GIMBIYA SA,ADIYYAH CHAPTER 44 THEND QARSHE

GIMBIYA SA,ADIYYAH 


CHAPTER 44 THEND QARSHE
RanarAsabar da sassafe Sarkin Kubaisu da tawagarshi suka rankayo zuwa Bilbah. Da misalin karfe sha daya na safe suka iso masarautar. Sun samu tarba ta musamman, domin kuwa abin ya hade ne da gagarumar walimar da mai martaba ya shirya ta farin cikin dawowar ahalinshi. 
Gimbiya Saadiyya na daki sai faman shirya ta ake yi. Musamman aka dauko mai kwalliya da gyaran jiki ta 20. Da taimakon Hafsa aka shirya ta ta fito gwanin shaawa sai budada kamshi take yi. Da murmushi a fuskan Hafsa ta ce, “Amarya kin ga wani irin kyau da kika yi kuwa? Gaskiya Yerima ya dace mata.” Halimatu ta rufe fuskanta alamunjin kunya. “To yi maza ki goge kwalliyan garin shegenjin kunyankin nan. Kowa fa ya san kina son mijinki. To kunya na me? Idan ma za kiji kunyan wasu ai bai kamata kiji tawa ba, ni da muka taso kusan a tare.” “Yaya Hafsa ke nan. Kina mantawa da halina at times. Kin manta kara da kawaicina ko?” Murmushi Hafsa ta yi, ta ce “Ban manta ba Halima. Amma a wannan Iokacin bai kamata ki ji kunyana ba. Lokacin da 23 ki daga hannunki sama ki gode wa Allah ne, ya cika miki burinki. Da gaske har cikin raina wani irin dadi nakeji mara misaltuwa. Da dukkanin zuciyata nake kaunar aurenku da Yerima Abu Sufyan. Kun yi wani irin dacewa da ban san ya zan kwatanta miki ba.” Gimbiya Saadiyya ba ta san abin da za ta ce ba sai ta rungumi yar uwarta cike da kaunarta. Jin komai take tamkar a mafarki. Suna cikin haka sukaji sanarwar daurin auren, har ma an daura. Indo da Salbiyya suka shigo cikin dakin, dukkaninsu sun sha ado da suturu masu tsada sosai. cikin fara’a Salbiyya ta rike ma Gimbiya Saadiyya hannu, ta ce, “Yata kin ga wani irin kyau da kika yi kuwa? Gaskiya kin burge ni sosai. Hafsa kun fiddo min ‘ya sosai ba kadan ba.” Hafsa ta murmusa, “Goggoji daga ita ne fa sirrin kyawun. Kin san abunka ga kyakkuawan mutum. Sai dai shi ya taimaki kwalliyar ba wai kwalliyar ne za ta taimake shi ba.” 
Dariya ce ta biyo bayan maganar Hafsa. Indo in banda murmushi babu abin da take yi. A kasan ruhinta kuwa tararrabin rabuwa da diyarta a yau kawai take yi. Ba ta zauna da ita ba bare su yi shakuwar uwa da ‘ya. Kuma ga shi bayan dan lokaci kadan da suka hadu aure zai raba su.Atake ta ji idonta na neman kawo ruwa. Ta gaggauta dakatar da su tun be a gane mata ba. “Har an daura, kin tashi daga Miss kin koma Mrs.” Anwar ya fada a daidai shigowar shi. “Congratulations Sister. Ina fatan kin shiga ke nan. Allah Ya datar da ke dukkanin farin ciki dajindadin aure. Gaskiya kin yi dacen miji. Kusan duk halayenku daya. Kun dace da juna sosai.” “Sosai ma kuwa Anwar. Yerima Abu Sufyan ya kara dukkan wani abu da la a so cikakken namiji ya mallaka. Ina musu fatan alkhairi.” Hafsa ce ta yi wannan maganar, tana tuna yadda ta kaunace shi, ta kaunaci aurenshi, ta silar haka har kaddarar auren Yerima Bukar ta fado mata. Sai dai fa a yanzu ta riga ta yakice kaunarshi. ta mallaka ma var uwarta, rabin iikinta. 
SananNa sukaji, cewa amarya da ‘yan rakiyarta su zama cikin shiri, da misalin karfe uku na rana ‘yan daurin aure za su juya tare da ita. Ido Gimbiya Saadiyya ta fiddo waje. Ta kalli lndo da mamaki ta ce, “Mama, yau kuma?” Indo da tun sadda ta shigo tsabar kara da kawaici ba ta yarda ta hada ido da Halimatu ba, ta daga mata kai. “Dazu da safe ne mai manaba ya canza shawara. Da ya ce sa nan da sati biyu za kI’ tare ne wai saboda abun yazo babu shiri. To kuma wai bai ga Fa’idan hakan ba. 
shi ya sa ya canza shawara. Suka yi magana da Sarkin Kubaisu tun kafm ma su taho, aka shirya komai a can, yau din nan la a tafi da ke.” Kuka Halimatu ta fashe da shi, cike da shagwaba ta ce, 
“Lallai ma, amma dai Abba bai kyauta min ba Mama. Komai fa ba mu hada ba. Ni dai don Allah ki rokar min shi ya yi hakuri, na yarda ma in yi sati guda kawai.” Salbiyya ta dago mata fuska hade da share mata kukan da take yi, ta ce “Kar ki wani damu diyata, dukkan komai naki za a iya hada su a cikin mintina talatin, ai ba wani abu ne mai wahala ba. Wannan hawayen naki ne ba na son gani. Ki daina idan ba so kike ni ma in yi ba.” Halimatu ta yi shim da kukan da take yi, amma fa ba ta daina hawaye ba. “Ki je ki yi naf‘lla rakaa biyu, ki gode ma Allah da Ya nuna miki wannan ranar. Ki yi addua ta zaman lafiya da zuria mai albarka. Ni kuma yanzun nan zan saka a hada miki komai. Kar ki damu kin ji diyata? Don Allah ki daina asarar hawayenki.” 
Da Indo da duk wadanda ke wurin sai suka ji kaunar Salbiyya ta dada shigarsu. Tana son faranta ran kowa, har cikin zuciyarta. Hakazalika tanadaukar dan wani tamkar nata. Musamman kuma Saadiyya da ta ga yanda mahaifiyarta ke kararta. 
Tun biyu da rabi mai martaba ya fara gargadarsu, don shi kam ya tsani a saba lokaci. Sanin hakan ya sa suka gama kikkimtsa komai, ya zamana jiran lokaci kawai suke yi. Uku na cika aka fito da amarya. Kamar yanda mai martaba ya mallaka ma Hafsa mota a lokacin aurenta da Yerima Bukar, haka yanzu rna ya mallaka ma Gimbiya Saadiyya tata motar, kirar anaconda kalar siminti. A gaban motar aka kawo ta, Salbiyya da kanta ta bude mata baya ta shiga, sannan ta wuce a motar da ita kuma za ta shiga. Ba ta san cewa yana cikin motar ba, sai dai kamshin turaren nan nashi da ta san shi da shi 
tun tsawon shekaru goma sha biyar bai sauya ba. Shi ne ya dakar mata hanci, ba tare da ta sani ba, ba kuma tare da ta shirya ba ta dago kanta daga rufen da yake a cikin alkyabba, ta kalle shi. Ba ta sani ba cewa shi din ma ita yake kallo, sai suka hada idanuwa. A lokaci kadan suka nemi rasa nutsuwarsu. Wata irin soyayya ce suke majunansu mara misaltuwa. Ta gaggauta sauke kanta saboda kunyarshi kuma da ta ji. Ba su san sadda aka tada mota ba. Duk daga musu hannun da al’umma ke yi ba ma su san ana yi ba. Sun yi nisa a shaukin kaunarjunansu. Hannunshi na hagu da ke kusa da ita ya sa ya riko nata na dama. A hankali yake wasa da yatsunta, yana dan mummurza su cike da bege da kauna. Ba ta yi kokarin kwacewa ba, sai dai ta kasa sake dago fuskanta saboda kunya. 
“Marigayiya…”
Taji ya fada cikin wata irin murya da ba ta san shi da ita ba. Sai taji wani irin yarrrr! Tsigar jikinta ta tashi. Murmushi ta saki daga inda kan nata yake a duke. 
“Gimbiya Saadiyya amarya.” 
Ta sakeji ya furta kasa-kasa. Da ma can haka yake, ba wai ga ita kadai ba, haka halinshi yake kasa-kasa yake magana. 
“Naam” Ta fada ita ma can ciki. “Kin ga al’amarin Allah k0?” Ta daga kai. “Ina fatan kin yi wa Allah godiya da wannan al’amarin naShi. Idan har kinyi din zan so ki dago kanki ki kalle ni, ki yi mini murmushin nan da na dade ban gani ba. Murmushin da na cire ran sake ganin shi har abada.” 
A , Ta danjanye hular alkyabbarta, ba tare da ta dago kan nata ba ta sakar mishi murmushin da ya yi silar lotsawar kumatunta. Kina nan da kyanki Gimbiyata. Babu abun da ya sauya daga gare ki face kyau ma da kika kara. Ina kaunar ki sosai. Ina matukar kaunarki Gimbiya Saadiyya.” 
Kunya ba za ta bar ta mayar mishi da martani ba. Sai dai kwayar idanuwanta da yake kallo sun tabbatar mishi da haka. Ya ga kaunarshi sosai a cikin idanuwanta. 
Sai da dare bayan isha sannan suka isa Kubaisu. Kai tsaye aka isa cikin masarautar Kubaisu, aka doshi bangaren da aka kawata na Yerima Abu Sufyan. 
Tun shigowar su aka fara buga tambari, mawaka da makada suka hau aikinsu. Wasu suka tsaya a inda suke, wasu kuma suka bi bayan motar su Yerima Abu Sufyan. Da gudu kuyangu biyu suka doso motar. Gefen da Halimatu take suka nufa, suka yi tsaye 
jiran izinin Yerima Abu Sufyan. Kafln fadawa su zo su bude mishi kofa harya bude, shi kam ba irin mutanen nan ba ne masu bakin mulki. Ganin ya bude tashi ya sa daya daga Cikin kuyangun ta bude kofa. Ciki girmamawa ta rusuna, ta ce, 
“Barkanki da isowa masarauta mai albarka. Muna miki lale marhaba da shigowa tsatson Sarki Abdurrahmanu. Takawarki laflya Gimbiya diyar sarki jikan Sarki, matar yeriman kirki.” Dayarta karbe da “Sassanyen ni’imtaccen kamshinki kadai ya tabbatar mana da nagartarki Gimbiya Saadiyya. Hakika munji labarin kyawawan halinki tun kafln ki iso. Muna miki fatan alkhairi. Sannan muna fatan kin shigo da kafar dama.” Tana kaiwa nan dayarta nemi ci gaba da magana, da hannu Yerima Abu Sufyan ya dakatar da ita, yace, “Ba ta son yawan magana, sannan kuma ta gaji. A shiga da ita ciki a yi duk abin da ya dace.” “An gama ranka ya dade.” Shi ne abin da Bintu ta fada bayan ta rusuna. 
Cikin jin nauyi Halimatu ta zuro kafarta waje ta flto. Ta dan dago fuskanta saboda yadda alkyabba ta rufe mata fuskar ba za ta iya ganin hanya ba. Bintu ta yi gaba, Shatu kuma daga baya. Sai kuma makada suka raka su har bakin kofar shiga gidan, sannan suka ci burki anan suna ci gaba da kade-kadensu. “ Babu abin da ba a zuba ba na more rayuwa a cikin gidan. Komai na zamani ne tamkar ba gidan sarauta ba. Bedrooms guda uku ne kowanne an kawata shi da gadon waje. Sai parlor biyu, daya babba sai dayan kuma matsakaici. Babban ya sha kujeru royal kalar maroon amd gold. Dayan kuma kirar Dubai kalar pink. Sai babban kitchen mai hade da store wadatacce shi ma an cika shi. Sannan daga baya akwai mi mai cike da kayan more rayuwa, ciki har da injinan motsajiki. Bedroom mai kalar golden aka kai ta, bayan ta zauna a bakin gado Bintu ta tsugunna har kasa ta ce, “Zan hada miki ruwan wanka ki gasajikinki ranki shi dade. Na san za ki bukaci haka. Kun kwaso gajiya.” Kai kawai Saadiyya ta daga musu. Ita kam wani iri takeji, ganin komai take yi tamkara mafarki. Bayan Bintu ta hada mata komai ta dawo ta fada mata. Ta ce su flta kawai sujira ta a parlor za ta neme su idan tana da bukatan wani abu. 
Alkyabbarta ta fara cirewa, sannan ta duba kan wata drawer ta kusa da toilet, towels ne kala kala ta dauki daya, ta cire kayan jikinta ta daura towel din sannan ta nufl wanka. Har da alwalla ta yi ta fitO. 
Ba ta wanI san kan dakln ba bare ta neml Inda kayan barc: suke ta saka. Sal kawal ta mayar da najikinta, ta duba kan mirror turaruka ne kala kala da body sprays da roll on. Ta shafa turare a kalla ya kai kala goma ko sha biyu, sannan ta hau kan daddumar sallan da ke shimfide har da babbar hijabi a kai. 
Bayan ta gama sallah ta yi zaune a daddumar tana tunanin duniya. Ta jima a haka shiru, ta ji duk ba dadi sannan ta mike, da hijabin ajikinta ta koma falo wurin su Bintu ta zauna. Suna ganin ta duk suka rusuna sunajinjina mata. “Sannun ku fa. Fatan na same ku latiya.” Ba su yi mamakin ganin rashin girman kai irin na Saadiyya ba, domin kuwa sun san labarinta tun ba yanzu ba. Sai dai abu daya ne kawai yake daure musu kai, wato yadda aka kawo Gimbiya Hafsa a baya, da kuma yanda ‘yar uwarta take. Kowa dai da irin halinsa. Suna zaune suna mata hira bayan sun gabatar mata da kansu, su ne hadimanta, sai ga Yerima Abu Sufyan ya shigo, biye da shi Shaheed ne rike da manyan ledoji sai sakin faraa suke yi. Su Bintu na ganin shi suka mike, “Sai da safe ranki shi dade. Ga wurin kwananmu can gaba kadan, idan kina da wata bukata kodayaushe ne ki buga kararrawar nan ta gefen gadonki, in shaa Allahu wata cikinmu za ta zo. Mu kwana laflya.” “ Da murmushi Halimatu ta ce, “To na gode sosai Bintu da Shatu, sai da safe.” Yerima Abu Sufyan ya kalle ta da faraa ya ce, “Ka ji ‘yar gayu har ta san mutanen gidan ma.” Shaheed ya yi dariya sosai, “To tun da ka barta ita kadai ai dole su ne kawayen hirartata.” Ya dan bata fuska cikin wasa, “Wato dai kana neman ka zuga ta wai na bar ta ita kadai ko? Babu komai, zan rama wurin uwar gida, gobe zan je in maka zuga ta hana ka abincin dare.” Ita kanta Halimatun sai da ta yi dariya. Wurin zama suka nema, Yerima Abu Sufyan ya zauna a kusa da Gimbiya Saadiyya, shi kuma Shaheed ya zauna dan nesa da su. Ya fara da sallama da yi wa Manzon Allah SAW salati, sannan ya hau yi musu nasiha sosai, tare da fatan alkhairi sannan ya mike. “Ni zan tafl. Allah Ya ba ku zaman lafiya Yerima da Gimbiya. Ina fatan nan da watanni tara cif mu dawo suna.” Kunya Halima taji ta sadda kanta kasa. Yerima kuwa hannu ya ba Shaheed suka gaisa sannan ya raka shi har bakin kofa, ya ce da shi ya gai da iyali, ya dawo. Hannu ya mika mata ta dora nata a ciki, sannan ta mike tsaye. “Shiga ciki kijira ni in kawo miki abinci.” Babu musu kuwa ta shige, don ita kam wani irin nauyinshi sosai takeji. Kitchen ya shiga ya dauko plates guda biyu sai cups biyu, ya dauki ledojin da Shaheed ya ajje sannan ya shiga ciki. Ledan farko gasasshiyar kaza ce kala biyu, da gashin injin, kazarturawa, sai kuma kazar Hausa da aka ma gashin gargajiya an bade ta da yaji. Ya dora kowacce a kan plate. Sai kuma natural drink, mixed fruit ya zuba a glass cups guda biyu. 
“To ga abinci ranki shi dade. Ki ci sannan mu yi sallah.” “Ba na jin yunwa ranka ya dade.” Tun haduwarshi da ita yau sai yanzu maganarta mai tsayin haka ta shiga tsakaninsu. Sai ya kwaikwaye ta cikin dariya. “Ba na jin yunwa ranka ya dade. Ji be ta k0 ma kunya babu wai ba ta jin yunwa. Tsakaninki da Allah duk yau me kika ci?” Shiru ta yi tana wasa da yatsun hannunta. “You see ba That’s means babu abin da kika ci. Ni bari in ba ki da kaina to.” 
Da kanshin kuwa ya hau ba ta, yana ba ta yana ci har suka koshi. Ya ba ta lemun ta sha sannan shi ma ya sha nashi. 
Daga nan suka yo alwalla, ya ja su nafula rakaa biyu. Bayan sun gama ya mata tambayoyi game da tsarki, dukkanin tambayar da zai mata sai ta ba shi amsa. Ya jinjina mata sosai. “Madallah da ke Gimbiya Saadiyya. Allah Ya yi miki albarka.” “Ameen.” ta fada kasa-kasa. “To sai kwanciya ko?” Ta daga mishi kai bayan ta mike. Kan gado ta nufa, shi kuma sai da ya sauya kaya, ya saka jallabiya ya feshe ta da turare sannan ya kashe wutar dakin. 
“Kin gaji k0?” “ Ya fada kasa-kasa bayan ya rike hannunta a hankali yana wasa da yatsunta. Ba ta ba shi amsa ba ta yi shiru, ya ce, “Ba ki gaji din ba ke nan. Ma shaa Allahu. Haka nake so ai.“ Da sauri ta ce “Uhm uhm fa Yaya, wallahi a gajiye nake sosai.“ Dariya ya yi sosai, ya ce, “Zan cire miki gajiyan ne ai.” A hankali wasan da yake yi da hannunta ya fara yin nisa, ya jawo ta a jikinshi tam, ya hada har kirzunansu na guganjuna, yanajin bugun zuciyarta itma tana jin nashi. “A yau cike nake da farin ciki Halimatu. Har ma ban san yadda zan misalta shi ba. Wallahi ina tsananin kaunarki. Ina son ki sosai.“ Kamar daga sama yaji ta ce, “Hakazalika ni ma ina kaunarka sosai Yaya Yerima. Wallahi da dukkanin zuciyata nake son ka.” Bai san sadda ya saita bakinshi da nata ya hada su wuri guda ba. Ya hau yi mata wani irin kissing da takejin shi tamkar zata zauce ba. Daga nan kuma sai kidan nasu ya sauya salo. Ya hau aika mata da sakwanni masu wuyar fadi, tun yana yi ba ta mayarwa har dai ta sadakas, ta fara mayar da martani. 
Sun raya darensu cike da kaunarjuna. Sun shayar da junansu zuma, ba tare da ya wahakar da kanshi ba, ba tare da ita kanta ya wahalar da ita ba. Shi da kanshi ya gyara ta, sannan suka kwanta barci mai cike da farin ciki da nishadi. Da asubah ya tada ta da kyar ta iya tashi saboda barcin da yake idonta. Shi ya nufi masallaci ita kuma ya bar ta tana alwalla. 
Washe gari da misalin karie goma na saf’lya dangin amarya suka shigo bangarenta. Hafsa ce gaba da wasu daga cikin dangin Indo. Ita kam Salbiyya ta ce ba za ta iya shigowa gidan diyarta ba. Tana can masaukinsu da ita da wasu daga cikin mutanensu. 
Hafsa da kanta ta ciro ma Gimbiya Saadiyya kayan da zata saka, saboda walimar da za a yi ta safe, anjima da yamma kuma za a sake yin wata. Wani irin material ne mai cike da duwatsuna masu kyau, sai alkyabba mai tsada. Babu wata kwalliya a fuskan amma ta sha kyau harta gaji. Daga nan suka rankaya filin walima. 
A nan Gimbiya Saadiyya ta ga kauna iya kauna daga wurin Fulani Maryama. Ta nuna mata gata tamkar diyarta ta cikinta. Da karfe daya da rabi na rana aka gama. Sannan ana yin laasar kuma ta canza wani dressing din suka nufl fada, inda 2a a yi wani sabon shagali. Ta safen ta mata ce, ta yanzu kuwa ta duka kowa ce. Wasu irin kawatattun kujeru ne aka ware ma Yerima da Gimbiya suka zauna. Mai manaba ya yi bayanin godiya da kuma murna, sai fatan kowa ya koma gidanshi lafiya. Daf da magrib aka tashi. a 
Da dare Mai manaba ya nemi Hafsa da Yerima Bukar. Ya musu nasiha sosai sannan ya mishi fada game da Uwani. shi kanshi ya yi nadama a yanzu, domin kuwa ya gano cewa duk wani tuggun da ake yi daga Uwani ne. In da a ce babu ita da tuni Jiddah da Hafsa sun shirya. Don haka ya ma Mai martaba alkawarin zai ba Uwani last warning, idan har ba ta canza halinta ba da kanshi zai sauwake mata. 
“Haka nake son ji. Sai batun Jiddah, don Allah Bukar a kula da ita sosai, ka ga marainiya ce. Kaji tsoron Allah, ka kula da iyalinka, ka daina zaluntarsu, wallahi dukkan abin da kake yi babu wanda ba ya dawo mini. Kai ba yaro ba ne ba, ka san abin da kake yi, don haka ba ka 
bukatan sanarda kai me za ka yi. Sai dai kawai ka sani cewa Allah yana ganin ka. 
Ga amanar Jiddah nan Hafsa, kin ga yanzu ta zama lalurarra, a daina tuna abin da ya wuce. Na tabbata ita kanta a yanzu ta ga kina kula da ita dole za ta bi ki ku zauna latiya. Ku ci gaba da hakuri dajunanku. lta kuma Uwani idan har ba ta daina ba kai tsaye kizo ki fada mini. Na san maganinta.” Nasiha sosai mai manaba ya musu, sannan suka mike suka koma bangarensu. shayeshayen dai kam zai yi wuya ya bar su. Domin kuwa ya zam addicted da abun. Amma kam ya kudura a ranshi zai ci gaba da kyautata ma iyalinshi. Sosai ya nadama a ranshi. Gimbiya Saadiyya in banda shagwaba babu abin da take yi. Shi kuwa sai faman ririta ta yake yi. Abu kadan ya tambaye ta lafiya? Nan kuwa tsabar shagwaba ne kawai. Dayan shaken takwas 
Abun mamaki, a cikin shekarun nan Gimbiya Saadiyya ta tara zuria, domin kuwa haihuwarta hudu, yara biyar saboda mst born dinta twins ne. Kaman za ta yi kuka ta ce, “Don Allah Yaya Yerima kar ka ce min a’a. Ka taimaka mini mu je a cire cikin nan. Wallahi ba zan iya ba ni kam.” Bakinta ya kama ya murje har sai da ta saki ‘yar kara. “Ji wani kuma salon muguntanka don Allah. Ni fa am serious gaskiya ba zan iya ba. Haba gwarnan na wannan ai ya fi kowanne. Ko fa yaye Sadiq ban yi ba kuma wai wani ciki. Yaya zan yi da shi?” Cikin seriousness ya ce, “Ki daina fadan haka Gimbiyata. Allah’n da Ya ba ki cikin Shi zai ba ki yanda za ki yi da su. Ki tuna cewa wasu suna can suna nema amma ba su samu ba. Ga dai Yaya Bukar can, har yanzu shiru har ma sun hakura. Me zai hana mu gode wa Allah da wannan karamcin da Ya mana? Yanzu ina Sadiq din yake? Ba yana wurin Hasna da Husna suna wasansu ba? Kin ga ai sai ki gode ma Allah Ya ma ba ki masu rainon.”Shiru ta yi tana gasgata magananshi. “Haka ne Yaya. Allah Ya raba ni da shi laflya to.” “Yauwa kece fa Matata kuma Gimbiyata. Ameen ya Rabb. Yanzu dai me zan samu kafln in flta?” 
Bakinta ta dora a nashi, duk ya sakankance ya ji tana kissing dinshi sai ya ji ta cije mishi lebo a hankali, sannan tajanye fuskanta tana dariya. “Na rama murje min baki da ka yi.” 
Ta koma bedroom dinta da gudu ta rufe ta bar shi sai dariya yake mata, sannan ya flce. Zama ta yi a bakin gado tana lekenshi ta wondow, sai wani irin kaunar mijinta ta ji ta dada shiga a zucuyarta. Watansu goma cif da aure ta haifi twins dinta duka mata, kyawawa masu kama da ita. Su ne Husna da Hasna. Suna da shekara biyu ta ham Ahmad, bayan wata shekara biyun ta haifi Aisha, daga Aisha ta haifi, Sadiq, yanzu kuma ta je asibiti an tabbatar mata da cewa tana da juna biyu. Ta shafl cikinta cike da kauna ta ce, “Ina kaunarku zuriata, Allah Ya raya min ku Ya albarkace ku. Allah Ya bar ni da mijina har karshen rayuwarmu.“ A Garden ya samu yaran nashi su duka biyar, sun yi grouping kansu, nan Hasnah da Husnah sun hau lilo da Sadiq, sai can kuma Aisha, da Ahmad zaune kan kujeru irin mai benci suna karatu. Yerima Abu Sufyan ya kalle su, sai yaji wata irin kaunarsu ta shige shi. Ya matsa kusa da su Hasna. Da saurinsu suka shigejikinshi, Sadiq sai yare yake yi yana dariya, sai da Yerima Abu Sufyan ya dauke shi sannan ya koma wurin su Aisha. 

“Yaran albarka karatu ake yi k0?” 

Husna ta kwakkwabe fuska, “Wayyo Dady mu ba ka ce mana yaran akbarka ba. Kuma muna yin karatu ai Momy ce ta ba mu rainon Sadeeqee“ Dafa mata kai ya yi ya ce, “Yaran albarka ne ai ku dukanku. Aci gaba da karatu sosai. Allah Ya yi muku albarka.” “Ameen Dady. Idan na yi na daya this term ai za ka kai ni gidan su Momy wurin Mama da Goggo in yi hutu ko?” 
Hasnah ta fada tana murmushi. “In shaa Allahu kuwa. Just ku ci gaba da mayar da hankalinku. Ke da Husna zan kai ku ku yo hutu. Aysha da Ahmad kuma in kai su wurin Ammi Hafsa.” “Yeeeeee! We love you Dady” Suka fada su duka hade da shigewa cikinjikinshi. 

HAPPY FAMILY ke nan. Me ya rage? Ina ga mun dinke komai ai. This is the end of our long story. 

About Ismail

Check Also

GIMBIYA SA,ASIYYAH CHAPTER 41

GIMBIYA SA,ADIYYAH CHAPTER 41 Da karfi Kursiyya ta mike tsaye, tamkar wadda aka kwalla ma …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *