[Advertisements⬇️]

GIMBIYA SA,ADIYYAH CHAPTER 42 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GIMBIYA SA,ADIYYA

CHAPTER 42


A cikin wannan halin da suke sai ga Indo ma ta mike zaune. Sai rarraba ido take tana kallon sarautar Allah. Bata san abin da yake faruwa ba, sai dai ta ga yan mata biyu rungume da junansu.
Rabonta da Gimbiya Sa,adiyya tun tana ‘yar watanni uku. Ba za ta iya cewa ga taba, hasali ma su duka biyun bata san ko su waye ba.
Tana daga idonta daga can gefe ta hangi Kursiyya sai mazurai take yi. Ga hannunta ta ko’ina jini ke fita, duk ta ciccije kanta. Ga kuma Zabba’u da idanuwa suka gama kumburewa dan kuka.
Cikin sanyin murya ta ce, “Fulani Kursiyya…” Tana kokarin mikewa ta isa gare ta. Da sauri mai martaba yasha gabanta. Yace. “Wannan muguwar matar sam bata cancanci wata maganar arziki ta hada ku ba. Abu mafi kyautuwa ma sai dai idan Allah ya isa za kiyi mata, bisa ga zaluntarki da tayi keda diyarki.” “Ban fahimta ba.” Indo ta fada kasa-kasa tana kallon mai martaba.
“Na gaza gane abin da yake faruwa. Ni dai a sani na barci na kwanta a dakina dazu, gashi kuma yanzu na farka na gan ni a dakin da ban san ko na waye ba. An canza shi zuwa ginin zamani tamkar ba a masarautar Bilbah din dana sani ba. Don Allah ku fitar dani daga duhu Mai martaba ya ce, “Ba barci kika yi ba Indo. Wannan makirar matar ce ta sa aka tsaface ki, yau kimanim shekaru talatin da daya ke nan, kina a tsaye kikam ke ba mutum ba keba gawa ba.
Indo ta zabura da karfi har tana neman faduwa. “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Mai martaba da gaske kake ko da wasa?” “Ba fa komai kika ji ba Indo, kadan ke nan daga sharrin Kursiyya da aminiyarta Zabba‘u.” Duk sai jikin Indo ya yi Iakwas, ta matsa inda Kursiyya take, cikin kuka ta ce, “Me na miki Kursiyya? Me nayi miki da na cancanci wannan zaluncin daga gare ki? Me na tsare miki a rayuwa?” cikin halin ko’inkula Kursiyya tace, ‘ “Babu fa abin da kika yi mini, kawai tsanarki nayi. Na ji bakin ciki ne da kika samu juna biyu, bayan jimawa da aurenku baki samu ciki ba. Na kuma tabbatar cewa abin da zaki
haifa sosai mai martaba zai so shi. Don haka naje na asirce abin da kika haifa, tazo da bakinjini tun tanajinjirarta. Ke kuma aka mayar dake mutum mutumi. Karfa ki zaci kin min wani abu ne. Kawai dai kiyayya ce. Kuma har yanzu na tsane ki. Na tsane ki Indo ke da ‘yarki.” In banda sunan Allah babu abin da Indo ke fadi. Su mai martaba kuwa tsananin mamakin Kursiyya ne ya cika su. “To ina ‘yata take?” Ta fada bayan ta juyo ta kalli mai martaba. Da hannu ya gwada mata inda Saadiyya da Hafsa suke. Cikin murmushi yace “Canki ‘yarki a cikinsu.‘ Ta matso kusa dasu. Hannun Hafsa ta fara rikewa, taji shi da dumi sai dai ba irin sosai din nan ba. Ta saki ta kama na Halimatus-Saadiyya, a nan taji wani irin dumi mai matukar dadi, ta shiga wani irin yanayin data nemi duk wata damuwa ta Kursiyya ta rasa ta. Ta jawo ta a jikinta ta rungume, suna jin bugun zukatan junansu. “Yanzu Halimata ce ta girma haka? Allah sarki!“ Sai kuka sosai. “Nice Mama, bayan shekaru goma sha biyar dana dauka a cikin kwalbar sihiri, har an cire tsammani dani duk an zaci na mutu.‘ lndo ta kara kankame diyatta, cikin kuka ta ce,
“Mu kuma a haka tamu rayuwar tazo mana. Allah sarki! Ashe da rabon zamu sake ganawa Halimatu.‘
Ta kara fashewa da kuka. Mai martaba yayi gyaran murya sannan ya kalli Waziri yace,
“A tafi da wadannan mutane a kai su sijin, a tabbata boyayyen sijin aka shigar dasu, dakin duhu nake magana. Aajje min su kafin in gama nazartar hukuncin da yayi daidai dasu. Amma kafin nan…”
Ya kalli Kursiyya fuskanshi babu alamun annuri ko kadan, yace, “Kursiyya, ina so dukkanin wadanda ke wurin nan su shaida, na sake ki saki daya, biyu. saki uku! Sannan ki sani, ba zan taba yafe miki ba dukkanin abubuwan da suka rinka faruwa. Kin mayar dani tamkar ba namiji ba. Kinjuya ni tamkar yadda uwa kejuya danta. Kin mayar dani wani sakarai alhali ni babban Sarki ne da ya yi suna wurin jarumta. Sannan a karshe kin saka na karya record, na rabuwa da mace alhali babu wannan tsarin a masarautar nan. Sai dai kuma rashin tsarin ba shi ne zaisa naki amfani da fadar
mahaliccina ba. Halal ne saki idan ta kama.
Don haka Waziri a tafi dasu. Don Allah kar a bar su inda zasu samu sassauci. A kai su inda za a rinka basu abinci sau daya tak a wuni. Har sai sun yi kwana biyu a ciki, kafin nan na yanke musu hukunci.” Da hanzari Waziri yace, “An gama ranka shi dade.” Kursiyya tayi kememe, tamkar bata da wata damuwa. Da hannunta da yakejina-jina ta ce,
“To sai me? Nace sai me zai faru Sarki Sani? Ina so ka sani, har abada ba zan taba yin
nadamar abin dana aikata ba. Har yanzu ina nan kan bakata, idan yanzu zan samu dama
sai na kashe Indo da diyarta Halima. Tsanarsu a cikin jinin jikina take. Wallahi na tsane su. Kuma bana nadamar abin dana aikata a gare su…“
Tun kafln ta rufe baki Waziri ya dauke ta da kyakkyawan mari. Dafe kumcinta tayi tana kallon shi. Sai ta ga abun tamkar a mafarki. Wai yau kaskantattun mutanen data gama renawa ne aka samu wanda ya karya record din rayuwarta. Tun data girma tayi wayo babu wanda ya taba marinta, wai yau Waziri ita ya mara. “Ni ka mara Waziri? To ina mai tabbatar maka da sai ka gane cewa kai karamin matsiyaci…‘ Ya sake wanke ta da mari a daya kumcin. Cikin huci ya ce. “Kina Kara cewa ko uffan ina kara dauke ki da wani. Dama abin da ya sa kika gana raga miki kawai don kina matar mai martaba ne. A yanzu kuwa ya yanke alakar da take tsakaninku. Don haka a matsayina na wazirin Sarki ina da damar daukar miki mataki idan
kika nemi kauce hanya.” Mai martaba ya jinjina mishi hannu, yace, “Baka taba burge ni ba kamar yau Waziri, ka ci gaba da saita ta, ka gyara mata zama idan ta kawo maka wargi. Ku tafl, na tsani ganin ta, na tsani jin ko muryanta.” Waziri ya hambare ta, tuni Zabba’u ta mike don ita kam a tsorace take sosai. Jikinta sai rawa yake yi. Duk iskancinta ba ta da taurin kai kaman Kursiyya. Ita kanta mamakin halin Kursiyyar take yi.
Duk abin nan da yake faruwa a kan idon Hafsa. Sosai taji babu dadi, domin kuwa komai zai faru uwa uwa ce. kuma dole zata damu da halin da uwarta za ta shiga. Sai dai kuma abin da ta yi imani da shi shi ne, ba za ka taba shuka masara ba ka girbi shinkafa ba. Don haka munanan halayenta na baya ne duka take girba, duk da dai cewa ba ta gama sanin kaf abubuwan da uwarta ta aikata ba. Kai tsaye Waziri da Khalili suka nufi dakin duhu. Babu kowa a cikinsa. saboda da ma can sai laifin mutum ya tsananta ake kai shi. Ko dai wanda ya yi kisan kai, k0 kuma fyade, ko kwartanci ko kuma makamancinshi. Kamar shi ne matsayin babbar prison ta garin Bilbah.
Da kafiya irin ta Kursiyya, a nan ma sai da ta sha duka sosai sannan ta shiga. Daga bakin kofa Waziri da Khalili suka tafi, bayan sun garkame dakin da katon kwado sun tafi da mukulli.
Da warin kashi suka fara cin karo. Ga shi duk inda zasu taka kashi ne, saukin ma duk ya bushe saboda an jima ba a kawo kowa a ciki ba. Cikinta Kursiyya ta fara ji ya ce kulululu, kafin ta yamutse fuska tana tunanin ta yadda za su
yi zaman wurin nan harsu kwana a ciki. ”Kin cuce ni Kursiyya, har abada ba zan taba gafarta miki ba.‘ Kursiyya ta dago kai ta kalli Zabba’u cikin mamaki ta ce, “Zabba’u yau ni ce kike kira da Kursiyya kai tsaye? Ni, Zabba’u?“ Zabba’u ta daga mata kai bayan ta shanye kukan da take yi. “Ban taba ganin azzalumin mutum kamarki ba Kursiyya. Sau da dama idan kin kawo wani abu kin ce mu yi ina ce miki ba zan iya ba. Amma sai kin san yadda kika yi amfani da kambun bakanki kika lubbace ni har na amince na yi. Yau ga shi a halin da kika jefa mu. Abu mafi kaskanci a rayuwa, an kawo mu inda ake kawo kasurguman masu laifl. Kodayake mu ma ai kasurguman masu laifin ne. Gwara ma kowa da mu.” ‘ Kursiyya ta falla ma Zabba’u marin da sai daya gigita ta. “Kar ki karisa kular da ni Zabba’u. Ayadda nakeji na a nan zan iya daukar miki kowanne irin mataki in dai ba ki kiyaye ni ba, kinji na fada miki.” Hannunta dafe da kumci ta ce,
“Ba zan fasa fada miki maganganu ba Kursiyya. Saboda sam ba ki cancanci a bi ki da dadadan kalamai ba. Wallahi ke butulu ce. Kuma azzaluma wadda ba zata taba shakar ko kamshin AIjannah ba.” Kursiyya ta kyalkyace da dariya. 
“To sannu wadda za taji kamshin Aljannah. Na ce sannu Zabba’u ‘yar aljannah. Ke ai naga zaki shiga ko? Tun da muke aikata mugun abunmu na taba saka ki dole? Na ce na taba shake ki na ce miki dole sai kin yi? Sa yau da kika ga tamu ta kare, alkadarinmu ya kare sai ki nemi jangwama laifl a kaina ko? Ki kiyaye ni kinji na fada miki.” 
Zabba’u ta kara fashewa da kuka. Tace”Ba zan taba kiyayarki ba Kursiyya. Kiyi duk abin da kike ganin za ki iya.” Kursiyya idonta na kan ballalliyar tagar da akajingine can nesa kadan da su. Ta saki murmushi hade da neman matsuguni ta tsugunna, ta hada kanta da guiwa sai tunanin rayuwa take yi Zabba’u ta bubbuga ta tace. “Kin ji tsoro ke nan. Ashe ma karyar iskanci kike yi tun da har magana ta kare miki.” 
Banza ta yi da ita ba ta ce komai ba. Hakan ya sa ita ma Zabba’u din ta gaji ta nemi wuri ta zauna. 
Kamar yadda Kursiyya ta kyala idota hango mabugi, haka ita ma Zabba‘u ta kyala ido ta hango mabugi. Kowannensu burinshi ya samu galaba a kan daya. ya kashe shi. Saboda a yadda sukejin kiyayyar junansu a yanzu, tamkar dama can basu kaunarjunan nasu. Sun jima a haka har kusan awanni biyu, har barci ya dan dauki Zabba’u. 
Bata ankara ba taji saukar karfe a bisa kanta. Ta mike da niyyar ta samu ta kwace amma Kursiyya taci karfinta. Hakan ya sa ta dafe kanta, ta duke hade da lubbatar Kursiyya da sauri ta dauko dayan barin karyayyar tagar, ita ma ta kwada ma Kursiyya shi a ka. A nan take fadan makamai ya kaure a tsakaninsu, kowaccensu dai fatanta shi ne tayi masara a kan ‘yar uwarta. 
Sun jima suna yi, duk suka yi jina-jina, suka majunansu rauni, kafin Kursiyya ta harzuka. Da karfi ta kwada ma Zabbau karfen a fuskanta. A take ta fadi a wurin hade da fasa ihu mai karfi,jini ya hau fita ta hanci da bakin Zabba’u. 
Murmushi Kursiyya ta saki, alamun ta yi nasara. A karo na karshe ta buga karfen da karfl a kan Zabba’u, wanda ya yi daidai da tsayuwar numfashinta. 
Tabbatuwar ta mutu ne ya sa Kursiyya ta fasa wata irin dariya da karfi. Ta daga hannunta sama tace, “Ke din banza Zabba’u! Me akai aka yi ki karamar kwaruwa data koyi tarin abubuwa daga gare ni? Da ma na fada miki. zan iya yin komai gare ki. Ga shi nan na gama miki aiki. Na tsayar da tsayuwar numfashinki. Sai dai wata bake ba Zabba’u. Nace sai dai wata ba ke ba. No more Zabba’u! No more Zabba’u in this World. Sai mun hadu a lahira karamar kwaruwa.”ma,aikata. Sai kuzo ku dauki gawarta, ni dai na gama aikina. In yaso ni ma din ku kashe ni, ko ba komai dai na cika burina. Kuma ko a yanzun nan Halimatu da lndo za suyi wautar zuwa wurin nan sai na kashe su da hannuwan nan nawa. Zan cika abin da ya yi saura na daga burikan rayuwata.” Ta kyalkyace da dariya, tamkar wata mahaukaciya. Da dare Waziri ya bada umurnin azo a kawo musu abinci, saboda dukwunin babu abin da suka ci. ‘yan aiken suna zuwa suka tarar Kursiyya sai barcinta take hankali kwance. Daga can gefe kuma ga gawar Zabba’u a baje, sai suka yi tsammanin ko ita ma barcin take yi. ‘ “Ke! Ke ku tashi ga abincinku idan kun ga dama.” Kursiyya ta bude idanuwa ta kalle su. Tace, 
“Ina fatan dai abincin na mutum daya ne kuka kawo. Saboda dayar dai gawa ce. Ka fada wa mai martaba da Waziri na kashe Zabba’u, su zo su dauki gawarta. Ni kuma su gaggauta raba ni da wannan dakin don na gaji.” Kai suka dora a ka idanuwa bude suna kallon ta. Har su mutu ba zasu taba ganin abun al’ajabi sama da wannan ba. Duk tarin laifukanta ta kara da kisan kai, kuma a haka take cewa azo a raba ta da dakin duhu. 
“Kuna mamaki ne? Ni dai ku bani abincina in ci don yunwa nakeji. ldan kun ba ni sai ku ruga ku sanar da sakona, kila kafin ku dawo har na gama cinyewa, sai a fitar dani din.” Ai abincin ma kwatsar da shi kasa suka yi tsabar mamaki. Da gudu kuwa suka bar wurin 
suka barta sai mita take yi wai sun zubar mata da abinci. “Ai na fada musu. ba na tsoron kowa ni kam. Aikin bur!” Taja dogon tsaki hade da murguda baki. Tana sauraren isowar mai martaba ne kawai, tana son ganin an yanke mata hukuncinta. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]