zai faki idon Laila ne ya diba. “Ke Laila kin gama mu tm koh?” “Eh gani bari na dauki mayafl“ Sun mo tana takama zata fita da miji a gaban mota, gata da shegen kaudi sai girgiza takeyi yan lalle sun sorna taruwa. Sameera ko gezau kawai ya bata kudinta. Taga rainin wayon yayi yawa. Tana nan tana cika mashin cefane su kuma suna cin dacfl. Saida Laila tayi yanda ta nuna sunci kaza. Maimakon ta saka kashin a bola sai wasu a gefe yadda zaka gani. 
Yasa ta dauki alwashin ko shi k0 ita dole ya bata kudinta, sun dumfare motar sai ya bama Laila key wai ta bude yayi mantuwa. Abin yayi mata armashi sosai. Girar sama dana kasa a hade tayi tareda kamewa a gaba, saita kunna waka ta soma bi a hankali. Shikuma kasan kafet yaje ya dauki 13k, anan ya ware dubu goma wanda zai bama Sameera. Dole ta yafe mashi sauran. Haka yaje gefen datake zaune ya bata kamar nashi. Mamaki take ainun yadda yace baida shi. “Toh ni zan kai iyalina anguwa sai mun dawo” yace tareda shan mur. Ko kudin cefane bai bada ba kuma bata isa ta tambaya ba. “Okay a dawo laflya” “Baba ka siyan min Bobo a hanya” Mubina tace “Allah yasa shagon su bude sanda zan wuce, balle kin f’Iye shan zaki. Bakya tsoron Basir tun kina karama” 
Sameera ta girgiza kai tana jimami, sai kuma ta gode ma Allah daba Saif bane babanta saboda tsufansa za’ayi kallo. Shiga motar yayi saiya Kalle Laila yana murmushi, itama shi ta mayar masa sai suka tafi. 
… 
Koda suka isa gidan azahar yayi, babu yadda Laila batayi ba akan ya wuce masallaci kafm ya shiga yaki. Yana tsoron karta zalunce shi idan an kai masu kayan motsa baki. Kaddara ta riga fata a kofa Haske ta taresu sannan tace ya wuce masallaci yayi sallah tukun kafln ya shiga. 
Haka ya tafi rai bai soba. Laila kamjikinta sake sanyi yakeyi. ‘Dakin yafl kyau a ido flye da hoto. Balle data zauna akan kujera, laushin su ya isa ya kawar maka da wani tunani daya dameka at that instance. 
Dariyaryake takeyi wanda yafl kuka ban haushi. Ji take kamarta rufe Haske da duka domin tsabaragen bakin ciki. Haka Haske ta wuce kitchen domin ta kawo mata ruwa. Drinks kala kala ta zuba akan tray mai kyan gaske. Daga na kwali, roba saina gwangwani. Ga kuma ranar Umma ta aiko harda samosa da spring rolls, haka ta zuba mai yawa ta bata. “Ai wannan ya mana yawa, idan mun sha sai mu tafi da sauran” 
“Babu damuwa zanma kara maki wallahi” saida ta shanye fin rabin Chi exotic kaf‘ln tace a bata darduma tayi sallah. lta Haske dama ta idar kenan. Bad kuma bai dawo ba. Haske tayi mata peppered chicken wanda shine farkon girkinta tun auren sai dafa ruwa da microwaving abinci. 
Tana cikin yagan nama sai ga Saif da Bilal sun shiga, ‘Kinyi asara Laila shegen kwadayi sai kace kina ciwon yunwa’ yace cikin ransa tareda watsa mata harara sai yayi kwafa. Ta bala’in bashi haushi. Ko minti ashirin batayi ba harta nuna halin ta. Shima kamewa yayi akan one seater suka gaisa da Haske sosai. Na zuba maka abinci ne kokuma tafiya zakayi?” Haske tace 
“A’a karki damu yanzu zai taW’ Laila ta chapke. Harara ya watsa mata amma bai ce komai bal Bai so yayi magana a gane halinsa. “K0 kadan ne bari na saka mashi” murna yayi tareda shi mata albarka cikin rashin. Bilal bai Kalle suba illa canja Channel abinsa. “Gashi idan yayi yawa sai a bama almajirai sauran” fried rice ta saka mashi da coslowda kaza mai uban yawa, ga kuma su somasa a karamin kwano. Gashi harda baked beans wanda yana bala’in san abin sosai. Bilal ya tashi ya koma daki wai zai kwanta saboda gabadaya baya san su. Su kuma su Haske suka je bedroom dinta domin Saifya sake sosai. Abincin mutane kusan biyu ta saka mashi ya cinye tas, sannan yasha maltina gwangwani daya da kuma flve alive. ltama Laila tana daki tana cin abinci sai zuba takeyi. Komai fes fes cikin durowa babu damar sata, gashi taga yadda Bilal ke shan mata kamshi amma kallon so yake bin Haske dashi. Duk inda tabi yana binta da ido duk tunanin sa kanta ya dulmiya. Zallan so ke damunsa, sai taji haushin kanta da batayi nazari sosai ba kafin bata shawara. Kawai yanzu zatayi regrouping ne ta nema hanyar rugurguza komai a mutu harda sarki. Saif bai damu ba shi kadai cikin falo, daukan remote yayi yana canza channel yana shan lemu. Wani ya shigo yaga yadda ya kame zaiyi zaton falonsa ne. Gashi DSTV Explorer suke dashi kuma sun biya full package babu tashar da babu. 
Haka yayita surfing hankali kwance kusan awa daya, sai gasu Laila da Haske sun fito. Ita tama mance dashi duk zaton ta zai tw ne. “Destiny ka tat”: anjima saika dawo ka dauke ni” “Karki damu nanda minti talatin zamu taW’ yace yana dariya. Bazai barta a gidan ba taci dadi babu shi gwara su tafi. Tunani yake tun randa zata gidan tare zasu rinka zuwa. “Lahhh harzaku tafi, toh bari na baku kayan biki” Haske tace saita shiga kitchen da sauri. Laila shiru tayi kafin ya watsa mata ashar. Haka Haske ta dauko souvenirs data ajiye mata a store, sai kuma ta cika mata yellow and black Leda dasu dublan. Har zasu bar kitchen sai Laila tayi magana. “Kin mance baki dauko drinks dinba” “Gwara da kika tuna min dan na mance” Katan daya na Fanta ta bata, idanun Saifyayi dara dara daya gani. Haushi yaji dama ita ya aura ba Laila ba saboda tat”: alheri. Sai kuma ya tuna bata san shi ta wannan fannin. Sauran kajin haka Laila ta samu foil paper ta zuba duka, taso ta dauki jakar Haske daya na Chloé. Tana tabawa kafln tayi magana Haske ta soma murmushi tareda sheda mata tana bala’in sanjakar. Relaxer kit ta bata da shampoo da conditioner mai uban tsada. Abin yayi mata dadi sosai. Sannan dan gashin kanta ta tsiyaya humra kala uku da daukan turaren wuta roba guda. Kamaryadda ta dauki alwashin cika jaka haka tayi kamarya tsinke dan nauyi. Taso haduwa da Bilal ko zai bata kudi amma Haske tana tura kofa ya rufe ido, dataji yana barci taso a tada shi amma bata ga fuskan fadin haka ba. Saif ya Mo yana rikeda roban smoove wanda ya bude yanzu, yana tafe yana shan abinsa. Haske taji dadin zuwan su inda tace itama zata ziyarce su idan ta fara flta. ¢ 
Ganin relaxer din yasa Laila tace gwara ya sauketa a salon na wajen 9-11 domin tayi gyaran gashi. Da kyarya bata dari biyar. Dama tanada dari biyardlnta. Kuma ta Zara dubu daya a wallet din Haske dukda a gaban tane. ldan wannan ne Hasken ta saba, sau da dama Laila zata bude ta kwashe kudin ciki, idan tayi magana sai tace zata biya shikenan yabi ruwa. Ta sauka daga mota tana cika da batsewa, taku daidai kamar dawisu. Yanga takeyi wanda yafi na Muhammadiya. Shima Saifdaga mota yana zaune saida ta burge shi. Saidai ba jiranta zaiyi ba. Waken aikinsa zai nufa yaga meke faruwa. Daga nan zai wuce gida da kayan ya soma ci kafin ta dawo.Banan ne ta shiga saloon din, mamanta tace taje ta canza kalar gashinta. Bata hanata kara gashi ba amma tayi mai natsuwa kamar baki. Asalin yar gayu ce ta saka Jens wando wanda aka yanyanka, sai kuma riga chiffon top mai furanni. Sannan takalmin hightop ke kafarta da gyale dan fiCiCi. Tauna take yi ‘kas kas kas kararas’ ko ajin kin ta. Ta tafi da imanin Laila inda ta shagala tana kallon ta. A hankali ta cire tabaran idonta.Magana takeyi kamar bataso, balle tanada bala’in nawa ga ra’ayi sosai da kuma shagwaba. Nan ta hakince ta daura kafa daya akan daya ta rinka danna waya. 
An soma kwance mata kai ita kuma Laila za’a wanke mata relaxer, su uku ne customers ciki kowa na harkan gabansa banda Laila. Wayan Banan ya soma ruri saita dauka tareda karawa a kunnen ta, da turanci take magana sai jefl jefl tayi hausa kadan, amma zakaga tsantsan tashin hankali akan fuskanta. Daga nan ta kashe wayan saita sake kiran wani. “Dija kimin rai na shiga uku” tace yayin da aka dauka. 
“Halan meya faru?” “Wai ance yayi aure last week! Can you imagine shine harda canza number dan wulakanci ko yau nayi trying wallahi” “Waya gaya maki” 
“Numberdin Hamza na samu sai nayi mashi text, shine yanzu ya kirani” “Toh kamshin gari, harya fada maki kenan. Kinsan halin Hamza be careful” “It’s not funny, Shawara zaki bani” “Me kike so nayi maki bayan yayi aure. Gwara ki tattara ki dawo nan” 
“Bafa inda zani, he is the love of my life. Baida wata mata a duniyar nan saini, Badman Bilal nawa ne ni kadai saboda bana sharing” “Allah koh!” “Dija please, support me karki min dariya, ni kawar ki ce you should be on my side” “Hello… Hello… ldan kinajina Banan network ya soma matsala. Zan shiga subway ne… Talk later” 
Saita kashe, tana gajiya da wahalar Banan, bazata kuma taba yarda ta ruguza ma yarinyar mutane rayuwa ba. Sarai tasan Banan gobe kuma zata iya cewa bataso. She‘s very confused.Jikin Laila ya soma rawa, Bilal ne ake maganar sa kuma yanzu tabar gidansa. ldan tanaso har dakin sa zata kaita. Gyara zama tayi sai ta soma murmushi, cikin salo tayi magana. “Hello ! Kamar na sanki a lnstagram” tace ma Banan. Basar da ita tayi kamar ba‘a ji ba. 
“BaiwarAllah kamar na sanki a Instagram” Banan nada bala’in takama da jiji dakai irin na Bilal. Ga ‘sabaragen wulakanci. Tasota sake sharewa sa’l ta lura Laila nada naci. A wulakance ta daga ido ta Kalle ta. “Bana Instagram” “Okay kila Facebook ne“ 
“Banayi””Allah sarki fah… Hi am Laila nice meeting you” “uhmm hmm” 
“Ai Bilal ya aure kawata… Badman ba” a lokacin ta samu hankalin Banan. “And why are you telling me? ” Kawai saboda…. Naga kina neman sa ne…. Kuma… Kuma na Iura kinada mutunci da bala’in kirki” tace 
Juya ido tayi, da farko bata yarda da Laila ba amma ina ruwan ta. “A ina yake aure?” 
Anan tace bazata gaya mata tukunan ba, su hadu gobe saita kaita gidan su Ammi domin su hada hannu yanda za’a fltarda Haske daga gidan har abada. Banan taji dadi sosai nan sukayi exchange din numbers. “Evil Witch” tayi ma Laila saving sai ita Kuma ta saka “Besty na” Saidai kuma mamakin Laila takeyi ainun, daga dukkan alamu sun shaku da matar Bilal amma take mata wannan abu. Ta rasa wannan hassada ne ko iya shege. Koda yake hassada shine ajin karshe da zaka shiga kafin ka zama maye. 
Kashegari sunyi da Banan zasu hadu bayan la’asar, sai tace bari tayi maza tayi aikin ta kafln lokacin. Walwala takeyi ranar sosai kamar an biya mata aikin hajji. Cikin nishadi tace zata bi Saif wajen aikinsa domin ta gani. Babu musu ya yardan mata. 
Sai ya futo da shargi za’ayi masa scolar. Dama yanada mai masa wanki a gida saiya kai guga wani wajen. 
Samun wuri sai Laila ta flta da nata, mai wanki ya dirga sai yaje dakin Sameera yayi ma Saif bayani akan kudin. Babu kunya ya aika mai wankin yace ta biya nata. 
Duk tana sha wasa ne, aikam tayi burus da zancen. 480 naira Saifya biya nashi aka bashi 20 ya saka a aljihu. Sanda suka flto mai wanki yanata aikinsa. Tana girgiza ta kalle Sameera “Zamu flta nida Destiny ne, zan raka shi aiki yau” “Babu damuwa Allah ya bada sa’a” 
“Uhmm hmm” Sai ta shiga gaban mota tana fancama, dayake ya tuna ranaryana dakin Sameera sai ya bada dari biyar ayi cefane. Sun isa wajen aikin sai fadanci ake ma Laila, taji dadin abin sosai harda ma wasu fada sun flye surutu maimakon aiki. 
Ana haka har azaharyayi, banda ruwa babu abinda take sha saboda kamfanin sane. Da Saif ya dawo daga masallaci saiya shigo da egg roll daya da Fanta daya. 
Duk zaton ta nata ne saboda daga waje yake kila yaci nashi a chan. Saidai aka sami akasin haka. 
Kujera ya zauna ya Kalle gabas, Kuma yadda gabas yake a wajen ya juya ma Laila baya. Murna yayi tareda magana ciki ciki ‘idan za’a ci abinci ance a Kalle gabas’ 
Haka ya cinye tas yayi gyatsa, ko tayi baiyi mata ba banda kiran yaro yazo ya mayar da kwalba saiya karbo mashi canjin sa na naira talatin, Mamaki ke fuskanta tayita kallon sa amma ko gezau. 
Gashi duk ta gaji da zaman bencijikin ta ya soma mata ciwo sosai. Sannan cikinta kamar anyi yasa babu komai a ciki. Kuma bata dauko wallet ba tunda batayi tsammani zai mata haka ba. 
Bayan awa daya ya flta ya dawo da gasarshen masara, ranta yana biyawa amma ya cinye guda uku. Ba’a yi minti talatin ba mai balangu yazo, irin masu sakawa a katon kwano suna talla. 
“Customer ina wuni?” “Laflya lau” 
“Ji dadin ka Alhaji, iya kudinka iya shagalin ka. Na nawa za’a kawo maka” “Saka min na dari shida” “Kai customer, laflya kodai ganin ido ne. Bafa ka cin na kasa da dubu daya… Ka kara kawai daga duniya sai Kaduna” Dariya Saif yayi yana sosa keya, “Ashe ka gane, wallahi kawai ra’ayi ne bawai ganin idon kowane shege ba” 
“Koda yake bani na dubu daya, gwara naci kudina tun ina raye kafin na matu na barshi” “Jar uba! Yo ba’a haifa uwar data haifa shegen da zai hanani cin kudina be a duniyar nan…. babu shi wallahi… Kutumelesi” ya ce cikin ba’a tareda Iankwasa baki kamar dan daba. ba Laila be her mai nama saida yaji babu dacfl. Sinna kai tayi kasa hawaye sirara suka soma sauka. Tayi nadamar binsa aiki, anan taga wautan ta sosai. ldan ba dole ba me zai kaita mu’amala dashi a waje. Kunun aya ya aka kai masa ma sanyi yana cin naman yana sha tareda rufe ido. lta kuma sai rawar dari takeyi yunwa yana addabanta. 
Cikin hakane sai Banan ta kira ta, anan tayi mashi magana zata gidansu Ammi domin Banan kawar Haske ne amma tana Kasar waje. Yanzu zataga asalin gidansu. 
“Kar kiyi dare” yace, ita kuma ta dauki alwashin bazata sake binsa ba koda zai roketa ne. Shikam gogan yasan daga yau ba zatayi marmarin binsa ba, wannan kenan! Babu kowa a gidan daga Fijr sai Ammi. Suna kallon The Doctors a MBC 4 inda Dr Steve ke maganar illar cire ciki. Sannan yana maganar cewa wasu yana zuwan masu da sauki wasu Kuma suna shan wuya. “Kinga kamar ni Ammi… I think… Wajen cikina na biyu da zan cire bai bani wahala kamar na farkon ba“ tace tana kokarin tuna yadda asalin abin ya faru kafin ta soma zuba. “Ke dan ubanki ni mamanki ne ba kawarki ba” tace tareda yin mata dakuwa. “Toh meye abin boye boye nida ke, cikin nan kinsan na saba dauka kuma na saba zubarwa… Dan kin samu zan baki labari” saita zuciya ta kwanta kamar ta fasa. Chan kuma sai ta sake zama. 
“Da cikin farko lokacin ban waye ba, da kuma na biyarshi saboda yawan cirewa sune nafl shan wahala” tace ko a jikinta. Ammi dafa kai tayi tana tunani. Tabbas kan Fijr yana motsawa sosai. Takaici tayi na haihuwarta. Banda annoba da tashin hankali bata kai mata komai. Suna cikin magana ne sai wayan Fijrya soma ruri, bata dauka ba harya tsinke. Haka a gabansu haraka kira sau biyar. “Ki dauka mana” “Naki” “Dan wulakanci ana so ayi magana dake kin share” “lsi ne kuma bazan dauka ba” “Ina ce neman sa kike ruwa a jallo” Kafln ta amsa sai suka ji sallama a bakin kofa, Fijr ne taje domin taga waye. Laila ne da Banan tsaye sunyi wiki wiki. Tsaki tayi saita soma masifa. “Amma dai kinji haushi, Allah yayi wadaran naka ya lalace, inace ance karki sake dawowa nan? yau sai nayi maki dukan kawo ceto shegiya mara zuciya. Bari naje na dawo na ganki anan, dan darajan annabi ki tsaya harna dawo“ ‘Daki ta koma domin ta canza kaya, na jikinta ya bala’in matse ta. Tana taflya tayi ma Ammi magana. “Kinyi baki Ammi, kawar yarinyar kishiyar ki ce ta sake dawowa, amma yau saina dake banza” “Waye kuma kishiya na?Alhaji yayi aure ban sani bane kome?” “kawar Shamsiyya fah, Hasken nan gidan yarinyar Hafsat twin sister dinki” Mamaki da tsoro ya kama Ammi, anan ta sake tsorata da Fijr. Babu haufi tana amfani da rafanai. Wannan kenan! 

Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]