[Advertisements⬇️]

GIMBIYA SAADIYYA CHAPTER 43 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

GIMBIYA SAADIYYA


CHAPTER 43

Wayarshi ta dauki kara. Ko daya duba ya ga Sarkin Kubaisu ne ke kiran shi. Da sauri ya
dauko kunshe da sallama a bakinshi. “Wa alaikumussalam warahmatullah. Barka da rana ranka ya dade.” Sarkin Kubaisu ya fada da wani yanayi da kai tsaye ba za a iya bambance a cikin halin farin ciki ne ko na bakin ciki ya yi maganar ba. “Da girman kujerarka ranka ya dade. Ya gida ya iyali?” Sarkin Kubaisu ya ce, “Kowa da komai sai hamdala. Ina ta so in kira ka tun da sakon rashin lafiyar Kursiyya daya riske mu. To kuma mu ma anan sai aka samu rashi, mahaifiyar Jiddah abokiyar zaman Hafsa ce ta rasu, mutuwar ban mamaki. Yanzu haka ita ma Jiddar babu lafiya, kamar dai ta samu tabin kwakwalwa ma.” Da sauri Sarki Sani yace “Subhanallahi! Ashe abun har ya kai haka?” “Ya ma zarce haka Yallabai. Tabbas mun ga abun mamaki. Domin kuwa gawar mahaifiyar Jiddah ma bacewa tayi, k0 sallah ba a samu an mata ba. An dai tabbatarta mutu, kafin a zo kanta kuma babu ita. To dai ka san surutai irin na mutane, wasu ma sun ce wai da ma can ba mutum bace. Kuma babu wanda ya san asalinta, mahaifinta Sarki Jaheed a haka yazo da ita ba tare da wani takamaiman bayani game da ita ba, kuma har ya bata sarautarshi dafda zai rasu. An dai shaida mana tana da abubuwan ban mamaki a tattare da ita. Allah kadai ya san gaskiya. Mu yanzu ta kokarin ceto lafiyar Jiddah ma muke yi.”
Sarki Sani ya sauke ajiyar zuciya, yace, “Duk naku mai sauki ne ranka ya dade. Domin kuwa mu a nan mutum biyu da suka mutu ne suka sake dawowa da ransu. Gimbiya Saadiyya da mahaifiyarta Indo Aisha.” Sarkin Kubaisu ya zaro idanuwa tamkara gabanjuna suke. Yama gaza furta komai tsabar mamaki. Nan dai Sarki Sani ya hau zayyane masa kaf abubuwan da suka faru wadanda ya sani. Sai da suka yi wayar kusan awanni uku. Suna cikin magana sai ga Waziri ya zo a tsiyace, cikin haki ya ce, Mai martaba,tunda nake a rayuwata ban taba ganin mutum irin Kursiyya ba. Yallabai, ta kashe Zabba’u, kuma da kanta ta bayar da sako a fada mana.” Bai san sadda ya janye wayar da yake yi daga kunnuwanshi ba, ya mike tsaye ya ce, “Innalillahi wa inna ilaihi raji‘un! Ya Allah ka raba mu da irin zuciyar matar nan. Mata dai
kamar wata Shaidan? Ya Salaam! Yanzu ke nan Zabba’u gawarta ce ajje a dakin duhu?”
“Haka na samu labari ranka ya dade, ni ma kaina ban samu naje ba. Saboda hankalina a tashe yake inzo in sanar maka.” Mai martaba yace “Mu je maza kar ta kara yin wata barnar.” Waziri ya yi gaba mai martaba ya mara masa baya. Sai a sannan sarkin Kubaisu ya kashe kiran, yana jin duk abubuwan da suka faru, ya yi mamaki sosai.
Kusan mutum bakwai suka bi bayan maimartaba suka rankaya zuwa dakin duhu. Bayan an bude suka ga Kursiyya ta hada kanta da guiwa yunwa ta dame ta. Jin motsinsu ya sa ta dago kanta, ta saki murmushi. “Yauwa ko kufa. Ai gwara ku fitar da ni daga wurin nan ko na huta da warin kashi da fitsari, kuma na tabbata gawar Zabba’u ma na daf da ta fara doyi, saboda zafin wurin nan. Na gaji haba.” Kyakkyawan mari Sarki Sani ya dauke ta da shi. Ta dafe kumcinta tana kallon shi, ya sake dauke ta da wani. Ke din banza Kursiyya. Ke har kin isa ki kawo mini shashanci? Ba a yi ki ba. Wallahi sai kin raina wa aya zakinta. Sai kin san cewa dani kikeja.”
Ya kalli wasu karti mutum biyu ya ce, “A fltar da gawar nan a sallace ta. lta kuma wannan matar a shigar da ita can ciki inda ke da duhun sosai ta yadda k0 tafin hannunta ba za ta iya gani ba. Gobe za a yanke mata hukunci.” Ya flce daga dakin cike da takaici. Waziri sai da ya yi kwallo da Kursiyya ya harba ta can nesa sannan ya kara kwallarta harta kusa isa bakin dakin. “Tashi ki shiga da kafafuwanki na ce.” Wani irin tsoron Waziri take yi tun sadda ya mare ta na farko. Jiki na rawa ta mike ta shiga dakin da ke da wata ‘yar karamar window. Ya jawo kaca ya rufe dakin. Sai da ta tabbatar ya rufe sannan ta leko ta window din ta ce, “Mugaye azzalumai, marassa imani, duk sai na kashe ku daya bayan daya.” Ta yi saurinja da baya ganin yana neman matsowa kusa da tagar. Tafiyarshi ya yi ko waiwayenta bai sake yi ba
Daidaikun mutane suka sallaci gawar Zabba’u. Mai martaba kam ya ce ba dashi za a yi ba, da dama wasu sun ce ba za su sallaci gawar Zabba’u ba.
“Fulani Maryama, hakika a yau na gasgata, cewa ba komai da mutum yake so bane yake zama alkhairi a gare shi. Na yi tsananin fushi da dana mafl soyuwa a gare ni,Yerima Abu Sufyan. Duk a kan bai auri Hafsa ba. A lokacin babu yadda ke da shi ba ku yiba a kan in saurare shi ba amma na ki, sabodajin haushinshi da nake yi. Abu Sufyan ya fara fada mini hasashenshi a kan mutuwar Gimbiya Saadiyya, sai dai a take na taka mishi burki. Sai ga shi a yau din nan gaskiya ta bayyana.” Cike da mamaki Fulani Maryama ke kallon mai martaba Sarki Abdurrahmanu, tana tuna rabon da zancen Yerima Abu Sufyan ya shiga tsakaninsu an kusa shekara goma sha biyar, amma wai yau ga shi shi ne yake tado mata zancen da ta gama rufe babinshi. Kallon shi kawai take yi tana son sanim hakikanin abin da yake nufl. Na san za kiyi mamaki sosai, amma kafin komai ina mai neman gafararku ke da Abu Sufyanu. Sannan ina mai farin cikin shaida muku Gimbiya Saadiyya ta dawo da ranta, ba ta mutu ba…” “What?” Ta yi gaggawar tambayarshi bayan ta mike tsaye. “Bata mutu ba kamaryaya?”
“Calm down Fulani. Zan miki bayani dalla-dalla.”
Tiryan-tiryan ya zayyane mata kafyadda suka yi da mai martaba a waya. Duk sai taji jikinta ya yi sanyi, ta dada jin tsoron Allah sosai. Ta jinjina karfin hali da kazamiyar zuciya irin ta Kursiyya.
“Lallai wannan abu da ban al’ajabi yake. Kuma wallahi ranka ya dade, Yerima Abu Sufyan tun kafin taflyarshi ya ba ni labarin abubuwan da ya rinka gani duk ana nunar mishi da haka. To ni sai na mayar kawai ai tsabar saka ma ranshi abun da ya yi ne ya sa haryake ganin haka. Ashe kuwa da gaske ne. Ashe dai da rabon Gimbiya Saadiyya za ta zama mallakin Yerimana.” Murmushi ya saki Sarki Abdurrahmanu. Ya ce,”Yi maza ki kira shi a waya ki sanar da shi wannan gagarumin albishir. Na tabbata gobe ko jibi ki gan shi ya kamo hanya. Da ma already ina missing dinshi, ba ni da yadda zan yi ne kawai. Amma shekaru goma sha biyar ba nan suke ba. Ke gwara ke kin ziyarce shi har sau
uku. Ni kuwa na dauki fushi da dana a kan abin da yake da gaskiya kanshi.” Fulani Maryama tace, “Duk ka daina tashin abin da ya wuce ranka ya dade. Kai da kanka ma ya kamata ka kira ka mishi wannan albishirin.” Ya gyara zamanshi bayan yajawo wayarshi. “Tabbas abin da ya kamata in yi din kenan. Bari in kira shi.”
Ko da ya duba wayar sai ya ga ashe fa bai ma da lambar Abu Sufyan ta can kasar. Sai da ya ce da Fulani Maryama ta ba shi sannan ya kira.
Shi kam yana da lambar mai martaba, kiranshi na shigowa sai da gabanshi ya fadi, don bai san kuma abin da ya kira ya fada mishi ba.
Cike da karfin hali ya dauka da sallama a bakinshi. Cikin girmamawa ya gaida mahaifinshi, sannan ya yi shiru, yana sauraren abin da zai ce.
Kwance take bisa cinyar Hafsa, Hafsa na mata tsifar kai sai fira suke yi cike da kaunarjuna.
“Yaya Hafsa na ce ki bari Shamsiyya ta tsefe min amma kin ki k0?“ Hafsa ta yi murmushi bayan ta ja wani tsoron gashin. “Ni da kaina nake son na tsefe miki, kuma na gyara miki shi ki fito tsaf Gimbiya Saadiyya dinki. Ba ki ga yadda kan naki ya yi bane, duk ya duddunkule sai an bi a hankali. ldan ba haka ba ma za ki ji zaflnshi ne sosai.
“To sannu da kokari. Haka wankan nan ma da kika min ba kiji ba wani irin iska da nakeji
yana shigana ta ko’ina gwanin dadi. Kai, gaskiya tsafta ni’ima ce mai girma.” Hafsa ta sake yin wani murmushin. Ta ce, “Sosai ma kuwa. Yauwa, ina so na miki wani albishir, amma tabbas sai kin bani goron albishirin, don mai tsananin dadi ne da zai faranta miki rai.” Zaune Gimbiya Saadiyya ta mike ta kalli Hafsa, “Ki fada dai inji tukunna, gwargwadon muhimmancinsa, gwargwadon goronki.” Hafsa ta kama mata hannu ta rike, ta ce “Tun bayan da bakya nan har yau maganan nan da nake miki, Yerima Abu Sufyan na nan bai yi aure ba. Bala’in kaunarki da yake yi yasa har kasar ma ya bari baki daya.” Zaro idanuwanta ta yi sosai ta gagara fadin komai, sai wani irin yanayi take tunowa mai cike da farin cikinsu ita da shi.
“Yes, bai yi aure ba haryanzu Halimatu. Infact, tursasa shin da Mai martaba mahaifinshi ya yi kan lallai sai ya aure ni ya sa ya tafi ya bar kasar. A karshe kin ga sai Yayanshi aka aura mini. Auren da na gwammaci zamana a gida fiye da shi.
Na yi da na sani sosai a rayuwata Halimatu, da na sani mara misaltuwa. Wallahi na ga rayuwa, rayuwar da k0 makiyina ba na fatan ya yi irinta. Duk daga cikin abubuwan da nake girba ne na samu matsalan rashin haihuwa. lnaji ina gani sai dai daure min mahaifata aka yi saboda yawan bari da nake yi. Halimatu, duk daga cikin alhakinki ne. Alhakin muzguna mikin da na rinka yi a baya. Ga 
kuma uwa uba abubuwan da Ummana ta miki…” 
Da sauri ta dode ma Hafsa baki. Ta yi gaggawar share mata hawaye da ya ci gaba da sauka a bisa kumcinta. Haba Yaya Hafsa. Har rokonki na yi da Allah a kan ki daina tashin abubuwan nan da suka wuce. Babu wanda ya fi karfin kaddara. Ko Allahn da Ya halicce mu muna maSa laifi mu roke shi gafara Ya gafarta mana. Mu din waye da za mu gagara gafarta wa dan uwanmu? Ki bari don Allah in dai ba so kike muna fada ba.” “Na bari to.” 
Ta fada tana kallon Halimatu. “Yauwa ‘yar uwata. Ki yi murmushi in ga kyakkyawan hakorin zinarin nan na bakinki. Kin san fa ba karamin kyau ya kara miki ba.” Dukkansu suka yi dariya a wannan gabar. Sallama sukaji suka daga kansu a tare, ganin Adnan da Anwar suka yi sai sakar musu murmushi suke yi. Da gudun Halimatu ta isa gare su, ta kama hannun daya da hannun dama, sai ta kama hannun daya da hannun haggu. “Sannunku da zuwa ‘yan uwana. Hakika yau ina cike da farin ciki da murna. Ko ba komai family dina ya tashi daga asalin wanda na san shi mai cike da tashin hankali, ya dawo wanda muke sa ran kwanciyar hankali dawwamamme, mai dorewa a cikinsa.” 
Anwarya sakar mata murmushi cike da soyayya yace, “Muna fatan haka Halimatu. Duk ba ki ji ni ba, ganin komai nake yi tamkar a mafarki. Wata irin kaunarki nakeji na yawo a cikin jinin jikina. Ashe akwai ranan da zan so ki a matsayin ‘yar uwata? Ban taba gasgatawa ba sai ranan da kika bar mu. Duk sai muka tsani kanmu saboda rashin kyautata miki. Sai ga shi yau kin dawo gare mu, kin dawo gare mu Halimatus-Saadiyya.” Awannan karon har sai da ya hada jikinsu tsabarfarin ciki. Ba ta san sadda ta shige nashi jikin ba, tana jin wani irin farin ciki na sauka a kasan zuciyarta, yana ratsa jini da jijiyarta, farin cikin da har sai da ta yi kwalla. Isowar Hafsa gabansu yasa ta raba su. Ta ce “Ku ji min ‘yan uwa sun hadu za su manta dani ma tasu ‘yar uwar ce. To gaskiya ba za,a yi babu ni ba.” Adnan ma ya yi murmushi ya ce “Ni ma din gaskiya da ni za a yi.” Dukkansu suka rungumi junansu su duka hudun, sai dariya da murna suke yi. 
Salbiyya kuwa a dakin lndo ta fara yada zango. Bayan ta shiga ta same ta ta fito daga wanka, ta kalli gabas sai faman tunani take yi. Ba ta koji shigowar Salbiyyar ba sai dai taji ta tabo ta. Ta yi Firgigit ta kalle ta. “Ban taba mafarkin wannan ranar ba Sarkin fada. Ashe uwar fada za ta dawo ga mai martaba. Ashe dai lokacin tafiyarki bai yi ba.” lndo ta sakar mata murmushi hade da hawaye. “Mun ga rayuwa Salbiyya. Hakika babu karfi babu dabara face a wurin Allah madaukakin sarki. Akwai darasi mai matukar muhimmanci a rayuwata ni da diyata Halimatus-Saadiyya. Hakika idan aka samu wani marubuci ya dauki tarihinmu ya rubuta a matsayin labari, sosai zai yi tasiri, zai yi amfani ga mutanen wannan zamanin. Abu dai mai ban mamaki da al’ajabi.” Ajiyar zuciya Salbiyya ta sauke ta ce, “Hmmm! Lamarin dai duka bai yi dadi ba. Allah ya sa iyakar abin ke nan, ya dauwamar da farin ciki a cikin zuriar nan.” 
“Ameen.” Indo ta fada bayan ta share kwallarta. 


Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]