[Advertisements⬇️]

HASKE CHAPTER 12 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HASKE

CHAPTER 12“Ke kuma uban me kike kallo?” ya Kalle Sameera a fusace. Da sauri ta sunkuyar da kanta kasa gabanta sai duka yake uku uku kafin ya watso mata ashar. Saif baida mutunci sosai kuma ya iya ashar babu kama hannun yaro. Baiko damu da yan lalle da suke wajen ba. Tsuma yakeyi sosai idansa ya kada ita kumajikinta duk yayi sanyi ta mayar da idanta kasa domin ta cigaba da Lalle. Hannun ta sai rawa yakeyi ta kasa saisaita wa. Hawaye siriri ke ziraro mata daga idonta. Bata san hawa ba bata san sauka ba kuma an cin mata mutunci.
“Kika sake kallona saina saba maki, algunguma kawai. Kinyi asara Sameera munafunci baida amfani. Sa‘idawa larabawan layi. Masu sujjada da kumatu. Ana ruwa kuna dirgawa” yace. Anan wata mata makwabciyar su tayi mashi magana. Dayake batada hak’uri itama. “Haba Baban Abul Khair matanka kake zagi kamar kana tasha” Kallonta yayi ya watsa mata harara, “Ban kasa dake ba karki kwasa, kika kara saka min baki na zage ki” yace ko ajinkin sa. “Idan ka fasa zagina ka raina Allahn daya halicce ka, mu zuba nida kai kada Allah ya raga ma wanda ya raga ma wani” saita tuge hijab dinta ta watsar. Sameera ta ruga da gudu ta riketa. “Dan Allah kiyi hakuri karki jawo min ya hanani sana a “Banda ma kaddara dube ki dube shi ina ke ina shi, mutumin banza mutumin wofi kana cin ma matan ka mutunci akan kudi” matar tace. Yaso ya amsa ta amma tunanin sa daya, yanzu idan sukayi dambe tayi mashi duka ya zaiyi da kunya wajen su Sameera da Laila. Matar tanada Kiba sosai wanda yasa ya kiyaye ta. Daki
ya wuce kawai sai ya zageta, “Daga yau karki kara shigo min gida na, shegiya annoba”
A daki ya riske Laila tana zaune bakin gado. Da sauri ta mike tsaye saboda ta tsorata dashi. Balle yadda yake watso ashar kamar bashi ba. Lallai ya iya fuska biyu. Bazata ce tayi dana sanin auren sa ba amma kamn tana hanya. Ta Kira Haske yafi a kirga bata dauka ba, Bilal ma duk ta kira amma bai daga ba. Nan ta kara rudewa saboda Saif yace yau saiya daketa. Bai ma tsaya yaji abinda tayi da kudin ba, cefane ne kuma shi zai ci.
“Dan Allah Destiny kayi hak’uri, wallahi kasuwa naje nayi mana shopping. Su kayan da muke amfani na siya fah su siga da bindin Sa, ba wani abin banza bane” tace a tsorace. A fusace ya juya ya kalleta, “Dake da Bindin Sa kunci kutumar ubanku. Jimin yar iska nace zanci ne? Koko dan Kinga ina kyale ki zaki kawo min raini. Waye ce maki ana taba min kudi na? Wallahi kinyi na farko kinyi na karshe” Cikin tattausan murya tana kuka ta cigaba, “Destiny ka bari na kira Haske yanzu zata ara min kudi” shiru yayi na kusan minti daya sai ya cigaba “Al’mura watau salan ace bana iya rike gidana koh? Tozarta ni kike so kiyi?” Sai ya soma tsuma ya nufeta yana nuna mata yatsa.
“Watau yawo dani a gari kike so kiyi kina min terere. Saboda ace min mutumin banza. Na samu Allah ya rufa min asiri shine kike so ki tona min koh? Toh dan ubanki bazai faru ba.
ldan Haske taji labarin nan nida kene” tafiya yayi yana sumbatu. “Salan mutane suce akan 4k na haukace a fara min kallon tsiya….” Bayi ya wuce ya zazzage cikinsa, ya kusan awa daya kamarzai haihu. Ko daya fito doyin wajen kamar dabba ya mutu. Gashi babu dama Laila ta saka turaren wuta yace tanayi dashi ne ya zage kan uwarta. Tana dai zaune chan kurya tana zare ido ba tasan me zaiyi ba.Durowa ya wuce ya dauko akwatin lefen ta. Nan ta zare ido tareda nufansa. “Meye zakayi da kayana?” “Kayanki kuma? Da kudinki kika siya? Malama bar nan ko ki daku” yace cikin masifa.
ltama tsiwan yana damunta saita saka hannu kan kugu tana jijiga. “Wallahi bazaka dauka ba” “Malama ki barni na fanshe kudina dan kasuwa zankai na siyar” “Toh ai ba haka akeyi ba? Kudin da zaka min gidan gona saika cire kudin ka” dariya yayi mai ban takaici. Laila batada hankali. Mamaki yake yi sosai yadda taci kudinsa a waje. Yanada bala’in mako dan ko kansa yana ma rowa wata rana. Kaman su hadu da Laila In data din shi ta kare saiyayi 3 days baya online. Wani lokacin fa saidai yasaya ta 1am to 5am night plan. Kuma gidan su masu kudi ne ba nauyin kowa akan shi balle ace nan yake kai kudinsa. “Gwara ki cire ranki, sabida saina kwashe kayan nan. Malama karki isheni kokuma na zuciya na sharara maki mari. Dan na dake mace ba abin wuya bane” Saiya soma fitar da zannuwa dasu gyale sabbi wanda zai kai ya siyar. Rikejakartayi, “Wallahi bazaka siyar min da kayana ba, gwara ka dake kudinka” 
“Kinsan Allah saina siyar, kuma na dake kudina idan baki matsa min ba” Saiya ingijeta yanda ta fadi kasa, aikam ta bige baki da gado inda jini ya soma kwarara. Ko kallon ta baiyi ba yaje ya samo leda ya zuba ya tafi abinsa. Koda ya dawo da magrib yan lalle sun tafi. Tuni Sameera ta kulle dakinta kafin bala’in sa ya ciyo shi ya antayo mata. Ita kuma Laila taci kuka kamar ranta zai fita. Ga idanu sunyi suntuntun kamar biredi bugun kato. Shi bindin san ko ci batayi ba yama fita kanta. Yanzu kam tayi dana sanin auren sa. 
Kuma saita fara lura Sameera batada matsala k0 kadan. Karya Saif yake shiryo mata akan laifin da batayi ba. Bakin ciki ta yini dashi ranar sosai. Da taji karar motarsa gabanta yayi mummunan fadi saboda batasan da wani tsiyar ya dawo ba. 
Shi kuma ya saida kusan 25k saboda da yawa ya kwasa. Yaji dadin samun kudin kuma ya dauki alwashin gobe zai kwasa sauran ya kai kasuwa. A falo ya riske ta tana zaune. Bata kulashi ba illa kallo data cigaba. Tsoron sa karya yi mata fuska ta hana shi naman tunda ya nuna baiso. Rage murya yayi sosai yana murmushi. “Rabin raina yau k0 dan fara’a babu” Ko kallon sa batayi ba, zuwa yayi kujerar ya janyota jikinsa. “Fushi kike dani? Ai haka aure ya gada. Ayi fada Kuma dole a shirya. Kiyi min murmushi kona samu sanyi a raina“ haka yayita mata surutai harta saki jiki. Anan yace ta kawo mashi abinci. Yaji dadin naman saboda akwai tsoka ga fatar da laushi. Sannan kashin akwai taunuwa. Kashegari dama wajen tara na safe zai koma dakin Sameera. Bai tafi ba tun wajen bakwa yace Laila ta dunduma mashi naman ta bashi. Haka su ka cinye tas gudun karya tafi taci banda shi. Da fara‘a Sameera ta tarbe shi, yaransa ma haka. Kafin ya zauna kan kujera ya raba idonsa kan centre table k0 akwai abinci. Nan yayimaraba da kuloli 2 da kayan shayi. Taliya ta dafa da miya wanda zasu ci. Yana basarwa yaje ya zauna gaban cooler ya zuba san ranshi. Ba tace mashi koma ba illa wucewa kitchen domin tayi aikin gabanta. Daya shirya zai tafi sai take masa magana, gas ya kare ga kuma kayan abinci duk babu. Ko taliyar daya gani shine na karshe. Anan ya soma masifa. Abinci baya karewa idan baya dakin sai yana dawowa. Bata k0 kalle Shiba ta dauki gas takai mashi bayan mota. Abin ya kona mashi rai. Dari biyu ya bata ranshi yana mai kuna kamar ana zare mashi rai. Wai ta siya garri gwangwani 2 da kubewa busarsa da manja tayi masu teba suci. 
Haske tazo ta dauki wayan Laila chan daga baya bayan ta natsu. Dadin abin tana gidansu Ammi ne babu daman ganin Haisam. Bilal yayi mata kashedi akan ta rabu da Haisam idan tana san aurensa. lta abinda yake bata mamaki da Chan baya santa haka sai yanzu data samu wanda sukayi dan connecting shine ya rude yana kishin ta. 
Anan ta gayama Laila komai tunda basa boye majuna magana. Sannan ta gayama Laila cewa gaskiya tana ganin mutuncin Haisam kuma yafi hankali. Kawai shekaru ne da sukayi kadan. Kuma ta tabbata idan zancen wanda zai riketa ne toh tana kyautata zaton shi din ne sabida kamalansa 
Laila tasan zancen nan gaskiya ne, kawai ta tsani Haisam ne amma baida aibu. Yanada bala’in mutunci ga sanin ya kamata. Kuma tabbas zai rike Haske babu kokonto. Sai dai bature yace, “Misery loves company’ bazai yiwu tana zaune cikin bakin ciki da Saif ba ya kasance Haske tana cikin kwanciyar hankali. Gwara su duka su aura mutanen banza. 
Yadda Bilal keda zafin nama haka Saif yake, idan yaso su duka ayita dukan su. Amma Sam Haske bazata aure Haisam ba. Nan cikin siyasa tayita nuna mata burin kowace ‘ya mace bai wuce ta samu wanda zaiyi kisa akan ta ba. Kuma karta damu da mugun halin Bilal idan yayi aure zai bari. 
Sau da dama yara maza lalatartu amma za’ayi masu aure, cikin ikon Allah kuma suna bari. Ranta bai kwanta ba. Meyasa bazata aure mutumin arziki ba, kamar yadda Sarkin Kano yace aure gidanjin dadi ne ba gidan hakuri ba. Meyasa bazata aure wanda zataji dadin aure dashi ba. Da Laila taga tana kokarin zillewa. Daga dukkan alamu Haisam ya soma kafuwa cikin ranta. 
Nan tayi mata bayani akan ba’a auren age mates, wannan dabi‘an turawa ne kuma baya lasting. Gwara ta aura Bilal wanda ya girmeta nesa ba kusa ba. Sannan Bilal yanada kudi duk bakin cikin da zata kwasa tana cikin daula. Ko kuka zatayi tana AC yana ratsa ta. Haka ta rinka binta da magana kala kala har Haske ta aminta da ita. Laila kamar yar uwa take wajen ta kuma bazata taba cutar da ita ba. Da suka gama na Haske sai Laila tace ta ara mata kudi, bata fada mata abinda ya faru ba kafin ta sake tsorata da aure. Duk ta kosa itama ta aure Bilal ya soma cin ubanta. Babu haufu Bilal baida yafewa, wannan haukan data sa yanayi a waje saiya rama dubun sa idan sun shiga. 
Nan take Haske tayi mata transfer na dubu goma, ita dubu biyar tace a ranta mata amma aka bata kyautar dubu goma. Taji dadi sosai harta soma tausayin Haske amma sai wani 
zuciya ya raya mata shawara data bada shine daidai karta karaya har sai Badman Bilal ya aure ta. Tana nan ta hakince tana waya a daki Saif ya shiga, wajen mai shago na saman layinsu yaje ya siya Leda baki da yellow. Kitchen ya wuce abinsa ya loda abinci nasu taliya da macaroni daga kayan garan da aka kai mata. Saiya tsiyaya man gyada a roban Swan babba Sameera tana barci lokacin saiya ajiye mata kamar shiya siyo daga kasuwa. Ya samu ya cike gas din ranshi bai so ba. Wannan kenan.
Bayan kwana biyu… 
Su Fijr sun dawo daga tafiyar da sukayi, basu gayama Daddy zasu dawo ba sai dai aka gansu kwatsam. A lokacin Haske tana kitchen tareda Lantana suna abinci. Sakwara sukeyi da miyan Affan sai lemun kwakwa da madara. Babu abinda bata sa a miyan ba domin ta kawata shi. Daga su crayfish, stockfish, dry mh, ganda, naman shanu, periwinkle duka dai. Dataje Abia NYSC ta koya irin nasu salon. Kamshi ya bade gida Ammi sai murmushi takeyi sabida tana tareda yar gusau. A falo suka ci karo da Haske zata kai cooler din abinci kan dinning table. Gaba daya gaban su ya fadi. Da farko Ammi tasha fatalwan Hafsat ne yake mata yawo cikin gidan. “Nikam Hafsat koda nina kashe ki ai bazaki rinka min sintiri ba cikin gida” tace a tsorace. Haske bata gane me tace ba, dukawa tayi kasa ta gaida ta. “Ammi sannu da zuwa” “Ai ashe Shamsiyya ne, ina ce wancan almuran ne” ta fada saita wuce. Fijr kuma ko kallon Haske batayi ba. Haushin Ammi da Hajia Yagana ya shafe kowa. Ammi ta roketa akan tayi mata rai ta fita harkan Ghali. Tayi mata alkawari har kano zata ta nema inda Isi yake. Fafur 
Fijr taki yarda. Yanzu babu wanda takeso kamar Ghali. Fijr tunani takeyi yadda zata samu kudi masu yawa. A sirrance zata koma Maiduguri wajen bokan Hajia Yagana. Shine yasan Hajia da dukka weakness dinta kuma dama da dan gari ake cin gari. Ta wajen shi zata samu damar mallakar Ghali babu wani wahala. Anan ta tuna Ammi ta siya fili a rafinguza. Zata dauka takardun ta siyar idan yaso bayan sun fara soyayya da Ghali ya bata kudin da zata siya wani. Sai data bari Ammi ta taf’l hanyar dakin Daddy tukun kam ta sidada taje ta kwashe takardun. Yanzu zata siyar hankali kwance ta kusan cinma burinta. Shi kuma data gayama Daddy sun dawo, a fili ya nuna bakin cikinsa. “Amma inace sati biyu zakuyi wannan wani irin rashin cika alkawari ne” abin ya bama Ammi haushi saita tafi bata amsa ba. Lantana ta aika ta kai mata abinci daki domin bata san ganin kowa. Taji dadin abincin sosai tunda bazata iya girka rabinsa ba. Bata san girki saboda tanada matsala da saka Maggi,yanzu zata zambada shi duka. 
lta ma bataga amfanin ajiye fili babu gini ba, nan ta yanke shawara akan ta siyar sai tayi amfani da kudin wajen wani abu. Koda ta duba lokacin Haske ta riga ta tafi. Anan Ammi tayita watsa ashar. Dama tanata mamakin dalilin zuwan haske gidan ashe sata tazo tayi mata Wannan kenan! 
Shi kuma Badman Bilalyayi ma Mahaifinsa magana akan auren Haske. Yaji dadi sosai 
saboda suna tunanin kila auren dole zasu yi masa idan bai yi cikin yan kwanakin nan ba. Balle da yaji yarinyar Alhaji Zailani ne mutumin kirki abin ya dadada masa rai. Sun san cewa zasu samu surika ta gari. Anan yace yayi shawara da Haske akan ranar da zasu saboda su a shirye suke. Hajia Lubna Umman sa itama tayi na’am da batun. Balle dataga hoton Haske kyakkyawa taji dadi sosai, kowa ya yaba da zabin Bad kuma Shima yaji dadin zai aure Haske. Dukda dai ba haka yaso 
ba. Yaso yayi tasting dinta kafin auren, sai dai yaga Haisam zai masa zarra dole yayi sauri. 
Haisam yaje gidan Mommy, yasan Haske bata wajen dama ba wajenta yaje ba. Yaje ne domin yayi mata magana akan yana son Haske ta taimaka mashi. A falo su Maimuna da Amina sunata murnan ganinsa amma da kyarya kula su. Baya jin dadinjikinsa ko Abubakar bai ma magana ba. A dakinta ya sameta tana cin fruits salad. A kasa ya zauna bai ce komai ba. Fuskan sa fal damuwa, tagumi yayi sosai bai ce komai ba. “Dan Lele yunwa ne?” Da Kai ya amsa mata alamar a’a, murmushi tayi sai tace, “Ko dai surikata ce? Shiru sukayi na kusan minti goma kafin ya soma magana. ” Mommy alfarma nake nema wajen ki ” ” Fadi inajinka Dan Lele” Kuka ya soma sai ya durkusa gwiwa biyu-biyu, “Dan Allah Mommy ku hadani Aure da Shamsiyya, Wallahi ina santa…. Tuntuni Mommy abin ke damuna…. Mommy Kuyi min Shiru tayi tana nazarin sa, na daya yayi ma Haske yaro tunda shekarar su daya. Bayan nan kuma koba Haske ba zata so ya kara shekaru kamar 25 k0 27 tukun. Babu Haufi yanada hankali kuma da rainon kauye ne da tuntuni da aurensa. Sai dai ba kauye suke ba kuma abin yayi mata bambarakwai. Kukansa ya tsananta harda dafa mata gwiwa, “Mommy Shamsiyya tana jin maganar ki, bazata ce a’a ba. Koda bataso bazata iya fadi ba. Kuma nayi alkawarin zan koya mata yadda zata soni” Mommy tana mamakin soyayyar zamani, idan Haisam yayi hakuri zai mance da Haske ya samu wanda ta fita.Kumataga Haske tanada saurayi wanda har falo Bilal ya shigo ya gaida ta. Taga yafi cancanta da ita. Sai dai Haisam kamar yaro ne wajen ta. Bazai nema abu ya 
rasa ba muddin bai saba ma addinin musulunci ba. 
“Haisam banso na takura ma Shamsiyya, yarinyar ta wahala, ya kamata taji dadin zaman aure” 
Da sauri ya chapke, “Wallahi Mommy zan rike ta, bazan wulakanta taba. Rayuwa na zaiyi baki mommy idan bata ciki. Itace farin ciki na, itace Hasken Annuri na, bazan sake murmushi k0 naji dadin wani abu a duniya ba idan ban sameta ba. Rashin Shamsiyya zai zama min bakin canji a rayuwa na. Mommy zan shiga kunci kuma rayuwa na zai salwantu a rashin ta. Zan shiga tashin hankalin da ko makiyina bazan so ya fuskanta haka ba” Tsoro Mommy tayi dagajin kalaman sa, tabbas babu wasa a fuskan sa. Yadda yake 
maganar haka take. Ya riga ya dauki alwashin abinda zaiyi. Haisam yaro ne mai saukin kai, 
amma yadda yake magana yau sai yayi kamar ba shi ba. Ya fita daban daga yadda ta sansh kuma tabbas rashin Shamsiyya zai maida shi abinda yafi haka. Mommy bata cire rai akan zata iya canza masa ra’ayi ba, “Haisam nima ina sanka da Shamsiyya, koba kaiba wani dangin mu ya sameta. Muma ko babu komai mu samu mai hak’uri a tsakanin mu. Amma baka ganin tayi maka tsu….” bata karasa fadin tsufan ba ya tsinke. 
“Kiyi wa Allah Mommy karki ce tamin tsufa… Wai meyasa ake haka ne? Na girme ta da watanni kuma ko ban girme taba Mommy inada Hankali mana Fusabillahi… Nasan meya kamata.” 
“Kawai maganar mutane ma nake gudu, kar ayi wani magana kamar munyi abin kunya” tace cikin takaici “Manzon Allah SAW yayi fa, shida ya aura wanda ta girme shi balle mu shekarar mu daya… To hell with people and what they believe” 
“Language Haisam…. Language” “Kiyi hak’uri” 
Suna cikin haka sai ga Haske tazo,itama ba’a san da zuwanta ba saboda ya kamata ta yi sati biyu. Murna fal ranta, Bilal yace zai tura mutanen sa. Haisam ta gani yana kuka. Anan tasha jininjikin ta. Tana tsoron kada ya bata mata lissafi. Yanzu ta tantance cewa Bilal take so ba kowa ba. Kawai Haisam zuciyar ta ke mata barazana amma infatuations ne. Kuma ta gode ma kawar arziki Laila data dawo da ita hanya. Sun zauna su biyu a kasa Mommy tana saman gado, dakin yayi shiru anaso aji abinda zata ce. Dukansu a matsayin yaranta suke. Tana cikin tsaka mai wuya. Duk abinda tace saita bata ma daya daga cikin su rai. Yanzu me zatayi ?Wannan kenan! 

Hmmmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]