[Advertisements⬇️]

WATA SHARI'A CHAPTER 21 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WATA SHARI’A

CHAPTER 21
Hayaniya kotun ta d’auka baki d’aya sai cece_kuce akeyi, Alhaji Abu Abu kuwa mutuwar zaune yayi ji yake tamkar a mafarki ne, Barr. Sa’eed kuwa sai k’arema Gentle kallo yake yana mai tsananin jin haushinta, inda ace batayi maganar ba da yasan ta hanyar da zaibi dan lalata waccan maganar, amma kuma duka ta b’ata zancen.
Bubbuga guduma alk’ali yayi da k’arfi sannan kowa yayi shiru, ‘Salmah Abubakar kinsan ko me kike fad’i kuwa?”.
Cikin hawaye Gentle ta d’aga kanta tace ‘Tabbas a duk bayanan da YB yayi babu k’ari ko kad’an a ciki, Da gaske ni nasa ayiwa Ummimah fyad’e, ni nasa aka satomin k’annenta ‘yan biyu duk dan in guma mata, Ganin kamar hakan bai dameta ba yasa da nasa aka kashe k’anwarta d’aya daga cikin wanda aka sato, Na samu labarin halin da suke ciki kuma na had’a baki da wanda yakeda gidan hayarsu na maka masa kud’i yaje ya koresu, A dalilin haka babanta ya had’iyi zuciya ya rasu, Naso insa a saki Amrah amma kuma koda na samu labarin cewa wasu Indiyawa zasu taimaki marasa lafiya saina fasa duk dan na b’ata ran Ummimah da mahaifiyarta, Cikin ana shari’ar nan na tura an satomin wata a matsayin Barr. Sultana, kasantuwar basusan fuskarta ba yasa suka sato wadda ba ita ba, Yanzu haka Amrah da mai aikin gidan Barr. Sultana suna wurina amma ba tare suke ba, Amrah tana Malali quaters can bayan gari, Mai aikin kuma tana cikin k’auyukan Barhim. Kai cona ni Salmah, na cuci kaina na cuci rayuwata, nasan yanzu tawa ta k’are saboda dole kotu zata zartar da hukuncinta a kaina’ ta fashe da kuka sosai wanda duk wani mai imani dole sai ya tausaya mata dukda yake ita d’in ba abun tausayi bace.
Shiru ne ya biyo kotun kasantuwar kowa na al’ajabib hali irin na Gentle, ko a littattafan hausa ko fina finan hausa babu wanda ya tab’a zaton akwai mai hali irin na Gentle, Babu imani ko kad’an a tattare da ita. Wasu ‘yan sanda mutum biyu ne suka shigo kotu, bayansu Safiyya ce ta jigatu sosai sai kuma wasu ‘yan sandan mutum biyu a bayanta, Rigar bacci ce a jikinta ammajinajina take tsabar azabtuwa da tayi, Tayi ba’ki ta tame tamkar ba ita ba. Kallo kowa ya miyar garesu har suka k’ariso cikin kotun,
Kallon mutane take d’aya bayan d’aya har taci karo da Sultana daketa binta da kallon tausayi,
Rungumar juna sukayi cikin soyayya, sun jima a haka kafin Sultana ta janyeta daga jikinta
tare da samar mata wurin zana daga inda audience suke. “Mai shari’ah waccan daka gani itace mai aikin da nasa aka sacemin, gata nan ta dawo bansan dalili ba, bansan yanda akayi ta gudo ba” Gentle ce tayi wannan maganar cikin rud’ewa sosai tana k’arema ‘yan sandan kallo.
“K0 zaku mana bayanin abunda yake faruwa?” Alk’ali ya fad‘a bayan ya miyar da kallonshi ga ‘yan sandan, Kafin su bashi amsa wasu ‘yan sandan mutum hud‘u suka shigo, hannunsu janye da mutane duka maza mutum shida kowane da ankwa rataye a hannunshi. ‘Ku k’arisa shigowa dasu” wani d’aya ya fad’a daga Cikin wanda suka shigo tare da Safiyya.
‘Ya mai shari’ah mune ‘yan sandan da aka sakamu neman Safiyya tunda aka shigar da case d’in a station, mun jima muna nemanta sai yau Allah ya taimakemu muka sameta a can k’auyukan Barhim, wannan samarin kuwa munyi nasarar cafkesu a bayan gidan da suka b’oyeta”ne wani d’an sanda ne yayi wannan bayanin cikin natsuwa. Kafin alk’ali ya sake yin magana wani saurayi ya shigo,
Kallo d’aya na masa na tunoshi lallai shine saurayin Gentle wato Abdul Kadir AK,
Babu neman izini babu komai ya k’ariso daidai gaban Gentle,
“Ya mai shari’ah wannan yarinyar da kake gani muguwa ce, batada halin kirki ko kad’an,
Ashe duk bayan halayenta dana sani bansan tana yaudarata ba, wai ashe tare take da mahaifina abun kunya har mutane kowa ya sani, da zarar na fita sai a ringa bina da gori ana yimin zunde
Bayan kuma duk wasu mugayen halayena itace ta koyamin,
Itace ta sakani na fara yin kisan kai ga abokina kawai dan ya nunarda yana sonta, 
Tun daga lokacin dana gane tana tare da mahaifina na d’auki alwashin illata rayuwarta saidai duk abunda za’ayi amin, 
Na tabbatar da akwai hukuncin kisa akaina daga ni har ita, Dan haka dole sai kinji makamancin rad’ad’in da naji na tarayyarki da mahaifina” da sauri ya lalubi aljihunshi, Wata ‘yar kwalba ya zaro ya watsa mata ita a fuska sannan yayi murmushin mugunta ya mik’a hannunshi ga ‘yan sanda da nufin su d’aura masa ankwa. Ihu ta fasa da k’arfi na azabar da takeji, Hannunta tasa ta ringa dirzar fuskarwai a tunaninta ko hakan zaisa ta ragejin zafi, Tattalewa fatar fuskarta hau yi har tsokar dakejikin fuskar ana gani, 
Kamar mahaukaciya take ihu tana tsalle tsalle tana neman agaji. 
Mamanta cikin kuka ta taso ta rungumi ‘yarta, Banda kuka babu abunda takeyi, Ummimah dake tsaye gefe sosai ta tausayawa Gentle, koba komai tun yanzu ta fara girbar abunda ta shuka. 
Alk’ali kanshi jikinshi yayi sanyi, lallai al’amarin Allah babu wanda ya isa ya dakatar dashi, lokaci d’aya Allah ya bayyana gaskiya ya kawo k’arshen shari’ar. ‘Kafin kotu ta zartarda nata hukuncin, Salmah zata kwatanta inda suka ajiye Amrah azo da ita, dole sai anga lafiyarta sannan komai ya wakana, kotu ta bada izini ‘yan sanda su tafi suzo da ita sannan aci gaba, za’a tafi hutun awa biyu kam nan suma sun dawo, za’aci gaba da tsaron Salmah, AK da wanda aka kame har sanda zamu dawo daga hutu” ya buga gudumarsa sannan ya mik’e ya fice. Da sauri Mama kamar tana jira ta rugo ta rungumi ‘yarta Ummimah, Kukan farin ciki sukeyi sosai tare da hamdala ga Allah, Zarah da Rabiatu ma tasowa sukayi suka dawo gareta suna k’ara tayata murna dukda ba,a yanke hukunci ba har yanzu. Wani d’an sanda maras mutunci ne ya d’aurawa Gentle ankwa da k’onanniyar fuskarta data gama lalacewa lokaci d’aya kamar ba ita ba. Rik’eta mamanta tayi tam tak’i sakinta ita kuka Gentle kuka, ‘Ke dallah malama ja can, kina sonta ne kika k‘i bata tarbiyyar kirki? Gafaramin can kafin inyi k‘asa k’asa dake” yaja hab’ar rigar Gentle da k’arfi tare da fita da ita daga cikin kotun ya kaita d’akin tsaro. cikin kuka maman Gentle ta koma kusa da mijinta, 
‘Yanzu Alhaji duk kudi’inka kanaji kana gani zaka bari a Tafi da ‘yarmu cikin ankwa? Shikenan fa idan aka dawo daga hutu hukunci za,a yanke mata“ ta sake fashewa da wani kukan. 
‘Karki sakemin maganarta kinji na fad’a miki, taya inaji ina gani yarinya zata kunyatani a gaban jama’a? Kin manta da koni waye? Kin manta dani d’an siyasa ne sananne? Yanzu fa shikenan bama za’a fitar dani a primary election ba saboda ansan ko an bani ba zanci siyasa ba, nikam na yafe Salmah, na bama duniya ita babuni babu ita, kinji k’arshen maganata” ya hankada babbar rigarsa tare da ficewa, 
Masu take masa baya ne suka mara masu baya, Maman Gentle kuwa tace babu inda zata je dan yarta tafi a kai mata ‘yarta wani wuri. 
Barr. Sultana kuwa tana wurin Safiyya suna ganawa tana k’ara tausaya mata. ‘Bayan awa biyu’ 
A daidai wannan lokacin ne kotu ta sake cika kamar yanda aka tsara, ‘Yan sandan d’azu ne suka shigo tare da wata budurwa wadda shekarunta ba zasu wuce sha shida ba, K’ara murza idona nayi sai yanzu na gane ashe takwarata ce Amrah, Ta rame sosai ta k’ara tsayi kad’an, Duk farinta yanzu babushi, ta koma baka wulik ga kayanjikinta kamar an tonota daga rami, Gashin kanta kuwa tamkar mahaukaciya haka yake duk ya cukurkud’e. Cikin fari’n ciki Ummimah ta cafke ‘yar uwarta tana k’are mata kallo, Bata tab’a tunanin zata sake ganin Amrah ba, sai gashi yau Allah ya had’asu, Lallai Allah abin godiya, shi yake fitar da gaskiya daga k’arya, sannan yake tabbatar da ita ga mai ita. 
Tabbatarwar da alk’ali yayi cewa ita ce Amrah yasa ya gyara alk’alaminshi ya d’anyi rubutu kad’an sannan ya fara bayani… 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]