[Advertisements⬇️]

HASKE CHAPTER 13 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HASKE


CHAPTER 13
Ajiyar zuciya Mommy ta sake yi wanda yafl a nada Gumi ke karyo mata duk da AC dake cikin dakin. Batasan me zata ce ba akan wannan lamari. Bata tsammani akwai Uwa wanda ta taba shiga irin tashin hankalin datake ciki yanzu. Duk hukuncin da zata dauka zai dadada ma daya kuma ya bakanta ma dayan. Sai dai kuma aure ba abin wasa ba. Bayan raya sunnan Manzo SAW ana gina shi akan soyayya da kuma mutunci. Daga Haisam har Shamsiyya babu wanda bazata iya mashi komai ba domin jin dadin rayuwa. Ita a yanzu bata ganin aibun aure tsakanin Haisam da Haske, mutuncida hakkinta yafi muhimmanci akan wani shekaru. Babu wanda zai tambayeta shekarar mutun sai dai a ce yanada hankali ko akasin haka. Nisa tayi saita soma magana, su kuma banda duka uku uku babu abinda gabansu keyi. “Nidai abinda zance shine dukkan ku ina kaunar ku fisabillahi, duk hukuncin da zan yanke akan dayan ku hak’uri zakuyi dani. Dan Adam ajizini ne kuma ina fatan wanda zan saba mawa cikin ku zai yafe min” ajiyarzuciya tayi domin ta huta, maganaryana mata nauyi a baki sosai. “Idan kun dauke ni a matsayin Uwa zakuyi abinda nace, tabbas mahaifa suna da ikon zaba ma dansu wanda zasu aura muddin bai saba ma addinin musulunci ba, yasa ni yanzu Binta inaso Shamsiyya ta aure wadda ya dace da ita” share gumi tayi, saita cigaba.
“Ina so ki aure Bilal sabida shine zabin ki, kin dade kina shan wuya a rayuwa ya kamata ki gina rayuwar aurenki bisa so da kauna. Bana so na takura maki sabida kamar naci amanar da aka bani ne. Nasa anyi min bincike kuma duka yan layinsu zance daya suke fadi. Mutumin arziki ne saboda baya fashin sallah a jam’i ” kallon Haisam tayi wanda fuskan sa yana kallon kasa. A hankali kakejin sautin kukan sa. “Kayi hak’uri Dan lele, ka mayarda komai ba komai ba. Allah ya musanya maka akan wanda yafl wannan zabin. Ka kaddarta akwai alheri a ciki” “Ba komai Mommy, nagode” yace saiya mike da sauri. Zura takalman sa yayi yabar gidan a sittin. Murna karara a fuskan Haske. Taji dadin wannan hukunci na Mommy. Duk zaton ta zata tursasa mata akan ta zauna da Haisam. Zatabi umurnin ta amma kam rayuwar ta zai cigaba da zama cikin kunci da tashin hankali. A sanyaye tace “Mommy nagode sosai, Allah ya saka da alheri“Amin Shamsiyya, Allah yasa shine abinda ya dace dake” “Amin” Tashi tayi ‘areda kwanan fruits wanda Mommy ta gama sha, kitchen ta kai saita dauki roban ruwa domin tasha. A yau ranta fes yake. Ta mance yaushe rabon data shiga cikin nishadi irin haka. Tunda take sai yau ta taba neman abu ta samu. Mommy ta kasance tana mata soyayya domin Allah babu san kai cikinsa. Taso ace itace asalin mahaifiyarta ba Ammi ba. Dan kam ta fln mata Ammi sau miliyan.
Bayan kwana daya dangin Bilal sukaje gaisuwan Haske. Fafur Ammi tace baza’a kai wannan sha‘ani gidanta ba sabida Haske ta kwashe mata takardun gida. Babu rantsuwar da batayi amma Ammi taki yarda da ita. Cewa tayi zata siyar mata fili domin ta siya kayan daki. Sai dai tayi mata alwashin auren bazai dade ba. Koda ya dade banda bakin ciki da tashin hankali babu abinda Haske zata fuskanta. Daddy Muktar dayaji labarin zancen kiran Haske yayi domin yaji ta bakin ta, yadda jikinta yayi sanyi tana kuka ya kara sheda mashi ba ita bace. Anan ya damka ma Ammi wani fili, cewa tayi bataso sai dai a rafunguza. Saida aka yi mata alkawarin za’ayi mata musanya.
Kawai ta janye bakin data ke ma Haske kuma ta flta daga filin dagan data shiga. Ba haka taso ba, sai dai daga baya amma yanzu filin bai wani dameta ba.Ta lura Haske sai gaba take yi abinta duk yadda taso ta watse. Tayi makaranta, tana aiki gashi yanzu ta samu hamshakin mai kudi zata aura. Bilal yaro ne ga Alhaji Bello Kampani. Ya shahara da kudi a Kaduna da kewaye, mamaki take sosai yadda Haske tayi goshi haka. Taso tayita jan maganarana bala’i har auren ya watse amma kuma an ki bate hadin kai.Daddy Zailani haka ya hakura aka je gidan Mommy domin gaisuwa, anan aka gayama baki nan ne aka rike ta kuma inda kara yafi kamata ayi anan. Mahaifm Bilal danijo mai dattako yaji dadi sosai kuma sun kara kima a idonsa. Shima Daddy yaji dad: saboda yadda Mommy ta tabbata komai ya tafi daidai babu karanci. Kanin Mahamn Bilal, sai Mijin yayarsa da abokin Baban sa su suka jagoranci komai. Shi Abbansa yana kawai kallo ne yana murmushi. Bilal ne babban dansa namiji. Sun Kawo su hunhun goro, swee‘, chewing-gum, tabarmu da sauran kayan saka rana da gaisuwan iyaye. Alhaji Zailani yace a saka biki nan da wata uku, a lokacin Alhaji Bello Kamfani yayi magana. Shi bayaso ayita jani in jaka. Duk dai kowa yana nan, yanzu ayi komai a watse. Baiso bikin ya wuce sati uku sannan yanaso a yanke masu sadaki su biya nan take. Mijin Mommy Engr Muktar Shima yaji dadin haka, anan ya yanke dubu hamsin. Abokin Alhaji Kamfani yace
zasu bada dubu dari da mator da bazai wuce miliyan goma ba daga cikin wanda yake
siyarwa. An bama Haske daman taje ta zaba kalan datake so. Daddy Zailani baiso ba abin yayi kamar auren jari sukayi. a Anan aka wayar mashi dakai akan cewa, su ba kananan mutane bane kuma bazai yiwu matar Bllal batada mota ba. Koba ranar ba dole su sashi siyan mata. Taron ya watse da ciye ciye da lashe lashe sannan akayi addu’a kowa ya kama gabansa. Bayan taflyar su, Haske mamaki take yi wai she is engaged. Wannan kenan! An soma hada hadan biki babu kama hannun yaro, Ammi kuma ta sake shiga tashin hankali. Tana bala’injin haushin yadda Fijr taki natsuwa kamar Shamsiyya. Da yanzu duka daular nan ita zata samo masu. Ita kuma Fijr taje ta siyar da Fili. Abin bai mata Wahala ba sabida ita ce Next of kin din Ammi. Anan tace su gaggauta su hado mata koma me suke dashi tana sauri. Dillalan sun lura batada wayyo sai suka damfare ta. Filin zai kai irin miliyan daya da dari biyu yanzu, ko sanda Ammi ta siya dubu dari bakwai. Sukace zasu bata dubu dari biyar. Taso karba sai wani zuciya ya raya mata domin ta kara. Anan tace dubu dari bakwai ko su barshi. Banki suka wuce domin komai ya kammalu. Da sauri sukayi kafm ta canza ra’ayin ta. Yanzu tanada kudi saura ta samu abinda zata ce domin tabar gidan ta koma Maiduguri. Kawai saita yanke shawara a satin bikin Haske saita sidada taje, zata gayama Daddy zata Koma wajen Mommy domin tayata shiri, idan taje zatayi kwana daya da zumar komawa gida saita gudu.
Laila kuma dataji an saka ranar bikin Haske da Bilal muma tayi sosai. Sai da Haske taje
gidanta taga yadda Bilal ke kiranta yana tarairaya. Anan ta soma tunani kila Bilal ya canza ne, kenan plan dinta bazai yi aiki ba. Taji haushin kanta sosai sabida Haske zata samu kwanciyar hankali wanda bata mata fatan shi. Tafiso yadda ta aure mutumin Banza ita ma tayi zaben tumun dare. Anan ta kira Bilal domin taji daga bakinsa ko ya soma san Haske ne, “Toh ke yanzu ina ruwan ki tunda bake kika haifan ba” ya fada rai a bace. Baki yana rawa ta cigaba, “Amma har ka mance ne. saura ce fah harciki tavi aka koreta” numfasawa vayi vana mamaki kawa irin Laila. “Karki damu wannan ba matsalar ki bane, ni yanzu nasan tana haihuwa. Ki samu ki dauki ciki a gidan ki tukun” saiya kashe wayar tareda dogon tsaki. Abu ya fado mata gwara ta gayama Haske Bad asalin dan iska ne kila ta wannan fannin zata fasa auren, Bazai yiwu ta aure shi ba tunda yayi hankali. Latsa wayanta tayi wanda Haske ce ma ta bata kwance IPhone 65. Bugu uku sai Haske ta dauka da fara’ar ta. “Tawan ya kike?“ Haske tace.”Lafiya lau, ya shirin biki?”
“Alhamdulillahi munata yi” Dama Ina so na gaya maki abu ne, kijini da kunnen basira. Kinsan bazan cutar dake ba. A matsayin yar uwa kike wajena. Munyi shekara kusan goma sha uku da saninjuna tun muna firamare…” “Wannan wani irin magana ne Laila da dogonjawabi haka. Halan gulma zaki min?” “Eh toh bazan ce gulma bane, kawai magana ne wanda ya kamata ki sani” “Please in dai akan Bilal ne ki rike abinki, tuntuni kike gaya min kyawawan halayan sa. Yanzu banso naji wani zance” “Maimakon ki tsaya kiji” “Nace banso, ki kyale ni. Kowa da guntun kashin 5a a hannu. Kuma koma yayi a baya Allah ya yafe mashi. Sai anjima” Saita kashe wayan, sekeke Laila take kallon wayanta. Tunani fal ranta yaushe Haske tayi wayo. Anya nan gaba zata zugata tayi ma Bad rashin mutunci harya kai ga cin Ubanta kuwa? a
Bata karaya ba sai ta tashi ta tafl chan gidansu Ammi. Dukda da nisa da gidanta bata damu ba. Ammi ne kawai zata daburta komai. Ance the enemy of my enemy is my friend, koda ta isa a falo ta iske Ammi da Fijr ana hira. Fijrtayi mata farar sani kuma ta san almura ce kamarta. Bayan sun gaisa sai tace, “Dama nazo zancen Shamsiyya da Bilal ne” Ammi ita kuma tana tunanin anzo zancen kayan daki ne. A fusace ta soma masifa “Amma Allah ya tsine maki, Ina ruwana da abinda Shamsiyya takeyi. Ki tashi ki fita tunda rai da arziki ko na saka Fijr tayi min waje dake” “Ammi ki tsaya kiji, da alheri nazo” “Babu Abinda ya dameni… Nace ki barmin gidana koh… kojikin ki ya yabama aya zaki” Fijr harta soma kwance kallabi jira take Ammi ta bata dama ta dake Laila san ranta. Da sauri ta tafi ranta baiso ba. ‘ “Aida bakiyi saurin korarta ba, dana dake banza” Fijr tace tana dariya. Kukan zuci wanda yafl na bayyane ciwo Haisam ya koma. Shi da kansa rokon hawaye yake ya flto masa amma abin ya faskara. Zuciyar sa daci yake masa duk ya tunkushe yayi baki. Ba yau ya saba neman abu ya rasa ba sai dai wannan karan yafi masa ciwo. Ya girglza da Mommy ta iya hanashi Shamsiyya. Tasan irin wahalhalun daya fuskanta a baya. Yadda yayi ruyuwa mai kunci marajin dadi. ‘Ba haka asalin sa yake ba, bayan wani mummunan kaddara ta afka mashi ya daina walwala, kullum cikin bacin rai yake baya dariya k0 kadan. Sam baida dadin sha’ani duk abinda kayi na ban dariya bazai dara ba. Hada girar sama dana kasa yakeyi tamau kamar maison shirin zuwa fllin daga. Daga baya ne bayan ya daidaita mutane suka gane cewa yanada wushirya tareda dimples‘ Bai magana mai yawa da zai bayyana Hakan. Tambayan kansa yakeyi laifln da yayi abu haka ta faru dashi a karancin shekaru. Zaman gidansu Firgita shi yakeyi duk yanda ake bala’in ji dashi. Kawai tsautsayi baya wuce ranar sa ne. Ya samu suna Dan Lele sanadiyar zama da namiji tilo wajen iyayen sa a cikin yara takwas. Daga baya zaman gidansu ya ishe shi saiya koma Bambale dake Zaria wajen kakarsa ta fannin Uwa, watau uwar mijin Mommy. Sannan saiya koma US wajen Mommy. Anan taylta mashi nasiha akan ya rungume kaddara mai kyau da mara kyau. Sannan yaje Therapy kala kala saboda yanada Post traumatic Stress Disorder. Cikin ikon Allah Mommy ta samu ya sakejiki sosai har ya fara fara‘a inda yake mayar da komai ba komai ba. Yanzu kuma daga dukkan alamu zai koma gidanjiya, mamaki yakeyi yadda Mommy bata damu koya fada irin rayuwar data tsinto shi daga ciki ba. Bayan gaida iyayen sa baya magana kuma cikin gidansu. Mum dinsa ta kira Mommy taji dalilin da Dan lele ya koma gidanjiya. Anan aka sheda mata. Shi kuma nashi kaddarar kenan cin wuya a hannun mace, duk da ba misali daya bane amma abu duk dayan ne. Mata ke daburta mashi LissaH. K0 a wajen aiki performance dinsa yayi kasa sosai. Bai taba tiyata mara kyau ba sai wannan karan. Na farko ya dauki wukar aiki yanaso yayi yanka, haka hannun sa yayita rawa kamar mai ciwo. Saida supervisor dinsa ya karba yayi. Basu hak’uri yayi inda sukayi masa uzuri. Bayan nan ya sake yi. Wannan karan kamaryana tsoron wuka ko kuma ya yanka mutum. Haka yayita hargitsa magani ya bada maganin ciwon daban, sannan ko bayani akan ciwo akayi masa tambaya ya daburce. Supervisor dinsa baida hakuri kuma yana tunani Haisam 
yaci ganye ne sabida kowa yana sanshi ya daina karatu. ‘ An bashi query saboda abin ya nuna rashin Kula da aiki. Sannan aka bashi suspension na sati biyu. Yaji dadln abin Saboda idan ba dole ba bazai jeba. Ana damunsa da surutu ga kuma matsananci ciwon ka dake addabansa. Tun kuma ranar bai sake zuwa gidan Mommy ba, baiso yaga Haske. Kamar yadda mommy ta bukata yanaso Shima ya mance da ita. Duk da ba abu bane wanda zai yiwu. Kamar yadda ba’a rana daya ya soma santa ba baya tsammani a rana daya zai bari. Kamaryadda yayi shekaru yana gina soyayyar ta cikin ransa haka zai dauke shi shekaru kafin ya cire. Shi yasan Haske tun a rayuwarsa na baya, itace kadai yake tunawa ta kawo mashi nishadi, sanyin ta da murmushi yana kawo mashi kwanciyar hankali. Ci Bai mance da ita ba amma Kuma baiyi tsammani zai sake ganin taba, cikin ikon Allah suka soma aiki waje daya. Shi bayada hanzari yana ganin sannu a hankali zai sameta yasa kallon (a daga nesa ya ishe shi. Nauyin bakinsa shiya jawo mashi duk matsalar dayake ciki. Dama an taba fada mashi zai zame masa abin tirwata rana. Kowa ya nuna bai dace da ita ba. Babu yaren da zaiyi amfani dashi akan ya fada masu ba haka bane. Kowa ganin yaro yake masa mai karamin kwakwalwa. Babu wanda yakeso ya fahimce cewa aure ba’a shekaru bane, Kuma hankali yafl ace ga shekararda ake samun ta. Abin dace ne idan Allah ya baka saika gode masa. Sau da dama zakaga tsoffln suna yarinta bayan yara suyi abu cikin hikima da dattako. Mamaki yakeyi ainun duk wanda ya samu da maganar za‘a ce,tayi mashi tsufa ko yayi mata yaro. Maganar kenan ya dulmiya akan shekaru. ‘what about love respect and friendship’ babu wanda yake maganarwannan. Jindadin auren shine abin tinkaho ba shekaru ba. Kowa yasan yafl kuturu naci, idan ya kafa kahon zuga a abu sai ya samu ko akwai matsala. Gashi haryanzu ya kasa koda hawaye dan dis kila ya samu saukin abin ke damun sa. Zuciyarsa sai masa barazanar fashewa yakeyi. Wani radadi yakeji da zugi. Sannan gashi makoshin ko yaushe a bushe duk iya ruwan da zai sha, rabin kansa kamar ana masa sarran gatari. Gashi sai hidima akeyi babu kama hannun yaro. Zai je masallaci yaji Mum tana magana da Sister dinsa wanda ke aure a Kano akan zasuje nanda kwana biyu siyyaya, taje shaguna ta fara duba abubuwa saboda yayi masu sauki. Cizon lebensa yayi wanda ya bushe kamar busarshen fura. Yana zaune cikin tashin hankali 
amma babu wanda yabi ta kansa. Kowa sabgan gabansa yakeyi. Shi yasan ba zai iya rabuwa da Haske ba, idan ma ya fada haka yayi ma kansa karya k0 mai sauraro. Ta riga ta gina wani babban sashe a zuciyar sa. In fact itace zuciyar baki daya. Itace take da makullin amfani dashi kuma bai san inda zai dauko ya bude ba balle wani abin daban ya shiga. Tunda ya dawo gida baya ko mai sai zaman daki da sallah, hard he kasafai yakeyi ba. Zallan tunani yakeyi. Mamakin Mallam bahaushe yake akan wannan nasa salon. Koda yake Shima gudun kada tace masa yaro Yasa ya kasa tunkarenta da maganar, kowa tunanin sa kenan abin ya zama ruwan dare. Wutan dakin a kashe sai AC dake aiki, baya ma iya kwanciya akan katifa sai dai kafet. Ido rufe yanata tunani ko ka shiga zaka zata barci yakeyi. Abubakar sau da dama yana biyawa idan ya dawo daga aiki amma ko ci kanka Haisam bai taba ce masa ba. Amsa sallama yake chan kasan makoshin sa sai ya rufe ido. Duk nasihar da zai bishi dashi baya tankawa. Idan ya gama zai mashi sallama ya rufe masa dakin. Kwana sai taflya yakeyi Haske zatayi aure, babu wanda ya kaita jin dadin abin da zai faru da ita. ltama yanzu zata samu iyali wanda zata kira nata. Taji dadi matuka yadda Haisam bai sake waiwayanta ba. Ya kara matsayi cikin zuciyarta kuma ya nuna yanada hankalin da kowa ke fadi. 
Badman yayi mata hadarin kudi sosai inda harta soma su dilke, sannan Kuma duk safe saita hada maltina da peak milk ta shanye. Wajen yamma ma haka takeyi. Fatan ta ya sake washewa yayi fluffy. Mommy da Daddy Zailani sai hada hada akeyi. Suna kokarin su siyan mata komai domin su kare mata yancinta. u Tsohon Gidan Alhaji Kamfani dake Yahaya road aka gyara shi fes, wajen gidan kalan madara sai cikin gidan fari tas kamar yadda ta bukata. Bata san hayaniya na kaloli tafi san komai nata a sanyaye. Ammi kam ko gezau, dabaru take nema domin ta wargaza aure. Sai dai kanta babu komai ciki sai koko, babu wani abin kirkin data iya samowa. Daddy yayi masu Fijr, Baraka da Anisa ankon su wanda dangi sukayi na Purple Swiss. Kawayen Haske kuma pink zasu saka. Fijr dariya kawai take yi saboda ranar bama ta gari, tana chan wajen boka domin ta samu dahir. Laila kam babu kunya tace dole Bilal zai mata anko da wasu kawaye uku. Kallonta yakeyi amma bazai lamunce Haske tayi ta’ammali da ita bayan bikin ba. Ya lura almura ce wanda bata san zaman lama. Bayan kwana biyu biyu sai Laila taje gidan Mommy domin taga ya ake ciki da biki, ta kara raina kanta yadda kowa ya sa kejiki yana hidima. Ko sisi bata bama Haske ba kuma batada niyyar badawa. Anan aka siyan ma Haske wasu purple coolers. Babu kunya ta kwashe wai yayi mata kyau. Azahiri Hasketa nuna babu komai amma Laila ta soma kaita bango. Kawai yanzu dannewa takeyi. Destiny ran farko da Laila takai dare yayita fada, amma dayaga tazo da takeaway na abinci kala kala wanda ta diba a kitchen din Mommy. Sannan ga lemu na kwali masu yawa. Siyasa yayi yace bawai baiso ta rinka ma bane. Kawai bai san tana dare ne amma ya bata go ahead taje duk sanda ta bukata. Yanzu haka tanada Number din Anty Umma mai aikin Mommy. Sai dai ta kira tace zeta ayi girki da ita sannan ga kuma abinda takeso. 
Mommy bata damu ba, Laila tayi ma Haske rana sanda take bukata, yanzu abinci bazai rabasu ba. Balle Laila nada miji kuma bazai yiwu ta koma a gajiye ta soma girki ba. Haka 
Saif ke rashewa yayka kwasan girki. Kuma yana bakin ciki sosai idan taje ranar da baya dakinta. ‘ 
Satin biki yazo komai ya sake kacamewa ma Haske, daga oflshin su an bata hutun sati biyu, taji dadi sosai yadda zata mayarda hankalinta. An kawo lefen Haske seti biyu mai yan shida. Da cobalt blue da Fusion Pink masu kyan gaske. Duka designers ke ciki daga Ralph Lauren, Prada, Gucci, Michael Kors, Nina Ricci, Chloe, Salvatore Ferragamo dadai sauran su. Babu ne kawai ba’a saka ba saboda komai dozen ne. 
Mommy tace dole Ammi zata tarba lefen a gidanta. Rai bai soba akayi haka. Sanda aka shiga da kayan saida taje daki tayita kuka wiwi na minti 15 domin tsabragen bakin ciki gashi kuma taji labarin Haske tayi mota wanda yafi nata daraja. Yadda Ammi keyi zaka sha Haske yarwata kishiya ne ba yarinyartwin sister dinta data rasu ba. Saisaita kanta tayi kar a gane Kana ta wanke fuskanta da ruwa ta ma. Ana mar da wasu abin da bata taba gani ba, ita harta soma tunanin yadda zata kyasta masu ashana ta kona. Anyi taro daidai Baraka kanwar Haske tana nan kuma tayi rawar gani. Ga kuma saka hannun Mommy, bata bar gidan ba saida Daddy ya dawo ya kalla sai suka tafi dashi. Anan tasa a mota ta mayar gidanta. Yan kukan nada yawa sabida harda Laila, a yau tayi dana sanin zugata akan ta aure shi. Ta bala’in girgiza hankalinta ya tashi. Kana ganin kayan kasan an siye shi ma wanda ake so ne. Gashi batayi wani shela ba akan yin memo irin nata na welcome to the tarban lefe of Shamsiyya. Taso ta diba wani abu amma Anty Bilkisu babban yarsu Ammi tana tsaya akan kayan. Haka ta hakura da zuma zata faki idon kowa koda designer bag ne ta dauka da 
takalmi tunda ita ha a saka mata ba. ‘ Hadiza tana Staff room wata tazo da katin auren Haske da Bilal mai dankarin kyau. Anan tayi mata korafl akan meyasa bata gayyace su ba. Nan ta soma inda inda kafin a gane mugun halinta. Bataso ba taje dakin Daddy domin ta kwashe kati. Haka tayita rabo ranta yana mata kuna. Sai dai ta sheda masu ba ita ke rike Haske ba suje gidan Mommy amma za‘a hade chan. Kowa yanata mata murna yarta tayi dacen miji. Ana fadin abin gumi yana karyo mata. Bakin ciki mara misaltuwa ke dawainiya da ita. Mommy tayi ma Haske kamu a Ceremonial canopy, abin yayi armashi sosai duk sunyi kyau abinsu daga Haske har Bad. Laila kam wani munafikin riga tasa kai zaka iya ranstewa 
batada aure. Sai feleke takeyi tana shige da fice. Da dangin miji sukazo kama amarya tace bazasu bude gyale ba sai an basu dubu dari. Vayar Bad tace Haske tat”: karfln haka domin tanada tsada. Anan ta bada 250k cash. Jikin Laila ya soma rawa saboda bata taba cin karo da yawan kudin ba. Nan ta flzge ta saka ajaka tareda hana sauran kawayenta. Anan sukayi ta Allah ya isa suna kiranta muguwa kuma bazasu yafe ba koda gawarta zai rinka ci da wuta. Bata ko girgiza ba sai dai mirsisi. Anyi kuma pre wedding dinner wanda mutane manya a Nigeria sun hallara, abin yayi armashi sosai babu kama hannun yaro. Anyi ma Ammi kara a nata wasata, moroka sai gode mata sukeyi suna fadanci akan yadda ta haifan wannan Hasken Lantarkin. Tun tana basarwa saida ta sake jikinta. Mommy tana kallonta ta bushe da dariya, anaso ana kaiwa kasuwa. Fijr kam rawa takeyi kamar yar club. Haka taje gaban DJ tanata juya mazaunan ta. Daga sama har kasa. Saida Mommy ta aika ace mata ta bari Kotaje ta sharara mata mari. Bataso ba haka taje ta zauna. Daga nan ta faki idon mutane ta koma gida ta kwashe kayan ta. Tasha ta wuce straight zata Maiduguri wajen Sweetie Ghali. Shima Bad yayi kyau, kuma abokansa sun masa kara. Anyi ciye ciye da lashe lashe sai aka rufe taro da addu’a saboda gobe daurin aure. Anma sai dai kuma ina Haisam? 
Zazzabi yakeyi sosai wanda magani baya aiki, babu yadda ba’a yi dashi ba ya daina wannan mugun tunani amma yaki. Koda suspension dinsa ya kare bai koma ba. Yan asibiti sunzo sunga yadda jikinsa ya canza akayi masa uzuri. Mum yanzu duk wannan biki da akeyi bataje ba. Tana gida tana ta sharban kuka yaronta yanaso ya salwanta. Baya cin abincin kirki kullum sai tunani, kukan har yau ya kasa. Rokon Allah yakeyi ya samu damar zubar da hawaye yaji sauki amma abu ya faskara. 
Ana gobe daurin aure tashin hankalinsa ya tsananta, sai dai Mommy ta ziyarce shi bayan dinner domin ana ta tunani kila bazai kwana ba. Anan ta kira Haske ta tambaya ko zata fasa auren Bilal ne. Ita kuma fashewa da kuka tayi wiwi kamar ana dukan ta. Sam bataso ta aure Haisam Bilal take so. Haka Daddy Muktaryayi ma Mommy fada akan dalilin haka. Suna cikin tsaka mai wuya duk wanda aka bakanta ma rai dole neya fada cikin tashin hankali kuma ai wannan Haisam ne baida gaskiya tunda kwace yakeso yayi. Mommy tayi kuka ranar kamar ranta zai fita, tayi dana sanin barin Bilal ya tura iyayen sa. Tasan Haske tanada hakuri kuma zasuyi saurin shawo kanta ba kamar Haisam mai uban naci ba. Yadda Haisam yaga rana haka yaga dare, yanata kirga saura awa nawa ya rasa Haske har abada. Wajen azahar ranar daurin auren Abbansa yana shiga dakin, durowa ya wuce ya ciro manyan kaya farare sannan ya umurce shi akan yaje yayi wanka zasu daurin aure. Ya kamata yabar zancen tareda rungumar kaddara. Haka ya shirya suka tafi, ya mance yaushe rabon dayaga hasken wuta saboda ko masallaci ya daina zuwa saidai salla a daki. An daura auren Shamsiyya Zailani Abubakar da Bilal Bello Kamfani karfe 2 na rana. A gidan Mommy akayi abin tunda yanada girma, Abbansa yace yaje dakin Abubakar ya zauna kafin ya gama gaisawa da baki sai su wuce. A hanya suka ci karo da ita. Sanye take cikin leshi mai ruwan madara sannan kallabin ta mai ruwan zuma. Tasha kunshi na baki da ja tayi bala’in kyau. Fuskanta zallan walwala ke nunawa. Tayi kashar kashar kana ganinta Kaga farin wata. Gabanta ne ya fadi sanda taga yadda ya canza fasali. Yayi duhu sosai ga kuma rama. Sannan idansa ya fito waje alamar wuya. Zai canza hanya saita kira shi. “Haisam tsaya mu gaisa mana” cak ya tsaya saita karasa wajen sa. “An daura auren” tace a sanyaye “I’m sorry Bilal na keso” ta kara fadi ‘ “Nagane karki damu, you should be happy. We all deserve it. I can’t be selfish na hanaki farin cikin ki, Allah ya sanya alheri. I’m so sorry for bothering you, nasan na shiga rayuwar ki sanda bai dace ba. Allah yasa ya rike ki fiye da yadda zan iya. Ina sanki Shamsiyya shi yasa zanyi respecting feelings dinki. Dole naso abinda kike so, saboda haka ake asalin soyayya. Karki damu bana fushi dake kokuma jin haushi ki, nasan yadda so yake kuma cikin mu mutum daya zai samu, gwara ace kece because I love you that much ” murya sa na rawa yake maganar. 
Daci yakeji a kirjin sa ga kuma dishi dishi idansa yana masa, kansa bala’in sara yake masa kamar zai fadi. kallon kasa yayi saboda bazai iya hada ido da ita ba. Sanyi yaji fuskan sa alamun hawaye yana ziraro wa. Kadan kadan sai gudun famfo. Gabanta yayi mummunan faduwa dataga haka. Gashi sai rawar sanyi yakeyi kamar mai zazzabi, kafansa yana bazanar zubar dashi kasa. Zuciyar sa kiris take jira ta fashe ta huta. Anan ta soma tunani anya batayi sankai ba? Wannan kenan! 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]